Shamsuddeen Hausa Novel Complete
SHAMSUDDEEN
(Gangster)
Story and written by oummu Amna
_Wanna labarin kirkirarren labari ne, wanda yayi daidai da yanayin rayuwar sa a rashi ne, ban kuma yarda a juyamin labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba_
Godiya ta musamman ga
(Xayyeesherthul-humaerath)
Tareda
( #NoorEemaan )
Allah ya kara mana basira ya tsarkake alk’alamin mu ya hanamu rubuta abinda bazai amfani al’umma ba Ameen.
Bismillaahir-Rahmaanir-Rahiim.
Page 1-2
*Abuja*
maitama
Maitama had’addiyar unguwa ce ta masu kudi mai kyau da tsari, gidaje ne ajejjere masu kyau gwanin ban sha’awa gini ne na zamani iya kallonka.
Wani had’add’en babban gida ne cikin jerin gidajen dake unguwar wanda yafi kowanne kyau da tsari acikin su, fentin gidan duka fari ne kamar dai white house haka tsarin gidan yake.
kofar gidan dauke yake da tangamemen katon gate wanda wasu manya security guda biyu ke gadinsa.
Babban falo ne dake zagaye da kofar glass ya sha blue and white na kujeru da labulaye da carpet baka jin komai a cikin d’akin sai karar ac da wani irin sihirtaccen kamshin room freshener mai masifar dadi.
Hausa romantic novels Wattpad
kyakykyawan matashi ne zaune a tsakiyan falon a gaban shi kwalaben giya ne guda biyar, uku daga cikin su ba komai aciki sai guda biyu suma da alama ba barin su zaiyi ba, ganin yadda yake ta huci yana hada gumi duk da sanyi ac dake cikin falon yasa papa dake zaune a gefe yana kallon sa kyale shi yayi ta durawa cikin shi wine dan yasan ko yace zai hana shi a wannan yanayi da yake ciki ba hanuwa zaiyi ba har sai da ya shanye kwalabe 3 ganin ya sake jawo na 4 zai bude ne yasa papa matsowa kusa dashi ya kama hannu shi, runtse idanun sa yayi da karfi yana jin wani irin zafi na ratsa zuciya shi, da bavdan yasan wanda ya rike mai hannu ba da babu abinda zai hana shi karya hannun, a hankali papa ya karbi kwalbar tare da daukan sauran yayi waje dasu…
Bude idanun shi yayi da suka kada sukayi ja tsabar bacin rai yabi bayan papa da kallo harya fice yanajin kamar ya kurma ihu koya samu sassauci abinda yakeji a cikin zuciya shi.
mikewa tsaye yayi ya nufi wata kofa dake cikin falo wanda zai sada shi da dakin baccinsa kai tsaye.
sanye yake da three quarter da farar riga harmless hakan ya baiwa zanen tattoo din dake jikin shi daman fitowa ta muscles din hannushi na hagu da dama, dogo ne kakkaura mai kirar karfi fari ne amma ba can ba yanada yalwar gashin gira da ido, idanunsa manya ne wanda suka dace da siririn dogon hancinsa, kansa cike yake d gashi baki sidik wanda ya hade da sajensa da gemun shi, kwayan idanu shi ruwan toka ne wanda a yanzu suka rine suka koma jajaye sbd tsabar bacin ran dake cin zuciyarsa, yana da faffadan kirji da six pack a cikin shi wanda lallausan gashin dake kirjin shi yasake k’awata shi.
murda handle din kofan yayi ya shiga, bedroom ne babba mai girma sosai wanda ke dauke d royal bed yana shiga ya fara cire kayan dake jikin shi wani lallausan gashi ne kwance a kirjinsa tare d wani hadadden zane a gefen kirji shi ta dama kayan duka ya cire ya saura daga shi sai boxer,
kan gado ya fada a rigingine ya lumshe idonsa a hankali kuma bacci mai nauyi ya dauke shi.
papa ne ya shigo bayan yaje ya zubar da kwalaben,
tsayuwa yayi yana kallo shi kafin ya matso ya gyara mishi kwanciya tare da jan duvet ya lullube shi.
juyawa yayi ya fita falo tare da kiran mai aiki yazo ya gyara falon.
zama yayi a daya daga cikin kujerun falo yana tunanin rayuwar wannan saurayin yana matukar kaunarsa da tausayin sa, da yana da hali daya raba shi da duk wata damuwa da take damun sa.
A daki kuma bayan wani d’an lokaci juyi yayi tare da kwabe fuska hadi da tura baki gaba ahankali kuma ya fara bude gajiyayyun idanunsa ya sauke su akan saman dakin, mika yayi tare da salati kana kuma a hankali ya fara saukowa daga kan gadon.
Bathroom ya shiga ya sakewa kanshi ruwan sanyi, ajiyar zuciya ya shiga saukewa akai-akai ya dauki tsawon 30 minutes a haka kafin ya kashe ruwan tare da jan towel yayi waje.
A gaban mirror ya zauna tare da fara shafa lallausan lotion a jikinshi kafin ya mike ya nufi wardrobe, budewa yayi tare da zaro wani farin yard, shiryawa yayi kamar wani ango sai zuba kamshi yakeyi ya fito falo.
zaune ya tadda dattijo tare da wasu daga cikin yaran da suke mishi aiki suna hira suna ganin shi suka mike suna gaishe shi ko kallon su bai yi ba ya nufi gurin dattijo ya zauna tare da daura kanshi a kafadarsa.
A hankali kuma cikin shagwaba yace “papa yunwa nakeji”
dungure masa kai yayi yana cewa “ba nace ka daina kira na da wannan sunan ba”
baki ya tura kafin ya sake maimaita kalmar yunwa yake ji,
dago kan shi papa yayi ya dubi samarin da har yanzu suke tsaye yace musu “zaku iya tafiya, kai kuma bilya jeka kitchen kace kuku ya hadowa shamsu abinci” yayi magana yana kallo daya daga cikin samari.
‘kwabe fuska yayi kamar zaiyi kuka yace “please papa ka daina ce min shamsu ni wllh ba sunana bane”
dawo da duban sa gareshi papa yayi ganin yanda ya wani kwabe fuska yana magana da iya gaskiyar shi shine yasa shi cewa “toh fadamin meye sunanka tunda ni ban sani ba?”
aiko yayi sauri wurin furta “deen ni sunana deeni idan bazaka iya fada ba kuma kayi shiru” yayi magana yana mikewa ganin an gama hada masa abinci
zama yayi a gaban abinci ya zubawa papa ido kamar mai neman wani abu a jikinshi, ganin yanda ya zuba masa manya idanunshi yana kallo sane yasa papa fadin “toh kaci abinci mana me kake jira ko kuma kaji nace zanci ne daka wani tsareni da ido kana kallo”
jin abinda papan yace ne yasa shi yunkurin tashi,
da sauri papa yace ” yi hakuri zauna gani nan zuwa” yayi maganar yana mikewa tare da zuwa inda yake ya zauna,
cokali ya dauka tare da debo jollop rice din ya kai masa baki amsa yayi tare da lumshe ido yana ci,
a hankali papa ke bashi abincin yana ci kamar yadda suka saba har ya kauda kai alamar ya koshi ruwa ya bashi yasha kafin ya mike ya koma kan kujera, zama yayi tare da dauka remote yana chanja channel zuwa news.
Duban shi papa yayi tare da cewa “wato amfani na ya kare koh shine harda tashi ka barni a gurin”
murmushi yayi wanda ya bayyana tsantsar kyan sa yace “yi hakuri papa na dauka kai ma zakaci ne”
harara shi yayi tare da cewa “sai ka sauke dan ni ba ci zanyi ba”
TV ya kalla kafin ya juyo ya kalli papa, murya a sanyaye yace “papa ina so zan fita” hade fuska papa yayi kafin yace “ina zakaje nifa banaso irin wannan yawon” marairaicewa yayi kamar karamin yaro yace “please papa Allah ba jima wa zanyi ba”
sanin halin shi na naci akan abu ne yasa papa cewa “naji toh amma ba kai kadai zakaje ba”.
da sauri yace “na yarda zan dauki baba manu muje tare” murmushi yayi irin tasu ta manya yace “toh Allah ya tsare amma dan Allah shamsu banda neman rigima kaji koh”.
“TOH” kawai yace ya dauki wayar shi yayi hanya waje, a haraban gidan ya hango baba manu yana zaune tare da mai baiwa fulawa ruwa suna hira ganin fitowar deeni yasa ya nufi gurin shi da sauri tare d gaishe shi.
amsawa yayi cikin jin dadi yace “deeni yau kuma shigan tamu ta hausawa ka tuna ne?” .
dan murmushi yayi yana shafa kanshi ba tare da ya bashi amsa ba yace, “baba fita zamuyi” jin hakan yasa baba manu lalubar aljihun shi yana jin makullin mota da sauri yace “muje” a tare
suka nufi parking space din baba manu ya bude mai baya ya shiga shi kuma ya koma ya shiga gaba yaja mota suka fita.
*************
Tafiya take tana sauri ganin har magrib ya kusa amma bata sami wani abun hawa ba, juyawa bayanta tayi jin maganan wasu dab da bayan ta, waro idonta tayi ganin samari hudu ke tunkaro ta, a kidime ta juya sai ji tayi d’aya daga cikin su yace, “haba yan mata tsaya mana kar kiji tsoro”
bata tsaya ba sai saurin data k’arawa tafiyarta jin basu daina biyota ba yasa tayi mugun tsorata ganin sun kusa cin mata suna fadin “haba y’an mata karki ba damu mana” yasa ta tattare kasan siket dinta bata jira komai ba tasa gudu suma suka rufa mata baya jin sun biyo bayan tane yasa ta fashewa da kuka, gudu take tana kuka hade da addu’a Allah yasa ta samu abin hawa…
*******************
bude musu tamfatsetsen gate din gidan security sukayi baba manu ya cinna hancin motan waje suka fice, suna fitowa suka maida suka rufe shi kirif.
Tafe suke a mota har lokacin kuma deeni bai cewa baba manu ga inda zasu ba har sun kusa iso wa titi, shi kuma bai tambaya ba, domin inda sabo yaci ace ya saba da halinshi wata rana ma haka kawai zai sa su yi ta yawo a gari sai ya gaji dan kanshi yace su koma ya karashe zance zucin davyin corner fita daga layin su…
Tun daga farko layi ya hango kaman mace ke gudu wasu maza na binta sake dubawa yayi tabbas wata ke gudu suna binta, kara gudun mota yayi yanason ya iso su domin sun dan yi musu nisa gashi babu kowa agurin,
dago kanshi deen yayi jin baba manu ya kara gudu sai dai kuma baice komai ba ya mai da dubanshi kan wayarsa,
horn baba manu ya fara danna musu,
jin kamar karan mota a bayan su yasa su juyawa ganin mota ya kusa iso sune yasa suka chanja hanya,
juyawa ta sake yi ganin ba samari ne yasa ta tsayawa tana haki, a tsorace ta dago ganin mota tayi parking kusa da ita.
Baba manu ne ya fito a mota yazo gurinta, baya ta fara ja tana girgiza masa kai, murmushi yayi yace “yarinya ba abinda zan miki taimako ki zanyi”
jin abinda yace ne yasa ta tsayawa tana sheshsheka,
tambayar ta yayi ina zata je, murya a dashe tace “gida”
sake tambayar ta yayi “anan kusa kike?”tace “aah” yace “toh kin yarda dani zaki shiga mota na ajiye ki ko a bakin hanya ne ki nemi abin hawa?” babu musu ta amince domin bata da wani zabi daya wuce hakan, mota suka nufa a tare,
ganin sun taho tare ne yasa deen jin ransa na zafi wani dogon tsaki yaja a dai-dai lokacin da suka shigo motar, a tsorace ta juya wani mugun kallo ya watsa mata ya maida kallo shi kan wayarsa,
ganin yanda ta tsorata ne yasa baba manu yin murmushi yace “karki damu ba abinda zai miki” daga kanta kawai tayi ba tare da tayi magana ba,
shiru duk sukayi ba wanda ya sake magana har suka iso bakin titi, tsayawa baba manu yayi tare da cewa mun iso,
kanta ta dago godiya ta mai ta sauka yaja mota sukayi gaba mai adai-adaita ta tsayar ta shiga tare da fada mai inda zai kaita,
suna fara tafiya taji ringing din wayar ta, zaro ta tayi a jaka tana duba sunan mai kiran zuciyar tane yayi mummunan bugawa ganin sunan yayan ta a fuskar wayan hannu na rawa ta daga,
jin ta daga kuma tayi shiru ne yasa shi yin magana a dan fusace yace, “kee miemah wai meya hanaki dawowa ne har yanzu?” murya na rawa tace “please yaya kayi hakuri wallahi abin hawa ne babu amma yanzu ma na samu ina hanya”
Ajiyar zuciya ya sauke jin tana lafiya, dan a duniya babu abinda yake so da kuma kauna kamar ta, ya tsani ya ganta cikin damuwa, jin yayi shiru ne yasa ta fadin “yaya”
da sauri yace “toh shikenan sai kin dawo” ya katse kiran.
********
Deen ne ya dubi baba manu a kumbure har yanzu bai daina jin haushin daukan yarinya nan da yayi ba, yace “baba nifa na gaji da zama kuma har yanzu banga mun iso inda zamu ba”
guntun murmushi baba manu yayi yace “toh banda abin ka Deenu yaushe kace ga inda zamuje da har zakace wai ka gaji” yatsina fuska yayi yace “shopping mall zamuje”
“toh” kawai baba manu yace mai ya nufi wani babban mall dake nan kusa dasu…
Tana sauka daga adai-adaita ta bashi kudi kafin ta wuce gida, a bakin kofa taga yayan nata da alama ita yake jira gun shi ta nufa tana zuwa ta fada jikin shi a shagwabe tace “yaya na gaji” dan tureta yayi hade da dungure mata kai yace “ni na aike ki ai da zaki wani ce min kin gaji wuce muje” ya karasa maganar tare da jan hannunta suka shiga gida.
har daki ya rakata kafin ya juya ya nufi nashi dakin.
kan gado ta fada hadi da sauke numfashi mai nauyi, a hankali kuma abinda ya faru ya fara dawo mata kwalla ne ya cika mata ido, a zabura ta tashi jin saukan duka a bayanta duba ta kai a bakin gadon momy ta gani tsaye a kanta tana girgiza,
baki ta bude zatayi magana ta buge bakin tana huci tace “wato ke dan ubanki bazaki chanja ba, kin raina ni, kin raina kowa ko, tun yaushe na aike ki amma sai yanzu zaki dawo, kuma kin dawo din ma bazaki iya zuwa ki fadamin yanda kuka yi ba, wato idan na damu nazo da kaina ko?”
kwallan daya taru a cikin idanunta ne ya zubo mata ta share da sauri kafin a hankali tace “kiyi hakuri na kai mata aiken kuma tace zata kiraki bayan haka ni bata sake ce min komai ba”
Tsaki tayi cikin takaici ta juya tayi waje
bayan fitan momy kuka ta fashe dashi tana Allah wadai da hali irin na matan baban ta, ita dai bata ga wani abu data tsare mata ba amma duk tabi ta tsaneta sai da tayi kuka mai isar ta kafin ta tashi ta shiga bathroom wanka tayi hade da alwala ta fito hijab tasa ta tada sallah jin ana ta kira a masallatai bayan ta iddar, doguwar riga kawai ta zura ta fito ta nufi side din yayan ta..
*********
Suna isa shopping mall din bangaren kayan zaki deen ya nufa chocolate da sweet ya diba da yawa sannan ya koma bangare wine ya fara zaban duk wanda ya masa, juyawa yayi ya dubi Baba Manu dake biye dashi jin bai ce masa komai bane yasa shi ci gaba da abinda yakeyi yana gamawa gurin biya yaje ya biya suka fita…
Ɓangaren driver Deen ya fada shi kuma Baba Manu ya zauna a dayan side din, da gudu deen yaja mota suka hau hanya, gudu yake sosai ganin har anyi sallah, har suka isa ba wanda yace wani abu.
Deen na parking, masallaci ya nufa sai da yayi sallah ya jira akayi i’sha kafin ya shige cikin gida, Baba Manu da papa suka biyo bayan shi, papa na tambayar baba manu ina sukaje ya fada mishi, suna shiga gida bayan deen papa ya bi ya same shi a falo yana k’ok’arin cire kaya, “a’ah Shamsu meye haka yau kuma anan din zaka cire kayan, toh in ka cire wa kake so ya dauke maka” kwabe fuska yayi kamar zai yi kuka yace “please papa ka barni mana na gaji ne, kuma wanka nakeso nayi” harara ya maka masa yace “toh ko anan ne zaka yi wankan tinda ka gaji?” turo baki kawai yayi ba tare daya ce komai ba ya shige daki ya bar kayan a wajen.
Bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya fito yayi shirin bacci, falo ya fito ya samu papa zaune yana duba wani littafi bai kula shi ba, wajen fridge yayi ya bude ya dauki chocolate da beer guda daya wanda Baba Manu ya shigo masa dashi dazu.
juyawa yayi zai koma daki da sauri papa ya taso yazo gaban shi kallo shi yayi tare da kallo kwalba dake hannun shi yace shamsu “meye wannan”
fuska a hade yace “meka gani?” kwalban hannu shi ya nuna masa yace “meye acikin wannan kwalbar” kallon kwalban yayi ya kalli papa bai ce komai ba yabi ta gefenshi zai wuce, sake matsowa papa yayi yace “ina tambayar ka kana tafiya” shiru yayi bai yi magana ba, tsawa papa ya daka mishi yace “wai ba tambayar ka nake yi bane?” a zuciye ya buga kwalban a kasa ya fashe cikin fushi yace “toh ga abinda ke ciki ka gani” ya fada a zuciye tare da watsar da chocolate din yayi daki…
Kallon shi kawai papa yake har ya shige daki, mai da duban shi kan kwalbar yayi, jini ya gani a kasa da alama kwalba ta soki Deen, runtse ido yayi ya bude yana jin ba dadi a ranshi, a hankali ya tattare kwalaben ya gyara falon dan mai aikin ya fita gun su bilya kuma bayason takura masa.
sai lokacin ya nufi dakin deen kwance ya gan shi akan gado yayi rigingine, kafan shi ya kalla har lkc yana dan fidda jini, akwatin maganin shi ya duba yazo ya kama kafar a hankali ya zare kwalbar dake cikin kafar, d’an yatsine fuska yayi alamun yaji zafin cire kwalban, yana gyara mai kafan ya fita ya koma dakin shi ya kwanta. Bangaren Deen kuwa gyara kwanciya yayi domin duk abinda papan keyi yana jin shi kawai dai shiru yayi bai yi magana ba, dan haushi shi yake ji a hankali kuma bacci ya dauke shi.
************
murda handle din kofar dakin yayanta tayi ta shiga, murmushi tayi ganin shi kwance a tsakiyar falo hannu shi rike da remove da alamu kallo yake, a hankali ta karasa kusa dashi tana lallabawa da karfi tayi tsalle ta fada jikin shi tana dariya,
kara yayi mai dan karfi dan yaji zafin hakan da tayi, mikewa yayi zaune tare da ita a jikin shi, kunne ta ya kama ya murda da karfi shi ma, ihu tasa masa da sauri ya sake ta yana kallo cute face dinta, dariya tayi kafin ta koma jikin sa tace “yaya yunwa nakeji”.
kallo ta yayi yace “baki ci abinci bane”
kai ta daga mishi, tashi yayi ya shiga kitchen dan yasan ba’a bata bane, abincin sa ya dauko musu ya dawo kusa da ita ya zauna,
zuba musu abinci yayi suka ci bayan sun gama ne ya kwashe komai ya mai da kitchen ya dawo kusa da ita ya zauna kallo ta yayi yaga hankali ta na kan tv a nutse ya kira sunanta,
juyowa tayi tana kallo shi da murmushi a kan face dinta, hannu yasa ya dan ja kumatun ta kafin a sanyaye yace “miemah gobe zan koma makaranta” da sauri ta juyo tana kallon sa tana yin rau rau da ido kamar zata yi kuka tace “ya Imran me kace?”.
jawota jikin shi yayi yana dan bubbuga bayanta a hankali yace “school zan koma gobe” kuka ta saka masa kamar karamar yarinya, lumshe ido yayi ya bude ya dube ta yace, “haba miemah kiyi hakuri mana ba fa jima wa zanyi ba idan naje makarantar, one month kawai zanyi na dawo kuma kinga ai kema next week zaki koma makaranta ko” yayi maganar cikin sigar lallami.
Kara sakin kuka tayi da ta tuna in har yabar gidan nan toh shikenan batada wani sauran jindad’i, dama shi ke debe mata kewa sai kuma dady toh gashi shi kuma dady bayan nan saukin ta ma ya kusa dawowa, dago fuskantar ta yayi yana share mata hawayen da suka ki tsayawa,
kallon ta yayi yace “kiyi shiru mana miemah ko so kike nima nayi kukan ne?” ya fada kamar zai sakar mata kukan, da sauri ta girgiza masa kai yace “toh shikenan in baki so nayi kema ki daina”.
Da sauri ta share idonta tace “toh ya imran na bari” murmushi yayi yace “good girl toh fadamin me kikeso na siya miki kafin na tafi” ”
babu” tace tana sake mannuwa a jikin shi, hararar ta yayi yace “bazaki fada ba kenan” tura baki tayi tace “ni kudi nakeso ka bani” dungure mata kai yayi yace na sani ai dama sukayi dariya….
Ganin ta fara lumshe ido alamun ta fara jin bacci yasa shi tashi yace “tashi muje ki kwanta ko my baby” ya fada cike da tsokana, murmushi tayi har daki ya rakata ta kwanta yaja mata bargo hadi dayi mata addu’a ya kashe wuta yace “good night love you” ya ja mata kofa sannan ya tafi na shi dakin….
*_Oummu Amna ce, mu haɗu a next page, yawan comments dinku zai sa na fahimci cewa kun karbi labarin da hannu bibbiyu Ngd_*[15/03, 11:11 am]
SHAMSUDDEEN
(Gangster)
* Oummu Amna*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Page 3 – 4
Washe gari bai tashi a bacci ba sai bayan sallah asuba sosai rashin tashin nashi ya bashi mamaki kuma Papa baizo ya tada Shiba
“toh kodai yazo naki tashi ne”
ya tambayi zuciyar shi tsaki yayi ganin babu mai amsa mishi tashi yayi zaiyi toilet aida sauri ya koma ya zauna yana rintse Ido jin wani azababen zafi cikin tafin k’afan shi
da hanzari ya koma ya zauna abakin gadon.
Dafe kanshi yayi daya tino jiya ya taka kwalba kafin ya kwanta, d’an karamin tsaki yaja yana sake daidaita zaman shi kamar bazai mike ba sai kuma ya mike yayi hanya bathroom yana d’an d’ingisa k’afan dan tanayi masa zafi saboda kwalban daya taka babba ne ba k’arami ba,
yana shiga shower ya kunna ya sakarwa kanshi ruwan sanyi yadau kusan minti 10 agun kafin ya kashe ya janyo towel ya daura brush yayi tare da alwala sannan ya janyo wani karamin towel a hanger ya fito.
Janyo kofan yayi ya rufe yana cigaba da tsane gashin kansa harya k’arasa gaban mirror ya dauko lotions dinsa mai k’amshi sosai daga tsaye nan ya shafa, yana gamawa ya jawo mayukan gashinsa ya shafa ya shiga combing gashin nasa
yana gamawa ya dauko wani mayin daban ya dauko yana ma matsi kad’an yana murzawa a hannu kirjinshi naga yana shafewa dashi take gashin gurin ya dauki wani irin kyalli da shek’i (niko nace wani sabon salo🤔😉😂lol)
Wardrobe dinshi yabude ya dauko wata riga harmless ta kamfanin Armani ya sanya sannan ya zare wando na kamfanin adidas shima ya sanya bayan ya sanya short niker aciki ,
Sai daya gama shiryawa ya dauki prayer mat ya shimfida sannan ya kabbarta sallah zama yayi a sallayan bayan ya idar da sallah sai daya kammala azkar dinshi duka sannan ya mike ya nade abin sallah ya koma kan gadon shi ya kwanta.
Wayarsa yajanyo wanda rabon shi da amfani da ita yau kwana uku kenan danne danne ya fara kafin ahankali kuma ya bude data news ya fara dubawa yana wuce duk wanda baiyi masa ba.
Daka tawa yayi dai dai kan wani photo dan harya wuce sama ya dawo baya ware manya farare ayes dinsa yayi yanabin wanda ke jikin photo da kallo wanda akeyiwa murna dawowa k’asar Nigeria bayan Shekaru masu yawa da yayi akasar waje da sunan yaje wani aiki.
Ido ya zubama photo tabbas koda ace zai manta kowa a cikin duniyan nan bazai taba manta fuskan najikin photo nan ba domin shine silar wargajewar duk wani farincikisa tin yana d’an k’aramin yaro, yarasa duk wani gata da kulawa wanda iyaye ke baiwa ya’yansu tin baifi d’an shekaru goma aduniya ba ya rasa d’an uwansa da suka fito tare alokaci guda ya rasa k’anwarsa dayafi kauna fiye da rayuwarsa.
Dafe kanshi yayi wanda yaji yana barazanar tarwatsewa gumine ya fara tsatstsafo masa tako ina acikin jikinshi jijiyoyin kanshi duk sun mike sunyi rud’u rud’u idanunshi sunyi wani irin ja kamar an zuba masa yaji aciki huci kawai yake yana b’ari dukkanin wani sassa na jikinshi rawa suke.
Kallo photo yake yana sakewa yanajin zuciyar shi nayi masa wani irin kuna kamar ana hura masa wuta aciki ayanda zuciyar shi ke bugu inda ace akwai wani atare dashi a wannan lokacin babu wani abu da zai hanaka jiyo sautin bugunta, dan sosai take harbawa har rigar dake jikinshi na d’agowa sama.
Numfashi shine yaji ya fara d’aukewa dan yanda zuciyar shi ke bugawa ya wuce limit din daya kamata ace ta buga, tari ya fara anajan numfashi da karfi juyawa yayi bakin gadonsa yana mika hannu da nufi dauko maganin shi dake cikin bedside drawer amma Ina ya kasa Koda bude drawer ne kirjinshi ya dafe yana wani irin tari kamar mai cutan asman idanunsa sunyi ja sun tara ruwan hawaye tsabar wahala.
Wani irin nishi yayi mai karfi wanda ya wuce da numfashi shi Chak numfashi sa ya tsaya wani irin mugun fadowa yayi daga kan gadon kansa ya bugu da tile’s din dake tsakiyan dakin yayinda hannusa ya bugi flowers rose d’in dake kan bedside drawer ya fado k’asa ya tarwatse.
Saida Imran ya kullo kofar gida sannan yayi flat dinsa nan ma rufe ko ina yayi sannan ya shige bedroom dinsa ya kwanta har yaja bargo ya tina bai had’a kayansa ba kuma gobe da safe yakeson tafiya d’an karamin tsaki yaja ya na mikewa wardrobe dinshi ya bude ya d’ibo duk wasu abubuwan bukatunsa ya shirya cikin k’aramin trolley dinsa, zuge zip yayi ya ajiye shi a gefe ya kwanta hade dayin addu’a bacci ya lumshe Ido.
Washe gari da safe ya riga Miemah tashi da ga bacci wanka yayi ya dauro alwala sannan ya nufi d’akin ta saida ya tasheta sannan ya wuce masallaci, ta jima tana kwance inda ya barta kafin ta mike ta shige toilet alwala ta dauro tazo ta tada sallah agurin ta kwanta ta sake komawa bacci dan sosai takejin baccin bai saketa ba.
Sai wajen k’arfe bakwai sannan Imran ya shigo gida kai tsaye dakin Miemah ya nufa dan yasan tanacan ta koma wannan bacci asaran nata da bashida wani fa’ida, yana tura kofar d’akin ya hangota kan sallaya aikuwa dai baccin take yi dama ya San za’a rina.
“Miemah, ke Miemah tashi mana ”
“Uhm ya Imran menene?”
“Kaniyar kine” ya bata amsa yana d’ago ta zaune.
Bude duka idanunta tayi ta na kallonshi
“Ya Imran na tashi” ta fada tana murza idanunta “yauwa tashi zakiyi ki chanja kayan jikin kinan sai kizo ki sameni a dakina mu karya dan da wuri nakeson tafiya karna rasa mota kinji”
“Toh ya Imran yanzu zanzo”
tayi maganan idanunta na cikowa da kwalla dan ko kad’an batason tafiyan nan nashi ayau taso ace tare zasubar gidan nan amma shine zai tafi yau ya barta
“Lafiya Miemah meya faru rakanin ne bakyason yi mo meye naga kina Shirin yin kuka?”
“A’ah ya Imran niba haka bane kawai dai banaso ka tafi ne”
ta fad’a tana share kwallan da suka zubo mata
“Toh amma ai nace miki bazan jima ba ko, kuma ai naga kema next week zaki koma naki
Makaranta ko? Dan haka kiyi shiru ki daina sanya wani damuwa aranki kuma ma in kinaso ai zaki iya komawa makaranta gobe ko? sai kiyi zaman ki a hostel ki jira randa zaku fara lectures koba haka ba tawan?”
ya fada yana kashe mata Ido
“Toh shknn yaya nima goben kawai zan koma na jira zuwa next week d’in acan”
ta fad’a tana dariya dan gaskiya ya kawo shawara mai kyau saboda batajin zata iya zama har sati acikin gidan nan ba tare dashi ko Dady d’ayan su na nan ba
Mikewa yayi ya na fadin “toh ko kefa yanxu dai kiyi sauri ki shirya sai kizo mu tafi
“Toh gani nan zuwa”
ta fada tana mikewa
Fita yayi a dakin ya nufi nashi dakin dan daura musu abinda zasuci kafin su fita,
yana fita doguwa riga ta janyo ta zura tana fadin
“wllh bazanyi wanka yanzu ba gaskiya saina dawo zanyi in yaso daga nan ma naje gidansu binta inji ita yaushe zata koma makaranta”
Tana saka rigan mayafin shi kawai ta dauko tare da jakanta wanda abubuwan bukatunta ke ciki ta fice a dakin tare da janyo kofa d’akin ta rufe tana juyo suka had’a Ido da momy dake tsaye kofar kitchen tana kallon ta, kallon kasa tayi tana fadin….
“Ina kwana momy”
“Lfy, ina kuma zaki da sassafen nan na ga kin fito harda wani jaka a hannu?”
Momy ta tambaye ta tana zabga mata harara kamar idanunta zasu fito
“Uhm dama ya Imran zan raka”
“Ina zaki rakashi!”
“Park zan rakashi ya hau mota wai yau zai koma makaranta” ta fada idanunta na cikowa da kwalla
“Daga tambaya sai kuma nace kimin kuka ko dan tsabar munafurci dake damun ki?
“Kiyi hakura”
“In naki fa ni wuce kiban guri shshahs kawai, yarinya kamar tafi kowa hawaye da zarar kai mata magana saita fara ma kuka kamar wacce aka daka”
Momy ta fad’a tana jan tsaki
Ita dai Miemah bata ce kokai ba sum sum ta wuce tayi flat d’in yayanta dan tasan in taci gaba da tsayuwa zata iya maketa,
saida ta tsaya ta gyara fuskanta ajikin madubin window d’akin shi sannan tayi nocking ta shiga d’akin tare da sallama a bakin ta,
Zaune ta same shi tsakiyan falon da kayan shi a gefe yana sipping coffee ga ga kuma cooler da flask a gaban shi da alama nata ne ita ya had’awa breakfast dan dama shi sam bai karyawa da sassafe
“Ya Imran karyawa ka farayi ba tare daka jirani ba”
Ta fad’a tana tura d’an karamin tsukekken bakin ta
Murmushi yayi yana fadin
“Toh y’ar rigima ni babu abinda naci
L coffee nake sha ba tea ba bare kice na shanye, ga tea nan da kwai na soya miki sai kizo kici mu tafi kiyi sauri kar atafi a barni”.
Wazai tafi ya barka bayan kuma motan haya zaka bi ai nasan ko wannan ta tafi za’a samu wata wanda zata tafi bayan ita
“Toh naji sarkin surutu zakizo ki zauna kici abinci ne ko zaki tsayamin surutu?”
“Zanzo ya Imran nawa”
Ta fada tana kashe masa Ido
Dariya yana girgiza kai kawai dan yasan halinta inya biye mata nan sai sukai k’arfe 10 basu tafi ba
Ruwan tea ta zuba a cup sannan ta debi soyayye kwan ta had’a da bread ta faraci, saida taci ta koshi sannan ta dubeshi tana d’an murmushi tace
“Ya Imran na koshi zamu iya tafiya”
“Su kuma sauran da kika rage wa kikeso ya cinye miki ya wanke kwanon?”
“Kai ya Imran waye kuma zai cinye bayan ni? ai in mukaje na raka ka ina dawowa nan zan dawo yau a dakin nan ma zan kwana insha AC yanda nakeso”
“Saboda a d’akin ki babu ko kuma me nifa banson gulma ya fada yana hararanta”
“Akwai mana kawai dai na d’akin ka yafi dadi ne”
Ko kulata baiyi ba dan yasan inya biyeta shiririta zatayi masa, mikewa yayi yana daukan jakan laptop dinshi d karamin trolley dinshi yana fadin
“Zaki tashi mu fita ne ko kuma sai kin gama surutu zaki fito”
Yayi magana yana duban wayan sa sake ringing
“Kin gama harya iso muna nan ko fita a d’akin ma bamuyi ba”
“Waye ya iso ya Imran”
“Ina ruwanki da koma waye yazo kekam ki tashi muje mana ai in mukaje zaki ga koma waye ne ko?”
“Toh muje naga kamar ma ka masu da tafiyan nan Allah Allah kake ka tafi ka barni dama na dameka”
“Kedai kika sani koma meye zaki fad’a sai kiyi ta fad’a neman magana ne na sani kuma ba kulaki zanyi ba”
“Ohh haka ma zakace ya Imran ba rarrashi na zakayi ba?”
“Uhm nidai kinga fita na inkin gama ki same ni a waje”
Ya bude kofa ya fice ya barta dan yasan inya biye ta Miemah bazai tab’a tafiya ba
“Kai ya Imran wllh ya ganoni”
ta fada tana dariya
Itama fitowa tayi ta janyo kofan d’akin ta rufe, abakin kofar gida ta same shi tsaye jikin wata mota sai dariya yake da gani dana cikin motan yake magana
“Yauwa kaga ga kanwar takama ta k’araso ko aida na dauka ma bazata fito ba”
Imran ya fada yana kallon Miemah dake tsaye bakin kofa tana murmushi
Sagir ne ya lek’o da kanshi ta window yana kallon ta yace
“A’ah k’anwarmu yau kuma babu magana ne kod’an gaisuwa nan ma yau babu to ina kwana”
“Rufe fuska ta yi ta na dariya ta ce kai ya Sagir banaso”
“oh gaisuwa tawa ce bakyaso kuma”
“Aah nidai bance ba””Toh me kika ce”
“Ba komai, ina kwana”
“Lfy klau y karatu””Alhmdllh dama tare zaku tafi”
“Ehh mana bai fada miki ba”
“Aah nikam bai fad’a min ba”
“Dan Allah kazo mu tafi kar kasa rana tayi muna garin nan inda baso kake muyi isan dare ba”
Imran ya fada yana sanya jakan shi a seat din baya
“Toh Miemah mu zamu wuce ga wannan sai ayi kudin abin hawa in an koma school ko” Sagir ya fada yana mika mata kudin dake hannusa
“A’ah ya Sagir ka barshi ya Imran zai bani” ohh kenan dani da ya Imran d’in akwai banbancu kenan”
“A’ah yaya ni bance ba” toh ki karb’a indai har da gaske ne kin dauke ni yayan ki” “toh nagode Allah y saka” “a’ah ni bance kimin godiya ba banso” “to shikenan Allah y tsare hanya” Ameen
Zagayawa tayi ta d’ayan barin tana tura baki tace ” Ya Imran wato shine harda shigewar ka kabarni ko to nidai bani kudin da nace ka bani inyi tafiya ta tinda kaima naga so kake ka tafi ka barni”
“Ohh sorry y’ar k’aramar kanwata ince dai ba fushi kikayi ba”
“Niba wani fushi da nayi kawai nidai ka bani”
“Yi hakuri to in wani laifin nayi kudin nakan gado na manta su acan ki kula karki karar dasu da wuri kinji ko”
“Toh badai ka bani ba kaikam ai shikenan kawai koma me naga dama shi zanyi dasu”
“Bye bye ya Imran bye bye ya Sagir Allah y tsare sai kun dawo a kawo tsaraba”
Tana gama fad’a ta shige cikin gida da gudu ta turo kofar
Girgiza kai kawai Imran yayi yana fadin “wato ma yarinya yanzu tabar jimamin tafiyan da zanyi na barta har wani murna ma naga tana yi”
Kwashewa da dariya Sagir yayi yace “lallaima wato kafison kullum in zaka tafi tayi tama kuka ko”
“Ehh mana”
“Toh kuwa baza tayi ba dan itama yanzu ta girma” Sagir ya fada yana tada motan suka kama hanya……
*_Oummu Amna ce, mu haɗu a next page, yawan comments dinku zai sa na fahimci cewa kun karbi labarin da hannu bibbiyu Ngd_*
[15/03, 11:11 am]
SHAMSUDDEEN
(Gangster)
* Oummu Amna*
08061474743
*Wattpad*
@OummuAmna123
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Page 5 – 6
Tinda ya fara tari ya janyo hankali kuku dake a falo yana aikin shirya breakfast toh amma saboda sanin halin shi yasanya baiyi gigi zuwar masa daki b yaci gaba da aikin shi karar fashewan rose dinne ya sake janyo hankalin shi barin shirya breakfast din dayake had’awa akan dinning yayi da sauri ya d’ago kansa tabbas karrar fashenwan abu kunnen sa yajiyo masa bayan haka ma kamar harda sautin fadowan wani abun yaji
“toh meye wannan meya samu yallab’ai da sassafen nan?”yayi maganan yana k’ara kallon kofar d’akin.
Ahankali ya nufi kofan d’akin danya kasa jurewa dole ne yaje ya duba halinda yake ciki koda ace hakan zaisa wani abu ya sameshi ne dan yana da tabbacin inhar ya sameshi Ido biyu to babu abinda zai hanashi yi masa mummuna duka dan in yana cikin fushi irin wannan wanda harya kaishi ga fasa wani abu toh babu makawa duk wanda yazo wajen shi a wannan lokacin shima zai iya fasa shi babu abinda ya dame shi.
Dai dai ya iso kofan dakin ya daura hannushi akan handle din kofan amatukar tsorace yake amma dukda haka bai hakura ba burd’a handle din kofan yayi ahankali kofan ta bude rintse idanunsa yayi yana tura kofan bai bude ba saida ya tabbata kofar ta bude duka ahankali yake bud’e idanunsa zuciyar shi na tsananta bugawa dan tsoron ganin fuskarsa yake har cikin ransa.
Ajiyar zuciya mai karfi ya sake ganin bai ganshi a gaban sa ba kamar yadda yayi sammani fes yake kallon ko Ina na dakin kafin ahankali ya sauk’e idonsa kan gadon Deen danshi a tinaninsa tinda yaji shiru maybe bacci yake ya buge wani abin bai sani ba ya fado k’asa.
Wani wawan tsalle ya dake sai gashi manne jikin kofan d’akin ya rungume ta kam kam meye haka idanunsa ke gani kamar dai yau baya gani dai dai, Deen ya hango kwance a kasa babu alaman numfashi ko wani rai ajikinshi ga bakinshi na fidda wani irin kumfa kamar wanda yasha omo, murza idanunsa yayi ya sake bud’e su tabbas shine yallab’ai ne
Da wani irin mugun gudu yayi hanyan d’akin Papa ko nocking bai tsaya yiba bare jiran izinin shiga ya banka kofan da karfi yana kiran “Alhaji your son your son” kasa k’arasa maganan yayi ganin babu kowa acikin d’akin bai tsaya duba yana cikin toilet ko bayinan ba kawai yayi cikin gidan d gudu.
“Alhaji Alhaji”
tin kafin ya k’arasa fita yake kwalama Papa kira cikin muryanshi ta y’an asalin Lagos danshi Sam bai iya wani Hausa ba zaman shi acikin gidanne ma yasa shi fara fahimta wasu abubuwa daga cikin Hausan.
Papa, Aliyu, baba manu tare da sauran samarin gidan zaune a wajen zamansu na kullum kamar ko yaushe yanzu ma zaune suke suna shan Lipton suna hira abinsu gwanin burgewa
Ganin yanda Samuel ya fito daga cikin falo a matukar tsorace ne ya sanya dukan su mikewa Aliyu ya sanya hannu bayan wando shi yana zaro wata y’ar k’aramar bingida ya rike ahannu shi, kai tsaye gaban Papa ya nufa wanda ya hango tun fitowarsa faduwa yayi agaban sa yana haki yana fadin.
“Alhaji Alhaji your son your son is died”
Dukansu Ido suka zuba masa suna kallo dan sun kasa fahimta abinda yake nufi kamar kunne su bai jiye musu dai dai ba haka sukeji.
Papa ko wani irin gigitacce mari ya zuba masa ba tare da sanin ma yayi hakan ba.
Dagosa Papa yayi yana fadin”Samuel do you know what are you saying”
“Yes sir I know I swear to God I saw him with my own eyes”
Ya fada yana kuka kamar k’aramin yaro.
Bai tsaya ya k’arasa jin abinda yake fad’a ba yayi cikin falon da gudu kai tsaye dakin Deen ya shiga hangosa yayi kwance baya ko motsi da hanzari ya k’arasa zuciyar shi na bugawa
ahankali ya durkusa kusa dashi daura hannusa dake rawa yayi akan hancinshi yaji baya numfashi wani irin tsoro ne yaji ya shigeshi amma ya daure ya maida hannusa kan kirjin shi shiru yayi ya Maida dukan hankalin shi kan hannusa so yake yaji zuciyar shi na bugawa kota tsaya shiru yaji babu alaman bugawa sai can yaji kamar tana bugawa ahankali ta can k’asa sake saurare yayi tabbas bugawa take,
Da sauri ya juyo ganin Aliyu na tare da biyu daga cikin samarin gidan ne sashi fadin Aliyu kira likitan Shamsu kace masa gamu nan zuwa yanzu, Kai Haruna Maza kuje ku tada mota Kai kuma Hashim zoka tayani d’aukansa duk yabi ya rud’e jikin sa sai rawa yake ya dawo abin tausayi.
Da sauri Aliyu yayi dialing number Dr kamar yadda Papa ya bashi umarni ‘shi kuma Haruna da gudu ya fita yayi gurin baba manu ya karba makullin mota yayi parking space fiddo motan yayi ya matso da ita bakin falon
Har wayan ta katse Dr bai daga hakan yasa Papa fadin “sake gwadawa wata kila baiji bane”yayi magana lokacin da yake taya Hashim daukan Shamsu, waje sukayi Aliyu yana sake gwadawa akayi sa’a Dr yadau wayan sallama Aliyu yayi kafin ya amsama Papa ya fizge wayan yana fadin,.
“Dr kana asibiti ko?” bai jira amsan shiba yaci gaba “toh gamu nan zuwa Shamsu ne bayi da lafiya yanxu ma bugun zuciyar shi sai k’asa yakeyi yayi kad’an dan ya kusa karewa ma”
“Subhanallah meya faru kuyi sauri ku kawosa asibiti ina nan bari nasa ashirya muku gado kafin ku k’araso”
Shidai Papa bai tsaya jin abinda Dr yake fad’a ba ya jefawa Aliyu wayansa ganin sun iso bakin mota ya shige abinsa Hashim dake dauke da Deen ma ya shigo bayan ya samu ya kwantar dashi abayan motan.
Gaban mota Aliyu ya shiga da sauri yana kara wayan a kunne shi ganin Dr bai kashe ba.
“hello Dr kana asibiti ko? Muna hanya dan yanxu ma mun fito daga gida”
“Ehh Aliyu ina asibiti sai kun k’araso”
“Toh Dr in sha Allah yanzu zamu iso” ya fad’a yana katse kiran.
Suna isa asibiti nurse suka taho da gudu suka daura shi akan gadon su ka tafi dashi har wajen emergency Papa da Aliyu suka bisu sai dai kafin su k’arasa ciki aka dakatar dasu
Taimakon gaggawa aka fara bashi amma sam jikin shi yaki amsan komai da akeyi masa gashi bugun zuciyar shi sai sake yin k’asa yake,
Sosai hankali Dr Adam ya tashi domin wannan alamace ta za’a iya rasa shi ako wani lokaci gumibe yake ta tsatstsafo masa tako ina dan lamarin ya fara wuce tinanin sa
“Sir bakaji nane? gudun zuciya nashi ya fara dawowa nrml kuma jikin nasa ma ya fara karban alluran da ake masa gashi numfashi nasa ma yana ta dawowa nrml”
Zancen nurse d’in dake gefen shi ya katse masa tinani da yakeyi da hanzari ya juyo yana kallon ta wani irin nannauyan ajiyan zuciya ya sauke yana hamdala acikin ransa,
Dan inda ace Deen ya mutu bayajin zai iya zuwa ya tinkari y’an uwansa da wannan zancen musamman ma Alh da Aliyu dan wllh yana da tabbacin wannan d’an daban yaron Aliyu zai shake masa wuya shima ya mutu tun lokacinsa baiyi ba
“Yauwa masha Allah duba can ki dauko wancan alluran kisa acikin drip din nan wannan kuma mika minshi na mai abarshi ya huta zuwa Anjima in sha Allah zai samu sauki”
“Ok sir”
Suna gamawa duk suka fito aka janyo kofan d’akin aka rufe
Papa dake zaune a kofan d’akin ya rafka uban tagumi ne ya mike da sauri ganin Dr Adam ya fito da hanzari ya k’arasa gurin shi yana tambaya ya jikin Shamsu “relax Alh jikin nashi da sauk’i yanzu mu k’arasa office ko akwai maganan da nakeso muyi da kai”
“To to! muje mu k’arasa ciki
Papa ya fad’a yanayin gaba tamkar shine Dr, murmushi Dr Adam yayi yana biye dashi abaya
Suna shiga kujera ya samu ya zauna Dr Adam ya k’arasa wajen zaman sa ya zauna yana gyara gilashin dake idonsa
“am Alh dama ba wani sabon abu bane yake damun Deen ba kamar dai yadda ka sani tsohon ciwon zuciyar shine ya motsa sai dai na wannan karon yafi na ko wanne lokaci hatsari domin kuwa wannan numfashi sa ya rike kuma duk abinda zai hana numfashi fita ba k’aramin abu bane
So ina tinanin da akwai wani abu daya ji koya gani wanda ya tina mishi da rayuwarsa ta baya wanda a sanadiyar hakane zuciyar shi ta fara bugawa fiye da ka’ida a dalilin haka kuma numfashi sa ya tsaya ya daina motsi kamar dai yadda kuka kawo shi
Ajiyar zuciya Papa ya sauk’e yana kallon Dr Adam kamar mai karanta wani abu akan fuskansa
Zumbur Papa dake zaune ya mike kamar wanda aka tsikara bakin shi na rawa ya fara nuna…………
*_Oummu Amna ce, mu haɗu a next page, yawan comments dinku zai sa na fahimci cewa kun karbi labarin da hannu bibbiyu Ngd_*
[…] Shamsuddeen Hausa Novel Complete […]