Littafan Hausa Novels

Surukar Mu Ce Hausa Novel Docs

Written by Hausa_Novels

Surukar Mu Ce Hausa Novel Docs

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

SURUKARMU

 

 

 

Na Jamila Adam sidi

 

 

Maman hanifa

 

 

 

 

 

Page 1️⃣&2️⃣

 

 

Dasunan Allah mai rahama mai jinkai ina rokon Allah yakawu muna zaman lafiya da kwanciyar hankali ga’kasarmu amin

 

 

Gargad’i

Banyar da wata ko wani ya juya min littafi ba

 

Labarin SURUKARMU qirqirarren labari ne, idan yazo daidai, da naka ko naki labarin to akasine

 

 

India

 

 

Wani wata anguwa ce kana shigo ta kasan kashigo anguwar masu kud’in tun daga yanayin ta zuwa tsarinta da kuma yadda aka ‘kawatata zakasan ba ugunwar ‘kananan mutane bace duk gidan da zaka kalla kasan kud’i sunyi kuka wani da gidan dake gefen damata na kalla naga ansa

 

 

(ABDULLAH MUHAMMED ‘DAN HAUSA MASHON)

Banyi wata wata ba nashiga gidan lalle masu kud’i suna jindad’in su, irin wannan gida haka kamar ba,aza mutu ba mutane gida suna zaune afalo sai rarrashin wata ba,India suke to, abun mamaki dukansu hausa suke to dama suna jin hausa ne koko hausa wane kallon wata mata nayi wadda naji suna Kira da mom bazata wuce shekara hamsin ba sai kuma mijin ta alhaji Abdullah shima bazai wuce shekaru sitting da wani ,abuba shima yana gefen ta sai yaransu guda hud’u maza ukku mace d’aya sai kuma yaron k’aninshi wanda yake rik’o tun yana yaro gefe guda kuma sarakan sune su biyu da yaransu biyu matar isma,il babban d’ansu yusra tana da yaro d’aya namiji sai matar hafiz takeda yariya mace” dukansu kana ganin su kasan basa cikin yanayi mai dad’i sabida zasu koma ‘kasar su tagado”safina ce yarinya suta ukku kafin auta ameer,, itace tayi k’arfin halin cewa mom kiyi hak’uri ki taya dad bin umurni kaka indai har kina sonshi to dole kibishi mukuma nageria da zama gaba d’aya

 

“kallon ta dadyn yayi”kafin yace safina, idan har momyn ku bazata kuma k’asata da zamaba to muzaje sannan bazata k’ara ganin muba shekara ta talatin ina zaune da ita cikin k’asar da batawa sai yanzu Dan mahaifiyata tabani umurni, inkuma k’asata shine bazata biniba bafa, azamfara zamu zauna ba, cikin, to yauko cikin jeji nace zan zauna da,ita ina ganin bazata gujeni ba balai ABUJA zamu zauna babu, abunda zata nema ta rasa cikin k’asar harfa masu aikin gidan nan duk dasu zamu tafi duk sabida farin cikin ta kenan, ni banida wayo dana zauna nan indabansan kowa ba namaida garin da banawa ba kamar k’asata?

 

 

Dasauri momy ta d’ago kanta ta kalli dady cikin shagwa’ba”tace nifa bance banason zuwa ba kasan kaka bata sona zata, iyasa ka rabu dani koka ‘kara aure wata dariya suka d’auka gaba d’ayan su cikin murmushi “AMER yace haba mom yanzu kamar ke kina tsoro kishiya?

Yadda Ake Tsara Budurwa A Waya

Amma naga da bakinki kikace saisu brother sun ‘kara aure to ashe harda kema bakya son kishiyar to nidai mata d’aya zanyi

filo dake gefen ta tajeho mai”tace amer ka rainani ko” yace kiyi hak’uri mom”cikin jindad’i hafiz yace yaka mata muje muk’arasa shiryawa kunsan gobe tashin asuba zamuyi kallon shi matarshi siyama tayi Dan tasan yayi maganar ne da wata manufa sabida yasan wannan itace damar da zaisamu suke’bance da,ita dan basu, isa, sushiga d’aki da matan da rana ba sadare ko dare sai lokacin bacci,, kafin ya k’arasa momy”tace babu inda zakuje kuna falon nan kenan ina cikin damuwa,,Amma kai ta matar ka kake to babu inda zakuje shiri kuma meye ba,a shirya makuba? Yace kiyi hak’uri mom dama kayan baby ne zata k’arasa shiryawa”hararar shi tayi kafin tace halin ka nasani,

 

sannan ta kalli su yusra tace kutashi kubani wuri,, aiko cikin sauri kuwaccen su tatashi kichin suka nufa suna dariyar ‘keta siyama tace maman boy kinjiman momy kamar wata yarinya tasa ‘ya’ya gaba sai kuka banza take masu kamar wadda zataje lahira”

yusra ta kalli siyama,,tace ni wallahi wani guri naji dad’i komawa gida sabida wannan mulkina ta mata sai bak’ar masifa wallahi gwara wasu sarakan, na gida da wannan bak’ar fitina,,yusra tace ked’ai bari yanzu haka my daer, abuk’ace yake amma Kinga tahana ko d’akin mushiga”

 

Siyama tace wannan kuma d’anta ta cuta bawani ba kenifa yanzu har namance wani abu waishi fira da miji kinsan shima ba ‘karamin tsorota yake ba,,

 

Haka dai suka cigaba da firar su cikin bak’in cikin surukarsu,, acha falo kuwa sai hira suke jan momyn tasu sabida hankalin taya kwanta

 

 

 

A gida nageria kuwa

Shirye shirye kawai suke masu aikin gidan kowa da aikin da yake da masu farin ciki da masu ba’kin dalili kowa shine gobe suna da manyan ba’ki dan babba yaro gidan da ‘ya’yanshi da jikukinshi zasu dawu nageria da zaman din, din din” wata tsohowa nadani zaune wacce ashekaru sai tayi shekara tamani zaune take tayi tagumi sai tunani take ( tunani take yanzu idan sundawu shikenan bazana k’ara bari babban d’anta yayi nisa da, itaba tuda yayi aure India ko wata bai ta’ba yigida ba har baban shi yarasu saidai yazo yayi sati biyu tasan waccen ba’kar matar tasace ke hanashi zuwa har aure tahad’a yaranshi da yaran’ danginshi amma hakan, a banza sabida wani mugun so da yakewa ba,india to yanzu,, Allah ya,amsa addu,arta yace zai dawu gida gaba d’aya,,)wani saurayine yashigo da sallama, saidai kaka tarigada tayi nisa bataji ba, Saida ya dafata yace kaka kina lafiya kuwa kallon shitayi,,tace umhh lafiya qalau yawwa fahat dama inason na tambaye ka shinda gaske kawun ku take zaidawu ko wasace yake?

 

 

 

Fahat ya kalle ta,, yace kaka da gaske yake kinsan kawu bazai maki k’arya ba kuma aikinga yayi gyaran gidan shi to yananan zuwa

 

 

 

Kaka tace nifa idan baganin shi nayi cikin gidan ba tare da waccen ba’kar matar ba to bazan yarda yadawu gida kenan ba, nan tafara fad’a yarasa wanda zai, aura saichan masu jajayan kunnuwa shikuma ubanshi Allah jik’an rai yaje ya d’aure mashi gindi, ni wallahi koda, akayi auren nan bada son Raina ba, itama tasani ba sonta nake ba amma hartaga damar da zata muzgunawa jikukina to bari, inanan inajiran ta shige kafasa dani da,ita

 

Shidai shiru yayi dan yasan fad’an kaka indai, akan kawun sune to yanzu tabara sai kuma yaji tana cewa fahat dame dame kake ganin ya dace, adafa masu?,

 

Cikin mamaki ya kalleta yasan d’a, da uwa sai, Allah yace kaka munyi waya da isma,il yace duk, abunda akayi yayi saidai ita momyn bansan me za,a dafa mata,,tace kai,indai wannan ce kyaleta danba, ayimata daidai,,.

Haka suka cigaba da firar su har lokacin salla yayi bayan kaka tayi sallah ta d’auki wayarta ta kira siyama saida tayi mata Kira ukku sannan ta d’auka”cikin k’asa da murya tace kaka bari zan kiraki yanzu muna tare da momy kuma taha namu d’aukar waya idan muna kusa da, ita,, da sauri kaka tace kam bala,i kibarni da, ita, idan tana tak’amar ita surukarku ce to nima surukarta ce Allah ya kawuku lafiya

 

 

 

Achan India ko momyce zaune, ad’akinta safina ce tashigo tare da sallama cikin harshen hausa tace mom lafiya naga kiyi shiru ko harda ke bakya son tafiyar ?” d’ago kai mom tayi cikin sauri tace a,a bahaka bane kawai dai, na fara miss d’in k’asa tane sannan akiga bansaba lafiya wani wuri na jima ba sai yanzu kinga dole nashiga damuwa sannan kiga bikin ku yana matsowa narasa yadda zanyi naso ace yarena kika aura, amma kinna cewa wancan yaro ke sarkin soyayya” safina tace kiyi hak’uri mom naga ko auren mukayi gida d’aya zamu zauna kuma my honey yanayi maki biyayya sosai”hannu ta d’aga mata tace ya,isa haka tunda kina sonshi aibazaki ga laifinshiba, ina, ameer yake yasan banaso yana nisa dani shine zai fita keje kikiran min siyama da yusra”safina tace momy Dan Allah kibarsu suhuta wai hala kinaso idan muje nageria sugayawa iyayensu ” cikin mamaki ta kalle ta kafin tace sugama iyayen su to susuke da iko dasu baniba sufa surukaina ne kuma y’a’yana suke aure dan haka sai, abunda naga damar yimasu, kedai babu ruwanki” safina tace kenan nima idan mukayi aure da yasir sai, abunda momyn shi tayi dani ko kema idan muka koma gidan gobe sai, abunda kaka tayi dake?,,da sauri momy tace safina wai maiyasa keda ameer kuka rainani tashi kiban guri kuma kice suzo,, tashi tayi soso tafita falo tasamu su siyama kamar kullun tace sister’s momy tana kiran ku tace sukayi kuwacce gaban ta yana fad’uwa suka hau sama inada d’akin momyn yake zaune suka same Saida sukayi sallama sannan suka shiga duk’awa sukayi har, ‘kasa kamar zasuyimata sujada tare sukace sannu da hutawa momy tace yawwa dama inaso naja kunnen ku idan mukaje negaria gobe kuka gayawa kaka yadda muke zama daku to zansa y’ay’ana su sakeku,, dasauri suka d’agu kai cikin rawar murya sukace insha Allah babu abunda zataji,, tace nadai gaya maku kuje kukunta hanan, to sukace, atare kafin su fice……….

 

 

 

Tonima nan zan tsaya saimun sauka nageria comment d’inko zaisa nacigaba idan babu comments to babu typing

 

 

Wannan littafin yasha banban da wancan kada kubari abaku labari zakuji yadda zata kaya tsakanin suruka da suruka wato tsakanin kaka da ba, India wato ayusha wadda kukafi sani da momy

 

 

Sainajiku muje zuwa

 

 

 

 

 

 

SURUKARMU

 

 

 

SURUKARMU CE

 

 

 

Na Jamila Adam sidi

 

 

Maman hanifa

 

 

 

Page 3️⃣&4️⃣

 

 

 

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai ina rokon Allah yakawu muna zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ‘kasarmu amin

 

 

 

Asalin labarin

 

 

 

Abdullah yakasan ce d’aga maryamu da baban su alhaji, Ibrahim sai ‘kannen shi sani da Wanda yake bimasa sannan balkisu suna zaune garin gusau kuma nan sukayi makaranta har suka kai jami, a lokacin ne Abdullah yace shi India yake so ya’karasa karatun shi dayake suna da hali nan take iyayen suka yarda nan sukayi mashi cuku,cukun tafiya lokacin da yaje baisan kowaba Saida gabaya ya had’u dasu muntari Wanda yanzu akekira da alhaji muktar ya kasance d’an jihar kako ne sai alhaji salis dake zaune akaduna dukansu abokaine masu da junan su shiyasa harsuka gama karatu suna zumunci ga kasuwan ci da suke tare wanan kenan,

 

 

 

 

Suna shekara ‘karshe ya had’u da aisha baifi saura shekara sugama karatun suba nan suka fara soyayya’mai tsafta duk dayake ita momyn sonshi take ba, a lokacin Amma daga baya sai tafara sonshi,

 

 

Bayan yagama karatun shi yasamu aiki mai tsoka anan india yace bazai zauna nageria saidai yazo yayi sati biyu ya koma lokacin da, iyayen shi sukace ya fito da matar aure saiyace masu yasamu Mata amma ‘yar India ce nan kaka tace batasan da zancen ba saida, akakai ruwa rana sannan ta yarda akayi bikin daga nan kuma saiya koma can da zama gaba d’aya saidai wani lokacin yana zuwa shida aisha dukda ba taso tazo lokacin da zatayi haihuwar farko yaso, ace nageria tayita saidai iyayen ta sunnuna basaso haka ya ha’kura ta haihu can yaro yace sunan fawaz bayan shekara ukku ta k’ara haihuwar Salim sannan safina sai auta Ibrahim wanda suke Kira ameer d’aga nan kuma bata k’ara haihuwa ba fawaz da Salim suntaso kansu d’aya shiyasa komai tare suke hatta kasuwan ci tare wani zuwan da sukayine hutu nan alhaji Abdullah yaga yaron ‘kanin shi sani dayake jinin su yahad’u da Salim shine yasa sukazo dashi sai yaza mana su biyar kenan haka suka cigaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali fawaz yada shekara ashirin da biyar yace ma iyayen shi aure yake kuma suka amince inda suka samu matsala shine kaka tace batayar jikukin ta suyi aure a, India haka yasa sukazo cikin dangi suka za’bi matan aure fawaz yana auren yusra ‘yar gidan ‘kanwar baban su sai salim yana auren siyama ‘yar baba sani wannan kenan,.

 

 

 

 

Ta wurin momy kuwa ton lokacin da kaka tace jikukin ta bazasu auri ‘yar India ba taji gaba da batason kaka badan tanason alhaji Abdullah ba da tuni tarabu dashi sai bazata, iya rayuwa babushi ba daga nan ta d’auki Karan tsana tasawa gaba d’aya dangin alhaji Abdullah hatta Nasir da itace tare neshi kuma ta gefe d’aya ga soyayya’ mai zafi d’aya shiga tsakanin Nasir da safina.

 

 

lokacin dasu yusra sukazo gida wurin haihuwa nanne kaka tafahimta kuma tayi masu alk’awari inda ranta saitayi masu aure yusra ce tafar haihuwa inda tasamu d’a namiji Wanda yaci sunan baban momy Wanda yarasu da dad’ewa Kabir suna Kiran shida boy bayan wata ukku da haihuwar boy siyama ta haihu tasamu ‘ya mace suka samata hafsat bayan tayi kwana, arba,in kuma sukayi babban rashi dumin kuwa alhaji Ibrahim lokaci yayi kuma wannan karon Mommy tazo gaisuwa to daga haka kaka tatsiro da saisun dawu gida gaba d’aya tunda shine babba wannan maganar ba’karamin k’ona ran Mommy yayi wanda shine asalin muzguna wasu yusrah da take.

 

 

Karanta Littafin Wani Uba Hausa Novel

Nan kaka taba alhaji Abdullah shawara da yayi gida Abuja dan chan yafi tsaro ya kuma yarda dahakan dan ya k’era gida najida gani babban fili yasiya yayi masu k’atun flat sai k’arami da yayiwa kaka shikuma nashi gidan gaba d’aya ya had’a da yaransu, idan kashi cikin gida zakaga gurin aje motoci sai wurin wasa da wurin boll cikin falon kuma angewaye shida d’akuna ba, adadi daga saman gidan zakaga staf guda biyar d’aya na fawaz d’aya Salim sai na kabir duk yanayin su d’aya komi d’aya dan flat ne d’aki ukku_ukku da kichin sai bayi gakowane d’aki,

 

 

 

Sukuma su momy nasu yana tare dana Ameer dan tace tare zata zaune da Ameer gudun kada matar shi tacutar mata dashi, shiyasa nasu yafi girma da tsarowa.

 

 

 

 

 

Ameer d’an gata wanda ba,ayiwa fad’a duk wani sona duniya momy ta d’auke shi ta d’urawa Ameer gashi auta yana shekara ashirin da ukku yagama karatun shi ya fad’a kasuwan ci tare y’an uwanshi wannan kenan

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Washi gari tunda magari ba jirgin su yasauka Abuja mota goma sha biyu ca tazo d’aukar su acan gida kuwa mutane kamar ana wani biki kodayake indai ga kakane wannan yafi biki.

 

 

 

Da d’ad’aya motoci suka fara shiga cikin gidan su momy suka fara fita kuwa suyake su gaida dasu dak’ar suka samu suka shiga cikin gidan…….

 

 

 

 

 

To masu karatu kada kugaji da hak’uri sai kuma jibi dan munada matsala wutar nefa kuma inada yarinya k’arama Sai mun had’u page na gaba

 

 

 

 

 

 

 

 

Muje zuwa

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment