Littafan Hausa Novels

Tantiranci Hausa Novels Complete

Written by Hausa_Novels

Tantiranci Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Tantiranci Hausa Novels Complete

Page 1

 

 

*Alhamdulillah Alhamdulillah💃🏻 nagodema Allah daya bani ikwan dawowa ya bani damar kawo muku wannan labari nawa wato 💁🏻‍♀ TANTIRANCI KO KARUWANCI.* 🤫

*Yanayin me d’aukar hankali ne. Tafiyar abar dubawa ce. Karatun abin tunani ne. Ina san nayi amfani da Wannan damar wajen rokwan masoya littattafaina wato ƳAN MATA way’anda nayi musu ba dai-dai ba kan SAMAREEN BANAH part 2 da LEEKITAN ZUCHIYA dana hanesu karantawa. Toh ga dama tazo gareku. Zanso kubud’e kunnuwanku👂🏼 da ware idanuwanku👀 dan Wannan littafin mallakinku ne. Na sadaukar dashi ga duk BUDURWAR da zata karanta. Sannan Inayi muku fatan kukai qarshensa da lafiya. Kamar yanda kuke yimin addu’ar gamawa cikin nasara. Rahma nalele dai🤷🏻‍♀ takuce y’an hannuna. (Auntyn luv)*😍

 

 

 

 

 

Waige waige yakeyi acikin layin nasu. Sam bazai wacce shekaru ashirin da biyar ba. Yaro ne kyakkyawa ajin farko wanda kallo d’aya zaka mai kasan ya had’u tako ta’ina.

Ya tara abubuwa kamar haka..Tantiranci. Wayewar zamana. Ilimi. Iya wanka…

ABDUL D’AN KASADA kenan me karatu…

Abokansa ne suka sakamai wannan sunan ashekara biyu kad’al kuma ya bishi..

 

ABDUL ya rasa abubuwa uku arayuwarsa..

Ya rasa soyayyar Mahaifiyarsa da y’an uwansa.

Sam mahaifiyarsa Mama Saude bata qaunarsa arayuwarta. Bata da abun qi kamarsa a rayuwa.

Tunda ABDUL ya tashi bai tab’a ganin ranar daya zauna shida ita sukayi magana irinta uwa da d’a ba.

Kullum cikin cikin hantaransa take da nuna masa tsana. Kai baqin hali dai iri iri ba wanda ABDUL baya gani agun Mahaifiyar tasa..

Kaf cikin gidansu da unguwarsu ba wanda baisan da zaman qiyayyar da Mahaifiyar tasa take masa ba. Hatta abokansa suna mamakin irin tsanar da Mahaifiyar tasa take masa.

ABDUL yana da aboki AMEER.

AMEER layinsu d’aya da ABDUL

Saidai AMEER iyayansa masu kud’in gaske ne. Sam bazaka tab’a had’a gidansu AMEER danasu ABDUL ba.

Saboda gidansu ABDUL shine gidan talakawa na biyar acikin unguwar tasu.

 

AMEER tun tasowarsa arayuwa yake da rashin ji. Sam AMEER baya ganin kowa da gashi.

Ya rigada yayi suna wajen rashin mutunci..

Ga satan kud’in iyayensa da shaye shayen tsiya dabin mata kamar d’an akuya.

Sam bazakiso had’a Y’arki aure da AMEER ba..

Gashi su biyu kacal iyayensu suka Haifa shida qanwarsa Abida.

Suna sansu suna qaunarsu shiyasa yake amfani da Wannan damar yake iskancin dayaga dama..

 

Azahirin Gaskiya iyayensa suna matuƙar qoqari kan ya kintsu..

Dan basu san halaiyarsa kaf. Dan ko kad’an baiyiyo halinsu ba

Kasancewarsu nagari. Kawai sun yarda bata yanda Allah baya jarabtar bawansa.

Hakan yasa suke mai addu’a babu dare Babu ranah

 

Bambancin rashin jin AMEER da ABDUL abu biyu ne

Sam shi ABDUL baya bin mata baya aikata zina.. Sannan idan abinka zaikai shekara agaban ABDUL bazai tab’a d’aukar maka shi ba. Ma’ana anan baya sata baya aikata zina.

Saidai fa duk rashin mutuncin AMEER ABDUL yafishi. Dan shi idan yace yes baya dawowa yace no

Idan yace saiya aikata abu to Wallahi saiya aikata kodako abin nan zai kaisa ga caji office ne.

Sam ABDUL bashi da tsoro.

Halin Rayuwa Hausa Novel Complete

 

Gidansu ABDUL gidan yawa ne gidane irin gidan family house d’innan

Akwalla ba akasara ba yawan mutanan gidan zasukai su d’ari..

Gidan babban gida ne wanda yayi suna acikin unguwar. Suna kiran gidan da GIDAN YAWA. Saboda tsabar yawansu..

 

Alhaji Ali me katifa shike da mallakin gidan.

Yana da yara Ashirin da d’aya aduniya dukkansu maza.

Kuma kaf d’insu sunyi aure kuma agidan suke zaune da matansu da yaransu. Kasancewar gidan babban gida kowa idan yatashi auransa yankan wani shashi yake anan cikin gidan ya gina ya zauna da iyalinsa…

 

Mama Saude Ƴa ce ga qanwar Alhaji Ali yar autarsu. Amma ta rasu shekarun baya da suka wucce wajen haihuwan qanwar Mama Sauden wato ZAINAB.

 

Toh tunkan Mahaifiyar tata tarasu Alhaji Ali yake san Y’a mace kasancewar duk yaransa Ashirin da d’ayan nan duk maza ne.

Hakan yasa ya d’auki Saude tun tana qarama ya kawota gabansa wajen matarsa Hajjiya Ladi wacce kaf y’an gidan suke kiranta da Hajjiya Kakah.

Ita ta raineta har takai munzalin aure. sai alhaji Alin ya Aurar da ita ga d’ansa Shehu..

Shine suke zaune suma agidan har tasamu cikin ABDUL ta haifesa wanda tunda ta haifesa take nuna masa tsana dan qiri qiri qin shayar dashi tayi. Wai nononta nayi mata ciwo idan takai masa nonon bakinsa jitake kamar kan nononta zai gutsire.. Jin hakan sai Hajjiya Kakah ta d’auki ABDUL tashayar dashi da madara irin ta yara kamarsa awannan lokacin..

Kowa agidan Gani yake anya kuwa Saude itace ta haifi ABDUL.

Saboda sunga yanda take nuna mai tsana da tsangwama kala kala..

 

 

ABDUL ya tashi a nutse bashi da kwaramniya irin ta yara marasa ji..

Saidai daga lokacin dayakai shekara Ashirin da uku aduniya daga lokacin ABDUL yazama TANTIRIN d’an iska.. Ammafa injisu da fad’a😳 (saidai me karatu kagyara zama muji shin da gaske ne ko akwai sab’ani cikin maganar tasu)

 

Lokaci d’aya kuma ya juye yazama hakan.

Saboda tunda ABDUL ya gama karatu zai fara aiki a companyn abokin babansa wato mahaifi ga abokinsa AMEER kasancewar business ya karanta. shikenan fa kamai ya jagule ma ABDUL d’in alokacin..

An rasa tayaya meyasa hakan yajuye masa..

 

Bashi da abokanaye sai y’an iska. Y’an daba. Y’an shaye shaye masu jaye jayen magana.

Masu aikata lefuka TANTIRAI dai kawai.😳😳😳

Toh alokacin ne AMEER ya kulla abokantaka da ABDUL kuma ABDUL ya yarda..

 

 

Hajjiya Kakah tatara malamai kan suyi mata istahara ko Allah zai basu haske kan lamarin nasa.. Sai malaman suka bata tabbaci akan asiri akama ABDUL d’in kuma wallahi mugun asiri ne..

Makaryar asirin shine ranar da za’a d’aura ma ABDUL d’in aure.

Dazaran an d’aura masa Aure to ba makawa wannan asirin ya karye kenan..🤔

 

Tunda Hajjiya Kakah taji hakan hankalinta ya tashi dan tasan me dai hankali bazai tab’a d’aukar y’arsa yaba ABDUL ba.

Nan tashiga ba ABDUL magungunan tsari da karya sammu amma kamar bata basa dan ba abinda yake canjawa.

 

Saita fara kici kicin neman wacce tadace dashi a dangi..

Saidai kaf iyayen yaran da sunji za’a had’a y’ay’ansu Aure da ABDUL nan suke tsalle su dira suce su bazasu yarda a d’aurama yaransu aure da ABDUL ba..

Saboda sunyi duba da yanda TANTIRANCINSA yake qara habb’aka..

 

Lokacin da mahaifin ABDUL yaji wannan batu har kuka sanda yayi saboda baqin cikin abin da sukace..

Amma daga baya dayayi duba da irin tsanar da Saude Mahaifiyar ABDUL d’in da take masa saiya share komai… Dan Inda ace bata nuna tsana agaresa da zasuji kunyar fad’in hakan.

Danshi dai kaf cikin y’ay’an nasa bashi da abinso kamar ABDUL d’in.

Kullum cikin yimai addu’ar kintsuwa yake. Tare da yimai nasiha akan ya kintsu.

Saboda har sakin Saude yayi kan tsanar da takema ABDUL danta dena ta y’antar dashi kamar yanda ta y’antar da sauran yaranta amma taqi.. Haka dai Hajjiya Kakah ta bashi hak’uri ya maida ita d’akinsa awannan lokaci..

 

Sam Hajjiya Kakah bata dena nemama ABDUL maganin tsari ba. Haka addu’ar babu dare babu rana haka take mai kan Allah ya karya lamarin dan tasan tunda dangi suka hanata y’ay’ansu danta aurama ABDUL d’in tatabbatar bare dai bame bata y’arsa danta Aura masa asirin ya karye.

 

 

Tunda asirin ya kama ABDUL shikenan ya dena ganin mutuncin kowa agidan saina Hajjiya Kakah da mahaifinsa da qanwar mahaifiyarsa wato AUNTY ZAINAB…

 

AUNTY ZAINAB qanwace ga mama Saude idan me karatu ya koma baya kamar yanda na fad’a muku..

 

Mama Saude tana da shekara goma sha biyar aduniya aka mata aure.

Kuma tana shiga d’akin nata tasamu cikin ABDUL.

Lokacin data haifi ABDUL lokacin shekarun ZAINAB qanwarta biyar aduniya..

Dake ZAINAB itama Alhaji Ali ya dawo da ita gun Hajjiya Kakah saiya kasance tunda ZAINAB ta qilla ido🤪 taga ABDUL sai taji ba wanda take so kamarsa..

Bini bini tana naniqe da ABDUL..

Tun a lokacin kowa agidan ya fara mamakin qaunar da ZAINAB takema ABDUL..

Idan taga ABDUL na kuka nan itama zata hau kuka wiwi har sai Hajjiya Kakah tayi nasarar shawo kan kukan ABDUL d’in..

 

Toh wannan shine silar faruwar shaquwar ABDUL da ZAINAB AUNTYNSA..

 

Tunkan ABDUL yayi wayo yasan ZAINAB me qaunarsa ce..

 

ZAINAB bata iya san abu ba arayuwarta.. Dan idan tatashi san abu sanshi take gabaki d’aya kuma da gaske..

Haka kuma bata iya qin abu ba. Idan taqi abu taqishi kenan har abada..

 

ZAINAB tana matuqar jin tsanar Ƴar uwar tata mama Saude aranta..

Saboda qiyayyar da takema ABDUL shine dalilin dayasa itama take jin qiyayyarta aranta..

 

Hankalin ZAINAB yayi matuqar tashi dataji wani sirrin Y’ar uwar tata akan ABDUL.. Wannan yasa taqara qaunar ABDUL a ranta da qarin jin tsanar Y’ar uwar tata…

 

Tunda mama Saude tagane qanwar tata taji sirrin nata shikenan suka samu rashin jituwa..

Dama ita ZAINAB tanajin qiyayyar yayar tata akan tsanar dataga tana nunama ABDUL d’in

Saidai koda wasa bata tab’a nuna mata afuska ba..

Sanda taji wannan sirrin nata tukunna tadena ganinta da mutunci tafito da tsanar da take mata afili har kowa ya gane hakan

 

Mama Saude ranta na b’aqi da yanda ZAINAB d’in tadena ganin mutuncin nata.

Saidai ta share tunda ta gane barazanarta tayi tasiri akan ZAINAB d’in dan gaya mata tayi idan har tatona mata asirin nan nata kowa yaji ya sani wallahi saita kashe ABDUL kotawata hanya saidai itama a kasheta..

 

Jin hakan shiyasa ZAINAB rufa mata asirin saboda tatabbatar a irin qiyayyar da Sauden takema ABDUL d’in ba makawa zata kashe shin. Saidai ko a kashetan dan Wallahi zata aikata hakan kamar yanda tace..

 

Ita kuma tana qaunar ABDUL d’in dan duk wani abu dazai tab’a mata ABDUL d’in ya shiga damuwa ko ciwo ya kamasa ba sanshi take ba hakan ne yasata yin shuru da bakinta kawai tazubama sarautar Allah ido dan tasan dole Allah saiya tona mata asirin da bata san kowa yasani.

 

 

Hakan ya faru ne ana saura wata biyar Auran ZAINAB d’in

ZAINAB takamu da san wani Salisu d’an gaye haka. Yana santa sosai kasancewarta abin san kowane d’a namiji.

Danta kasance kyakkyawa ajin farko. Tatara duk wani abu da d’a namiji yake so ajikin mace..

Farace sul sul gwanin ban sha’awa

 

ABDUL yakan zauna yata kallanta lokacin yana qarami yace. Wai AUNTY ZAINAB dani dake wayafi wani kyau ne..

Murmushi kawai take yi dan shi ABDUL wankan tarwad’a ne bazaka kirasa fari ba kuma bazaka kirasa baqi ba.

Kalansa abinso. Ga fatarsa kogaggiya dan gaskiya mahaifinsa yayi qoqari sosai wajen ganin ya kyautata rayuwar ABDUL d’in..

Dan sam ABDUL ba abinda yake nema ya rasa agun mahaifin nasa.

Daga kayan sawa na wanka irin na yaran zamani. kud’in makaranta har d’an dai kud’in kashewa ba wanda ABDUL yayi missing arayuwarsa har yagama karatunsa yasamu nasarar amshe takaddarsa cikin nasara.

Gashi dai bawai suna dashi bane kawai wadatar zuci ne irin na mahaifin nasa da qaunar da yake masa..

Haka wajen Hajjiya Kakah bata yima ABDUL rowar duk wani abu nata naci da y’ay’anta suke bata..

Dan haka sam ABDUL bai tashi ta kwad’ayi irin na yara ba..

 

 

 

ZAINAB sanda ta Auri Salisu tagane tantirin d’an iska ne manemin mata d’an shaye shaye..

Tayi kuka tayi kuka lokacin data gane hakan

Saboda tasan bazata iya rayuwa babu shi ba.

Dan tana mai wani so ne wanda yafi qarfin akirasa da MASEEFAR SO

 

Baya dawowa gida sai qarfe goma sha d’aya ko sha biyu na dare..

Sannan abuge yake dawo mata..

Wani lokacin ya mata dukan tsiya idan tana masa fad’a kan yadena abunda yake yi. Sai yace wai tayi mai rashin kunya dan haka sai ya hauta da duka..

Idan washe gari tayi kuma saiya hau bata hak’uri

Ahaka zaita lallab’ata har ta hak’ura

 

Ahaka ahaka har tadena hak’uri. da zaran ya daketa sai tayo GIDAN YAWA.

Haka zai zo bikwanta idan yadawo hayyacinsa..

Sam Hajjiya Kakah bata bashi ita saita ciccimishi

Daga baya tagane idan tana mai fad’a ran ZAINAB d’in na b’aci. sai kawai tadena yimai

Idan ZAINAB d’in ta gudo cemata take tazauna idan yazo tafiya da ita tabishi ba saima tayi mata sallama ba..

 

Sarai ZAINAB tagane gatse tayi mata amma bata damuwa dazaran yazo ko tana d’an jamishi aji kad’an ya lallameta Saidai Hajjiya Kakah tanemeta ta rasa😂 tabi mijinta..

 

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*☆

 

{Fad’i alkairi ko kayi shuru)🤫

A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

 

 

 

” بسم الله الرحمن الرحيم

Page 2

 

 

Sam Salisu bai qare ZAINAB da komai na rayuwa ba.

Komai yanayi mata na rayuwa hakan ne yake sawa kaganta fes kamar wata y’ar tsana. Fatarta kullum agoge take. Tana dai jin dad’in rayuwa na kayan more rayuwa..

Matsalarta biyuce arayuwa. Na farko shine bin matan da mijin nata yakeyi da shaye shayen daya keyi. Na biyu shine rashin haihuwanta. Dan yanxu haka watanta tara da auren nasu amma uwar mijinta dake bata santa haka tabi tasata agaba wai bata haihuwa dan maseefa kamar shekara taran tayi ba wata tara ba..😊

 

 

___Wannan shine labarin ABDUL D’AN KASADA da mahaifiyarsa Mama Saude da AUNTYNSA ZAINAB da kakarsa Hajjiya Kakah.

 

 

*****************************

Andawo labari..

 

ABDUL na gama waige wai gensa ya fad’a gidan AUNTYN tasa ZAINAB kasancewar anan bayan layin nasu gidan nata yake sam gidanta baiyi nisa da gidan nasu ba..

 

Da sauri ya fad’a falan nata da sallama sam bata jishi ba. Sai hakan ya bashi damar b’oyewa cikin wani lungu anan cikin falan nata…

Gam gagam.. Zainab taji ana buga mata ƙofar falan nata kamar za’a b’alla.. Da mamaki tafito daga kitchen d’inta tana me yarfe hannu da qarema y’an sandan biyu kallo daga sama har qasa tace.. “Lafiya. meya faru..

Afusace d’aya daga cikinsu yace…”ABDUL D’AN KASADA mukazo nema.. “ABDUL.. Ta maimaita da mamaki. Kana taciga da cewa. Toh baizo nan ba.

“Kinga malama karki raina mana hankali. Dama ance kece kike b’oyesa anan gidan. To bari kiji idan kullum kin saba b’oyesa yau baki isa b’oyesa ba dan lefinsa me girma ne..

Wallahi sai mun shiga ko’ina lungu da sak’o nacikin gidan nan mun zak’ulo shi d’an iska Yaro kawai..

 

Dama na gaya muku arayuwar Zainab bata da abin so kamar ABDUL. Kuma duk yanda kuke da ita idan zakaci mutuncin ABDUL nan zata sab’a maka. Sun shaqu iya shaquwa ita dashi. Kowa yasan da wannan shaquwar dake tsakaninsu..

Dan haka nan take taji ranta ya b’aci da titsiyan da suka sakata agaba suna masu yi mata.. Dan haka cikin tab’e baki tace.. “Rainin hankali kuma na nawa. Ainad’e da raina muku hankali. Tunda nace muku baizo ba aisaiku ba wandanku iska ku qara gaba.

Wane ma rainin hankali ne wannan zaku shigomin gida ina matar Aure kanku tsaye batare da sallama na baku izini ba. Haka dukar takoya muku. To Wallahi baku isa ku shiga ko’ina acikin gidana kucajemin shi ba.

Tunda wanda kuke nema nagaya muku baizo nan d’in ba.

Baku da hurumin daza ku shigarmin gida ina matar Aure mijina baya nan kuhau cajemin shi haka siddan ba..

Dan haka saiku qara gaba tunkan na kulla muku wani sharrin dazaku rasa aikinku dan kunsan ba wanda yakai mace iya sharri. Bare ni kuma da nake matar aure wacce kuka fad’oma cikin gida kamar wasu dabbobi. Taqarashe zancan nata da turo d’an kwalinta gaba alamar duk rashin mutuncin da suke tafe dashi nata yafi nasu.. Dan tasha zuwa wajen y’an sanda ana artabu da ita akan ABDUL d’in.. Sam ZAINAB bata tsoran y’an sanda.

 

Da matuqar b’acin rai sukace mata haka tace.. Tace haka tace!!!

Rai b’ace suka ficce daga gidan suna masu cewa wallahi saidai in kwana zaiyi agidan amma indai zai fito suna nan suna jiransa akofar gidan nata..

Jan tsaki tayi da cewa.. “Aikin banza.. Tana fad’in hakan ta koma falanta da zama kan kujera mecin mutum biyu tana meci gaba da cewa.. Wato shi ABDUL bazai dena jawoma kansa magana ba ko. Wai har sai yaushe zai dena abubuwan nan ne..

Kai amma mama Saude tacuci rayuwarsa. D’aga hannunta sama tayi🤲🏻 daci gaba da cewa.

Ina rokwanka ALLAH dakayi gaggawar warware Wannan kullin. Kaifa kace muroqeka zaka biya mana buqatunmu. Gashi dare da rana aikina kenan wajan rokwanka kan way’annan al’amuran😭..

 

ABDUL d’in dake inda yake b’oye fittowa yayi da nufota yana cewa.. “Kici gaba dayi min addu’a MY AUNTY insha Allah zan zama yanda kike so.

Kallansa tayi a d’an tsorace dan bata san da gaske yazo gidan ba.. Taja numfashi da cewa. “Wai dama da gaske kashigo ne ban sani ba..

“Eh. Har nayi miki sallama naji shuru alamar kina kitchen.

“ABDUL kama kanka fad’a kadena aikata abubuwan nan dan Allah.

“AUNTY zan dena insha Allah..

“Toh yanxu gayamin meya faru suka biyoka. “Kawai AUNTY kishare. “Idan naqi sharewa fah. Wai har sai yaushe zaka gane raina na mugun b’aci idan naga ka aikata wani abu wanda akema kallan Allah wadai. Har sai yaushe zaka gane ina jin ciwo araina idan naga ankawo qararka ko anzo da niyar kamaka.

Kallanta ABDUL yayi cikin wani hali yace.. “Nasan kina jin b’acin ran dajin ciwo aranki MY AUNTY. Amma nima ina iya qoqarina wajen Ganin ban baki kunya ba. Kuma nasan kema kinsan da hakan..

Wata shegiyar harara ZAINAB ta galla masa da cewa.. “Wane qoqari kakeyi ABDUL. K’ok’arin ba’a cikakken sati sai anzo nemanka. Koko qoqarin qara qirqiran tantiranci.😡

Shuru yayi mata..

Ganin hakan sai yasata jan numfashi da tashi taje ta duba abincinta tadawo kamar zatayi kuka taci gaba da cewa.. Dan Allah Dan Annabi ABDUL kaji tausayina ni me qaunarka. Ka duba qaunar da nake maka kadena jawoma kanka magana..

Kawar da kallansa daga gareta yayi da cewa. “Toh.

“Yauwa ABDUL kokai fah.

Yanxu bani labarin me yasa suke nemanka..

“AUNTY kinsan bana gujema hukuma akan duk wani lefi da nasan bani na aikata ba.

“Kana nufin yanxuma kai ka aikata lefin kenan.

D’aga mata kai yayi akunyace..

Murmushin yaqe ZAINAB tayi dacigaba da cewa.. Toh ina jinka meya faru..

“Wani Alhaji ne yazo wucce wajen majalisarnu shine fa ya wani fitto yana zaginmu wai y’an iskan yara marasa tarbiya iyayenmu basu iya aihuwa ba. Tunda suka haifa y’an daba y’an wiwi way’anda basu san darajar na gaba dasu ba. Kawai AUNTY ki share dan yayi mana zagin cin mutunci. Kinsan kuma ni bazan iya jurewa ba. Musamman danaga ba abinda muka masa haka kawai ya fitto ya fara b’arar mana da kalamai.. Dan haka ina tashi na d’aga Addata da niyar sauke mai aka dan ya San dasuwa yake. Amma sai Allah ya temakesa ya kauce nasamesa a kafad’a. Yankan bai wani shigesa ba. Dan haka na qara d’aga sandar na sauke mai a damatsan hannunsa. Nanma naga bata shigesa ba. Saina qara d’agawa da niyar nayi mai me gabaki d’aya. Sai Allah ya temakesa abokan nawa sukace in barsa haka saboda yarigada ya sume MY AUNTY…

Shine fa muka tafi muka barsa agun… Toh da alama jama’a sun gammu ne shiyasa yanxu da muke kan hanya dan zuwa duba AMEER jami’an tsoran sukaso Ram damu. Sai kuma muka ankare dasu. Hakan yasa muka watse ni nayo nan

Jan numfashi ZAINAB tare da girgiza kanta hawaye ya zubo mata. Aduk duniya ba macen datake jin tsanarta kamar Yayarta Saude mahaifiyar ABDUL d’in..

Dan duk itace tajama ABDUL d’in wannan matsalar.

ABDUL da ko jini yagani ajikin mutum yana zuba hankalinsa tashi yake. Amma yanzu da kansa yake yankan mutum har yazo yana fad’a ba wani jin komai aransa..

 

AUNTY kidena kuka nasan amin da ciwo ace yau naka ya lalace.. AUNTY nima bansan ya akayi nazama haka ba. AUNTY ina tashi natsinci kaina cikin wannan bala’in. Kina dai gani duk da iskancina bana wasa da ibada.. Kuma rokwan Allah nake kan ya dawo dani daidai yanda nake da danutsuwa dan kawai naga farin cikinki… ABDUL yakai qershen zancen nasa da damuwa akan fuskarsa..

 

Goge fuskarta ZAINAB tayi dacewa.. “Nadena ABDUL, Kuma nasan duk abinda kakeyi badasan ranka kake ba.

Nasan kasan baka kyautawa.

Nidai fatana kadinga ragewa kadena kodan kaba maqiyanka kunya..

Akan idona kwanaki Hajjiya Kakah taso yimaka aure da yaran dangi amma fur iyayensu sukaqi saboda wannan halin da kake ciki. Kaga da ace kai nutsattsene ba iyayen da zasu qika. Saboda katara komai da ƴa mace take buqata agun d’a namiji…

 

Kallanta ABDUL yayi da tab’e baki yace.. “Itama Hajjiya Kakah da rikici. Banda haka miye nawani yimin aure ina qaramin Yaro haka, tukunna mah. Inkai matar ina.🤔

Kai wani aikin sai tsofaffi.

 

Ita dai ZAINAB shuru tamai. Danta fuskanci sam baisan meyake faruwa akan batun da ita tasani na yanda Hajjiya Kakah tagaya mata wai asirine yake d’awainiya dashi ba..

 

Tashi tayi taje ta sauke abincinta da zubomai tana mai cewa… “Kaga mutuniyarka nayi wato shinkafa da miya da salat…

“Aunty nifa bazanci ba!!! harsai kingaya min dalilin dayasa Hajjiya kaka taso yimin aure batare da sanina ba.. Kumama wai acikin dangi. Dangin da take da tabbacin basu sona.

“Haba ABDUL abinda nasani Shifa nagayama. Zanqi gaya maka wani batu ne wanda ya dace kasani… Ko kad’an bansan wani dalilinta ba..

“Nayarda saidai kinsan bana cin abincin gidanki.

” Yauwa meyasa baka san cin abincin gidana. Tunda aka kawoni daqer kakesan ruwan gidana.

“Kwantar da hankalinki bafa wani abu bane kawai naga mijin naki ne d’an rainin hankali ne. Saiya dingama mutane wani kallo haka haka. Kamar wani abu nake zuwa yimasa agida..

Wallahi kija masa kunne yadena yimin wannan d’an iskan kallan idan ya ganni dake.. Idan ba haka ba toh..

“Idan ba haka ba tome😳… ZAINAB tafad’i atsorace.. Dan bata san iskancin ABDUL d’in ya tab’a mijinta dan tasan sarai idan yace zaiyima mutum abu Wallahi saiyayi hankalinsa yake kwantawa…

“Idan ba haka ba wallahi zan yanke masa kunne d’aya..

Musamman idan ya qara dukanki shima saina nad’a masa na jaki Wallahi. Haka kawai Dan iskanci saiya dinga garoki gida cikin dare kamar wata taya…

“Ba garoni yake ba nice nake zuwa dan ganin damata. Wallahi Salisu bai tab’a cewa naje gidanmu.. Sannan dan Allah bani san katab’amin lafiyar miji. Dan wallahi idan naga kunansa a yanke narantse saina sab’a maka. Sai nayi maka abinda baka tab’a tunani ba.

Saboda kasan ina mutuwar san mijina.. ABDUL ina qaunar mijina kasan sarai ban iya so ba. Haka ban iya qin abu ba.

Karka aikatama mijina wani abun dazaisa naqika..

“Wallahi kozaki mutu idan ya aikata ba dai dai ba agabana saina mishi hukunci daidai da abunda yayi..

ZAINAB najin hakan tasaka kuka wiwi. Aiko yana ganin hakan yaci gaba da cewa kawai AUNTY ZAINAB ki matse. Najenye tunda kina san abinki. Amma wallahi kija masa kunne yadena yimin wannan kallan iskancin

Sauke ajiyar zuciya ZAINAB tayi da sakin murmushi tace. “Yau ce ranah tafarko danaga kafara sauke abu idan kad’auka da zafi. “Eh yanxun ma dan naga kukanki ne.. “To yanxu kabi ta k’ofar baya kaficce daga gidan nan tunkan suqara shigowa. Dan kasan yau asabar Salisu yana dawowa iyanxu yayi wanka ya yayi gidansu daga nan ya wucce yawan nasa na fama.

kuma kasan yana ganinsu zaune kofar gida ce musu zaiyi sushigo su caje gidan kasan tsoran y’an sanda yake ba d’an kad’an ba..

Tashi ABDUL yayi da murmushi yana cewa. “Sai AUNTYNA takaina.. Har abada bazan mance qaunar da kikemin ba. Insha Allah shekaru masu zuwa idan nadena wannan abubuwan nayi Aure sunan y’ata tafari AUNTY ZAINAB 😃..

Murmushi tayi da cewa “Allah ya kaimu lokacin ina maraba da zuwan little zainab.. Tana fad’in hakan ne tana bud’e masa wata k’ofarta tabaya wacce zata sadasa da layin nasu cikin sauqi basai yayi wani zagaye ba..

Ficce yayi yana tafiya irinta gogaggun tantirai d’innan.

Murmushi kawai tayi da kulle kofar tadawo falanta da soma cin abincin data zubomai tana zancen zuci dayi mai fatan alkairi arayuwarsa..

 

Can kuma saita fara tunanin karfa yayar tata tayi abinda tasaba yimai idan y’an sanda na nemansa..😳

Aiko nan tafara kallan agogo tana Allah Allah mijin nata ya dawo tayi gidan nasu…

 

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment