Littafan Hausa Novels

Prince Salman Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Prince Salman Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

PRINCE SALMAN

 

 

 

by teemarh cool

 

 

*Elegant online writer’s*

 

 

Bismillahi rahamanirrahim

 

wannan littafin free ne amma rashin comments,zai sa na mai dashi na kudi,natsara labarin ban yadda wata ko wani ya juyamun labari ba, sai da izini na.

 

 

 

wannan littafin sadaukar wane ga masoyana, kuma masoyan Elegant online writer’s.

page 1

_______Zaune take tana duba takardar dake hannunta,ajiyar zuciya ta sauke kana ta ajiye takardar kan tabarmar da take zaune akai, ta tashi cikin nitsuwa ta buta ta shiga banɗaki,

Karuwar Gida Hausa Novel Complete

tana ganin shigar ta bandakin yasata fitowa ɗaki da sauri ta ɗauki takardan ta fara karantawa kasan cewa da hausa aka rubuta,dariya tasa mai sauti tana cewa “Umma fito ankuma halin,”fitowa Umma tayi cikin sauri jin taji abun da yake faranta mata rai,wanda yayi daidai da fitowar Tasleem daga ban ɗaki,Husnah ce tace” kinji kunya Tasleem anrasa mashin shini shima wannan din ma ya gudu”tayi mgnr cikin tsantsar farin ciki, Umma ma nataya ta sanda sukayi mai isarsu sannan Umma ta kalleta a yatsine tace” me kika tsaya kallo yar tawa kikeso ki cinye da manyan idanun naki kamar na mayu,tayi mgnr tana jan Husna ciki daki tana cewa” karta cinyeki naga ta kureki da idon nan nata da bata kiftawa. tsakin butar hannunta Tasleem tayi tashige ɗaki da gudu tana kuka, saman gado ta kwanta tana rera kuka mai ban tausayi, dahaka har bacci ya dauke ta.

 

Shigowa gidan Mama tayi da sallama a baƙin ta,”jin an amsa mata ciki-ciki yasata yin tsaki ta shige ɗakinta tana cire mayafinta,ganin Tasleem kwance ne yasata karasawa kanta da sauri dan tasan Tasleem bata baccin rana sai dai in batada lafiya,”gani tayi idonta sun kubbura fuskarta yayi jajir kasan cewa ita fara ce, jikinta yayi zafi sosai,

hankalin mama yatashi sosai,”fita tayi sakar gida dan ta hura huta ta daura girki kafin Tasleem ta tashi,”

“Umma ce ta fito tana cewa ashe kin dawo”eh Mama tace rai a ɓace,dariya tayi kasa kasa tana cewa”ah a ina Tasleem din keda kanki zaki hura hutar? “shiru tayi bata kulata ba dan batada lokacin magana yanzu,

Umma ganin ba fuska tayi ɗaki abunta,

ta gama girka abincin ta Tasleem bata tashi ba dan haka tashiga ɗakin ta taso ta,

mai ya same ki Tasleem?”shuru ta ɗanyi kana tace mama yaushe kika dawo ne?”kallon ta Mama tayi tace ki amsamun tambayata nace,ganin ran Mama ya ɓaci yasata ne yasata sa karwa mama tana cewa,”Nabil ne ina dawowa daga school shine ya bawa abokin sa letter ya bani,”

daga nan kuma sai ta saki kuka mai tsuma zuciya,

“Umma itama jikin ta yayi sanyi amma bata nuna mata hakan ba”

dukkan su shiru sukayi na naɗan wani lokacin,

“kiyi hakuri Tasleem wannan jarabawane daga Ubangiji,kiyi kokarin cinyewa dan allah Tasleem ”

cizan laɓanta tayi tare da girgiza mata kai”

yauwa tashi kije kiyi wanka

 

tashi tayi jiki ba gwari ta fita danyin wanka,

 

tattare ɗakin Umma tayi,tare da zibawa Tasleem Abinci.

 

 

*********************

*Borno state*

 

fadar Shehu Muhammad Ali

shiru akayi dukkan fadan “da alama jiran fitowar sarki akeyi”

 

“sai da aka dauki wajen 20 kafin nan sarki ya fito cikin kasaita yake tafiyar cikin izza da mulki,karasowa yayi ya zauna akan kujeran da aka tanadar masa”gaishesa suka farayi tare da sun kuyar da kai, daga musu hannu yayi”

fadar ce ta sake shiru sai da aka jima a haka kafin sarki yace…….!

 

Comment and shared

 

By teemarh cool

PRINCE SALMAN

 

 

by Teemarh cool

 

 

 

 

*Elegant online writers*

 

 

 

Page 2️⃣

 

 

_________”Yarima ya kammala makarantarsa,zai dawo,dan haka kowa ya fara shirye-shiryen dawo wan Yarima,in sha allah a satin nan zai dawo,dan haka Galadima zai muku bayanin komai,”

“gaskiya ne sarki” cewar galadima tareda rusunawa yana cewa”wani ma yayi rawa balle dan makada,in sha Allah zamuyi abunda kayi umarni harda ma wanda baka furta ba dan farincikin Yarima”

 

“daga masa kai sarki yayi”

 

 

zaune take cikin izza da mulki,akan wani kata faren kujera wanda yafi ko wanne kyau a cikin parlor ta ɗaura kafa daya kan daya,tana girgizawa,

“Jakadiya ce zaune kanta a kasa,

 

“zamuyi aikin nan tare dake amma ba na bukatar asamu wani wani matsala,ni ban san matsala ba a rayuwa ta dan haka kika kuskura furta mun kalman matsala to zakiyi kuka da idonki,inkuma akasamu to wallahi ranar zaki kwana a kabarin ki,”

tayi maganar cikin ɓacin rai,

“ina fatan kin fahimta dan haka gobe nakeson ki fara aikin ki,”

 

watsa mata wasu kudi tayi masu yawa wanda ita kanta batasan iyakan su ba,

“kije ki fara da wannan inda bukatar wani sai kiyimun magana,”

 

“godiya nakeyi ranki ya dade,babu maganar matsala kamar yadda kika gani a fuskata bana dariya ko murmushi to haka nake ko yaushe irin wannan aikin nakine yake sani farinciki,dan haka bazamu samu matsala ba,na barki lafiya,”

 

 

 

 

********************

abinci take ci tana da dan wasa da hannun ta daya “oh ni Binta,Tasleem yau kuma abun da zakiyi kenan?kina cin abin ci kina wasa da hannunki,”

sun kuyar da kanta tayi kasa tana cewa”a’a,Mama kawai”….tafara magana irin mara gaskiya nan,”kimun shuru,ni kiyi ki gama na aike ki, kije ki kar bomun kuɗin dashe na,

inason gobe na futa kasuwa zanje siƴayya,”

to Mama bari na karasa,gobe karki manta ki siyamun jaka,”

“to bazan manta ba in sha allah in baki da lecture ma sai muje tare dan ki zaɓa da kanki,

“zan duba time table na,”

 

“Mama natafi,”

“kice mata dan allah kasuwa zanje a hada mun yanzu dan allah ”

“to zai nadawo”

 

“Allah kiyaye hanya,karki manta da addu’a fita daga gida,ki kula sosai ban da tsayawa ako ina,

 

“Malam ya shigo gida da sallama a bakin sa,”

Mama ce take tan kaɗen garin tuwo ta amsa masa tare da masawa dan ya zauna akan tabarman

“sannu da aiki Binta,”

yauwa Malam,sannu ya kasuwa naga yau kadawo da huri,”

eh wallahi kawai na dawo ne ba dan dadi ba na tashi daga kasuwa,”

“subbanallahi me yake faruwa”cewar Mama,

a maimakon ya bata amsa sai kira ya kwalawa Umma yana cewa”Hussaina kina ina ne bakiji shigowa na ba,sai da ya kirata kusan sau uku kafin ta fito tana gyara zanin ta,

tare da yamutsa fuska tana cewa

“sannu da zuwa Malam,ashe ka dawo,”

“eh nadawo, ina wayarki yake ne?,nakiraki baya shiga?”

“inaga Rahina ta fita dashi kasan nata yasamu matsala,”

“ni ina zan sani,duk ba wan nan ba,ana ta naiman ki agida basu sameki ba shine suka sameni a waya suke fadamun cewa Hassan ta rasu,”

 

“wayyo allah na,namutu na lalace,nashiga uku na,”

subbahallahi karki manta ke musulma ce anbamu al’qur’anic kuma ya koyar damu cewa “in musiba yasame mu mudinga anbatar allah,shiya aiko mana da haka dan ya jarrabemu,mai yasa zaki dinga kalan wannan magan ganu irin haka,’Mama ta karashe maganar tare da share hawayen ta dan taji mutuwar nan sosai itama,matace mai mutunci batayi halin yar uwarta ba tana girmama mutum,duk da allah ya bata arziki amma bata hula kan ci ,gashi yau allah ya karbi abunsa takoma ga allah,

duniya kenan,

*Kullu nafsin za’ikatul maut*

 

haka taci gaba da ihu abunta da kyar mama tasa mata hijab ta bata charbi a hannun ta,suka tafi tare,suna isa ana mata wanka,nan tafara ihu tana cewa

” wayyo allah nikam ina zansa kaina ne ta mutu ta barni yar uwata tare muka fito duniya muka girma tare mai yasa haka zaki tafi ki barni,to ni mai zanyi a duniyan,gwara nima na mutu,”

 

anyi anyi ta daina fadan haka amma takiyin shuru sai abun da ya karu,sai kaita wani gida akayi aka rufeta dan masu wanka da masu yimata sallah su samu nutsuwa,

 

sai wajen 11na dare Mama ta dawo, tasamu malam a filin gida akan sallaya

“allah ya dawo dake lafiya?”

“eh wlh Malam,

ya hakuri?”

“ni nayi tinanin ma kwana zakiyi ”

“a’a wallahi abun da yasa ma na dade haka Hussaina ce taki ta nutsu,”

“allah rufa asiri bari na kwanta” cewa Malam yana shiga ɗakinsa itama nara ɗakin ta shiga taga Tasleem tayi bacci,har zata kwanta sai kuma ta tashi taje ɗakin Umma ta duba Rahina sannan ta dawo ta kwanta,

 

da asuba Tasleem ta tashi tayi hadin kumallo,ta gama komai da huri dan zata fita yau da huri tana da lecture 8 haka,abinci take ci kafin ruwan wankan ta yayi,ta gama cin abin ci tana fita sai taga an kwashe ruwan nata,

mamaki ne ya kamata sai ta daga kanta taga banɗakin sai taga zanin wankan Rahina a rataye kasancewa ta makara 7:28 yasa ta ta janye zanin ta jefa mata shi ɗakin su,

ta wanke jikin ta tayiwa Mama sallama,”cikin bacci ta amsa mata tare da yima nuni da ta dauki kudin mota a jakarta,

natafi

“allah tsare”

“Ameen”

gama wanka tayi ta nemi zanin ta tayi tarasa har lekawa tayi ta waje koya faɗi amma bataga alamar shi ba abun ne yabata tsoro tayi tinanin ko aljanu ne suka dauke , yasa ta fita da gudu dan shiga ɗaki,

“Assalamu alaikum” cewar wani,yana ganin ta ta ruga ɗaki da gudu yasashi fita daga gidan a ɗari yana cewa…………

 

 

 

 

 

MORE TYPING

MORE COMMENT

 

 

 

 

By Teemarh cool

About the author

Hausa_Novels

2 Comments

Leave a Comment