Littafan Hausa Novels

Shaidaniyar Yarinya Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Shaidaniyar Yarinya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

SHAIƊANIYAR YARINYA

 

 

BY

 

ZAINAB A BARDE

 

 

 

ALƘALAMI YAFI TAƘOBI WRITER’S ASSOCIATION (A.Y.T.W.A)

 

 

 

******

 

 

Page 1-2

 

 

 

Afirgice ya tashi daga nannauyan baccin da ya dauke sa jin ringing din wayarsa, a kasalance ya janyo wayar daga kan bedside drower ba tare da ya duba mai kiransa ba ya daga wayar yana karawa a kunne tare da lumshe ido, a gigice ya tashi zaune saboda jin muryar da bazai taba iya mantawa da ita ba a rayuwar sa koda kuwa a cikin bacci yajita, muryar da ya dade yana mararin sake jinta a rayuwar sa koda sau daya ne kafin Allah subhanahu wata’ala ya dauki ransa, ashai zai sake jin wannan muryar a rayuwar sa, “Yaya Damisa” ta kira sunan sa da wata iriyar kasalalliyar murya, lumshe fitinannun idanuwansa yayi da suke tsorata yan maza a filin daga jin sautin muryarta ya sake dukan dodon kunnen sa a karo na biyu, “Ameera! ya kira sunanta a chan kasan makoshin sa, a tare suka sauki ajiyar zuciya har ko wannen su na iya jiyo bugun zuciyar dan uwan sa ta cikin waya, fashewa tayi da kuka, jin sautin kukan nata ba karamin tayar masa da hankali yayi ba, lokaci daya ya birkici saboda jin yadda sautin kukan nata yake duƙan dodon kunnen sa, hakan ba karamin taba masa zuciya yakeyi ba, “Ameera kiyi shiru ki gaya min abinda yake faruwa, kinfi kowa sanin cewa banason ganin kukan ki” ya fada cikin wata irin kasalalliyar muryar da shi kansa baisan yana da ita ba, “Yaya Damisa zasu kashe mu, dan girman Allah kazo kanwar ka na matukar bukatar taimakon ka wanda a halin yanzo nasani kaf fadin duniyar nan a yanzo banida sama dakai” jiyai kamar an ta soka masa mashi a kirjin sa, “su waye zasu kashe ku?” kitt yaji ta kashe wayar, Kiran wayan ya yi ta yi bayan ta katse abin takaici amsa ɗaya yake samu a kashe take.

Secondary School Hausa Novel Complete

Yanayin yadda Amira take magana ya yi mutukar tsorata shi, tabbas akwai matsala, da alamu wani abu na shirin faruwa? Kirjinsa ya buga dam! A lokacin da ya tuna kalmomin da take amfani da su wajen nuna ana shirin kashe su? To wa ke shirin aikata hakan?

zumbur ya mike tsaye tamkar wanda aka tsikara da allura, lallai zama bai same shi ba.

A lokacin da ya fara tafiya ne fuskarsa ta bayyana a madubin ɗakin dogo ne sosai yana da haske da manyan idanuwa ga dogon hancinsa kamar biro, wanda kyawunsa ya fito rangaɗaudau! Tashin hankali da yake ciki yasa idanunsa suka chanja launi daga fari zuwa ja, “gani nan zuwa gareki kanwata” ya fada a fili babbar trolly dinsa ya dauko ya hada kayan da yasan zai bukata a ciki, tiolet ya fada a gurguje ya watsa ruwa ya fito, kayansa ya zura na kakin sojoji tare da feshe ilahirin jikinsa da turaruka masu kamshin gaske, zanso kuga irin kyawun da yayi a cikin kayan amma ɗai ku ƙiyasta wayoyinsa kawai ya dauka ya fito daga dakin, saukowa kasa yayi ko ina fes fes sai kamshi ke tashi, yana fitowa harabar gidan masu tsaron lafiyarsa suka mike suna tsara masa tare da ƙamewa, ko inda suke bai kalla ba ya bude wata jibgegiyar mota ya shiga, cikin azama suma suka fara kokarin shiga tasu motar hannu ya daga musu alamar baya bukata haka aka bude masa get ya fita daga gidan badan ran masu tsaron lafiyar tasa sun so ba saboda sanin yadda ake farautar rayuwar adalin ogan nasu, fatan Allah ya dawo dashi lfy suka bisa dashi, bai zarce ko ina ba sai headquarter dinsu ta sojoji, duk inda ya gifta tsara masa akeyi amma tashin hankalin da yake ciki bazai barsa ya bi takansu ba, darect office din shugaban sa ya wuce knowking yayi amma shiru ba’a basa izinin shiga ba, saida ya shafe kusan minti biyar sannan aka basa izinin shigowa, yana shiga ya tsarwa wa mutumin da ke zaune akan kujerar da alama shugaban sane, “Damisa lafiya na ganka yanzo bayan nasan aikin dare gareka” shugaban nasa ya tmby yana tsaresa da jajayen idanuwan nasa, takardar hannunsa ya mika masa yana kara tsara masa, daukar taƙardar yayi ya fara karantawa, dagowa yayi yana kallonsa cike da mamaki, “mai yasa kake naiman hutu harna tsawon shaikara daya?”,”Sir wata ujilace ta taso min daga gida dole ne saina tafi”,”amma kafi kowa sanin cewa bazamu taba iya baka wannan hutun mai tsayi harna shaikara daya ba ko?”,”nasani Sir, shiyasa ma na taho da takardar ajiye aiki” mika masa taƙardar daya zaro daga aljihunsa yayi, cike da tsantsan mamaki yake kallonsa ganin da gaske takardar ajiye aikin ce, ya sani cewa Damisa yana aikin soja ne badan ya samu kudi ba, yanayi ne dan burinsa ne aikin sojoji, amma mai yasa lokaci daya zai ajiye aiki, lallai akwai abinda yake boyewa wanda bayaso a sani, tabbas koma mene zaisa Damisa ajiye aikinsa to ya tabbata ba karamin abu bane ba, kuma a yadda suke alfahari dashi a cikin sojojin su bazai taba bari ya subuce musu ba, “bamu yarda ka ajiye aiki ba, mun aminci zamu baka hutu, amma ka sani hutun da zamu baka bazai wuce na wata daya ba”,”amma Si… daga masa hannu yayi, “na gama magana, zaka iya tafiya” haka ya fito daga office din badan ransa yaso ba, motarsa ya shiga ya nufi gida hankalin masu tsaron sa bai kwanta ba saida sukaga ya dawo gida, booking din jirgin da zai tashi daga kano zuwa Abuja karfe 4 na yamma yayi, a gurguje ya shirya dan lokaci ya rigada ya tafi, saura minti ashirin jirgin ya tashi, daya daga cikin yaransa ya kira suka fito masa da kayansa, a boot suka saka kayan shi kuma ya shiga bayan mota ya hakimce, da sauri Sunday ya shiga yaja motar suka bar gidan suma masu tsaron lafiyar sa baya suka rufa musu, saida yaga sun hau kan kwalta sanna ya tmby sa ina zasuje, “filin tashi da sauka jirgi na malam Aminu kano” cikin mintuna kalilan suka isa, suna zuwa aka fara kiran sunayen fasinjoji, sallama yayi da yaransa ya shige cikin jirgin yaran nasa basu tafi ba saida sukaga tashin jirgin ogan nasu sannan suka shiga cikin motocinsu suka kama hanyar komawa gida, “hello Sir yanzo jirgin Damisa ya tashi, ya hau jirgin da zaije Abuja ne” bansan abinda wanda yake wayar dashi yace masa ba, nagade ya saki murmushi mai cike da ma’anoni tare da kashe wayar keken sa mai kafa uku ya hau ya bar wajan, gyara zama mutumin yayi a cikin kayataccan falon sa, ajiye wayar hannunsa yayi akan kujerar da yake kai, “kaji fa Dattijo, Damisa ya hau jirgin da zaije Abuja yanzo daya daga cikin yaran da nasa suna samin ido akansa ya kirani yanzo yake fada min” lallausan murmushi wanda aka kira da Dattijo yayi ba tare da yace komi ba.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Shere fisabilillah.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment