Littafan Hausa Novels

Sweet 22 Hausa Novel Complete

Auren Yarinta
Written by Hausa_Novels

Sweet 22 Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

SWEET 22

(Age is just a number)

 

 

 

Page 1

 

Mr Dattijo da Barr Hauwa mamansu daya babansu daya, Mr Dattijo shine babba, ya bata shekara goma cif cif, su biyu iyayensu suka haifa a duniya har Allah ya amshi rayuwar su….Mr Dattijo yana matukar son ‘kanwarsa kamar rayuwarsa, baya son abinda zai tabata, kuma ya yi alkawarin ba zai yi aure ba sai ‘kanwarsa ta yi

 

Abdul Ahmad amintaccen Mr Dattijo ne, shi yake kula masa da kamfaninsa dake ‘kasar America…..ganin hankali da natsuwa da gaskiya irin nasa yasa Mr Dattijo yasa shi ya nemi ‘kanwarsa Barr Hauwa, idan sun daidaita, sai ya yi musu aure…..ai kuwa cikin sa’a Abdul Ahmad da Barr Hauwa suka daidaita junansu, soyayya mai matukar ‘karfi ya shiga tsakaninsu…..bayan ta kammala karatun degreen ta na biyu aka daura aure

Gamon Jini Hausa Novel Complete

Amarya da ango sun tare a America, wata goma Na cika Allah ya albarkacesu da ‘ya mace da ta ci suna YESMIN, bayan haihuwar YESMIN da shekara biyu Allah ya Kara azurtasu da yaro namiji, Suka yi ma Mr Dattijo takwara wato Abdullahi, sunansa Na gaskiya kenan amma ana kiransa da Junior, haihuwar Junior da shekara daya da watanni Mr Dattijo ya yi aure, matarsa mai suna AISHA ‘yar asalin garin Gombe

 

Haj Aisha matar Mr Dattijo ta samu ciki Amma cikin yazo da gardama, tun daga farkon shigar ciki tai bankwana da lafiya, suka tattara suka koma Asibity da zama, kullum cikin suma da tashin hankali take, dakyar ta iya rike cikin zuwa wata bakwai Sannan aka mata aiki aka ciro yaro namiji, babu bata lokaci aka sashi cikin kwalba, kwararru suka cigaba da kula dashi har ya yi ‘kwari….. yaro ya ci suna ADNAN, tun daga wannan lokacin Haj Aisha bata kara daukar ciki ba kuma ta dauki son duniya ta dorawa dan ta daya tilo wato ADNAN

Adnan na da watanni biyar a duniya Barr Hauwa ta sake sullubo da ‘yarta mace, wacce ta kasance auta, ta ci suna Mufeedat….A wannan lokacin Yesmin shekarunta biyar a duniya

Haka rayuwa ya cigaba da tafiya har tsawon shekara biyar, a wannan lokacin Yesmin ta cika shekara goma a duniya kuma dai dai da kammala karatun primary

 

Barr Hauwa ta roki Abban Yesmin daya amince Yesmin ta dawo Nigeria gidansu Mr Dattijo domin yin karatun matakin secondary dana islamiyya kuma domin ta koyi al’adunmu Na gida Nigeria, musamman ma na Arewa….Abban Yesmin ya amince da ‘kudirinta dari bisa dari

 

Haka kuwa ya kasance, Yesmin ta dawo Nigeria gidansu Mr Dattijo da zama dake birnin Abuja, ta fara karatun secondary a makarantar da yafi kowanne tsada, hakama Islamia, Alh Dattijo Na kula da ita hakama matarshi Haj Aisha…….A wannan lokacin Adnan shekarunsa biyar da watanni

 

Haka rayuwa ya cigaba da tafiya har tsawon shekaru biyar, a yanzu Yesmin shekarunta goma sha biyar kuma matakin ‘karshe take a secondary……Adnan kuwa shekarunsa goma da watanni, yanzu ya fara karatunsa Na secondary

Adnan ya tashi cikin gata da jin dadi, yaro ne mai matukar zuciya kuma mara jin magana, hakan yasa basa shiri da Yesmin, ita Yesmin tana son ya rinka kiranta da Aunty Yesmin, shi kuma a kullum nuna mata yake bata isa ba ya kirata Aunty, sai dai ta duke shi, kuma duk abinda zata yi masa baya kuka, hakan na matukar bakanta mata rai

 

****

Matasan soldiers da basu wuce shekaru ashirin da biyar ba tsaye jikin wani bakar mota, a harabar makarantar su Yesmin…….daga nesa Yesmin ce da Areef suke takowa a hankali cikin uniform, rike suke da Jakar makaranta, kana ganinsu kasan masoyane

 

Areef yaron wani babban soja ne, ajinsu daya da Yesmin, shekara uku kenan da suke soyayya

Suka ‘karaso suka tsaya daga gefen motar suna tattaunawa

 

“Baby you mean immediately the exam you are going to America?”

 

“Yes and I don’t know when I’m coming back”

 

Areef ya yi shuru yana tunani, can ya ce honestly we are going together, ba zan iya cigaba da zama a Nigeria ba, batare dake ba

 

“Are you serious”

 

“Yes, I am, ko bakya farin ciki da hakan?”

 

“I’m so excited, zan yi farin ciki ka dawo America, ka ga sai mu cigaba da karatunmu a can ko?”

 

“Yes, yanzu Ina komawa gida zan fadawa Daddyna”

 

Hankalinsu ne ya koma wurin Adnan daya karaso rai a ‘bace, Yesmin Na ganinshi ta hade rai tana fadin “me ka zo yi?”

 

Budan bakin Adnan ya ce ke Yesmin din nan kin wani shanyamu tuntuni saboda wannan (ya nuna Areef)

Areef ya ce wai Kai Adnan meyasa baka da kunya?

A fusace Adnan ya watsawa Areef wani mugun kallo sannan ya ce baka koya min ba

 

Cikin fushi Yesmin ta ce Adnan waye sa’anka a nan?

Adnan fuskar nan a tumke ya ce ni kawai kizo mu tafi

 

Areef ya ce to babu Inda zata tafi saina bata izini ka ji ka

 

Budan bakin Adnan ya ce what the bull shit, fuck you

 

Areef ya ce the hell of you (sannan ya kalli sodojin da suka zo daukarshi ya ce musu) ku yi min maganin wannan yaron

 

A take sodojin suka rike Adnan suna tallabe masa keya, sosai Yesmin ta ji zafi a ranta, kallon Areef tai ta ce miye haka? Is my brother, komai zai yi bai kamata ka yi masa wani abu ba, kuma ai yarone

 

Areef yai ‘karamin tsaki sannan ya ce sorry baby, ya ‘bata min rai ne…. ya kalli sodojin da suke kokarin sa Adnan tsallan kwado, amma yaki yi saboda tsananin taurin kai…. ya ce musu “ku kyaleshi” a take suka yi umarni da abinda ya ce

 

Adnan juyowa ya yi yana kallan Areef da idanuwansa da suka yi ja, sai ya nuna sa da dan yatsa ya ce you, hmmmmm! Sannan ya fice

 

Yesmin ta kalli Areef ta ce bari Na wuce mu yi magana ta waya

 

Areef ya ce okay

 

Yesmin ta wuce, Areef ya shiga mota gidan baya, sodojin suka shiga gidan gaba

 

****

Babu magana Adnan ya ‘karaso inda motar da aka zo daukarsu yake fake, ya bude ya shiga ya zauna yana ajiyar zuciya……Can sai ga Yesmin ta bude motar ta shigo ta zauna ta kalli Adnan tana fadin “ba kai baka da kunya ba, dana bari sunyi maganinka”

Kallonta ya yi ya ce Yesmin, babu abinda suka isa su yi min, kuma sai Na rama

 

Kama kunnansa tai ta murda da karfi “Adnan sai Na ci mutuncinka indai ba zaka daina kirana da Yesmin ba, ko ni sa’arka ce? Shekara biyar Na baka, ba wata biyar ba”

 

Kwace kunnansa ya yi da karfi yana fadin “leave my ear”

 

Dai dai lokacin direbansu ya shigo ya ja motan suka tafi, sai rikici suke yi a hanya

 

Bayan sun karaso gida Adnan ‘bangaren Mahaifiyarsa ya wuce Haj Aisha, ya sameta tare da Daddynshi Mr Dattijo, suna ganinsa sun San akwai damuwa a tattare dashi

 

Haj Aisha ta ‘karaso da sauri ta rike hannayensa tana fadin My Adnan meya faru ne?

 

Kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce Mummy I wanna be a military man in future

 

Mr Dattijo ya kalli Adnan da sauri ya ce meya birgeka da aikin soja? Just forget it ba za ka yi aikin soja ba my boy

 

Adnan ya ce Daddy i already made my mind, soja zan zama

 

Haj Aisha ta kalli Mr Dattijo ta ce ba zamu takura masa ba, abinda yake so shi zai yi

 

Mr Dattijo ya ce eh hakane, amma shi kadai gareni, shi zai gajeni kuma shi nake so ya cigaba da gudanar da kamfaninina

 

Haj Aisha ta ce ba wani damuwa bane ai, zai kasance yana aikin soja kuma yana gudanar da kamfanoni yadda ya kamata

 

Mr Dattijo ya ce to Allah yasa hakan shi yafi zama alkairi

 

“Ameen thumma ameen, bari Na je na watsa masa ruwa”

 

“Ok”

 

Haj Aisha ta ja hannun Adnan zuwa dakinta, ta tube masa Kayan makaranta sannan suka shiga bayi, tana cikin yi masa wanka Yesmin ta shigo bayin tana magana “Mummy sannu da gida”

Haj Aisha ta ce yauwa Yesmin, ya makaranta?

 

“Lafiya lau Mum”

 

Yesmin ta kalli Adnan ta ce ko kunya, har yanzu baka iya wanka da kanka ba

 

Adnan ya kalleta ya ce Ina ruwanki

 

Haj Aisha ta ce Yesmin ki dinga kama girman ki kada Adnan ya rainaki

 

Yesmin ta ce to sannan ta fito daga bayin tazo ta zauna kan gadon bedroom tana lallatsa wayarta

 

Can Haj Aisha da Adnan suka fito, Adnan Na goge jikinsa da tawul

Kiran Haj Aisha aka yi a waya, kallon Yesmin tai ta ce ki shafa masa mai, ni zan amsa waya

 

Haj Aisha ta amsa wayar ta fita daga dakin, Yesmin ta ce Sai ka dakko mai Na shafa maka

 

Adnan ya hade rai ya ce bana so

 

Yesmin ta hade rai itama ta ce ni sa’arka ce, ko so kake sai Na tashi Na kamoka

 

“Ni bana so, dole ne sai kin shafa min mai”

 

Mikewa Yesmin tai ta je ta samu kanshi ta bashi rankwashi masu zafi guda uku sannan ta ce sai Na yi maganinka a gidan nan wallahi…..tana gama fadan haka ta fice ya bita da kallo cikin ‘bacin rai

 

Haka rayuwa ya cigaba da tafiya, bayan Yesmin ta yi jarabawan WAEC ta koma America wajen iyayenta, bada dadewa ba Areef ya biyota suka cigaba da karatunsu, ita Yesmin tana karantan computer science, shi kuma Areef Na karanta Chemical engineering

 

Cikin ‘kankanin lokaci suka kammala degree dinsu Na farko suka dora da masters, yanzu PHD suke yi, Yesmin shekarunta yanzu Ashirin da biyar, Areef Na Ashirin da shida

 

Ta ‘bangaren Adnan kuwa yanzu shekarunsa Ashirin cif cif, yana thermal 4 a Nigeria defense academy, cikin rundunar Mogadishu (Mogadishu battalion) yana karatun B.sc hydro biology

 

A lokacin da Yesmin ta kammala P.hd dinta, a wannan lokacin Adnan ya kamalla program dinsa a NDA sannan ya tafi portacourt domin yin course dinsa na zama cikakken sojan ruwa, wato “Navy”

 

****

Areef ninke kayayyakinsa yake yi yana jerawa a cikin akwatina

Yesmin ta shigo, ganin yana hada kayayyakinsa yasa ta je ta rikeshi ta baya tana ajiyar zuciya, wasu hawaye suka fara fita daga idanunta

Tsayawa Areef ya yi cak, zuciyarsa Na yi masa zafi, juyowa ya yi yana fuskantarta

 

“Baby why are you crying? Bafa mutuwa zan yi ba”

 

Yasa hannu yana share hawayen fuskarta

 

Ta ce yanzu idan ka tafi dawa zaka barni?

 

“Nima bana son tafiya, Daddy ne ya takura min Na dawo, sannan komawar Na da amfani, kin ga zan samu Na zauna da Daddyna Na yi masa maganarki, kin ga sai a fara maganar auranmu, ko baki so ki haifa min yara masu kama dake ne?

 

Sai yanzu Yesmin tai murmushi sannan ta ce Ina so mana

 

Ya ce good, kinga Ina komawa Nigeria zan yi wa Daddy maganarki

 

“Kasan miye?”

 

“A’a sai kin fada”

 

“Kana komawa zan biyoka, nafi son ayi shagalin bikinmu a Nigeria”

 

“Nima nafi son haka, yanzu ki kwantar da hankalinki kin ji, yi murmushi mu gani”

 

Wani murmushi ya baiyana a fuskar Yesmin, a take Areef ya manna mata kiss a goshi kamar yadda ya saba a koda yaushe, iya kacinshi ya sumbaceta a goshinta, bai taba wuce nan ba, ‘kara rungumeshi ta yi tana fadin zan yi kewarka

 

Areef ya ce nima zan yi kewarki sosai, ki kula min da kanki please

“Zan kula maka da kaina, nima ka yi alkawari zaka kula min da kanka”

“Ai dole ma Na kula miki da kaina, babban addu’arta nidai Na ga ranar auren mu, Na ganki a dakina, bansan wani irin farin ciki zan yi ba”

 

Yesmin ta ce nima wannan ranar kawai nake jira, Allah ubangiji ya kaimu…….haka suka cigaba da nishadantar da junansu, daga ‘karshe Areef ya gama hada kayayyakinsa Yesmin tai masa rakiya har airport, sai da jirginsu ya tashi sannan tabar airport din

 

****

Dawowan Areef da watanni mahaifinsa ya sama masa aiki a babban masana’anta sannan ya yi masa alkawarin zai samu lokaci ya je ya ga Mr Dattijo domin a fara maganar auransa da Yesmin

 

Adnan ya kammala course dinsa, an yi shagalin bikin passing out dinsa an gama, yanzu ya zama Officer Adnan Dattijo, cikin sa’a anyi posting dinsa a garin Abuja kusa da gida, an bashi apartment a bariki amma baya kwana, yana tashi office gida yake dawowa

 

****

Yau asabar babu aiki, Adnan na gida

Haj Aisha sai zirga zirga take yi a kitchen saboda Yesmin Na kan hanyar shigowa Nigeria…..ta kammala duk wani ayyukan daya kamata, ‘kwalawa Adnan kira ta shiga yi, ji kake ana Adnan! Adnan! Adnan

 

Can sai ga Adnan ya ‘karaso da waya manne a kunnansa, da alamu waya yake yi, Katse wayar ya yi yana kallanta gami da cewa “Na’am Mummy”

 

“Ka shirya zuwa airport yanzu, in the next 30mins Jirginsu Auntynka Yesmin zai sauka”

 

Kamar ya ce ba zai je ba, sai wani zuciyar ta ce dashi ya je kawai

 

‘Bangarensa ya wuce ya sauya kayan jikinsa zuwa manyan kaya, farar gyazna tasss, ya yi matukar kyau a cikin kayan sosai

Adnan matashi Dan shekara ashirin da biyu dogo ne sosai mai fadin‘kirji da cikakken structure Na da namiji, bakar fatane dashi, idanunsa ba manya ba kuma ba kananu bane sosai sannan ba farare bane, hancinsa ba wani dogo bane sosai, dan dai dai ne, hakama bakinsa dai dai fuskarsa, Adnan ya Kai namiji har namiji da kowacce mace zata so ya kasance mijinta

 

Daukar wayoyinsa ya yi, ya dauki makullin motarsa ya fice sai Airport

 

Zuwan Adnan Airport bada dadewa ba jirginsu Yesmin ya sauka

Adnan sa ido ya yi yana kallan matafiyan da suke shigowa

Can ya hango wata ‘yar matashiya da ba za ta wuce shekara ashirin da bakwai ba, amma Wanda bai San shekarunta ba zai yi tunanin ba zata wuce ashirin da uku ba zuwa da hudu ba, saboda kyan jikinta da hadaddan diri da Allah ya bata

Riga da wando take sanye dashi, sai wani half abaya data daura a kai, ta manna katuwar bakin gilashi daya amshi fuskarta sosai, Jan akwatinta take yi tana tafiya cikin ‘kwarewa……Adnan ya ‘kasa dauke ido daga kallonta, a wannan lokacin ido ke aikawa zuciya sako, zuciya Na kaiwa ‘kwakwalwa, sai yanzu Adnan ya ga abokiyar rayuwa, farin cikin rayuwarsa…….zuwa tai ta wuce shi, bin bayanta ya yi da kallo, zuciyarsa Na fada masa “kabi ta, ka fada mata yadda kake ji a ranka, karka bari ta kubuce maka, idan ta tafi ba lallai ka ‘kara ganinta ba”

Bin bayanta ya shiga yi, idanunsa Na kan mazaunanta dake juyawa, fadi yake a zuciyarsa “hadadden shape, gaskiya kin hadu” ji yake kamar ya je ya rungume bayan

 

‘Kokari yai yasha gabanta, tsayawa tai cak tana kallonsa, ko ba’a fada mata ba tasan Adnan ne, don tana ganin hotunansa a wayar Mummynta, har da hotunansa da ya yi passing out, amma yanzu a zahiri girmanshi ya bata mamaki, yadda ya yi tsawo sosai, ga cikakken structure Na da namiji

 

Cire gilashi tai tana murmushi tana fadin “Dan karamin ‘kanina Adnan” cikin rikicewa da mamaki Adnan ya tsura mata ido, sai yanzu ya gane Yesmin ce, sa hannunsa ya yi ya shafo ‘keyarsa sannan ya wayince yana fadin “sannu, ya hanya?”

 

“Lafiya lau, gaskiya yaran yanzu baku da wuyan girma, gaka dai yaro amma mai jikin manya”

 

Maganarta ‘karamar dariya ya bashi sai ya ce “Amma kinsan da zan iya aje kamarki, Na ciyar da ita kuma Na yi mata ciki ta haihu ko?”

 

A take Yesmin ta hada rai ta ce bana son rashin kunya, ka dai sani?

 

“Nan dai babu yaro, we are all mature, kuma gaskiya Na fada miki” Adnan ya fada yana daga mata gira

Kawar da kanta ta yi da sauri tana magana cikin fushi “muje ka kaini gida” tai hanyar ficewa, yabi bayanta

 

Mu hadu a page 2

 

Taku har kullum Maryam M. Hasheem

(Mjaruma)

09049493054

SWEET 22

(Age is just a number)

 

 

 

 

Page 2

 

‘karasowa suka yi filin parking, Yesmin ta juyo ta kalleshi tana tambayarsa motarsa

 

Kallonta ya tsaya yi cikin wani yanayi batare da amsa ba

 

“Kai Adnan wani irin kallo kenan” tai maganar cikin tsawa

 

Adnan bai ce da ita komai ba ya yi gaba, tabi bayanshi suka tsaya wurin wani hadaddan mota, ya dannan madannin makullin dake hannunsa motan ya bude

 

Yesmin ta saka akwatinta a gidan baya, sannan ta shiga gidan gaba ta zauna, Adnan ya shiga ‘bangaren direba sannan ya tayar da motar suka tafi

 

Tafiya suke yi babu mai yiwa daya magana, saita madubin motar ya yi saitin fuskar Yesmin, kallonsa ya sauka kan idanunta farare tasss masu daukar hankali, cizon lebansa ya yi na ‘kasa a lokacin da kallonsa ya Kai kan dan ‘karamin pink din bakinta…..A hankali yake ‘kara jin kaunarta na ratsa zuciyarsa, koda yasan ba abu mai sauki bane ta amince da ‘kudirinsa amma yasa a ransa ba zai yi ‘kasa a gwiwa ba, zai yi iya ‘kokarinsa har ya cika burinsa

 

Wayarta ta ciro daga cikin jakar hannunta dake ringing, ta danna kore sannan ta manna a kunnanta “Hello baby love” shuru tai sai can ta cigaba “kasan fa Na yi missing Dinka, Na so a ce kai nafara gani a Nigeria, please ka zo gida yanzu”

 

Adnan tsintar kansa ya yi cikin tsananin jin haushi, baisan lokacin da ya yi wani wawan parking ba, sai da duk suka yi gaba, suka dawo baya, Yesmin tai salati, wayar hannunta tuni ya fadi ‘kasa

 

Kallon Adnan ta yi tana fadin “ka yi hauka ne?”

 

Bai bi ta kan maganarta ba ya shiga fadin “please and please bana son Ina driving, wanda ke gefena yana waya”

 

Cikin mamaki ta ce aljanu gareka? Ko kuma isa ne irin naka?

 

Bai ce mata komai ba, ya fisgi motar suka cigaba da tafiya

 

Yesmin girgiza Kai ta yi ta shiga magana “yara Sam sam basu da tarbiyya, daga sun balaga sai su fara ganin kowa ma sa’ansu ne” haka ta cigaba maganganu har suka ‘karaso gida, a harabar aje motoci Adnan yai parking sannan ya fito, Yesmin itama fitowa ta yi, ganin Adnan yai hanyar barin wurin yasa ta Kira sunansa “Adan” juyowa ya yi yana fadin “ya aka yi”

 

“Ka bude backseat ka daukar min akwatina ka Kai min ciki” tai maganar tana tafiya zuwa ciki…..Adnan ya bita da kallo cike da soyayya, ‘Karamin murmushi ya yi yana fadi a zuciyarsa “Akwai aiki a gabana, yakamata na fara nuna miki ni ba yaro bane”

 

****

Haj Aisha zaune a falo,Yesmin ta shigo, da sauri ta je ta rungume Haj Aisha tana fadin “oyoyo Mumcy”

 

“Yesmin ke ce haka? Gaskiya I missed you”

 

“Missing you too”

 

“Ya kika baro mutanan America?”

 

“Lafiya lau Na baro su, suna nan shigowa suma month end”

 

“Allah ya kaimu”

 

“Amin”

 

“Yanzu ki je ciki ki yi wanka, nasa an gyara miki dakinki, komai Na ciki sabo ne, idan kin huta sai ki fito mu yi lunch”

 

Yesmin cikin murna ta ce Tom mummyna sannan tai hanyar zuwa dakinta, dai dai lokacin Adnan ya shigo cikin sallama, amsa sallamar tai sannan ta ce my Adnan an dawo

 

Ya ce eh mummy….sannan yai wucewarsa

 

****

Yesmin tsayawa ta yi tana kallan yadda aka canza komai Na dakinta, ta yi farin ciki sosai, aje jakar hannunta ta yi ta zauna kan kujerar dake dakin tana cire takalmin ‘kafarta…..hankalinta ya koma ‘kofar shigowa dakin, Adnan ne ya shigo

Yesmin da mamaki ta ganshi babu akwati a hannunsa

“Ina Akwatina?”

 

Adnan ‘karasowa ya yi dab da ita sannan ya ce nazo na fada miki motar a bude take, idan kin shirya zuwa daukar akwatinki, sai ki je ki dauka, ni kin ga tafiyata…..kallanshi take cike da mamaki, juyawa yai zai fita, tai saurin dakatar dashi “Wato Adnan Kai rashin kunyarka a kullum gaba yake yi ba baya ba ko, tun wuri kafin raina ya ‘baci ka je ka dakko min akwatina idan ba haka ba sai na hukunta ka” maganarta ‘karamar dariya ta bashi, bai ce mata komai ba ya fita ta bishi da kallo tana fadin “Ina jiranka, ka yi sauri ka kawo min yanzun nan” ta cigaba da cire takalminta, bayan ta gama, ta tube kayan jikinta, ta daura tawul sannan ta shiga bayi

 

Adnan dakinsa ya wuce Kai tsaye, tube kayan jikinsa ya yi, ya rage daga shi sai farin gajeran wando, ya fada kan gado ya rungume filo ya shiga kawo hoton fuskar Yesmin a idanunsa, abin gaba yake yi bai baya, komai nata birgeshi yake yi, hatta maganarta, tunaninsa yanzu yadda zaiyi ya baiyana mata yadda yake sonta, bai taba jin son wata ‘ya mace ba kamar yadda yake jin son Yesmin, already yana da budurwa sunanta Zainab Amma Zee ake kiranta, tare suka gama secondary, tana masifar sonsa kamar rayuwarta, yanzu haka matakin ‘karshe take a private university, tana karatun medicine…..akwai alkawarin tana kammala karatu zasu yi aure

 

Yesmin fitowa wanka tai tana goge jikinta da tawul, sai data tsane jikinta gabadaya sannan ta shiga duba cream da zata shafa….kayayyakin amfaninta na cikin akwatinta, sai yanzu ta kula Adnan bai shigo mata da akwatin ta ba, rike kugu tai cikin mamaki tana fadi a fili “wato Adnan yana son ya nuna min ban isa ba kenan, ai kuwa zan yi maganinsa” bude durowan dakin ta yi ta dauki dogon hijabi ta saka, kasancewar babu komai a jikinta yasa manyan nonuwanta suka yi dai dai a cikin hijabin, ana ganin kan nonuwan duk sunyi tsini gwanin ban sha’awa, fita ta yi…..Dakin Adnan ta wuce Kai tsaye, batare da sallama ba ta fado cikin dakin, yana ganinta ya tashi zaune idanunsa suka sauka akan ‘kirjinta….ji ya yi bananansa Na zurrrrr, a take idanunsa suka canza launi

Nuna mishi hanyar fita ta yi tana fadin “maza mike ka je ka dakko min akwatina kafin Na saba maka”

Yanzu mayar da kallonsa ya yi cikin idanunta yana magana cikin dashashshiyar murya “abinda kika yi yanzu kin kyauta kenan?”

Cikin rashin fahimta ta ce me na yi?

 

“Baki ga cikin yanayin da kika shigo min daki ba, nifa lafiyayyan namiji ne, abu kadan ke tayar min da hankali, ji yadda kika bar breast dinki Na yawo cikin hijabi, yanzu ya zaki yi dani kin tayar min da hankali”

Cikin tsoro Yesmin ta zaro ido tana fadin “Adnan me kake nufi?” Sauka ya yi daga kan gadon ya tsaya gabanta, nuna mata ‘kasanshi ya yi, yadda katuwar bananansa ya mike sambal a cikin gajeran wando, har yana lekowa “kin ga yadda ya tashi ko?” A gigice cikin tsoro Yesmin ta juya da sauri tabar dakin….abin dariya ya bawa Adnan, ya koma ya kwanta kan gado amma har yanzu nonuwanta yake gani cikin idanunsa..ji yake da a wannan lokacin ta bashi dama, wasa zai yi dasu sosai

 

Yesmin shigowa tai dakinta tana ajiyar zuciya, hannunta biyu dafe a ‘kirjinta tana fadin “Na shiga uku ni Yesmin” a hankali ta zauna bakin gado tana ‘kara tuno yadda ta ga bananan Adnan…a hankali ta furta “Allah ka rabamu da mugun ji, mugun gani, gaskiya Na yi mummunar gani yau, Allah karka ‘kara nuna min irin wannan ranar” tashi tai ta cire hijabin jikinta ta mayar da kayanta sannan ta fita can harabar fakin, ta dakko akwatinta, ta dawo ta canza kaya, doguwar riga tasa mara nauyi, nonuwan nan sun cika ‘kirjinta tam, Yesmin akwai dukiyar fulani, Allah ya taimaketa a tsaye suke don ko breziya bata sakawa, sai idan ya kama dole

 

****

 

Mr Dattijo da Haj Aisha takawa suke yi suna tattaunawa a tsakaninsu har suka ‘karaso Dining area, suka zauna, Haj Aisha ta shiga serving Mr Dattijo

Dai dai da zuwan Yesmin dining din, tana smile ta shiga gaida Mr Dattijo

 

Mr Dattijo ya ce you are highly welcome my dear

 

Yesmin ta ce thank you dearest father sannan ta zauna

 

“Ya mahaifiyarki da sauran ‘yan uwanki?”

 

“Duk suna lafiya”

 

“Masha Allah, mun yi magana da mahaifinki ya ce zuwa ‘karshen watan nan zasu dawo Nigeria gabadaya ko?”

 

“Eh hakane”

 

Haj Aisha ta ce ai gwara su dawo kusa damu, muna ganinsu suna ganinmu

 

Haj Aisha ta yi serving Yesmin, Yesmin tai smile ta ce thank you mummy

 

“You are most welcome”

Tai serving kanta ta zauna domin cin abinci

 

Adnan ne ya ‘karaso wurin cikin ‘kananun kaya, farin t-shirt da farin three quarter, ya amshi jikinsa sosai ya yi kyau, kakkaurar jikinsa da farfajiyar ‘kirjinsa sun baiyana sosai, kallo daya Yesmin ta yi masa ta kawar da kanta da sauri sanadiyar wani irin kallo da yake mata

 

Zama ya yi a kujerar dake fuskantar nata ya kalli Mr Dattijo yana fadin “sannu Daddy”

 

Mr Dattijo ya ce yauwa my boy

 

Nan Haj Aisha ta shiga serving Adnan, bayan ta kammala yai mata godiya

 

Yesmin neman natsuwarta ta yi ta rasa gabadaya a dalilin wani kallo da har yanzu Adnan yake mata, koya ta dago kai, sai su hada ido…..ji ta yi kamar ana taba kafafuwanta, sai yanzu ta kula da Adnan ne ke tokarinta da ‘kafa, kallonsa ta yi suka hada ido, harara ta watsa masa sannan tasa ‘kafa ta tokareshi sosai…….hankalin Mr Dattijo da Haj Aisha ya Kai kan movement dinta

 

Haj Aisha ta ce Yesmin lfy kuwa?

 

Yesmin ta ‘kwakulo murmushi sannan ta ce lafiya lau mum

 

Mr Dattijo ya ce santin abincinki ne kawai, abincin ya yi dadi sosai

 

Adnan ya ce hakane Daddy, kasan Mummy ta ‘kware a girki, ina addu’ar samun mata wacca ta iya girki kamar ita

Haj Aisha ta ce Insha Allah ma zaka sami wacca ta fini sosai

 

Mr Attajiri ya kalli Yesmin ya ce Yesmin kin iya abinci kuwa?

 

Yesmin da sauri ta ce eh, Daddy Na iya

 

Adnan kallan Yesmin ya yi ya ce yakamata ki kware sosai saboda ina son abinci

 

Wani kallo Yesmin ta watsa masa sannan ta ce miye hadina da son abincinka?

 

Kafe idanunsa ya yi a kanta ya ce saboda ki dinga girka min

 

“Kasan ni sa’arka ce ai da zan girka maka abinci ka ci”

 

Haj Aisha ta kalli Adnan ta ce bana son rashin kunya, Auntynka ce fa

 

Yesmin tana harararsa ta ce ina yasan haka

 

Haka suka cigaba da yin lunch suna santin abincin Haj Aisha

 

Bayan kammala lunch, Adnan dakinsa ya wuce, Mr Dattijo kuwa ‘bangarensa ya wuce ya yi baki

Haj Aisha da Yesmin su kadai suka rage a falo suna hira

Kira ya shigo wayar Yesmin, kallon Haj Aisha tai tana murmushi ta ce Mummy shine, Ina ga ya ‘karaso

Haj Aisha ta ce okay, to ki shigo dashi ciki, bari Na bar muku falon

“Mummy ai da kin tsaya kun gaisa”

 

“Ba yau ba, ki bari ranar daya shirya zuwa gaisuwa, sai mu yi masa tarba Na musamman, yanzu oyoyo yazo miki”

 

Murmushi kawai Yesmin ta yi, Haj Aisha ta mike tana fadin bari Na shiga daga ciki, ki gaida min shi

 

Yesmin ta mike tana fadin “Tom mummy” sannan tai hanyar fita

 

****

Areef tsaye jikin motarsa a harabar gida, Yesmin tana fitowa da gudu ta je ta rungumeshi ya cabeta sannan ya dagata zuwa sama “oyoyo babyna”

 

“Baby ka ganka kuwa? Ka ‘kara kiba, har wani ‘karamin tumbi ka aje”

 

Areef ya ce wallahi kuwa baby kuma fa kullum sai Na fita gudu, kawai dai yanayin jikina ne

 

Yesmin ta ce gaskiya baby nan da wasu shekaru gari guda zaka koma

 

“Idan Na koma gari guda, zaki daina sona ko?”

 

“Habadai babyn baby, idan ka ga Na daina sonka, Na daina numfashi ne”

 

Manna mata kiss ya yi a goshi yana fadin “I love you”

 

“Love you more”

 

Suna rike da hannu Juna suka shiga ciki

 

A falo ta sauke shi, ta sashi ya zauna comfortable sannan ta kawo masa Lemun kwali, wine da ruwa, sai glass cup

 

Zama tai gefensa sosai, ta shiga tsiyaya masa lemun kwali a cup, kallonta kawai yake yi yana jin farin ciki a ransa, ta mika masa…. baby gashi ka sha….amsa ya yi yana fadin “thank you”

 

Hankalinsu ya koma kan Adnan daya shigo falon, mutuwar tsaye ya yi yana kallansu,

Areef aje glass cup din hannunsa ya yi yana kallon Adnan sannan ya ce Adnan kaine haka ban ganeka ba, ‘karaso mana mu gaisa

 

Tuni idanun Adnan suka kada, nuna Kansa ya yi yana fadin “nine zan ‘karaso Na gaisa da kai, amma da alamu ‘kwakwalwarka bata aiki dai dai”

 

Zumbur Yesmin ta mike tana nuna Adnan “rashin kunyarka ya tsaya a kaina Amma banda mijin da zan aura”

 

Wani radadi da zafi Adnan ya ji a ranshi amma ya jure, nuna Areef ya yi yana fadin “wannan abin kike kira da mijinki, ki jubeshi fa, ki kalleni ki kalleshi, ke kinsan the difference is clear, ki je ki fara soyayya dana miji ba mace ba”

 

Jiki a sanyaye Areef ya mike yana fadin “Adnan laifin me na yi maka kake cin zarafina haka, ko abin daya faru shekarun baya da suka wuce shine har yanzu baka manta ba”

 

Yatsine fuska Adnan yai ya nuna hanyar fita yana fadin “Ka fitar mana daga gida kuma kadaka sake dawowa, zaku iya haduwa a wani wuri ku yi soyayyarku amma ba’a gidan nan ba”

 

A fusace Yesmin ta tunkaro Adnan, cakume masa kwalar riga ta yi “Adnan ni sa’arka ce? Ina wasa da kai, shekara biyar Na baka, ko Abdullahi daya girmeka baya min abinda kake min” bata San lokacin da Areef yai hanyar fita ba, sai dai jin ‘karar bude kofa tai, kafin ka ce miye har ya fita, sake Adnan tai ta bi bayanshi da sauri tana kiransa Baby! Baby! Baby! Bai saurareta ba

Adnan ‘karamin tsaki ya yi ya wuce dakinsa

 

Mu hadu a page 3

 

Don Allah ku tayani sharing group zuwa group

 

Taku har kullum

Maryam M. Hasheem

(Mjaruma)

09049493054

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment