Littafan Hausa Novels

Tarihin Annabi Yusuf Fitowa ta 3 Complete

Tarihin Annabi Yusuf
Written by Hausa_Novels

Tarihin Annabi Yusuf Fitowa ta 3 Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tarihin Annabi Yusuf fitowa ta 3

 

Tarihin Annabi Yusuf alaihis salam da Darussan da ke Cikin sa Professor Mansur Sokoto, mni FITOWA TA UKU Annabi Yusuf alaihis salam Daga Kurkuku Zuwa Fada Annabi Yusuf alaihis salam ya samu kansa a kurkuku ba tare da wani laifi da ya yi ba illa kawai ya ki amincewa ya bi son zuciya ya saba ma Allah kamar yadda muka gani a baya.

 

 

 

 

Daga yanayin alakarsa da fursunoni abokan zamansa sai suka fahimci lallai akwai wata baiwa wadda Allah madaukakin Sarki ya yi masa ta ilimi. Domin kuwa yakan labarta masu daga cikin abubuwan da Allah yake yi masa wahayi yana yi masu wa’azi da kiran su zuwa ga kadaita Allah. Ta fuskar dabi’unsa kuwa nan take suka fahimci shi mai saukin hali ne ta yadda duk wanda ya kusance shi yana karbar sa hannu bi-biyu ba tare da nuna kyama ba.

 

Ramadan Day 1 To 30 Quotes

 

Ban da wannan kuma a kullum in za a kawo masu wani wani abinci yakan sanar da su kafin a kawo cewa, yau fa abinci iri kaza aka dafa maku. Da zarar an kawo kuwa sai su ga lallai shi din ne kamar yadda ya fada.

Tarihin Annabi Yusuf

 

Don haka suka hakikance lallai shi mutumin Allah ne wanda kusancinsa yake da amfani.

 

Daga cikin fursunoni abokan zaman sa akwai yaran Sarki guda biyu kuma hadimansa wadanda aka shigo da su gidan maza da zargin sun kulla wa Sarki sharri sun sanya masa guba da zimmar su kashe shi.

 

A bisa wannan tuhumar sai aka kai su gidan wakafi kafin a gama bincike a yanke hukunci. A wani dare kwaya daya sai su biyun suka yi mafarkai mabambanta.

 

 

 

 

 

 

 

Mai shayar da Sarki abin sha daga cikin su shi ya yi mafarkin ya koma bakin aikinsa har ma Sarki ya zauna kan karagarsa shi kuma ya zo da abin sha yana zuba masa.

 

 

 

 

Mai dafa masa abinci kuwa sai ya yi mafarkin ya dauko faranti cike da abinci a bisa kansa, tsuntsaye suna biyar sa suna cinyewa daga saman kansa.

 

Da aka wayi gari suka labarta ma junansu wannan labari sannan suka garzaya wajen Yusuf suna neman fassarar mafarkansu.

 

 

 

 

Annabi Yusuf alaihis salam take ya gane abinda mafarkan nasu suke ishara da shi. Amma sai ya fara masu da wasu bayanai masu muhimmancin gaske da suke bukatar sani fiye da fassarar mafarkin.

 

 

 

 

Ya ce masu, in kun lura duk lokacin da za a kawo maku abinci nikan sanar da ku abinda za a kawo maku tun kafin abincin ya iso. Suka ce masa haka ne.

 

Ya ce, to wannan wani ilimi ne da Ubangijina yake sanar da ni saboda ni, ina bin tafarkin Allah ne mahalicci ba ni hada shi da kowa a wajen bauta. Kuma shi wannan tafarkin na kadaita Allah shi ne mikakken tafarkin da iyaye da kakannina suka bi, cikin su har da Annabi Ibrahim da Annabi Ishaka da Annabi Ya’kub.

 

 

 

 

Dukan mu ba mu yi ma Allah abokin tarayya a wajen bauta. Wannan kuma wata falalar Allah ce a kan mu da kuma a kan sauran mutane (saboda muna kiran su zuwa ga wannan tafarkin tsira), amma da yawan mutane ba su da godiya (ga ni’imomin Allah).

 

 

 

 

Annabi Yusuf alaihis salam ya ci gaba da wa’azinsa a gare su yana cewa: Ya ku abokan zamana a kurkuku! Yanzu kuna ganin bautar gumaka barkatai ta fi zama daidai ko kuwa bautar Allah kadaitacce mai rinjaye? Su fa duk wadannan gumakan da kuke bauta ma ba wani abu ba ne illa kawai ababen da kuka ba su sunaye daga son ranku, ku da iyayenku, ba don akwai wata hujja da Allah ya saukar a kan haka ba. Shi kuwa hukunci na Allah ne.

 

 

 

 

ya kuma riga ya yi umurni kada a bauta ma kowa sai shi kadai. Wannan shi ne addini mikakke amma fa mafi yawan mutane ba su sani ba. Sannan sai Annabi Yusuf alaihis salam ya shiga fassara masu mafarkansu. Ya ce da na farkonsu, fassararka ita ce daidai abinda ka gani: an riga an kammala bincike kuma an wanke ka ba ka da laifi.

 

 

 

 

Don haka za a mayar da kai a bakin aikinka. Kai kuma “ cewa da na biyun “ bincike ya nuna kana da laifi kuma an yanke maka hukuncin kisa ta hanyar tsirewa. Don haka wadannan tsuntsaye da ka gani su ne wadanda za su rika fizgar naman kanka bayan an tsire ka a bainar jama’a. Wannan hukunci ya riga ya tabbata. Sai ku tashi zuwa sauraron sanarwa. Sannan ya kalli na farkon ya ce masa, idan ka koma wurin maigidanka ka ambace ni.

 

 

 

 

Yana nufin a sanar da Sarki cewa, yana nan tsare a bisa zalunci ko da Sarki zai tausaya ya sa ayi bincike a kan lamarinsa. Amma kuma da yake ba haka madaukakin Sarki ya tsara ba sai Shaidan ya mantar da wannan mutum bai yi zancen Yusuf ba sam a wurin Sarki har aka dauki tsawon shekara masu yawa.

 

 

 

 

A kwana a tashi watarana sai Sarki ya yi wani mafarki mai ban al’ajabi wanda ya ta da masa da hankali.

 

 

 

 

Ya ga wasu shanu ramammu guda bakwai suna cin wasu shanu bakwai masu kiba. Sannan ya ga wasu zangarkun abinci guda bakwai da wasu irin su cikakku guda bakwai. Sarki ya farka yana ta juyayin wannan mafarki. Da aka wayi gari sai ya tara manyan gari da mashawarta tare da wadanda ake ganin masu kaifin hankali ne da hangen nesa, ya labarta masu mafarkinsa da zimmar ya samu fassararsa.

 

 

 

 

Amma kuma dukansu babu wanda ya fahimci komai a cikin wannan mafarki saboda iliminsu bai kai ba.

 

 

 

 

A maimakon su ce masa ba su sani ba kai tsaye sai suka ce, ai wannan – ranka ya dade – yaye yayen mafarki ne kawai. Kuma dai mu ba ma’abota fassarar mafarki ba ne.

 

 

 

 

A nan ne fa tsohon fursunan nan mai shayar da Sarki ruwa ya ahamo da zancen Yusuf da ya baro shi a kurkuku.

 

Don haka sai ya kada baki ya ce ma Sarki a aike ni zuwa gidan maza akwai wanda zan nemo maku fassarar mafarkin nan a wurinsa.

 

Da ya je wurin Yusuf ya sanar da shi abinda yake tafe da shi Annabi Yusuf bai ce masa ya aka yi na daina jin duriyarka ba tun a wancan lokaci? Illa dai kawai ya fassara masa mafarkinsa, shi kuma ya juya ya koma wajen Sarki.

 

Fassarar da Annabi Yusuf alaihis salam ya yi masu ita ce, za a samu ruwan sama tare da ni’ima da wadatar abinci da amfanin gona har tsawon shekaru bakwai a kasar. Amma su yi kokari su yi kyakkyawan tanadin wannan abincin kada su cinye shi sai da gwargwadon lalura.

 

 

 

 

Bayan wadannan shekarun, wasu shekaru bakwai za su zo da za a samu fatarar abinci da lalacewar noma, to a wannan lokacin ne za su rika dibar abinda suka ajiye, shi ma da gwargwadon bukata.

 

 

 

 

Ya ce, bayan haka wata shekara za ta zo wadda komai zai tafi daidai; ayi noma a amfana kowa ya shana ya yi dariya.

 

Da Sarki ya ji wannan fassara sai ta kama hankalinsa sosai, ya auna ko ina ya ga fassarar ta tsayu, ga shi kuma tana nuna cikar ilimi da nasiha ga Sarki da al’ummarsa daga wanda ya ba da wannan fassara.

 

Don haka nan take sai ya ce, aje azo masa da shi. Da dan aiken Sarki ya zo sai Yusuf ya ce masa, koma wajen maigidanka ka ce masa ko ya san dalilin da ya sa nake a nan gidan wakafi? Kafin na karba kiran sa ina son ya yi bincike kan lamarin matar nan da aka zarge ni da ita ta hanyar matan nan da ta tara a gidanta wadanda suka yayyanka hannayensu a yayin da suka gan ni kuma suka mara mata baya akan abinda take nema na.

 

 

 

 

Abinda ya sa nake son ayi bincike shi ne, ina son maigidana ya tabbatar cewa, ni fa ban ha’ince shi ba. Kuma ai daman Allah ba ya sa nasara ga kaidin masu ha’inci. Ba wai ina son in wanke kaina ne ba. Ita daman rayuwa mai kawata ma mutum ya aikata laifi ce sai fa wanda Allah ya yi masa jinkai. Hakika, Ubangijina mai gafara ne mai jinkai. Jin haka, sai Sarki nan take ya sa aka kira taron manyan mata a fadarsa ya tambaye su gaskiyar abinda suka sani a cikin wannan lamari. Mata suka yi jawabai inda suk suka wanke Yusuf daga zargi.

 

 

 

 

Daga karshe ita kanta Zulaikha ta mike tana cewa, ya mai girma Sarki! Yau fa gaskiya ta riga ta yi halinta. Babu shakka ni ce da kaina na neme shi zuwa ga laifi kuma hakika shi ne mai gaskiya.

 

 

 

 

Bayan kammala wannan taro da fitar da sakamakon bincike sai Sarki ya sake aikawa aka zo masa da Yusuf yana cike da girma da daraja a idon Sarki.

 

 

 

 

Suka kebance suka tattauna batutuwa da dama da suka shafi kasar Masar ciki har da makomar tattalin arzikinta.

 

Sarki ya ba shi tabbacin shigar da shi a cikin majalisar zartaswa ta yadda ba za a sake yanke wata shawara da ta shafi al’amarin kasar ba sai a tare da shi.

 

A nan ne Annabi Yusuf alaihis salam ya ce, to idan kuwa haka ne, sai a ba ni jagorancin ma’aikatar tsara tattalin arziki da sarrafa shi (Finance, Budget and Planning) domin ina da ilimi da kwarewa ta fuskar adana da rikon amana ga duk abinda aka wakilta ni. Haka dai Allah “ cikin ikonsa “ ya daukaka Yusuf wanda ya zo a kasar Masar a matsayin bawa, aka sayar da shi a kasuwa domin aikace aikacen gida.

 

 

 

 

Allah ya ba shi wannan daukaka ne bayan ya ci wasu jarrabawoyi guda biyu masu wahala da suka hada da hakuri da kauce ma jin dadi na haram, da juriyar wahalar kurkuku saboda tsira da mutuncinsa.

 

 

 

 

Ga duniya ta yi kyau, lahira kuma mafi kyau tana can tana jiran sa. *Darussa:*

 

 

 

 

1. A ko ina ana samun na kirki. Annabi Yusuf alaihis salam yana a kurkuku “ gidan masu laifi “ amma sai shaida ake ta yi masa a kan gaskiya da kyautatawa.

 

2. Darajar ilimi: Sanin da Annabi Yusuf alaihis salam yake da shi a fassarar mafarki shi ne sila ta duk daukakar da ya samu.

 

3. Kyan halitta baiwa ce. Amma musibar da ya ja ma Annabi Yusuf tun farkon rayuwarsa da kuma a lokacin da yake matashi a gidan Firayiminista ta isa.

 

Ba domin kirkinsa da hakurinsa ba, da kyansa ne zai zama dalilin halakarsa.

 

4. Hakuri maganin zaman duniya. Jin dadin da Annabi Yusuf ya samu halastacce bayan ya jure wadancan wahalhalu, ba zai iya samun sa ba da ya ba da kai ga Zulaikha sun afka cikin barna.

 

5. Mai wa’azi yana da kyau a san shi da kyawawan dabi’u domin ya zamo abin koyi.

 

6. Mai wa’azi ba ya wasa da duk wata dama da ya samu.

 

Annabi Yusuf alaihis salam bai yi kasa a Guiwa ba a duk inda ya samu kansa yana karar da mutane da iliminsa da kiran su zuwa ga gaskiya.

 

7. Tauhidi shi ne ginshikin Da’awar Annabawa. Saboda babu tsira ga mutane matukar ba su kadaita Allah ba.

 

8. Butulcin dan Adam: Bai kamata ace mai shayar da Sarki ya manta da alherin Yusuf har tsawon shekaru ba.

 

9. Mutanen kirki ba su tona laifi, sukan ba shi baya. Annabi Yusuf alaihis salam bai waiwayi rokon da ya yi ma abokin zamansa a kurkuku ba lokacin da ya zo da bukatarsa.

 

10. Yunkurin kisan mai mulki ko anniyar hambarar da shi daga kan mulki manyan laifuka ne da ko ina a duniya suke cancantar hukuncin kisa.

 

11. Amfanin tsimi da tanadi: Bai kamata mutum ya rika ma sha’a cikin abinda Allah ya ba shi ba tare da la’akari da gobe ba. Abinda aka samu kamata ya yi, aci, ayi sadaka, sauran kuma ayi wa gobe tanadi.

 

12. Natsuwa da rashin gaggawa sukan kawo nasara a cikin kowane lamari. Jinkirin da Annabi Yusuf alaihis salam ya yi wajen karbar kiran Sarki har sai an yi bincike ya taimaka matuka wajen wanke shi daga zargi da daukaka darajarsa.

 

13. Jinkirin karba kiran Sarki har sai an yi bincike ya nuna duk shekarun da Annabi Yusuf alaihis salam ya yi a gidan maza bai sa ya fita daga hayyacinsa ya manta dalilin zaman sa a wurin ba ta yadda babbar burinsa zai zama kawai ya fita daga wahala. A maimakon haka, tunanensa na nan a kan tsaron mutuncinsa da kariyar girmansa a idon jama’a duk da yake ya san cewa, shi wankakke ne a wurin Allah.

 

14. Wani hani ga Allah baiwa ne. wani jinkiri alheri ne. Barin Yusuf har sai lokacin da Allah ya kaddari Sarki ya yi nasa mafarki shi kan sa wani tsari ne na Allah madaukakin Sarki.

 

15. Rundunonin Allah suna da yawa. Mafarki ma a cikin wannan tarihi runduna ce mai zaman kanta; da ita Allah madaukakin Sarki ya kai Yusuf ga kujerar mulki.

 

16. Mai gaskiya yana tare da Allah. Kuma komai dadewa gaskiya sai ta yi halinta, ta kunyata karya.

 

17. Babbar nasara da ci gaban kasa shi ne ta samu shugaba mai hangen nesa, mai neman shawara, mai karbar ta, mai nada mukamai bisa ga cancanta.

 

18. Ba laifi ba ne idan ka nemi ka wanke kanka daga zargi. Yin hakan ma yakan zama tilas idan aka shiga hakkenka kuma ka tabbata kana da gaskiyar da kake iya karewa.

 

19. Mai ilimi yakan iya bayyana kwarewarsa da cancantarsa ga mukami idan ya san zai iya ba mukamin hakkensa, kuma idan bukatar hakan ta kama. Kamar yadda Annabi Yusuf da kansa ya zabi ayi masa ministan tattalin arziki a wajen Sarkin Masar kuma har ya bayyana irin hazakar da Allah ya ba shi da amanarsa ga kiyaye kayan jama’a.

 

20. Jarrabawa iri biyu ce; akwai ta ni’ima wadda ake son mutum ya kauce ya yi hakuri saboda ni’imar ba ta halas ce ba. Akwai kuma ta wahala wadda takan fado ma mutum bisa ga kaddara sai a bukaci ya yi hakuri a kan ta.

 

21. Jarrabawa akwai wuya, amma cin nasarar ta akwai dadi.

 

22. Kada ka raina mutum, domin farkon mutum ba shi ne karshensa ba. Annabi Yusuf alaihis salam ya zo kasar Masar a matsayin bawa wanda aka saida a kasuwa, amma ya wayi gari daga cikin ministoci masu karfin iko da fada aji.

 

23. Allah shi ne masanin gaibi. Amma yakan sanar da bayinsa manzanni abinda ya ga dama.

 

24. Falalar Allah ce ga mutane da ya aiko Annabawa domin su karantar da Tauhidi ga jama’a su samu tsira.

 

25. Mai wa’azi yana da kyau ya rika amfani da hankali wajen lurar da jama’a su gane gaskiya. Kamar yadda Annabi Yusuf alaihis salam ya ce ma abokan zaman sa na kurkuku: Ya ku abokan zamana a kurkuku! Yanzu kuna ganin bautar gumaka barkatai ta fi zama daidai ko kuwa bautar Allah kadaitacce mai rinjaye? Su fa duk wadannan gumakan da kuke bauta ma ba wani abu ba ne illa kawai ababen da kuka ba su sunaye daga son ranku, ku da iyayenku, ba don akwai wata hujja da Allah ya saukar a kan haka ba.

 

Shi kuwa hukunci na Allah ne. ya kuma riga ya yi umurni kada a bauta ma kowa sai shi kadai. Wannan shi ne addini mikakke amma fa mafi yawan mutane ba su sani ba.

 

 

 

 

26. Masu fassara mafarki suna yi ne bisa dalili da hujja daga cikin mafarkin ba bisa son rai ba.

 

Annabi Yusuf ya fassara mafarkin hadiman Sarki ne daidai yadda mafarkin yake nunawa. Haka ma a mafarkin Sarki ya fassara zangarku cikakku da shekarun wadata sai ya hada su da shanu masu kiba saboda in aka samu wadatar noma ana samun lafiyayyun ababen kiyo.

 

 

 

 

Kuma ya fassara zangarku ramammu hade da shanu ramammu da shekarun fatara wadanda za su bukaci cin abinda wadancan shekarun suka tanada. Ita kuma shekara ta goma sha biyar da ya ce za aji dadi ya samu haka ne duba da cewa, mafarkin ya riga ya kare, wadannan shekaru bakwai na wahala sun zo karshe. Ita kuma daman wahala bayan ta sai jin dadi kamar yadda Allah ya ce: Hakika a tare da tsanani akwai sauki Suratus Sharh: 6

 

27. Ana son tawali’u a cikin zance. Cewar da Annabi Yusuf alaihis salam ya yi, ba wai ina son in wanke kaina ne ba, amma ina son maigidana ya san cewa, ni fa ban ha’ince shi ba. Wannan magana ta kai gaya ga tawali’u da kankan da kai irin na bayin Allah nagartattu.

 

28. Malami yakan yi la’akari da mai tambaya da yanayinsa da kuma bukatarsa. Babu laifi idan ya surka fatawa da wa’azi da lurarwa.

 

Misali, namijin da yake tambaya a kan halascin sakin aure, babu laifi a fadakar da shi game da muhimmancin rika iyali da yin hakuri da su kafin a fada masa cewa ya halalta ayi sakin in dalilin haka ya kama.

 

Muna fahimtar wannan daga tasarrufin Annabin Yusuf alaihis salam wajen yin fadakarwa a kan tauhidi kafin ya fassara ma fursunoni mafarkinsu musamman da yake dayansu zai bakunci lahira kuma ana bukatar ya cika a kan imani.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment