Littafan Hausa Novels

Sanin Gaibu Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Sanin Gaibu Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

SANIN GAIBU

_Sai Allah_

ͲϴᏢ-ΝϴͲᏟᎻ 2023

*Mai_Dambu*

Page:01

Sadaukarwa ga Sa’adatu Ambassador, Maman Rumaisah, Shafin gabaki daya ta ce , Na gode da karamcin ki tare da gudummawar da kika bawa labarin nan Allah ya saka da alkhairi

 

 

_Shimfida_

 

“Ummina ki min addu’a!” Ya fada cikin matsanancin azaba, hawaye na zuba mata ta ce mishi. “Abu Turab naga gawar Abubakar ban yi kuka ba, na ga gawar Umar ban yi kuka ba, Abu turab me yasa nake kuka akan ka? Me yasa nake kuka???” Mother tears…….!

 

 

Emir of ilorin palace.

𝗔𝘀𝗮𝗹𝗶𝗻𝘀𝘂

 

Wadanda suka fara zama a Ilorin su ne Baruba wadanda suka zauna a can tsawon shekaru kuma suka dauki yankin nasu ne; sun tafi ba tare da sanin dalili ba. Sai kuma Ojo Isekuse, wani basaraken Yarabawa, wanda ya zauna kusa da dutsen kaifi inda mafarauta suka taru suna wasa da kayayyakinsu. An yi wa Ilorin suna ne bayan da dutsen kaifi da har yanzu yake wanzuwa. Ana zargin Ojo Isekuse ya fita ne bayan ya yi lalata da ‘yarsa, kuma wani dangi mai suna Asaju ya sauka a kusa da dutsen da ake yankan. Bayan Asaju ne mutane da dama suka zauna a kauyuka masu zaman kansu daban-daban da ke kewayen yankin da ake kira Ilorin a yau.

Cin Amanar Aure Hausa Novel Complete

A farkon karni na 19, Ilorin yana arewa maso gabashin daular Oyo, yana da yawan Yarabawa, Hausawa da Fulani. Ya zama hedikwatar wani Janar na Oyo, Afonja, wanda ya kasance sarkin yakin da kujerar Ilorin ce kuma wanda daga baya ya gudu don guje wa yakin kunar bakin wake da aka tura shi ya kashe shi bisa ga umarnin Alaafin na Oyo. Shi kuma wani malamin addinin Islama mai suna Shehu Alimi, wanda ya gudu daga Oyo saboda muzgunawa kungiyar asiri ta Ogboni.

 

Shehu Alimi da Afonja sun kulla kawance domin yakar sojojin Oyo da ke gaba sannan suka fatattaki sojojin Oyo a yakin farko. Alaafin ya yanke shawarar tura wata babbar rundunar da ta tabbata za ta kashe Afonja tawaye tare da kawar da malamin, Shehu Alimi, wanda ya ba da tallafin soji ta hanyar gayyatar Jama’a. Dakarun Jama’a da na Afonja sun kai wani harin ba-ta-kashi a Oyo-Ile, hedkwatar tsohuwar Daular Oyo, inda suka kona ta.

 

Ilorin ya zama babbar siyasa da soja bayan faduwar tsohuwar Oyo. Ba tare da sunan shugaba ba, Afonja da Alimi sun ba da jagoranci ga mutanen da ke zaune a yankin. Afonja da Salih Janta, wanda kuma ake kira Shehu Alimi, sun samu kyakkyawar alaka har zuwa lokacin da Alimi ya rasu a lokacin tsufa.

 

Bayan rasuwar Shehu Alimi, an yi takun-saka da sarautar Ilorin, gari ne mai tasowa. Alfas sun so kafa Halifancin Musulunci bisa ilimi, yayin da Afonja ke shirin sake kafa cikakken mulkinsa, amma Abdulsalam ya fito da taimakon mayakansa. Suna da kwakkwaran iko da Jama’a wanda shi ne mafi yawan sojoji a Ilorin. An kashe Afonja ne a lokacin mulkin Abdulsalam, a lokacin da wata hatsaniya ta barke tsakanin sojojin Yarbawa da Jama’a, wanda ya haifar da matsi na Afonja. An dakatar da addinin Yarbawa da Egungun a Ilorin saboda wannan lamarin. Ilorin ta zama masarautar Khalifancin Sakkwato.[1]

 

Na wani lokaci, Ilorin ta kasance babbar cibiyar cinikin bayi. A da, an fi tura bayi zuwa arewa ta hamadar sahara, amma yanzu ana tura su kudu ta kasashen Yarabawa zuwa bakin teku don samar da bukatu daga Amurka, Indiyawan Yamma, da Brazil. An kwashe bayi daga kasashen Ibo zuwa gabas da kuma garuruwan Yarabawa da aka ci da yaki, da kuma daga yankunan da ke gaba zuwa arewa, ana cinikin tufafi da sauran kayayyaki.

 

Ilorin ya ci gaba da fadada kudu har sai da aka duba shi a cikin 1830s ta ikon girma na Ibadan, jihar Oyo. Sojojin dawakan Ilorin ba su da wani tasiri a cikin dajin da ke kudu, kuma a cikin shekarun 1850 Ibadan ta sami damar samun bindigogi daga ’yan kasuwar Turawa a bakin teku.[1] Kamfanin Royal Niger ne ya mamaye babban birnin kasar a shekarar 1897, sannan kuma aka shigar da filayensa cikin yankin Arewacin Najeriya da Ingila ta yi wa mulkin mallaka a shekarar 1900, duk da cewa masarautar ta ci gaba da gudanar.

𝗗’𝗮𝗸𝘂𝗻𝗮 𝘂𝗸𝘂 𝗱𝗮 𝘀𝘂𝗸𝗮 𝗴𝗮𝗷𝗶 𝘀𝗮𝗿𝗮𝘂𝘁𝗮𝗿.

 

 

Saboda irin tarihin da ya ke da shi na musamman na Ilorin, na farko a matsayin Yarbawa daga cikin Daular Oyo, sannan a matsayinta na fulani mai mulkin Halifancin Sakkwato, tana da al’adar yin sarauta wadda ta kasance gauraya da al’adun gargajiya da aka samo daga bangarorin biyu. Duk lokacin da sarautar Masarautar (wadda ke hannun Fulani zuriyar Shehu Alimi) ta kasance babu kowa, wakilin kowace kwata a masarautar wato; Balogun Gambari (Hausa), Balogun Ajikobi (Yarabawa), Balogun Fulani (Fulani) da Balogun Alanamu (Yoruba) – tare da shugaban gidan sarautar Afonja, Mogaji Aare, da kuma babban hakiminsa mai suna Baba. Isale na Ilorin – a taru domin zabar sabon sarki tare da nada sabon sarki, bisa amincewar gwamnan jihar Kwara. Sannan an ba wa Balogun mafi dadewa sarautar Balogun hudu sarautar Balogun Agba, wanda hakan ya sa ya zama na biyu a kan Sarkin Ilorin. Dukkan Balogun na da gundumomi da suke gudanarwa a madadin sarki.

 

Akwai kuma sarakunan gargajiya da kowanne ake kiransa Daudu (ko Hakimin Lardi). Suna aiki ne a matsayin hakimai masu wakiltar sarki a garuruwan dake fadin masarautar Ilorin kamar su Afon, Bode Saadu, Ipaye da Malete, da dai sauransu.

 

Lakabi masu daraja a cikin.

𝗦𝗮𝗿𝗮𝗸𝘂𝗻𝗮𝗻 𝗠𝗮𝘀𝗮𝗿𝗮𝘂𝘁𝗮𝗿

 

Masu mulki

Gyara

Sarakunan Masarautar Ilorin:[3]

 

Fara Ƙarshen Mulki

1824 1842 Abdusalami dan Salih Alimi

1842 1860 Shita dan Salih Alimi

1860 1868 Zubayro dan Abdusalami

1868 1891 Shita Aliyu dan Shittu

1891 1896 Moma dan Zubayru

1896 14 Janairu 1914 Sulaymanu dan Aliyu

1915 Nuwamba 1919 Shuaybu Bawa dan Zubayru

17 Fabrairu 1920 Yuni 1959 Abdulkadir dan Shuaybu Bawa

30 Yuni 1959 1992 Zulkarnayni Gambari dan Muhammadu Laofe Dan Bawa “Aiyelabowo V”

1992 Agusta 1995[4] Mallam Aliyu dan Abdulkadir

1995 Zuwa Yau Ibrahim Sulu- Gambari

𝗠𝗮𝘀𝘂 𝗠𝗮𝗸𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗺𝗮𝘀𝗮𝗿𝗮𝘂𝘁𝗮𝗿

Masarautar dai ta shaidi irin karramawa ga fitattun ‘ya’yan Masarautar da Sarki na yanzu ya yi. Wadannan sunaye ne da aka ba su;[5]

 

Waziri of Ilorin Emirate

Turaki of Ilorin Emirate

Zanan of Ilorin Emirate

Dan Iyan of Ilorin Emirate

Grand Mufti na Masarautar Ilorin

Madawaki of Ilorin

Malami Ubandoma of Ilorin Emirate

Tafida of Ilorin Emirate

Shettima of Ilorin Emirate

Mutawali of Ilorin Emirate.

 

August -12- 2009

*10:30pm*

_Hawaye ne ya zubo mata, sakamakon hango shi da tayi yana wucewa duk da kasancewar dare ne amma hasken da ya haska harabar gidan ya hasko mata shi, yana tafiya cikin ruwa dauke da lema, da alamu ita yake nima. Tirjewa tayi mutumin da ya shake wuyarta ya kuma matseta, tare da jin wani bakon al’amari yana ratsa jikinta, cikin tsannanin azaba da masifar da bata tab’a haduwa da shi ba. Wani irin ajiyar zuciya take saukewa, tana jin kamar ta mutu ta huta. Haka ya gama keta alfarmarta sannan ya tashi a kanta, duk da bata ga fuskar shi ba, sai dai kamshin turaren shi ya tabbatar mata da waye a tare da ita. A hankali ta yunkura zata mike suka sake mai da ita, haka su hudu nan suka keta alfarmarta. Kafin daga bisani suka shake ta, sai da suka ga bata motsi sannan suka kyale ta_

******************************************

Sokoto State… Binji LG

Maikulki

Rabewa gefe tayi, ta dauki kokonta ta koma can jikin bango ta tsuguna tana sha hawaye na zuba mata. D’ago fararren idanunta tayi tana kallon Mahaifin su da ya shigo. Yana kallon tsakar gidan, “wallahi duk lokacin da na kalli Sa’adatu sai naji kunya ta kama ni, musamman idan ta fita cikin mutane ana nuna mu. Duk sai naji na muzanta. Shi yasa bana kaunar tana fita da shegen idanunta a wurin.” Ya fada yana tsaki. “Larai zuba min abin karyawan nan, kuma ki tabbatar sun shirya su tafi makarantar idan Allah ya jarabce ka da haihuwar bakar ƙaddara babu yadda ka iya, yanzu don Allah taya zata fahimci karatu.” Tab’e baki yayi yana kallon matar da ta fito daga madafin. Duban inda yarinyar take tayi na dan lokaci kafin ta ce mishi. “Bawa baya tab’a kaucewa ƙaddaran sa, Malam itama ba sayawa kanta tayi ba, duk da haka ba zai saka mu tsane ta.” Ta fada tana wuce shi. Tsaki yayi yana faɗin.”haka kawai an tashi an haifa min nakasashiya a cikin Yarana.” “Sai ka gayawa Ubangijin da ya baka ita ka ji” ta bashi amsa, daukar ƙara yayi nufi Yarinyar.

Ganin shi dauke da kara yasa ta sake kofin kunun hannunta, ta mike zare mata idanu yayi cikin masifa ya kira Yan uwanta. “Harirah, Rabi” fitowa suka yi sanye da Uniform, fari da hijab din su iya cinya. “Na’am Baffa” “ku bata kayanta itama ta biku tunda abin na munafunci ne ta tafi tunda na san ba gane kome zata tab’a yi ba.” “Wai Malam meye Sa’a ta maka ne? Makarantar nan dai wallahi ko kana so ko baka so dole ta je” “Assalamu alaikum, iyyi lafiya?” “Yaya wa’alaikumunsalam sallama, Alhamdulillahi gara da kika dawo wallahi na rasa yadda zan yi da Malam akan Sa’a ” kallon shi matar tayi,.kana ganin fuskarta kasan ranta yayi azababben ba’ci.” Gyada kai tayi sannan ta nufi wurin Yarinyar me suna Sa’adatu” “Tashi ki shirya yanzu na saka hansiya ta dinka miki kayan ki.” Murmushi tayi tana share hawayen ta.” “Innah laminde zamu makara fa” “kuje zan kawo ta” “ba da yawuna ba zaki fita na dai gaya miki” Malam ya fada yana kad’a babban rigar shi. Juyawa tayi ta ce mishi, idan kaga ban fita ba, tow bana numfashi shi ne fita ya zama wajibi ne” ta riko hannun Sa’a ta kaita banɗaki ta wanke mata jiki, zasu fita ta riko hannunta. Ta kanne mata ido daya, tare da mata alamar ta mata wanka kawai don Allah. Murmushi tayi tana faɗin.”Sa’ade zaki makara dai” hakan ta kuma dibo ruwa ta mata wanka tass. Sannan ta fito da ita shirya ta tayi, ta dauko mayafinta tana faɗin. “Larai bari na kai Sa’a makarantar.” “Tow Yaya sai kin dawo” bata ga malam a cikin gidan ba, alamar yana kofar gida, koda ta fita ta same shi tare da mazan makotar su.

Haka ta wuce su, bata mishi magana ba. “Aminu idan Sa’ade ta kara girma ka aurar da ita mana tunda kaga ita Uwarta bata san harkan arziki ba.” Kallon mutumin yayi kafin ya ce. “Ilya babu me auren Sa’adatu, duk da ni kaina nasan duk cikin Yarana babu me kyanta kuma ba za a kuma samu ba, sai dai ina jin takaicin haihuwar ta da aka yi a gidana babban kuskure na, shine gaya mata Yarinyar zata tafi kurmi niman kudi gashi abin haushi daya yadda Uwar lamaran ta kwadaita min arzikin da suke samu. ” Shiru suka yi kafin Malam Musa ya ce mishi. “Kuma kaga kuma Laminde bata kyauta ba, ai bai dace ta kai ka gidan me gari ba domin dai nasan idan kuka samu arzikin nan tare zaku ci shi,ba kai daya ba waye ya sani ko har da Hajji zaku tafi.” Kwafa. Malam Aminu yayi yana faɗin”Yo shima me garin ai bakin munafiki ne, ina cewa kin min magana yayi sai ganin dogarai kawai bisa kaina, wai daga gidan Hakimin Binji” kwafa ya kuma yana kallon hanyar da suka bi, yana tuna irin cin zarafin da aka mishi, anan yaji wani yana cewa za a kara musu malaman makaranta. “Tass mai gari ya ci zarafina, da goyan bayan hakimi, duk amanar da yake tsakanin mu na tsawon shekaru wai don Laminde ta kai ƙarata akan nakasassshiyar yarta ya zauna ya tsefe ni kamar ya samu kitso har da cewa bani da imani. Waye zai yarda a haifa mishi nakasashe kuma abin takaici nifa ban hanata kome ba, Bara kawai zata tayi mu samu kayan alatu amma uwar ta hana mu na dai san da ace ta tafi meye ba zamu samu ba? ?” “kai Malam Aminu ka ji tsoron Allah bayan haihuwar ta tasamu ciwon ba haifarta kuka yi da shi ba.” “Eh meye maraban dambe da fada? Gaya min meye bambancin? An haife ta da shi ko ta samu ai duk daya ne, babu abin da ya min ciwo kamar kashe kudina da nayi na bin hawa, sannan itama Laminde aka saka ni na biya mata, Allah ya isa min” ya fada kamar zai yi kuka.

…. Inna Laminde har kofar aji ta raka Sa’ade. Sannan ta leka ajin, “Malam ayi hakuri ta makara ” “Ba kome innah ” “mun gode sosai” sannan ta nuna mata cikin ajin, rike yar jakar buhun simintin ta tayi me littafi kwaya uku. Zama tayi Innar ta leke ta, tare da d’aga mata hannu. Bata fuska tayi kamar zata yi kuka. Domin rashin yarda irin na Sa’ade. Murmushi Inna tayi ta bar makarantar.

A hankali taji hawaye ya zubo mata, tausayin rayuwar Sa’a take, tayi kankanta da fuskarta al’amari me girma haka. Sai dai kamar yadda Uwani matar me gari ta gaya mata dole ita zata tsayawa Sa’a..

Asalin su yan garin Maikulki ne, ko nace mazauna garin. Fulani ne da suka fito daga yankin sahara, domin yanayin su ya fi kamancecceniya da bororoji. Sai dai su fararren ne, ba bakaken fulani ba. Duk da suna yawo ne da dabobbi kafin su zauna a garin Maikulki na karamar hukumar Binji, Garin…

SANIN GAIBU…!!

_Sai Allah_

ͲϴᏢ-ΝϴͲᏟᎻ 2023

*Mai_Dambu*

Dedicated to Handicapped

 

“`Ina mata yan kamshi matan yan yayi TOH ga turaren mu nan.

Ga turaren orientica kuzo kusiya arha kwasha kwasha 1700“`

Page:02

Gari ne mai cike da albarka, lokacin da suka zo garin tana amarya kusan shekaru arba’in kenan. Tana da yara shida da Malam Aminu, uku maza maza uku mata. Haka abokiyar zaman ta, Larai tana da yara biyar. Ƴaran Inna Laminde sune manya akwai Zakari ya’u, suna kiran shi Ya’u sai Yusuf suna kiran shi Dabo,sai Ibrahim suna kiran shi Iro, sai Alaweeyah suna kiran Addah Weeyah sai Shamsiyah tana kiran Maman Sailuba, sai Auta wacce haihuwar yazo mata a bazata domin a tunanin su tun kan Shamsiyah don sai da ta girma sosai domin takai shekaru goma aka haifi Auta Sa’ade. Ya’u yana zaune a Sokoto shi da iyalin shi, domin da taimakon Allah da samun jajjurtaciyar Uwa Ya’u ya samu ilimin boko, na Addini kan dama suna yi. Na bokon ne Malam Aminu yaki cire kwandalar shi su amfana da shi. Fadin irin wahalar da Inna Laminde ta sha akan Yaran ta sai Allah, domin har surfe sai da tayi ita burinta Yaranta su samu ilimin. Alhamdulillahi Ubangiji ya dafa mata domin bayan Ya’u ya samu diploma akan aikin jarida, wata gidan Radio a sokoto ta dauke shi aiki, dama Yusuf yana na shi karatun domin shi jami’an danfodiyo ya samu, inda yake bangaren kimiyya kere-kere. Iro kuwa kasuwanci ya faɗa, domin yaki bokon tunda ya gama secondary ya ajiye boko, sai Allah ya saka mishi albarka shi kan yana garin Binji a can yake kasuwancin shi. Wani ikon Allah yaran duk sun san wahalar da Uwar su ta sha, haka yasa basu da wacce suka sani sai ita. Ɗakinta kuwa da ita kanta da suturan da take sakawa wallahi zaka dauka wata hamshakiya ce, nan kuwa ba kowa bace. Duk karshen wata suna hanyar me kulki dukkan su kuwa. Haka yana mugun yiwa Malam Aminu ciwo duk da ya hana su, moran shi amma Yaran basu mishi kugunta ba. A kome sukawa Mahaifiyar su zasu mishi, shima albarkacinta yake ci. Ba karamin al’amari ba ne domin lokacin da suka ce su boko zasu yi ba zasu yi kiwo ba, cewa yayi sai dai tana fita mishi da kiwo. Haka ta amince dake tana da wata kawa matar mai gari ita ta bata Shawaran ta saka Yaranta a makarantar boko, babu amfanin barin su suna yawo a daji da sunan kiwo. Ita kuwa ta amince. Shine fa aka fara samun matsala da Malam Aminu. Har aka haifi Sa’ade yarinyar ta taso cikin kulawa da soyayyar yan uwanta. Musamman Addah Weeyah da ta kusan aure. Domin itama tayi karatu har zuwa aji uku na secondary su, kafin Uban ya daka tsalle ya ce bai iya ji ba, duk da kiri-kiri yake fifita yaran Larai akan Yaran Inna Laminde. Yaran Larai sun, Yakubu, sai Jamilu, Ikilima tana aure, sai Harirah da Rabi. Ikilima tana aure a Binji gidan Sarkin Fulani. Domin Larai Mahaifiyar ta yar gidan ce, Malam Aminu kyakyawan gaske ne, idan ka gan shi ba zaka tab’a yarda shi ya tara Yara har goma sha daya haka ba. Haka itama Innna Laminde tana da kyau na asalin Fulanin Somalia. Laluran Sa’ade ya faru ne sakamakon cutar bakon dauro da aka yi, wanda kowa yasan yadda ciwon yake,. Shi ya tab’a mata wuyarta da kunnen ta daya. Bata ji da kunne daya sannan bata magana. Domin tana da shekaru biyar ciwon ya same ta, da farko har an fasa kukan ta mutu, sai da aka zo mata wanka sai a ka ga tana da sauran numfashi. Haka ta sha jinya kafin Allah ya bata lafiya. Sai dai fa bata hmm-bata humm- haka laluran ya same ta. Yayunta har asibitin Udut suka kawo ta, amma ba baki ba ido a lokacin karfi imani ne kawai yasa Inna Laminde bata mata fatan ta mutu kowa ya huta ba. Gashi a lokacin bata isa ta fita wasa ba, idan yara suka mata magana suka ga bata amsa ba, sai su watse su barta. Idan tana jin wuyan haka zata zauna tayi ta kallon uwar hawaye na zuba mata, sai taga kwano zata dauka tana budewa. Akwai lokacin da Inna Laminde ta tafi zaman bikin Ikilima da ta haihu, Yarinyar nan ta sha wahala domin ba kowa ke gane abin da take so ba, dama idan Innarta tana nan kwanciya take a jikinta ta hakan take fahimtar bata da lafiya. Sai kuma idan tana jin yunwa zata yi ta buɗe kwanika tana kuka. Tow tunda uwar ta tafi dake tana da kulafuci, don ta Uwar ce tare zasu tafi malam ya hana wai zata ja mishi magana a ce gidan shi a kwai kurma. Haka ta tafi tabarta cikin jinya domin bata da lafiya sosai, ita kuwa Inna Larai bata sani ba, sai da ta kwana bata ga tazo taci abinci ba, shi ne da safe ta leka dakin nan ta ganta a gadon bunun Innarta, yadda ta d’aga labulen dakin ta bude idanunta da suka yi jajjur, tana kallon ta kafin hawaye ya zubo mata. “Ni Maimunari yarinyar nan Allah yasa ba wani abu ke damunki ba” ta shiga ta tab’a kanta, jin yadda ya dauki zafi yasa ta fitowa ya cewa Malam da yake zaune a tsakar gida. “Malam taimaka ka bani cafeno yarinyar nan bata da lafiya, jikinta yayi zafi sosai.” “Ke Larai bana son munafunci, ta mutu mana ko an gaya miki ina mara ba ita ne gara ta mutu kowa ya huta.” Shiga ɗakinta tayi ta bankade zanin gadonta ta dauki kudi, ta fita yana mata magana amma ta bawa banza ajiyar shi yaji haushi kuwa, haka ya shiga dakin da tsumagiya ya shiga zane Sa’ade. Ga ciwo ga duka, Allah ya gani ya tseneta kamar ya kashe ta, yana cikin dukarta Inna Larai ta shigo gidan. Dakin ta nufa da ta ga takalmin shi. Ganin yadda yake dukar ta yasa fasa ihu, don ta suma. Fada sosai suka yi da Malam ta maida Sa’ade ɗakinta domin Rabi da Harirah sun bi Inna Laminde sunan Ikilima. Fadar irin kiyayyar da Malam yake nunawa Sa’ade sai ya baka mamaki. Haka ta taso da mugun tsoron shi, tana ganin yadda yake dariya da farincikin da yan uwanta amma ban da ita.

Lokacin da ta cika shekaru tara Ya’u da Yusuf sun tsayar da shawarar su tafi da ita wurin su, amma bawan Allah nan fir yaki kuma ya hana a sakata a makarantar. Haka suka hakura itama bata son nisa da Innarta. Ana haka wata mata da take zuwa sayan madara a gidan ta jima bata zo ba. Dama bata da aiki sai daukar yara tana kaisu birni aikatu, masu laluran kuma tana kai su irin su Abuja da Lagos bara. Haka yasa ta wannan zuwan da zata koma an bata sakon madara zata saya shi ne ta ga Sa’ade, shi ne ta tuna akwai wani me kudi a can Lagos da ya ce ta nima mishi kurma mace ko namiji zai dauki nauyin a mishi jinya. Ganin Sa’ade yasa abin da take hangowa zata samu ya kara rikita mata lissafi, tasan Malam Aminta da mugun son abin duniya, don haka tana gama amsar madaran ta dauki kuɗi me yawa ta bashi kudin madaran sannan ta bawa Sa’ade kudi me yawa tana faɗin. “Malam Aminu ga arzikn a cikin gidan ka, amma ka kasa amfana da shi, gaskiya ya kamata ka san darajar haka.” Ta fada tana kallon Sa’ade. “Kina nufi wannan abin Arziki ne? Hhhhh” ya fashe da dariya, yana nuna Sa’ade da take zare idanu. Domin tasan duk lokacin da Baffan su ya nuna ta yana magana tow ba abin dadi yake fada akan ta ba. Mikewa tayi daga bawa dan ragon ta madara a fidinbotul,ta koma dakin Innar su. Da take kallon kofar dakin. Kallon juna suka yi ta koma bayan Inna Laminde ta kifa kanta tana sauke ajiyar zuciya, hawaye ne masu zafi suka zubo mata, tana matukar tausayin yarinyar da bata ji ba bata gani ba. Malam Aminu suka fita da Tabawa, anan ta tsara shi da kudin da zai samu, akan Sa’ade, ta mishi alkawarin wani sati zata zo in sha Allah. Bai fadawa Inna Laminde ba, kawai yayi gaban kan shi. Sati na zagayowa kuwa sai gata da uban kudi dama tun ana gobe zata zo, ya ke cewa Inna Laminde ta shirya Sa’ade gobe tabawa zata zo ta tafi da ita. Aikuwa tace bata san zancen ba, duk abin da za ayi sai ayi. Yarinya shekara tara ya hana a saka a makaranta sannan ya ce za a kaita wani wuri. Haka suka kwana suna rigima, washi gari sai ga Tabawa ta zo, ganin da gaske rabata zasu yi da Yarta. Don haka bata yi kasa a gwiwa ba, ta dauki yarinyar suka nufi gidan Mai gari, tun safe ake babu ɗaya shi kuwa ya kafe sai an tafi da Sa’ade, Mai gari ganin al’amarin yafi karfin shi yasa su a gaba har zuwa gidan Hakimi. Anan aka yi ta ta kare, har yake barazanar sake ta, dake suna shiga garin Binji ta samu wani Yaro a gidan Hakimi ta tura shi ya kira mata Ibrahim, can sai gashi a gaban shi aka yi Shari’ar inda Hakimi yasa a bincika mishi Makarantar Maikulki ko akwai malamai, nan me gari ya gaya mishi babu wasu malamai ba sai an kai da bincike ba, a duba kodan rayuwar Sa’ade. “Zan yi magana da shugaban karamar hukumar Binji zai yi magana Baturen ilimi in sha Allah za a kawo ma’aikata da yarda Allah, ita kuma Sa’adatu Mai gari idanun ka ya tsaya akan ta, sannan duk abin da yake tafiya zan na tuntubar ka.” “In sha Allah zan saka Idanu ” “kai kuma wallahi naji labarin wani abu ya kuma faruwa sai na tura sakon zuwa shugaban ƙaramar ƙungiyar kare hakkin dan Adam sun daure ka. Kuma itama Tabawa a gaya mata ta bar kasar Binji kafin na same ta.” Da wannan aka kashe zancen, Allah da ikon shi ya hadata da matan me gari, tayi ta bata shawara. Yadda zata kula da Sa’ade. Koda suka dawo gidan ma tashin hankali da masifa, dama shi Ibrahim tun a can ya bawa Babar su hakuri domin yasan halin Baban su, ba zai iya rigima ba. Haka ya tasata a gaba da bakar magana kamar zai doke ta. Laminde ke nan, a yayinda takwarorinta suke kurmi da kudu niman abin Arziki shi ne zaki tozarta ni ta hanyar kai kara na, gidan Anamimin can wato ki jindadin ayi min dariya tow na gode tunda a iya gidan hakimin Binji kika tsaya na zata zaki wuce har lahira ne da ni. Karewar Gidan hakimi, tow wallahi na rantse da Allah babu hannuna a kan Yarki ku nima mata wani Uban ba ni ba.” Haka gefe guda Abokan shi zuga shi suke akan Laminde tafi ƙarfin shi ashe kuri yake da karyan yafi karfin gidan shi. Ita kan Inna Larai babu ruwanta domin har ita bai kyale ba, shi yasa bat shiga cikin hayaniyar su.

— a dawo labari.

Federal Ministry of education

Sokoto State

Kamar yadda Hakimi ya tura sakon shi, haka Shugaban karamar hukumar Binji ya tura zuwa ga Commissioner ilimi. Dr Sharif Hamidu. Kasancewar yau satin shi biyu da dawowa daga Umra. Ya kuma yi daidai da kwanakin da ya ɗauka na Hutu. “Yallabai akwai takardun da aka turo da kuma na aiki, daya daga karamar hukumar Binji. Kwantomar Binji da kan shi ya kawo yana bukatar a baka sakon” kallon sakataren shi yayi kafin ya ce. “Ok na ga ni” mika mishi takardan yayi, ya duba kafin ya zuba mishi idanu. “Suna bukatar malaman makaranta ne.” “Tow ko za a tura wurin me girma Gwamna ne” girgiza kai yayi sannan ya ce. “A tura musu yan bautar kasan da za su yi service makarantun mu, sannan zan tuntubi me girma Gwamna da maganar.” “In sha Allah za ayi haka.” “Allah ya sa” ya furta,

Fita sakataren yayi shi kuma ya fara aikin shi da ya bari. Yana nazarin maganar da shugaban karamar hukumar ya turo mishi. Akwai yara masu yawan gaske da suke buƙatar kulawar Malami da gwamnati, a halin da ake ciki har an fara diban yaran nan zuwa birane domin niman kudi wasu Bara, da sauran su. Babban abin damuwar yarinyar da ake son a fita da ita bata ji bata magana kuma a haka za a fita da ita birni ba a san inda za a tsaya da ita ba. Cire glass din shi yayi yana mamakin wannan al’amarin. Me ya dace su? Dole a tura musu malaman, wayar shi ya janyo ya gwada kiran me girma Gwamna…

ASHRAF, SANIN GAIBU,TSINTUWA is not free, Pay N400 ONE, TWO N800, THREE 1K to 0008219237, Jaiz bank Azizat Hamza

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment