Littafan Hausa Novels

Sword Of Evil Love Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Sword Of Evil Love Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

SWORD OF EVIL LOVE

*#surayyahms repost series*

*#nice na makurar tsanarsa,snn nice nafara kashe wanda yake kauna a duniyarsa. Mezai faru idan ya zamo bani da wani abun muradi face shi?????*…..

 

 

 

 

*Page▶1⃣*

 

 

 

 

*17years foward……*

 

Daki ne wanda aka masa kwalliyar baby pink and white,Iska ne mai sanyi wanda ya gauraya da qamshin turarrukan jiki sai bada wani daddadr atmospher suke zaka ce alokacin ne ake fesa su.

Ruf da ciki tayi ta dan matso pillow kan kirjin ta sai zuba murmushi take da alamn tayi nisa cikin wani yanayin tunani,

 

A hankali kofar dakin ta budu ‘wata budurwa ce kyakkyawa wacca bazata wuce 16/17yrs ba fara sol da ita tayi tsayin daka bakin kofar tana murmushi itama hade da zaro madaidaitan idanunwa cikin sigar zolaya….

Sanye da white mini gown na kanti wanda ya kai dai dai gwuiwar ta

Ta nade suman kanta duka sama kamar chuku sai wutsil wutsil take da kafar tana murmushi ita kadai bata ma san akwai mutum a kanta ba

Mutum Ko Zaki Hausa Novel Complete

Saida ta kare mata kallo sannan tayi gyaran murya”uhm uhmm

Jasmine”

Jas.. Minnnnee.. takai hannu ta dan tsakure tal

 

 

Da sauri ta juya tace ‘Huh?innalilhh ..cewar jasmine wacce ta dan raxana ta mike zumbut

Hannu ta sa Tana famar kare qirjin ta “ohh my god haba salma .meyey hakan ? ta karashe maganan a shagwaban ce tana turo baki

Rufe baki salma tayi don dariyar data ci karfin ta amma ena sam ta kasa daurewa

Sosai ta gurfana kasa ta cigaba da zuba dariya abun ta…

“sai da tayi mai isar ta sannan ta juya ta kalle jasmine da ta riga ta kule ta sa fuskan kuka

‘ Ke haba da Allah,ni yaushe zaki dena wannan tsinannan tunanin ne iye? Kinsan tun yaushe na shigo dakin nan?

Yo’ don kin shigo shine zaki wani raAnar da ni salma?

Mikewa tsaye salma tayi ta ajiye bag din ta kan stool ta dawo gefen ta ta zauna” ok im sorry”shikenan?

Ni ba wannan ba ne na tambaye ki

Tunanin me kike ko ince tunanin wa kike ?

 

Hmmm what, Tunanin wa fa kikace ?

Allah ya kiyaye, kinsan wuce nan ..tafada tana zare ido tare da kau da kai

 

Dan tabe baki salma tayi tace” Tooo lallai fah, amsa ta ai ta fito

Ashe kuwa tunanin wanin kike tunda tambaya biyu na miki kika amsa min daya’

 

Dan juyi tayi alamn bata son zancen

Sannan tace ” ni wallhy salma kin ishe ni da maganan wanin nan

Ni kenan ba dama na

Zauna ina feeling kaina a daki na “Ah’ ah ,ni bance ba kiyi abun ki ..ai is part of relaxation ‘ sai kuma ta sake cewa “ummmmm jasmine,

 

Yes ‘ tafada a kasale

 

Naga kamar

Wani abun kike kallo ko ?ko kawai imagination na keyi

 

‘Dan duka takai mata suka kwashe da dariya duka biyu ‘ tana cewa wallhy na dauka wani abun zaki ce iskanci kawai…Dan hira sukayi sosai irin na kawaye da suka gama secondry schl .

 

Chan wajen karfe 5 da rabi na yamma suka fito daga site din granny (ammy) Anan suka gaishe ta tare da mata sallama,Sosai taji dadi dan haka dukkan su ta bisu da albarka

 

Granny Wacce duka suke kira da ammy’ ita kadai ce ma jazmine matsayin family uwa Da uba.

 

Wannan karon fitted gown na material brown jasmine ta saka tayi rolling da golden brown mayafi a hanyar su ta rakiya Suna tafiya suna ta surutu

 

Nan salma tace” Kawata ashe badaga nan ba

Kice yayan mu zai dawo shiyasa yau kaf na kasa gane miki,Dan murmushi tayi Ta kalli salma

Murya a sanyaye tace

“wani murna?

Daga ammy tace yaya zai dawo sai kuma kice ena murna?Wallhy kin raina ni salma

 

Hhhhh rufe min baki dai..uhm uhm fah?

What eva..jasmine ta fada tana rolling eyes dinta Toh en ma nayi murnan haramun ne yaya na ne fa? Cikin sigar masifa ta dan fada

 

‘Dariya salma tayi tace

Ai gaskiya ma zata fito

Auu, na manta kinga na fasa tafiya gidan nan ma mu koma kawai ..

 

Akan me?Jasmine tafada cikin mamaki tana kallon salma dake shirin juya wa da ita cikin gida

 

Ohh tambaya ta kike ?

Nima jiran yayan mu zanyi Kinsan fa am a die hard crush Wallhy ena mugun jin….

 

Heyy ya isa ”

Wtf! Jasmine ta karashe da tsuka mai sauti tare da dakatar da ita da hannu

 

Da kamr zata fashe da dariya sai tace

Meye kuma?

Ba dama mutum ya dan yi maganr yaya ash sai ki wani dakatr da shi

Yayan ki ba yaya na bane? Tafada da serious look

 

Mhmm I know salma”but can you just be serious for once Ta fada sounding seriouus itama

 

Ohh’ jasmine I am ,..Kinga ni fa ko aure yayan ki yace yanzuu im readyyyyyy..cewar ta harda tafi tana murna sosai kamr da gSke

 

Wani gum taji a kunnenta

a take ranta ya soma baci Sai tayi kokari ta danne abun cikin juya mata ido tace” Not in your wildest dream salma. My brother isnt for you or any oda girl.

 

Dan ja baya salma tayi tana kallon yadda jasmine ta daure fuska take maganan ba Alaman wasa Ohh god calm down girl ..meye haka jasmine

Daga wasa?

 

Jin haka yasa tayi saurin kau da yanayin fuskan nata da karamin murmushin dole

Don gaba daya abun yakan zo mata ne ba zata Ni ma wasa nake salma..lets go

 

Murmushin yake salman tayi Batace komai ba Suka cigaba da tafiyar su

 

Ki koma haka jasmine

Kar naja ji muyi ta tafiya an bar ammy ita kadai da shirye shirye

 

O’ oh

Ni ma binki zanyi ‘

 

Dan waro ido tayi tace ki bini ena jasmine ?

Nafada miki zan tsaya a shoping mall ko? And its late fah To 6.

 

Ni dai wallhy sai na biki

Toh wai ke ena

Ruwan ki dan ma na nace zan biki?

 

Hahaha muje toh

Princess jasmine yar gidan ammy na yayan ta shika dai.

 

Wani lumshe ido tayi ta sake murmushi mai wuyar fassara,Tayi shiru batace uffan ba Dariya kawai salma tayi ta bude mota

A kunyace itama ta zaga ta shige motar salma

Suka bar wajen

 

 

Dal ya kunna wutar gaban motar sa kirar rolce royce sport

P cap dinsa fara mai zanen tambarin arewa ta gaba wanda ya kusan rufe kyakkyawan halittar sa mai dauke numfashin duk abunda yayi tozali da shi, Jikin sa a gine take da kwarjini da hutu ba fari tas bane amma arabian milk mai dauke da madaidaicim lips wanda ya soma yin pitchy-pink

..suman kansa tamkar na jariri baka wuluk ce har tana neman kwanciya dakan ta ‘yayi masa saje luf luf a fuskan sa wacce ta sha gyara tubarkallah.

 

Sanye da designers polo shirt fara kat da bakar wando na companyn whitehorse los angeles, wato can na kasar america.

Haka ma katin sa dake gefe Alaman shi ma nada alaka da harkan wasan dokuna wato “polo” ASHWEEN A.R kenan wanda Aka fi ganewa da logo *ASH.R*

Yan mata masu bibiyan sa da abokan tarayya kowa yakan kira sa da ASH a takaice

 

Shiru yayi bayan ya rage volume din karatun qur’ani dayake ji yana dube dube dai dai setin kwanar shiga makaken mansion din su

 

Dan tabe baki yayi

Yace good for you”

 

Kaiwa nan ya buga horn ba tare da bata kokaci ba ya lume cikin wata hamshakiyar gida data ji komai da komai na duniya,Kai tsaye Wajen Jerin sport cars ya ajiye nasa sannan ya zaga baya ya dauko wata karamar gift bag guda biyu ya sa kai zuwa cikin gida

Bayan minti biyar mai aiki ta biyo sa da karamar trolley dinsa.

 

Ko da ya shiga gida bai wuce ko ena ba sai shashin sa

Tsaf ya kimtsa kansa ya sauya zuwa white jallabiya mai kyau..ya dan jeme kansa ya kame shi kadan abaya kamr na yan kwallo

Sannan ya kuma feshe kansa gaba daya da mild perf mai sanyin kamshi ya fito..

 

Zaune take rike da kofin shayi tana kallon adventure channel

Wani faffadan murmushi ne ta kufce masa kamr kullum

Don a duniya duk lokacin daya ganta hankali kwance farin ciki ne ke mamaye zuciyar sa na musamman

Bata hankara ba taji saukan bakin sa a gefen kuncin ta

Da murmushi ta damko sa tace'”alhmdullhi

Ka dawo kenan!

 

Yanzu nagama zancen ka araina dan albarka

Welcome home my prince..

Tafada tana mikewa tsaye cikin tsananin farin ciki tana taba fuskan sa

 

“Zo muje na baka abinci’ nasan ka gaji ko?

Ena Fata komai lpya dai , hwas ur journey? Dauke da Faffadan Murmushi kan fuskan ta tace

Tell me my boy ..’

Dariya ya fashe da shi sanda white teeth dinsa suka bayyana sannan ya zaunar da ita nan ya kwantar da kansa kafafun ta ya cigaba da yin dariyr sa hankali kwance

 

Hannu ta sa tana dan shafa kansa tana murmushi sosai tasan farin cikin ganin ta ke damun sa..can kuma sai salon dariyar sa ta soma canzawa nan take taji saukar hawayen sa

A nitse ta sunkuya saitin kansa ta kure sa da ido “awww

Ashween? Yau kuma ka dawo baby ne ‘wannan wani irin sakalci ne hakan? Kukan me zaka min

 

‘Ohh sakalci ma zakice ko ammy?cikin muryan shagwaba ya fada

Shima yana facing din ta..

 

Of cous my prince .to idan ba sakarci ba kato da kai old enough ka bani jika ka zauna kanamin kuka ‘ haba jarumi na ?

Ko nice nasa ka kukan?

Toh kayi hakuri ,afuwan,’

 

…shhhhh ammy

Ni bance ba..

 

To me ye ne? Tell me,tace tana duban sa

ko ya kula shikam

Dada lume kansA yayi kan cinyar ta idon sa alumshe a hankali yace

Stay ammy”

Kar ki taba rabuwa da ni kinji?Wallhy bazan iya ba in babu ke. ena ga Zan…zan…sai ya kasa karshewa muryan sa ya soma rawa.

 

Shiru ne ya ratsa wajen yayin da hjiya shahida (ammy)ta cigaba da sassaita sa tana shafa suman kansa a hankali ba tare da tace uffan ba

Itama daurewa tayi sosai din tasan meya ke nufi .

 

 

Sam ashween Baya so ya sake dandana zafin rashi me a rayuwar sa..

Ita kanta tasan ya shaku da ita shakuwa na ban mamaki,Don Ko da kudin da suka mallaka za’a bayar ace ba ita ta haife shi ba ba mai yarda da hakan

 

‘ Ashween ka tashi min nikam zaka karya min tsofafin kafafuwa ta ba fa makai na ajiye ba

WannN na Jikoki na ne..tayi maganan cikin wasa don ta kawar da yanayin su a lokacin

 

Kamr an tsakure shi ya mike zumbut Yace too in ba jikan fa?Ai har yanzu tenure na bai kare ba

 

Dan zungurin sa tayi tace

Come here..

Share wannan abun a fuskan ka And promise me bazKa sake min haukar da kamin yanzu ba,shiru yayi baice komai ba sai ma daure fuska dayake shirin Yi,Zaka goge ko nayi tafiya ta?Da sauri ya sa hannu kamr karamin yaro ya share hawayen san

Baice komai ba

 

Good ..muje ka ci abinci don tun tuni nake jiran ka

 

No ammy .na koshi

 

Meyasa? Kai

Bana son sakalci fa, kaji min iyeyi tashi muje inga guri

 

Zaman diris yayi ya make kafadun sa ”

Im not going untill u promise me nima,

 

ikon Allah,tace tayi tsaye tana kallon sa

Ehen go ahead ena jin ka

” juyawa yayi gwuwar sa na kasa yace ammy

Na amince bazan sake kuka ba in kika min alkwari bazaki barni ba har abada” Serious face din daya sa ne ya so ya bata dariya amma sai tace “Promise son”

Oya tashi muje

Allah shi zai bar wanda ya ga dama kar ka damu

 

Bai saKe cewa komai ba ya bi bayan ta

Suka nufi dininng

Cikin so da kulawa ta sa shi ya cinye abincin sa tas bisa kan tsari kafin suka dawo palour suna taba hirar su

 

Ammy, ena jasmine ne bangan ta ba tunda na shigo

 

Uhm well,, kawar ta tazo ne shyasa bazaka ganta ba.

 

Ok suna daki kenan?

 

No.

 

What. ?Cewar sa yan dan yamutsa fuska

 

Sun fita nace ..na dauka ai ka gansu don basu wani jima ba

 

‘haba ammy, amma kinsan na hana ta wannan yawon tsiyar ko to meyasa kika barta ?

 

Ahh kaji min dan nan,yo ita kenan kullum daki sai kace amarya? Da sannu na nace taje ,Kaga ni bana son dramn ku nan kar kuma ka taba min yarinya ehe

 

Shiru yayi baice uffan ba don ji yake kamr yayi iska

Ya tsamo ta daga duk inda taje yanzu

 

Har kusan 6’:15 pm

Suna zaune da ammy

Nan ya tashi ya tallafawa kakar nasu zuwa sashin ta ya kammala mata komai da komai kamr yadda kullum ya saba tun kafin ya tafi abroad ..

Sannan ya mata sai da safe ya sauko falo abunsa

Can abun bai masa ba ya tashi ya nufi massallaci daganan ya yi tsayuwar sa a farfajiyan gida”

 

Suman tsaye tayi tana kare masa kallo daga nesa yayin da suke shigowa Cikin motar salma data dawo da ita, Ita kan ta salma saida ta maida hankalin ta Don kuwa da ban wani abu ba sai ace wani aljanin suke gani

Ga hasken wutan ko ena tamkar rana haka wajen yake, Suman Kanshi sai sheki yake hannun sa dauke da tasaddaen classy phone dinsa yana latsawa

 

Dagowa yayi Kamr ya san ana kallon sa

Charaf suka had ido da salma da shike itace a driver seat Batan tama ta bude kofar ta sauko Jasmine na biye da ita dauke da gift bag na prada a hannun ta zuciyan ta sai dum dum yake kamar zai fita ta tsakure gefe shiru,

Fuska ba yabo ba fallasa

Yace susu?

Kece kika girma hakan

Salma da kunya ya rufe ta ,A sanyaye tace sannu da dawowa yaya ash

 

Thank you..ya gida ?fatana kuna lpya right?

 

Lpya lau Tace da dan karamin murmushi ,Ni zan wuce yaya sai da safe, Ok ..yace a takaice idon sa nakan jasmine da tuni ta sunkuyar da kanta

Daf da ita salma ta zo ke kuma me haka ? cikin rada tafada tana dan pinchin dinta a dabaran ce Wanda ya sata dada rudeWa ta riko hannun salma tare da dan

‘juyawa zata bita kuma

 

Jasmine!!!

Taji yace

 

Da sauri ta juya enda salman itama tayi saurin lumewa abun ta

 

Kamr bazata taka ba haka har ta iso daf

Da shi ta dan rusuna a ladabce tace “barka da dawowa yaya

ka dawo lpya? Shiru ya danyi sakamakon wani kira dayake shiga wayrsa

yayi ya sakeyi amma bai daga ba kuma bai kashe ba

 

Kamr baiji gaisuwan nata ba haka ya sa hankalin sa akan wayar sa

Sai can ba tare da ya kalleta ba yace”

“for whateva reason kar ki sake kaiwa wannan lokacin awaje kinaji na?

 

Gyada kai tayi murya ciki ciki tace Naji”.

 

Good ‘ tashi ki shiga.

 

Ba musu ta mike ta shige ciki da sauri

 

Kallon ta yakeyi har ta lume Zuciyan sa gauraye da wani irin yanayin da ya kasa fayyace

wakansa. Ganin ta kawai yaji nauyin dake kan kirjin sa ya sauka ,Ko ena a sasaan jikn sa yayi light bayajin komai Sai murmushin daya ke sakewa shika dai

 

Gefen jasmine

Kuwa tana shiga dakin gado ta haye

Da gudu ta fashe da wani irin kuka ‘ wayyo Allah na

Na shiga uku..

Wannan wani irin azaba ne nakeji a raina?

Lumshe idon ta tayi gam tana kawo lokacin daya barta tsugune ya maida hankalin sa kan wayr sa

 

To Wace ce wannan take kiran sa?

Meyasa take kirar sa..zir zir wani hawayen ya sauko mata

Tayi wirgi da pillown kasa”he’s mine tafada a raunane tana cigaba da sharban kukan ta’kamr ance mata dagasken mace ce ke kiran sa

Saida ta yi mai isarta sannan ta shige bath ta kimtsa kanta,Gaba daya mood dinta ya canza

Tunani kala kala take yi

Ita kadai ..nannauyan ajiyan zuciya tayi tace

“i missed yhu alot ka kara kywu da kwarjini

Ure d most perfct handsome guy ive eva seen so cute”amma yaya kamr baiyi missing dina ba, Salma kawai fa ya kula’har da cewa ta girma” ta karashe tana tabe baki, Shiru tayi kamr mai tunani can sai ta kashe lamp dinta ta ja bargo ta rufe kanta jim kadan bacii ya dauke ta.

THE SWORD OF EVIL LOVE BY SURAYYAHMS.

 

 

FOLLOW ME FOR MORE

SWORD OF EVIL LOVE

*#surayyahms repost series*

*#nice na makurar tsanarsa,snn nice nafara kashe wanda yake kauna a duniyarsa. Mezai faru idan ya zamo bani da wani abun muradi face shi?????*…..

 

 

*Page▶2⃣*

 

 

 

 

5.21am dot ya farka tare da addua abakin sa”la ilah illah wahdahu la sharika- la, lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai in qadir,subahallh ,walhamdullhi,wa laa’ilah illah wallahu akbar..rabbigfirnii ..sannan ya daura da bismillah ya sauko daga kan gadon sa

 

Bathrum ya nufa a cikin mintina 12 ya fito a gaggauce ya kimtsa ya nufi masjid’

Gefen ammy kuwa komai ta sanya anyi sa akan tsari musamman breakfast din su na ranar

Don kuwa ita da kanta ta hada masa wasu abubuwan

da shike shi ba mutum bane da ya cika son cin junks ..akasari ya fi ganewa natural flavours na tradional foods kamr vegetables ko fruits.

Don haka ko drinks din daka jera su awajen duka handmade ne bana kampani ko daya.

 

Wajen karfe 9 da rabi saura Video call suke yi yayin da jasmine din ke rike da setin dresses yakai kala hudu a hannun ta sannan ga wasu chan zube kan gado

‘fuska kalar tausayi tace

Haba salma

Munfi awa daya anan in banda tsokana ta ba abunda kikeyi

Pls now””ke ba dama mutum ya neme taimakon ki baki shiru?

 

Hannu biyu salma ta rike tana jan kunnen ta

‘Am sorry jasmine.ke fa wallhy wani lokacin baki san wasa ba

Ai na riga na fada miki kisa normal atampar ki zaifi kamar waccan ta mata nuni da wani chan wanda ta yasar gefe..dark green da ratsin ja

” ohk shikenan

Amma kin tabbata zanyi kyuw?

Oh my god jasmine ..ki sa toh na ganki yanzu..

Ba musu ta mike ta sanya skirt da rigar atmpr a dresing room sannan ta fito da sauri tanayi tana jan skirt din don ya mata das das yabi curve din jikin ta

” wow,

Kinga ni ,i told u wAnnan zaifi

U look terrific .waye ma tayi miki wannan dinki?

Dan murmushi tayi tace

Kathy anthony mana kin manta ne?

Ni wallhy hr wani kunya nakeji ta karshe maganr a shagwaban ce

Sannan suka kwashe da dariya

 

A hakan har suka rabu enda tayi maza ta kammla kwalliyar ta

ta shirya tsaf ta fito

Tayi kywu sosai duk da ma bata tula make up ba

Sai round cute face dinta ya dada bayyana dimples dinta dake gefe gefe..

Tun daga kan steps ammy ke kallon ta bAta hankara ba sai yauki take tana takowa

Tubarkallh masha Allah ammy ta fada a zuciyar ta tana dan mirmushi

 

Karasowar ta ke da wuya ta fada kan cinyar ta da gudu

“good morning again most gorgeous ammy in d world

 

Kokarin dagota ammy take amma sam sai narkewa take ajikin ta tana dariya ciki ciki

Zan ci kaniyar ki fa princess karya ni zakiyi ne

Nan ta dago tace

Wane ni?

Kinyo kyau ne sosai yau ”

Ta dan kashe mata ido

Murmushi kawai ammyn tayi ta ture ta gefe

Tana cewa

Bani son shirme bayan kin barni anan tun tuni kinata kwalliyar ki

Karfa kice min wani wajen zaki kinsan yayan ki baiso ko?

 

No” ammy ni bance zanje ko ena ba fa

 

Ok fine to, taso muje dinning bari na dubo sa

Dan tabe baki tayi

Sannan ta kalli wristwasch din ta

Karfe 10 da rabi?hmm lallai yaya na hutawa

Toh nima zan biki

 

Ah ah, ki tashi kije chan kijira ni dai ena zuwa ammy tace…amma ko ta kula

Nan ta soma chune fuskan ta tana maganan cikin kiriniya da shagwaba

Ammy kuwa ta biye mata ta fada ta sake na natawa amma sam taki jin ta

Suna Cikin haka wani sassanyar qamshi ya dosu su’ wayr sa ce makale a kunnen sa

 

A hankali yake magana fuskan sa dauke da wani annuri da annashuwa gaba dayan su saida suka juya suna kallon shigar tasa data masa bala’in kywu

Simple jumpa ya sa fara ta yadi shara shara

Hannun sa dauke da wata kafurar wristwatchh na hublot wacce hasken fatar sa ya dada sata yin baki ajikin sa ‘baisa hula ba don haka suman kansa suka zube kadan a bayan kunnen sa sai

sheki yake

Ko ya daga kai Yana magana yana dosu su”

‘ gefen ammy yayi ya daura mata light peg a gefen kuncin ta

Yana cewa” sai na ganki

And dont be late please

Sannan ya katse wayar

 

Ido hudo suka yi da shi lokacin gaba daya yanayin jikin ta ya sauya

Duk da asirtaccen murmushin daya jefa mata

Itako Wutar kishi ba karamin huruwa yake a ranta ba

‘ yanzu nake cewa zan duba ka

Kaga sai kaga nan ma

 

“yh,na tsaya waya ne ammy

U look great ..ya fada ma ammy amma idon sa nakan kallon jasmine

Ganin haka yasa ta dan dukawa kasa

A ladabce tace

Ena kwana yaya ?

Katashi lpya,,

 

Lpya lau..ya fada a takaice tare da mikewa tsye yana rike cikin sa

Ammy am so hungry.

 

Ahh Muje mana

Dama ai kai kawai nake jira ka fito

Princess shall we?

Nan hankalin ta ya dawo daga nisan tunanin bacin ran data ke ciki a lokacin

 

Ba tace uffan ba ta mike tabi bayan su

Sama sama ta ke cin abinci don kuwa tunda ya zauna kira ke faman shiga wayar sa

Gashi sam ta kasa tantance namiji ne ko mace ne

Idon ta fam ya cika da hawaye amma ta kasa sauko da su sai ma dura ma cikin ta ruwa data keyi

Sosai suke tadin su na kaka da jika mai kama da na đa da uwa ita da ashween suna ta dariya

 

Shirun da tayi ne ya sa shi kai kallon sa kanta

Shi dai sosai abin ke damun sa sai yaga kamar a takure take

Dan haka ma ya mike tsaye”yace ni zan fita ammy

Amma bazan dade ba zan dawo

 

Nooo way ,tace tana dan hararar sa

Zauna ai ba mu gama maganan mu ba

 

Wani sanyi jasmine taji aran ta da ammyn tace haka amma tayo xugum tana wasa da spoon

Toh ena jin ki ammy

 

First of all

To kai din ena zaka yanzu bayan nace ka huta na sati agidan nan

 

Zanje na siya abu ne kawai i need some toiletries ammy

 

Ok yayi’

 

Dama maganan waliman ka dana hada

Auntyn ku hajiya hadiza

Tun jiya take famr son taji ra’ayin ka amma kamin shiru ko kunyi waya ne

Dan jingina kai yayai da chair

Yace

Na kira ta da safe ammy

Amma gaisawa kawai k

Mukayi na sanar da ita na iso lpya

She called me tun ena japan har tai min addua

 

Dats nice tace atakaice..

Toh ya ake ciki

How do yhu want it kasan wannam duk dan kai zaa shirya sa ko?

 

Yes ammy

Ni ai bani da matsala ko yau ne ma am ready

Dan rau tayi da ido tace

Ready?

Uhm ,uhm

I want it to be a grand welcoming party

So ena son ka gayyace kowa da kowa naka

 

Dan murmushi yayi yace done .

Angama ammy ur wish is ma command

 

Kema haka princess cewar ammy tana maida kallon ta kan jasmine dake kai kawo a zuciyan ta

 

Ye..sss ammy tace a sanyaye

Nan ta mike tayi dakin ta sum sum

Kallo duka suka bita da shi ba wanda ya iya tanka mata

Yana dauke kai suka hada ido da ammy

Waccw ta sake dan karamin murmushin daya sa shi jin kunya

 

Na tafi nikam..

 

Zo nan…bangama ba

 

Ba musu ya juya yana kallon ta

Nace ba ..

Why dont yhu take your sis along

Ai sai itama amata toileteries din ko?

 

Ah’ a

Ammy ki bari ba yau ba ..zan kaita intana so yanzu am in a rush

 

Ok toh a dawo lpya tafada tana kokarin haurawa sama

 

Cikin Babbar motar sa ya shiga kirar matrix marron ya fice bai tsaya ko ena ba sai wani katafaren ma’aikata mai suna k and k agro-chemicals industy

Kai tsaye ya mike wata office ya kusa kansa ciki tare da sallama

A tsaye ya tarda shi yana jeka ka dawo cikin suite dinsa baka wanda tayi ma dark skin dinsa kywu sosai

My man”…suna hada ido ya fada suka kwashe da dariyA ya zago cikin sauri sukayi musabaha suka rungume

Juna

‘Welcome back bro..so dama da gaske kake yi?

Na dauka irin abun kan nan ne sa kasaba

 

Toh yanzu dai gani na taho so whats up’

 

Kalau am just glad Ka dawo dai finally

 

Yeah alhmdullhi ..abu kamar wasa yanzu dai

Kasan me ?

 

No sai ka fada

 

Wai welcome partyn nan da nake gaya maka aunty na ta na shirin hada min shine yanzun

Suka dago da magana

And yhu know akwai abubuwa agaban mu”

 

Dan shiru kamal yayi kamr mai nazari sannan yace

Tashi muje gida mu karasa achan

I have an idea..

 

Ba musu ya tashi suka nufi gidan su kamal din

..

Gefen ammy kuwa ta gama sanar da kusan duk friendly business patners din ta na ciki da waje don

Ta gama sawa a ranta ranar ne zata nuna ma ashween clients dinta ta kuma sake masa dukkan harkokin ta na business itama ta huta tunda tsufa ya kamata sosai

 

Zaune Cikiin wani tunanin akayo sallama

‘doctor?tafada tana mikewa da kyr

Ah zauna hajiya shahida

Ya jikin

Doctr sikirat lawal tafada

 

Toh jiki dai alhmdullhi doct tafada tana dan dube dube

Bayan sun kammla gaisuwa nan ma ta dan mata tambayoyi game da kanta kamr yadda suka saba..

Ammy tace

Yawwaa likita nace yanzu zamu dinga haduwa a office dinki kawai saboda yaro na ya dawo kasar nan gaba daya and you know very well ba na san su gane me nake ciki ko?

 

Haka ne ‘ajiya

Amma nidai har yansu ena shawartn ki da bayyana musu ko da mashi babban ne

Gudun kar wata rana wani abun yafaru unxpected.i think thy dersv to knw d truth

 

Ah’ a likita ,insha Allahu bazai faru ba ai ena kiyaye wa likita

Gaskiya bazan iya sanya ma yara na wannan dawainiyar ba .nasan su sarai zasu daura wani damuwa akan su ‘cikin ranta tace musamman ma shi babban da kike tunanin zai iya rike wa

 

Toh Muyi sauri kafin yaro na ya dawo yace bazai dade ba

Ba musu likita ta shiga mata kwaje kwaje

Sannan ta bata magani kamar yadda suka saba

Ita da kanta ta taimaka hajiya shahida har zuwa site dinta

Sannan ta samu ta kwnta

Jim kadan bacci mai nauyi ya kwashe ta..

 

Jasmine da ke dakin ta ba abunda suke kullwa illa yadda zasu fuskanci babban taron yaya ash dake gaban su

” komai sun fara tsara yadda zasuyi shi itada aminiyar ta salma kama daga spa, gyaran gashi..

Make up,dresses,shoes jeweries ..hatta gift saida suka tsara yadda zasuyi masa ranar

 

Misalin karfe takwas na daren ranar kamal ya soma broadcasting event dinsu a media

Yana tura iv ma family and friends musamman yan mata wato slay queens ke kokuwar samun wannan Ivn duk da ma wasun ta social media aka sanar da su,

Ko kafin yagama ajiye wayar sa ya amsa kirar mata sunfi akirga kowacce da salon ta na neman samun shiga hidiman

 

Karshe kashe wayar sa yayi ya dauko dayar wacce private ce ba kowa ya san shi da shi ba ya kira

” cikin murmushi mai kama da dariya yace “Ash akwai chwakakiya

Ladiea are on dis team 100%

Dan karamin tsuka yayi yace

Chan musu.

Just make sure kasan kalar da zasuyi matching da plans din mu dai

I want highly classical and unique girls

Kasan zahida ta wuce yadda kake tsammani ko?

Ni wallhy duk fargaba nake bansan ko tania zata iya ba gobe in munje

 

 

C’mon ash ,

Have faith mana,kamal yace’ komai zai zo mana cikin sauki

Ita zahidar sarauniyar ena ce ?

I dont think tania is less agaban wata ya mace kaima kasan ta hadu iya haduwa

 

Yh naji…Allah ya kaimu goben

Ya katse wayar sa

Juyawar da zaiyu sukayi ido hudu da jasmine wacce tuni ta tsane gefe daya fuskn ta a dan daure

Wani zazzafan ajiyan zuciya yayi a boye

Sannan ya mata hannu alamn ta karaso

Ba musu ta taho sum sum. Jiki a sanyaye hannun ta dauke da paranti

” haddaen french fries ne da egg souce wanda yaji nikakken namar kaza’

Gefe guda kuma glass jug ne

Mai dauke da fresh apple and cocunut juice

 

A gaban sa ta ajiye sannan ta juya zata bar wajen batare da tace uffan ba

Kauda kansa shima yayi

Ya cigaba da latsa waya

Sai da takai kusan rabi da tafiyar ta

Taji yace ” daki zaki kaimin Ba nan ba

Dum taji a ranta don kuwa tuni yanayin ta ya canza musamman intaji yayi maganar mace a waya

Dan tsayuwar minti 2 tayi ta nitsar da kanta sannan ta juyo tana dawo wa

” a dabaran ce yake kallon duk wani motsin ta wanda ke matukar burgesa amma sam bata sani ba

Shi ya fara gaba

Tana biyo sa ..enda wayar sa ta sake kara har sau biyu sannan ya dauka

” bae,yace cikin sanyin murya

Yana turo kofar dakin sa

Da dayan hannun

‘ cikin harzhen turanci suka gaisa

Sannan yace

Gidan mu zaki zo kuma?

Ahh nooo

Mudai hadu a enda na fada miki kinji

Dan shiru yayi kafin yace toh shikenan gudnite ya katse

Wayar

Hannun ta dake bari ya sata saurin dangwala abincin kan table

Tana kokarin boye hawayen dake sauka mata a hankali

Sai mutsi mutzi take bata so ta daga kanta don bata dauka zai kammala wayr da wuri haka ba

kuma tasan tabbas ta mike tsaye zai gane kuka take shirin yi

Shiru yayai yana lura da ita ya kuma kure ta da ido abunsa

Ji tayi an kargamu hannayen ta bazata zuwa gaban sa

A nitse ya kalleta har yanzu taki dagowa sai ma bugun da zuciyar ta ke yi

Jasmine? Meke damunki

Akwai matsala ne?

 

Gyda kai tayi da sauri batace uffan ba

Chak ya sake ta abunsa yace toh shikenan

U can go’

Da sauri ta juya da dan gudu xata fice

Ta fada kasa tayi wani tumbul tana murkususu tace wash

Inna lillhi tana rike da kafarta

Da sauri ya karaso ya dago ta

Yayi mata sannu

Sai jimamin kafar take don kuwa ta buga kan yatsr ta sosai bakin kofar

Saurin me kikeyi ne haka

Ya fada shima yana kai lallausan hannun sa kan yatsar

Ko da ya daura hannun sa yana duba mata hawayen ta datake boyewa ne suka tona mata asiri suka sauko akan hannun nasa

Tears?

Cewar sa cikn hanzari ya dago ya kalle ta da alamn tambaya a fuskn sa

‘ jasmine yanzu abun nan har yakai na kimasa kuka?

Ita dai shiru tayi sai ma dada bulbulo su take

Dan tabe baki yayi yace toh

Sannu ,Allah ya sawwke

Zaki iya tafiya?

A marairace ta dago murya ciki ciki tace ah’ ah .

Bai jira wani karin bayani ba ba ya daga ta

Ya zaunar da ita a gefe nan kusa da shi

‘ bari na duba miki to”

Sorry, yafada a takaice.ya bar ta anan a dakin, koda ya fice

Mikewa tayi garau ta sauke ajiyan zuciya tana kalle kalle dan tuni wajen ya sassauta zafin

Wani haddaden diary ta hango daf da inda ta ajiye abinci

Cikin azama ta miko hannu zata dauka charaf taji an bude kofar’

Da sauri ya kau da kansa

Itama haka don kunya ne ya soma damun ta tunanin ta karya dauka kwadayin abincin shi take

Bai nuna alamn komai ba,

Gaban ta ya tsuguna daf tana shakar daddar turaren sa wanda ke sata taji kamr ta lume a jikin sa har washe gari

Nan ya kamo kafar yana duddubawa

A hankali yake matsawa sai matse ido take

Don kuwa ciwon Baikai yadda ta tsawwala sa ba

 

Cikin kula ya mata first aid’ tayi nasha nasha kan gadon sa sai ruwan hawayen karya take

‘ koda baiso ya nuna tsananin damuwar sa ba sosai fuskan sa tadan bayyana cewa ya damu

” musamman ma kukan data keyi sosai yake hanasa sukuni a zuciyar sa

‘ruwa ya tsiyaya daga mini freezer mai sanyi

Yace gashi

Ba musu ta mike da kyr tanayi kammr bazata karba va

Karshe haka ya tallafa mata ya bata ruwan abaki ta sha

Parace tamol ya bare ya mika mata

Tuni ta soma ya mutsa fuska cikin shgwabar da ita kanta bata san tana aiyyanawa ba

” sosai abun ya mata kywu

Sai dai ya kauda kansa cikiin dabara yace oya take kinsan

Bana son sakarci ..tare da dan daure fuskan sa

 

Ko ajikin ta ,sai da yayi da gaske sannan

Da kyr ta sa abakin ta ta kara shan ruwa

 

Kafin ya hankara ji yayi ta hankade sa tayi bayi da gudu sai kakarin amai take

Don kuwa ko hadiye maganin batayi ba da sauri ta kunna kan tap akai tayi flushin dinsa da ruwa sai yarfe hannu take tana nishin karya,

” wani tashin hankali ya shiga

Yayin da ya karaso ya same ta tana kokarin sake kunna ruwa akan amai data kwawklu

 

Murya ba yabo ba fallasa yace Sorry” jeki kwanta zan karasa

Wani dadi ne ke ratsa ta yadda taga na kula ta don haka tayi kane kane kan gadon sa tana maida numfashin karya

 

‘ “tanajin murda kofaa ruf ta rufe idanun ta

Kamr wacce ke jin bacci

Shiru ne ya ratsa wajen

Daga bisani ya zauna gefen ta ya jawo abincin

” jasmine””ya kira ta amma sai tayi

Shiru abun ta saida

Ya sake cewa “jasmine

Kafin tadan motsa

C’mon Taso ki zauna

Yafada yana kure ta da ido

Cikin wani irin yanayin kasala da yauki ta tashi

Ta zauna

‘ ci abuncin sai kisha magani yace a takaice

‘ ah ‘ a

Na koshhhi..

Ko kula ta bai sake ba ya shiga debar abincin a spoon fuskan sa a daure ya kai bakin ta batare da yace uffan ba

” dadi daya gama lullube ta yasa nan take ta bude bakin sama sama ta soma amsa fuskan ta

Kamr zatayi kuka amma cikin zuciyar ta fall yake

 

Shiko baima san me takeyi ba inbanda tausayin ta daya kamasa sosai

 

Ahakan har ya kammla bata kusan rabin abinci sannan ya sake balla mata paracetamol ta sha

 

Ko da ta kammala ya sata gaba har zuwa dakin ta

Sai yauki take tana riirrike shi a dole wai bazata iya tafiya da kyu ba..

Kallo daya ya ma dakin nata sannan ya tallafa mata zuwa kan gado ta kwnta

Nan ma Ya ja mata blanket ya kashe wutar dakin abunsa ya juya zai fita

Siriyar muryan ta ne ya dakatar da shi

In da tace ” nagode yaya

Gudnite,

Murmushi kawai yayi bai juyo ba ya sa kai ya fuce kuma bai tanka ba

Tanajin motsin saukar sa kasa ta tayi wulli da bargon ta mike tsaye

Sai murna take tana dariya..THE SWORD OF EVIL LOVE BY SURAYYAHMS.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment