Littafan Hausa Novels

Surbajo Sabon Salo Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Surbajo Sabon Salo Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*SURBAJO SABON*

*SALO

 

 

 

*ZAHRA SURBAJO*

 

 

 

*Bissimillahirrahmanirraheem*

 

*da sunan ka Allah nake farawa da kuma sunanka zan gama,yardar ka nake fata,Allah ka bani ikon rubuta alkhairi,in kuma nai kuskure ka yafemin*

 

 

*na sadaukar da littafin gaba dayanshi ga Inna Ibrahim kime,kinsan daraja da kimata Inna,dole nima nasan taki,Allah ya albarkaci rayuwarki Inna,in nace ban sonki wlh nayi karya,kina sani nishadi*

 

 

*1*

 

 

“Bakar mayya,wlh ko zaki mutu sekin fitar da sauran furar n dandali kin siyar da ita,tunda ba ubanki zan tasawa agaba yacinye ba”cewar wata mata dake tsaye a tsakar gida a kusa da wata bukka.

Fulani Hausa Novel Complete

Jin shuru ba’a amsa mata bane yasa,ta bankada kofar bukkar ta shiga ciki.

 

A zaune take akasan bukkar hannunta rikeda zare da Allura tana dinke wani zani daya gama jin jiki.

 

 

Ganinta zaunen ne ya hassala matar,takai mata wani wawan duka me kama da barin makauniya.

 

Yarinyar seda ta wuntsila ta bugu da bangon bukkar.kan tayi wani yunkuri matar ta rufeta da duka,seda tagaji dan kanta ta kyaleta.

 

Cike da masifa matar tace.

 

“wlh abu bazaki sani hawan jini ba,dama kina jina ashe amman baki bani amsa ba kuma baki fito ba”.

 

Cikin wata siriruwar murya tace cikin kuka.

 

“inna Ramma don Allah kiyi hkr,wlh zanina ne ya gage nake dinkewa,kuma kinsan banida wani bare na sauya”

 

Bakinta inna ramma ta kaiwa duka,gamida cewa.

 

“Haka fa kika iya,baki zaizai kamar na uwarki,dallah wuce muje ki dauki talla ki fice”

 

Ba musu Abu ta dauki yagaggen zanin nata ta daura,ta fice zuwa tsakar gidan,gammo tayi ta dauki kwaryar furar ta fice tana share hawaye.

 

 

Inda sabo Abu ta saba da masifa da bakin hali irin na inna Ramma,dan haka tun kan ta isa dandalin ta share hawayenta.

 

Tana isa dandalin kamar kullum kawayenta,suka kama mata ta sauke furar.

 

Kamar kullum suka shiga hira ita da kawayenta,wanda hakan ya taimaka wajen yaye mata damuwarta.

 

Abu bata jima da zuwa ba,suka fara jiyo karar harbi.

 

Kan suyi wani yunkuri,suka hango wasu ayarin fulani sun nufosu da wani mahaukacin gudu.

 

Suna isowa suka shaida musu kowa yay ta kansa,dan barayi ne ke musayar wuta da yansanda.

 

Kan kace me dandalin ya kaure da guje guje.inda Abu ma baa barta abaya ba,da gudu ta nufi gida.

 

Har takai kofar gidan ta tuno masifa da balai irin na Inna Ramma in taji cewa ta baro mata fura adandali.

 

Dan haka juyawa tayi zuwa dandalin zuciyarta cike da fargaba.

 

Har takai dandalin a tsorace take,dan gani take karar kwanace ta dawo da ita dan dalin.

 

Koda ta isa dandalin ba kowa se wasu motoci da batasan kona su waye ba.

 

Yayin da gefe guda kuma gawarwakin mutane ne, akwance akasa ga wasu kuma anji musu ciwo suna kokarin guduwa.

 

 

Cike da karfin hali ta isa gurin kwaryarta wacce ke ajiye a inda ta barta,dukawa tayi ta dauka cike da tsoro ta nufi hanyar gida.

 

Sede me tana fara tafiya,taji wani sabon harbin na tasowa,

 

agigice ta yarda kwaryar furar,kamar ance ta waiga.

 

Wani saurayi ta hanga,kwance akasa yana jan jiki kafarshi se zubar da jini takeyi,kuma daga dukkan alamu makahone,dan ta lura da glass a fuskarshi, kuma se laluben hanya yakeyi.

 

Muryarshi ta jiyo yana fadin.

 

“Ataimakamin don Allah”

 

Da zata gudu,se tausayinshi,ya kamata,ta juya zuwa gurinshi da gudu.

 

Isarta gurinshi yay daidai,da sake harbo bullet zuwa gurinshi,wanda hakan yaba bullet din damar shigewa kafar Abu wacce isarta gurin kenan.

 

Wata Razananniyar kara tasaki,tayi sama ta fada kan saurayin sumammiya.

 

Muje zuwa

 

 

Surbajo for life.

 

 

*SURBAJO SABON*

*SALO*

 

 

 

 

*Zahra Surbajo*

 

 

 

*korafinku ya amsu,surbajo sabon salo yadawo typing,memakon audio,so zuwa nan gaba zan ci gaba da posting,*

 

 

*Dedicated to Inna Ibrahim kime,alkhairinki gareni baze faduba,Allah ya albarkaci gidanki da zuriarki,da dukkan alkhairi,surbajo ta sadaukar miki da wannan littafin badan ta biyaki ba,sedan dake acikin zuciyarta*

 

 

*2*

 

 

 

A gigice saurayin yayi baya yana ihu jin an fado masa akai,

 

Hannu yasa yana laluben inda yaji alamar mutum din.

 

A hankali yasa hannunsa yana shafa jikinta,hakanne ya bashi tabbacin mace ce akwance akasan.

 

Yana tsaka da tunanin ko wacece,yansanda suka karaso gurinshi.

 

A gigice sukai kanshi suna fadin.

 

“Sannu ranka ya dade,dafatan de bakaji ciwo ba?”

 

Da kyar ya basu amsa da cewa,

 

“Da sauki,”

 

Ayko dukawa sukai suka dauke shi,waigawa yayi yana kallon baya kamar wani me gani,ahaka har suka shige dashi cikin mota.

 

Suna shiga,suka ja motar da gudu suka nausa kan hanya dashi dauke da jiniya.

 

 

Wayyo Abu a haka suka barta agurin,har zuwa wayewar gari.

 

Inna ramma tunda ta sami labarin abinda ke faruwa,ta kulle gidansu,batare da tayi tunanin abu ba.

 

Koda gari ya waye,jamaa suka fito,gawarwakin barayin sukaci karo dasu.

 

Se abu dake kwance can gefe rai a hannun Allah.wacce sanyin asuba yasa ta farka adole.

 

Kowa ya jimama lamarin daya samu abun,

 

Suna nan tsaye inna ramma ma ta iso,da kwaryarta ta fara cin karo a fashe ayko cikin fushi tace.

 

“matsiyaciya makira,wato sabida ranta beso tallan ba yasa ta fasamin kwarya abanza”

 

Karasawa tayi gurin data hangi abun a kwance jamaa sin zagayeta.

 

Dukawa tayi ta fincikota,da karfi tana fadin.

 

“tashi muje gida makira,yau wlh senaci ubanki”

 

Duk yadda mutanen dake gurin sukaso ganar da ita amman taki bi takansu.

 

Haka taja abu wacce ko tafiya bata iyayi,sabida kumburin kafa da azabar da kafar takeyi.

 

Ahaka tajata zuwa gida tana masifa.

 

Bayan wucewarsu ba jimawa yan sanda suka dawo da motocin daukar gawa,suka kwashe,gawarwakin dake gurin suka wuce.

 

Abu suna isa gida,inna ramma ta wurgar da ita tsakar gida,tana ci gaba da fada.

 

“Abu bazaki kasheni ba,wlh baki isa ba,me namiki da kikeson ganin bayana?in banda rashin imani meyasa kika fasamin kwarya”

 

Abu ba baka se kunne,azabar da kafarta ke mata kadai ta isheta,kuka kawai take tana girgiza kai alamar Ba haka bane.

 

Kikkifamata mari tayi,sannan tabi takan kafarta ta wuce.

 

Ihu abu tayi batasan sanda ta saki fitsari a zaune ba.

 

“kadan kika gani,wlh sena tabbatar da kin koma gurguwa,tunda baki da imani,”.

 

 

Kuka kawai abu take,tama rasa abunyi ji take kamar zata mutu.

 

 

Wasa wasa seda abu ta kwashe sama da sati guda inna ramma na gana mata azaba.

 

Abu har addua take akan Allah ya amshi rayuwarta dan azabar tafi karfin kanta da tunaninta.

 

Duk wani aykin gidan ahaka abu takeyinshi,jan duwawu take yayin tafiya,dan bata iya mikewa.

 

Nasan me karatu zeso yaji shin abu bata da ubane?

 

Abu nada mahaifi araye kuma zaune suke gida guda dashi,sede baya iya morar kansa ma bare wani ya moreshi.

 

Sakamakon cutar shanyewar barin jiki dayake fama da ita.

 

Duk abinda ake mata yana gani yana ji sede vaze iya hanawa ba,dan ko motsi baya iyawa.

 

Komai abu ke masa,inna ramma bata ko bi takanshi,neman kudinta kawai tasa agaba.

 

Yauma kamar kullum,abu zaune tasa kafarta agaba tana kallon yadda ta koma,wasu hawaye ne kebin idonta,na tausayin kanta,ganin kafar tata gab take da rubewa,

 

Gashi magani kona naira guda bata taba sha ba,se azaba da takesha.

 

Share hawayenta tayi,ta shiga tunanin rayuwarta,sanda mahaifiyarta keda rai.

 

Tabbas tasan da tananan bazata barta cikin wannan azabarba.

 

Ganin tunanin beda amfani ne yasa ta rarrafa ta nufi gurin mahaifinta,

 

Gyara mishi kwanciya tayi,ta goge mishi miyau din daya zubo masa,

 

Tana hawaye shima yanayi,na tausayin junansu.

 

Inna ramma ce ta kwala mata kira.

 

Jiki na bari ta nufi tsakar gidan dan gudun kar tai laifi.

 

Tana fita innar tace.

 

“dan kan ubanki,dauko turmi da tabarya ki kirba furar nan,dan wlh na gaji da ciyar daku bana morarku,ki kirba ki fitar da ita dan dalin”

 

Ba musu Abu tayi kamar yadda ta bukata,tanayi tana kuka har ta gama.

 

Tana gamawa,ta shirya,ta dauki kayan tallan,akanta ta rarrafa.

 

Da yake dare ya fara,ba kowa ya lura da ita ba har ta isa dandalin.

 

Kowa tausayinta yakeji,dan abar tausayi ce.

 

Zamanta ba jimawa,sega wata mota kamar an turo ta.

 

Da gudu tayo kan abu tana parking,wasu maza guda biyu suka fito daga motar.

 

Kan kowa ya ankara sun dauki abu cak sun jefa a mota sun ja da gudu sun bar gurin.

 

Ihu mutanen Dake gurin suka sa suna bin bayan motar,da gudu,sede basu cimmusu ba dan tuni sun basu rata.

 

Wai wacece abu ne,kuma menene matsayin inna Ramma Agurinta.

 

 

Muje zuwa

 

 

surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*SURBAJO SABON*

*SALO*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

 

 

 

*ZAHRA SURBAJO*

 

 

 

*Don Allah aduk sanda kuka tunoni kusani a addua,ina da wata bukata gurin Allah,don Allah ina barar adduarku😭Allah kada kadorawa duk wani musulmi abinda yafi karfinshi Ameen*

 

 

*Dedicated to Innah Ibrahim Kime*

 

 

*3*

 

 

 

Abu ihu takeson yi amman ta kasa sabida tsananin,tsoro.

 

Tuni ta jima da yin fitsari ajikinta,ga mamakinta,suna barin nahiyar garinsu kartin da suka sato ta suka saketa,a motar wanda da rike suke da ita.

 

 

Tafiya me dan tsayi sukayi,kamin suka shigo birnin kaduna,wata anguwa,me kyawawan ginegine suka shiga da ita.

 

Wani gida suka shiga da ita me matukar kyau.

 

Suna parking suka umarceta data fito.

 

Duk yadda taso fitowa ta kasa,sabida tsamin da kafarta tayi,dan haka kuka tasa musu gwanin ban tausayi.

 

Tsayawa sukayi suna tunanin abun yi,kamar daga sama suka jiyo wata sassanyar murya daga bayansu yana fadin.

 

“ku bari zan daukota,kuje kawai abunku”

 

Cewar wani kyakkyawan saurayi daya nufosu.

 

Ba musu suka matsa masa ya karasa bakin motar inda abu ke zaune tana kuka.

 

 

Dan rusunawa yayi yana murmushi yace.

 

“sannu da zuwa princess”

 

Kauda kai abu tayi tana ci gaba da kukanta,dan tsoro ne fal cikinta,ko motsin kirki batayi,gudun ko akwai bindiga ajikinsu su harbeta.

 

Hannu yasa ahankali ya daukota gaba dayanta daga motar ya nufi cikin gidan da ita.

 

Sosai gidan yayiwa abu kyau,sede tsoron da take ji ya hanata kalle falon da suka shiga.

 

 

Wani daki na musamman ya shiga da ita,inda yay mata masauki,akan gado.

 

Ajiyeta yayi sannan ya nemi guri nesa da ita ya zauna,yana murmushi.

 

Abu kallon shi tadan saci yi,inda ta samu shima ita yake kallo,da shanyayyun idanuwanshi.

 

Cikin kuka abu tace cikin muryar ta ta fulani.

 

“do Allah do Annabijo,kado ka maidani wuro,aradun Allah,ko jikka guda bani da,bare ka sace”ta karasa maganar cikin kuka.

 

Sosai yanayin maganar tata taba saurayin dariya,dan haka cikin dariya yace.

 

“ba abinda zan miki princess illa maganin kafarki na daukoki nai miki, Sunana Haisam Abu Marafa,ni dan kaduna ne,kawai na tausaya miki ne”ya karasa mgnr yana murmushi.

 

Abu binshi da ido tayi tanaso ta karanto iya gaskiyarshi daga idonshi.

 

Dakyar de ta bude baki tace.

 

“yo in hakkane a ina kika shamo labarina?”

 

Murmushi yayi kamim ya bata amsa da cewa.

 

“gurin me garin garinku,kinga mubar mgnr,ki tashi kiyo wanka kici abinci kiyi sallah,dan zuwa dare,zan fara aykin dayasa na daukoki”

 

Yana kaiwa nan ya mike ya nufi toilet,ya hada mata ruwan wanka,sannan ya dawo ya dauketa,yakai ta toilet din,ya nuna mata yadda zatai amfani dashi,sannan ya fito yabata guri.

 

Abu dakyar tsoron da takeji yabata damar yin wankan,

 

Koda ta shiga ruwan wankan dakyar ta gama sabida azabar da kafarta take mata,ahaka de ta daure tayi tana kuka.

 

Bayan ta gama alwala ta daura,tawul din daya nuna mata taja ta daura,sannan ta yafo wani,ta rarrafo zuwa wajen toilet din.

 

Azaune ta sameshi yana danna wayar hannunshi.

 

Rakubewa tayi gefe cike da tsoro da kunya.

 

Mikewa yayi ya bude maajiyar kaya na dakin.

 

wata doguwar riga me haΙ—e da wando ya dauko mata ya mika mata,sannan ya fice daga dakin

 

 

Saka kayan tayi,abun mamaki,daidai size dinta ne.

 

Tana gamawa ya shigo dakin,dauke da kulolin abinci ya ajiye agabanta.

 

Da kyar ta iya bude baki ta rambayeshi inane gabas,domin tanaso tai sallah.

 

Nuna mata yayi,gamida miko mata,hijab,da darduma,tayi sallar.

 

Bayan ta idar abinci ya bata taci,shima seda yay mata jan ido kamin ta bude baki taci abincin.

 

Tana gamawa,ya kwashe kayan ya fice dasu.

 

 

Be jimaba ya dawo,dakin,ba abinda yace mata,ya duka ya dauketa ya fice da ita.

 

Saman gidan taga ya haura da ita.tsorone me tsanani ya sake kamata.

 

Wani daki me kama da asibiti ya shiga da ita.

 

Kan gado yaje ya kwantar da ita.

 

Sannan ya mata allurar bacci,wacce dakyar, Abu ta bari akayi mata.

 

 

Mintuna kadan baccin ya dauketa.

 

ayko beyi kasa aguiwaba,ya debo kayan ayki,yashiga yimata duk abinda ya dace.

 

Sannu a hankali,yake gudanar da aykin kafar ta abu,har ya gama,batasan anyiba.

 

Shiko Haisam dakyar ya gama aykin amman kuka ya gama cin karfinshi na tausayin abun.

 

Yana gamawa,ya dauketa daga dakin zuwa wanda yakaita da farko.

 

kan kujera yaje ya zauna,yana jiran farkowarta,duk tausayinta ya gama cika zuciyarshi.

 

 

Muje zuwa

 

 

Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*SURBAJO SABON*

*SALO*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

 

 

 

 

*ZAHRA SURBAJO*

 

 

 

*Dedicated to Inna Ibrahim Kime*

 

 

*4*

 

 

 

Abu bacci take cikin kwanciyar hankali,dan haka bata farkaba se da garin Allah ya waye.

 

Haisam kwana yayi azaune yana gadinta,dan beso ya gusa ko kadan daga gurinta.

 

Tana farkawa,taji wani radadin azaba daga kafarta,dan haka bata san sanda ta kurma ihu ba.

 

Arazane Haisam ya matso kusa da ita,dan jin abinda ya faru.

 

“princess me ya sameki,pls fadamin me kikeso?”ya tambayeta cikin kulawa.

 

Abu ko kafar ta rike tana kuka tace.

 

“kado shifa timakko,ba she anyi azaba ba,Aradun Allah ji nake Rai na na lilo”ta karasa maganar cikin kuka.

 

Murmushi yayi daya kawata kyawun fuskarshi,sannan yace cikn rarrashi.

 

“Ayya,to kiyi hkr,ba abinda ze sami ranki,zakiji sauki insha Allahu kinji ko”

 

Kai ta gyada masa tana ci gaba da kukanta.

 

Allurar rage radadi yay mata,ayko baa jimaba taji saukin azabar.

 

Taimaka mata yay tayo alwala tazo tai sallah a kwance,dan bazata iya yi azaune ba.

 

Sannu a hankali Haisam keba Abu kulawar duk da ta dace.

 

 

Cikin sati biyu sega Abu ta fara takawa,kafa tayi kyau,

 

Ita kanta Abun tayi wani kyau na musamman sakamakon hutun wahalar data samu.

 

 

****************

*RIJANA,KAUYEN SU ABU*

 

Acan Kauyen su Abu kuwa,Agigice akaje har gida aka sanar da inna ramma abinda ya faru,

 

Budar bakinta cewa tayi.

 

“ina fatan bada kwaryar furar tawa suka hada ba ko?”

 

Wanda ya dauko kwaryar furar ne ya sauke agabanta yace,”eh bada ita suka hada ba”

 

Wani murmushi tayi,sannan tace

 

“Ala raka taki gona,”

 

Kowa ya tausaya batan abu amman banda ita Ramman.

 

Mahaifin Abu ma hawaye kawai yake zubarwa dan de beda yadda zeyi ne yasa ya hakura.

 

*KADUNA*

 

 

Abuce rike da hannun haisam suna zaga cikin lambun gidan,kai da gani kasan yana koya mata tafiya ne,

 

Sun dan jima suna zagawa,Abu na kukan ita ta gaji,dole tasa Haisam,nema musu gurin zama acikin lambun.

 

Zamansu ba jimawa Abu tace.

 

“Aradu kado kina da kirki,ke yar aljannashe”

 

Murmushi yayi,sannan yace.

 

“Kirkin me nayi miki princess?”

 

Dariya tayi,akaro na farko tun zuwanta gidan,sannan tace.

 

“ke kado ki dena bata min shuna na,Abu ne sunana,fa”

 

Dariya shima yayi sannan yace.

 

“ok wato sunanki,Zainab kenan,shiyasa ake ce miki Abu?”

 

Murmushi tayi gamida share kwallar data zubo mata sannan tace.

 

“Innata ba Abu tasamin ba,dan ba sunana zainabu ba,Inna Ramma she,ta sanyamin sunan,sabida ashewarta shine sunan daya fi dacewa dani”ta karasa maganar tana share kwalla.

 

Tausayinta ne ya kamashi,cikin tausayawa yace.

 

“To wanne suna Innar taki tasamiki da har ya janyo aka sauya miki wani?”

 

“Inna ta tazo binni aykatau,lokashin da cikina,shine tayi ayki agidan wani mutum me mutunshi,yanada yaro,me kirki,dan yaron nashi shine yake kulawa da inna ma,in bata da lfy agidan nasu,to shine ta haifeni,agidan,kuma shi yaron shi ya amshi Haihuwata,to inna tayi alkawarin yimishi takwara in namiji ta haifa,to se Allah be nufa ba,ta haife mace,shine shi yaron da kanshi yasamin suna *SAMHA*,acewarshi tunda be samu aboki ba,to ya samu mata”

 

 

A hankali yasa hannu ya share wasu hawayen tausayinta da suka zubo masa,sannan yace.

 

“Kibani labarin ki mana naji”

 

Ba musu ta fara bashi labarinta kamar haka.

 

 

“Samha Adamu Rijana,shine cikakken suna na.

 

Mahaifina Malam Adamu Rijana,mazaunin garin rijana ne.

 

Matarshi daya,me suna fatima,wacce ta kasance inna ta.

 

sun jima da Aure Amman Allah be basu haihuwa ba,

 

hakan yasa Innata sa mahaifina kara Aure,ko zaa dace.

 

Dakyar Mahaifina ya amince da Batun,dan beson tashin hankali.

 

Ana haka se Allah ya hadashi da Inna Ramma,ya Aureta.

 

Tunda ya Aureta kullum cikin fada take acikin gidan da kowa,ko kadan Baffa na beson Hakan,haka itama Inna ta bataso.

 

Ana haka se Allah ya ba Inna ta ciki,murna sosai sukayi,duk da kasancewarsu fulani basu ki nuna farincikinsu ba.

 

Tunda Inna Ramma taji labarin ta dagawa kowa hankali acikinsu.

 

sabida damuwar Inna Ramma,Wata rana Baffa na yaje bayi wanka ya fadi,se daukoshi akayi.

 

Gaba daya barin jikinshi ya shanye,ko motsi bayayi.

 

Innata ce ke kulawa dashi,ga laulayin ciki,abinda zasu ci ma yafi karfinsu.

 

Hakanne yasa inna ta neman izinin Baffa na akan zata birni aykatau,dan tasamu takaishi Asibitin Birnin.

 

Baffa ya amince mata,dan haka kaninta ta nemo yazo ya kula mata da baffa kan ta dawo.

 

Shine taje birnin,Gidan Alhaji tasamu ayki,lokacin cikina nada wata shida.

 

 

Watanta hudu agidan ta haifeni,bayan kwana biyu ta nemi izinin tafiya,gida.

 

haka suka hada mata kayan arziki,tai musu sallama azuwan zataje ta dawo,lokacin dan Alhajin bayanan yaje karatu,shiyasa besan ta tafi ba.

 

Bayan ta dawo gida,afuskar babana ta fahimci farinciki. Ganin mi da yayi.

 

Dan haka,kwana tai da shirin kaishi asibiti washegari,sede cikin dare Inna Ramma ta shiga dakin innata ta sace duk abinda tazo dashi.

 

koda gari ya waye inna taga ba kudin sosai ta kadu,wanda hakan har hawan jini yasa mata.

 

 

Tsawon shekara Goma sha biyu aka kwashe ahaka,batare da anyiwa Baffa magani ba.

 

Ga inna ta cikin rashin lfy take kullum,kuma gaba ciwon yake ba sauki.

 

A wannan tsakaninne,innata ta bani labarin komai,daya faru abaya,inda tacemin,tayiwa dan Alhajin birni alkawarin aura masa ni,dan haka ko bayan ranta,inje in nemeshi.

 

 

Awannan lokacin innata ta kwanta ta mutu,rukona ya koma gun Inna Ramma har zuwa yanzu da nakeda shekaru goma sha hudu.

 

Ko ciwon kafata talla ta turani,gurin taimakon wani mutumi aka harbeni.

 

Ba irin azabar da bata gana min nida baffa na,wannan shine tarihina,kado,shiyasa nace ke yar aljannashe,dan kin taimakeni”ta karasa maganar cikin matsanancin kuka gamida dora kanta akan kafadarshi.

 

 

Hannu ya dora akanta alamu. Rarrashi,shima yana share hawayen tausayinta,

 

 

Muje zuwa.

 

 

Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*SURBAJO SABON*

*SALO*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

 

 

*ZAHRA SURBAJO*

 

 

*Dedicated to Inna Ibrahim Kime*

 

 

 

*5*

 

 

 

Sun jima suna kuka,kamin daga bisani,Haisam ya share mata hawayen ta.

 

Da kyar de ya samu tai shuru,sannan yace mata cikin rarrashi.

 

 

“shi alhajin birnin bata fada miki sunan shi ba?”

 

“ta fada min na manta ne”

 

Shuru yayi nadan lokaci sannan yace.

 

“to yanzu baba yanacan rijana kenan cikin halin rashin lfy?”

 

“eh yana can”

 

 

“to zuwa sati me zuwa lokacin kin sake samun sauki,semuje muzo dashi ay masa magani”

 

 

Sabida tsananin murna,Mikewa tayi tana tsallen murna.

 

Bin ta kawai yake da kallo yana murmushi,shi kadai yasan yanayin da yakeji game da ita,tausayinta yakeji sosai.

 

Cikin gida suka koma,

 

Sannu a hankali takejin sauki har,ta warke.

 

Dan haka yau suka shirya ita dashi,suka kama hanyar Rijana.

 

Da Azahar suka isa kauyen.

 

Ba wanda ya gane Abu akaf cikin kauyen,har ita kanta Ramma,bata ganeta ba.

 

Haisam ne ya gaisheta, sannan ya shaida mata abinda ke tafe dashi.

 

Cikin masifa ta fara balai.

 

“kazo ka sace abu ka kaita burni ka maida ita karuwarka,hakan be isheka ba,shine kazo ka hada da ubanta kai luwadi dashi ko?,to wlh dan burni kayi kadan”

 

Ran haisam in yayi dubu ya baci dajin mugayen kalaman da yake jifanta dashi,dan haka cikin fushi yace.

 

“duk yadda kikace hakane,kuma zan dauki baffa,ke baki isa ki hana ni yin hakan ba”yana kaiwa nan yakai dubansa gun,Abu yace.

 

“princess ina dakin baffan?”

 

Ba musu ta nuna masa,kai tsaye ya shiga dakin,se gani sukai ya fito dauke dashi a hannu.

 

Ihu da kururuwa ba irin wacce ramma batayi ba akan ya ajiye mata mijinta,amman yaki.

 

Ahaka ta bisu har mota,yan garinne suka tsaidashi suji ina ze kaishi.

 

Bayani yay musu,sanna. Abu wacce se lokacin suka ganeta tai musu karin haske.

 

Ba musu suka barsu suka tafi dashi inna ramma na ihu ba wanda yabi kanta.

 

 

Tunda yazo da Baffa birni,Asibitin garden city ya kaishi,acan aka dunga kulawa,dashi harde ya fara dawowa cikin natsuwarshi.

 

Shawara sauran likitocin suka bashi,akan ya fita dashi zuwa india zefi samun kulawa.

 

Haisam beyi wani tantama ba,yafara shirin fita dashi india.

 

Saida komai yazama ready,sannan ya kira Abu domin yay mata bayani.

 

“Princess ciwon baffa na bukatar akaishi kasar india inda zefi samun sauki,to na shirya tafiyar tsakanina dashi kawai,ke zaki koma Rijana har zuwa sanda zamu dawo”

 

Da sauri ta dago fararan idanuwanta tana kallonshi,baki na rawa tace.

 

“kado in na koma kauye inna zata kashe ni”

 

Murmushi yayi,sannan yace.

 

“bazata kasheki ba,kinji ko,in kuma baki amince ba,to ki nemi wani gida anan birnin ko makwabtan mune ki dunga yi musu aykatau kamin na dawo”

 

Hawayene kebin fuskarta kamar ruwa sannan tace.

 

“kado karsu siyar dani kan kadawo”

 

Sosai tausayinta ya kamashi,da da yadda zeyi da sun tafi tare,to lokaci ya kure,dan awa daya ta rage subar garin.

 

“ki ta Addua princess ba abinda ze faru da yardar Allah har mu dawo,in kuma bakison aykatau din ki koma rijana ze fi”

 

Da sauri ta girgiza masa kai tace.

 

“zanyi aykatau din”

 

“to taso muje ki zabi gidan aykin,dan anguwarnan suna fama da rashin masu ayki,da ace inada mata ne da se na barki tare da ita to banida ita dole tasa zaki aykin kan na dawo”

 

kai kawai take gyada masa,har suka fito zuwa gurin mota suka shiga yaja suka fice daga gidan.

 

Gurin Baffa yakaita sukayi sallama tukuna,da kuka suka rabu,sannan yajata zuwa rukunin gidajen masu kudi dake malali kaduna.

 

Duk kofar gidan daya nuna mata setace be mata ba,ahaka har suka iso wani dankareren gida,suna zuwa tace.

 

“wannan yayi,Allah yasa su daukeni kado katayani da addua”

 

Murmushi yayi sannan yace.

 

“me yasa kika zabi gidan da yafi kowanne kyau a layin?”

 

murmushi tayi sannan tace.

 

“taimakon mu da kayi nadan lokacine,da zaran baffa yasamu sauki,gida rijana zamu koma,to baffa beda sanaa,shiyasa na zabi wannan dan nasan zasu fi biyana albashi me kyau ta yadda zan tara naba baffa ya sani amakaranta”ta karasa mgnr tana share hawayenta.

 

Murmushi yayi sannan yace.

 

“kinason makaranta kenan?”

 

Kai ta gyada masa.

 

“to maza ki shiga ki tambaya Allah yasa su daukekin,”

 

Bude motar tayi ta fice ta nufi cikin gidan,megadi,tambayarta yayi gun wa zata,budar bakinta se cewa tayi.

 

“gun hajiya Babba”🀣

 

Ba musu ya barta ta shige cikin gidan.

 

Allah ne ya taimaketa ta gano kofar falon,dan haka da sallamarta ta shiga falon.

 

 

Wata hamshakiyar mata ta gani zaune ita kadai a falon rike da waya tana dannawa.

 

fadin kyau da haduwar matar da falon kauyancine.

 

da murmushi matar,ta amsa sallamarta.

 

zubewa Abu tayi agabanta baki na bari,tace.

 

“sannu hajiya babba”🀣

 

murmushi tayi sannan tace.

 

“yauwa yata,”

 

Shuru ne ya biyo bayan hakan can de hajiya tace.

 

“ya ta daga ina kike?”

 

Baki na bari tace.

 

“Daga rijana nake,nazo neman Ayki ne,don Allah karki koreni”

 

Murmushi tayi sannan tace.

 

“muna da maaykata,amman tunda kin hadani da Allah Zan daukeki inyaso daga baya asan aykin da zaki dunga yi,ina fatan da sanin iyayenki kikazo?”

 

“eh da saninsu nazo,yayanane ma ya kawoni,ngd bari inje in fadi masa nasamu”bata jira amsar hajiya ba da yake ba kai ta mike da gudu ta fice zuwa Gurin Haisam dake zaune a mota yana jiranta.

 

Ganin faraar fuskarta yasa ya gane ta samu aykin.

 

tana zuwa ko tace.

 

“kado nasamu ayki aradu,hajiyar nada kirki”

 

“to mungodewa Allah, princess,to dauki kayanki,zan wuce,kar muyi latti”

 

Jakar kayanta ta dauka,jiki asanyaye,

 

Cigaba yayi da mgn yace.

 

“duk wuya My Samha,ki rike mutuncin ki, ki zama me gaskiya, da hakuri, ga waya nan karama da kwai number ta aciki,duk sanda kika samu dama ki kirani”

 

Mika mata wayar yayi wacce batasan yadda zata danna ba.

 

Tana kallo yaja motar yana daga mata hannu,har yayi nisa.

 

Jiki asanyaye ta juya ta shige cikin gidan.

 

Tana shiga cikin gidan tajiyo wata zazzakar murya,tana kwalawa wani kira.

 

“Abban Samha,Abban Samha”

 

da sauri Abu takai dubanta,gun wanda ake kira din.

 

Tsaye yake,rike da sanda,ahannunsa,fuskarsa sanye cikin glass.yadda yake dogara sandar ne yayin tafiya, ya bata tabbacin makahone.

 

A gigice ta kure fuskarshi da kallo,take ta gano shi,

 

Makahon da gurin taimakonshi aka harbeta ne.

 

Muje zuwa

 

 

“Surbajo for life.”

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*SURBAJO SABON*

*SALO*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

 

 

 

*ZAHRA SURBAJO*

 

 

 

*Ya hayyu ya qayyum bi rahamatika astagis*

 

 

 

*kuyi hkr Allah bazan iya yin fiye da yadda nakeyi ba,sede duk sanda nake da time zanyi page biyu,ngd da kulawarku*

 

 

*Dedicated to Inna Ibrahim Kime*

 

 

*6*

 

 

A hankali take binshi da ido,duk inda akeson kyau yakai gurin.

 

Tana nan tsaye,taga wata matashiyar budurwa ta karaso gurin shi rike da wata leda,tana isowa gurinshi taji tace.

 

“Abban samha ina zakaje,da ranar nan haka,gashi masu rakaka basa nan,pls kadawo in suka zo seku fitan”

 

A hankali ya motsa bakinshi kamar beso yace.

 

“garden zani,ba wani guri ba”

 

Tana kallo budurwar ta rakashi hanyar garden din.

 

Jiki ba kwari ta nufi cikin gidan,hajiya na zaune a inda ta barta .

 

Da faraa ta sake tarbarta.

 

Guri ta samu dede kafar hajiya ta zauna tana tunanin Abban samha.

 

Hajiya ce ta katse mata shurun da cewa.

 

“yata ya sunanki,daga kuma ina kike?”

 

“sunana Abu daga rijana”abu ta bata amsa.

 

“yayi kyau sede babu wani ayki dazan iya baki,a yanzu amman Abban samha me gyaran dakinshi taje ganin gida,dan haka seki dunga gyarawa zansa delu meyi masa ayanzu ta nuna miki yadda akeyi kinji ko,sannan se kinyi hkr dashi dan yanada saurin fushi”

 

Murmushi Abu tayi sannan tace.

 

“ba komai hajiya zanyi duk yadda yakeso,insha Allahu,”

 

“Ba komai yata,Allah yasa mudace,in ya shigo zan tambayeshi ko nawa ze dunga baki albashin”

 

Godiya sosai Abu taimata har da kuka.

 

 

Matashiyar dazu ce ta shigo,da dan gudunta ta fada jikin hajiyar tana kukan shagwaba.

 

“to me kuma ya faru, iya rigima”cewar hajiya cike da kulawa.

 

Cikin muryar kuka,tace.

 

“Abban samha ne ya kwalamin sandar shi,akaina,dan kawai ina masa hirar kawata husna dake sonshi”

 

Dariya Hajiya tayi, sannan tace.

 

“to in banda abunki Jawahir,tun yaushe yake shaida miki beson zancan amman kinki denawa gwanda daya fara dukanki”

 

Se alokacin idon jawahir ya sauka kan Abu dake zaune akasa.

 

Tashi tayi ajikin hajiyan,tana murmushi tace,

 

“wow hajiya wannan pretty dinfa,yar waye?”

 

“Abu sunanta daga rijana,me gyaran dakin Abban samha ce kan furera ta dawo,dauketa kuje dakinki da ita,kamin anjima delu ta koya mata gyaran”

 

Cike da murna,jawahir taja jakar kayan Abu gamida rike hannunta suka nufi part dinta.

 

Suna shiga,ta hada mata ruwan wanka,Abu ta shiga tayi,gamida wanko kanta.

 

Koda tafito jawahir da kanta,ta gyara mata gashin kanta yayi kyau sosai,sannan tai mata kwalliya cikin kankanin lokaci tayi fess da ita

 

Wata doguwar riga ta bata tasaka mekyau,da tsada,itade abu kirkin jawahir sosai ya burgeta.

 

Suna gamawa,jawahir tace mata.

 

“ke bakya hira ne?ajinki nawa a makaranta,meye sunanki na gaskiya?”

 

Murmushi Abu tayi sannan tace.

 

“ina hira mana,amman bana zuwa mkrnt,Abu sunana”

 

“wanne irin Abu ko dadin ji,zainab kenan ko?”cewar jawahir tana dariya.

 

Murmushi Abu tayi tace.

 

“Sunana na gaskiya *Samha Adamu Rijana*”

 

 

“what!!!!sunanki samha?”jawahir ta tambaya cike da zumudi.

 

“Eh sunana samha”

 

 

“wow kice Abban samha ya samu ya asama”cewar jawahir tana dariya.

 

Itade Abu murmushi kawai tayi.

 

 

Kiran sallah ya katse hirar suka tashi sukayi sallah.

 

Delu ce ta shigo taja Abu part din Abban Samha domin ta koya mata aykin gyaran part din.

 

Koda suka isa,dakin hoton wata kyakkyawar jaririyane,zagaye da part din ta ko ina,ko baa fada mata ta fahimci itace samhan tashi.

 

Cikin lokaci kankani ta fahimci yadda ake gyara ko ina na dakin.

 

Delu ta rigata fita,ita ta tsaya kara gyara labule,tana gama gyarawa,ta juyo zata fita.

 

Atsaye yake bakin kofar yana kallonta,fuskarshi sanye da glass hannunshi rike da sanda.

 

Adan tsorace,Abu ta duka tace.

 

“Sannu Abba”

 

 

Hannu ya mika yana lalube yace cikin dakakkiyar murya.

 

“wacece ke”

 

Abu arude take dan haka baki na bari tace.

 

“Samha ce”

 

“what!!,samha daya ce a duniya,itace tawa,so kice iyayenki su sauya miki suna,dan wannan Abban samha ya rigasu”

 

Abu da rarrafe ta rarrafa tafice daga dakin batare daya san ta fitan ba,kasancewarshi wanda baya gani.

 

Da haki ta samu ta karasa dakin jawahir.

 

Koda jawahir taganta akidime tambayarta abinda ya faru tayi,ba musu,Ta kwashe komai ta fada mata.

 

Dariya jawahir tashiga yimata harda kwallah.

 

Tun daga Ranar Abu basu sake haduwa dashi ba.

 

Ga hajiya kullum cikin yimata kirki take ko kadan batason damuwarta,

 

Yau kamar kullum Abu taje gyaran dakin,ta gama komai,seta shiga toilet dan ta gyara ayko kamar jira tana shiga ta yanke jiki ta fadi.

 

Abu uwar kyankyami,koda ta tashi kyamar fita tayi da kayan.

 

Dan haka tubesu tayi tayi wanka,abinta,tawul ta daura ta yafa wani akanta,sannan ta wanke kayanta a toilet din.

 

fitowa tayi domin tabi ta kofar baya taje ta shanya kayan tunda tasan Abban Samha baya nan.

 

Tana fitowa,ta sameshi zaune akan kujera,jin motsinta ne yasa ya juyo da sauri,yana lalube da sandar hannunshi.

 

Abu ko agigice ta saki kayan hannunta,duk ta gigice,can kuma ta tuno makahone seta natsu abunta,ta dauki kayan ta fice daga dakin.

 

Shiko ci gaba da lalubawa besan ta fice ba.

 

 

Yau jummaa,kowa na gidan taga se shiri yake,yayinda itama taga an bata sabuwar atamfa me kyau.ance tasaka.

 

Jawahir ta tambaya.

 

“jawahir meke faruwa, ne yau agidannan”

 

“Wlh Abban Samha ne yake amarya yau shine muke shirin tayashi murna,danma lalurar shi tasa beson taron bikin.”

 

“Allah sarki Allah yasanya Alkhairi,amman duk wacce ta aureshi,zata samu lada”

 

Daga haka wanka tayi ta shirya itama abinta suka nufi part din hajiya.

 

Acan taga yan uwansu se zuwa taya murna sukeyi,

 

Har dare baki basu dena shigowa ba.

 

Itade Abu jiran akawo amarya tai tayi amman Baa kawo ba,dan haka dakinsu ta wuce dan tai wanka ta kwanta.

 

tsawon sati uku kenan da daura Auren Amman ba a kawo amarya ba.

 

Yaune Abu ta ciro wayarta taba Jawahir tace ta kunna mata ta kira mata kado.

 

Ba musu Jawahir tayi kamar yadda ta bukata,ayko kiran farko ya dauka.

 

Cikin tattausar murya yace.

 

“haba princess meyasa se yau kika nemeni,baffa nataso yay mgn dake amman kin kashe wayar”

 

Cikin zumudi Abu tace.

 

“Wayyo kado yi hkr,aradu ban iya bane,yakuke kai da baffan?”

 

“Baffa ya samu sauki sosai,cikin satin nan muke sa ran dawowa,me kika tanadar mana?”

 

dariya tayi kamar yana kallonta tace.

 

“komai ma Kado kaso zan tanadar maka,”

 

“Allah princess,to inde hakane girki me dadi nakeso kimana”

 

“ba damuwa zanyi muku kado,bari naje gurin Abban samha ya bani albashina se nai muku”

 

“Waye Abban samha kuma princess,banason shige shige fa”

 

“wlh kado agidan nan yake,amman bansan matsayinshi agurinsu ba,shine de akace ze biyani albashina”

 

“ok to badamuwa amman ki kula da mutuncinki kinji ko”

 

Da haka sukayi sallama akan Ze kirata anjima in ya je gun baffa a asibiti

 

Suna gama wayar,ta mike ta nufi gun Abban samha.

 

Da sallamarta ta shiga dakin.

 

Zaune yake rike da wayarshi,wacce gama amsa wayarshi kenan ta shigo dakin.

 

Dukawa tayi,agabanshi tace.

 

“sannu Abban samha”

 

be kulata ba illa ma kishingida da yayi akan kujera.

 

Bata damuba taci gaba da mgn.

 

“Abban Samha dama kudin aykina nakeso ka bani zanyi amfani dasu”

 

 

Cikin fushi yace.

 

 

“tashi ki bani guri ni na daukeki aykin dazaki zo amsar kudi”

 

Jiki na bari ta tashi tabaro dakin tana kuka.

 

Dakinsu ta wuce tana kukan, bakin ciki.

 

duk yadda taso ta daure ta kasa.

 

Da daddare wajen karfe tara jawahir ta shigo dakin tace mata.

 

“pretty kije Abban samha na kiranki”

 

Dakyar ta mike jiki ba kwari ta nufi dakin nashi.

 

Muje zuwa

 

 

surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*SURBAJO SABON*

*SALO*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

 

 

*ZAHRA SURBAJO*

 

 

*Masoya abun alfahari,ina sonku koda yaushe,*

 

 

*Dedicated to Inna Ibrahim Kime*

 

 

*7*

 

 

 

Da sallamar ta ta tura kofar dakin ta shiga.

 

Zaune yake inda ta barshi,dan haka daga daidai kafafuwanshi ta samu guri ta zauna daga kasa.

 

Cikin dasasshiyar murya dake nuna Alamun tayi kuka tace.

 

“Abba gani,jawahir tace kana nemana”

 

Dan gyara zama yayi sannan yace.

 

“me yasamu muryarki”

 

Shurutayi ta kasa bashi amsa,be damu ba yaci gaba da fadin.

 

“naga alama can gidanku a sangarce kike,to nan bazaki mana ba,kudi zan baki 50k nasan zasu isheki,Amman Bazan juri iyashege ba.”

 

Dan farinciki kafafunshi ta rike tana ta masa godiya.

 

Kudin ya dauka ya bata,tana amsa ta ruga da gudu dakinsu.

 

Tana shiga ta samu jawahir na shirin bacci,ayko kanta ta fada tana fadin.

 

“gobe se kasuwa,kaddo ze dawo dole muyi masa girki me dadi”

 

Dariya jawahir tayi tace

 

“tofa,waye kado kuma,Samha”

 

Dariya itama tayi sannan tace.

 

“yaya nane”

 

“Ah to dole mu shirya tarbar shi tunda yayanmu ne”cewar jawahir tana dariya.

 

Ranar Hana jawahir bacci Abu tayi tana ta taya ta lissafin abinda zata siya da kudin.

 

Washe gari,gurin Hajiya Abu taje ta shaida mata,yayanta zezo.

 

Ayko sosai Hajiya ta tayata murna,dan Abu nada muhimmanci agurin Hajiya.

 

Haka suka je kasuwa ranar,jawahir taci yawo kamar kafarta zata tsinke dan yawo.

 

Haka suka zo suka hada duk abinda sukeson amfani dashi,

 

 

Yau tun safe Abu tai waya da Haisam ya shaida mata yana hanyar zuwa.

 

Wayyo Abu rasa gurin sa kanta tayi.dan farinciki.

 

 

Da laasar ya shigo,gidan,lokacin Jawahir batanan sun fita ita da Abban samha,daga Abu se Hjy.

 

Megadi ne yay masa jagoranci zuwa sit room din gidan kamar yadda hjy ta bada umarni.

 

Iya kyau haisam yayi kyau,ba dan kadan ba,kallo daya zaka masa kasan yana da kyakkyawar muamala da naira.

 

Gurin hjy Abu taje,ta nemi izinin fita,zuwa gurinshi.

 

Hjy bata hanata ba, amman ta mata fadan sanin darajar budurci,se fatan adawo lfy da tai mata.

 

Abu jiki na bari ta nufi sit room din dan ganin,Haisam.

 

Abakin kofa ta tsaya tayi sallama da sanyayyar muryarta.

 

Daga ciki ya amsa mata.

 

Dakyar ta shiga cike dajin kunya.

 

“oyoyo my princess,i missed you so much,”cewar haisam dake zaune yana kallonta.

 

A hankali ta bude idonta ta saukeshi akan nashi,

 

Tsigar jikinta ce tayi wami mugun tashi,sanda tai Arba da irin kallon da yake mata.

 

A hankali ta taka zuwa kusa da kujerar da yake,kai domin ta zauna.

 

Carab taji anrikota ta baya.

 

Kamin tai wani yunkuri ya dorata kan cinyar shi.

 

Kunya in akwai ta dubu Abu tajita,ganinta zaune kan cinyar haisam.

 

Kokarin mikewa takeyi ya hanata,dan haka sunkuyar da kai kasa tayi.

 

Dago kanta yayi yana karewa fuskarta kallo,runtse ido tayi,tana murmushi.

 

Cikin salon kwarewa,yace mata.

 

“princess kinyi kyau sosai kinyi girma kuma,me suke baki ?”

 

Kara sunkuyar da kai tayi,tana murmushi.

 

Dakyar de tace

 

“sannu kado,ina baffa shi bakazo dashi ba?”

 

Gefen fuskarta ya shafa sannan yace.

 

“Baffa nacan yace se next month ze dawo,ni kuma bazan iya jurewa banzo naganki ba”

 

Murmushi tayi sannan tace.

 

“kaji Baffa da samun guri ko kado”

 

Ahankali ya tallafo fuskarta dede tashi,ya rada mata yana sinsina wuyanta.

 

“samun guri ay abu ne me kyau princess”

 

A hankali da dabara ya dora bakinshi akan nata.

 

Kissing dinta yake ta yadda dole ya daga mata hankali,sakin jiki tayi.

 

Shiko yaci gaba da kissing bakinta kamar sweet.

 

A hankali,ya dora hannunshi kan boobs dinta,masu kyau da daukar hankali,dan duk da karancin shekarunta tana kira me kyau.

 

Kokarin cire mata riga yake itako ta rike iya karfinta.

 

Kuka tasa mishi dole ya kyaleta ya koma rarrashi.

 

Ammar furr taki yin shuru.

 

Rasa abunyi yayi,dan haka tsarabar daya kawo mata ya ajiye,ya mata sallama ya tafi.

 

Ta jima zaune tana takaicin abinda haisam yay mata taci kukanta ta koshi sannan ta mike ta fito daga sit room din.

 

A tsaye taga Abban samha,Ajikin wata mota me kyau, inda take yake facing dan haka gaba daya ta firgice ta rasa natsuwarta.

 

Zuwacan ta tuno ay makahone,dan haka cib ta natsu tazo ta wuceshi batare daya ganta ba.

 

Haka ta wuni sukuku,ta rasa abinda ke mata dadi,

 

Koda dare yayi takaiwa Abban Samha tea dinshi bata cikin walwala.

 

Tana ajiyewa,ta juya domin baro dakin,amman me se ji tayi ya rukota.

 

Dama akan gado yake zaune,mikewa tsaye yayi,ya kamo kwankwasonta,ya mannata da jikinshi.

 

wayyo Abu sabida tsabar tsoro ji take kamar tai fitsari a wando.

 

A hankali,ya rada mata akunne.

 

“Kin jima kina wahal dani Samha,pls ki barni iya haka kinji ko”cewar Abban samha da Abu ke kallon abun kamar film.

 

Kokarin kwacewa take daga rukon da yay mata,amman ba hali.

 

Karshe ma kan gado ya jata suka fada.

 

se mutsu mutsu take,nason guduwa shi kuma yaki sakinta

 

 

Haka ya dunga luguiguita ta,har seda tai laushi,Ita tsabar tsoro da mamaki ma sun hana Abu kwace kanta a hannunshi.

 

Sosai ta godewa Allah da be kwance mata zani ba.

 

Duk yadda taso kwace kanta ta gudu abun yaci tura,dole ta kwana adakinshi vadan ranta ya soba.

 

Da kuka tabar dakin da Asuba.

 

Dakinsu taje tai Sallah sannan ta nufi dakin Hajiya,domin ta sanar mata,gudun kar wataran ya cuceta.

 

Akan abun sallah ta samu hajiya tana jan carbi.

 

da gudu ta karasa jikinta tana kuka.

 

A gigice hajiya take tambayarta,abinda ya faru.

 

Cikin kuka Abu tace.

 

“Hajiya don Allah ki jawa Abban Samha kunne Wlh jiya sani yayi na kwana adakinshi,ni kuma ba yar iska bace wlh,”ta karasa maganar tana,kuka.

 

“Taya kike tsammanin Hajiya,Zata iya Haram tawa Haisam Princess dinsa,Abban Samha Samhar sa,Dan Alhaji Abun sa?”

 

Tajiyo wata murya daga bayanta,na jefo mata,tambayoyin masu kama da zubar ruwan sama.

 

 

Muje zuwa

 

Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*SURBAJO SABON*

*SALO*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

 

 

 

*ZAHRA SURBAJO*

 

 

 

*Fans masu son hira dani,ta whatsapp,kuyi hkr don Allah,abun da yawa ne,ga groups ga inbox rasa wanda zaka kula kakeyi,shiyasa amma muje instagram can yafi sauki ba mutane sosai,@Zahra_surbajo1,ngd*

 

 

*Dedicated to Inna Ibrahim Kime*

 

 

*8*

 

 

 

A razane Abu ta dago kanta tana kallon me maganar.

 

 

Agigice ta mike tsaye tana kallonshi Haisam ne.

 

Murmushi yay mata,gamida karasa shigowa falon,ya samu guri ya zauna.

 

Tsaye Abu take tana kare musu kallo,ganin hajiya na murmushi shima Haisam din haka.

 

“me ke faruwane dani,kumin bayani,kado taya kasan gidan nan har kasamu damar shigowa da asubar nan,waye kai ne?”Abu ta tambaya cikin karaji.

 

A hankali ya taso ya karaso gabanta,yana murmushi yace.

 

“Princess,kuma Samha,nasan zaki yi wannan tambayar,shiyasa na zabi yau amatsayin Ranar baki Amsa”

 

Ja da baya tayi,cikin fushi tace.

 

“waye kai?fadamin in sani”

 

 

“Nine Haisam Abu Marafa,kuma nine Abban Samha na gidan nan,kuma nine wannan Dan Alhajin birnin da ummanki tabaki lbr,hajiya itace mahaifiyata”

 

Murmushi Abu tayi na takaici sannan tace.

 

“Kai a yan renin wayau ma babbane,taya zaka zama mutum uku alokaci guda,wannan renin wayan naka be amsu ba”

 

Be kulata ba,illa ciro glass dinsa a aljihu da yayi yasa a idonsa,da yake glass din babbane,ya mamaye rabin fuskarshi,take yanke yakoma Abban samha.

 

A razane Abu taja Baya,tana shirin faduwa.

 

Rukota yayi yana murmushi,ya cire glass din yace.

 

“ki kwantar da hankalinki,mu ba cutarki mukai niyyar yi ba,ni me kaunarki ne,fiye da tunaninki,ki zauna kiji ko waye nidin”

 

Jiki asanyaye ta zauna tana ware ido

 

Hajiya ce ta janyota jikinta tace.

 

“Samha ki kwantar da hankalinki,haisam me kaunarki ne,ni shaidace kuma ni na haifeshi,shiyasa na goyi bayan auranku keda shi har aka daura”

 

A razane ta dago tana duban hajiya tace.

 

“dawa aka dauramin Auran?”

 

“Dani aka daura miki Aure Samha”cewar haisam yana murmushi.

 

Mikewa tayi afusace tace.

 

“Akan wanne dalili zaka Aureni bada sanina ba,Inna ta tace dan Alhajin birni zan Aura,me yasa zaka Aureni me yasa nace”ta rushe da kuka.

 

“Sabida shine dan Alhajin birnin,”cewar hajiya dake zaune.

 

Da Sauri ta waiga gurinta tana kallonta,

 

Zaunar da ita hajiya tayi,sannan suka fara bata tarihin su kamar haka.

 

 

*ALHAJI ABU MARAFA*

 

 

Shine mahaifin Haisam,

 

Alhaji Abu su biyu iyayensu suka haifa shi da yayanshi,me suna Lawal.

 

Da yake akwai tazara tsakaninsu,da wajen shekaru goma,shiyasa Abu ke mutunta lawal.

 

Bayan rasuwar mahaifansu,lawal shi yaci gaba da kulawa da Abu da karatun shi.

 

 

Haka yake masa duk abinda uba kewa yayansa.shiyasa shima Abu ke masa biyayya kamar dansa.

 

Alhaji lawan nada mata daya hajiya Lanti,

 

Hajiya lanti irin matan nanne masu shegen son abun duniya,shiyasa Abu be jin dadin zama da ita dan tasa mishi ido.

 

Alhaji lawan da yake yana da nasibi akasuwancinshi shiyasa yakeda rufin asiri,

 

Gida ya siyawa Alhaji Abu,sosai hakan ya bata Ran Lanti.

 

Awannan lokacin Alhaji Abu ya Auri hajiya wacce sunanta na gaskiya khadija.

 

Tunda ya Auri khadija hajiya lanti ta dauki karan tsana ta dora mata,

 

lokacin yayan lanti biyar duka mata,burinta ta haifi namiji,to Allah be nufa ba.

 

Sanda khadija ta tashi haihuwa se ita Allah ya bata Namiji aka sa masa haisam.

 

Sosai bakin cikin hakan ya bayyana karara ga hajiya Lanti.

 

Bata da yadda zatayi dole ta hakura.

 

Bayan haihuwar Haisam Da shekaru goma sha biyar sannan khadija ta haifi,jawahir,

 

Lokacin haihuwar jawahir ne hajiya lanti ta haifi ya mace itama,me Suna Khairat.

 

Tunda hajiya lanti taga ta sake haihuwar mace,tace taba Haisam auran Khairat ko bayan Ranta a daura Auran.

 

 

Muje zuwa

 

 

Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*SURBAJO SABON*

*SALO*

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

 

 

 

 

*ZAHRA SURBAJO*

 

 

 

*Ya kamata wasu readers susan irin mgnr da zasu dunga fadawa writers din da basu da burin da ya wuce su faranta ranku,shikenan ita writer bata da uzuri,bata da lalura,bata da damuwar,dazata hanata posting,?dukanmu fa yan adam ne,toko da kudin sub aka bar writer ay tana da uzurin daze hanata posting,bare sauran lalurori,har da wasu suke fadawa mutum mgn,akan abinda ba albashi aka biyaka kayi ba,inde nice kun jima baku zageni ba,zaginku jini yake karamin ajikinaπŸ€’*

 

*masoyana akoda yaushe kuna raina,ina sonku ina alfahari daku,Allah ya bar zumunci,ko dan wanzuwar farin cikinku surbajo zan dunga dorawa,ngd sosai da kulawarku gareni.kuyi hkr bisa rashin jina akan kari*

 

 

*Dedicated to Inna Ibrahim kime*

 

 

*9*

 

 

Wasa wasa haisam ya dauki mgnr dan gani yake shi din nawa yake da har zaa masa zancan aure.

 

Shiyasa ya ajiye batun khairat agefe ya fuskanci karatunsa,dan likitan mata yakeson zama

 

haka rayuwar keta tafiya su khairat na tasowa,kullum hajiya lanti cikin cusawa khairat son haisam take,tun khairat bata dauki abun da muhimmanci ba har tazo ta fara.

 

Haisam nada shekaru ashirin Sukayi sabuwar me ayki agidansu,sosai jininsu ya hadu da me ayki,yana tausaya mata musamman cikin daya lura tana dashi.

 

Kulawar da yake bata yasa tai masa alkawarin yimishi takwara in ta haifi namiji.

 

Cikin ikon Allah se bata haifi namiji ba ta haifi mace.

 

Sosai haisam yayi murna da haihuwar babyn,dan haka me hoto ya dauko yazo yay tai mata hoto kala kala.

 

Inna me ayki da kanta taba haisam damar ya radawa babyn suna ayko.

 

Se ya hada Sam na karshen sunan shi,da HA na farkon sunan nashi ya bada Samha,

 

Kulawar da yake bawa samha yasa kowa na gidan ke kiranshi Abban Samha,dakinshi ko ado yay masa da hotunanta.

 

Samha nada sati biyu aduniya,Takardar karatun Haisam ta fito inda ze kwashe tsawon shekaru biyar akasar Uk yana karatu.

 

Sanda yazo yiwa inna sallama da kuka suka rabu dan ta shaida mishi itama agoben zata koma kauyensu Rijana.

 

A wannan lokacinne inna ta bashi auren samha matukar in yana sonta to in ta girma bata da miji se shi.

 

haisam ba tare da bata lokaci ba,yayiwa inna alkawarin auran samha matukar yana raye.

 

Sosai Haisam ya mata sha tara ta arziki,sannan suka rabu cike da kewar samha.

 

 

 

Washe gari haisam yabar kasar,itama innar ta tafi garinsu.

 

Tun bayan tafiyar haisam babu wata rana ta banza da bazeyi tunanin samha ba,har ya kwashe shekarun dazeyi acan ya kammala karatun nashi.

 

 

*BAYAN SHEKARA BIYAR*

 

 

Haisam ya dawo cike da dumbin nasara,wanda lokacin su khairat na ss2 a makaranta.

 

Sanda haisam ya dawo,garin su inna ya fara nema,sede ya mance sunan garin,hajiyarshi ma haka ta manta,shiyasa yay ta yawo kauyuka amman be samuba.

 

Ga khairat da ta sakoshi agaba da batun aurensu,wanda abun har daure mishi kai yakeyi,ganin be taba ce mata yana sonta ba.

 

Hajiya lanti tada balai tayi akan ayi auren haisam da khairat.

 

Hakan yasa Alhaji baban khairat din yayiwa mahaifin haisam mgn.

 

Batare da bata lokaci ba ya amince,harsuka tsaida rana ba tare da haisam din yasani ba.

 

 

mahaifiyar haisam abun be mata dadi ba amman kasancewarta mace me hkr yasa ta bar mgnr,amman can ranta batason auran.

 

Badan komai ba sedan masifar hajiya lanti.

 

Haisam a bakin mahaifiyarshi yaji batun auran.

 

Ayko sosai yatashi hankalin kowa na gidan akan shi be shirya aure ba yanzu.

 

Rarrashin duniya yaki amincewa inda akarshe ma se cewa yayi,mace me degree yake son aura dan haka inde so ake ya auri khairat dole taci gaba da karatu.

 

Mahaifin haisam be amince da sharadin na dansa ba,amman shi mahaifin Khairat ya amince dan haka daga bikin akayi zuwa shekaru biyar masu zuwa.

 

 

Sosai haisam yaji dadin hakan

 

Hajiya lanti ji tayi kamar ta kasheshi dan bakin ciki.dole ta hakura badam ranta yaso ba.

 

Haisam ko NDA ya nufa domin neman aykin soja,dan baze iya zama gari guda da khairat ba dan takurashi zatayi.

 

cikin hukuncin Allah ya samu abinda yaje nema,duk wata wuya ya shanyeta.

 

Cikin kankanin lokaci ya samu aykin soja.

 

Yanada juriya ako ina yasa yadunga samun daukaka agurin.

 

 

tsawon shekaru biyar ya kwashe a gidan soja,wanda zuwa lokacin khairat ta tafi service dinta,bayan ta kammala degree dinta afannin jarida.

 

 

 

Haisam yayi ayki a garuruwa daban daban,kuma ko ina ci gaba yake samu.

 

Sanda aka turashi Abuja Ayki ne,yasamu karin girma me tsoka,wato major general.

 

A lokacin aka tsaida ranar auranshi da khairat,wata biyu masu zuwa.

 

Dan bakin ciki har kuka haisam seda yayi,sabida ya ga duk gujegujenshi gashide se ya auretan.

 

Haka akai ta shirin biki ba wani motsi daga bangaren ango,amarya kawai keta bidirinta.

 

Tsawon wannan lokacu haisam kullum cikin neman garin su samha yake dan ya cika alkawarin daya daukarwa inna.

 

 

Haka har aka daura aurenshi da khairat sam baya cikin walwala.

 

Har amarya ta tare agidanta,amman bata ga idon angon nata ba.

 

Muje zuwa,yanzu zaa fara wasan,me karatu zega nadan ja labarin,nayi haka ne dan in hado labarin guri guda.

 

Muje next page.

 

surbajo for life.

 

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment