Littafan Hausa Novels

Sandace Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Sandace Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

*SANDACE*

 

Paid book

 

 

Story and writing by *Dr zarah Lg*

 

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*

*(Sarki da Sarauniya Writers)*

 

 

” *We Rule the World of Writing* ”

 

 

 

 

 

🅿️1

 

 

Wata matashiyar matace zaune tayi tagumi ,saiga wani mutum yashigo batama saniba saboda tayi Nisa atunanin datakeyi ,ya iso inda take yace haba sadiya waiyaushe zakibar damuwa Akan wannan abun?kisanifa komai Allah bebekaba bamantawa dakai bane ,yanasane dakai lokacin badawarne baiyiba kiyi haku’ri kicigaba da addu’a kawai ,sai asannan tacire tagumin tadubeshi tace to malam badamuwa Allah yatabbatar Mana da alkhairinshi ,Amin,yauwa kokefa amaryar malam dagake baka’ri,to aka’rota Mana aibanjin komai kowa ya iya allonshi shizai wankeshi ,tonidai naji dandai Kinsan bazanyibane ku Mata dakeda kishi kamarme ,yanzu yunwa nakeji zokibani abincina naci,tatashi tadau’komai kular tuwo da Miya tazubamai yaci yako’shi suka zauna suna firar Mata da miji ,saisukaji sallama,dukansu suka ansa tare dacewa Abdul harka dawo ?nadawo umma nagaji sosai yarda bakitunani ga yau nade’bo yunwa to ainagama abincin zokaci ?to umma barinaje nacire kayana sainazo naci ,”

 

 

Gidan Aunty Hausa Novel Complete

 

 

 

 

Yau garin antashi da sanyi sanyi saboda haka basutashi dawuriba gashi yau asabar malam Umar bazaije wurin aikiba ,saboda hakane yazauna gida suna ta fira da matarshi da dan’shi,suna cikin fira sai Abdul yakecewa?umma inaso kiyimin yar’ kan’wa wadda zamudunga tafiya school”tare muci abinci tare ,inaganin yan’ makarantarmu da kan’nensu wasu sukezuwa Kuma ummana Allah yabaki di’ya mace,Amin ,”kaita addu’a kajiko yarona inhaifo maka yar’kan’wa kyaukyawa ,”malam yayi dariya yace ?yarinyarnan zataga gata nasan ,badolebama malam Tasha gata,”

 

 

 

 

 

Wani mutum ne dakakalleshi zakasan matafiyine ,yanami wurin kwana baisamu ba ko Ina yaje basa bashi ,kowa natan tama ankanshi balle yanzu yarda mutane batsoron Allah ,Kuma yayi wata irin shigama ga gashi buzu buzu akanshi ,yanaso yasamu wurin kwana dasafe yawuce ,ya iso kofar wani gida yazauna y aje jakarshi agefenshi yadau’ko abin ruwanshi yasha,malam Umar yazo zaitafi sallar magarib yaganshi ako’far gidanshi yabashi hannu sukagaisa yawuce masallaci ,yadawo zaishiga gida yasake ganinshi yawuce abinshi,ya iske sadiya zaune Akan kujera yace Kinsan wani abu?wani mutum nagani da alama matafiyine Anan ko’far gidan naganshi yanzukuma naka’ra dawowa nasameshi yabani tausayi gaskiya daga gani yagaji sosai daga ganinshi makwanci yakenema ,kamar na tambayeshi?saikuma nashigo gida nace bari nazo nafaada’maki ,hakane malam tokasan mutane yanzu abin tsorone dukda baduka akataru akazama da’yaba daga taimako kana iya ganin abin yacanza,a uzibillahi ,karkiyi wannan furucin Mana indai kaikataimaki mutum dazuciya da’ya ,to inshi bahakabane Allah zaisakamaka karkidamu kinjiko matata,mu da Allah muka dogara danhaka inshallah babu abinda zaisamemu face Allah yakawomanashi dasauki ‘,to malam badamuwa kaje sallar Isha ,inyananan saikashigo dashi,”

 

Malam Umar yafita sallah yaka’ra ganinshi baimashi magana ba saida yadawo ,yace bawan Allah lafiya?naganka tunda’zu zaune Anan cikin shaka’kka’r muryarshi ta tsofaffi yace lafiyalau malam inaneman wurin kwanane inatafiyane dare yayi gashi inada Nisa da inda zani ,shine nanemi wurin kwana bansamuba saina zauna Nan nakwanta,malam Umar saida yaji maganarshi yakalleshi tsaf yaga Ashe tsohone Amma haryadan’ bashi tsoro yanayin fuskarshi ,saiyadanne yace ,Allah sarki ba’a’yihakaba bawan Allah Nan gidanane kazo mushiga kakwana,in Allah yakaimu goben,saikawuce gobe dasafe,kamar yanajira yace nagode sosai bawan Allah ,Allah yasa taimakona dakai yazamanma alkhairi,Amin,nagode ,barinashiga nasanarma matata zanshigo da bako’ ?to badamuwa,”malam yashiga yacema sadiya tagyara da’yan da’kin bako’ zai kwana aciki?takau gyarashi tas tace yashigo dashi,yafita yace yashigo ,sukashigo ciki da sallama,sukawuce da’kin yacemai ga katifa yaje yazauna yanata yan’ rabe’_rabe’ kamar wani Mara gaskiya yazauna ,saiga sadiya tayi sallama tagaisheshi yada’go yakalleta gabanta yafadi’ sauran kadan’ tazubar da abincin ta ajemashi tafita Tana ajiyar zuciya,shikanshi yalura dahakan yamaza yace nagode malam kaida matarka da wannan karamcin ,Nan yazuba abincin yafara saka Loma ka’tuwa yanaci ,baifi minti biyarba yacinye , har malam namamakin wace irin yunwa yade’bo?nandai malam yayimashi sallama saida safe yatafi ya isketa kwance kamar mejin tsoro ,Amma bakinta yakasa fada’ma malam abinda tagani aka’far mutumin,”malam yakwanta shima,saida safe tatashi tahada’ kayan Karin kumallo takaima bakon’nan yaci yanagamawa yayi shirin tafiya yacema malam yakiramashi matarshi suyi bankwana ,Kuma yayimata godiya,suna zuwa dukansu sukatsaya agabanshi,yace tabbas kumutanen kirkine Kuma nasan kowane Hali kukeciki,sukahada’ ido da mamaki,kunason haihuwa Amma bakutaba’yibako?sukace hakane , yabude’ jakarshi irin tabuzaye yadau’ko wata ,SANDA ,yamika’masu da tsoro suka kasa amsa ,wannan sandar kukarbe’ta zata sharemaku hawaye inshallah karkudamu,,tamicece,?bakunason haihuwaba?suka amsa da sosaima ,tonizantaimaka maku da itane ,Akan kyautatawar dakukayimana bakuji kyamata ba ,nasan Baku da damuwa datawuce rashin haihuwa ,kubarta Anan saman gadon takai wata Tara ,kukulle da’kin kar abude’ harsai lokacin yayi,malam haryace baikamata mukarba’ba itakau tarude’ abinka ga mace mukarba’ gaskiya ,tajidadi’ganinta take kamarma tahaihu,malam munsa anmamu addu’a ,sosai ,gashi yanzu Abu hargida mungode tanata jindadi’,kawai saimutum yaba’ce taji tsoro tasume,”malam yadau’keta yakaita saman gado takwanta yawatsamata ruwa tafarfado’ Tana malam wayyo cikina namin ciwo , yarude’ yabata magani Tasha tajisauki’,”

 

 

Kawai ranarda wata Taran yaciga taganta daciki ka’to kamar zata haifeshi dakyar take tafiya,malam dasafe yaga abin mamaki shima ,sudukansu kowa namamaki ,Amma Basu damuba saboda tuna maganar mutuminnan ,Aiko tace malam kakaini da’kincan,a bude’shi dakyar tatashi sukatafi sudukansu ,kowa natsoron shiga ,saikawai tafara shiga abinda tahangone yasa tasuma jaririya daidai inda aka aje sandar Nan babu sandar sai jaririya nakuka. …….

 

 

 

 

. tirka’shi abin al’ajabi ne ciki da wannan littafin ,to masu karatu labarin SANDACE yanzuma yafara .

 

Inaka’ra mika’ tarin godiya ga Abdul king article.

 

 

Watsap number 09078772252/09167352441

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment