Littafan Hausa Novels

Rai da Ruhi Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Rai da Ruhi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

RAI DA RUHI

 

Page 1

 

The writers of

 

Zuciya

Kangin bauta

Aure biyu

Amanata

Duniyar aljanu

Sarautar zalinci

Dakin duhu

Kogon tsafi

 

And Rai da RUHI

 

Zaune take a bakin kofa, sai faman tazar kai take a yayin da Kuma wani bak’in hadari ya taso ganga ganga,sama sai walkiya take alamu dai ruwa yana daf da saukowa.

 

Daga cikin daki aka fara magana “yanzu sabo da Allah ihsan ke bakya Jin magana ko?

Wacce aka kira da ihsan ce ta mike tsaye tana karkade jikinta tare da fadawa cikin dakin ta Sami gefan kujera ta zauna sannan ta kalli mahaifiyar tata wacce ranta yake a bace tace”mama babu komai fa,kafin na fara tsifar sai da nayi addua Kuma ma ni wallahi ban yarda wai a bakin kofa akwai wasu aljanu ba kawai fa canfi ne na mutane.

Cikin hasala maman ta kalle ta rai a b’ace tace “ke dallah Shashasha zaman bakin kofar ne canfi?ah lallai baki da hankali to wannan maganar haka take babu inda aljanu suke zama sama da bakin k’ofa Amma ke lalacewar taki da isa har tsifar Kai kika hau kina yi a wannan daminar ,Allah ya kyauta Amma kinyi na farko kinyi na karshe .

Mikewa ihsan din tayi tana dan dariya sannan tace wai aljanu Kai Allah ya kyauta mama kenan ita har yau bata manta da zancen su na mutanan da ba.

Bin bayanta da kallo mama tai sannan tace” Allah ya shirya ki wallahi ihsan.

A dai dai lokacin aka fara kwalla Kiran sallah inda Kuma hadarin da ya had’o Shima yake washe wa a hankali.

Mashahuri Hausa Novels Complete

Bayan Ihsan ta dauro alwala tazo tai sallah sannan ta dau wayarta kirar Infinix ta kunna data Dan ganin meyake tafiya a duniya.

WhatsApp ta leka inda ta shiga cikin group dinsu na makarnta bayan sunyi candy aka bude shi Dan sada zumunci.

 

“Hey yan group yane? Kalmar da ihsan ta fara turawa kenan.

 

Kusan minti biyu bbu wanda yay magana, har ta fara wani typing din sai Kuma ta tsaya ganin wata number tana typing.

Samira ce ta tura “ihsan manyan gari kina online ashe?

“Kwarai da gaske ihsan ta bata Amma tare da tambayar ta ya jikin naki saboda kwana ki taji ance bata da lafiya.

“Alhamdullah nasamu sauki wallahi Amma tafiyar tawa ce yanzu sai a hankali Samira ta Kara turawa.

Dan tura emoji tayi na zare Ido sannan ta rubuta a kasan emojis din “menene ya sameki haka har ya taba miki kafa?

 

“Kedai bari wallahi ihsan wannan mutanan namu ne suka rike kafar ai da har da hannu Amma yanzu hannun da sauki sai dai iya kafa kawai .

Emoji ihasan ta Kuma sawa wannan wanda ya rike hab’ar Sannan ta Kuma rubutu wa kasa “wanne mutanan kenan?

Da mamaki Samira ta Kuma tura mata”aljanu fa nake nufi.

 

“Mtws abinda ihsan ta tura kenan sannan tabar online tana mitar “karyar banza wai aljanu nabi aljanu da gudu ba wando na tsani irin wannan abun mutane Basu da aiki sai canfin masifa aljanun uwar wa Kai gaskiya zamu Sha kallo a lahira.

 

United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

 

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan

 

 

 

RAI DA RUHI

 

page 2

 

Na Maryam dangi

 

The writers of

 

Zuciya

Kangin bauta

Amanata

Aure biyu

Wazan aura

Duniyar aljanu

Sarautar zalinci

Dakin duhu

Kogon tsafi

 

And rai da ruhi

 

 

Gaba daya ta kashe datar ta mike tai sallah ishai sannan ta kwanta, ta kunna wani film da ta turo a wayarta.

Sai kusan karfe Sha daya sannan ta ajiye wayar ta kwanta bacci.

 

Misalin karfe biyar na asuba ta barka tai sallah asuba sai dai Kuma ta tashi da ciwon Kai sosai wanda da kyar take iya daga idanunta.

A daddafe ta mike ta shiga dakin mahaifinta,a kan sallaya ta sameta itama ta Idar da sallah.

Tana rintse Ido ta shiga dakin bayan ta gaisheta ta kalleta tana dan cije baki tace”mama kina da paracetamol?wallahi kaina mugun ciwo yake min.

 

“To subhanallahi ciwon Kai Kuma?wallahi babu magani a wajena,kiyi hakuri gari ya waye sai a karbo miki a chemist ki kwanta wata Kila kan yay sauki, sannu kinji maman ta fada tana duban fuskarta.

 

Mik’ewa tai zata fita wata hajijiya ce da ta d’ebeta ta tawo luuu zata fad’i da sauri mama ta mike ta rukota tana cewa” ‘subhanallahi zauna anan jiri kike ne?

Dan d’aga Kai tai tana cewa”wallahi jiri ne yake diba ba dishi dishi nake gani ,inaga asibiti zanje gobe ai min test na maleria itace kadai take saka ciwon kai ta karasa maganar tana kwanciya a gefan gadon mama.

 

Misalin karfe bakwai da rabi suka shirya ita da mama domin tafiya asibiti.

 

Murtala sukaje inda dr ya rubuta musu test kala biyu maleria da typot sannan yadau BP ta sai dai bbu abinda yayi normal jininta baiyi low ba baiyi high ba.

 

Bayan sun dawo daga test din Dr ya karbi result duba wa yayi inda yaga komai normal babu maleria babu typot magani ya rubuta musu sannan yayi musu bayani kawai dai ciwon Kai ne bbu komai,

Tun kafin suje gida ihsan tasha magani.

 

Suna tsaye kan titi sun rasa abin hawa kusan minti goma da futowarsu daga asibitin Amma shuru kakeji.

 

Wata dalleliyar mota ce ta zo daf dasu tai parking ,inda na ciki ya bude murbin motar ya futo.

Wajen su mama ya zagayo fari ne sosai tamkar bature gashi dogo gashin kansa ma na turawa ne fuskarsa wani irin kyau ya bayyana sosai jikinsa kananun kaya ne shigar turawa dai.

Sallama yayi wa su mama da mamaki mama tace”iKon Allah hausa kake ?

 

Murmushi yayi yace”eh sosai mama sannunku,yana magana Yana satar kallon ihsan wacce kanta yake kafadar mama.

“Yauwa sannu mama ta bashi amsa,

Dan shafa Kai yayi sannan yace”mama dama wucewa nai har Sau biyu sai na ganku a tsaye ga rana Kuma da alama kamar marar lafiya kuke tare?

Sai a lokacin ihsan ta bude Ido suka hada Ido da ita ware Ido sosai tai ta kalleshi a zuciyar ta Kuma tace “mijin novel

“Wallahi mama tace asibiti mukaje to kaga wiyar abun Hawa .

Ayyah mama in da hali in kaiku gida mana?

“”Ahh aa yaro bbu komai wallahi yanzu zamu Sami abin hawa ai karka dam.

Dan Jim yayi sannan yace to Amma mama ga jinya ga rana sai ciwon ya dadu ai .

 

Haka saurayin Nan yayi yayi Amma mama taki yarda ya kaisu gida haka ya hakura daga karshe dai Kuma ya karbi number ihsan ya shige motarsa ya tafi.

Mama ce tai murmushi ta bishi da kallo tace”dama dai abinda ya kawo ka kenan Amma yaushe daga haduwa sai mu shiga motarka.

Yana tafiya suka sami adaidaita ya kaisu har gida.

 

Tun kafin suje gida kan ihsan ya daina ciwo saboda Tasha magani dama tun a asibiti.

WhatsApp ta hau inda tana hawa taje status ta rubuta sick need your prayer da d’an emojis na hawaye tana posting Kuma sai ta dauki hotunan magungunan suma tai posting a status kasan maganin ta rubuta , headache.

Nan dai akai tai mata sannu Allah ya Kara sauki .

Shamsiyya kawarta wacce suke makota ita tace ta rubutu mata “kaii ihsan banda karya yaushe kika kwanta jinya Kuma?

“Ke wallahi ciwon Kai nayi yau kamar zan mutu ai yanzu yayi sauki munje asibitin murtala sun bani magani Ina tunanin rashin bacci ne dan Dr yace min babu maria babu typot Kuma jinina normal yake ihsan tawa shamsiyyah amsa.

 

“Ayya sannu bari nazo yanzu na duba ki.shamsiya ta Kuma tura mata.

 

“Okey sai kin zo ki tawo da kayan gdksvdujsosmbahavsu

 

“Mekika rubuta ?? Shamsiyya ta tura mata .

 

Tsaki ihsan tayi tace matsalar wanda yayi primary kenan sai ta Kuma tura mata cewa nai ki tawo min da kayan hsgsksbsuslsbsg

 

 

{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

 

 

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_

 

 

 

 

RAI DA RUHI

 

page 3

 

Na Maryam dangi

 

The writers of

 

Zuciya

Kangin bauta

Amanata

Aure biyu

Wazan aura

Duniyar aljanu

Sarautar zalinci

Dakin duhu

Kogon tsafi

 

And rai da ruhi

 

Shamsiyya ce tace “iKon Allah ke gani nan zuwa gidan naku kawai .

 

Minti biyu sai ga shamsiyyah tazo da yake gidan babu nisa tsakaninsu da su ihsan din.

A tsakar gida ta tarar da mama bayan sun gaisa ta shige ciki,a kwance ta sameta kan katifa, fuskar ta dauke da murshi hannunta rike da waya.

Sallama shamsiyyah tayi ta shiga,gefan katifar ta zauna ta kalli ihsan tace sunnu fa haka ne baki da lafiya mayyar online?

Zaune ihsan ta tashi tana dan ya tsina fuska sannan ta dubi shamsiyyah tace “banji shigowar ki ba wallahi,sai Kuma tayi murmushi ta Kuma duban shamsiyyah tace”ke wallahi saurayi nayi bansan yanda zan kwatanta miki shiba Amma wallahi inda kika san Dan india kinga kyau?

Murmushi shamsiyyah tayi tace yaushe kikai saurayin bayan yanzu gari ya waye jiya Kuma muna tare tun safe ko a Facebook kuka hadu?

Tsaki ihsan tayi tace “dama ni Ina yin Facebook ne ke ba Kya cin ribar zance ko kadan dazu fa da mukaje asibitin murtala ne shine muka hadu a hanya shine yanzu muke chat dashi .

Kama hab’a ihsan tayi tace “kice daga haduwa har kin kamu?

Dariya ihsan tayi tace “bazaki gane ba Amma wannan shine irin mazan da ake cemusu mazan novel dan kuwa karshen haduwa sai dai bansan ya halinsa yake ba tukunna dai ,Amma Ina fatan halin ma yazama mai kyau Amma ni naga miji fa.

Gaba daya suka kwashe da dariya shamsiyyah tace “to Allah ya tabbatar da alkhairi zamuce,ya jikin naki?

“Jiki da sauki wallahi ciwon Kai nai mai tsanani Amma yanzu nasha magani ya sauka .

Ajiyar zuciya shamsiyyah tayi tace”a Ina saurayin naki yake wai?

Dariya ihsan tai ta kalli shamsiya tai Kuma tunturewa da dariya sai Kuma tai shuru tace”dazu fa muka hadu gaskiya ban tambayeshi ba Amma ni ya tambayeni dan yace anjima zai zo ma wajen magariba dan na matsu lokacin yayi.

Tab”shamsiyya ta fada tana kallon ihsan”ke gaskiya kin kamu da yawa Kuma zanso naga wannan saurayin naki naga kin wani mayance.

Dariya ihsan tayi har tana Dan dukan shamsiyyah kallon ta yay tace”kin san Allah sham……….kanta ta rike jin yanda yayi mugun sarawa “innalillahi ta furta tana rike Kai “wayyo Allah kaina.

Da sauri shamsiyyah ta rike ruko ta tana lafiya kuwa ihsan?

“Shamsiyya kaina kamar zan mutu wallahi wayyo Allah na ta fada tana kwanciya akan gado

Da sauri Ihsan ta fita tana kwallawa mama kira a gigice mama ta tawo har tana tuntube kamar zata fadi saboda mama tanason ihsan sosai .

Da sauri mama ta karasa cikin dakin kwance ta sami ihsan ta rik’e kanta tana wayyo Allah kaina,

“Ihsan ihsan mama ta fada tana d’ago ta,ganin fuskar ihsan tayi tayi mugun ja idanunta tamkar jini zai futo”innalillahi wa inna ilaihir rajiun mama ta furta tana Kuma Kara kallon jikin ihsan “meye haka Kuma naga jikin ta Yana canza wa haka ?

Shamsiyya ce tai jikin bango ganin yanda ihsan take komawa kamar jan gauta mama ce tace shamsiyya dauko min ruwa wannan fa kamar aljanu gaskiya dauko min ruwa in mata addua a ci.

Da sauri ihsan ta fita ta dauko ruwa a Kofi ta kawo wa mama .

Addaua mama tai a cikin ruwan zata watsawa ihsan kenan Kuma sai taga jikin nata ya dawo yanda yake ajiyar zuciya ihsan ta sauke sannan ta Mike zaune tana Kai wannan ciwon kan har ina

Mamaki ne ya kama mama da shamsiyya ,kallon ta mama tai sannan tace”Maza karbi wannan ki shanye aljanu ne suke neman taba ki kinga yanda dazu jikinki yayi caa kuwa.

 

Dariya ihsan tasa har da tafawa tace”aljanu Kuma?nice mai aljanun,ai wallahi mama bi ba fariya ba Amma nafi karfin aljanu,kawai daga ciwon Kai sai ace aljanu a Ina na samu kenan?bacci ne kawai Amma ni bazan Sha wanann ba ga magunguna na nan zan sha anjima inna ci abinci Amma bazan Sha wanna ba tab wai aljanu kwanciya tai ta dau wayata ta cigaba da chat da sabon saurayinta

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment