Littafan Hausa Novels

Sai Baba Buhari Hausa Novel Complete

Hausa Novels
Written by Hausa_Novels

Sai Baba Buhari Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

🥰 SAI BABA BUHARI 🥰

 

(Ummu azaan)🚶🚶

 

🍂Dasunan Allah mairahama maijin ƙai

Page 1 ✍️✍️✍️

 

 

________ Yaya Dan Allah kayi hakuri kabar wannan kukan, kuma fa, zaka iyasawa muyi, cike ba ɓacin ran hakurin da take bashi, ya kwada mata mari har sanda tayi tambul ta faɗi ƙasa.

 

Yace” dan uwar ubanki idan banyi kuka ba, rawa kike son na tashi na ku? Ya sake fashewa da wani sabon kuka mai sauti…

 

A Dalilin Da Namiji Hausa Novel Complete

Yana fasa asusun yana ci gaba da kuka wiwi, cikin kukan yake faɗin mesa? Ka mana haka Baba? Yarin yar daka kwaɗawa mari ɗazo, cikin razanan ganin kuɗaɗe haka tace” kai yaya Bulama dukka wannan naka na? Dama kana da kuɗi har haka, sharce majina yayi, ya kalli mahaifiyar shi zatayi ta gumi yace” Inna wallahi nawa ne. Halak malak babu ɗigon haram aciki, amma gashi sun gagare mu ci damafa injin niƙa nakeson na siya Miki dasu…..

 

 

Inna wallahi Baba Buh…… kada dakata min, inna ta katse shi, cikin bacin rai tace” A lokacin da ake zaɓe bakai bane wannan yazo har nan yana kuka wiwi akan sai dai na je nazaɓi Baba Buharin ku ba? Harma da bani dari uku, wai soma taɓi ne da zarar babu Buhari yaci zamuga canja, to me na kuka kuma? Tonda ga canjin da kukane ai kunsamu,, dan hana ni babu ruwa na…. kallon asusun dake gaban sa yayi ya sake fashewa da kuka sosai har yana neman shidewa…..

 

 

Wani tsoho ne ke shigo wa gidan, yana waƙar, kai ku bani kiɗar janaral a sama masu gudu su gudu.. sai Baba Buhari, talakawa, dai Baba Buhari, masu kuɗi.. ga malam audu yace”…….

 

Turuss malam audu dake shigo wa yanzu yaja gefe guda ya tsaya dan ganin uban kuɗaɗa, wanda ma bai taɓa kallon suba tunda yake, amma yau ga su agaban Bulama….

 

 

Hmmm azuciyar shi yace” ko waya bawa Bulaman kyautar kuɗi haryasa shi kukan murna haka? Barin dai je in gani, ya karasa shiga cikin gidan, fuskar shi dauke da annuri yace” kai lafiyar ka kuwa?

 

Malama inafa yaga lafiya, gyara tsayuwa malam yayi yace” to Meya faru? Nuna kuɗin inna Ladidi tayi, tace” dama wai ashe Bulama nada waɗannan kudade haka? Malam bamu sani ba har wata rana muke tsana da yunwa agidan nan,,,

 

hhhhh audu yayi dariya irin nasu na tsoffi yace” Masha Allah, Hamdan kasiran, Eh hhh shikenan kuce ashe kakar muce ta yanke saƙa ɗana.

 

Da sauri inna Ladidi tace” ko kuma kace yanzu kakar ku zata fara daura saƙar ba. Cikin rashin fahimta malam audu yace” me kike nufi?

 

Ohoo dama baka saniba? Ke ko ina zan sani Ladidi tunda ba’a faɗa min ba, gyara tsayuwa inna tayi tace” wannan kuɗin da kake kallo, na Bulama ne, yanzu yaje banki akace andena karɓar shi kotaku shine yanzu yake kuka,

 

Cikin fargici Malam Audu yace” Yanzu da gaske andena amsar wannan kuɗin? Eh mana malam yakai sati biyu ma da dena amsar su Wallahi …

 

Kan Bala’i malam audu ya faɗa yana zare idon waje, to yanzu ya za’ayi dasu kenan? To kai Malam ance maka abu andena amsa ai sai zubar wa ko ƙonawa,, Iyeee Ladidi malam audu yafaɗa da karfi,

 

Kinsan me kike faɗa kuwa? Waɗannan kuɗin za’a kona?

 

 

To aradun Allah ba’a isaba kuma a tsaya agani ni ya tsunguna ya dauki dubu ɗaya acikin kuɗaɗen yace” wannan kuɗin, tsohon dubu dayan sainaci abinda ya kaina dubu goma, ya sa a aljuhu sannan ya fice……✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

 

To be continue. My guys

🥰 SAI BABA BUHARI 🥰

 

(Ummu azaan)🚶🚶

 

Page 2

 

 

Malam Audu na fina kofar gida ya tsaya yana tunanin taya zaifara,? wani mai napep ne, ya katse mai tsananin, da faɗin” Baba tafiya ne?……

Murmushi malam audu yayi

Azuciyar shi yace” yauwa bari a fara da kai, ɗan yaro…… Eh ɗan nan, Kasuwar jan bulok zaka kai ni, to shiga muje Baba, Amma fa kuɗin ka ɗari biyu ne Baba,dan kasan mai yayi tsada sosai yanzu…

 

Eh babu komai Malam Audu ya shiga, sai Kasuwa,,, kan su isa wajen da akwai mutane, Malam Audu yace” yauwa sauke Ni nan, mai napep yayi parking, Malam Audu tafiya, yace” to ina yaro? Gani nan Baba,

Laluɓen kuɗin malam audu yafa, kan ya gane kuɗin daƙer, yace to ungo… Rikeshi da kyau karsu bi’iska, ka dauki halalin ka kabani nawa halalin… Kallon kuɗin mai napep yayi yace”

 

Kai baban ai ba’a karbar su Baba Buhari ya hana, tunda dadewa, da sauri Malam Audu ya dafa kirjinsa yace” kai dai yaro da gaske? Eh wallahi Baba da gaske an dena,

 

Innalillahi wa’inna ilaihir’raju’un, yafaɗa yana dafa hannunsa, to yanzu yaro ya za’a? Eh to yaxa ayi kuwa, jeka kawai baba tunda baka sani ba ne,

 

Mai napep yaja abinshi yaya gaba, malam audu ya daga mai hannu yana dariya… cewa” acikin dubu goma, na kashe ɗari biyu, saura nawa kenan???

 

To dai yanzu bari na ƙoshi saina haɗa nayi lissafi… Yana zuwa wajen mai gurasa yaga jama’a dayawa, sai yaji kamar ya tafi amma saiya, tsaya yace” abashi na ɗari biyar, mai gurasa ya sa mai, tsaban yanda yake jin yunwa, nan take ta cinye..dama mai gurasar na wajen yana tattara kwanuka,

 

Malam Audu yace” mai gurasa ina fasan dai kanada sanjin dubu ɗaya ko? Eh Baba baza’a rasa ba in sha Allahu, to Masha Allah, gashi yi sauri kaban dan yanzu haka maganin zazzaɓi zanje na siya da sanjin…

 

Da wani kuɗin Baba? Da wannan mana yaro,… haba ina ai yanzu wannan Kuɗin da su da takarda duk ɗaya suke, yanzu basuda amfani ai Baba, Zaman ƴen buri Malam Audu yayi, akan kujera, yace” kaico Allah, Shiyasa mama yau yazo ya biyani bashin dana ke binshi, da wannan kuɗin, Allah Sarki, ga ƴata na konce ba lafiya… ya buɗe ido ɗaya yana kallon, mai gurasa ta gefe…..

 

Hmm yanzu dai baba kaima kama son cewa baka san andena karɓar suba? Kuma cutar ka akayi? Eh wallahi yaron ƙoranƙosa bansa nibah…to Shikenan jeka, Allah na nan…

 

Kuka Malam Audu yasa yana cewa” Allah Sarki ɗan nan na gode sosai, Allah ƙara muku, imani, ameen Baba Kai ma Allah baka jumriyar rashin Dubu ɗayan ka, amen yaro amen,

 

Wani dake gefe yace” Allah Sarki wallahi har tsohon yabani tausayi, kajifa wai magani zai siyawa yaran shi da kuɗin, Hmm Eh ai wallahi canjin kuɗin nan ya tozarta mutane ba kaɗan ba… haka suka ci gaba da hirar su, har Malam Audu yafita, yana fita yace” kai alhamdulilah, amma wannan sana’ar tawa da akwai ribah sosai…

 

Har zai tafi, saikuma ya Juyo dan ganin mai, kifi….. Murmushi yayi yace” mai kifi kaima yau Allah yanufa zaka fitar da Zakka, kenan Assalamu alaikum, yayi Sallah ma…

Yaa Baba kifin ta nawa za’a baka? Eh…..Da sauri malam audu ya juya dan ganin mai gurasar ɗazu yana zuwa, yadai baba kana lafiya mai kifi ya tambaya…

 

 

Cikin sauri yace Eh, to Asa maka kifin ne? a’a yaro tsohon kuɗi ne dani ba sabo ba karkasa kayi asara,, ya tashi da sauri, zaibar wajin dan ya tabbata idan har mai gurasa ya Ganshi to, cin daɗin shi ya ƙare kenan, kuma shi bazai so hakan ba dan a ganin shi baima fara cin komai ba yanzu….

 

dan haka ya tashi yabarwajen, da sauri sauri, sanda yayi nisa sannan ya tsaya yana tunani, kai jama’a mene ne nadaɗe banciba? Ya daura hannu Abaki alamar tunani, kai suna dayawa amma in sha Allahu a sannu sannu zanci duka amma yanzu bari a leƙa mai koyi da burodi………. ✍️✍️✍️✍️

 

To be continue. My guys

 

 

KAI DA GASKE COMMENT ƊIN NABADA NISHIƊI SOSAI WALLAHI 😂😂😂😂😂

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment