Littafan Hausa Novels

Sanadiyar ta Hausa Novel Complete

Soyayya Da Karamar Yarinya
Written by Hausa_Novels

Sanadiyar ta Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

SANADIYYAR TA

 

Zainab (Indian Girl)

 

Mikiya Writer’s Association

 

_Bis-millahir-rahmanir-raheem_

*NOTE*

 

Dan Allah dan Annabi Muhammad s.a.w duk wanda ya iya gyara whatsapp idan ya samu matsala kowacce iri ce dan Allah yai min magana privet ya gyara min amma dan Allah a taimaka

Page 1&2

 

Tsaye take a ɗakin tana ɗaɗɗaga hiniform ɗin makarantarta da suka kasance ash da baƙi duk sun koɗe sun yayyage, kwallace ta zubo daga idanunta ya yin da a zuciyarta take cewa “yanzu saboda Allah a haka zan din ga tafiya makaranta da wannan yagaggun hiniform ɗin sai kace wata mara hankali” kuka ne ya suɓce mata.

Cuta Ta Dau Cuta Hausa Novel Complete

Kiran da Ummanta ta kwalla mata yasa ta aje hiniform ɗin ta fito zuwa tsakar gida tana ta goge hawaye, Umma dake ƙoƙarin raba kunun data dama ta ɗaga kai ta kalle ta kafin Ta ce”A’a Kubra lafiya me kuma ya same ki kike kuka?” “Yanzu Umma saboda Allah kamar ni ace na din ga zuwa makaranta da yagaggun kaya sai kace wata mara hankali ko mara gata” Kubra ta faɗa tana fashewa da wani kukan.

 

Umma ta saki baki tana kallon Kubra kafin Ta ce”Tofa! Yanzu Kubra dama ke me gatace? Ai na zata gatanki Allah ne tun da kin san ba mu da halin hakan” Kubra ta goge hawayan fuskarta kafin Ta ce”Eh na san ban da gata; amma wallahi ba zai yiwu na cigaba da zuwa makaranta da wanna yagaggun kayan ba idan za’a canza min a canza idan kuma na zauna ba ilmin shikenan” Tana gama faɗar haka ta koma ɗakin.

 

Mamaki Umma ta shiga amma ko da yake ba abin mamaki bane tun da ai ta san halin Kubra sa rai na kai kanta in da Allah bai kaita ba. Haka ba yadda ta iya ta saka hiniform ɗin domin ta na son zuwa makarantar ba zata iya fushi taƙi zuwa ba, haka ta fito ta sunkuya ta ɗauko kofin da aka zu ba kununta a ciki ta kafa kai tana sha; sai da tasha sosai sannan ta ajiye kofin tana yatsina fuska tana Ce wa”Kunun ma babu sugar idan naje makaranta na san Rahma ta zo mana da lafiyayyan break fast sai na ci amma wannan kunu haka sai kace kayi amai” Umma dai tana ɗaki tana jinta bata tanka mata ba har ta fice.

 

Misalin ƙarfe 8:00am kowane aji babu abinda kake ji sai muryar malami yana karatu, haka ajin su Kubra ma wanda ya kasance aji 6; kowa yayi shiru ana sauraran malamin dake gaban allo yana rubutu. Kubra ta dubi ƙawayanta Rahma da Waleeda kafin Ta ce”Rahma,Waleeda!” Duk suka amsa suna kallonta don jin me zata ce musu. Kubra Ta ce”Ku saurara da kyau kuji abinda zan faɗa muku kuma wallahi idan kuka ɓata min bajet wallahi! wallahi!! wallahi!!! kun dai san halina ai” Rahma Ta ce”Ke ma kin san ai ba za mu baki kunya ba” Waleeda Ta ce”Duk yadda kika ce haka za ai” Kubra tai murmushi kafin Ta ce”Yawwa to ku saurara ku ji abinda zan faɗa muku” A hankali ta faɗa masu abinda za su aikata yau a makarantar wanda sai ya tashi hankalin kowa, shewa suka saka jin abinda Kubra ta faɗa musu. Da sauri ɗaliban ajin dashi kansa malamin suka juyo dan ganin masu yin dariyar amma sai suka maze tamkar ba su bane suka yi dariyar wanda aka rasa wanda yai amma su ƴan ajin sun sani amma tsoran halin Kubra yasa su ku shiru. Cikin ɓacin rai malamin yake tambayar ƴan ajin su wane suke masa dariya a aji yana karatu amma babu wanda ta tanka shi, ganin sun ƙi bashi amsa yasa ransa a ɓace Ya ce”Ok, ba za ku fito da su ba to wallahi yau kowacce sai taci ubanta” bai ƙara cewa komai ba ya juya ya fice daga ajin rai ɓace. Ai yana fita aji ya hargitse da hayaniya ana Ce wa”Wallahi ku su Waleeda kawai ku fito karku ja mana tun da dai kune ku kai dariyar nan” wata tsawa Kubra ta dakawa ƴan ajin wanda yasa duk su kai shiru domin suna bala’in jin tsoranta gata ita ba ƙatuwa ba amma sai sharri dan ita ba ƙaramin aikinta bane yanzu tajawa mutum a kore shi dag makatantar. Cikin bala’i Ta ce”Wallahi duk ƴar iskar data sake ta faɗawa malamin nan cewar mune mu kai dariyar nan wallahi sai ta gwammacewa wahalar da zata sha a wajansa fiye da abinda ni zan mata” Jin abinda Kubra ta faɗa yasa kowacce taja bakinta tai shiru.

 

A fuce malamin ya dawo ajin da bulala a hannunsa murtukekiya fuskarsa a ɗaure tam yaja ya tsaya gaban allo kafin Ya ce”Dan ubanku tun da ba zaku faɗa ba yanzu jikinku zai gaya muku” Take kowacce idanunta ya sake raina fata gashi ana tsoran a faɗi su waye ana tsoran abinda zai biyo baya. Malamin ya nuna site ɗin farko yace su fara fitowa, haka ba yadda suka iya suka fito. Sai da ya zane kowa na ajin amma ban da su Kubra dan tace wallahi babu mai dukan su, ai tana ganin saura su uku ta daddage ta kwalla wata uwar ƙara kafin ta zube ƙasa babu alamar numfashi a tare da ita. Ai su Waleeda suna ganin haka sun san da cewa shirin Kubra zai fara aiki ne dan haka a fakaice su kai dariya. Ƙarar da Kubra ta kwallace ta janyo hankulan jama’ar dake makaranta aka rankayo zuwa cikin ajin. Shi kuwa Malamin mamaki ne ya kama shi ganin ko taɓa ta shi bai ma yi ba amma gashi kamar ma ta mutu, a hankali ya taka zuwa in da take a kwance su kuma su Rahma suna kuka suna mata fifita da gefan hijabin su. A hankali ya sunkuya dan ya duba yaga ko da numfashi a jikinta amma me abinda ya faru ne yasa duk ɗalibai saurin kaucewa daga wajan ciki kuwa har da su Rahma cike da firgici, ai malamin yana sunkuyowa ta danƙi wuyansa tana zazzare ido tana wasu muzurai. Ƙoƙarin kwatar kansa ya shiga yi amma ya kasa domin ba ƙaramin riƙo tai masa ba, da sauri wata ɗaliba tai office ɗin malamai ta kira su suna zuwa suka shiga ƙoƙarin kwatar malamin wanda da kyar suka kwace shi. Buge-buge da duka Kubra ta shiga yi tana wasu maganganu irin na wanda yake iska ganin haka yasa jikin kowa yai sanyi su kuwa su Rahma kuka suke sosai sai kace gaske nan kuwa idan suka haɗa ido da Kubra dariya suke. Karatun alqur’anin da aka kunna a waya ne yasa ta dena buge-bugen ta kom ta kwant lakwas, a hankali wani malami yai ƙarfin halin ƙarasawa in da take yana addu’a ya durƙusa gabanta kafin Ya ce”Bayin Allah kuyi haƙuri kun san fa cewa Allah ne ya halicce mu kuma ya halicce ku amma kuke son cutar da wannan ƙaramar yarinyar?” Cikin wata kalar murya Kubra ta fara magana “Dakata! Nace dakata bil’adama, mu ba masu cutarwa bane an taɓa mana jaririyar mu ana ƙoƙarin cutar da ita” Malamin ya sake Ce wa”Kenan ku mutanan jikinta ne?” Tsawa ta daka masa kafin Ta ce”Dalla rufe min baki kana tantama ne?” “A’a wallahi! Wallahi ban tan tama” “To kui mana abinda muke so mu tafi mu barta ta huta” aka faɗa cikin tsawa. Malamin Ya ce”Muna jinku me kuke so ai muku” “Kuɗi, kuɗi muke so a ba mu domin gyara ɓarnan da akai mata” Malaman suka kalli juna kafin malamin Ya ce”To nawa kuke buƙata?” “Dubu 10 muke da buƙata” Rahma da Waleeda suka kalli juna suka ƙunshe dariya. Su kuwa malamai mamaki suka shiga yi jin aljanu masu son kuɗi, “Ba damar yin tunani na baku ba umarni nake so a cika yanzun nan ko yanzu kowannan ku ya fita babu ido” kallon-kallo malamai da ɗaliban dake cikin ajin suka shiga yi kowanne cikinsa ya ɗuri ruwa, kafin kace me tuni aka shiga haɗa kuɗi a cikin malamai har aka haɗa dubu goban. Tambayar in da za su ajiye kuɗin su kai cikin tsawa tace a je wajan bishiyar kuka dake kusa da ajin a ajiye, haka kuwa akai ana kai kuɗin ba a ɗaɗe ba Kubra ta dawo hayyacinta amma tayi wujiga-wujiga da ita. Da ido taiwa Waleeda alama da taje ta ɗauko kuɗin idan ta ɗauka kuma karta dawo ajin, haka komai ya tafi yadda ta tsara. Bayan an tashi daga makaranta ta ba su naira dubu ɗaya tace su raba ita kuma zata siyo hiniform da sauran kayan karatu da bata da su, haka kowa ya koma gida.

 

Washe gari ya kama weekend ne babu makaranta dan haka bayan Kubra ta gama karyawa dake dama bata komai na aikin gida, rana tana ɗan dagawa ta shirya domin zuwa kasuwa ta yankowa kayan makaranta. Bayan ta gama shiryawa ta fito tace da Umma sai ta dawo, Umma ta tambayeta ina zuwa?. Kubra Ta ce”Haba Umma sai kace ɓata zanyi ko kuma baki yarda dani bane?” Umma ta girgiza kai Ta ce”Ba wai ban yar da dake bane Kubra amma ai naga ni ban aike ki ba sannan naga babu makaranta” Kubra ta sauke ajiyar zuciya sannan Ta ce”To Umman su Waleeda ce zata aiketa shine tace na zo na rakata” Umma Ta ce”To a dawo lafiya Allah ya tsare” Kubra ta fice ba tare data amsa ba. Bayan ta dawo daga kasuwar bata ƙaraso gida ba sai da ta biya ta kai ɗinki sannan ta nufo gida, tafi take abinta hankalinta kwance burinta ya cika zata sake hinform. Wata ƙatuwar baƙar mota ce ta shigo layin a guje wanda hakan yai dai-dai da ƙarasowarta in da Kubra take aikwa ji kake facal motar ta fallatsata da ruwan ƙasa irin wanda yake taruwa a kan hanyar nan, zafafe Kubra ta bi motar wadda taja burki ta tsaya da kallo sannan ta ƙarewa kanta da yadda duk jikinta da kayanta suka ɓaci ji tai kamar ta saka kuka dan takaici. A hankali motar ta fara dawowa baya har ta dawo dai-dai in da Kubra take ta kasa cewa komai tsabar takaici. A hankali aka buɗe murfin motar kafin wata kyakykyawar ƙafa wadda ke sanye da safa cikin takalmi baki sau ciki kafin kuma ya zuro duka jikinsa ya fito, cikin rashin son magana Ya ce”Please dan Allah kiyi haƙuri ina sauri ne shine yasa ban ganki ba har na ɓa…” Wani lafiyayyan mari Kubra ta wanke kumatunsa duka biyun dashi wanda ita kanta da tai marin ta san yayi wuta da yawa, cikin bala’i ta fara magana “Dabbane kai? Ko kuwa baka da hankali? Mahaukacine kai ko kuwa wawane kai? To wallahi kaje Allah ya isa ban yafe ba ɗan iska ɗan tasha kawai” masifa take ko ta ina wanda ko tsayawa ta kalli fuskarsa ma ba tai ba, tana gama faɗan tai tafiyarta. Tsintar kansa yai da binta da kallo ya rasa dalilin da ya sa ya kasa ɗaukan mataki akanta da har ya iya tsayawa tai masa wannan cin mutuncin, ta san kuwa wane shi da zata kira shi ɗan iska ɗan tasha?. Kwafa yai ya koma mota ya zauna ya tayar ya bar wajan kalmomin na masa ciwo a rai.

 

Ita kuwa Kubra a fusace ta shiga gida babu ko sallama ta shiga gidan ba tare da ta kula kowa ba ta ɗebi ruwa ta shiga wanke jikinta tana cigaba da zagin mutumin, zage-zagen da take ne yasa Umma fitowa daga ɗaki ta tsaya tana kallonta kafin ta tambayeta. “Wani ɗan iska na haɗu dashi yai min haka ko dan yana taƙamar shi ɗan mash kuɗi ne to ni wallahi babu ruwa na da kuɗin su shiyasa na zage shi na ci masa mutunci” Kubra ta faɗa cikin takaici. Umma Ta ce”To Allah ta kyauta” Tai komawarta ɗaki domin itama kanta Kubran ba kyaleta tai ba. Haka Kubra ta gama wanke duk in da ruwan ya ɓata ta tana ta sababi sannan ta koma ɗaki domin cire kayan jikinta.

 

****

Ransa duk a jagule ya isa gida kai tsaye ɓangaransa ya nufa domin maganganun yarinyar nan sun taɓa masa zuciya ba ka ɗan ba, wai har shi zata duba ta cewa ɗan iska ɗan tasha; kalarsa ce ta nuna haka ko kuwa shigar jikinsa? Shi ba shigar ban za yai ba amma yau shi aka gayawa magana maganar ma daga ƙazama kucaka. A haka dai ya samu ya shiga wanka ya fito ya shirya cikin yadi mai matuƙar kyau da tsada sannan ya nufi part ɗin iyayansa domin yunwar da take ƙoƙarin hana shi kuzari, da sallama ya shiga falon farko har zuwa falon da zao sa da shi da ɗakin Mammynshi. Da sallama ya shiga falon Hajiya Aisha tana zaune akan ɗaya daga cikin kyawawan kuma tsadaddun kujerun dake cikin falon, tana sanye cikin shiga ta alfarma tayi matuƙar kyau; hannunta riƙe da waya da alamar wani take son ta kira. Sallamar da yai yasa ta ɗaga kai ta kalle shi da ƴar damuwa akan fuskarta, ƙarasowa in da take yai ya zauna kusa da ita kafin Ya ce”Mammy sannu da hutawa” “Ina ka shiga kasani a damuwa sannan wayarka busy?” Hajiya Aisha ta faɗa ba dariya. Ya ce”Sorry Mammyna wallahi naje ball ne kuma a hanyar dawowata na haɗu da…” nan ya kwashe duk abinda ya faru ya faɗawa Mammy. Hajiya Aisha macece mai tsauri sannan kuma bata ƙaunar talaka ko da da misƙalan zarati amma yau wai ace talaka ne yaiwa jininta wulaƙanci irin wannan ai ba ma zai yiwu ba dole a ɗau mataki, cikin zafi Ta ce”Amma My Son me ka tsayayi da har ta faɗa maka wannan baka ɗau mataki ba? An ya Afdal zuciyarka irin tawa ce kuwa?” Cikin kwantar da hankali Afdal Ya ce”Kiyi haƙuri Mammyna kinji ki kwantar da hankalinki” Hajiya Aisha Ta ce”In kwantar da hankali na fa kace? To idan kai baka kishin kanka ni ina yin kishinka dan haka dole na ɗau mataki” tana gama faɗar haka ta ɗauki wayarta ba tare da ta jira mai zai ce ba ta shige ciki da matsanancin ɓacin rai a fuskarta. Dafe kai Afdal yai ya san sarai halin Mammy babu abinda ba zata iya aikatawa ba akansa duk wanda yace zai wulaƙanta shi; gashi yanzu ta ɗau zafi wanda Allah ka ɗai ya san abinda zata aikata.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment