Littafan Hausa Novels

Soyayyar Gaskiya Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Soyayyar Gaskiya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

SOYAYYAR GASKIYA

 

*Page 1 to 3*

 

 

*By meerah*

 

*King and Queen Writing Chamber*

 

 

 

Bismillahirrahamanirrahim

Tafe take cikin shigarta takamala dinkin rigada Zane da hijab dinka Wanda ya dace da kayan jikinka kyakkyawa CE me dogowar fuskq tana da dara daran ido masu kyalli da maiko tana da gowan hanci tare da madedecin baki wankan tarwada CE ita ba doguwa can ba kuma bagajeriya ba tana da shape din nan me suna coca cola shape ne din nan,

Yar Harka Hausa Novel Complete

Kwanar gidan su tashanyo kenan se ga wani yaro da saurin sa yace aslm ta jiyo tana me amsa sallamar tashi tane me kare masa kallo domin bata San shiba cike da faraa tace ya de Dan saurayi tana me kallon sa takarda ya mika mata yace gashi ance a baki dasauki ta karba tana fadin waya baka INA yake duk ta tambaya a lokaci daya cike da rashin fahimta yace bansan shiba domin a hanya ya tsaidani ya bani yana gama fadan haka ya wuce Dan kalli kalli tasoma daga baya baxe fidda taba tayi gaba tana me tunanin waye wanan me turo mata wasika fiye da shekara batare da ya gajiyaba sede tamvayar shin me yasa yake boye kansa da wanan tashi ga gida xuciyata fal da tunani ko da tashiga gida ta tarar da sallama mama dake tsakar gida tana shirin Shiga daki taji sallamarta juyowa tayi tare da amsawa cike da faraa ta amsa tana me fadin Haneefa kin dawo daga makarantae yau kunyi yamma , rumgume maman tayi cike da shagwaba tace Allah mama yau lectures din sunyi xafi sosai duk nagaji kallo tayi cike da kulawa tace maxa je ki yi wanka kizo yau abincin da kikafiso nayi tsallen murna tayi cike da yarinta tace yeyyyyy naji dadi mamana kice yau dambu kikayi mana kai nayi murna tafada tana me shigewa dakinta

. takardar hannunta ta ciro tare da ajiye ta kan katifarta tayi tafada toilet wanka tayi tare dayin alwala dogowar Riga tasanya tare da yin sallah bayan ta idar tare dayin aduaa takarda ta dauko da soma karanta wa kamar haka. a farkon katar dar yasa** Smile before u open** haka taji murmushi me sanyi ya subuce mata tamkar yana ganinta kafin tasoma karanta wa… *HY UR LOOKING SO WEAK YET STILL LOOKING SO CHARMING TAKECARE URS* **D** daga bayan takardar ansa * kiss after reading ** tsintar kqnta tayi da kissing din papper tana Dan murmushi tayi tare da shafa kyakkyan rubututun tana wani kankame takardar haka take tsintar kanta da nishadi deepdown tana cewa who is he, I really can’t wait to meet him tafada tana Mr lumshe ido mamace ta kwallah mata kira tare da cewa Haneefa kifito kici abinci naki mana sif dinta ta bude tare da tura hannu karka shin kayanta nan wata katuwar ambalon ta bayya ta dauka ta bude takardu ne birjik kowanne da kwanan wata a jikinsa anan ta cusa wanan ma ta boye tare da fitowa tsakanar gidan inda ta soma cin abinci tana tambayarta abban mama ke shaida mata ya fita kasuwa be dawo ba anan take tambayarta INA haneef yaje Wanda ya kasance kani agunta cike da Dan damuwa take shaida mata cewar haneef bayani na hanashi fita ko INA saboda rashin lafiyarsa amma Sam bayaji da inda yaga abokansa nan shima ba xama se ya fitan cike da yar damuwa itama Haneefa tace kiyi kawai mama kibarshi domin fitan yana Dan San yawa jikin nashi sauki saboda ganin jamaar da yake yi yafi xakan gidan hakane kuma kinji mama ta fada Allah de ya bashi lfy Ameen inji mama

Asalin labari

Mahaifin Haneefa ana CE dashi mal kabeer wato Abba Wanda ya kasance Dan asalin garin jigawa akaramar hukumar guru asalin bafullatani ne yanada kani me suna sani su biyu Allah yabawa iyayensu wato mal Isah da matarsa hauwa shi Mal kabeer yakasance yana harkar saida fata wacce ya farayi a can guru har Allah yasa ya shigo garin kano inda Allah ya hadashi da mama me suna Aisha wacce ta kasance yar kano anan kasuwa suka hado tazo siyayya shikenan Allah yahada abin shi yabita gida yasamu iyayyenta aka dedeta ya anan unguwar rimi yasamu hayar gida suka tare daga baya yakaita can gida yaga yan uwa yan uwa suka ganta sun shekara biyu babu haihuwa har Allah ya sa wata ranar labara suna xaune ciwon ciki ya kama Aisha mal kabeer ya kwashe ta ya kaita asibitin gwannati awon farko se ga ciki murna ba a magana haka ma yan uwa da abokan arziki haka sukayi ta rainon cikin har wata Tara ranar jumaa antafi sallar jumaa aka haifo kyakkyawar yarta aka Sanya mata suna Haneefa kasan cewa sunan da mahaifinta yake so kenan

Haka tunda aka haifi Haneefa babu jimawa aka haifo haneef domin shekara daya ta bashi haka daga Kansu ba a kara haihuwa a gidan ba

Haneefa da Haneef sun samo SOYAYYAR mahaifa haka sun samu tarbiya Dede gwargwado haka ma karatun boko dana islamiya ba a barsu a baya ba yanzu Haneefa tana da shekara 22 tana shekarar ta biyu tanayin NCE ne a FCE kano shi kuma Haneef yana level one a poly Haneef Allah ya jarrabeshi da wata rashin lafiya ta farfadiya Wanda tun yana karami yake fama da ita anyi maganin hausar har Dana asibiti sede shuru Har yau Allah be kawo warakar ba sede tun suna na nashi fita har sun hakura sun barshi yakan Dan fitan dayake se yayi wata wani sain har fiye da wata abun be tashi ba se de tayi masa tsamari domin har suma yanayi wani lokaci

Haneefa kuwa tun wata rana ta dawo daga makaranta aka biyo da yar takarda wani yaro ya kawo ta tambayi waye yaron yace shima besan waye ba tabude taga rubutu a bayan takardar ansaka Smile before you read sanan taga wani kyakkayan rubutu Wanda akayi shi cike da kwarewa tare da burgewa kamar haka ** Hyy mis cutes , u knw ur the love of my life the apple of my eyes I having loving for a long time but I could not confess let along show up to u but I promise I wil show up one the but before then its me see how long u can waittt for meeeee*** Daga karshen takardar yasaka ** *KISS* after reading** Hmmm wanna kenan tunda ranar duk bayan sati biyu se taga sakonsa Wanda a kullun kalamansa se ratsa yake a kullun tana cike da muradin son sanin waye shi

. *KUCIGABA DA BIYONI A NI Merah acicikin litattafina me suna *SOYAYYAR GASKIYA*

 

*BY MEER@H

(09045256504)

*SOYAYYAR GASKIYA*

 

*BY* *MER@H

 

 

 

*JAGORANCI TA KUNGIYAR*

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*

*Bismilahirrahmanirrahim*

 

 

 

( *Page 4_8)*

 

Kamkame takardun tayi cike da bege da kaunar Wanda ya mamallakin wannan kyakkawan rubutun ” Who is he ,tafurta tana me tuna baya

Asalin labarin

Aisha Abdulkadeer ( *Ameera* ) Mahaifin Ameera ya kasance me saida fata acikin asuwar abbatua dake jikin jahar kano yana da mata Ameena dake kira da mama Suna da yara 3 aduniya Aisha(Ameera) Se Ibrahim *(Khaleel)* se autar su Rabia( *Mimi* )

Iyalan malan *Abdulkadeer* cike suke da tarbiya sanan beyi kasa a gwaiwaba gurin nema musu ilimi na boko da Arabi inda Ameera takeyin *NCE* ta kano wato *FCE* tana shekara ta 2 kenan , yayin da shi kuma khaleel ke poly yana year se auta Rabia dake ss 2 a secondary, Rayuwa CE ta rufin asiri Allah yayi musu Mal Yakasance me hakuri da juriya tare da Neman nakai haka mama takasance macece me dauriya tare da hakuri da duk abun da mal yakawo haka take karba hannu biyu

khaleel Allah ya jarabceshi da wata cuta farfaditaya wacce take tasar masa lokaci lokacin anyi maganin har anfawwalawa Allah sede duk sanda cutar ta tashi yana shan wuya har asibiti yake kwanciya

wannan kenan

Ameera dawowar ta daga makaranta kenan anatukar gajiye tashanyo kwanar dazata sadata da layinsu se ji tayi wani yaro yana kiranta juyawa tayi tana me karewa yaron kallo tace ,, Ya akayi ne tafada cike da sanyinta da gajiyar makaranta data debo takarda fara kal ya bata tare dacewa,, gashi ance inbaki Dan kallon takardar tayi tare da yaron kafin tace ,, injiwaye yace Ka bani tana me tsare yaron da manyan lulu eyes dinta dayasaka yaron rudewa take yace ,,wallahi nima bansanshiba har xata tafi se kuma tadawo takarba tare dayin gaba

bayan tashiga gida ne taci abinci sanan ta bude takardar se kamshi take xubawa ahankali take warware ta tayi tozali da wani haddaden rubutu kamar Haka:: Hy my world I know u don’t really know who I am but don’t over think and keep on thing in ur mind that am ur one and only lover and I will wayz love u, Soon ur goona meet me dear but let’s see how much more u can’t wait for me ur *D* smile after reading nan take taji wani lallausan murmushi ya subuce mata kafin tasamu bakinta da furta * I will wait for u whom ever ur are**

Tundaga ranar duk bayan sati setaga sakonan sa da kalmomi masu dadin gaske tare da burgewa Wanda ayanxu anshiga wata 2 da faruwar hakan

wanna kenan

cigaban Labari

Mama CE ta kawlla mata kira Ameera ! Ameera !! Har Sau biyu kafin ta amsa da naam mama tana me maida takardun maajiyarsu tafito tsakar gida inda tasamu Maman suna San iska tace ” Mama gani” mama takalle ta tare da cewa shin yau bakyajin yunwa halan Dan Sosa kai tayi tare dacewa ” inaji wallahi mama tace tohm maxa jeki kitchen kixubo nan taje taxuba suna Dan taba hira babu jimawa se ga khaleel shima yadawo daga school haka suna hadu a tsakar gidan suna hira gwanin shaawa auta daman ita tun 2 sukadawo dab da magariba se ga baba yashigo shima daga bisani aka kira sallah khaleel da baban suka wuce masallaci sukuma su mama sukayi taso a gida

Yau takama Asabar Dan haka basu da lectures ta nemi azinin mama akan zataje gidan kitso nan mama ta bata kudin kitso tana adawo lfy kar a Dade “To ” ta amsa tare da ficewa dayake babu nisa gidan kitson Dan haka a kafa take xuwa tadawo ta danyi tafiya kadan se taji mashin yana binta basarwa tayi tare da cigaba da tafiya se taji ansa ” Ameera* juyowa tayi tare da kallonsa jin ankira sunan ta laa yaya Waleed tace dayar faraarta ( Waleed yakasance makocinsu gida 3 Ne tsakaninsu tun tana kara yake sonta Wanda har iyaye sunsan da haka )sede iya Samko awancan lokacin basonsa takeyi ba Inda take shaida masa iya karatu takeyi azatonta ko xece ya hakura sede shi Sam babu gudu bakoma ja dabaya yana nan manne da iya sautari idan yaxo tadi se ta tsiri cewa bata da lfy amma shi Sam yaki saurarawa

wannan kenan

kucigaba da bina a wannan littafi nawa me suna *SOYAYYAR GASKIYA*  Wanda ni Merah na rubuta tare da jagorancin King and Queen Writers

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment