Littafan Hausa Novels

Sanadin Hijira Hausa Novel Complete

Tarihin annabi yusuf
Written by Hausa_Novels

Sanadin Hijira Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

SANADIN HIJIRA

 

By

 

UMMU FADEELA

 

 

 

TYPING

 

 

*CHAPTER 01.*

 

 

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

 

 

 

(ABUJA NIGERIA)

………..A gaggauce ta ke tura abincin bakinta tamkar zai gudu ya barta,duk ta ‘bata tsakar kitchen din da rice kai kace kaji ne suke dambe a wajen.Tsaye ta ke gaban tukunyar da bai juma ba aka sauke duba da yadda hadadden jollof d’in ke tururi, amma haka take jefa hannu ciki tana dumbusan abincin gami da cusawa a bakinta yayin da rabi ke shiga bakin saura ku ma yake bin jikinta kana ya gangara kasa ya watse.Duk yawan abincin haka ta caccakala shi ta watsar gami da ture tukunyar gefe,ledan biredi dake gefe ta janyo ta yageshi da karfin tsiya ta yanko wanda yafi karfin bakinta har ta nufi bakin dashi sai kuma ta tsaya tana kare mishi kallo kamar mai son karantar yadda aka sarrafa shi,goga shi ta farayi saman kanta da babu dankwali tana bubbugawa da karfi karfi sannan ta cire ta yayyanka shi into pieces da hannunta ta watsar a tsakar kitchen din.Da hanzari ta koma bakin sink ta kunna ruwa ta kafa kanta akai ta fara daddaka like her life depend on it,ruwa tasha fiye da kima sannan ta nufi hanyar fita kamar ba ita ta yi barnar ba.

Aameenat Bazawara Hausa Novel Complete

Kofar kitchen din ta bude a hankali,kanta da babu dankwali ta leka ta tsakanin kofa da jikin ginin,kamar wacce take fahimtar abun da ke faruwa take kare musu kallo.

 

Hamshakiyar macece wacce ta amsa sunan hajiya ta ko wanne bangare baƙace amma jikinta yana sheki da walwali irin na hutu da jin dadi da suka samu matsugunni a gareta,shigar jikinta ta alfarmace kai kace first lady ce a wajen taron mata HAJIYA FANTA,gefen hagunta wata matar ce itama da za’a kirata da hadaddiyar mace HAJIYA TITI, suna zaune bisa kujera mai zaman mutum uku suna tattaunawa kasa kasa….

 

Wulkita idanunta ta yi zuwa daya gefen na cikin kasaitaccen palon da ya amsa sunan palo,still akan kujera mai zaman mutum uku wata matashiya ce da akalla zata kai shekaru talatin a duniya,jibgegiya ce sosai irin masu jiki mai gaɓa gaɓa dinnan,tana sanye da vest wadda ya bayyana damatsenta tamkar yar wrestling kanta dauke da hula sai single zani da ta daura hannunta rike da waya tana aikin daddanawa,SAUDAT,kusa da ita wata ce da zata iya kaiwa sa’anta itama katuwa ce sosai kana bata cika tsawo ba,fuskarta farine sol amma pimples yayiwa hasken tarnaki dan ya cika fuskar taf babu masaka tsinke,wanda hakan ke tabbatar da hasken ba nata bane janyoshi ta yi ta hanyar dole duba da hannunta da kafafunta da suka kasance baƙaƙe,sanye take da doguwar riga mai yankakken hannu na shan iska kwance bisa kujerar tayi filo da cinyar Saudat itama tana ta faman danna waya kamar rayuwarsu ya dogara a kaine kacokam.BADARIYYA.

 

Takawa ta farayi zuwa cikin palon,bata da wani jiki salau salau take kamar ka hureta ta fadi,farace tas dan zaka fi dangantata da larabawa gashin kanta da babu dankwali ya sauko har kan gadon bayanta shi ba fari ba kuma ba baki ba,kacau kacau kacau haka sound na tafiyarta din ke fita wadda ya janyo hankalin mata hudu dake palon gaba daya suka dago suna binta da kallo.Chains ne daure a kafafunta irin wadda ake daure mahaukata dashi hakan yasa duk takun da tayi yake bada kara kacau kacau,duk ido suka zuba mata suna kallonta cike da mamaki dan babu wadda yayi zaton tana cikin madafar.A zabure Saudat dake zaune kan kujerar ta tashi tana zaro idanu kamar zata fire sama ta nufi matar da bata kara kallon gefen da suke ba, “Kan babban*******can,ke mahaukaciya yar macukule barnar me kika mana a kitchen?wa ya wuce dake ta nan duk bamu gani ba?me kika aikata mana na ce,”ta kuma fada a harzuke.

 

“Saudatu!!kul bana son abun da kike yi dinnan,ita sa’ar kice?ko bata haifeki ba ta haifi wanda ya fiki so ki kama kanki bana son ganganci” cewar Hajiya Fanta tana daga zaune a inda take.”Ammafa Ummah kina gani barna ta mana,i believe yanzu kitchen dinnan bazai shigu ba,ga hannunta da jikinta duk ya baci da abincin da masu aikin nan suka sha wuyar dafawa tsabar rainin hankali,da kinga abun da take kinsan sarai da hankalinta,”Saudat ta fada gami da daga hannun matar sama ta sake da karfin gaske.Rufe ido tayi da karfi ta bude tsabar wani irin radadin da taji kamar hannun ya rabu da gangar jikinta..Muskutawa hajiya Titi ta yi tana kallon na kusa da ita cikin kasa da murya ta ce,

 

“Hajiya Fanta dama har yanzu wannan bakar jarabar tana nan a gidan nan bata bi bola ba?”.Hmmmm Hajiya Titi kenan,idan kuna irin wadannan maganganun mamaki kuke bani,taya zamu barta tabi bola alhali tana damu a raye,wannan lalurace ubangiji ya daura mata kuma a kowanne lokaci zai iya yaye mata,and muma bamufi karfin Allah ya jarabcemu da irin hakan ba” cewar Hajja Fanta cike da imani.”To ai shikenan Fanta tunda ana nuna maki Annabi amma kina rumtse idanu….”Kafun Hajja Fanta ta ce wani abu suka mike gaba dayansu a firgice hadda Badariyya da dama ke kwance a kafar Saudat dazun sakamakon ihun Saudat din da suka jiyo da masifar karfi kamar zai ɓalla palon.Wani irin shaka mahaukaciyar nan ta kai mata bana wasa ba,duk iya kokarinta na son kwace kanta da take yi hakan ya gagara kai kace hannun kattin majiya karfi goma ne aka hada wajen shakarta.

 

Gabadayansu suka nufosu a sukwane ganin numfashin Saudat na kokarin bankwana da gangar jikinta ga idanunta da suka kwalalo waje,duk su ukun suka hadu da nufin kwatar Saudat amma juyi daya mahaukaciyar nan ta yi sai gasu dukkansu a kasa sun zube wanwar,da hannu daya ta rike Saudat daya hannun kuma ta dinga jibgansu dashi kamar wacce aka aikota yayinda a nasu bangaren suke jin dukan tamkar saukar rodi a jikinsu gashi kuma sun kasa tashi dan ba karamar buguwa sukayi da tiles dake shimfide a wajen ba.

 

Da kyar Hajja Titi ta iya mikewa kasancewarta mai rangwamen girman jiki,tana gama mikewa ta ranta a na kare ko gyale bata yafa ba bare aje ga batun daukar jakarta dake saman kujera da wani irin gudu ta fice a palon bayan ta sanya takalmi wari daya ta rarumi daya kuma a hannunta motar ta ta fada mai gadi ya wangale mata jibgegen kofar ta bar gidan tana ta sauke numfashi.

 

*______,,,,______,,,,______*

 

A can ciki kuwa,ta maza Badariyya ta yi ta kwaci kanta,da taimakonta Hajja Fanta itama ta mike suka yi ta kansu,gaba daya sai mahaukaciyar ta koma kan Saudat sai bugunta take kamar ta samu buhun dawa,yayinda Saudat ke ta kururuwa tana kiran “Ummah come help me”….Fanta da ta samu ta tsere bayan curtains ta shige ta buya sai zaro ido take tana hada zufa kamar wacce ta hadiye kunama,tunda uwarta ta haifeta jikinta bai taba shan bugu ba irin wannan.Badariyya kuwa kitchen ta nufa a sukwane….

 

Tun tana wanka a dakinta dake upstair take jiyo hayaniya da ihu a downstairs kamar da muryar Mommynta dan haka tana fitowa ko ta kan kayanta bata bi ba ta sauko da gudu daga ita sai towel yarinya ce da bazata fi shekaru goma sha biyar ba,kana ganinta kaga Saudat dan yadda suke kama…”Subhanallahi Mommmyyyy!”ta fada da karfi sai kuma ta juya a guje har jikinta na rawa ta koma dakinta,hakan kuwa ya yi dai dai da fitowar Badariyya daga kitchen rike da wani murdedden tabarya,bata yi wata wata ba ta mukawa mahaukaciyar tabarya a kafa,aiko a take ta saki Saudat ta durkushe a wajen tana sakin wani irin azababben ihu,kama Saudat dake kokarin kaiwa kasa tana ta shafa wuyarta Badariyya ta yi ganin haka Hajja Fanta ta fito itama.

 

Tana shiga dakin ta rarumo wayarta hadi da daddanawa ta kara a kunnenta kirjinta sai hawa da sauka yake,ji take kamar bazata samu wadda take nema ba dan shi kadai ne zai iya dakatar da abun da zai faru a gidan nan yau……

 

*********

 

Driving yake a kan babban titin Murtala Muhammad Way dake a unguwar MAITAMA a babban birnin Abuja,wakar Justine Bieber na (Love me,love me)ne ke tashi cikin motar.Wayarshi ce ta fara tsuwwa kamar bazai dauka ba har saida ta kusa katsewa ya kama yana karawa a kunnenshi sai dai bai ce komai ba.Daga daya bangaren ta fara magana da dan sauri sauri,”Unclee where are you?idan kana gari kazo gida babu lafiya…..Bayani ta fara mishi sai dai bai jira ta gama ba ya yanke wayar kittt gami da karawa motar tashi speed kamar zai tashi sama,kasancewar ya kusa dama minti goma ya shigar dashi street nasu da ke hadadden anguwar nan MAITAMA dake cikin kwaryar abuja,shine unguwa na biyu mafi tsaruwa da tsadan gidaje bayan ASOKORO,mazauna unguwar rikakkun yan siyasa ne masu rike da manyan mukamai a gwamnati, da kuma masu harkokin diplomasiyya,sai few manya manyan yan kasuwar kasarnan….

 

Horn ya danna a bakin wani babban get da ya kasance baki mai yarfin golden a jiki,danna hancin motar ya yi zuwa ciki bayan mai gadi ya wangale mishi kofar,daga inda yake yana iya hango dandazon ma’aikatan gidan da suka taru waje guda dukkansu,kusan mutum goma sha biyar.ko parking mai kyau bai yi ba ya balle marfin motar cikin zafin nama ya fito,suna hango fitowarshi gaba daya suka watse a wajen kafun ya riskesu.ba tare da ya bi ta kansu ba cike da karfi da izza yake takowa har cikin wani varender mai dan fadi ya shiga sannan ya bude main door corridor ne dogon gaske a wajen,yayi tafiya mai dan tsayi kafun ya zuge wani faffadan door glass ya jefa kafarshi cikin tsararren palon da ya yi nasarar lakume setin kujeru guda biyu amma kamar babu komai cikinsa tsabar girma.

 

“Ya Salam!” ya furta yana dafe goshinsa gami da lumshe matsakaitan idanunsa ganin yadda palon ya yi kaca kaca,gaba daya kujerun dake palon sun kwanta upsidedown,glass center table ya tarwatse a wajen showglass manya guda biyu duk sun zama tarihi,wasu manyan madubi da aka kawata jikin ginin palon dasu suma sun farfashe,rike take da tabaryar sai rotsawa wawakeken television dake wajen tamkar Allah ne ya aikota ta ke,duk farin fatarta ya baci da jinin da glasses suka yayyankata.

 

“Ammi!!”ya fada cikin sanyin murya mai cike da tausayawa halin da ta ke ciki.Cak ta tsaya da abun da take yi,duk da cewa murya kasa kasa ya ambaci sunanta,hakan bai hanata jin kiran ba,juyowa ta yi ta sauke idanunta a kan takalminshi na sojoji dake sanye a kafarshi har zuwa kan wandonshi da ya kasance na sojoji shima,cigaba da daga kai ta yi har zuwa sama.yana tsaye harde da hannuwanshi saman faffadan kirjinshi ya tsura mata idanunshi da suka yi jawur kamar garwashin wuta.Fari ne sol kamar ka taba shi jini ya fito haka kuma dogone na gaske yana da zagayayyen fuska mai dauke da idanu matsakaita masu lumshewa,sai dogon hancinshi da ya sauka har kan kyakkyawan bakinshi mai dauke da redlips,babu gashi ko kadan a fuskarshi hakama kanshi babu wadataccen gashi alamar yana yawan yin aski hakan na nuna alamar shi din cikakken Soldier ne,tsaye yake kyam a kan kafafunshi sanye cikin kakin sojoji wanda ya yi masifar amsarshi tamkar dan shi aka kirkiri aikin soja.Wani irin dariya ta fashe da shi har idanunta na zubar da hawaye bayan ta gama kallonshi sai kuma ta juya ta cigaba da bugun tvn still bata daina dariya ba.

 

“Ammi!!plsss stop it”. ya kuma fada with low voice,kamar wanda yace ta kara ta cigaba da bugu iya karfinta,zuwa lokacin temper na shi ya fara hawa,sosai yake kokarin ganin ya yi calming kanshi down dan ganin bai shouting at her ba,idanunshi sun kada sosai jijiyar wuyanshi sun mimmike.ya kuma fadin “Plsss Ammi ki dainaaa”.amma kamar yana kara mata kaimi ne.

 

“I said stop it!!!!!!!”.

 

Ya fada da wani irin sound da ya karade illahirin gidan duk girmanshi kuwa,a ta ke ta sake tabaryar ya zame kasa jikinta ya dauki rawa kamar ana buga mata ganga,su Hajja Fanta da Saudat da Badariyya da suka makale a daki suma duk sai da suka firgita amma sun ji dadin mai takaita musu wahalan yana gari ashe,da sauri Humaira dake sama ta sauko itama jin unclee ya iso.Sosai jikin mahaukaciyar ke rawa,babu abun da ta tsana a duniya irin shouting yanzu ne zata rikice gabadayanta,takowa ya fara yi zuwa inda take ganin yadda jikinta ke cigaba da mazari har tana kokarin kaiwa kasa ga hawaye dake ambaliya saman fuskarta…Ganin yana tunkarota ta yi azamar durkusawa ta damko tabaryar da ta saki tana nunashi dashi kamar dai mai yi mashi gargadin kar ya iso gareta,bai fasa matsowa ba hakan yasa ta daga tabaryar sama da iya karfinta ta kai masa bugu lokacin da ya iso gareta…Cikin zafin nama ya rike tabaryar ba tare da ya sameshi ba,kokarin dambe ta farayi dashi hakan yasa shi kuma katsamata wani tsawa da ya fi na dazu,wani irin kara ta saki tana toshe kunnuwanta da cigaba da kururuwa kamar wuta ne ya kama a jikinta hannayenta duka biyu ya kama ya rike da karfi ya dauketa har zuwa dakinta dake nan downstairs.

 

Tana turje turje da ihu mai cike da kururuwa amma bai direta ba sai akan kyakkyawan gadonta dake cikin hadadden dakin da bazaka taba zaton mahaukaciya ce ke rayuwa a ciki ba.Saman gadon ya kwantar da ita cike da taka tsantsan ya zaro wani injection a aljihun bayan wandonshi,yasan idan har ta gani ba karamar dambe zasu kwasa ba anan kafun ya samu nasarar yi mata.Bata ankare ba sai saukar allura taji a jikinta,sai dai bisa mamakinsa bata kara wani yunkuri ba sai ma kafeshi da tayi da idanunta masu tsananin kama da nashi,wasu irin hawaye masu turereniya da juna suna bin kuncinta da wani irin gudu.kasa ya yi da kansa dan sometimes tana yi masa irin wannan kallon dake rudar dashi dan haka baya daurewa kallonta a irin lokacin.Kamar daga sama kamar a mafarki,kamar kuma a zahiri yaji bakinta yana motsi ta ce.

 

“AMEENULLAHI!!!!”

 

A dan firgice ya dago kanshi ya daurasu a kanta,wani irin murmushi ne ya subuce mishi wanda ya kara kawata kyakyawar fuskarshi,shekaru goma sha biyu ba wasa ba,shekaru goma sha biyu ta kwashe ba tare da ta furta sunanshi ba sai yau,shi kam wani irin godiya zai yiwa ubangiji,tun yana saurayi dan shekara ashirin take cikin wannan hali gashi yau ya zama matashi mai 32yrs.

 

“Ya Allah” ya furta yana tattare fatan goshinsa waje daya kafun ya dan rankwafo yana leka fuskarta ganin allurar baccin da ya mata ya fara aiki,inda yake adana first aid box a dakin nata can saman wardrobe ya janyo,ciwukan da taji ya goggoge mata ya shafa mata aidine addu’a ya tofe ta dashi sannan ya ja mata duvet ya juya ya bar dakin fuskar shi dauke da matsananciyar farin ciki da duk wanda ya sanshi zai sha mamaki ganinshi a hakan.

 

A palo ya samu Hajja Fanta da ma’aikatan gidan suna ta aikin fitarda kayan da suka farfashe,almost an fitar da komai na palon dan ya tashi aiki except kujeru,da dan sauri ta nufoshi,.”Dan Albarka ka dawo ashe?kaga yau kuma da abun da muka tashi ko?wannan lamari dai Allah ya kawo mana karshensa ya bata lafiya”Cewar Fanta tana matsar kwallah.Fuska ya daure tamau kamar bai taba sanin wani abu dariya ba ciki ciki ya ce,”You don’t worry Ummah”daga haka baice komai ba ya kama kafar bene ya fara haurawa,kai ta dago ta bishi da idanunta dake cike da tausayawa rayuwar dan nata.Cije yatsa Saudat ta yi da karfin gaske tana ji kamar taje ta shake shi ko zata huta da takaicin duniya,Badariyya kuwa jiki na rawa ta bi bayanshi Saudat na rakata da harara,gefen Ummah ta raba zata wuce ta yi saurin cafko hannunta, “To sarkin rawan jiki ina zaki je,ke kullum sai kin nuna kanki a gaban Son?waya fada miki ana nunawa namiji rawar kai haka?”.

 

Fisge hannunta ta yi da karfi tana yamutsa fuska ta ce, “Ni dai kawai Anty ki barni babu ruwanki gaskiya” daga haka ta nufi saman,sake baki kawai H.Fanta ta yi tana binta da kallo.

 

Yana isowa bakin palonshi dake sama tana isowa cike da kwarkwasa tana makale murya ta ce, “Sojana zuwa haka kwatsam babu labar….” kafun ta kai karshe ya watsa mata birkitattu kuma lumsassun idanunshi,murya chunkushe fuska a miskile ya ce yana daga hannu, “Look Badar, i need rest plsss”.Bai kara bata daman cewa komai ba ya banko kofar hadi da murza makulli…..

 

 

 

*BORNO STATE*

 

*4:30pm BAMA LGA*

Karfe 4:30 na maraice a garin Bama dake jihar Borno.Sassanyan yanmacine mai cike da ni’ima dake kadawa ta ko ina,kowa ka gani cike yake da farin ciki.

 

 

(NUJUMUL HUDA TAHFIZUL QUR’AN)

Babbar makaranta ce ta islamiyya wadda farfajiyarta ke cike makil da al’umma zazzaune bisa kujeru na roba dake jere a cikin rumfuna da aka kawata wajen dasu,gefen dalibai daban,gefen sauran jama’a daban kana daga can tsakiya akwai wata rumfar da manyan malamai ke zaune da kuma manyan baki na mussaman.Sautin karatun qur’ani ke tashi cikin daddadan murya wanda ke alamta taron yaye dalibai da suka haddace qur’ani mai girma ake a wajen.

 

“ALLAHU AKHBAR”gaba daya jama’ar dake wajen suka furta bayan yarinyar dake saman stage ta kai karshe a karatun da take yi,mai gabatar da jawabi ya yaba mata sosai lokacin da ya karbi abun magana sannan aka bukaci daliba ta gaba,muryarshi dake fita ta cikin mic ne ya karade wajen “Daliba ta gaba ita ce, (FANNAH MODU BULAMA)”.

 

Cikin jerin daliban dake wajen ta mike cike da nutsuwa mai bayyana kamala,baƙa ce sosai babu abun da ke da haske a fuskarta sai idanunta da fararen ciki suka kasance fari sol baƙaƙen kuwa baƙiƙƙirin,sai kuma jerin hakwaranta da idan ta yi magana ko tayi murmushi suke bayyana haske,amma sabanin wannan baƙace irin sosai mai walkiya ɗinnan.Doguwace fiye da shekarunta duk da kankantarta tana da cikar halitta mai daukar hankalin mai kallonta,kirjinta a cike yake dam dam kana tana da hips mai fadin gaske wanda ya taimaka wajen shafewar cikinta tamkar babu hanji a cikinsu,tana da manyan mazaunai da idan tana tafiya suke juyawa su kadai kamar da gangan take yi sai dai hallita ce kawai ta ubangiji,bakar fuskarta dogone irin oval shape dinnan mai dauke da dara daran idanu masu yalwar lashes gazar gazar da bakinta mai dan fadi kadan da cikakkun lips irin masu tsoka da tsaga tsaga a kansu tana da dogon hanci da wani tsago da ya taso daga saman goshinta passsss har zuwa karshen hancinta,gashin girarta kuwa tamkar da pensir aka zana mata shi sun kwanta mai kyau da cikar gashi tamkar zasu hade da juna,da ka ganta kaga typical KANURI, a misalce bazata fi shekaru goma sha biyar zuwa sha shida ba FANNE Kenan ko muce FANNAH MODU BULAMA.yarinya mai kirar manya.

 

 

Mubi alkalamin Ummu Fadeela da kyau dan ganin ina ta nufa da mu ne wannan karon kuma?Da alama zamusha yawo a tsakanin ABUJA DA BORNO.

 

Ya Allah kasa Annabi MUHAMMAD S A W ya cecemu🙏.

[12/05, 10:12 am] +234 806 343 4430: 🐫SANADIN HIJIRA🐫

 

 

 

By

 

💞Ummu Fadeela💞.

 

*Elegant Online Writer’s*

 

*Chapter 02*

 

*AR-RAHMAN*

 

 

 

 

 

________Cike da nutsuwa take takawa sai faman kare jikinta ta ke da hijab nata wanda ya sha jiki ya kode sosai,ruwan bula ne mai haske amma sai da ya koma fari tsabar yadda yake shan wanki,a gefe guda kuma wani dattijone da bazai gaza shekaru sittin ba,dama dashi wani saurayine da shima bazai haura shekaru ashirin da takwas ba ke ta faman murmushi, farin ciki ya kasa boyuwa saman fuskokinsu tunda aka kira sunan Fanne Modu Bulama.

 

A can tsakiyar fili kuwa ko da Fanne ta iso microphone aka mika mata ta fara karatu cikin zazzakar muryar da Allah subhanahu wata’ala yai mata baiwa dashi, ita din mummunace kamar yadda da yawan mutane suka dauki wanda fatarshi take baƙi cewa mummunane ko da yana da wani sirrin kyau wannan baƙar fatar ta kan ɓoye bayyanan hakan,amma Allah ya mata baiwar murya da ko waye kai idan tana magana sai ka nutsu ka saurareta balle kuma idan tana karatun Qur’an.

 

Zazzakar muryarta ya karade illahirin wajen dama wajajen da suke kusa inda iska ke kadawa yana daukar karatun da take yi cikin SURATUL-IBRAHIM,cike da kwarewa da bawa ko wanne harafi haqqinshi take rero karatun tana tuna fassaran ko wacce aya a ranta, ta ke Imani ya shigeta a hankali muryarta ta fara rawa shauqin Alqur’ani ya fara dibarta,(Malaman tafsiri sunce duk wadda aka karantawa suratul Ibrahim amma baiji Imani a ranshi ba ko zuciyarshi bata rusuna ba,tabbas sai sa’a idan yana da rabo).Ba bu abun da kakeji a wajen sai Allahu Akbar,Masha Allah,Alhamdulillah.Sune ke tashi a bakin jama’ar dake wajen.

 

Tun tanayi muryarta tana rawa har kuka yaci karfinta,cike da rashin sanin abun yi kawai ta kama raira kukanta ta cikin loudspeaker din,sosai hakan ya yi tasiri a zukatan wadanda suke sauraronta,mai jawabi ne ya yi saurin amsar mic din daga hannunta tana share hawaye da bakin hijab ta koma wajen zamanta,ba karamin burge jama’ar dake wajen ta yi ba ciki kuwa harda babanta Modu Bulama da yayanta ALMUHAJIR dake zaune a wajen.

 

Haka aka dinga kiran dalibai daya bayan daya suna gabatar da karatu,bayan kammala karatun kuma manyan malamai suka gabatar da laccoci masu matukar fa’ida kana aka bawa ko wanne dalibi da daliba satifiket da ke nuna shaidar sun haddace Alqur’an akayi addu’oi sannan aka fara gudanar da liyafar cin abincin da ko wacce daliba ta kawo manyan kuloli daga gidansu.

 

Tana zaune cikin kawayenta ana ta rabon abincin da ta tabbata idan ba don Allah ya sa tare da yar uwarta YAGANAH suka kammala islamiyyar ba ko tsinke bazata kawo ba,amma dalilin yaganah an musu kyakkyawar waina da miya ga kuma white rice da stew da ya sha naman rago da yayansu ya kawo…

 

Tsaye ya ke jikin machine na shi mai kafa uku (Keke napep)ya harde hannu a kirji,sai kallonta yake with smile on his face,Baki ne dai shima sai dai bai kai Fanne duhun fata ba,yanayin skin na shi kamar ka hada bakin shayi ne ya ji bournvita fiye da madara,a cikin yankin da yake idan za’a hadashi da wasu mazan,zamu iya kiranshi da kyakkyawa ajin farko kuma dan kwalisa.zagayayyen fuska ne dashi mai manya manyan idanu girarshi cike take da gashi mai yawan gaske,yana da suma mai yawa da alama ya barshi ne dan gayu,yana da cikakken saje wanda ya taso daga kanshi har ya hade da gemun gayu da ya tara,bakinshi mai fadi ne yayinda lebenshi suka kasance bakikkirin kamar na mai shan taba/sigari,sai dai shi ko warin hayakin icce bai so balle na sigari,hallita ce kawai ta ubangiji.

 

Jikinta ne ya bata ana kallonta dan haka ta daga kai saitin inda take jin idanun na yawo a kanta caraff idanunta ya sauka a kanshi,murmushi ya sakar mata itama murmushin ta mishi a lokaci guda kuma ta mike ta nufi inda yake,duk takun da ta yi haka jikinta ke rangaji tamkar reshen bishiya a yanayin damuna. da yawan mutane suna ganin tamkar da gangan take juya jikinta idan tana tafiya basu san itama Fanne bata son wannan yanayi ba kawai dan babu yadda ta iya ne da hallitar Allah.

 

“Ndaah Dubdi Ya Almuhajir,”(Barka da yamma yaya Almuhajir). Bai amsa mata gaisuwar da ta mishi ba sai kafeta da idanu da yayi,,,”Ya Muhajir!” ta kuma fada murya a shagwabe.

 

Firgigit ya dawo jin muryarta, “Uhmmm” ya fada sannan ya sake hannayenshi dake harde ya dan taso daga jinginan da yayi da napep din yace, “You make us proud today,kin yi karatun da babu wacce ta yi kamarshi,you did good recite with your golden voice,keep up the good work dear,”.sai kuma ya yi kasa da murya yana dan rankwafowa kanta kadan yace, “my future kids bazasu taba samun matsala ba wajen karatun addini i swear”.

 

Da sauri ta sa hannu tana rufe fuskarta dan sosai ya bata kunya yadda ya yi a karshen maganar.”Wangina Ya Muhajir”(banaso)”!ta fada da muryarta dake kara narkar da shi da sake dulmiyashi cikin kaunarta…”Nikam ina so,kuma lokaci kadan ya rage mana da zan yi kaca kaca da wannan kunyar taki”.A bazata naji maganartashi dan haka na dago a dan zabure,jinjina min kai ya yi alamar ‘yesss’.Fakam fakam ta iso wajen kamar zata tashi sama,fuskarta a murtuke murtuk tana kallon Fanne a kasan ranta take ayyana wani abu da ita kadai ta sanshi,murmushine ya subuce mata tana dan kaiwa duqe kadan tace, “Yaya Almuhajir ko ka nemeni,bayan kasan kannenka biyu ne sukayi sauka yau din”.Yaganah kyakkyawace sosai a fuska fara tas,saidai fuskarta cike take da zane a kalla zasu kai guda tara gefe da gefe da kuma saman goshi kuma manya manya,jikinta kuwa tamkar an daurawa tabarya zani tsabar rashin kumari,daga sama har kasa daidai suke bata da shape ko kadan sai uban tsayi kamar zalbe.

 

“Oh sorry sister,kinsan idan ina tare da ita mance komai nake yi.So ya saukar kema kinyi kokari sosai amma ina fatan zaki kara zage damtse wajen gyaran tajweed na ki,ko idan mun koma gida Fanne ta dinga gyara miki ohk?kun samu farin ciki sosai yau din muna alfahari daku”…Zuwa lokacin Yaganah ta cika ta yi fam kamar zata fashe har idanunta ya fara kawo ruwa dan haka ta juya kawai ta bar wajen cike da takaici.

 

******

 

Bayan kammala ciye ciye hotuna suka daddauka saboda tarihi sannan kowa ya kama gabanshi,Fanne da Yaganah suka shiga bayan machine din Almuhajir,Babansu kuma da sauran tarkacen kanne da suka zo saukar suka shiga wata tsohuwar motar baban kirar akori kura suka koma gida.

 

Babban anguwace da galibin mazauna wajen masu rangwamen karfi ne,sai dai ba a rasa daidaikun gidaje da masu hannu da shuni ke dashi a anguwar tsilli tsilli.Gaban wani gida suka tsaya gidan yana da kyau ba laifi,tsarin ginine irin na masu kudin shekarun baya,akwai get baki amma ya kwashi zamani dan haka garkame yake da katon kwado sai ta karamar kofa ake bi,cike da farin ciki suka shiga gidan amma banda Fanne dake dan raƙubewa a gefe zuciyarta na ɗan bugawa kadan kadan dan ta tabbata yau UWA bazata barta ba,ta san hukuncin yau mai tsauri ne a gareta.

 

Babban gida ne sosai mai dauke da sassa daban daban,direct sashinsu suka nufa wanda ya kasance ya fi kowanne sashi girma da kyau a gidan harda gidan sama yake dashi amma irin ginin da sosai,duk ya kode ya kukkuje,da dan hayaniyarsu ta farin ciki yaran suka shiga saboda sanɗar da Fanne ke yi hakan ya sa ta shigo a karshe,caraff kuwa idanunta ya fada cikin na UWA dake zaune da wani shirgegen daron silba cike da ƙuli ƙuli da kuma jarkan farar mai a gefe sai faman karkaɗa ƙafa take yi..Suna hada ido gaban Fanne ya bada wani irin sautin bugu Dammmm,a lokaci guda kuma cikinta ya ƙulle,ji ta yi tamkar ta juya da gudu ta koma inda ta fito tsabar bala’in da ta hango a idanun UWA. Sai dai babu yadda ta iya,haka ta tako cikin sanyinta cikinta yana hautsinawa ta iso gabanta.

 

Gabadaya jama’ar dake wajen sun taru ne ana jiran dawowarsu dan taya su murnan sauƙa,amma ko tari babu wadda ya yi suna jiran ganin yau kuma wane irin tijara Uwa zata sauke a kan Fanne?.

 

“Na dauka daga wajen sauƙan ƙauyensu uw**ki zaki koma ai,munafuka mai baƙar fuska da baƙar zuciya,wato baƙin cikin abun da zan samu na cinikin ki kai min ko,to don kaza kazanki sai kin fitar da ƙulin nan yanzun nan sannan kar ki yadda ki dawo min da ko guda ɗaya cikin gidan nan,idan ma sata za kiyi ki kawo min kuɗina kawai na sa ni dan ub**ki,kin wuce kin ɗauka ne ko sai kin gama ƙare min kallo da idanunki kamar na mujiya a wajen?”.

 

Durƙusawa na yi saman guiwata daga inda nike tsaye haɗe hannayena na yi duka biyu,na ce,”Dan girman Allah Uwa ki barni in duba Maaah ta sanya min albarka yau na yi sauƙa kafun in wuce tallar dan Allah Uwa!”na karishe hawaye suna shatata saman fuskata.

 

A hasale ta miƙe kafun ta iso gareni na tashi da sauri,dan nasan matuƙar Uwa ta damƙe ni yau sai na ya bawa aya zaƙinta,baya baya na fara jikina na rawa ina cigaba da roƙarta,duk jama’ar dake tare a wajen yawanci matan ƙannen mahaifinane amma babu wadda ya samu liver ɗin cewa wani abu.

 

Hannuna naji an riƙe ta baya kafun muryarshi ta furta,”Ala ro riyine Uwa”(ki ji tsoron Allah Uwa).cewar mahaifinmu da shigowarshi kenan,ƙwafa kawai Uwa ta yi ta koma wajen zamanta,ba don mutanen dake tare wajenba ta tabbata sai ta sauƙe masa kwandon rashin mutunci.Modu Bulama kuwa jan hannun Fanne ya yi har jikin kafar tsohon benen dake wajen wanda zai kaika sama,a saman akwai ɗakuna guda uku,daga ƙasan benen kuma akwai ɗakuna uku suma,har lokacin jikin Fanne bai daina rawa ba,a bakin ƙofar ɗaki na farko ya sake ta, wufff ta faɗa shi kuma ya shige ɗaki na tsakiya.

 

Da sallama ta shiga dakin ta samu mahaifiyarta da take kira da Maah a saman wata yar yololuwar katifar da ta sha jiki hannunta rike da carbi tana lazimi,da gudu ta karasa wajenta gami da fadawa kanta tana dariya mai hade da kuka.Rumtse idanu Maah ta yi jin irin yadda Fanneh ta cukuikuyeta.Tsawon minti daya tana rike da ita tana dariya hawaye na sauka bisa kumatunta kafun ta dago,zaro idanu ta yi ta sake Maahh da sauri ta koma gefenta ganin yadda ta rumtse idanu,sai a lokacin ta tuna halin rashin lafiyar da Maahh din ke ciki,”Kiyi hakuri Maahh,farin ciki ne ya min yawa”.Cikin murmushi da murya irin ta marasa lafiya Maahh ta kamo hannunta duka biyu ta rike cikin nata ta ce, “Nima ina cikin farin ciki mara adadi Fannetu nah ta haddace Alqur’ani mai girma.Ina rokon ubangiji da ya baki ikon aiki dashi ya kuma hadamu a cikin wannan alkhairi na babbar baiwa da yai miki ke da sauran dalibai,a duk inda kika samu kanki fanneh duk yanayin da rayuwa ta juya maki kada ki kuskura ki mance da alqur’ani,ki karanta shi kana kiyi aiki da ayoyin dake cikinsa,fanneh ina ji a jikina tamkar cewa rayuwata ta zo karshe ina ji a jikina na kusa tafiya in barki,zan barki cikin wahala da rashin mai kula amma ina farin ciki cewa Fannetu na jaruma ce,ina da yakinin cewa bazata taba yin kuka bayan babu ni ba zata tsaya akan kafafunta don haka nasihar da zan maki wadda na ke ji tamkar ita ce ta karshe,Fanne duk tsanani kada ki kusanci zina,ki kiyaye kanki da zuriyarki Allah yai wa karatunki albarka Allah ya miki albarka kema”.

 

Wani irin gunjin kuka Fanne ke yi tana sauraron Maahh,sai da ta kai aya Fanne ta rike hannayenta da karfi tana girgiza kai, “Maahh bazaki tafi ki barni a cikin wannan duniya mai cike da ababan tsoro ba,ke kadai na sani ke na budi idanu na gani a matsayin kawata aminiyata,bazaki mutu ba Maahh idan ba ke rayuwata zata zamto tamkar shuka ce da ba’a bata ruwa,kinga kenan bushewa zatayi karshe ta mutu ,da izinin mai sauke mana ruwan sama zaki haife wannan cikin lafiya nima in samu abokiyar shawara,dan Allah ki daina irin wadannan maganganu Maahh”.Murmushin da ya fi kuka ciwo Maahh ta yi ta ce, “In Sha Allah……”Kafun ta daura da maganar tata aka banko kofar dakin nasu,Uwa ta shigo rai a hade, “To uwar kinibibi da kwainane,me kika ajiyeta a daki kike kitsa mata munafuka dangin farar kafa dangin jaraba,ai ninaga jaraba,tunda aka auroki a gidan nan muke ganin masifu da jarabta kala kala,komai ya kare kamar an yi ruwa an dauke,kin talauta min miji to ahir dinki wllh ni kam nafi karfin ki talauta ni kuma kurwa ta kurrr haka zaki ganni ki kuma barni,”..Ke kuma yar kaza kazan uba kin mike kin fitar min da sana’ata ne ko sai na babbalaki na zubar da banza?”.Tun ba ta kai karshe ba Fanne ta mike jiki na rawa ta nufi waje kafun ta kai mata bugu dan karamin aikin uwa ne ta mata dan banzan duka kuma duk girman gidan babu wadda ya isa ya karbeta sai in tayi sa’a Yaya Almuhajir yana nan,hawaye ne suka cika idanun Maahh na tausayin yarta,da wannan farar maghribar za’a daura mata tallah kuma tana gani babu yadda ta iya,ga yanayin gari babu tsaro kullum al’umma da fargabar yiwuwar yan ta’adda zasu iya kawo attack suke kwana su hantse,haka tana gani Fanne ta fita Uwa ta bi bayanta.

 

 

***********

 

Tana tafiya tana sharar hawaye kanta dauke da babban daron silba cike da kuli kuli,hannunta rike da jarkar mai.Cike da rashin sanin inda ta nufa ga maghriba ta kawo kai gaf ake da fara kiraye kirayen sallah,kamar almara ta fara jiyo karar harbe harben bindiga masu tsananin razanarwa gami da firgita duk wani mahaluki da ya ji wannan kara,cikin kiftawar ido gaba daya garin ya turnuke da kura kasancewar yankin kamar sahara take,duk ta inda Fanne ta juya jama’a ne kawai ke gudun ceton rai kowa ya miki gabas sai ihu da kiran Ubangiji masu imani ke yi wasu kuwa tsabar firgici babu abun da suke fadi sai, “Sun shigo sun shigo,sun kawo hari Innalillahi sun kawo mana hari”abun kamar wasa karar harbe harbe sai daduwa yake yi ganin hakane yasa Fanne sakin daron da ke kanta itama ta runtuma a guje tabi ayarin masu gudu.dan zuwa lokacin ta fahimci yan ta’adda masu ikirarin jihadi a arewa maso gabas ne suka kawo musu hari kamar yadda suke jiyo labari sun kai hari a garuruwan da suke makwabtaka,yanzu haka ma garin na su cike yake da yan gudun hijira.Gudu kawai suke yi,kowa ta kanshi ya ke haihata haihata,ya yinda karar harbe harbe ke kara kusanto cikin garin,babu mai tuna komawa gida kowa daji ya durfafa cike da tashin hankali.

 

 

 

***ITALY***

 

 

Leonardo da Vinci-Fiumicino Airport Rome city Italy.Kasaitaccen filin tashi da sauƙan jirage na ƙasa da ƙasa dake birnin Rome a ƙasar Italiya,jirgin da ya taso daga birnin barcelona na kasar Sifaniya (spain)ne ake bada sanarwar sauƙarshi.ba bu jimawa bayan ya daidaita a kasa fasinjoji suka fara sauƙa,da yawansu yan ƙungiyar wasar ƙwallon ƙafa ne da suka zo buga wasan sada zumunci tsakanin Spain da Italy don fara shirye shiryen kofin duniya da za’a buga ba da jimawa ba, sai magoya baya da yan kallo da jirgin ya kwaso.

 

Shine ya fara sauƙowa,sanye cikin jessey (kayan yan ball) red and yellow kalar tutar kasar Spain,kasancewar rigar mai karamin hannu hakan ya bayyana zanen TATTOO daya cika ko wanne bangare na hannunshi daga sama har ƙasa babu masaka tsinke,kafarshi sanye da wasu shegun takalma irin na ƴan ball,fari ne tasss kamar babu jini a jikinshi irin dai farin turawa na asali, dogo sosai mai kakkarfan jiki,yana da faɗin kirji da manya manyan damatsa wanda ya taimaka wajen bayyanar da kirar majiya ƙarfi da Allah ya bashi,yana da dogon fuska mai ɗauke da manya manyan idanu kalar ash,wato baƙin cikin sun yi kalar toka toka da zara zaran lashes kamar mace da dogon karan hancin da ya sauko har kan zagayayyen pink lip nashi,gashin girarshi kuwa kaɗan ya hana su haɗewa da juna,gashin kanshi mai yawa ne sosai a tsatstsaye amma gefe da gefen an saisaiyeshi daga tsakiya kuma a cike kamar za’a kitsashi,kyakkyawane ajin farko,kana ganinshi kaga baturen asali.Captain JACK Smith Edward,Captain ɗin ƙungiyar kwallon ƙafa ta Spain ɗan wasan gaba mai sanya riga lamba 7.

 

 

 

*THE STADIO OLIMPICO*

 

Filin wasan stadio olimpico,a yaren italy,ko Olympic Stadium a turance babban filin wasane mai girman gaske,shaƙe yake maƙil da yan kallo a ƙalla 70,000 yan wasan spain da italy ne ke fafatawa, sai dai har bayan minti talatin da farawa babu ƙasar da tayi nasarar jefa ƙwallo ko guda a raga.ko wanne bangare ya galabaita bayan dawowa daga hutun rabin lokaci amma babu nasara,yan kallo sun cika wajen da ihu kowa yana karawa kungiyarshi karfin guiwa,a cikin haka ne Allah ya bawa Jack ikon karbe kwallo daga kafar wani, nan ya fara lilata yana wani irin juyi a wajen cike da kwarewa da sanin sirrin kwallo cikin kasa da minti daya ya yi baya baya ya fara kamar zai kwanta a kasa still ball din tana kafarshi,wani irin shoot ya bawa ball din ta mike dodar sai cikin ragar yan Italy ta shiga ta bugi raga ta kara fitowa daidai Jack ya kawo kafarshi kenan ya kuma bugunta da wani irin karfi,fiit ta kuma shigewa ciki duk yadda goalkeeper dinsu ya so tareta hakan bai samu ba,ihu magoya bayan spain suke yi iya karfinsu ganin cikin minti daya an sha kwallo har biyu.A tsakiyar fili kuma wani irin tsalle Jack ya yi yana bankare kirjinsa gami da hade babbar yatsarshi da kuma yatsar tsakiya,daya hannun kuma ya ware yatsu guda uku ya tankwashe biyu,ya bude baki yana wani irin ihu mai karfin gaske,gaba daya jijiyoyin jikinshi suka mimmike yayinda ake iya hango har cikin makwogoronsa,wannan shine sign na shi duk sadda ya ci kwallo,bare ma irin wannan ci biyu a bugu daya. tuni wadanda suka fahimci abun da ya yi suka fara kwaikwayonshi suna ihun murna da fadin,’Jackie,jackie jackie’.Haka wasan yayi ta gudana har aka tashi ba tare da daya bangaren sun rama ba,da wannan nasara ta ci biyu da babu 2:0 tawagar su Jack suka samu wucewa kofin duniya.

 

 

 

Joseph tarradellas barcelona-el prat airport spain.

 

 

sabanin tafiyarsu sanye da jessey,dawowarsu ko wanne dan wasa cikin kayanshi normal ya dawo,filin jirgin cike yake makil da magoya baya sai daga musu hannu ake yi kowa burinshi su gaisa da yan wasan mussaman Jack da ya kasance captain kuma fuskarshi sananne ne a kowacce nahiya ta duniya,sanye cikin wasu riga da wando pencil farare sol sai wata bakar jacket da ya daura a kai ba tare da ya zuge zip na ta ba hakan ya bayyana rubutun dake gaban rigarshi da manyan baki kalan black an rubuta HANDSOME,kafarshi sanye da wasu arnan sneakers samfurin gucci kalar baki,hakama tsintsiyar hannunshi daure da wata makeken agogon azurfa itama samfurin gucci din,wuyarshi makale da wata chain na zallar diamond ya sauko har kan kirjinshi sai walwali ta ke yi,gashin kanshi ya sha gyara a tsatstsaye daga tsakiya,ash colour eyes nashi tarwai akan magoya baya sai daga musu hannu yake yi fuskarshi tamkar gonar auduga dan fara’a,da haka har suka isa jerin gwanon motocin da ya zo daukarsu,club center na su suka wuce dan halartar liyafar da aka shirya musu na murnar nasarar da suka kawo gida….

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Ga dai Sojanmu mai Redlips, da kuma Captain namu mai pinklips, ga kuma Yayanmmu mai Blacklips,mu cigaba da bin alkalamin Uwar Fadeela don jin wanene Kaddarar Fanneh ke makale da tashi.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment