Littafan Hausa Novels

So Makaho Ne Hausa Novel Complete

Abinda Zuciyata ta zaba Hausa Novels
Written by Hausa_Novels

So Makaho Ne Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

O MAKAHO NE*

_(LOVE IS BLIND)_

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Assalamualaikum warahmatullah, ina farawa da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.

 

 

 

 

 

 

My first novel, ina fatan zaya nishaɗantar da ku haɗi da ilimantarwa, short an romantic novel.

 

 

 

 

 

_Written by_✍️✍️✍️✍️

*Qwinn minerhly*

 

 

 

Part 1-5

 

 

Noor !noor!!

nasir ne yake ƙwala mata ƙira da misalin karfe 6:30pm a wani katafaran babban hotel wanda ya haɗe, da duk wani abu na more rayuwa aciki wato A N N palace hotel (ASHMIR NASIR NOOR) PALACE HOTEL.

nan ya hangota akan wani resting cheer tana lilo haɗe da hot coffee a hannunta tana sha, tana hangoshi tace “yaya nasir what happened?” Yace “bansaniba, tun ɗazu naketa neman ki”.

Assadiya Hausa Novel

shagwab’e fuska tayi tace “to yaya nasir meye laifi na dan nazo nan, nifa hutawa ta na keyi“, yace “gud ba laifi, dama tambayarki zanyi ina babban yaya yake?”

taɓe baki tayi, sannan tace “maybe yana chan gefen sweeming pool yana wanka kasan babban yaya akwai son wanka kamar shark” ta karasa fada ta na dariya,” Nasir yace “wlh ba ruwana, ke kika sani idan yaji ki”

riƙe baki tayi tace “ni na isa ma nafada har yajini hmm babban yaya ba sauki”.

Juyawa Naseer yayi yace “Noor am coming” tace “ina zaka je” yace “zan danga managers ɗin gurin nan ne” ya faɗa haɗe da juyawa,”

tace “alright sai ka dawo.

 

Kwance yake akan resting chair by the pool side, ya ɗaura hannun sa a karkashin Kansa, staring at the cloudy sky, iska ne mai cike da ni’ima da saka zuciya natsuwa ke kaɗawa hakan yasa flowers da tall trees din da ke gurin kadawa. His eyes are closed, amma ba barci yake ba idan kayi ma sa kallon tsaf zaga gane yana da sihirtaccen kyau,his thick eyelashes zara zara, eyebrow ɗinsa kuma so thick and black kamar Wanda yayi caving, his pointed nose and cute pink lips kamar wadan da aka shafa ma lipstick, he is a body builder dan jikin sa a murde yake, sanye yake da all black armless shirt sai 3/4 trouser shima black.

Haɗaddiyar sweeming pool ne, wanda ke zagaye a gun, mai cike da kayan alatu, na more rayuwa, wato VIP ɗin gurin, guri ne aka ta nade shi na musamman, domin manyan mutane irinsu ashmir,

Shi kaɗai ne agun, ko masu gadin shi ya kore su, a cewar shi baya son hayaniya, hmm babban yaya kenan.

 

 

Tsaki yayi jin wayar sa na ringing for the 5th time kafin ya dauka amma bai ce komai ba sai dai yana sauraron abunda ake fada daga daya side din, after like 3 minutes “ok” kawai yace cike da yanga kafin yayi hanging off.

 

 

 

*Sanye* take da kayan sarauta a jikin ta red nd black wow abunka da farar mace sai kayan suka amshi jikin ta tayi wani mugun kyau sai sheki take ga kamshi yana tashi ajikinta, sai shan kamshi take ko magana bata son yi sbd sarauta amma fa akwae tsiwa gimbiya kenan yar sarki wato PRINCESS NEEHAL. se kuma tawagarta da suka rakota gurun shakatawar kasancewar yau weekend ne,

niko nace yayan masu dashi dai akwae son hutu,

 

Juyowa tayi ta kalli bayinta cike da isa da izzar mulki “tace ku dakata daga nan” sukayi cirko cirko kuwa ita kuma ta nufi VIP SWEEMING POOL CENTER ga sign board a gurun, tana zuwa ta iske masu gadin gurun sai ko kallonsu batayi ba tace masu zan shiga vip ne, sai babban ya durkusa har kasa yace “mata ranki ya daɗe ahm kiyi hakuri wlh babban yaya ne aciki wato yallabai” sakin baki tayi tana kallonsa, waye kuma babban yaya? To ko ma waye shi wlh sai ta shiga, sabida itama tasaba idan tazo gurun nan take zuwa, kuma itama bata son hayaniya ita kaɗai take kama gurun.

sai tace masa “dallah malan matsa kabani guri na wuce dan wlh babu wanda ya isa ya hanani shiga gurin nan yau” shidai da yake duk suna tsoranta sai ya matsa mata yabata hanya ta wuce, tana shiga gurun ta samu wani resting cheer ta zauna tana shan wani hadaddan ice cream wanda aka ajiyewa babban yaya wato ashmir, kuma hankalinta kwance batada damuwa kona sile daya, shikuma gogan duk wainar da ake toyawa yana gani a wani karamin system din dake gabansa hhmm ashmir knan,

Sukuma masu gadin gurun suna chan sunata gulma sun rasa yanda zasuyi yau sun shiga ukunsu, ga dan governor ga yar sarki kuma sun haɗe a guri daya, sai dayan yace “yau zamuga abinda zai faru agurun nan izzah ta hadu da izzah”

 

woow masu karatu ku hasko min abunda zai faru a next page….

✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

 

 

Taku

Qwinn minerhly

 

Mrs Yusuf

❤️❤️❤️

[8/26, 11:21 PM] Qwinn Minerhly: SO MAKAWO NE

 

 

(LOVE IS BLIND)

🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🖤🖤🖤🖤🖤🖤

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*📖

 

 

 

 

 

 

My first novel, ina fatan zaya nishadantar daku fans, very short nd romantic novel.

 

 

 

 

Writer✍️✍️✍️✍️

Na Qwinn minerhly

 

 

 

 

Part 5-10

 

 

 

 

 

Nan take ashmir ya soma fito wa ahankali daga cikin pool din yana taka matattakalan gurun, yana fitowa ya samu wani hadad’iyar coat baki me ratsin fari ya ɗaura akan kananun kayan dake jikin shi inda yakara wani sihirtaccen kyau, ga ruwa yanata sauka ajikinshi gashin jikinshi yadad’a kwanciya gwanin sha’awa.

Nan fa ya dirfafi inda gimbiya take,

Yana tafiya yana wani shan kamshi yana basarwa yana ta wani yauki kamar mace, hmm tofah!

Ita ko gimbiya yar sarki sai shan ice cream ɗinta take tana lumshe ido, dan tunda take bata taɓa shan ice cream din daya gamsar daita ba irin na yau,

Yana isowa gurin ya tsaya chakk yana kallonta kallo irin na mamaki gata dai yarinya ƙarama bata wuce age ɗin little sist dinsa ba wato noor, gata kuma kyakyawa gata daga gani hutu ya zauna mata sosai, saida yayi dogon nazari akan ta sannan ya samu kujera wanda yake facing ɗinta ya zauna akai, in a slowly voice murya me dadin gaske, yace ke!

Da sauri gimbiya ta dago kanta jin sautin murya akanta, yaci gaba: “ke wacece ke da zaki shigo gurin, nan ehe nace who are you? Yafada da tsawa, daga ganinki ke karamar mara kunya ce ko? to bari kiji wlh saina yi maganinki stupid girl”,

take gimbiya ta ɗago kanta da sauri ganin ana ci mata mutunci abinda ba’a taɓa yima ta ba a tarihin rayuwarta ba sai yau, aikuwa ta ɗago fuskarta tayi masa wani irin kallon raini, tasaka yatsanta a daidai saitin bakin shi tace “shshshh” alamar yayi shiru, ai sabida mamaki baisan lokacin daya saki baki ba yana kallonta.

“Hmm har kaisa kaci min mutunci wlh baka isaba, okay! tambaya ta kake ko ni wace ce ko to zaka san ko ni wacece kuwa yanzu, amma saika fara faɗa min kaima ɗin wanene kai”?

Ai ta ke ran maza ya ɓaci, ya ɗaga hannu zai sharara mata mari knan, phone ɗinsa yayi ringing, sai ya fasa marin ta, ya ɗauko phone ɗin sa yana dubawa yaga sunan little sistern sa ce, tayi masa kusan five misscalled, bai ma san ta ƙira ba, ai kuwa ya ɗaga cikin slowly voice ɗin sa kamar ba shi ba ne ransa yayi mugun ɓaci yanzu, yace “baby luv ya akayi”? nan fa noor ta shagwaɓe fuska tace “sweet brother wlh tun ɗazu muke neman ka, nida yaya nasir”, yace “to ya akayi ne baby luv”? tace “wlh yaya mun gaji ne gida muke so mu koma”, yace “okay babu damuwa gani nan zuwa 5 mnts bari na shirya saina fito mutafi ko”? tace “yauwa my sweet brother sai ka fito” nan take ya ajiye wayar sa a gefe,

Ya matso inda gimbiya take azaune, sai cika take tana batsewa yace mata “ke be careful bcause ni ba tsaran ki bane da zakizo kina min misbehave anan, wlh kinci sa’a yarinya sauri nake zan tafi, yau da saikin yaba wa aya zaƙin ta nonsense girl”, itako gimbiya da ranta ya gama ɓaci saboda ta ɗauka da budurwar sa yake waya ya kyaleta tana jiran sa, ga shi basu gama faɗan nasu ba sabida ita taso yau tayi maganin shi saiya bata hakuri, tayi masa wulakanci tukun saita hakura amma wai dan rainin hankali saida ya gama wayar sa wai kuma zai tafi sauri yake wlh yau yaci sa’a sosai.

 

Nan fa gimbiya tace “ai ban san kai matsoraci ba ne sai yanzu, da ka tsaya mana kaga aikin karamar yarinya wlh”,

Shiko ashmir ya juyo sai tin ta yasa ɗan yatsarsa ya buge mata baƙi sannan yace “banda lokacin ki karamar yarinya, amma nayi alkawarin ko ba yau ba sainayi maganinki small rat kawaii”, nan fa ashmir ya sa kai yayi tafiyar sa ya bar gimbiya agun riƙe da d’an karamin leben ta, wanda har ya tashi sabida abunda yayi mata yayi mata zafi sosae hawayen bakin ciki ne kawa yake kwarara a fuskanta, nan gimbiya ta durkushe agun tana hawayen bakin ciki bata ankara ba kawai saita ga duhu yafara yi alamun anyi magriba ma, sai kawai ta miƙe ta fita da gudu.

Su kuma masu gadin gun tunda sukaga D.ashmir ya fito ransa matuƙar bace suka san an tabka tsiya knan gashi suna so su kulle gurin sabida gurin yanada tsaro sosai amma suna tsoron gimbiya da take gun, ai kuwa tana fitowa suka samu suka kulle gurin.

 

 

 

Shiko ashmir yana fito wa yaga nasir da noor da bodyguards dinsu sunyi cirko cirko shi kawai ake jira agun, aikuwa ba ɓata lokaci ya shige mota, lil sist ma ta shiga nashi motan, shikuma nasir ya shiga wani daga cikin motocin nan da nan aka tashi motocin aka hau kan kwalta dasu ana basu wuta.

 

A hanya kuwa duk surutun lil sist yau ba tayi surutu ba sbd taga ran babban yaya aɓace yake shiyasa tayi shiru.

 

Shi kuma ashmir ran sa ne a matuƙar ɓa ce, wai yau shi karamar yarinya tayiwa rashin kunya, hmm wlh daya san ko yar wace ce da yau sai ya sa an dauko mai ita yayi maganinta amma bari ya san me zaiyi akai ai!

 

 

 

 

Ita kuma gimbiya tana fitowa tayi ta waige waige ko zata ga ashmir ta rama abinda yayi mata dan wlh taso ta ganshi da saita mare shi taga abinda ya isa yayi, mugu kawai babba dashi amma sai mugunta, ai wlh sai ta nemo shi tayi maganinshi duk da ran daɗe wa mugu kawae.

 

Nanda nanda bayinta suka nufo ta suka duƙa suna kwasar gaisuwa itako bata ma san sunayi ba ko kallo basu ishe taba balle ta amsa musu.

 

 

Su kace “ran gimbiya ya daɗe tafiya zamuyi ne”? to anan ne ma ta daga musu kai alamar yes, su kuma ko ajikin su daman sun saba da hakan, wulaƙanta su takeyi dama, ita ala dole yar sarki jikan sarki yar na gada.

To nan fa itama gimbiya aka buɗe mata mota suka shiga bodyguard ɗinta suka rufa mata baya suka hau kwalta sai gida.

 

 

 

Doctor ashmir kuwa suna isa gida wato government house ya nufi part ɗinsa, wanda haɗuwar wajan ya isa,

Kai tsaye shiga ciki yayi,

ya shiga wata hadadd’iyar bathroom ɗin sa zai yi wanka, nan fa yayi wankan sa ya fito ya saka wasu kayan shan iska ya tafi dressing mirror ya taje gashinsa da sajensa, yatashi ya dauko sallahya ya shimfiɗa ya tada sallah yayi sallolin sa yayi nafila yayi azkar ɗinsa na dare, take anan yaji ya dai na jin bacin ran dayake ji zuciyarsa tayi masa wasai.

ya tashi ya tafi main parlor na gidan yana zuwa ya tafi gun mum, yayi hugging ɗinta yace “sweet mum am back, sannu da gida”,

Mum tace “wlcm my luv” yace “mum so sorry mun barki ke ka dai a gida ko”? mum tace “no ba komai son ai dadyn ku yana gida kasan yau weekend ne,”

Ashmir ya shafa kan sa yace “ohh mum ina dad yake?” tace “yana sama amma yanxu zai sauko, sai ayi lunch”

 

Sai ga noor ta sauko da gudu tana zuwa tayi hugging ɗinn mum tace “mum sannu da gida” mum tace “yauwa sannu my princess, ya gajiya?” noor ta shagwaɓe fuska tace “wlh mum yau nagaji sosai,” mum tace “sorry tunda kinyi wanka za kiji warware ko.”

nan fa noor ta kalli ashmir tace “sweet bro yau kamar kana fushi ko?” yace mata “no ba ba fushi nake ba,” sai tace “okay, to yayi kyau bros, shi kuma yayi pecking dinta a kumatu yace lil sis kiriniya ko? tace “aa yaya,” yace “okay ba damuwa ai,” sai ga nasir ya sakko shima yana zuwa yaje kusa da mum yace “mum sannu da hutawa” tace “yauwa my son ya kuka dawo?” nasir yace “lafiya lau mum,” yatafi yayi hugging ɗin babban yaya yace “sannu bros” ashmir yace “yauwa my luv sannu kaima ya gajiyan mu?” Nasir yace “alhmdlh bros.”

nan suka zauna a dinning cheers ɗin suna jiran dad, sai ga dad ɗin juwa nan ya sauko, aikuwa nan duk suka miƙe amma banda mum, sai da dad ya zauna tukun suma suka zauna, duk suka gaishe da dad ya amsa yana ta doka murmushi afuskar sa nan fa dad yace “bismillan ku” kowa yafara cin abinci, sai da aka gama cin abinci sai dad yace “ahm kun dawo lafiya? sukace “lafiya lau dad” yace “to Masha Allah,”

yace wa ashmir “amma dai gurin babu matsalan komai ko? suka ce “eh dad babu matsala,” noor tace “dad kasan yaya nasir ne ya gana da managers din fa, dad yace “alright yayi kyau, “shi sarkin miskilancin mai yayi acan? noor tace “dad yana chan wajan sweeming pool, sai dad “yace ai na sani sarkin wanka ko agwagwa albarka,” nan fa akai ta dariya, shi ko gogan murmusawa kawai yayi bai ce komai ba,

to nan fa dad yayi gyarar murya, kowa yayi shiru sannan yace “yanzu dare yayi kowa yaje ya kwanta, gobe da safe inada magana daku.

 

Kawai ashmir yaji gaban sa ya fadi, amma sai ya dake, to nan dai kowa ya watse yatafi ɓangaren sa inda noor tabi bayan mum, domin ita dakin ta yana kusa dana mum bata yarda tayi nisa da mum ba.

 

To wannan knan

 

A can part ɗin babban yaya kuwa yana Chan yana ta juyi yara sa mai ke yimasa dadi a duniya, da ya rufe ido sai yaga wannan fitsarariyar yarinyar, to shi wai me hakan yake nufi ne?

Shi dai yasan bawani k’are mata kallo yayi ba amma dai ya ɗanga fuskar ta lokacin da take yimasa tsiwa da wani ɗan ƙaramin bakin ta daya gwabje mata shi,sai kuma kyau tabbas kyakyawa ce ba laifi amma kuma ai daga gani yarinya ce baza ta wuce 18 ba sa’ar noor ce ai,

To fah nan dai ashmir ya dinga tunanin gimbiya kuma shi dai yasan ba son ta yake ji ba to amma kuma me hakan yake nufi???

 

 

“Hhhh niko nace babban yaya ka tambayi kanka zamu fi samun amsa.”

 

 

To masu karatu mai ya ƙare anan, amma kuma kada ku gaji kuci gaba da bin mu a sannu a hankali domin jin ita kuma gimbiya awani hali take ciki yanzu…

 

 

 

More comments more typing✍️✍️✍️✍️✍️

 

Taku

Qwinn minerhly

 

 

Mrs Yusuf

❤️❤️❤️

[8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO* *MAKAWO* *NE*

(LOVE IS BLIND)

🖤🖤🖤🖤🖤

🖤🖤🖤🖤🖤

🖤🖤🖤🖤🖤

🖤🖤🖤🖤🖤

 

 

 

 

 

My first novel,ina fatan zaya nishadantar daku Fan’s very short and romantic novel.

 

 

 

 

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment