Littafan Hausa Novels

Ramin Mugunta Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Ramin Mugunta Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

*RAMIN MUGUNTA*

 

By

Beebah Aminu

08108062092

 

📚Elegant online writer’s📚

 

1_2

 

 

“Wallahi ka ji na rantse ma ka sai ta yi surfen nan, kanta farau samun ciki ko ko ita y’ar gwal ce, su dije ba mutane ba ne sai ita y’ar so,ka fita idona hashimu tun ka fin in sassab’a ma”. Ce war Iyah tana furzo dabzar goron bakinta.

Mijinki Mijina ne Hausa Novel Complete

“Haba Iyah ,ko dan tsohon cikin,jikin mairo kun tausaya mata. Naga dijen da ki ke fada ba ta taimakon ki da ko mai,ki yi hakuri in ta ho maki da furar ba sai ta daka ba.

Innalilahi wa’inna ilaihi raji’un,yau ni hashimu ke fada ma, magana kan wannan lalatattar matar, ka za b’ata sama da uwar da ta haifeka” .ka dai ji kunya,kuma wllh sai ta yi da kannan ko haihuwa za ta yi, yanzu . ta k`a rashe maganar, tana b’allawa mairo harara.

 

“Allah ya ba ki hakuri Iyah,ni na ta fi kasuwa,sai na dawo”

.

Juyawa ya yi kalli mairo, “ki yi hakuri kiyi da kan, sai na dawo hashimu, ya fad’a ya na kallon mairo da ke ta daka.

“Allah ya tsare,a dawo lafiya, mairo tace masa .juyawa ya yi,ya nufi hanyar fita gidan ya na amsawa da ” Ameen “cikin zuciyarsa.

Iyah d’aki ta nufa tana ki yi saurin gama da kan nan tun rana ba, ta ida zafi ba. Ka da wani ciwon,ya kama ki, a ce ni ce.

 

To kàwai mairo ta ce, suka had’a ido da dije,wa tsa mata harara ta yi,”munafuka” dije ta ce ta na shi ga d’aki.

 

Mairo ba ta bi, ta kantaba ta ci gaba da dakanta, bayanta ke ciwo,da kugunta, amma haka ta ke ta da kan, ga zafin rana da ta ke she.

 

Sai da ta gama da kan furar,ta k’arb’a sannan ta nufi d’akin Iyah, da dawon; ga shi Iyah na gama.mairo ta fad’a.

 

“Ni zan da ma furar, ki ke nufi ko me?!.Mairo! Ki fita idona. Allah ki bar ga nin cikin nan, zan sassab’a maki, ka manni, wa wuya kawai wato kinga kin samu ciki, sai rawar kai ki ke ma mutane ko? Zan yi maganinki, marar kunya.

“Ki yi hakuri iyah ” mairo ta fad’a ta na juyawa da nufin ta je ta dama furar……,

“Ina Kuma za ki ,iyah ta fad’a….zan damo maki ne .

A’a bani nan, salan ki je ki sa abinda zan kasa shan furar,ba ni in dama da kaina,iyah ta fizgo furar daga hannun mairo, wuce wa mairo ta yi cikin rashin jin dadi.

 

****

D’aki mairo ta nufa saboda ciwon da ta ke ji, kwanciya ta yi ko ta samu bacci ya dauke ta, ko ta samu nutsuwa.

 

Cikin barci mairo ta ji wani irin ciwon mara,ko da ta tashi, wani abu ta ji yana bin k’afadunta,da gudu,k’ara ta kwalla wanda ya jawo hankalin mutane Gidan…….✍️✍️✍️✍️✍️

 

 

 

 

Commands

And

Share

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment