Littafan Hausa Novels

Romantic Hausa Novels Complete

Romantic Hausa Novels Complete
Written by Hausa_Novels

Romantic Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

Romantic Hausa Novels Complete
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

Dedicated to Rumaisa Aliyu Inuwa, Allah ya bar ƙauna

 

Episode0️⃣3️⃣
___________________

Babu komai jikin AZIZA na rauni ko kumburi kawai ihu da hargowa ne, Inna ta ce” wai wacce yarinya ce ne ta fasa tulun ne?” AZIZA da ke lanƙwaye-lanƙwaye a gaban Inna ta ce “Lantana ce yayar su Zahradeen ” Lahhh ilah wannan gansamemiyar budurwarce ta dake ki, ayya ai daga ji babu adalci a wannan lamarin”
Maigari ya sa aka ƙaraso da BABA sai mita yake ya na ganin ba’a kyauta ba, Inna ta kamo AZIZA suka nufi gaban Maigari dan ganin wana hukunci zai yanke akan hakan.

Maigari ya yi gyaran Murya ya ce ” BABA wannan jikar taka ta fiya neman husuma dan duk abinda ya faru ita ce sila” Malam Isa ne ya labarta duk abinda ya faru.

AZIZA sai harare-harare ta ke tana jikin Inna a raɓe, Maigari ya ce “a kira masa Lantana da Mahaifinta domin ayi musu tsakani sanin halin AZIZAN BABA kamar yanda ta ce sai ta kasheta da duwatsu to kuwa tabbas Lantana zata sha jifa.

Malam Barau mai faskare ya na faskarensa a ƙofar gida yana cinikinsa, yaga Lantana da ƙawayenta sun dawo ta na kuka, ajiye gatarin ya yi yana faɗin lafiya me ya sameta, nan su Ai ƙawarta ta ce”AZIZAN BABA ce ta yi mata tsindir a bakin famfo

“innalillahi wa’inna’ilaihirrajiun garin ya ya, ke ba ki da hankali za ki kula wannan yarinya ai shikenan” ya koma ya ci gaba da faskarensa, a cikin gida kuwa Baba Nafi najin abinda ya faru ta hau Lantana da faɗa, inda ta ɗora laifin akan Lantana.

Babu abinda ke ƙara tunzura zuciyar Lantana kamar yanda aka ganta daga ita sai ɗan zani abunka ga ƙauye ko arzikin bra babu, ga yara cike a wajen, hakan yasa take ƙara kuka.

Su Ai su ka koma famfo dan ɗauko ruwansu tare da na Lantana, Yaron Maigari ne ya yi sallama wajen Malam Barau, Malam Barau ya ji faɗuwar gaba, abunka ga Fulani tsoro ne ya kamashi ya ce ” ince dai lafiya?”

Malam Inusa yaron Maigari ya ce” lafiya lau Maigari ke kira ku je fada yanzu tare da ƴar wajenka” Barau ya ce ” gamu nan” ya shiga gida ya na mita “ai ga shinan ina zaman zamana kin ja min magana, ta shi mu je Maigari na kira” wani mugun razana Lantana tayi, ta hau kuka tana faɗi, ni kam aradu bazan koma wajen nan ba” Barau ya ce “kin tashi ko sai na bigeki babbar kwabo wuce mu je”

Baba Nafi bata ce komai ba sai cigaba da aikinta da tayi.

Fadar maigari ta cika da jama’a, Lantana da Babanta suka iso, durƙusawa sukayi Barau yayi gaisuwa ya ce ” gamu mun iso ranka ya daɗe”

BABA sai auna masa harara yake yana jin kamar ya zane Barau.

Maigari ya ce ” Lantana ba ke ba AZIZA ko a hanya ban yarda wani ya tsokani wani ba, AZIZA ƙanwarki ce kinji abinda na faɗa miki ko,sannan ko ba ita ba kar ki ƙara fasa wa kowa tulu duk da yanzu an biyata w…..”

me wallahi banason wance alkur’an namu muke so” AZIZA ta faɗa tana ƙara maƙalewa a jikin Inna, BABA ya ce “ungo nan AZIZAN BABA, ya yi mata daƙuwa, ana magana kina magana kar na ƙaraji” ɗauke kai tayi ta na cuno baki.

Romantic Hausa Novels Complete
Lantana ta ce “to bazan ƙara ba”
Malam Barau ya ce “ayi haƙuri Allah baka nasara in sha Allahu ba za’a ƙara ba wannan ma tsautsayi ne”.

Malam Isa ya ce “ranka ya daɗe ajawa yarinyar kunne abun da tayi ba bu daɗi, kaga rigar can a kwata wallahi ba ta kyauta ba sam”

Maigari ya ce ” ashsha ke AZIZA ki ɗauko rigar ki wanke mata ki kai mata gida, ba ta haƙuri”

Wani irin bala’i ne ya turniƙe zuciyar AZIZA, ihu ta ƙwalla ta miƙe tsaye ta kwasa da gudu ta na faɗin ” idan na ba da haƙuri Allah ya tsine min, kuma ba rigar da zan wanke”
Maigari da sauran jama’a aka bi ta da kallon mamaki ta sallami kanta.

BABA sai fara’a yake ko haka AZIZA ta biya shi, Barau ya ce “yarinta kenan, in banda abun yara ma mene abun faɗa akan ɗaukar ruwa” Maigari da kunya ta rufe shi, na burus ɗin da AZIZA tayi da umarninsa abun da bai zata ba ta aikata masa, da yasani bai faɗi ba kawai yake.

Haka ya ƙara bawa Lantana haƙuri tare da iyayenta,BABA ya tashi yana faɗin “ai dole in ne mawa yarinyar nan maganin baki,an sa ta a gaba idan na tsaya sai a sabauta min jika, marainiyar Allah ta’ala Allah ya taimake ka mu zamu koma” Maigari ya ce ” to a gaida gida Allah kiyaye gaba”
Inna ta miƙe ta ce ” a dai yi haƙuri da sha’anin yara,ke kuma ki riƙe girmanki kinji, du dai a taru a yi haƙuri” Barau Mahaifin Lantana ya ce “babu komai Inna mun mungode ƙwarai”
BABA ya ɗauki sandarsa ya yi gana, Inna ta bi bayansa.

 

Baba Tabawa tunda suka tafi ta zauna a bakin ƙofar ɗakinta ta na fatan Allah ya sa ba wani abu ba ne ya sami AZIZA ba, can kuma sai ta tashi ta leƙa ko sun tawo, sai kuma ta dawo, duk tsoffin ba sa son wani abu ya sami AZIZAN BABA.

Romantic Hausa Novels Complete

AZIZA kuwa gudu ta ke cin ƙarfinta, duk yaron da ya tare mata hanya sai ta bi ta kanshi,ko ta bangaje ka ta ture yara kusan biyar duk ta sa su kuka, Anas da ke kan keke ji yayi kawai an hankaɗa shi, ya faɗi ƙasa ba tare da ta juyo ba tayi gaba,kukkurjewa yayi ya na ta kuka, BABA ne ya hango shi ya na duba hannunsa, Anas ya nufo BABA ya na nuna masa abinda AZIZA tayi masa, BABA ya ce ” ayyah sannu kaji yi haƙuri, 20 ya ɗauko a aljihu ya ce “ungo je ka siyo ja da yalo ka haɗiya” ya yi gaba.

romantic hausa novels complete
Anas ya ja kekensa ya na kuka ya koma gida aiken da bai je ba kenan.

Garam, Baba Tabawa ta ji an banko ƙofa, a guje ta ga AZIZA, ” idan na wanke Allah ya tsine min kuma tulu ne sai an biya mu” Baba Tabawa ta ce “Alhamdulillahi babu abinda ya same ki dai ko?”
AZIZA ta na haki ta zauna a kan cinyar Baba Tabawa ta hau bata labari ta na tafa hannu ta na faɗar duk abinda tayi, Baba Tabawa ta ce “a’a ba ki kyauta ba, ai ta rigaki zuwa meyasa kika janye mata bokiti kar ki ƙara irin haka”

“Tayi ɗin, wato kuma anan ɗin ma a baki za’a sata wai meyasa Tabawa ba ki da kara ne,ko dan baki san darajar ƴaƴa ba”
Baba Tabawa ta ce ” ba wani abu na ce ba Malam ina nuna ba ta kyauta ba n…..” ta so nan ni nan zan iya da marainiyar Allah yau ɗin nan zan sa a fara yi miki rubutun lahaula ki na sha haba ƴa ɗaya tal an sa ta a gaba”
Allah huci zuciyarka” Tabawa ta faɗa ta na shigewa ɗaki, halin da BABA ya koya kenan da ta yi magana akan abinda AZIZA ta ke na ba dai-daiba to zai goranta mata, tunda ita ba ta taɓa haihuwa ba.

Littattafan Hausa Novel Complete

Inna ce ta shigo ta na nata faɗan, dan tasan AZIZA ba ta da gaskiya tunda aka mai da magana. “ni wallahi da Malam zaka amince Aminu kawai za ka sa ya ɗauke AZIZA ya tafi da ita can burni mu ma ma huta da magana”

“Au ke ma yo ni za’a yiwa iya shege, babu wanda zan bawa yarinyar nan, dan ba ku san ɗumbin ladan da ake samu ba idan ka riƙe maraya ba, wallahi babu mai raba ni da AZIZAN BABA sai Allah”
AZIZA da daɗi ya rufeta, ta fashe da dariya ta na juyi ta ce ” BABA ni fa ko babu wanda zai yi min na barshi, ina tulun yake?” Inna Gaji ta ce ” an yafe musu ai ba shi ɗaya ba ne ko, ga su can sun isa zaman duniya”

AZIZA ta ce ” kut har sabon ma an bar musu” sai ta miƙe zata koma, BABA ya riƙota ya ce “idan kika koma Maigari sai ya sa an zaneki, tunda kika gudu baki yi biyayya ga umarninsa ba” dawowa tayi ta nemi guri ta zauna.

 

Baba Tabawa ce ta fito tana lallaɓa AZIZA akan ta yi shiru, kayan makarantarta ta ɗauko dan ta wanke mata da azahar akwai makaranta, AZIZA ta ce ” yauwa Baba kinsan me, sai ta fashe da dariya ta ce ” bari kiga yanda BABA ya ke tafiya hahhhh” ta miƙe zata kwatanta.
Inna ce ta duma mata dundu a baya, daman haushinta take ji ta sa sun je sunyi faɗan rashin gaskiya.Numshin AZIZA ne ya ɗauke dan dukan ya shigeta cikinta ya ƙulle jan numfashin da tayi bai dawo ba, faɗuwa tayi a ƙasa.
Baba Tabawa ta hau jijjigata, ta na kiran AZIZA, AZIZA,
Inna Gaji ta ɗora hannu aka, BABA da ya ke fama da ciwon ƙafa saurin da yayi ya sa take masa ciwo, ya na shafa man zafinsa.
Ya ji ana kiran AZIZA cikin tashin hankali, da sauri ya tashi ya nufi tsakar gida mugun gani yayi wanda ya sa BABA jin jiri na neman kama shi.
Da sauri ya ce “me akayi mata?” Baba Tabawa ta ce ” faɗuwa tay….Wani ihu AZIZA ta kurma ta na faɗin ” wayyo Allah sun fasamin ciki na” gaba ɗayansu suka sauke ajiyar zuciya jin ta dawo, amai ta shiga kwarawa.
duk sun ruɗe, mugun so suke mata, jiƙon magani BABA ya ce a kawo.

 

Wani yaro ne ya shigo ɗauke da ƙwarya a fashe da gari mai ƙasa ya na kuka, “BABA ya doka masa tsawa ” kar ka ƙaraso nan koma inda ka fito duk kun cinye min yarinya, kai dole mu bar wannan garin, tun kafin na rasa jikata”
AZIZA ta kalli yaron da tasan ita ta ture shi.Gwalo tayi masa, aikuwa yaro ya ƙara sautin kukansa.

Sanda BABA ya ɗauko ya bi yaro, a guje yaro ya bar gidan………

 

KANO

 

Gaba ɗayansu har Daddy suka ce” mene ne damuwar Mami?” murmushi ta yi ta ce” sai ta takurar da kuke min akan cin abinci mara maggi da gishiri” hahhhh duk suka sa dariya.
AZEEZ ya sauke ajiyar zuciya ya ce “kinji inda hantar cikina ta kaɗa, da kika ambaci damuwa Mami” dariya ta sa ta na mai jin farinciki, kullum burinta kenan ta gansu a haka suna nishaɗi.

 

Bayan sallar Isha Daddy ya ƙira BABA dan jin ya suke, wayar BABA da ke cikin kwano a rufe ruf, bayan ya kwanta bacci ya ji ƙarar wayar, buɗewa yayi ya ɗauko wayarsa ƙaramar panasonic key pad ya amsa, Alhaji Aminu dollers ya russuna ya na gaishe da BABA, nan BABA ya amsa ya na tambayar sun dawo lafiya, Daddy ya ce “Alhamdulillah ya su Inna fatan komai lafiya” BABA ya ce “lafiya lau, ɗazu ne ma AZIZA tayi kumallo amma yanzu tayi bacci ma” Daddy ya ce “Allah ya bata lafiya” ya ce “amin ya Allah”
Nan Daddy ya ce ” BABA akwai wani gida a nan bayan layin mu to shine nake ganin ko zaka dawo nan ɗin saboda security, hankalina yaƙi kwanciya da zamanku a nan”

BABA ya ce” sikorito na ce sikorito ni babu inda zanje ina nan, watukun dan na hanaka ƴar ɗan’uwanka shine zaka ɓillo ta nan ko” Daddy ya ce ” a’a ba haka ba ne BABA yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba, kaga masu garkuwar nan ba su da imani da zarar sun san ɗanka yana da ɗan wani abu na duniya sai su hari iyayen mutum wallahi ina tsoron wannan abu” BABA ya ce ” kai Aminu ko me zaka ce babu inda zanje kaji ko”
Haƙura Daddy yayi ya yi masa sallama ya ajiye wayar.

Shekara biyu kenan Daddy ya na lallaɓa BABA akan ya dawo burni da zama amma yaƙi.

Mami ce ta shigo ɗauke da tea da zuma, ganin fuskar Daddy da damuwa ya sa ta ajiye akan bedside table ta ce” me ya faru Alhaji”
Daddy ya ce” ni da BABA ne” taɓe baki tayi ta ce ” ai sai haƙuri ina ruwan BABA”
Daddy ya ce ” hankalina ba zai kwanta ba indai su Inna ba su dawo kusa da mu ba”

Mami ta ce” kasan a can ya saba da rayuwarsa, ka bar shi mana tunda bayason dawowa nan ɗin” Daddy ya ce ” ina ga next week zan je garin in sha Allahu ki sanar da su AZEEZ zamu je Mazoji gaba ɗaya……….

 

 

*Zinariya ce

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment