Littafan Hausa Novels

Sirri Nah Hausa Novel Complete

Yadda Ake Rikita Maigida Yayin Kwanciya
Written by Hausa_Novels

Sirri Nah Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

SIRRI NAH

 

_K_SHITU

 

_FREE BOOK_

*[2023]*

 

*_ƊANƊANO_*

 

Kallo ɗaya zaka mata kasan ba chikakkiyar mutum bace! duba da yanda take tafiya a lan-lanƙwashe,wata guguwa ce haɗe da iska ta fara kaɗa ilahirin Maƙabartar, wani baƙin hayaƙi ne ya fara fitowa daga bakin ta, kafin wani madubi ya bayyana mai ɗauke da wata matashiyar budurwa wacce take kwanche, bisa wani makeken gado,

Likitan Mahaukata Hausa Novel Complete

 

A razane ta diro daga bisan gadon, madubin tsafin ta ta ɗauka ta fara kallon sahash dake cikin maƙabartar tana ƙoƙarin ƙona mata fuska, wani murmushi ne ya suɓuce mata cikin izza ta buɗe bakin ta sai ga wani farin abu ya fito ya shiga cikin madubin, tana tsaye sai kawai ta faɗi ƙasa cikin ƙunar rai ta miƙe tare da nutsawa cikin maƙabartar, Wani kabari da yayi daban taja ta tsaya tare da sakin murmushin mugunta.

 

Wata ƴar ƙaramar wuƙa ta zaro, sannan ta yanka tafin hannun ta, ta saita dai-dai kabarin jini ya fara zuba, wani farin haske ya fito daga idanun ta ya shiga kabarin, ta fara karanto wasu dalasimai, ƙasar kabarin ce ta fara rugur-gujewa wani baƙin hayaƙi da iska suka fara kaɗawa kafin wata guguwa da iska baƙa suka taso, dunƙulewa iskar tayi wani ƙatoton halitta ya rikiɗe kamar dodo hannun sa ɗauke da waso zaƙo-zaƙon akaifu, ya riƙe wata baƙar sanda magana halittar ya fara, da wata murya marar ɗaɗin sauraro “Zaki samu biyan buƙata! hahhhha zaki samu Nazaan zai dawo wannan diniyar taku! amma ɗan lokaci zai yi aiki a ƙarƙashin ki dole kiyi taka tsan-tsan, Aikwai wanda zai yi yunƙurin dakatar da faruwan hakan a daren chikar baƙin wata zaki samu ƙarfin ikon ganin bayan Aliyaa dole kece sarauniyar da zata, mulki *_MANAAJ_* Amma dole sai kin taka zuwa _TEKUN JAZAL_ kin ɗauko makullin sihiri.” yana gama faɗin haka ya ɓace…ita ma ɓacewa tayi, Numfashi Aliyaa ta sauke tare da zama bisa gadon ta, Ɗakin binciken sirrin ta ta bayyana, ta fara binciken _TEKUN JAZAL_ ɗin da ya faɗa, tayi kusan awanni biyu amma allon tsafin ta ya gaza nuna mata komai wani blue ɗin zobe mai sheƙi ta fido tare da latsawa, sai gata gaban tsoho ARAR tun da ta bayyana gaban shi ya ƙura mata idanu bata jira cewar sa ba ta fara jero masa tambayoyi…..”Kaka waye _NAZAAN?_ Ina zan samu _TEKUN JAZAL_ ina so na ɗauko makullin sihiri.” Da wani irin mamaki yake duban ta ya gaza furta komai, A hankaki ya dube ta yace “Aliyaa! Nazaan kike magana kenan, ya zama dole na fayyace miki komai akan sa sannan, dole na dakatar da dawowar nazaan cikin wannan duniyar.”

 

Gudu yake yi da motar kamar zai tashi sama, kaucewa kawai mutane ke yi, wani danƙareren gate ɗin masarautar ya nufa, ba tare da tsai-tsayawa securities ɗin dake tsaron gate, ɗin suka wangale masa ya shige da hancin motar sa, ba tare da an yi yunƙurin tsaida sa ba, duk nisan dake tsakanin gate da ɓangaren mahaifiyar sa bai yi minti biyar ba ya isa bai gama parking ba ya fito, da sauri-sauri ya buɗe ƙofar ya shiga ba tare da kowa yayi yunƙuri yi mishi iso ba, bedroom ɗin ta ya shiga kwanche ya same ta bisa gadon sai ƴan uwan ta, duk sun zagaye ta yana isa ya kamo hannayen ta cikin raunin murya ya fara magana, “Amma kiyi haƙuri in sha Allahu zaki samu lafiya nayi alƙawari zan je TEKUN JAZAL zan samo miki magani, bana son sake ganin ki cikin wannan yanayin.” Jikin kowa yayi tsananin sanyi jin wai zai je tekun jazal, amma babu yanda suka iya sabo da Amma na cikin mawuyacin hali, ga kuɗi ga mulki amma babu lafiya.

Ace mutum tsawon wata biyar yana kwanche ba umh ba A’a ba motsi, kamar gawa amma ga kuɗi da mulki ikon Allah kenan, babu yanda za’a yi dole a sake neman malam Surajo, domin shine yayi iƙirarin yayi alƙawari Sarauniya zata warke in har An samu anje TEKUN JAZAL a tsinko ganyen BITIR amma dole, sai an san wace duniya tekun yake ma tukun, dan manyan sheɗanu ne kawai suka san da zaman tekun, sai shahaarrin masu ƙarfin ikoh, dan haka ba kowa yasan wace duniya tekun yake ba, gano duniyar kanta akwai wahala dan sai mai chikakken ƙarfin ikoh ana wahala sosai da tunanin kafin a samu nasara gano duniyar kanta, kuma koda an sani akwai gagarumin hatsari tattare da zuwa, dan ba lallai bane mutum ya dawo ko, ya isa da ransa ba.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment