Littafan Hausa Novels

Ribar So Hausa Novel Complete

Hausa romantic novels Wattpad
Written by Hausa_Novels

Ribar So Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

RIBAR SO

 

*Alhmdulillah I thank God for giving me the ability to start writing this book safely. I pray to God that I can finish it safely*

Greetings to you people of trust, Miss Hajjo’s true love wherever you are, I greet you and wish you all the best

 

*Ku gyara zama fatan a shirye kuke Dan the style is different da ko wani irin salo ku tanadi Time tare da isashshiyar data anyhow lol Dan Tafiyar Nan ta Musamman, ce zazzaface ,Kuma Doguwar tafiya Mai dogon zango Kunsai dai Alkalamin miss hajo baya rubuta labaran banza*

 

بسم الله الرحمن الرحيم

12✓06√202

 

*LAGOS STATE*

*_Banana island_*

 

“Aljannar duniya “Abunda bakina Kawai ya iya furtawa,tabbas Nace Zan fada tsaruwa girma da kyan gidan littafin Gaba Daya zai karene a Haka ban Isa iya tsara fayyace Muku bayaninka wannan Katafaren gidan ba dake Cikin katafariyar unguwar,da ko ban fada ba kunsan ya zarce Duk abunda bakina zai iya furtawa.

Duniyar Shahara Hausa Novel Complete

Kasancewar unguwar ta na da tsaro Hakan yasa Basu bukace wasu security’s da yawa ba security Hudu ne kawai Masu gadin Hadadden get din gidan da ya yi zarra a area.

 

Kai tsaye kutsa kaina nayi Bayan na wuce get Ukku Kafin na Isa harabar Gidan,

,part part ne kala-kala har ban iya lissafawaba Kuma kowannensu tsararru,Ukku dake cikinsu ne Mai dauke da benaye,Sauran Duk flat ne, ,shuke-shuke gwanin ban sha’awa sai parking space guda ukku a gidan Wanda Duk Daya a kalla zai Dauki mota sama da ashirin.

 

 

“To naji next week zanzo da kaina ganinki shikenan bar kukan kinji baby na ko so kike Nima na Fara kukan Eyye babyn momy”

 

 

Matashiyar matar da Bata haura shekara 32 ba a fuska,

Kyakyawace dukda kib’ar dake tare da ita Bai Hana baby face Dinta Fitowa ba,.

fara ce badai chan ba masha Allah Kallo Daya zaka Mata kasan tabbas hutu,gayu, aji,sun zauna a wajen sanye take Cikin Lafcecen Lace Dinkin yabi jikinta na manyan Mata.

 

,ta k’arasa fada Ta na Dadda’ba bayan matashiyar budurwar dake Makale jikinta dukda ta boye fuskarta a k’irjinta sautin shashekar kukanta kawai kakeji.

 

 

Bakinta ta d’ora daidai saitin kunnanta Tayi minti Biyar ta na rad’a mata wani Abu kafin Naga ta d’ago Kusan Daskarewa na kusanyi cin Karo da zukekiyar halitta,tubarakalla Masha Allah,tabbas shine kawai abunda baki na Zai iya furtawa.

 

Tabbas Tsarki Ya tabbata ga Allah s w a mak’agin Halittta,Kyakyawar matashiyar budurwa ce Kuma fa karkuga na rude a iya kyanta kawai ku Dauka Wai wata Fara ce sosai , Chocolate colour ce,fatar ta Mai matukar daukar Hankali,tabbas Chocolate colour suna Suka Tara ga asalin Inda kyan fatar ya fito bazaka kirata da Fara Kai tsaye ba Saidai Kuma kayi karya ka kirata da bak’a ,Zan iya cewa cikin Mata dubu dakyal zan ware goma masu kalar fatar,Kyan fatar ya wuce na fari haka black beauty.

 

 

Ba abunda fuskarta take sai shek’i Mai matukar daukar Hankali,tabo ko k’urji ko wani Abu da ya shafi matsalar Fata Banga ko alamun sun taba Zama a Kyakyawar fuskarta ba ,Babban abunda ke hauhawa baiwar kyanta Bai wuce Dara-daran Idanunta da Kuma Dogon siririn hancinta ,tabbas wannan biyun sune babban abunda Zaka Fara kalla yaja Hankalinka game da kyawun halittarta ta.

 

 

ta na da y’ar doguwar fuska Mai Kyakyawan shape,madaidaicin bakinta duk Yanda Zan kwatatanta muku Kyawunta tabbas bazan iya fada muku asalin gaskiyar Hakan ba ,dole Zan rage wani Abu ku dauketa a kyakyawa ta bugawa a jarida.

 

 

Doguwace siririya Bata da wani k’iba Saidai Bata da Rama Kallo Daya zaka Mata kasan Cikakkiyar gogaggiyar y’ar gayu ce ta wuce misali,sanye take cikin abaya black Tayi rolling gyalen Masha Allah sosai rigar tayi masifar yiwa Kyakyawar fatarta kyau Mai Cike da hasken annuri .

 

Ga mamakina Kuka take sai Naga wasu y’an siraran hawaye a fuskarta ta na kwabe fuska cikin siririyar muryarta Mai matukar dad’in sauraro da zak’i ta ce.

 

“Mommy Promise?Murmushi dauke Da fuskar momy ta ce”Nataba Miki Alkawari Ban Cika ba “Batasan Lokacin da ta Sanya Dariya ba wanda ya lotsar da dimple Dinta D’aya dake gefen Dama tare da fito da fararen hakoranta Tass Mai dauke da hakorin zinare da ya Kara haskasu Tayi d’an tsalle tare da Sake Rungumeta ta ce”I love you more mommy Shiyasa nake sonki da yawa”.

 

D’aya daga Cikin samarin Dake Tsaye a wajen da bazai Haura 24 years ba ya ce”Wlh Aunty ke ke sangarta Noor da yawa ji sai wata shagwaba take Kamar wata jaririya”.

 

 

Kallonshi momy Tayi ta ce”Ba ruwanka Hassan Idan ban sangarta y’ata Daya tilo ba wazan sangarta ”

 

D’ayan Mai matukar Kama dashi ya ce “Fad’a Masa dai Aunty Idan Auta Batayi sangarci ba Wazai yi Nima wlh ji nake kamar nayi kukan Dan Karatun Nan yazama dole da ba abunda zaiyi Mana nisa da batool dinmu shiyasa banso nesa dinnan da Babban Yaya yasa aka kaita ba duk ga makarantu a Nan birjik Ni America ma Naso Ta Tafi makarantar mu”.

 

 

Yawwa Hussain Kai ai Daman kai na bangarenmu ne Yanzu dai ku tayani Lallashinta Kar ta Soma gudowa “Hassan ne ya Kyalkyale da Dariya Ya ce”Andaiji Kunya Katuwa Dake Kina gudowa a university common sati biyu da zuwa”.

 

 

D’an diddira kafa Tayi a Shagwabe Ta ce “mommy did you hear him ko,Allah ya Hassan zamu b’ata”Saurin hade hannayensa biyu yayi Yana dariya yace “afuwann maman dady tuba Nake “Hussain ne ya ce “Naso Nayi rakiya to Babban Yaya Ya Kiya,Amma Kwatsam Zaki ganni”kallonshi Tayi Tana narai-narai da fuska ta ce.

 

“to Yaya ni kace Mana Kai zaka kaini , “Yana waro Ido ya ce”Ni asuwa da babban Yaya a wajen “.

 

Let’s go da Allah kinsan banson wasting time “Matashin da a kalla zai Kai 36 years dake Karasowa wajen ya fada,duk cikinsu shine kawai suke Kama da Noor dukda ba sosai ba satar Kamannin ne Daka kalli fuskarsa kasan ba Wasa a tattare dashi “Yana Karasowa wajen Ta nutsu ta ce.

 

“to Yaya “Kafin ta kalli momy Tana niyyar sake hug Dinta ya ce,”bazaki wuce ki shiga ba saina b’alla ki Banson shirme wuce mu Tafi”.

 

 

har tuntube take hadawa dashi wajen Saurin shiga mota ta na waiwayen mommy da duk jikin ta yayi sanyi ta na shiga mota ta hade Kai da gwuiwa ta na hawaye ,ta na Jin su Hassan Nayi Mata bankwana Bama ta d’ago ba Saida Taji tashin motar su Kafin ta d’ago Ta gefen Ido ta d’an hararesa,.

 

,ba b’ata lokaci suka bar Lagos Kai tsaye hanyar Abuja suka Dauka ba Wasa,gudu kawai ya ke falfalawa na tashin Hankali sunyi nisa sosai Kafin ta tsinkayi muryar sa da cewa

 

 

“Wlh Koda Wasa Kika kuskura Kika sake gudowa Sai na sauya Miki kamanni,ke yarinyace,ko boarding school kin gudu bare University ko Kunya bakyaji Katuwar wofi to wlh ki sake guduwa kiga yanda zamu Wanze dake”a natse ta Ce “to Yaya ni makarantar ce bansan kowa ba ko fa k’awa banda ita Kuma kasan bansaba missing din Gida ba .

 

 

“ya na hararenta ya ce” da wannan shegen miskilancin naki zakiyi k’awa ,dukda ba son tarkacen kawayen nake ba Amma kiyi ‘Daya Mai Hankali da nutsuwa Banda Rashin ji da kula samari dukda nasan ba d’abi’arki bace ki nutsu level one Kinga Kika shiga kiyi karatu Dan Allah kinji Kanwata”

 

 

“Insha Allah Yaya Zanyi”ta Fad’a a sanyaye .

 

maganar k’awa Kuma ga Menal nan makwabtanmu duk Nan makarantar suke kuma Suma level one suke banbancin course ne I think ke tsakaninku.

 

 

“yaaya su Menal Kuma a a a ni bansaba da su ba ” girgiza Kai ya Yi ya ce”Rashin son mutanenki ne dai kawai zakice Shi ke hanaki sabo da mutane Amma ai nasan Kuna Haduwa Dasu Gidan mamy Dukda ba zuwa kike ba shine zakice Baki Saba Dasu ba ?”.

 

 

“girgiza Kai Tayi ta na Murmushi ta ce”Allah Yaya ba haka bane ba Ina son Mutane hulda Dasu ne kawai banso”Uhm Yaya Kacewa Aunty Mamy Nayi fushi ,har Amal Nayi fushi Dasu shine har Zan Tafi ko Tazo muyi bankwana”

 

Kunfi kusa Ai bana shiga tsakaninku “tun Suna Hira har noor ta gaji Bayan taci snacks din da momy ta Shirya Mata saboda hanya a Hakan har bacci ya dauketa.

 

 

Karfe 5:30 tayi musu a birnin tarayya danma sun tsaya sunyi salla a wani gari Kai tsaye Bai zarce ko Ina ba Sai hanyar Baze University dake 2c44+7cr plot 686 jabi airport road bypass codastral zone Abuja da shigarka makarantar ma kasan Ba ta tagajan-tagajan bace harkar da Manya da Manya ce tundaga manyan motocin dake shige da fice.

 

Noor ko shiru tayi Ita Harga Allah Batason school dinnan saboda a sati biyun da tayi Ita Kadai Tasan Cikin tashin hankalin da ta yi sa sosai ta lula Duniyar kogin tunani ta ya ma zata Fara Rayuwar school d’innan ,Taya zata iya ,tabbas Babban Yaya da yasan Halin da take Ciki da bazai nisanta ta da Gida ba ,rayuwar da ta taso Cikinta tun Bata San Ita wacece ba….. ringing din Wayarta ne ya katse Mata tunaninta bayan Babban Yaya yayi parking firgita tayi Tare da lalubo wayar Tana Kara wayar a kunne ta tsinkayi muryar momy a sanyaye da cewa.

 

“Tun d’azu nake ta trying kiranki bata shiga Auta Fatan kunje lafiya”

 

gaba Daya jikinta yayi week Jin muryar momy kamar Zatayi Kuka ta ce”yanzu muka shigo makarantar momy”.

 

ta na jin yanda ta sauke ajiyar zuciya dan ta Cikin wayar ma ta Gane Tana Cikin Halin damuwa”okay Idan kin huta zamuyi waya goodbye ki kulamun da Kanki “kittt ta kashe wayar.

 

Nasihohi sosai Babban yaya yayi mata masu shiga jiki Kafin ya tambayeta Tana bukatar wani Abu Tace a a.

Uwar Sayayyar da aka Mata ya Sanya aka kwashe aka shigar mata Dasu hostel Kafin ya Kara Mata transfer kudi masu yawa saboda ko zata bukaci wani Abun Zatayi Kuka da zai Tafi ya hanata Yana hade fuska Tayi Saurin goge hawayenta ta ce”

 

“Yaya Ina zaka kwana yanzu dare yayi karka juya “Murmushi yayi ya ce “karki damu Hotel zanje na kwana Da asuba Zan juya “Yaya bazaka kwana Gidan su Aunty mamy ba “murmushi yayi ya ce “Gidan surukan nawa Zan kwana”.

 

To Yaya ga gidan abokin dady Abba Kabir Da ba chan kake kwana ba Kuma Shima dady duk zuwan da zaiyi Yana sauka gidansa Shima kaga gidanmu yake sauka nidai kaje chan ka kwana Banason hotel”

 

murmushi yayi ya dafa kan autar kanwar tasu da suke matukar ji da ita ya ce”Auta…Bai karasa maganar da yake son Fad’a ba sakamakon ringing din da wayarsa ta Fara Ganin Mai Kiran Ne ya sanyasa murmusawa tare da Saurin picking cike da barkwanci yace afuwan madam Karki Dauka an dauke Miki miji mun Isa lafiya”

 

Suna Gama gaisawa ya bawa Noor Sukayi waya Kafin Suyi bankwana .

 

kamar wacce kwai ya Fashewa haka ta nufi hostel dinsu Zuciyarta chunkushe Da tunani Ja tayi ta tsaya bayan shigarta room din Ganin Wata Hamshakiya D’are Kan Gadonta Gabanta Cike da Kayan marmari yayinda waya ke hannunta ta na ci ta na Charting Hankalinta kwance Ja tayi ta tsaya ta na kare Mata kallo

 

” haka zance”kalli gado na Ne Ki koma Naki”Koko zance Mata ne”ki tasar mun a waje.?

 

“A ranta take ta ayyanawa Tama rasa me zatace mata Saboda ita Daman chan haka take ko primary da secondry da tayi bata iya Fad’a ba ko kadan,ko da kuwa janta Akayi Bata kulawa Saboda masifar miskilancin da Allah yayi Mata Amma ba kowa KE Gane ta na da tsoro ba Wanda shine ya kara hauhawa miskilancin nata y’an gidansu Kadai ta Saba dasu Kawai take doguwar magana Amma bayan su ko cousins Dinta Fama suke da halinta na shegen miskilanci Wanda wasu ke Dauka hada rainin wayau da yayi Mata yawa Hakan yaja mata Rashin Iya hulda da Mutane.

 

 

gyaran muryar da tayi ne ya sanyata Dagowa karaf Idonta ya sauka a na noor dake tsaye kallonta ta dingayi Batace da ita Komai ba Itama Batace Mata Komai ba Ganin Bata da Shirin Mata magana ne ya sanyata cigaba Da harkar Gabanta Amma ta K’asar Ido take kallon Noor din Saida taja numfashi Kafin Cikin siririyar muryarta Mai Cike da gayu ta ce.

 

“Hey”Ta na latsa wayar ta mayar mata da hey”cikin karfin Hali ta ce”please bed di na ne Kika kwanta na dawo inason zama”Dagowa tayi ta kalleta kallo Daya tayi Mata taga shegen jiji dakan da gareta abunda ta Dauka Keenan harara ta b”alla mata ta ce”

 

da yake kwai kika dasa a bed din da ya zama naki ko dashi Kikazo Daga Gidanku,to Shi nayi niyyar Zama Ki kwashe Sauran kayanki ki koma wancen spare side din Ni wannan na zaba”But ranar da kikazo you don’t see my clothes there alamun da mutum a gun?ta Fada Cikin nutsuwa

 

Tana sake balla Mata harara ta ce”zuwa zakiyi ki Ciccibeni ki Daukeni Zan tabbatar da eh gadonki ne”.

 

 

“Amma Iman kinsan Baki da Gaskiya Meyasa kinsan Sarai wajenta ne zakija rigima in ba so kike ayi ba ,tun farko dakin Nan Kafin ma kizo ita kadai ce tayi Tafiya da kwana biyu kema kikazo Kuma ai tunda kikaga kayanta a lockers da Sauran tarkacenta kinsan da mutum a wajen KE na lura tun zuwanki neman fitina Ne dake”.

 

cike da jaraba ta hayayyako mata ta ce”Ke Kuma azare ba a Zara ba shiga likkafani sukuf waya kasa dake ballantana ki Dauka?da ke ake bana son shishiga da iyayi Ina ruwanki ko gadonki nahau ko room dinki naje munafuka ubanwa ma ya kawoki Nan din tukun gidan ubanwa ma Kika San Suna na bada izini na ba algunguma Ni tun kallon farko da na Miki na tsaneki saboda na lura munafuka ce ke uwar shshigi Kawai nonsense.

 

 

,Cikin sauri Noor ta juya Kallonta Ga Islam da har ta iso room din sun Fara Fad’a da iman din Ta CE “Dan Allah kiyi shiru shikenan Ni naji Zan zauna a Chan din Dan Allah karkuyi rigima please “Islam ta ce”Bata Isa ba wlh saita tasar Maki waje ,ko daukarta tsoronta ake da zatawa Mutane iskanci”.

 

Menah da suke tare da Islam ta ce “To ke Wai kike Zazzakewa Nan Islam Ina ruwanki yarinyar da ko magana batawa Mutane har Zaki wani zake ayi Fad’a a kanta”.

 

 

Islam Tace “Ke Nifa kinsani ban Daukar raini,yarinyar Nan tunda tazo take neman rainawa Mutane wayau,Waye ubanta a Nigeria?iman ta Mike ta ce”uban da ya haifi uban ki ne uba na Dan uwarki…..zagi ya kaure tsakaninsu Fad’a Wanda dakyal Noor kamar tayi Kuka ta janye Islam Tana ta Bata hakuri Dakyal suka samu Sukayi shiru.

 

Noor da Batason tashin Hankali Dauke kayanta tayi ta mayar dayan Side din daman mutum biyu ne ko wani room sai Mai d’ai-d’ai sai yanzu take ji Daman one person ta zab’a kamar Yanda babban Yaya yaso to saboda ko motsin mutum Taji da Dadi ya Sanya ta zabi mai two persons din dukda ba abunda babu na more rayuwa banbancin wancen kad’an Ne Amma Kuma indai taga zamansu da wacce aka Kira iman bazaiyu ba Ta yanke shawarar Komawa Mai one person Hankalinta kwance.tana wannan tunanin harta kwashe kayanta tas.

 

 

Ta kasar Ido iman take kallonta harga Allah Tasan Bata kyauta ba,Amma Daukar da tayiwa yarinyar ne kamar Zatayi rainin wayau da jiji dakai Yasa tayi mata haka a tunaninta zata biyeta Saikuma taga sabanin haka Kyakyawar yarinya kamar wannan Amma Bata iya Fad’a ba “?.

 

dukda Tasan mafi yawanci Mutane Suna kiranta da kyakyawa saboda ko cikin kawayenta sunaji da kyanta saboda farinta da dirin jikinta dake Daukar Hankalin mutane har tanaji tafi kowa Amma ga mamakinta Ita kanta yau ta shaida da wacce ta fita kyau,Kuma Gashi tasan ta fita haske Uwa uba Shape din jiki a tunaninta farinta ya isheta komai a kyau sai Gashi yau taga wacce Bata kaita ko rabinta haskeba Amma tafi ta kyau .

 

 

haka dai tayi ta tunani barkatai yayinda Noor Tana Gama watsa ruwa Ta kwanta Abunta Harta Fara bacci Kiran momy ya shigo Wayarta Saidai Jin Tana gigin bacci ya Sanya momy rabuwa da ita a cewarta ta kwanta ta huta sun shawo gajiya,Kafin wani wahalallen bacci ya kwasheta chan cikin bacci taji murdawar maranta tun Tana daukar Abun wasa harta farka.

 

Rumtse idonta tayi sosai tanaji bakon yanayin na sake shigarta tuni ta Fara hawaye tare da lalubo Wayarta kallon iman tayi dake sharar baccinta number momy ta dannawa Kira ringing biyu ta Dauka Tana Shirin Fashewa da Kuka ta ce”mommy yazanyi da rayuwata, I couldn’t sleep wlh cikina ciwo momy help me please ji nake kamar Zan mutu Daman nafada Miki Bazan iya zaman school dinnanba……✍️

 

*Ga Masu bukatar a tallata Musu hajarsu su tuntubeni Akan number wayata 07026166536*

 

*Sabon salo,sabon sauyi,sabon darasi,sabuwar Makaranta Mai dauke da malumma kala-kala da mabanbanta darussa ,lissafi da amsarsa,fayyacewa Cikin abunda ya shige Mana duhu,Cikin hikimar iya salon rubutu,,sabon salon soyayya Mai tsayawa a Zuciya,Nishad’i ta wani,fannin tausayi ta wani fannin kuma ban Haushi,Sabon Littafi Mai dogon zango,Doguwar tafiya da ba asan Lokacin sauka ba,,Kudai Kawai ku kasance da Ni miss Hajo Dan Jin wannan Karin da wani salon nazo, ? Comment tare da sharhi Shi zai tabbatarmun da shaidar amsuwar Littafin a Cikin zukatanku masoyan Asali*

 

*idan kin karanta ki Daure kiyi sharing Sauran groups fisabilillah*

 

 

 

_*Miss Hajo ce*_

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment