Littafan Hausa Novels

Rafeeq Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Rafeeq Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

RAFEEQ

 

 

 

*PAID BOOK….* #400

 

NA

*_ASMY B ALIYU_*

Da

*_HAJJA CE_*

 

 

1.

 

Wata shahararriyar mota ce ƙirar zamani ash color da ta gaji da haɗuwa tayi parking a gaban katafaran store ɗin nan wato Sahad store. Sai da aka kusan shafe mintuna biyar kafin a ɓalle murfin motar wacce take ciki ta fito gabaki ɗayanta waje. Tafe take cike da nishaɗi da walwala sanye cikin shigar wata doguwar rigar jallabiya ƙirar ƙasar (Oman) kalar sararin samaniya. Kallo ɗaya zakayi mata kasan da cewar tana taƙama da kuɗin da Allah ya baiwa mahaifinta. Cikin isa da wata irin izza ta shiga ciki tana ware idanunta a cikin store ɗin. Duka-duka minti talatin tayi a cikin shopping store ɗin ta ɗakko duk wasu abubuwan da take da buƙata ta biya aka kai mata cikin mota. Maimoon Gwarzo kenan kyakkyawar yarinya ta gaban kwatance, farace tas irin farin nan na larabawan asali, haka kuma doguwa ce bata da jiki sosai, gabaki ɗaya dai zubinta irin wanda zaka kalleta ne ka kasa ɗauke idanunka a lokaci ɗaya. Ƴa ce ga Alhaji Mustapha Gwarzo wanda mutum ne shi mai kawaici da tawakkali, sannan shi mutum ne mai tausayin gaske, uwa uba kuma mai riƙo ne da addininsa. Yana da matuƙar mutunta jama’a da son maƙotansa fiye da tunanin mutane. Shi ɗin mai sakin fuska ne a wajan mutane, Allah ya bashi wani irin sihirtaccen kyau domin shi ɗin jinsin Fulani ne na asali. Matarsa ta farko ta rasu ne a wajen haihuwar ƴarsa Maimoonatu. Ɗansu na farko shine Abdul-Shaheed Gwarzo sai Moobarak Gwarzo sannan kuma Maimoonatu Gwarzo. Tun bayan rasuwar mahaifiyarsu da kusan shekaru goma sai lokacin Alhaji Mustapha Gwarzo ya ƙara yin wani auren yana da matarsa suna tare. Sai kuma yaron da yake riƙo a wajanshi wato ɗan ƙaninsa wanda tun yana ƙaraminsa iyayen sukayi haɗari suka rasu wato RAFEEQ Habeeb Gwarzo. Sosai Alhaji Mustapha Gwarzo yake riƙe dashi yana jinsa tamkar ɗan cikinsa da ya tsugunna ya haifa, haka kuma ya haɗeshi cikin yaransa baya taɓa nuna mishi wani banbanci a komai na rayuwarsu. Shekarun Maimoona huɗu a duniya ta fara zuwa makaranta, tana da shekaru goma sha ɗaya ta gama matakin primary school, a shekaru goma sha bakwai kuma ta kammala karatunta na secondary school. Babu yadda yayunta ba su yi ba akan mahaifinsu ya tura Maimoonatu karatu can ƙasar waje amma yaki, a cewarsa yana son yaga ƴan matan Nigeria suna kishin ƙasarsu. Dan haka ya samar mata gurbin karatunta a can (A.B.U Zaria). Suma kansu mazan dakyar yabarsu suka fita zuwa ƙasasashen waje karatun. Maimoonatu tun tana ss1 tayi saukarta ta karatun alkur’ani maigirma da kuma sauran wasu littattafai na addinin musulunci. Abdul-wahaab shine mutum na farko da ya fara shayar da ita zaƙi da kuma ɗanɗanon garɗi irin na soyayya. Wato Wahaab mutum ne mai matuƙar hakuri da sanin ya kamata. Abdul-Wahaab mutum ne da yake da ƙarancin haƙuri dan ya zamto ba komai Maimoonatu keyi masa ta ɓata masa rai ba. Gabaki ɗaya Wahaab ba kyakkyawa bane, sai dai kuma baya cikin layin da za’a kirashi da munana ba. Kalar fatarsa mai duhu ce, amman da kaganshi kasan cewar yana cikin hutu da jin daɗin rayuwa. Yazo bautar ƙasa ne cikin makarantar A.B.U, wanda a nan ne alaƙarsu ta fara shida Maimoona.

Sirri Ne Hausa Novel Complete

Shekarar su uku tare. Tana komawa gida toilet ta shiga, cikin jacuzzi ta shige tana sakarwa jikinta ruwa mai ɗan zafi.

 

 

Tana zaune a cikin ɗakinta taji kamar hayaniyarsu Yayah Shaheed, ta duba agogon bangon ɗakin lokacin ƙarfe goma na safe. Ta runtse ido da sauri kafin ta ƙara buɗewa dan san tabbatar da cewar ba wai mafarki take yi ba. Da gudu ta fita daga ita sai kayan bacci a jikinta na riga da wando masu ɗan kauri, ko hula babu a kanta sai kananun kalabar dake ta faman reto a tsakiyyar bayanta. Sosai nayi matuƙar tsaye a wajan dan ganin Yayuna guda biyu a wajan, daman Moobarak Gwarzo ba ƙasa ɗaya suke karatu ba. Shi yana Germany su kuma suna ƙasar Cyprus. Da gudu ta ruga ta faɗa cikin jikin Yayah Shaheed tana ta faman dariyar farin ciki take faɗin. “Yaya kai ne kuwa? Anya kai ne Yah Shaheed?” Yana sake ɗago da fuskarta suna haɗa ido yake cewa. “Yeah ni ne nan mana autar Daddy me kika gani?” Ya faɗa yana ɗage mata gira ɗaya. Cikin murna take cewa. “Gaskiya Yaya ƙasar nan ta karɓeku kai da Yayah Rafeeq, Uhmmm kaga wani kalar haske da kuka yi kuwa?” Ta maida idanunta ta kalli gefen inda Yayah Rafeeq ɗin yake tsaye, ga mamakinta sai taga ya ɗauke kai daga kallanta. Ta marairaice fuska tare da kamo hannunsa cikin shagwaɓa take cewa. “I’m so sorry Yayana, kasan fa bama ƴar haka da kai, ko so kake Yayah Shaheed yayi mana dariya?”

Fisge hannunsa yayi wanda a dai-dai lokacin Daddy da Aunty suka fito. Da murmushi a fuskar Daddy yake faɗin. “Ku kuma haka ake zuwa babu wani sanarwa?” Dukansu suka juya tare da rungume Daddy. Rafeeq ne mai faɗin. “Mun gama komai Daddy har kwalayen karatun mu mun karɓa munyi bankwana da ƙasar Cyprus.” Da farin ciki Daddy yake faɗin “Alhamdulillahi Allah yasawa karatun naku albarka.” Duk suka haɗa baki. “Ameen.” Suka amsawa Daddy. Haka Aunty ma ta tayasu murna. Tare suka shiga cikin kitchen da Aunty muka shirya masu abincin rana. Ƙarfe biyu suna gamawa Maimoona ta shige wanka, daman kuma tana son leƙawa gidan Aunty Amra wato ƙanwar Daddy. Har cikin parlor ta samu Daddy ta sanar dashi zataje yayi mata fatan sauka lafiya shi da Auntyn su. Harta shiga mota sai kuma ta fito da sauri ta nufi part ɗin su Yayah Shaheed, kai tsaye ɗakin Yah Rafeeq ta nufa, sai da taje sannan ta tsaya a bakin ƙofa tayi knocking kafin ta tura ƙofar ɗakin ta shiga. Ɗagowa yayi da sauri suka haɗa ido yayin da ya yiwa ruwan faron hannunshi wata irin kyakkyawar zuƙa. A hankali ta ƙarasa wajanshi ta karɓe jarkar ta wurgata ta window sannan ta dubeshi cikin muryar damuwa tana faɗin. “Meyasa hakan Yah Rafeeq? Ashe daman baka daina yiwa ruwa irin wannan shan ba tun a lokacin daka kace ka dai na?” Ranta ya ɓaci ta juya zata nufi ƙofa yayi saurin riƙo hannuta ya zaunar da ita a gefenshi. Ta harɗe hannunta akan kirjinta tana faman shan toka. Ganin yadda tayi ne yasa saura kaɗan Rafeeq ya fashe da dariya amman ya danne dan yasan idan har ya yi dariyar ya ƙara takalo wata rigima ne. “Okay na dai na but ina zakije hakan?” Kawar da fuska tayi gefe “Gidan Aunty Amra zanje.” Ta faɗa still shaye da toka. Kallonta kawai yake with out blinking kallonta kawai yana sake faranta ranshi domin bashi da wani burin da ya wuce a duniyar nan Maimoonatu Gwarzo ta zama matarsa ta aure ba. “Me kake tunani haka?” Yaji sassanyar muryarta ta sake dukan cikin kunnanshi. Ya sake cijewa yace. “Babu komai, ina zaki hakan?” Sai da ta miqe tsaye sannan take faɗin. “Zanje gidan Aunty Amra ne.” Numfashi yaja mai sanyi tare da faɗin. “Alright muje na rakaki toh.” Ba tayi musu ba yabi bayanta su nufi motarta. Maimoona ke driving ɗin shi kuma yana gefenta da waya a hannunsa yana dannawa. Har ƙofar gidan Aunty Amra ta ajiye su sannan suka jera suka shiga cikin gidan. A falo Maimoona tayi sallama, da gudu Suhaila ta fito tana mata Oyo-yo-yo. Maimoona ta ɗagata sama tana zagaye parlorn da ita, wanda kuma hakan da tayi yasa Rafeeq Gwarzo ya harɗe hannayenshi akan kirji yana kallonsu yaji tankar a lokacin Maimoonatu matarsa ce da kuma ƴarsu. “Suhaila ina Mami take?” Cikin fara’a take faɗin. “Mami tana ɗakin Abba.” Sake janyo hannunta tayi tana cewa. “Okay Suhal fa.?” Tace shima yana ɗaki yana buga game. Dai-dai lokacin Aunty Amra ta fito daga cikin wani ɗaki da fara’a take yi musu sannu da zuwa. Cike da mamaki kuma take tambayar Rafeeq yaushe a garin? Ya faɗa mata cewar ɗazu da safe. Da murna take faɗin. “Allah yasa wannan karon da matanku na aure a hannayenku kai da Shaheed? Dama ga auta nan Daddy na shirin yi mata aure banda ku. Da wani irin yanayi ya juya yana kallon Aunty Amra fuskarsa cike da tsantsar mamaki, kalmar auren da Maimoonatu zatayi yafi ko mai tsaya masa arai. Zai yi magana kuma aka kira Maimoonan a wayarta, dubawa tayi ganin yanayin yadda ta ɗora a jikin kunnan ta take wani amsa wayar ya tabbatar masa da cewa da namiji take wayar. Tashin hankalin da Rafeeq Gwarzon ya shiga a wannan lokacin ba zai faɗuba. Ya rinse ido yana lasar ƙasan lips ɗin shi da harshe yana cewa. “Aunty bari zanje na dawo zuwa anjima.” Rafeeq ya faɗa yana ƙoƙarin barin cikin parlorn cike da tashin hankali yana kuma jin wani mugun sanyin na shigar masa duk wata ƙofa ta cikin jinin jikinsa. Tun daga tsakiyyar kansa har cikin tafin ƙafarsa haka yake jin sanyin. Sai da ya fita compound ya tuna baya tare da car key, juyawar da zaiyi ya hango Maimoona na fitowa da fara’a cikin fuskarta. Ganin yanayinsa yasa taji walwalar da take ciki na ɓacewa a hankali. Hannu kawai ya miƙa mata yana cewa. “Bani key ɗin.” Kallonsa take ganin irin damuwar dake kwance a cikin fuskarsa yasa taji wata irin damuwa itama, dama kuma gashi duk cikin yayunta tafi jin Rafeeq Gwarzon har a ranta wanda batasan dalili ba. Jiki a sanyaye ta miƙa masa key ɗin tana faɗin. “Daman shi na fito na baka, but wai ina zaka haka kake ta sauri?” Batareda ya kalleta ba yake faɗin. “Yanzu zan dawo ba wani daɗewa zanyi ba.” Daga haka ya shiga motar yai mata key yana yiwa mai gadi horn, tana kallon motar har tabar cikin compound ɗin sannan ta ɗan yi ajiyar zuciya ta juya ta koma cikin gidan tana jiran isowar Abdul-wahaab…

 

****************

Har parlorn baki takai Abdul-wahaab, ya ɗaga kai ya kalleta yana faɗin. “Sai da aka gama shanyani ko?” Ta sakko da tray ɗin agabansa mai ɗauke da kayan motsa baki sannan ta zauna akan kujera mai fuskantarsa fuskarta kunshe da murmushi. Sake kallanta yai cike da soyayyarta yace. “Yanzu ke madam duk wannan abubuwan da, kika ajiye min su kike na cinye komai?” Maimoona ta sake yin wani sassanyan murmushi muryarta a sanyaye take cewa. “Idan har ka cinye zanfi kowa jin daɗin haka, ko babu komai nasan baka tafi da yunwa ba.” Idanuwa suka haɗa tayi saurin ɗauke nata saboda kunyarsa da takeji. “Shikenan sakko muci tare.” Ta buɗe ido tana kallansa. “Nifa kai kaɗai na kawowa kaci kabar ragowar.” Yayi ƴar dariya kafin ya ɗauki juice ɗin yasha. Abdulwahab bai jima ba yayi mata sallama, anan kuma Aunty Amra ta roƙeta alfarma akan ta kai Suhail da Suhaila wajan shan ice cream ɗan tun jiya tayi masu alƙawarin zata kai su gashi bata samu lokaci ba, kuma yau Abbansu yana azumi zata tsaya ta haɗa masa abun buɗa baki. Daga haka Maimoona ta kwashesu a motar Aunty Amrah zuwa wajan shan ice cream. Tana gama yin parking ta hango motar ta a wajen, mamaki ya kamata, kenan Yah Rafeeq nan yazo? Aikuwa fitowar da Maimoona tayi daga cikin mota ta hangoshi cikin motar shi da wata budurwa zaune a gaban motar. Ƙarasawa sukayi gaban motar ita da yaran, kallo ɗaya tayiwa budurwar da irin shigar dake jikinta ta ɗauke kai tana taɓe baki kafin subar wajen da sauri. Budurwar ta kallonshi tana faɗin. “Ita kuma wannan wacece?” Sai da yaja numfashi mai ƙarfi kafin ya iya buɗe bakinsa. “Ƙanwata ce.” Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba yana tada motar gamida barin wurin. Kusan awa biyu sukayi a wajen sannan suka dawo gidan. Ganin Rafeeq yaki dawowa ne yasa ta yiwa Aunty Amrah sallama tare yi mata ƙaryar cewa Rafeeq ɗin yana waje yana jiranta. Tana fitowa tayi tsaye a gefen hanya tana jiran abun hawa ranta duk a ɓace, sai ga Rafeeq ya tsaya ya sauke glass yana faɗin ta shigo. Ai kuwa ta wani haɗe rai tana faɗin. “Kawai ka tafi zan samu abun hawa na koma gida.” Baki buɗe yake kallanta. “Kinsan Allah ranki zai ɓaci idan baki shigo ba.” Ya faɗa da ɗan ɗaga murya. Ta buɗe ƙofar motar a fusace ta shiga tana jin wani irin takaici. Har suka hau babban titi babu mai kallon ɗan uwansa. Wayartace ta fara ringing sai dai tana ji taki ɗauka. Cike da mamaki Rafeeq ke faɗin. “Kina jin waya amma bazaki ɗauka ba.?” Tayi shiru tana faman cuno baki, sai kawai taga yayi parking a gefen hanya ya buɗe jakar ya ɗakko wayar yana dubawa, sunan da yaga yana yawo akan screen ɗin wayar ne ya karya masa duka wani kwarin gwiwarsa. Gani kawai tayi ya tada motar tare da harbata kan titi sun ci gaba da tafiya. Ita kam tana mamakin canjawar yanayin sa, ikon Allah kawai ya kaisu gida ba wai tuki cikin nutsuwa ba. Suna cikin cin abincin dare Daddy ya kalli Shaheed da Rafeeq yake sanar dasu zancen auren ƴar uwarsu Maimoon nan da wani watan, sannan zata cigaba da karatunta a ɗakin mijinta. Rafeeq Gwarzo yafi kowa shiga cikin tashin hankali lokacin da yaji haka a bakin Daddy. Wata irin dariyar farin ciki Shaheed ya fashe da ita yana kallon Maimoon da takeji tamkar ta nutse cikin ƙasa saboda kunya. “Finally ƙanwata zatayi hankali very soon Inyeeee.” Ya faɗa sounding so very happy a muryarsa. Da gudu Maimoon ta tashi ta nufi ɗakinta tana dariya. Shaheed Gwarzo na kwala mata kira amma bata ko kalleshi ba. Rafeeq kuwa gabaki ɗaya kasa cigaba da cin abincin yayi, ji yayi kalaman Daddy suna taɓa zuciyarsa, da murmushi yake faɗin. “Allah ya sanya alkhairi.” Aunty ta karɓa da “Amin.” Tana sake cewa. “Ya kamata kuma kuzo ku fito da matan aure duk ku shiga gidajenku dan abin kunya ne ace kaf cikin ku babu mai tsayayyar budurwa.” Dariya kawai Shaheed yayi amma Rafeeq barin parlorn yayi yana jin kirjinsa nayi masa wani irin nauyi. Yanzu dagaske rasa Maimoon Gwarzo zai yi? Ya zai yi da soyayyar da yake mata shekaru kusan goma sha biyar zata tashi a banza? Ya dafe gefen kansa yana jin komai na cikin duniyar yana tsaya masa cak! Ko kafin wayewar gari jikinsa yayi mugun zafi haka ya tashi da wani irin zazzabi. Jin shirun yayi yawa Rafeeq bai fito ba yasa Shaheed ya leƙa cikin ɗakinsa a nan Rafeeq ɗin dunkule cikin duvert yana rawar sanyi. Hankalinsa yayi mugun ɗagawa, ya ƙarasa da sauri ya ɗagoshi duka zuwa cikin jikinsa yana tambayarsa meke damunsa, ganin duk yabi ya ruɗa ɗan uwansa kasancewar kaunarsu dabance a cikin gidan yasa Rafeeq sake rufe ido. Babu kalar tambayar da Shahed bai yi masa ba amman yaki buɗe baki yayi masa magana. Waya Shaheed ya ɗaga ya kira family doctor ɗin su. Kai tsaye cikin gidan ya tashi ya nufa, Aunty ya samu a kitchen tana shirya breakfast ita da ƴan aiki ya gaisheta yana tambayarta daddy fa? Ta faɗa masa cewar yana parlorn sa. “Lafiya dai ko?” Ta tambaya tana kallon yanayinsa. “Daman Rafeeq ne baya jin daɗi.” Cikin sauri tace. “Meya samesa?” Cike da rashin sani yace. “Wallahi nima ban sani ba, amman jikinsa yayi zafi sosai.” Aunty ta girgiza kai tana faɗin. “Toh Allah ya kara sauki, bara na haɗa tea akai masa ya samu ya sha sai ka kira family doctor ɗin.” Daga haka Shaheed ya nufi parlorn mahaifinsu. Da sallama ya shiga duk da sun gaisa dan tare sukayi sallar asuba, amman sai da ya ƙara gaisheda Alhaji Mustapha Gwarzo. Cike da fara’a ya amsa yana kallon yaron nasa dake tare da damuwa cikin fuskarsa. “Lafiya dai koh?” Anan Shaheed ya faɗawa Daddy yadda ya tarar da Rafeeq. Dashi da Daddyn suka nufi part ɗin su wanda shine na farko a cikin gidan mai ɗauke da ƙaton falo da kuma ɗakunan barci dauke da karamin parlor a kowanne. Kai tsaye room ɗin Rafeeq suka nufa Shaheed na ɗauke da ƙaramin tray wanda Aunty ta haɗa masa tea da wainar kwai a cikin plate…

 

 

 

 

 

#Hajja ce

#Asmy b Aliyu

#Rafeeq Gwarzo

#Maimoon Gwarzo

#Wahaab Bamalli

#Haske Writers Association……

*RAFEEQ*

 

 

*PAID BOOK*

 

 

NA

_*ASMY B ALIYU*_

DA

*_HAJJA CE_*

 

 

 

 

 

 

2.

 

 

Tunda yaji muryar Daddy a cikin ɗakin sai kawai yaji duk gabaki ɗaya ana sake hargitsa masa ƙwaƙwalwarshi, ya sake curewa cikin duvert tare da rintsa idanuwa yana sauke wahalallan numfashi. Alhaji Mustapha ya ƙarasa wajan bed ɗin tare da sanya hannunsa ya yaye duvert ɗin jikinsa yana ƙarewa ɗan marayan yaran nashi kallo. “Rafeeq meke damunka haka?” Maimakon yayi magana kawai sai ya fara ƙoƙarin tashi zaune, Shaheed ya taimaka masa ya jingina bayansa jikin gadon yana furta. “Gajiya ce kawai Daddy kuma na kasa yin bacci.” Cikin tsananin tausayawa Daddyn ya sake taɓa forehead ɗinshi, jin zafi sosai yasa shi cewa. “Wannan zazzabin na jikinka yafi ƙarfin ace na gajiya ne kaɗai, ka buɗe bakinka kasanar dani ainahin abinda yake damunka, ko kanada wanda ya fini ban sani ba?” Cikin sauri Rafeeq ya shiga girgiza masa kai yana cewa. “Haba Daddy har akwai wani da zaifika a gurina? Please kayi hakuri idan na ɓatamaka rai.” Ganin yadda ya wani gigice ne yasa Daddy cewa. “Shikenan naji yanzu dai karɓi tea kasha Dr Arham yana hanyarsa ta zuwa gidan nan ya dubaka.” Shaheed ya shiga miƙa masa tea cup ɗin ya karɓa tare da kaiwa bakinsa. Wani amai ne ya taho masa, kafin kace wani abu ya fara sakinshi a duka jikinsa. Alhaji Mustapha ya riƙeshi a jikinsa yana matse mishi shoulder yake faɗin. “Subahanallahi wannan wane irin ciwo ne yake damunka?” Hankali a tashe Shaheed ke cewa. “Da alama ba wai zazzabin bane kaɗai.” Daddy ya jinjina kai. Wayar Shaheed ce ta fara ringing ya zarota daga cikin aljihu, Dr Arham ya gani ba tare da ya tsaya ba ya fice daga ɗakin yana amsawa. Tare suka shigo cikin ɗakin, a lokacin Alhaji Mustapha ya shiga gyarawa Rafeeq jikinsa wanda gabaki ɗaya ya rasa duk wani ƙwari na jikinsa. “Yauwa Dr bari na saka masa riga sai ka duba shi.” Ya faɗa yana buɗe wardrobe ɗin kayan Rafeeq ɗin. Riga da wando na bacci ya zaro masa suka sanya masa shida Shaheed, sannan suka taimaka masa ya bar kan gadon wanda bedsheet ɗin ya lalace da amai. Cikin soofa yake ƙoƙarin kwanciya suka hanashi, Daddy yace a maidashi room ɗin Shaheed kafin a gyara masa nashi. Sosai Dr Arham ya duddubashi kafin ya rubuta wata allura da magani sai kuma drip da za’a yi masa sakamakon rashin kuzarin da bashi dashi, sannan jikinsa yana buƙatar hakan saboda babu abinci a cikinsa. Kallansa kawai Alhaji Mustapha keyi yana faɗin. “Yanzu sabida Allah meyake shirin haifar maka da heart attack Rafeeq? Ko dai wani abin ake yi maka wanda ka kejin babu daɗi a cikin gidan nan? Ka sanar dani zanyi maganin abin da yardar Allah.” Rafeeq yai shiru yana jin zuciyarsa na wani irin bugawa, yasa hannunsa cike da dauriya ya kamo na Daddy yana kuma rintsa ido. “Alhaji ku tsagaita da yi masa yawan tambayoyi yanzu, duk wani abu da zai yi dogon bayani yanzu a ɗan barshi har mu samu zuciyarsa ta daidaita, yanzu bari naje a ɗakko allurar da sauran abubuwan da za’ayi masa, kafin na dawo a samu ya ɗan ci wani abun koyaya yake kafin na zo.” Cike da sauraro Alhaji Mustapha ya amsawa Dr, yana fita ya kalli Shaheed yana cewa. “Shaheed kira mai kula da side ɗinku ya gyara room ɗin Rafeeq yanzun nan.” Babu ɓata lokaci kuwa Shaheed ya fita ya sanar dashi kafin ya koma ɗakin ya zauna sukaci gaba da jiran Dr. Kai tsaye wajan dining room ta nufa inda aka gama shirya breakfast, kallan wormers ɗin ta shiga yi kafin ta fara buɗewa dan ganin abubuwan da suke ciki. Kujera taja tare da janyo flask ɗin kunun madara ta zuba cikin glass cup, jin an shigo cikin parlorn ne yasa ta ɗan waiga kaɗan, Yaya Shaheed ne ya haye stairs still idanunta suna kan hanyar taga ya shiga ɗakin Daddyn su. Cikin sauri taga ya sake fitowa zai fice ba tare da ya kulata ba tayi saurin cewa. “Yaya Shaheed Daddy bayanan nima naje mu gaisa na tarar babu kowa.” Cikin yanayin sauri yake ce mata. “Yeah muna tare dashi a wajan Rafeeq za’a sanya masa drip.” Da sauri ta miƙe ganin ko tsayawa beyi ba tabi bayansa. Maimoon tasha mamaki lokacin da taga yanayin da Rafeeq ke ciki, ta dinga zaro ido cike da tashin hankali take tambayar Alhaji Mustapha. “Daddy me ya samu Yaya haka?” Alhaji Mustapha Gwarzo ya kamo hannunta ya zaunar da ita a gefenshi yana cewa. “Muma bamu sani ba kiyi masa addu’a kinji ko?” Jikinta yayi sanyi ta shiga leƙen fuskarsa da take a lumshe yana jan numfashi kaɗan-kaɗan. Hannun mahaifinta ta kamo cike da tsantsar damuwa take cewa. “Ikon Allah sai kace jiya ba muna tare da shi ba. Daddy haka mutuwa fa takeyi ko? Kuna tare da mutum lafiya lau sai kaji ance ya mutu.” Alhaji Mustapha ya sake damke hannunta yana kallanta yace. “Haka ne auta . shi yasa a kullum ake son mutum ya dinga yafiya dan kar a mutu ana jin haushin wani ko wata.” Sosai jikinta ya mutu da yanayin da taga ɗan uwan nata a ciki. Har aka gama masa allurar aka daura masa drip ɗin be motsa ba bare ya buɗe idanunsa. Yana jin duk wasu kalamai nata da suke fitowa daga cikin bakinta suna sauka a duka sashen jikinsa wanda har baya so yaji tayi shiru. “Shaheed kaci gaba da kula dashi bari naje sitting room zanyi baki.” Cewar Alhaji Mustapha yana miƙewa tsaye ya fice daga cikin ɗakin. Maimoon ta koma wajan da Daddyn nasu ya tashi wato kusa da ƙafafuwan Rafeeq ta zauna har jikinta yana shafarsa yaji wani irin zirrr har cikin brain ɗinshi. “Kije kiyi breakfast ɗinki mana.” Cewar Shaheed yana buɗe wardrobe ɗinshi. Da yanayin damuwa take cewa. “Wane irin breakfast zan iya yi Yaya Shaheed? Wallahi bazan iya ba yadda naga Yaya Rafeeq a cikin wannan yanayin.” Rafeeq da idanunsa ke lumshe jin kalamanta ya sake jefa masa wata irin wutar soyayyarta a cikin ransa, ya dinga jin tamkar ya janyota zuwa cikin kirjinsa da yake jin tamkar zai rabe gida biyu. “Zaifi miki kyau dai kije kici karki janyowa kanki wata matsalar, kina gani dai shima harda ulcer da take damunsa.” Girgiza kai tayi tana sake maida idanunta kan Rafeeq cike da tausayi take faɗin. “Jiya beci abinci ba ina kallansa.” Rai a ɗan ɓace Shaheed yace. “Waike kin fimu damuwa da halin da yake ciki ne? Oya ki tashi ina san na kintsa a ɗakina kinzo kin zauna, sai kwana -kwana nake yi miki dan ki fita kin kasa ganewa.” Maimoon ta juya tana kallan Rafeeq tana jin kamar idan har ta bar ɗakin wani abu marar daɗi zai iya samun shi, dan haka ta kawar da kai gefe tana cewa. “Yaya Shaheed ba wanka zakai ba? Taya za’a barshi shi kaɗai anan wajan, kawai kaje kayi ka barni na kula dashi.” Baki wangale Shaheed yake kallanta, sai kuma ya juya ya shige bathroom bayan ya ɗauki ƙaton towel. A hankali ya shiga buɗe idanunsa ya ɗora su akan kyakkyawar fuskarta, bata san yana yi ba sakamakon wayarta da take faman dannawa suna chatting da Abdul-Wahaab. Kira ne ya shigo wayar ta ɗan saki murmushi tare da daga wayar ta kara jikin kunnenta tana cewa. “Wato chatting ɗin beyi maka ba dole sai munyi waya ko?” Rafeeq yaji kirjinsa ya sake yi masa wani irin nauyi, idanunsa suka sake ƙanƙancewa, zuciyarsa ta shiga yi masa zugi. Cikin wata irin murya Maimoon taji yana cewa. “Please get out.” Jin yayi magana ne yasa tai saurin waigowa tana kallansa, sai dai idanunsa still a rufe suke. “Yaya Rafeeq magana kakeyi?” Yai mata banza sai lips da ya shiga cizawa da hakorinsa. “A’a bada kai nake ba nida Yaya Rafeeq ne bashi da lafiya.” Cewar Maimoon tana sanarwa da Wahaab. Da yake bayajin abinda Wahaab ɗin ke cewa sai dai ita idan tayi magana yaji tace. “Eh shine bashida lafiya ka ganshi nan kwance ana masa ƙarin ruwa.” Da salon muryar da yaji tana magana ne yasa shi kasa jurewa sauraranta, dan haka cikin azabar ciwo taji yace. “I said ki tashi ki fita.” Tayi saurin kallansa da mamaki take faɗin. “Yaya Rafeeq wai dani kake ne?” Cikin tabbaci ya shiga ɗaga mata kai. Maimoon ta miƙe tsaye tare da ficewa tana turo baki.

 

Shiru ya ziyarci cikin ɗakin sai kuma yaji duk babu daɗi, ashe har gwara tana wajan yana jin motsinta hankalinsa yafi kwanciya. Yanzu kuwa da ta tafi sai yaji wani irin kunci, tsanar Abdul-Wahaab ta shiga cikin zuciyarsa ta zauna, duk da bai taɓa ganinsa sai da ya hango yanayinsa a cikin idanunsa ya kuma ji cewa Maimoon bata dace dashi ɗin ba. Shaheed ne ya fito yana ware ido ko zai ga Maimoon a cikin ɗakin amma baiganta ba, yaje ya murzawa ƙofar key sannan ya fara shirya jikinsa. Sai da ya kammala komai sannan ya ɗakko wayarsa ya kirata, bugu ɗaya ta ɗauka tana faman ɓata rai yace ta shiryo masa breakfast ta kawo masa ɗaki. “Zansa Lami ta kawo maka.” Cike da mamaki Shaheed ke cewa. “Ke mekike yi da bazaki kawo min da kanki ba?” Maimoon ta sake cuno baki kamar tana gabansa take faɗin. “Toh ba Yaya Rafeeq ya koroni ba.” Kallon inda Rafeeq ke kwance yayi ganin yadda yake tun ɗazu haka yake yanzu yasa Shaheed cewa. “Shida yake bacci tun ɗazu shine zakice ya koreki? Kinga malama idan bazaki kawo min ba ki barshi idan na shigo naci.” Yana kaiwa nan ya katse tare da dire wayar yana jan ɗan ƙaramin tsaki. Rafeeq yana jinsa babu abinda yai masa daɗi irin yadda zata dawo ɗakin, yasa a ransa idan har tazo kawo breakfast ɗin bazai barta ta kuma fita ba bare taje suyi waya da Wahaab. Bakinta da sallama ta turo ƙofar da kafarta hannunta ɗauke da tray idanunta akan gadon da Rafeeq ke kwance. Tunda yaji isowarta shi kuma ya buɗe idonsa, kallanta ya shiga yi sanye take cikin wasu riga da wando Pakistan pink da ratsin white ɗin fulawoyi a jiki, tayi kyau sosai kai kace ita tayi kanta . Wajan Shaheed ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin tana cewa. “Ni duk bansan abinda zakaci ba shi yasa kawai na zubo maka sinasir dan naga kamar shine ka daɗe bakaci ba.” Shaheed na duba wasu book’s yake cewa. “Kin kyauta kuwa sister dan a Cyprus ina mukaga wani sinasir.” Ta juya zata fice Rafeeq ya buɗe baki a hankali ya kirata. “Moon.” Tana jinsa amma tayi kamar bataji ba, sai da Shaheed ya kalleshi yana cewa. “Ah ashe ka farka? Maimoon Rafeeq na magana fa.” Cak ta tsaya taki juyawa su haɗa ido saboda taji haushin korar da yai mata ɗazu. “Bakiji ba ne?” Shaheed ya faɗa da ɗan fushi ganin taki zuwa. A hankali ta juya ƙarasawa tayi wajanshi tana wani kifta idanuwa. “Zauna.” Cewar Rafeeq idanunsa suna kanta. Gefen gadon ta zauna tana wasa da mayafin Pakistan ɗin jikinta. Idanunsa ya mayar ya lumshe, ta kalleshi cike da mamaki ganin bece komai. “Yaya Rafeeq gani fa.” Ta faɗa cike da haushi a cikin muryarta, ya ɗan miƙa hannunsa da babu drip a jiki ya riƙo nata, ta kalli hannunwan nasu tana ware ido. “Kiyi zamanki naga kamar ɗazu kinji haushi right?” Cikin gaskiyarta tace dashi. “Sosai ma.” Sakar mata hannun yayi yana sauke numfashi, kallosa take yana jinta har tsakiyar zuciyarsa yace. “Idan na mutu zaki damu?” Kafin tayi magana Shaheed yace. “Haba guy ya da wannan maganar kuma? Dan Allah ka dena maganar mutuwa sai munyi aure mun ajiye jikoki.” Maganarsa tasa Maimoon tuntsirewa da dariya, yanayin yadda take dariyar cikin farin ciki shine ya haddasawa Rafeeq jin duk wani ciwo a jikinsa ya warke. “Wayaga Yaya Shaheed da jika ah.” Ta faɗa tana sake fashewa da wata dariyar. Daga haka kuma sai duk ta manta da ɓacin ranta suka shiga hira duk da cewa Rafeeq baya sanya musu baki. Har ruwan ya ƙare Shaheed ya zare masa sannan ya maidashi ɗakinsa. Maimoon ce ta shiga bathroom ɗinshi ta haɗa masa ruwan wanka mai zafi, sai da ya shiga cikin bathroom ɗin sannan ita kuma ta fice zuwa sashen su…

 

 

 

 

#Asmy b Aliyu

#Hajja ce

#Maimoon Gwarzo

#Shaheed Gwarzo

#Dr Arham

#Haske writer’s association…

RAFEEQ….*

 

*PAID BOOK….* #400

 

 

NA

*_ASMY B ALIYU_*

Da

*_HAJJA CE_*

 

 

3..

Ɗaure da milk ɗin towel ya fito a ƙugunsa yana sake sharce ruwan da yake kwance a saman fuskarshi, kai tsaye closet nashi ya nufa ya zuge murfin wardrobe ɗin yana san tantance waɗanda zai sanya. Waɗanda suka kwanta a cikin zuciyarsa ya ɗakko domin ya daɗe beyi irin shigar ba. Gefe bed ya ajiye kafin ya isa wajan mayukansa masu matuƙar kyau da gyara fata, jikinsa ya shafe dasu sannan ya miƙe yasa kayan. Shigar riga da wando yayi na farar shadda wacce aka yi masa ɗinkin zamani masu gajerun hannuwa, ya janyo hularsa zannah bukar baƙa ya ɗorata akansa tare da isa wajan madubi yana gyara botir ɗin gaban rigarsa. Tsayawa kawai ya yi yana zubawa tsari da kuma kamala irin wacce ubangiji Allah ya zuba masa, yasa hannu yanajan dogon karan hancinsa da ya ƙara ƙawata kyaun fuskarsa sai wani buɗe idanuwa yake kamar mai san gano wani abu a cikinsu. Rafeeq Habeeb Gwarzo kenan matashi mai ji da taƙama, uwa uba kuma kyawun da Allah subahanahu wa ta’ala ya zuba mishi. Sai dai abinda yake matuƙar bashi mamaki shine yadda yaga Maimoon Gwaro batayi masa irin soyayyar da yakeji a cikin zuciyarsa, kallansa takeyi tamkar yadda take kallan su Shaheed Gwarzo da suka fito ciki ɗaya. Juyawa ya yi a hankali ya zaro takalmi yasa ya ɗauki car key yafito. Kai tsaye wajan tsaleliyar motarsa ya nufa wacce Alhaji Mustapha Gwarzo ya sissiya musu, tashi black marsandi ta Shaheed kuma white sai ta Maimoon red color yayin da Mubarak sai ya dawo za’a bashi tashi. Yana ƙoƙarin shiga yaji zazzaƙar muryarta mai sauke masa duk wani noti dake ɗaure a jikinsa. Kallonta yake da dukkan nutsuwarsa har ta iso gabansa idanunshi suna zagaye jikinta. Sanye take cikin doguwar riga armless tayi matuƙar karɓar surar jikinta, kanta da hula kamar net ana hangen tarin gashin dake kanta. “Yaya sai ina kuma?” Ya riƙe murfin motar yana faɗin. “Unguwa.” Wajansa taje itama ta riƙe murfin motar tana leƙa ciki, yadda kusancinsu yazo har yana jin ƙamshin turaren jikinta yana shigar masa cikin kai ne yasa shi faɗin. “Kina da saƙo ne?” Maimoon ta dago tare da kallansa da manyan idanunta farare tas tace. “Naga kasha kwalliya kamar wanda zashi taɗi, da alamar Auntyn tawa ƴar Nigeria ce, ko itace wacce naganku tare?” Cikin haɗe rai Rafeeq yake kallanta yana ƙoƙarin shiga cikin motar ya zauna yake faɗin. “Idan itace menene?” Maimoon ta samu kanta da haɗe rai, cikin yatsina fuska take faɗin. “Batai min ba tun lokacin da na ganku tare, haba Yaya duk macen da zaka aura karka bari idanunta su buɗe da zuwa irin wajajan nan indai ba matarka bace ta aure. Kawai ni yarinyar batai min tun kallan farko dana ganku.” Kallanta ya yi sosai yaga dagaske take maganar, sai da ya murza key a jikin motar yake cewa. “Waye ya zaɓar miki Abdul-Wahaab?” Tambayar tazo mata a wani irin yanayi, ta turo baki tana wani kifta idanuwa take cewa. “Wahaab daban ne Yaya Rafeeq, ita kuma waccen daga gani bata da kamun kai.” Cikin tsuke fuska ya kalleta zai yi masifa sai kuma yaji ya kasa, yasa hannu zai rufe motar Maimoon ta riƙe tana cewa. “Dan Allah karkaje wajan yarinyar nan baku dace da juna ba sam.” Fizgo ƙofar yai ya kalleta yana cewa. “Kema ai baki dace da wanda zaki aura ba, so kowa yaje yaji da matsalarsa bye sai na dawo.” Yaja motarsa da ɗan karfi har Maimoon tana saurin yin gefe guda ganin kamar zai mangareta. Har sai da ya fice daga cikin gidan sannan ta juya ta koma ciki tana jin takaici indai har wajan wannan yarinyar zashi, bedroom ta wuce ta ɗauki wayarta tana daddanawa. Rafeeq na fita kai tsaye wani store ya shiga, kayan masarufi yasa aka jidar masa yasa a booth ɗin motarsa sannan ya nufi gidan marayu dake nan cikin ƙwaryar Kano. Daman tun ba yanzu ba Rafeeq yake zuwa kai taimako hakan yasa duk masu gadi da masu kula da gidan suka sanshi, ko baya cikin ƙasar yana turo da kuɗi ayiwa marayu abinda sukafi buƙata. Mutum ne shi da abin hannunshi baya rufe masa ido, yana matuƙar jin daɗi a duk lokacin da yayi irin wannan zuwan, yakan ji duk wata damuwa tashi Allah yana yayewa. Ɓangaren bebaye masu buƙata ta musamman aka fara rakashi, cike da tausayawa ya dinga shafa kawunansu yana sake godewa ubangiji da ya kaishi hannun Alhaji Mustapha Gwarzo, banda haka yasan shima da Allah zai iya kawo gidan nan yayi rayuwa makamanciyar da yaran nan keyi. Sai da aka rakashi ko’ina sannan ya fito ya bada umarnin sauke kayan dake cikin booth tare da yin alƙawarin kawowa yaran da suke under 6years suturar sakawa dan ya lura tayiwa yaran karanci a jikinsu. Yana cikin tuki yaji wayarsa na ringing, janyota yayi daga inda ya ajiye yana dubawa yaga mai kiran nashi, kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya daure yai daga batare da yace komai ba. “Jan aji ma da yazo wajanka sai da ya sara maka, uhmm kana ina ne?” Ɗan yatsina fuska yayi kamar tana kallansa yake cewa. “Tuki nakeyi.” Yanayin yadda taji yana maganar ne yasa ta gane baya cikin walwala, Zee Leeman ta kuma kashe murya cikin san janyo hankalinsa take cewa. “Ina Ado Bayero mall ko zaka ƙaraso?” Kalaman Maimoon ne ya faɗo masa inda take nuna masa cewar ba ajinshi bane yawan fita da mace zuwa wajan shaƙatawa wacce ba muharramarsa ba. Sai dai kuma shi mutum ne mai yawan san fita outing, yana so yaga yana zagawa cikin duniya dan ya dinga ganin yadda rayuwa take garawa. Karya kan motar yayi yana cewa. “Ganinan zuwa.” Katsewa sukayi yana wani rintsa ido gani yake kamar bayajin shawarar ƴar uwar tashi, sai dai kuma in har beje wajan Zeee ɗin ba to babu wani waje da zashi, gida ne kuma ko yaje babu abinda zai yi a can ɗin. Tunda ta hangoshi takejin wani irin farin ciki yana cika mata zuwa, lokaci ɗaya kuma ta miƙe tare da nufowa inda yake. Kallan juna suka tsaya yi Rafeeq ya ɗage mata girarsa guda ɗaya alamar “Lafiya?” Handbag ɗin dake hannunta ta janyo tare da rungumeta a kirji. “Muje ko?” Ta faɗa tana nuna masa hanyar shiga wajan wasanni, shi yayi canji sannan suka biya suka shiga gurin.

Kai tsaye wajan zama suka nema suka zauna, Rafeeq yana karaɗe idanuwansa a wajan tamkar wani bako. Zee Leeman da takejin wata irin soyayyarsa tana taso mata takai hannunta tare da riƙo nashi, kallanta yayi sosai kafin ya janye idonsa acikin nata idon yaji tana faɗin. “Na ƙagu naji kace zaka fara zuwa gidan mu dan su san da matsayinka , amma kai sai naga kamar baka shirya aure na ba why?” Ya sauke wani irin numfashi yana zare hannunsa daga cikin nata yake cewa. “Zee har yanzu kin kasa gane inda zuciyata ta dosa, please mubar maganar auran nan yanzu.” Cikin yanayin damuwa take sake kallansa, tana so ta gane sonta ne bayayi ko kuwa dai shirya yin aure yanzu ne baiyi ba? Gabaki ɗaya bata gane inda zuciyarsa ta nufa akan alaƙarsu, baya mata wulakanci haka kuma soyayya yake yi mata tamkar yadda saurayi da budurwa keyi. “Kasan ni macce ce Rafeeq, rayuwata kalilance zan so ace duk wannan zaman da mukeyi da kai ya zama mata da miji ne mu. Dan Allah baby ka shirya ka fara zuwa gidan mu su Abba su san da zamanka.” Kallanta yake yi cike da tausayawa, yana jin mugun nauyinta akan yace ba itace a cikin wannan zuciyar ba. Maimoon gwarzo ta riga ta gama cika xuciyarsa da soyayyar ta”Kayi shiru baby kodai baka sona ne?” Ya kalleta da mayun idanunsa masu kama da madara farare tas dasu yake cewa. “Tun farkon haɗuwar mu dake nace ki daina yi min maganar aure saboda bana so kiyi tunanin zan aureki, Zee bana san yaudara a cikin tsari na shi yasa nake ce miki idan har kin samu wani wanda hankalinki ya kwanta dashi toh ki amince masa kiyi auranki. Zuciyata tana cikin wani irin yanayi wanda na rasa ta yadda zan ɓullo masa. Kiyi min addu’a kawai Allah ya cika min buri na.” Hawaye suka fara zirarowa daga cikin idanunta, yana kallanta ta gefen ido haka kuma yana jin kukan nata har cikin jininsa saboda shi a rayuwarsa baya kaunar yaga ana kuka nan da nan yake jin tashin hankali. “Kana tunanin idanuwana zasu iya ganin wani bayan kai? Rafeeq idan wata ce a cikin zuciyarka ka gaya min hankalina zai fi kwanciya, idan kuma wani hali ne nawa da baka so ka sanar dani sai na gyara, wallahi zan gyara Rafeeq indai akan farin cikinka ne.”wani irin karayewa xuciyar Rafeeq tayi lokaci ɗaya ya Xaiyi da Zainab idan ya fallasa mata sirrin dake cikin xuciyarsa xai iya karya xuciyarta.tun farko bai so wannan kusancin nasu ba,bai so tafiar su ta kawo nan ba duk laifin shaheed gwarzo ne da ya ta cusa masa ita alhalin ba itace aransa ba.haka kuma baya so ya cigaba da boye mata ,idan aka cigaba da tafia a haka xatayi wani tunani daban ne akan wanda ke ransa.

Damke hannunsa yayi yana kallonta da dukkan idanunsa,wani irin bugawa xuciyar zeey keyi a wannan lokacin tana jin bugawar da zuciyarta take har cikin tafin ƙafarta.A hankalin ya kamo hannunta abunda bai tabayi ba tsawon rayuwarsa riqa hannunta ,runtse idonta tayi xuciyarta na bugawa fisge hannunta tayi lokaci ɗaya ta fashe masa da kuka tana girgixa kai take faɗin”dan Allah karkace banice a ranka ba Rafeeq’ xan iya mutuwa ka taimakeni karka fadamin dan Allah.

Ta fada tana kara sakin kukan da Rafeeq gwarzo keji har cikin xuciya da ruhi,Dukansu Abu ɗaya suke nema Amman kowane nasa ya banbanta da na dan uwansa,Zainab liman tana sonsa wanda ya lura a shirye take da ta sadaukar da farin cikinta saboda shi,shi kuma maimoon gwarzo ce acikin tashi xuciya shekaru goma sha takwas a baya ,wanda xuciya da gangar jiki basu taba gajia ba.banbancin shine yana son maimoon gwarzo Amman bata ma san yanayi ba,yasan xainab na tsananin sonsa da kaunarsa,sai dai shi kuma ba itace a tashi xuciyar ba dukan su suna cikin matsala.Hannu yasa yana squeezing sumar kansa gefe ɗaya kukan Zainab na hargitsa masa lissafi..Zainab goge hawayenki muyi magana,ya faɗa sounding so very cool cikin muryarsa, tissue ta fiddo acikin handbag nata tana goge hawayen idonta still wasu na kara fitowa…

 

 

#Hajja ce

#Asmy b Aliyu

#Rafeeq Gwarzo

#Zeey leeman

#Team tagwaye Novels

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment