Littafan Hausa Novels

Oum Sharifa Ce Karin Bayani Akan Novels Group Namu

Written by Hausa_Novels

Oum Sharifa Ce Karin Bayani Akan Novels Group Namu

 

 

 

 

 

 

 

 

OUM SHARIFA CE

 

 

*Assalamualaikum* *warahmatullah mutane oum Sharifat palace barkan mu da* *wannan lokaci barkan mu da kasance a satin farko na gabatar da daya daga cikin shirye shiryen mu* *muna fatan Allah yasa mu fara a saa*

 

 

 

Ammin junior

 

Ameen wa alaiki salam warahamatullah

 

 

 

OUM SHARIFA CE

 

*zamu so jin cikakken sunan bakuwar mu*

 

 

Ammin junior

 

Sunana Nana khadijatu lawal anma anfi kirina da Abla

 

 

OUM SHARIFA CE

*Sannu takwara*

 

 

Ammin junior

 

 

Godiya nake name sake

 

 

OUM SHARIFA CE

 

*Zamu so ji takaitaccen tarihin bakuwar mu*

 

Ammin junior

 

 

To kamar dai yanda na fadi sunana anhaifeni ne a kasar Niger a garin Maradi a12/29/ 1990 nayi makaranta a garin Maradi nayi primary da secandry duk a garin Maradi daganan akayiman aure a 8 /28/2016 nayi aure a wani gari dake cikin jahar Diffa N’gourti kasancewar mijina soja ne yanzu kuma ina da zama a garin Niamey inada yaro na daya Abdoul Malik ana cemasa junior an haifesa 12/29/2020

Malamai Ne Sila Hausa Novels Complete

 

OUM SHARIFA CE

 

 

*waw ma sha Allah Allah yayi wa albarka*

 

Ammin junior

 

Ameen nagode

 

 

OUM SHARIFA CE

 

*yauwa ko zamu san me kika fahimta da kalmar aure?*

 

 

Ammin junior

 

To abinda na fahimta shidai aure ibada ne kuma jijiyon sa shine hakuri kuma a wani Abu ne da yake nufin kebantar mutane biyu Wanda idan bakayi hakuri ba zaka sha wahala

 

 

 

OUM SHARIFA CE

 

 

*Gaskiya ne wannan to Amma ana samun matsaloli da dama aciki aure daga dukkan bangarorin a ganin ki menene jigon abnda yafi kawo matsala tsakanin maaurata*

 

 

Ammin junior

 

 

To matsala naga remu mata daya kasance gurbataciyar tsokar nan ta cikin hakar karinmu Bata barin mu seta hallakr damu dakuma rudu nashedan domin ita Macé duk inda take a kasan namji take to majority matsalar shine idan namiji yayi mana muce se mun rama ko kuma gani ga wane kace wance gidanta kaza akeyi kai kuma ba haka Alhalin Allah da yayo mu ma ya babbantamu sannan kuma wasu Mazan ne kome kayi masu dasa gani to anma nu mata da zamuyi hakuri mu rike ibada da adu’a da abin yazo da sauki domin naga Matar da mijinta idan yashigo gida zaita zagin mahaifanta ko kanzil bazata cemasa ba idan ya kare masifar sa kuma tace Allah yabasa hakuri

 

 

OUM SHARIFA CE

 

*Gaskiya ne kina ganin kenan rashin hakuri shine matsalar mu mata ? to Amma matan sa suke hakurin da kauda kai kina ganin wata rana zasu iya samn farin ciki daga mazan nasu*

 

 

Ammin junior

 

To yanzu dai aure ba irin na zamanin kakan ninmu bane da zakiga anata farin ciki da annashuwa bance duka ba anma wasu Zaki samesu babu fira tsakanin iyalen babu taimakon juna koda da taya aikin gida ne ko kuma gyara Yara babu shikawai ya auro jaka aninfunshi kiyi girki komai na gida ga wankin Yara ga naki ga nasa duka ke daya to kinga babu taimako Kenan babu farin ciki auren yanzu idan kace seka samu farin ciki kamar a novel to ka dauki dala ba ganmo kawai ka kudira a niyar cewa ibada ce Allah yace muyi fakat seka jira farin ciki Wanda baya yankewa a gidan Aljanna insha Allah

 

 

 

OUM SHARIFA CE

 

 

*gaskiya ne Ammin junior*

*To akwai matan da zaki ga su da kan su suke jawo wa kan su matsala daga mazajen su zaki ga namiji yana son soyayya da kulawa da tsafta Amma wata macen abn sai ahankali me zaki ce musu?*

 

Ammin junior

 

To wannan kam sunada aiki domin ita tsafta ma cikwon muslunci ce bayan haka idan ka gyara kanka kaima zaka ji dadi ita kuma soyaya nishadi ce wannan do wa ya semeta zaiso idan har kasan me kake to wannan yakamata su gyara domin daga rayuwar takare babu wata seta lahira gara ka mori soyayar anan idan kaje cen ma ka mora insha Allah inaka Kira ga mata masu kazanta da su gyara koda kuwa basada tutafi da yawa ko kuma kudi suyi wankan su sannan suwanke Kayan koda kuwa da tokan murhu ne se suka

 

 

 

OUM SHARIFA CE

 

*Ma sha Allah muna godiya*

Akwai *yammatan da suka shirya shiga daga ciki suka ci burin zaa sha shagali irin sun tsammaci abubuwa da yawa na jin dadin a gidan sabanin rayuwar bata dorewa cikin farin ciki* *zaki basu shawara*

 

 

 

Ammin junior

 

To shwarata a garesu kada suyi wannan burin domin ba lailai su samu abinda suke tsanmani ba yakamata su sa aransu za suje bauta kuma zasuga abinda basa so kinga idan yazamana Sun samu Wanda yasan rayuwar to Sun huta idan ma basu samu ba dama Sun san za arina

 

 

 

OUM SHARIFA CE

 

*Gaskiya ne muna godiya wace hanya zaki fada mana koda guda daya ce wacce mace zata bi ta gyara jikin ta*

 

 

Ammin junior

 

 

 

To gyran jiki na mata yanada yawa kam Macé zata iya anfani da lemon tsamin a wajan hamotan ta kafin tayi wanka ta murza sa sosai a wajan dakuma kasan nononta nan ma ta shafa shi da cen wajan oga ma ta goga setayi wanka wannan Yana fida wari jiki koda baka saka turare ba lfylau ne sanan zaka ri ka wanke baki da gawayi da gishiri ko da baba maclean sannan Macé ta rinka anfani da kananfari a bakinta yanasa kamshin baki idan kana magana babu doyi

 

 

 

OUM SHARIFA CE

 

 

 

*A lallai shagali muna godiya Ammin junior*

*To me zaki rufe mana wannan tattaunar tamu dashi*

 

 

Ammin junior

 

 

Abinda zan fadi a karshe dai Abu biyu ne zuwa uku shine mu mata muyi hakuri babu abinda yake dorewa se ikwon Allah mujure duk kuncin da Muke gani a gida zanmu na biyu mu yaran mu tarbiya ingantaciya yaro tun Yana karami ka koya masa abubuwan muslunci kama daga sallama Bismillah idan zaici hamdala idan ya koshi adu’a kina mai idan zai kwanta to idan ya girma bazai iya kwana ba se yayi domin yasa ba saboda yanzu dama shekaransa biyu da wata uku anma koda bacci ya daukeni sena falka nayi masa yanzu yakai idan banyi ba se ya shafama kansa kuma Nina seta sa hannuwa a baki ya tofa yawu ya shafaman suma mazajen muci gaba da kula dasu koda su basa mana muyi hakuri

 

 

 

OUM SHARIFA CE

 

 

*Alhamdulillah mungode sosai da wannan shawarwari Allah ya bamu ikon yin amfani da abin da mukaji*

 

 

*Sannan muna miki fatan alkairi kema da fatan idan mun sake gayyato ki zaki Kara dawowa kuma Allah yasa gajiyar* *tambaya kar ta sa ki koma gida ki dan sha ruwa a toh asha ruwa lfy mngode Ammin junior*

 

 

 

Ammin junior

 

Nima nagode sosai

 

 

 

OUM SHARIFA CE

 

 

*Duka duka anan muka kawo karshen shirin tauraruwa na wannan satin fatan zamuyi amfani da abinda muka ji bakuwa Allah ya maida ke gida lfy*

 

 

 

Amin y Rabb

 

 

Domin shiga group 08069167242

OUM SHARIFA CE

 

 

Karkashin jagorancin

Jarumai writer’s association💪🏻

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment