Littafan Hausa Novels

Surkulle Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Surkulle Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

*SURKULLE*

NA

AMINA ABUBAKAR YANDOMA

(Meenat A Yandoma)

 

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

 

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan littafin gareku alkhairin Allah ya kai maku har gadon barcinku.

ABBA ABUBAKAR YAKUB

BINTA UMAR ABBALE

 

GARGAƊI/WARNING

Ban yarda ayi Mani amfani da wannan littafin ta ko wace hanya ba sai da izinin na, yan Youtube ku kiyaye.

 

 

Page 1

Hadari ne yayi ma gari ƙawanya wanda kallo ɗaya zaka yi Mashi hankalinka ya tashi domin ko tafin hannunka baka iya gani, iska me ƙarfi ce ta fara kaɗawa tamkar guguwa itatuwa suka riƙa rangaji tamkar zasu karye ruwa me ƙarfi tare da iska ne ya sauka tamkar da bakin ƙwarya, duk wannan ruwan da ake sheƙawa Hibba da yaranta barci suke cikin falon a hankali ƙofar falon ta kulle kanta wutar nepar ce ta fa ra fafarniya, bugun da ake yinma ƙofar ne ya saka Hibba miƙewa agigice ta buɗe ƙofar.

 

Yankan Wuka Hausa Novel Complete

Tozali tayi da mijinta Abdallah ruwa ya jiƙeshi sharkaf sai kyamar sanyi yake.

“Ki bani hanya in wuce ko sai ruwa ya ƙara sa ƙarewa a kai na”?

Abdallah ya faɗa a ƙufule.

Da sauri Hibba ta kauce dan tasan laifi ta ne yau kam ta ɓatama Abdallah rai.

Bayan ya sauya kaya fitowa yayi dai-dai lokacin yaransu Biyu suka farka Namijin yayi saurin miƙewa yana ma Mahaifinshi oyoyo

“Amir barci kuke, in ana ruwa addu’a ake domin lokacin ƙofofin rahama a buɗe suke.”

“Abba barcin ne ya sace mu”

Cewar Amira.

“Abba ina Amra take”?

Amira ta faɗa.

A gigice Hibba ta miƙe Abban Amra ina Amra take.

Cike da mamaki yake kallonta shida ya shigo yanzu ina yasan inda Amra take.

“Dawowata kenan daga aiki na tara r daku kuna barci amma kike tambayata ina Amra”?

“Na shiga uku! Ina ɗiyata take”?

Ganin Hibba zata ɓata ma shi rai kai tsaye ɗakin yaran ya nufa sai dai wayam babu kowa.

Cike da mamaki ya dawo falon.

“Kin tabbatar Amra tana cikin falon nan kafin ku fara barci”?

“Wasa suke yi sai na ɗan kishin giɗa daga nan ba san meke faruwa ba sai da naji bugun ƙofarka.”

“Ku jirani in fita in duba ko ta fita baki sani ba”

A tare suka fice daga falon duk da ruwan da ake sheƙawa a lokacin ko idonsu ya rufe burin su ɗaya shine suga Amra.

Babban abinda ya ƙara tayar masu da hankali shine duk faɗin tsakar gidan su bincike amma babu Amra, walƙiyar da aka yi ce Hibba ta hango kamar Amra jikin bango tsaye, hannun Abdallah ta Kamo tana nuna ma shi wurin mutuwar tsaye yayi domin kuwa tabbas Amra ce tsaye kamar tana magana da wani a jikin Bango.

Cikin hanzarin suka ƙarasa jikin bangon tare da kiran sunanta

Bata juyoba sai da suka sake kiran sunanta sannan suka ji ta amsa.

“Amra me kike yi a nan wurin ki taho mu je ɗaki bakiga ruwa ake yi ba”?

Abdallah ya faɗa.

Shuru bata juyoba kuma bata tanka ba.

“Amra magana muke maki ki taho muje ɗaki ki so kike sanyi ya kamaki”?

“Umma ke kika ce mu riƙa girmama na gaba damu ku kalli jikin bangon nan wata mata ce ta kirani zata faɗa man wani abu ko dai baku ganinta ne”?

Amra ta ƙarasa maganar ba tare da ta juyoba.

Jikin Hibba kyarma ya fara yi cike da tsoro ta matsa kusa da Abdallah laɓɓanta na kyarma.

“Abban Amra Aljannu sun shafi Amra ni nasan wannan ba Amrata bace.”

Hibba ta ƙaasa maganar tamkar zata fashe da Kuka.

Cikin zafin nama Abdallah ya fizgo Hannun Amra juyuwar da tayi aka dallah walƙiya nan Abdallah ya hango fuskar da bazai taba mantawa da ita ba, fuskar da rabon shi da ita kimanin shekaru ashirin da shida kenan.

Murmishi Amra tayi tare da matsowa saitin kunnen Abbansu ta raɗa mashi.

“Barka da sake haɗuwarmun karo na biyu.”

Cikin hanzari ya juyo da fuskar Amra domin tabbatar da abinda ya gani amma a wannan karon fuskar Amra ce.

Hannunta ya kama suka shige cikin falon.

Bayan an canza ma Amra kaya barci ne yayi awon gaba da ita.

Cike da damuwa Hibba ta fara magana.

“Amir ku tafi ɗakinku ku kwanta”

Ba tare da gardama ba a tare suka nufi ɗakin.

“Abban Amra ina so muyi magana”

Hankalinshi ya maido kanta.

“Abban Amra batun yau ba nasha faɗa maka Amra bata da cikakkiyar lafiya amma kaƙi yarda dani, tun sa’in dana haifi Amra nike ganin baƙin al’amura a tattare da ita, a halin da muke ciki yanzu shekarar Amra hudu kullum al’amuran ta sake rikicewar suke abinda ya faru yau ya tayar Mani da hankali na kasa jurewa.”

Ta ƙara sa maganar hawaye na bin fuskanta.

Cikin tausasa kalami ya fa ra magana.

“Bani so in ga kina tayar da hankali ki koda munje wurin masu magani addu’a ce zasu yi ma Amra kuma nima ina iyakar bakin ƙoƙarin a mu ɗauki wannan a matsayin jarabta ce daga Allah.”

“Na aminci amma maganar zuwa wurin danginsa fa, na matsu in kai yaran nan suka dangin mahaifinsu ina tsoron in suka kara wayo suka tambayeni dangin Mahaifinsu me zance masu”?

Ji yayi tamkar an soke shi da wuƙa a ƙirji sakamakon abinda Hibba ta faɗa ma shi, duk wani Annuri dake fuskar shi ɗaukewa yayi.

“Sau nawa zance maki ba yanzu bane lokacin da ya kamata ku haɗu da Dangina ba.”

“Na gaji! Na gaji da wannan kauce-kaucen da kake yi Mani, karka manta kafin aurenmu kayi Mani al’ƙawarin zaka haɗari da Danginka amma bayan aure sai ka nuna Mani bakasan da wannan maganar ba, yaran mu uku a halin yanzu amma dai-dai da rana ɗaya basu taba ganin dangin mahaifinsu ba, rayuwa bata da tabbas Ni da kai bamu da tabbacin zamu yi doguwar rayuwa da yaran nan in muka rasu wurin wa zasuje wa zamu barma su ina zasu nemo dangin mahaifinsu”?

“Na gama magana ba yanzu ne lokacin ba dan haka ki daina yi mani wannan maganar”

Ya karasa maganar tare da shigewa ɗaki.

Hibba kuwa ƙara sa zamewa tayi ƙasa tare da sakin kuka me tsuma zuciya.

Daren ranar bata yi barci ba tana saman kafet tana kai kukan ta ga Allah dan shine kaɗai zai yaye mata damuwarta, nan barci yayi awon gaba da ita sai da asuba Abdallah ya tayar da ita tayi sallah.

Kamar yadda yaran suka saba in gari yayi haske suna shigowa su gaida mahaifansu yau ma haka ce ta kasance.

Yar auta Amra tana gefen Abbansu suna labari inda rabi da kwatan labarin soki burutsu ne take yi ma shi

“Abba me Umma tayi maka zaka hauta da faɗa jiya da dare”?

Ba Abdallah kaɗai ba hatta Hibba sai da gabanta ya yanke ya faɗi.

Ƙasa magana suka yi cike da mamaki suke kallon ta dan lokacin da suke maganar yaran duk suna ɗaki sunyi barci.

“Wa ya faɗa maki wannan maganar”?

Abdallah ya jefa mata tambayar.

“Abba Ni ko ina barci ina jin duk wata magana da ake yi kuma in na tashi zan iya bayarda labarin abinda ya faru.”

Ƙut! Hibba ta haɗiye wani irin yawu.

Amir da Amira kuwa a tare suka kalli juna suka fashe da dariya.

“To yanzu faɗa Mani da kina barci jiya me nayi”?

“Ka shiga toilet kayi fitsari har kaga wata baƙar mage da ta kawo Mani ziyara ka fito a guje.”

Ihu suka ɗauka a tare ganin Amra ta faɗin gaskiya.

Yaran murna suka riƙa yi ganin yadda ƙanwarsu ke faɗar abubuwa ba tare da ta gansu ba a lokacin da suke aikata abun.

“Wannan ba abun murna bane koda wasa kada ku sake in ji wani ya faɗi abinda ya faru cikin gidan nan in ba haka ba wanda duk ya faɗa mutuwa zai yi.”

Cewar Abdallah.

Tabbas badan Abdallah yayi masu haka ba da babu abinda zai hana su Amir in sunje makaranta su faɗi abinda ya faru.

Bayan tafiyarsu makaranta ya rage daga Hibba sai Amra a cikin gidan barci Hibba ta koma sakamakon kanta dake mata wani irin ciwo.

Cikin barcin Hibba taji kamar Surutu ƙasa-ƙasa saukowa tayi daga saman gadon tare da nufar inda taji surutun na fitowa.

Amra ta taras zaune cikin Falon ta baza kayan wasansu tana ta kallon gefen ta tana magana tare da tuntsurewa da dariya.

Cikin hanzarin Hibba ta nufota.

“Amra me kike yi haka”?

“Ana ƙara sa bani labarin jiya ne baki Ga falon a cike yake ba, kibi a hankali kada ki taka masu yara.”

A rikice Hibba ta zo zata ɗauke Amra sai ji tayi wani abu ya dakar mata ciki da ƙarfi, wata uwar ƙara ta kwala tare da zubewa ƙasa jini nabin ƙafarta

Amra kuwa tamkar wadda aka kama ma hannu haka ta shige ɗakinsu tana shiga barci yayi awon gaba da ita.

Abdallah tunda ya ɗauko su Amira yake jin gaba shi yana wata irin mummunar faɗuwa wadda bai taba jin irinta ba.

Saka ƙafarshi cikin falon nan yayi tozali da Hibba kwance cikin jini, shi da yaran agigice suka ƙara sa wurin Hibba amma shuru Babu alamun tana raye.

Umurtar yaran yayi su tsaya gida shi kuma ya ɗauki Hibba suka nufi asibiti bayan yayi me gadi gargaɗin kada ya kuskura ya buɗe gidan kowa ye yazo.

Gudu yake tamkar zai tashi sama musamman da yaga halinsa Hibba ke ciki, kai tsaye Emergency aka wuce da ita likitoci biyu ne a kanta Abdallah kuwa sai faman kai kawo yake zuciyarshi a jagule fatanshi ɗaya Allah yasa ba mutuwa Hibba tayi ba tabbas in Hibba ta mutu shima bazai ƙara second ɗaya ba a raye, maganar da Hibba tayi ma shi jita ce ta dawo ma shi sabuwa.

“Ka nuna Mani dangi ka rayuwa ba tabbas in muka rasa rayuwarmu wa zai riƙe mana yaran mu ina zasu gano dangin mahaifinsu”?

Wata zufa ce taci gaba da wanke ma shi fuska gaba shi na mummunar faduwa.

Likitanne ya fito daga dakin yana sharce zufa suna hada ido da Abdallah sai ya sadda kanshi kasa, da sauri Abdallah ya karasa kusa dashi yana tambayarshi lafiyar matarshi, shuru likitan yayi tare da zare farin glass din dake maƙale a fuskarshi

Wata kururuwa Abdallah yayi tare da cakumar kwalar likitan,

“Ina Hibba take ka fada mani wane hali take ciki”

Ya karasa maganar cikin karaji.

Ganin irin shakar da yayima likitan ya saka jami’an tsaro rugowa da gudu suka yo kansu…

 

 

 

Masu bukatar shiga group din Surkulle kuyi mani magana dan gaskiya na daina bada link

08133562798

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment