Littafan Hausa Novels

Rayuwata Hausa Novels Complete

Written by Hausa_Novels

Rayuwata Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

RAYUWATA

 

Story and Writing By Fatima Ahmad Abdullahi

(Queen Zarah)

 

Page 1&2

Bismillahir rahmanir raheem

 

1-2

 

Kyakyawar yarinyace shekarunta bazata wuce 9yrs ba acikin uniform, farar Riga da red skirt sai necktie a samar rigar, kyawun dana ga gashin kanta yasha kananun kalba yasha normal beads da iron bead, kallon farko zakai mata zakaga irin butter din nan ce lolz.

 

 

“Zahra..zahra….”, wata budurwar yarinyar ke maimaitawa daga cikin wani aji, daga sama anrubuta primary 5, kyakyawar yarinyace zaune cikin ajin wanda aka kira da afrah looking sad dagani akwai abunda ke damunta lunching box a gabanta.

List of Hausa Novels Docs PDF and Text

“Zahra tashi muje muci abinci duk an fita break sai ke daya a class?”

 

Tsawa zahra tad’a gawa Juwairiyya tare da cewa “Kifita hanyata nagaya maki Juwairiyya kike kowa?”…

“Ni natsani shishigi nan ina ruwanki in banfito break din bah”.

 

 

Sororo juwairiyya ta yi tana mamakin masifa irin na miskilar na Zahra wanda shekarunsu zaizo daya.

 

Hakan yayi daidai da shigowar ‘yan ajin da gudu unknowingly su kayi ball da lunch box dinta, take d’umamen abincinta ya zube akasa ya na wani turirin tsamin lalacewa hakan yasa Zahra fashewa da kuka.

 

 

Ganin abunda ya faru da sauri ‘yan class din yasa kowa nik’e hancishi suna “Uhmmmm uhmmmm it smells odour” suka fice da sauri suna dariya cikeda k’yank’yami.

 

Itako juwairiyya tausayi tabata ta duka tareda kamota tana faman maimaita mata sorry

 

Dakko nata food flask din ta yi ta mik’a mata tana kara lallashinta har saida taga tasaki ranta data ga haka sannan tafita ta barta.

 

Juwairiyya school canteen ta nufa ta sai short cake da drinks.

 

 

Closing hour

Wani dan saurayi ne da bazai wuce 17yrs ba naga ya nufo primary section tafe yake hannunsa dauke da technical board a hannu da sauran tarkacen colouring

 

Tafe yake yana faman hura hanci adole ga senior ‘yan SS2.

 

Gab da zai shiga get din primary section din Zahra nafitowa ta ce “Gud afternoon senior

Kauda kai ya yi kamar baiji mai taceba ya yi wucewar sa abinshi.

 

Juwairiyya ya hango tunda ga nesa tana gudu tana haki…

 

“Eyyah sorry my boo amma na new aunty ne ta tsayardamu ta dudduba book d’inmu shi yasa banfito ba, but kai na bisa wuya”, ta d’an dukar dakai tana murmushi.

 

Dariya khalil yayi tareda shafa kanta never mind baby mu tafi driver na jiranmu

 

Amsan tarkacen colouring d’in tayi tareda gyara zaman schoolbag dinta a baya.

 

Basket d’inta yakar ba suka jera har mota gwanin ban sha’awa.

 

 

Gab da zasu shiga motarne ta hangi Zahra na tafiya reluctantly sauri ta yi takamo ta tarik’o hannunta tare da fadin “My kawa zo mu rage maki hanya.

 

Buge hannunta ta yi wanda ya yi daidai da zuwan Khalili wurin, janye ya yi tare da kuma kallon Zahra ya ce karki kuma.

 

 

Ya rik’o hannun Juwairiyya suka shiga mota, driver yaja su suka fara tafiya, bayan sun fara tafiya ne Juwairiyya ta juyo ta kali Khalil tace “My boo yarinyar nan tana bani tausayi gata da k’okari sosai amman dai akwai fada ga miskilanci”, ta fada tana murmushi.

 

Tankata beyi ba

Sake cewa ta yi “My boo kadaina kyaranta don Allah”, nan ta kwashe duk abunda yafaru dazu a class during break tafadamai.

 

Shiru ya yi har tacire ran zai mata magana sannan ya ce baza kigane bane kwata-kwata bana son alak’arku kawai sai inajin kamar a jikina wani abu zai iya faruwa dake sanadiyyarta”.

 

…interrupting din shi tayi tare dacewa “kai yayah don bakwa jituwa bai kamata kai mata mummunar fasara ba haka haba..haba my boo”.

 

Mtsseww tsaki yaja ya ce “Toh ai shi kenan sai ki ta yi”, fushi ya yi har sukaje gida ba wanda yasakema d’an uwansa magana.

 

Suna isa gida ko gama parking driver baiyi ba tafita da sauri ta yi cikin gida ganin motar Mommy.

 

“Mamee…Mamee…Mamee kifito ki min oyoyo kuma ni kadai zaki mawa banda yaya”.

 

Mami ne tafito da shirin fita da labcoat a hannunta da alamu dai likita ce rungumeta ta yi tare da manna mata feck a goshinta.

 

Aje duk wani kayan hannunta ta yi tareda dagata sama tana wulwulata.

“Oyoyo my queen Allah nagode maka daka dawomun da baby na lafiya”.

 

Leken fuskanshi tayi tana masa gwalo

Turb’ine fuska yayi tare da cewa “Mamee ni fah?”.

 

Eyyah son kai din kasan kaina wajena ne, kawai dai d’an kara nake mata kar ace sankai nayi amma wazai ki babansa

Ya kama uwarwasu”, lolz

 

Hada su duka ta yi ta rungume su tana dariya mutsu mustun sauka Juwairiyya takamayi.

 

“Ammm let’s cut d story short

Baranaje hospital inada emergency convention in kunyi wanka da sallah ga Mary tabaku abinci”.

 

Adawo lafiya sukai mata tareda saurin shiga cikin itakuma ta tafi cike da kaunar ‘ya’yanta.

 

Dr. Hafisat kenan Amarya kuma uwargida a wajen Alhaji Mustapha Yusuf Gwadar……

 

Sai mun hadu a next page domin jin wanene su kuma wacece Zahra.

My first novel pls show me love by commenting

RAYUWATA

 

Story and Writing By Fatima Ahmad Abdullahi

(Queen Zarah)

Story and Writing By Fatima Ahmad Abdullahi

(Queen Zarah)

 

Page 3&4

Kofar wani gida ne mai dauke da dan madaidaicin shagon shagon siyar da abinci akai mai rumfa daga kofar gidan

Tebur ne dauke da manyan kuloli da basket na robobo da sauran tarkacen kwanonin abinci

Daga cikin shagon babban freezer ne shaqe da ruwan leda da en tsirarun lemona

 

 

Mama meenal ce tsugune gaban murhun tana faman fifitar itace dagani wutan nabata wuya gefe bencinane da costomernta ke zama kafin a sallame su

 

 

Zahra ce ta wuce ba tareda takalli matar ba tayi cikin gidan…

 

Adan razane ta juyo tareda ganin giftawar zahra saurin bin bayanta tayi

 

 

Daughtee kin dawo shiru tai mata ba tareda tace komai

Oh god dear akwai matsalane

 

Babu tafada tareda shigewa daki tana kokarin canja kaya

 

 

Share zufa maman meenal Tate tareda komawa wajen saida abincinta

 

Zahra koda tafito plate ta dauka taje ta Debi shinkafa da miya da kifi takoma daga cikin shagon tadauki ruwan Leda takoma cikin gida

 

 

Fitowar kamal daga backyard din gidan yayi daidai da zamanta a kan kujera yar tsiguno

Fitowarsa keda wuya yayi ball da plate din yace da ita kingaida mama da gida kuwa saboda wannan dabban halin naki baxai canjaba tunda naji muryarta tana maki magana amma banji respond dinki ba

 

Yaya kamalwai meya haka ni bana shiga rayuwar mutane amma sai an shiga naka

 

Buge bakinta yayi zai kaimata duka tayi wuf tayi daki tare da banko kofa tana kuka

 

 

Kamal yaro ne da bazai wuce shekaru 17yrs ba makarantarsu daya zahra sai fai shi yana cikin wa enda aka ba scholarship ynxu haka yana ss2 yana da kirki inkasan yanda zaka zauna dashi amma yanada zafi akan mahaifiyarsa,indai kanaso kaga bacin ranshi to tabi maman meenal

 

 

…………………………………

 

 

 

Mamee kinga mug din da yanzu zamuna break dasu…kai wow nidai nawa zanen yafita tas kamar fuska na aka Ciro aka manna

 

Juwairiyya ne suka Hada ido da abba tare da daga ma juna gira suna dan murmushi

 

 

Abba warware takardan sauran mug din uku yayi sai ga zanen fuskar abba, khalil saina juwairiyya

 

 

Kai…kai…wannan Zane ya kwashene son idan banyi dagaske ba xuwa zakayi lace gyara ban waje manyan nan Baku iyah komai ba

 

 

Murmushi khali yayi na farin cikin an yabi zanensa

 

 

Butt juwairiyya tamiqe cike da fushi rike da mug mai dauke da hotonta a jiki

 

Mamee, abba Ku kalli haka take ta juyi tayi tare da rike kugu kaga zindiriyar yarinya, fara,doguwa, yar dumaduma,ga dimple,ga wushirya,ga pink lips ga..ga..ga… Haba

 

Dariya suka kwashe dashi your work is automatica…. yayi mata jinjina da hannu

 

 

Angama ranki ya Dade canji dole nagode da gyara khalil yafada yana wani qanqan dakai kamar mutumin kirki

 

 

Dariya mamee da abba suka sakeyi harda tafawa kai wannan yara u’re so dramatic

 

 

Turbire fuska tayi tana dan dukan kafanta a kasa cikin sigan shagwaba abba nifa gaskiya wannan bata kama dani ba kamar wata budurwarsa

 

 

Ke ,ke stop that banson raini wata budurwar

 

 

Ya daka mata tsawa shout up

 

Binta yayi dagudu tayi dakinta tarufo kofa tana masa gwalo

 

Kano state

 

Yau masarautar cike take da murna sakamakon dawowarda prince mujahid da daya tilo a wajen sarki Abdullah da gimbiya maimuna da dawowar shi daga turai bayan kwashe shekaru shidda daya yi baya kasar tun bayan kammala primary shi,yake tare da uncle din shi kabir da matarsa da yayansu acan

So,bayan kammala secondary din shine yazo masu Hutu kafin admission tafita

 

 

Wata yar dattijuwa nagani dauke da burner na turaren wuta bayan bayi biyar ne dauke da wasu en kewayayyun tasoshi masu dan fadi a like lif da fararen kyalle

 

 

Wani sassa naga sun nufa dayasha kawan furanni

Daga bakin wani tafkeken falone naga tadan tsaya ta rankwafa tare da Dan shiga daga cikin

Manyan Royal cushions ne set 2 a falon daga gefe wasu shimfidar daddumai Nagani jajaye da zanan golden ajiki sai manyan Tim Tim a gefe da gefe

Hatta labulayen da ke kewaye da parlour duk red da golden ne haskene tantar duk da hasken gari hasken fitlun na dabanne hakan yasa nadan daga kina sama wani rungujejiyar fitila naga ni daga sama yana wilwula yana canja kaloli daga red,blues,green and white

Sanyin a.c har yaso yayi yawa a gurin

 

barka da hutawa gimbiya maimuna ,uwar yarima mujahid bakin turai yaro qarami me kwalwar manya da hangen nesa alfaharin masarautar na kano ta dabo tunbim giwa tattalin talakawanta

Tadan rankwafa tareda Jan fasali

 

Wannan babatun surutan danaga dattijuwar nan nayi shiya dawo dani daga kalle kallen da nake

 

 

 

Wata hamshakiyar matane zaune kan shimfidun daddumannan walwali take kota INA sakamakon adon gwalagwalai dataji kota ina

En mata biyu ne a gefe da gefenta suna mata firfita in a slow motion

 

 

Gyada kai Wanda aka kirada gimbiya maimuna tayi tare da furta

Barka dai jakadiya qaraso daga cikin

 

 

Ranki yadade angama gyara bangaren yarima isowarshi kawai mike jira

 

OK kushiga da sauran kayan

Angama ranki yadade tareda dan rusunawa kafin su tashi su tafi

 

Part din suka kara gyarawa tare da turare dakin da turaren wutar hannun jakadiya tareda feshe koina da room Freshen

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment