Littafan Hausa Novels

Rayuwar Hibba Hausa Novel Complete

Yadda Ake Rikita Maigida Yayin Kwanciya
Written by Hausa_Novels

Rayuwar Hibba Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

RAYUWAR HABIBAH

 

 

 

 

 

_BY Fatima Zahra_

 

 

 

_Shinfid’a_

_Wannan shine karo na farko dana fara rubutun labari ina_ _rok’on Allah ya bani iko da damar rubuta abinda zai amfani al’ummar musulmi ya kiyaye_ _hannuna daga rubuta abinda ba shine ba Allahumma Ameen_

 

 

Page 1)

 

 

Bismillahir Rahmanir Rahim.

 

Y’arinya ce y’ar kimanin shekaru 18yrs zaune kan kujera yar tsugunno ta bani baya wannan dalilin ne yasa ban samu damar ganin fuskarta ba a gaban murhu girki takeyi amma idanunta na zubar da hawaye sakamakon hayak’in itacen daga bayanta taji an kirata da sauri ta mik e tana goge hawayen ta juyo sai sannan na samu damar ganin fuskarta

   Mahaifina ne Hausa Novel Complete

“Kyakkyawace Masha Allah bak’a a kalar fata irin bi’kin da akeso mai k’yalli tana da kyawawan fafaren idanu wanda suke madai-daita sai cikakken gashin gira da zararan gashin ido tanada hanci dogo madai-daici sai d’an bakinta madai-daici la’b’banta irin wanda yake tattarewar nan gashi brown dashi gwanin ban sha’awa tanada gashi dai-dai wa dai-ta bak’ik’irin mai laushi wanda ya sauko har dokin wuyanta wanda yake dogo dashi bata da wani k’ibar azo a gani amma ba ramamma bace tana da cikar k’irji dai-dai misali haka ma k:ugunta sai dogayen yatsun k,afar ta da hannu masu d’auke da farin farce komai dai Masha Allah.

 

“Amsawa tayi da wata zazzak’ar murya mai sanyin dad’i “Na’am Inna”

 

“Sannan ta nufi cikin d’akin nasu lokacin na samu damar k’arewa cikin madai-daicin gidan nasu kallo tsakar gidane mai fad’i amma ba sosai d’akuna uku na gani daga gefe guda wanda suke a jere sai kuma wasu dakuna biyu daga gefe daf da k’ofar fita daga cikin gidan daga gefe can kuma rijiyace rufe gefen arewa kuma nan na madafa {kitchen} daga gefen kitchen d’in ne kuma murhu ke ajiye can kudu daga cikin gidan kuma band’aki ne da suke jere guda biyu na wanda dana bahaya cikin gidan share yake tsaf ba alamar datti dagani mamallaka gidan sunada tsafta sosai.

 

“Bakinta d’auke da sallama ta shiga cikin d’akin Innar nasu tayi wanda yake ciki da falo. Falon na k’arewa kallo wanda yake d’auke da korayen labulaye masu haske wato {Light green} sai set d’in kujera masu kalar kore suma mai haske da mai duhu daga gefe TV ce saman tebur sai DECODER da CD dake kasan tebur {table} d’in zama tayi kan two siter tace “Inna gani” Kyakkayawar matar data kira da Inna ta d’ago wanda kallon farko idan ka mata koda bakasan matashiyar yarinyar dake zaune gabanta ba zakasan mahaifiyar tace saboda kamar da suke da juna sai dai ita tanada hasken fata..

 

“Kallonta tayi tace y’ar albarka baki gama girkin bane? ga lokacin makaranta na k’aratowa kar kiyi latti a dakeki, d’ago idanunta da sukayi d’an ja tayi saboda hayakin daya sata hawaye”

 

“Tace ya kusa k’arasawa Inna yanzu ma wanka zan shiga nasan kafin na fito ya karasa”

“Inna tace toh maza kije karki makara”

 

Mik’ewa tayi ta fita daga d’akin d’akin dake kusa dana Inna ta shiga d’akine madai-daici mai d’auke da labule ruwan toka sai madai-daiciyar katifa dake shinfide k’asa saman carfet wanda yake ruwan toka shima mai d’auke da zanen flower bak’i gefe akwatin kayan sawanta sai jikin bangon d’akin inda naga jakunkuna guda biyu na baya dana ratayawa wanda da alama na boko da Islamiyya daga bayan k’ofar d’akin kuma jikin bango shoe rack ne irin na bangon nan tubewa tayi a gurguje ta d’aura zani fitowa tayi ta d’auki bokiti ruwa ta juye taje bakin rijiya ta surka sannan ta nufi band’aki a gurguje tayi wankan ta fito..!

 

“D’akinta ta nufa zama tayi gefen katifarta ta janyo jakan kayan shafanta wani k’aramin towel ta d’auko ta goge jikinta ta shafa mai sai man baki a la’b’banta komai cikin sauri takeyinsa shiryawa tayi cikin kayan makarantarta wanda suke light purple wando da hijab sai farar riga bakar safa tasa a kafarta jakarta ta d’auko ta d’aura farin d’ankwali ta d’auki niqab da hijab hadi da jakarta janyo k’ofar d’akin nata tayi ta nufi d’akin Innarta da sallamarta ta ajiye kayan kan kujera ta fito ta nufi wajen girkin nata saukewa tayi dan ya gama takai tukunyar kitchen faranti da d’auka ta zuba musu ita da Innarta tasa cokula biyu ruwa ta d’ebo cikin jug ta nufi d’akin Innar..

 

Ajiye farantin tayi nan tsakiyar d’akin kusa da Inna zama tayi itama suka faracin abincin suna kammalawa ta mi’ke ta kwashe kayan ta nufi kitchen ta ajiye dawowa tayi ta saka hijab d’inta ta d’aura niqab d’in ta d’auki jakarta.

 

“Tace Inna saina dawo”

 

“Inna tace toh y’ar albarka adawo lafiya Allah ya tsareki” da Ameen Inna ta amsa sannan ta fita…..

 

 

 

By

FATIMA ZAHRA….

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment