Littafan Hausa Novels

Oga Habib Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Oga Habib Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

OGA HABIB

YADDA NA FARA LAFIYA ALLAH KASA IN GAMA LAFIYA.

 

ABINLURA.

BANYI OGA HABIB BA DA NIYYAR CIN ZARAFIN KOWA BA.

 

GARGAD’I!

BANYADA BA BAN KUMA LAMINTA BA, WANI KO WATA YA CANZA MIN LABARI BA BATA RE DA IZININA BA, KO A JUYAMIN LABARI BA, YIN HAKAN KUSKURE NE BABBA, AKIYAYE!!.

 

SADAUKAR WA.

OGA HABIB DAGA FARKON SHI HAR K’ARSHEN SHI SADAUKAR WA CE GAREKI ‘YAR’UWTA D’AYA TAR KAM DA DUBU, OGA HABIB KYAUTA CE GAREKI KIYI YADDA KIKE SO DA SHI, HASSANA SANI MPAPE ABUJA BARRISTER.

 

 

SAK’ON GAISUWA GAREKU ABIN ALFAHARINA.

YAYA SAIFULLAHI SANI MPAPE ABUJA.

BARRISTER HASSANA SANI MPAPE ABUJA.

AUNTY ZEE MPAPE ABUJA.

AMARYA MAMAN AMATULLAH MPAPE ABUJA.

AUNTY MARIYA FUNTUA.

AUNTY ZAINAB YAHAYA BAKORI.

SISTER HAFSAT YAHAYA

BAKORI.

 

 

GODIYA.

INA GODIYA GA MASOYANA A DUK INDA KUKE, BA KU DA TA HANYAR DA ZA KU NUNA MIN K’AUNA SAI TA HANYAR COMMENT D’IN KU.

 

 

DUNIYA KAMAR INUWARKA CE;DUK INDA KA TAFI ZA TA BI KA, AMMA IDAN KA TAFI NEMAN TA ZA TA RIK’A GUDU, KUMA BA ZA KA TAB’A CIM MA TA BA. WASU MUTNE KAMAR SUKARI SUKE A CIKIN RAYUWARKA. KO KA DAINA GANIN SU AMMA D’AND’ANONSU YANA NAN.

ALLAH YAYI MI KI RAHAMA MAHAIFIYATA.

 

 

 

 

Shafi na 1&5.

 

 

Bismillahir rahamanir rahim.

 

 

GARIN ABUJA.

Wani tabkeken Company ne, asamansa ansa,: SANAT YOGHURT.

Daga k’asan sunan kuma ayi rubutu da k’anan bak’i, kamar haka, :sanat yoghurt company , zone e apo Abuja.

tsaye nake ina kallan tsaruwar SANAT YOGHURT company, ina nan tsaye, sai naji wani yana cewa, “Barka da fitowa Oga Habib “. koda na juya dan ganin wannan wanda aka kira da Oga Habib.

Na makara sai dai motar da yashiga nabi da kallo, koda na duba motar da kyau sai naga, corolla S ce.

Motar nabi da kallo, motar black ce, mai pure white glass.

Gudu sosai motar ke yi.

Sunyi tafiya mai nisa sosai, dan har sun shiga garin kaduna.

Tafiya suke sosai, su biyu ne a motar Oga Habib, sai driver shi.

Habib cikin siririyar muryar shi, mai cike da izza, ya ce, “Bilya tsaya!.

D’an tsawa ce ya yi maganar, wanannan nature ne na Habib haka yake abisa lurar da nai me.

Auren Bauta Hausa Novel Complete

Bilya, cikin girmama Ogan shi, ya ce, “Oga Habib Lafiya zamu tsaya anan? kabari mushiga gari mana, kasan yanzu ba ko’ina ake parking ba”.

Habib cikin tsawa, ya ce, “Bilya na ce kayi drup d’ina anan kana kawo min wasu Questions”.

Bilya tsayawa ya yi, Habib ya d’auki faron da yasha ya rage ya fita da shi.

Bilya driver da mamaki, ya bi Habib da kallo, ya ce, “Oh wai dama gayannan fitsari zai yi ya ke min wani muzurai.

Habib da sauri ad’an tsorace ya dawo ya na haki alamun kamar yaga wani abun tsoro.

Bilya driver da sauri ya bud’e ma Habib burfin motar ya shiga.

Bilya cikin girmama ya ce, “Oga Habib lafiya kuwa? “.

Habib kamar ba zai magana ba, sai kuma ya ce, “Bilya gawar mutum nagani anjefar”.

Bilya cikin tsoro ya ta da motar zasu ta fi.

Habib ya da ka mai tsawa yace, “meye haka?, baka ji abinda na ce bane!? “.Bilya driver cikin bin umarnin Ogan shi Habib, ya tsaya da motar, ya kalli Habib, ya ce, “Oga Habib zamu d’augawa ne a mota?, kasan fa yanzu rayuwa ba kamar daba, gaskiya ricks ne Oga mu d’auki gawar da…… “.

Tsawar da Habib ya yi ma Bilya ne, ya sa ya yi shiru.

Habib cikin d’aga murya, ya ce, “ka fita ka duba min ka gani”.

Bilya fita yayi kawai dan bashi da yadda zai yi, amma a ainihin gaskiya a tsorace ya fita.

Bilya cikin tsoro ya fita ya dudduba amma bai ga wata gawa ba.

Bilya dawo wa ya yi, ya kalli Habib cikin girma, ya ce, “Oga Habib banga gawar kowa ba fa”.

Habib tsaki ya ja, ya fito daga motar.

Habib na ta fiya, Bilya na binsa aba-abaya.

Habib kallan Bilya ya yi, yana nuna mai abinda ya gani, ya ce, “Can me ye? “. Da d’an k’arfi ya yi maganar. Yana nuna gawar mutum da yagani kwance agun.

Bilya cikin tsoro ya ce, “Oga Habib zamu fa jefa rayuwarmu cikin had’ar…… “.

Tsawar da Habib ya yi ma Bilya ce tasa ya yi shiru, ya kama bakinsa bai k’arasa fad’in abinda ya ke fad’aba.

Habib cikin b’acin rai dan ya tsani arik’a jayayya da shi, cikin fushi ya ce, “Your very stopped, ina maga kana quarrel da ni, Bilya baka da wani amfani Wallahi”.

Idan da sabo Bilya yasaba da fad’an Habib. Hakan yasa Bilya cikin bin Umar nin Ogan shi yak’arasa inda gawar ta ke.

Bilya cikin al’ajabi ya ke, kallan gawar matashiyar budurwar, Bilya matsawa ya yi kusa da ita sai yaji kamar tana numfashi kad’an-kad’an.Hakan yasa Bilya dawo wa inda Habib ya ke tsaye.

Cikin girmamawa Bilya ya ce, “Oga Habib ba gawa bace,dan da alamun tana numfashi”.

Habib batare da ya kalli Bliya ba, ya ce,”ka d’akkota ka shigo mu tafi”.

Bilya da mamaki ya kalli Habib, amma gudun kar ya yi laifi yasa baice ko mai ba ya bi Umarnin Ogan nashi, ya je ya d’akko ta.

Habib tashi ya yi ya koma site d’in driver ya zauna.

Ita kuma Bilya ya shimfid’ar da ita a mazaunin baya.

Tafiya kad’an ta idasa da su Oga Habib kano.

Suna shiga kano sun yi tafi bawani sosai ba. Habib ya ce, “Bilya samu gu kai parking”

Bilya tsayawa ya yi, kamar yadda Ogansa ya Umar ce shi, ya ce, “Oga Habib mun tsaya”.

Wata private hospital Habib ya nuna ma Bilya ya ce, “Bilya ka shiga hospital d’in nan ka kaita”.

Bilya kamar zai yi kuka, dan shi a ganinsa idan ma tai mako Habib d’in ya ke son yi tom shi yi yi mana da kanshi ba sai ya bashi wahala ba.

Baliya badan ya soba ya d’akko wannan baiwar Allah da ke kwance kamar matatta ya shigar da ita hospital d’in.

Bilya na shiga aka amsheta.

Bilya kallan likitar ya yi, ya ce, “Likita dan Allah tare da Ogana muke, ki bata duk wata kulawa da ya ka mata zan dawo yanzu”.

Likitar cikin mamaki ta kalli Bilya ta ce, “Haba bawan Allah ya za ai bamu sanka ba, ka kawo mana yarinyar da bamu san taka mai-man abinda ke damunta ba, kuma ka ce mana wai za kaje ka dawo. Gaskiya ammana irin haka da yawa anan kano kuma basu dawowa. gaskiya haka ba zai yuwuba “.

Bilya cikin rok’on likitar ya ce, “Karki damu Insha Allah ni zan dawo nai miki alk’awari”. Likitar kallan Bilya ta yi ta ce, “sure”. Bilya cikin tabbatar wa ya ce, “Yess am very sure insha Allah “.

Bilya number shi ya ba likitar ya ce zai dawo ba da dad’ewa ba.

Bilya fitowa ya yi inda ya yi parking d’in motar Oga Habib, ya shiga.

Habib bai tambayi Bilya ya sukai ba, shin tana da rai ko bata da rai make damunta, bai tambayi komai ba.

Shima kuma Bilya ganin bai tambaye shi ba yasa shima yaja bakinsa ya yi shiru.

Direct inda Oga Habib keda Meeting Bilya ya kai shi.

bliya na yi parking Habib ya sauka, hotel d’in da za su yi meeting d’in.

Lokacin da Habib ya shiga har sun gaggaji da jiran shi, dan harma sun fara fidda ran zai zo, in da shi Ka d’ai su ke jira dama.

Habib be fi hour d’aya da shiga taron ba ya fito ranshi a b’ace.

Habib cikin jin haushi ya bud’e murfin motar ya shiga ranshi da alamun b’ace ya ke.

Habib na shiga ya kalli Bilya cikin jin haushi, ya ce, “Jamu bar gurin nan aikin banza ai kin wofi”.

Bilya da sauri ya sa ma motar key suka bar gurin.

Bilya cikin jin tsoro ya kalli Habib ganin ranshi kamar ab’ace ya ke, ya ce, “Oga Habib ina zamu”.

Habib shiru ya yi ya yi banza da Bilya.

Bilya cigaba da tafiya ya yi batare da yasan ina zasu ba, so yake ya k’ara tambayar Habib amma kuma yana jin tsoro.

Wayar Habib ce ta yi ringing, Habib da sauri ya yi picking call d’in, dan ringing tone d’in mommy shi ce.

Habib cikin sakin fuska da murmushi, dan indai kaga Habib na waya yana murmushi tom mutum d’aya ce, wato Mahaifiyarshi.

Habib cikin sweet voice d’in sa, ya ce, “Mommyna kina lafiya”.

Banji mai akaje ba daga can b’angaran sai dai naji Habib ya ce, “Mommy ina hanya fa, na kusa dan Allah kijirani mana”.

Banji mai Mommyn Habib ta kuma cewa ba, sai ji nai ya ce, “Mommy ki barsu kawai, ni dama nasan bawai maganar kirki bace dan dai ma kin matsamin ne shiyasa nazo, Mommy wai fasaha suke so mu saida masu, suma su rik’a irin yoghurt d’in mu ak’asarsu, Wallahi Mommy tsabar haushi ko magana ban musuba nabar gun, dan dana san wannan maganar ce Allah Mommy da banje ba”.

Can b’angaran bajin me ake cewa nake yi ba, sai dai naji Habib nai mata fatan Allah ya dawo da ita lafiya, kuma dan Allah karta dad’e kamar yadda ta yi wannan karan.

Bilya ko jin wayar Oga Habib ce ta sa ya fahimci, Habib yagama abinda ya kawo shi kano, yanzu Abuja zasu nufa.

Hakan yasa Bilya ya kama hanyar Abuja.

tafiyar 4 hour’s ta kai su garin Abuja.

Bilya direct gida ya yi da Habib dan ya san ba zai koma Company ba, in dai ya yi tafiya ba ya komawa sai washe gari.

Bilya na aje Habib , Ya koma Company, dan Bilya aiki biyu ya ke ma Habib, yana aiki a SANAT YOGHURT.

Sanan kuma shike driving d’in Habib duk in da Habib zashi.

Albashi mai tsoka Habib ke biyan duk mai aikacin da ke aiki ak’ark’ashin sh. Wannan shine da lilin da yasa kusan duk suka jure cin mutuncin da Habib ke masu.

Bilya bayan ya koma SANAT YOGHURT COMPANY har an tashi ya koma gida, da ya ke gidan Oga Habib ya ke zaune.

Bilya bayan ya koma gida ne wayar shi tai ringing yad’aga, daga can b’angaran, fad’a sosai ta ke, ta ce, “Haba ya za ai kabarni da yarinya mara lafiya gashi ta farkaba tun d’azu amma kuma baka dawo ba”.

Bilya zaune ya tashi daga kwancan da ya ke, dan ya manta sham da maganar, wata Yarinya.

Bilya cikin damuwa alamun shima bai ji dad’in haka ba, ya ce, “Ayyah dan Allah ki yi hak’uri Wallahi na manta sham. kuma Wallahi yanzu haka ina Abuja, amma ki yi hak’uri da safe zan ma Ogana magana”.

“Gaskiya ni ba inda zan kaita, sai dai in tasan in da zata. Cewar likitar.

Bilya kashe wayar ya yi, ya ce mata dan Allah yana zuwa ta bashi minti d’aya.

Bilya cikin fargaba dan yasan Oga Habib ya hana shi kiran shi in dare ya yi.

Habib na kwance kan makeken gadonsa na alfarma sai game ya ke awayar shi dan shi Mayan game ne. Habib na cikin game kira ya shigo wayar shi.

Habib k’in picking call d’in ya yi, har sai da Bilya ya yi mai kira Uku.

Habib d’aga kiran ya yi ya, ya kanga akun nan shi, yana sauraran abinda Bilya zai ce masa.

Bilya ko cikin tsoran halin Ogan nashi da ba wuya ka b’ata mai rai, ya ce, “Oga Habib dama Yarinyar da muka tsinta ce d’azu, wadda muka kai hospital , tom shine likitar da naba Yarinyar ta kirani, yanzu , akan in zo ta far………. “.

Habib cikin tsawa ya katse, Bilya ya ce, ” Bilya kana ko da full sense, awannan lokacin zaka kirani kana min wannan maganar!?, Yarinya kuma da ka ke magana,duk yadda kaga dama kayi da ita bai shafan ba, karka kuskura ka sake min magana akanta!. “.

Wata zufa mai zafi ce ta fara karyoma Bilya. Ko tunanin mafita Bilya bai fara yi ba, kira ya kuma shigowa wayar shi.

Bilya koda ya duba yaga Number likitar nan ce, Bilya cikin rashin sanin abinda zai ce mata ya yi picking d’in call d’in.

Tun kafin ta yi magana, Bilya ya rigata da cewa, ” Ki yi hak’uri kinga yanzu dare ya yi ba damar in zo Kano, amma zuwa gobe zaki ganni”.

Likitar jin abinda Bilya ce yasa ta kashe wayarta.

Bilya sosai abinda Habib ya yi mai ya b’ata mai rai, taya zai ta kuramai ya d’auki ya rinyar, yanzu kuma yazo yana nai man lik’amai bala’i.

Bilya shiru ya yi, ya na nazari, ya ce, Tom ni yanzu ko ma kano nace zan je in d’akko ta ina zan kaita.

Bilya da sauri ya ba kanshi amsa da cewa, Wallahi sai dai in barma likitar ita, idan ma ta sake kirana bazan d’agaba.

Bilya blocking number likitar ta ya yi.

Cikin jin dad’in shawarar da yankema kanshi bacci ya kwasheshi.

Washe gari misalin k’arfe goma na safe, kamar yadda Habib ya saba sai ya je office sannan ake kai mai abin break fast , haka aka yi.

Bilya ko dama so ya ke ya yi magana da Oga Habib , amma bai samu dama ba, dan tunda ya d’akko shi da safe ya ke waya har suka isa company bai dai na ba. Wanan shine ya hana Bilya yi ma Oga Habib maganar Yarinyar.

Ga shi kuma tunda safe likitar ta da mai da kira, dan tana ganin ya yi blocking Number ta ta kira shi da wata Number. Hakan yasa Bilya ya ke son ganin Ogan nashi sosai.

Gashi in dai Habib ya shiga office d’in shi ganin shi na da wuya sosai, sai dai in Allah yasa ya fito.

Bilya na nan tsaye yana nai man hanyar da zai bi yaga Oga Habib , Sai ga masu kawo mai break fast sun iso, tattawan mata ne guda biyu, amma ba wai sun tsufa bane sosai.

Bilya na ganinsu cikin da bara, ya yi gurin su, ya ce, “Baba lami sannunku da k’ok’arin kula da Ogan mu “.

Tsofaffin cikin girmamawa su ka amsa ma Bilya.

Bilya kallan Baba Lami ya yi, ya ce, “Baba abin k’arin Ogan mu ne ko? “. “Eh Bilya shi ne”.

Suka bashi amsa.

“Baba ku kawo dan Allah in kai mai dama ina son magana da Oga Habib Wallahi amma narasa yadda zan yi”.

Wadda ya kira da Baba lami, wayayyar tsohuwa, murmushi ta yi, ta ce, “Tom Bilya ka dai son ko mai,ka san babu wanda Hajiya turai ta yadda ya ba Oga Habib abinci hannu da hannu sai mu, tom kuma dai kasan Oga Habib yadda ya ke abu kad’an za kai mai babu ruwansa da bashi ya d’auki mu aiki ba, yanzu sai ya da katar da Mutum aiki ba ruwansa, dan haka kayi hak’uri, amma idan nashiga zan gwada mai magana kana son ganinsa k’ila idan akaci sa’a yabari ka shiga”.

Godiya Bilya ya yi ma Baba lami. Sannan suka shiga.

Su Baba lami sun dad’e atsaye suna jiran Comment. Amma shiru.

Habib sai da ya gama abinda ya ke sannan ya basu izin shigowa.

Bayan sun Baba lami sun kaima Habib abin break fast ne. Har za su fita, Baba lami ta yi k’arfin halin bada sautin Bilya.

Baba Lami cikin girmamawa kamar yadda ta saba ba Habib d’in, ta ce, “, Oga Habib, dama yaran nan ne, driver ka, Bilya ya ke Son magana da kai wai”.

Habib batare da ya kalli Baba Lami ba, ya ce, “Ba yanzu ba”.

Baba Lami fita ta yi, tana alawadai da dukiyar da zata sa Mutum ya d’auki kan shi haka, kamar yadda Habib ya d’auki kan shi.

wata zuciyar ta ce mata tom kodai kyan shine yasa ya ke yin haka ne.Nan dai su Baba Lami suka fito suna mai Allah wa dai da ji da kai da tak’ama irinta Habib.

Bayan su Baba Lami sun fito ne.

Bilya ya k’arasa in da suke da saurinsa ya ce, “Yauwa Baba ya ce in shiga ko? “. Baba Lami cikin nuna rashin jin dad’in ta, ta ce, “ka yi hak’uri Bilya kasan yaron nan dama ba wai mutunci gare shiba, bai ganin kowa da Mutun ci, Wallahi ya hana. Sai dai ka yi hak’uri idan ya fito, ko in za ka kaishi wani gun”.

Bilya cikin d’an bacin rai ya ce, “Wallahi Baba Oga Habib na mulkamu yadda ya ke so, amma babu da muwa, ko mai nada lokaci, akwai lokaci”.

Baba Lami ta fiya su kayi bayan sun ba Bilya Hak’uri.

Bilya ko yana nan tsaye yana ganin fitowar Habib amma shiru, har akai Sallar azahar.

Bilya na nan tsaye kira yak’a shigowa wayar shi tai ringing, Bilya na dubawa yaga Number likitar ce, sosai gabansa ya fad’i dan k’aryarsa ta k’are.

Biya na d’auka ya ce, “Ki yi hak’uri dan Allah nima banso haka ta faruba, ko ba komai na k’arya alk’awarin da nai miki, amma Wallahi duk abinda kika ga ya faru ba laifina ba ne laifin Ogana ne, amma bari yanzu in turomiki Number sa, dan Allah ko kinkira bai d’aga ba karki gaji ki ta kira zai d’aga”.

Bilya na kashe kiran ya tura mata Number Habib.

aiko tana ganin Number ta danna mata kira, dan bata son yau ta sake kwana mata agida.

Habib ko na zaune a Office d’in shi yana aiki a laptop, kira ya shigowar shi.

Habib ko duba Number bai tsayiba ya ci gaba da aikinsa. Ita ko da yake taji abinda Bilya ya ce mata, hakan yasa taita kira.

Habib cikin jan tsaki ya d’aga kiran ya sa akunne, yana sauraran mai magana.

Ita ko likitar tana jin and’aga kiran ta ce, “Ranka shi dad’e dan Allah, kuzo ku amshi amanar da kuka ban dan Allah “. Habib cikin rashin fahimtar maganar, ya ce,”Wrong Number “. Yana fad’in haka ya katse kiran.

Likitar ko bata gaji ba k’ara kira ta yi, cikin b’acin rai ta ce, “Oh wai kunyi satar Yarinyar ne kuke tsoran asirinku ya tuni, koko ku ‘yan kidnappin…… “.

Habib cikin daka tsawa ya tsayar da ita, yana kunfar baka. Magana ya ke son yi ya kasa, kawai sai ya kashe wayar shi baki d’aya, dan shi harga Allah ya manta wata yarinya da suka kai hospital.

Bilya ko tunanin ko anda ce ne, yasa yakira, likitar dan ya ji yadda su kai da Habib.

Likitar cikin b’acin rai ta ce,ma Bilya “Karka rainamin hankali malam, yarinya kuma ku kuka sani, amma daga yau na gama kwana da ita”.

Bilya hak’uri ya ba likitar sosai sannan ya ce, mata,”Wallahi ba maganar wasa gobe zai yi samma kon zuwa kano d’in “. Ai ko haka akayi Bilya tun da daddare ya nemi permission gurin Ogan shi, akan tafiya kano.

Washe gari da wuri Bilya ya tafi kano, hakan yasa 12:00pm a kano tai mai.

Bilya bacin ya biya likitar hak’uri Sosai ya ba ta.Sannan ya zauna yana jiran fitowar ‘yar tsuntuwar tasu, shiga Ogan shi, wanda shi ya ma manta da batunta.

Bilya na nan zaune ‘Yar tsuntuwar su ta fito sanye ta ke da wata doguwar riga ta atamfa wadda likitar ce ta bata dan ganin bata da kaya, yasa likitar ta bata a tamfar.

Bilya kallanta ya yi, sannan ya ce, ” ‘Yan mata ke ‘Yar wana gari ce, yanzu in kaiki gidan ku, dan mu ahanyar mu ta zuwa kano muka tsince ki”.

Matashiyar budurwar da bazata haurama shekara goma sha bakwai ba.

Cikin siririyar muryarta ta ce, “Ni marainiya ce, bani da kowa, dan Allah ka tai ma ke ni”.

Bilya da tausayi ya ke kallanta, dan shi aganinshi tabbas marainiyarce. Bilya shiru ya yi, dan yasan bai da in da zai kaita.

Ito ko Yarinyar ganin Bilya ya yi shiru alamar ba zai tai maka mata ba, ya sa, ta ce, “Dan Allah katai makan Allah banda kowa”.

Bilya cikin tausaya mata ya ce, “zan tai make ki ki, amma tai makon ba mai tsawo bane, zan tai make ki ne kafin Hajiya turai ta dawo,kuma ni ba nan nake ba Abuja nake kin yarda zaki bini?, Sannan kuma duk sanda Hajiya turai ta dawo zaki kama gabanki , kin yarda? “.

Da sauri ta ce, “Eh na yarda na godee.

Bilya tashi ya yi Yarinyar na binshi aba suka je in da ya yi parking d’in motarsa da Ogan sa Habib ya yi masa kyautarta, suka tafi. Suka kama hanyar Abuja .

Kasan cewar Bilya yana gudu sosai da mota, hakan ya sa, ana Sallar magriba suka shiga gida.

Allah ko ya tai maki Bilya sosai dan lokacinda suka shiga ba kowa, duk ‘yan aikin gidan sun shi cikin gida, hakan yasa tana fitowa daga mota Bilya yaja hannunta da sauri ya kaita d’akin shi. Dan yasan gidan cike ya ke da magulmata.

Bilya dama tun kafin ya iso ya kira Baba lami ya yi mata bayanin ko mai, hakan yasa Bilya na isowa ya kira Baba Lami ya sanar da ita sun iso.

Baba lami na shiga d’akin Bilya.

Bilya ya kalleta ya ce, “Tom Baba kin san dai yadda gidan nan ya ke, Baba lami ga Yarinyar nan, dan Allah ta zauna gunki kafin Hajiya turai ta dawo”.

Baba lami batare da taima Bilya magana ba, gudun matsala dan ba wani lokaci sosai,Baba Lami taja hannun ‘Yar tsuntuwar ta yi d’akinta da ita da sauri.

Bayan sun shiga d’akine Baba Lami ta kalli Matashiyar budurwar ta ce, ” ‘Yan mata ya sunan ki? “. Cikin sanyin murya ta ce, “Sunana Hassana”.

“Yauwa Hassana dan Allah ki yi zamanki nan, karkisake ki fita waje, muta nan gidan nan magulmata ne, dan Allah ki kula, kafin Bilya ya samarmiki gurin zama”.

Sosai Baba Lami ke k’ok’arin b’oye Hassana.

Sai dai kash abinda Baba bata sani ba, aminiyarta wadda su ke aiki tare da ita da kanta ta kira Hajiya turai ta kai gulmar Lami ta kawo wata bak’uwar yarinya agidan, kuma abisa lurar da ta yi, Bilya ne zazo da Yarinyar ya ba Baba Lami ita”.

Hajiya turai ko, sosai hakan yab’ata mata rai, acewar ta ba laifin Bilya ba ne, lafin Oga Habib ne, saboda shi ya ba Bilya damar shigowa kai tsaye gidan.

Hajiya turai ranta ad’an b’ace takira Habib awaya.

Habib ko lokacin yana zaune a office d’in shi na SANAT YOGHURT, kiran Mahaifiyar shi abin soyuwa a zuciyar, ya shigo wayar shi

Habib cikin kirarin da ya saba yi ma Mommy shi, ya d’aga kiran ya ce, “Sai Mommyna ni kad’ai Allah ya k’arami lafiya, lafiya dai ko wannan kira haka a wannan lokacin? “.

Hajiya turai cikin basar da zancen Habib d’in ta ce, “Habib wacece ta ke zaune a gida”.

Habib cikin rashin fahimtar abinda Mahaifiyarta shi ta ce,ya ce, “Mommyna bangane maganarki ba”. “Habib za kai min maganarta ka ko ta banza, tom wacece aka ce min Bilya ya kawo gidan da zama?, Habib ni fa ina tsoran abinda ya faru ne ya sake faruwa”.

Habib cikin kwantar ma Mahaifiyar shi hankali, dan yaga alamar ta tsorata sosai da abinda ya faru Kwanakin baya.

Habib cikin sanyin muryar shi, ya ce, “Mommyna Allah ban san da zaman kowa ba, amma ki bari zan yi bincike yanzu”.

Hajiya turai kashe wayarta ta yi.

Habib ko Mahaifiyar shi na kashe kiran, ya kira Number Bilya. Bilya na d’agawa Habib ya ce, “Bilya da kai da wadda ka kawo da kuma wadda ka ba ajiyarta, kuzo yanzu”.

Cikin bilya sai da ya yi k’ara jin abinda Habib ya ce, hakan yasa da sauri ya bar SANAT YOGHURT, ya koma can gidan Habib d’in.

Bilya tun kafin ya isa yakira Baba Lami awaya ya ce su had’u wajan get harda Yarinyar da yabata ajiya.

Bilya na zuwa suka ya iske Baba da Hassana wajan get d’in suna jiranshi.

Bilya kallan Baba ya yi, ya ce, “Baba Wallahi ban tab’a ganin muna fukai ba kamar ‘yan aikin gidannan ba, yanzu wai har an samu wanda ya kaima Oga Habib gulmar zaman Yarinyar nan agidannan, yanzu haka yana nai manmu mu dukanmu”.

Baba lami dafe k’irji ta yi, ta ce, “Bilya kasan Allah yaron nan korarmu zai yi”.

Bilya kallan Baba Lami ya yi, ya ce, “Baba ni ba abinda ke damuna ba yanzu kenan”.

Bilya a motar shi ya d’auki su Baba, zuwa SANAT YOGHURT.

Koda suka shiga wajan Hassana kallan sunan da ke d’auke da tank’ameman Company ta ke, da kuma tsaruwa irin ta gurin, ko ina ‘yan akine sanye da Uniform d’in su green and orange .

kasan cewar Habib ya san da zuwan su Bilya , hakan yasa kai tsaye suka shiga tank’ameman Office d’in Oga Habib.

Habib na zaune yana ta aikinsa a laptop d’in shi, yana jin su Bilya amma yaci gaba da aikinshi. Habib sai da yagama abinda ya ke yi, sannan ya d’ago kai yana kallan su d’aya bayan d’aya.

Habib mai da kallan shi ga Bilya ya yi, ya ce…………………..

 

 

 

 

Labari ne mai cike da CAKWAKIYA, ku dai ku bini asannu zaku fahimce ni nan gaba kad’an

 

 

 

DUk mai son kasan cewa a group d’in Oga Habib.Tom Comment dole ne ‘Yar’uwa.

 

 

In kinkaranta daure ki Comment.

 

COMMENT PLEASE

 

OGA HABIB

Ba kowane lokaci ne mutane za su fahimce ka ba. K’aramar k’wak’walwa ba ta gane manyan kalamai. Babban kifi sai babbar gora.

Allah kasa mu dace.

 

 

 

 

Shafi na 6&7.

 

 

 

 

….. Bilya wacece wannan?, Habib ya yi maganar ba alamun fara’a a fuskar shi.

Bilya cikin girmamawa ya fara magana, kamar haka, “Oga Habib ita ce Yarinyar da muka tsinta, kace in d’akko ta ranar da muka je kano”.

Habib wani banzan kallo ya yi ma Bilya, sannan ya ce,cikin fad’a-fad’a ” da nace ka d’akkota sai kuma nace ka kaita gidana!? “.

Bilya cikin alamun ban hak’uri, ya ce, “ka yi hak’uri Oga Habib, na aikata kuskure, insha Allah haka bazai sake faruwa ba”.

Habib banza ya yi da Bilya yaci gaba da typing d’in sakon da ya ke yi, a laptop d’in da ke gaban shi. Habib sai da yagama abinda yake yi, duk su Bilya na tsaye suna jiran sakamakonsu. Sannan ya d’ago kai ya kalli Bilya ya ce, “Bilya daga nan karku koma min gida ku dukanku”.

Bilya cikin tsorata da jin kalaman Oga Habib, duk da dai yasan zai iya ai kata hakan,Bilya ya ce, “Oga Habib dan Allah k…….. “.

Habib hannu ya d’agama Bilya, sannan ya nuna masu k’ofar fita”.

Baba Lami da sauri ta k’araso in da Habib ya ke, ta ce, “Oga Habib dan Allah ka yi hak’uri munsa…. “.

Habib ranshi a d’an b’ace ya nuna ma Baba lami k’ofa ya ce, “Baba dan Allah ku fitarmin Office! “.

Baba lami fita tayi tana mai da nasanin amincema Bilya da ta yi ta amshi Hassana, gashi abin ja mata kurarta aiki.

Bilya ya je dai-dai k’ofar fita ya tsaya, cikin taushin murya raunanna, ya ce,”Ka yi hak’uri Oga Habib da abinda zan ce maka. Oga Habib amma da kasan bazaka taimaki yarinyar ba, da baka sani na d’akkota ba, Oga Habib sanin kankane bani da gida, ni ba d’an garinnan ba ne, yanzu da kakoreni ina ita zan kaita?, da ace mun barta a’inda muka ganta da Allah zai kawo wanda zai tai maketa, amma mu tai makon da mu kai mata ya zamana bashida amfani. Oga Habib ita fa mace ce,Idan munbarta tatafi ina zata?, Oga Habib dan Allah ina rok’onka dan Allah idan ka koreni tom ita dan Allah ka yi k’ok’ari ka ci ka aikin alkairin da ka yi niyyaryi tun farko akanta. Inda dama kai kayi niyyar taima kon….”.

Habib katse Bilya ya yi, alamun ranshi ya fara b’aci da magan-ganun Bilya. Ba kamar maganar shi ta k’arshe ba, wai dama shi ya yi niyyar taimakon ta bashi ba. Habib wani banzan kallo ya yi ma Bilya sannan ya ce, d’an zafafe, “Bilya ni na ce maka zan taimaketa?, dama da nace ma ka ka d’auketa sai aka cema hakan na nufin agidana zata zauna kenan!? “. Habib ya tambayi Bilya cikin d’aga murya.

Bilya shima da yake sosai Habib ya b’ata mai rai, cikin k’ok’arin danne fushinshi, dan yasan in dai ya ce zai sa fushi tom Habib ba zai ya yi abinda ya ke so ba, gara ya yi hak’uri ya danne fushinshi. Hakan yasa Bilya cikin danne fushinshi ya ce, ” Oga Habib hak’uri za kai ka tai maka mata, dan na tambayi yarinyar garinsu in kaita, ta ce min ita marainiya ce, shine ma dalilin da yasa nakaita gidanka”.

Habib cikin had’e rai ya ce, “Sai aka cema kuma shi maraya bashi da ‘yan’uwa, kira min yarinyar”.

Bilya fita ya yi, ya iske Baba Lami da Hassana tsaye.

Baba Lami kallan Bilya ta yi, ta ce, “Bilya ya hak’ura ne? “. “Hmmm Baba wannan ne zai hak’ura da wuri haka bai wahalar da mutane ba. Ni Baba Lami dama abinda ke damuna wannan yarinyar ya nuna Hassana da ke tsaye, kuma shine yasa ni taimakonta, shine na ke son yasan yadda zai yi da ita inda shi ya yi niyyar tai makon dama bani ba, shine yanzu da nai mai complain akanta, shine ya ce in kira mai ita”.

Baba lami kallan Hassana ta yi, ta ce, “Je ki kinji Allah ya tai make ki, yabarki. Baba lami mai da kallanta ta yi ga Bilya ta ce, ” Bilya mufa? “.

“Baba Lami ki rabu da shi kinji, ni na san yadda zan mai, Hajiya turai ta yarda da ni sosai, kuma kinga kema ta yarda da ke, shiyasa ta zab’eki da ki rik’a yi ma Oga Habib girki, dan haka ki bari kawai nasan yadda zanyi, Allah dai yasa in nakirata ta d’aga”.

Ameen Baba Lami ta ce.

Bilya kallan Hassana ya yi da har yanzu ta ke tsaye ta k’i tafiya, ya ce, “Je ki Office d’in ce inda muka fito yanzu”.

Hassana ko da bata fatan k’ara ganin Habib, kallan Bilya ta yi, ta ce, “Dan Allah ni dai kutai dani inda zaku, ni bana son zuwa dan Allah “.

Bilya dariya ya yi, dan yaga alamar ta tsorata da Habib sosai. Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce, “kinga ni yanzu haka nasan ni da Baba zai mai da mu, saboda Mahaifiyar shi tana son mu, da ma ke nake ji, inda bazasu yarda ba ki zauna agidansu, dan yanzu suna tsoran bak’o saboda abinda ya faru da su kwanakin baya, ki yi hak’uri ki je, idan Allah ya taimaka, duk da Oga Habib shegen mutum ne, k’ila ya barki”.

Hassana a tsorace ta tura Office d’in Habib ta shiga, dan ita bata son wulak’anci kuma ta lura OgaHabib irin masu wula k’anta mutanan nan ne, saboda kud’insu.

Habib na zaune yana mai cigaba da typing d’in da ya ke a laptop d’in shi, kayan da za’a kawo masu ne ya ke ta aikin lissafawa. Habib na zaune ya ji anturo k’ofa anshigo ba naiman izini ba komai. Habib d’ago kai ya yi yana mata kallan baki da hankali ne, Banza Habib ya yi da ita, ya ci gaba da typing d’in shi ya barta nan tsaye.

Hassana ko magana ta ke son yi tana tsoro dan taga Bilya ma yana mai fad’a bare ita. Hassana jin ya yi banza da ita babu alamunma zai gama abinda ya ke yi bare har ya yi mata magana. Hakan yasa ta ce,cikin rawar murya, kamar yadda ta lura kowa na cewa, “Oga Habib dama Oga Bilya ne ya ce min kana kirana”.

Habib ko cigaba da aikin da ya ke yi ya yi kamar bai jita ba, bamu ma wata ala da ta nuna mata yaji abinda ta ce, hakan yasa ta kuma cewa, “Oga Habib dama Oga bilya ne ya ce min inzo kana son gani n…… “.

Tsawar da Habib ya yi mata ce yasa ta yi shiru, cikin d’aga murya Habib ya nuna ta da d’an ya tsa, ya ce, “get out from my Office “.

Hassana fita ta yi jikinta na rawa, dan sosai ta tsorata da tsawar da Habib ya yi mata.

Hassana inda tabar Baba lami da Bilya ta je, amma bata gansu ba. Hassana guri ta samu ta zauna ta yi shiru kamar za tai kuka, tabbas tun yanzu da ba aje ko ina ba, ta fara da na sanin barin gida. Hassana na nan zaune tana kallan ma’aikan gurin kala-kala sai aikinsu suke, can wani d’aya daga cikin staff d’in gurin wanda tun d’azu ya lura da Lokacinda Hassana ta fito daga Office d’in Oga Habib. Inda Hassana ta ke tsugunne ya zo ya sameta, kallan Hassana ya yi, ya ce, “Bai war Allah lafiya kuwa? Nalura da ke tun d’azu keke gurinnan. Idan aiki kika zo naima aiba Office d’in Oga zaki ba, gurin manager zaki”.

Hassana d’aga kai ta yi tana kallan shi, sannan ta ce, “Ni ba aiki nazo naima ba, amma inna samu aikinma zan yi”.

“Ok, amma dan Allah ko zan iya sanin mekika zo naima, in ba aiki ba? “.

Hassana kallan shi ta yi, sai taji bata da zab’i kamar ta fad’a mai, inda taimo ta ke naima k’ila ya tai maketa. Hakan yasa Hassana ta kallai, ta ce, “Bansan kowa ba a nan Abuja, su Oganku suka tsinceni ahanyarsu ta tafiya kano,suka kawo ni nan, shine yanzu shi Wanda ake kira da Oga Habib, wai bazan zauna agidan shiba, shine shi Oga Bilya ya ce in je Office d’in shi ya na kirana, tom na je kuma ya Koreni”.

murmushi ya yi, staff d’in nan, ya ce, “Bilya ai ba wani bane staff ne kamar kowa anan, dan dai shi yana driving d’in Oga Habib ne, kuma in dai Oga Habib ne ya ce yana kiranki a Office d’in shi zai saurareki, sai dai in da kika je ne, kin mai ba dai-dai bane. Kuma maganar gaskiya in ma komawa kikayi ki mai magana kan ya d’aukeki aiki, amma maganar gaskiya Oga Habib ba zai kaiki gidan shiba, dan gidansu akwai tsaro sosai. Idan harshi ya ce kije, ki tashi ki koma ki je zai saurareki, in da yasan da zuwanki”.

Hassana tashi ta yi ta nufi office d’in Oga Habib, saboda bata da zab’in da ya wuce ta tashi ta je d’in.

Staff d’in nan kallan Hassana ya yi da tausayawa, dan mata masu ajima Oga Habib ba saurararsu ya ke ba bare ita.

Habib na zaune yana waya da Mommynshi, Hassana ta yi sallama ta shigo.

Habib kallo d’aya ya yi mata ya d’auke kanshi ya ci gaba da wayar shi. Jinai Habib na cewa, “Mommyna dan Allah ki barsu kawai, idan mutum na laifi irin haka ya kamata ai funishiment d’insa. Banajin abinda akecewa daga can b’angaran, sai dai naji Habib ya ce, “Ok, Mommy zasu dawo, amma ni idan tanine ma nafi son inyi driving d’in kaina. Abinci kuma ki rabu da Baba Lami inda ga Baba dije nan”.

Mahaifiyar Habib sosai ta nuna ma Habib in dai bai dawo da su bilya ba ranshi zai b’ace. Tana kaiwa nan ta kashe wayarta.

Habib ranshi b’ace ya kira bilya awaya, kira d’aya bilya ya d’aga, yana d’agawa Habib ya ce, “Bilya kazo Office d’ina yanzu”.

Habib mai da kallan shi ya yi ga, Hassana da ke gefa tsaye arakub’e.

Doguwar rigar da Likitarnan ta bata ce har yanzu ajikinta, sai wani haif hijab da tasa.

Habib d’auke kai ya yi daga kallanta, sannan bazato ba tsammani Hassana ta ji ya ce, “Ke ‘yar wata jaha ce?,kuma me yarabo da ke daga gidan ku? “.

Hassana kallan Habib ta yi taga ba’ita ya ke kallo ba hankalinsama akan laptop d’in gabansa ya ke, ba akanta ba. Hassana muryarta na cracking ta ce, “Ni yar kano ce, mamana da babana duk ‘yan jahar kano ne, Babana nada mata biyu. matar Babana tana da fad’a sosai, kuma macece mai son kanta da yawa. Babana tunda ya auri mamana Allah bai bata haihuwa ba, hakan yasa kakata wato Mahaifiyar Babana ta matsama Babana ya k’ara aure. Babana ya auri Umma Rabi ba dad’ewa Allah ya bata ciki ta haifi Aunty jamila, sai da Umma Rabi ta haihu uku sannan Allah ya ba Mamana cikina, tom kuma itama Umma Rabi lokacin tana da ciki, kusan tare sukayi rainon ciki ita da Mamana. Mamana ta haihu da kwana biyu Umma Rabi ma ta haifo yarinyarta mace. Hakan yasa Babana ya ce, sai dai ahad’a sunan mu.

Tom Mamana dama tunda ta haifeni bata da isassar lafiya, hakan yasa kwanana biyar aduniya Allah ya yi ma Mamana rasuwa. Babana sosai hankalinsa ya tashi da mutuwar Mamana saboda yafi jin dad’in zama da ita fiye da Umma Rabi. Tom mamana da ma ita ma ita kad’aice awajan Iyayanta kuma Allah ya yi masu rasuwa dad’ewa, hakan yasa Babana badan ya soba sai dan bashi da yarda zai yi ya d’auke ni ya ba Umma Rabi ni, ya ce ta had’amu ta shayar damu tare da ‘yarta.

Da da farko Umma Rabi ta Nuna ma Babana baza amsheni ba, amma sai Babana ya nuna mata dole ta amsheni, in da bai san Wanda zai kai ma niba. Hakan yasa dole Umma Rabi ta amsheni. Ranar suna Babana ya sa mana Hassana da Usaina ni da yarinyar Umma Rabi. Nasha wahala sosai awajan Umma Rabi dan ko kuka nake sai taga dama ta ke ban nono insha. Kuma koda zan riga Usaina tashi in dai Usaina ta tashi tom Umma Rabi sai ta d’auki Usaina ta lallasheta ta yi shuru sannan koda zata kulani.

Ahaka har muka girma. Tunda nafara wayau na fahimci Umma Rabi tafi son Usaina akaina. Babana dawuri ya samu Islamiya, ita Usaina bata cika zuwa ba saini, saboda ni kona ce ba zani ba dole za’a turani. Tun ina ‘yar k’arama ta na iya duk wani aikin gida, dan hatta wankinmu Nida Usaina ni ke mana, acewar Umma Rabi ni ce babba.

Babana duk lokacin da zaizo gida ya iske ina aiki sai yi ta fad’a ya ce Usaina tazo muyi tare. Wannan abinda da Babana ke yi shiya k’ara jawo min tsana sosai gurin Umma Rabi.

Ahaka rayuwa taita tafiya har muka girma , muka shiga secondary school. Tom da akwai wani teacher mu, wanda ya ke kula da duk abinda ya shafemu Nida Usaina, sai dai yana yawan yi min complain, akan wai Usaina ta fi ni tsafta, ni dai ban tab’a fad’amai wani abuba game da gidanmu, shine ya tsinto labari acikin gari. Tunda teacher Kabir ya tsinci labarin halinda nake, ya zamana yake yawan yimin kyautar kud’i. Sosai teacher Kabir ke min hidima hakan yasa har Babana ya sanshi.

Muna gama j. S. E. Babana ya ce, bazamu cigaba da karatuba aure zai mana. Tom dama ita Usaina akwai wini dake zuwa gunta harma ya yi ma Babana magana, ni kuma dama teacher Kabir shike Sona shima ya naimi izini gurin Mahaifina ya kuma bashi. Lokacin da Babana ya je ma da teacher Kabir maganar ya turo manyasa gidanmu ai maganar aurena da teacher Kabir . Teacher Kabir rok’on Babana ya yi akan dan Allah ya barni in kamma secondary school sannan. Kasan cewar Babana na son tarayyata sosai da teacher Kabir yasa ya yarda da abinda teacher Kabir ya ce. Koda Babana ya kaima Umma Rabi maganar saina kamma secondary school sannan za ai aurena, cewa ta yi itama Usaina abarsa sai ta kammala sai ayi duka tare. Aiko haka akayi. Muna S. S. S 3 first term, Babana ya sa ranar aure na da Teacher Kabir. Ita kuma Usaina da wani Jamilu d’an layinmu. Umma Rabi bata son tarayyar Jamilu da Usaina ko ka d’an bakamarma da taga teacher Kabir na min hidimaba sosai, ita kuma Usaina babu abinda ke shiga tsakaninta da Jamilu na kyauta. Da akwai wata rana teacher Kabir ya kawo min waya. Wannan kyautar da ya yi min tab’ata ma Umma Rabi rai sosai,hakan yasa tace sai dai in maida mai wai in ya auran ya sai min agidansa. Babana koda yazo yaji abinda Umma Rabi ta ce hanawa ya yi in maida ma teacher Kabir wayar shi”. Hassana shiru ta yi, tana goge hawayanta saboda wani kuka da ke son k’wace mata, saboda tunowar rabuwarta da teacher Kabir ta k’arshe da ta yi.

Hassana cikin murya mai kama da ta kuka taci gaba da magana kamar haka, “Ranar da bazan mantataba arayuwata, ita ce ranar wata laraba, Iyayan teacher Kabir suka zo gidan mu wai d’ansu Kabir ya janye maganar auran shi dani ya mai da ta kan Usaina. Bani ba har Babana ya girgiza da jin haka, mamaki da al’ajabi suka cika shi, saboda shi kanshi asanin kanshi Kabir bama sa wani jutuwa da Usaina, sai yau rana tsaka wai ace Kabir ya janye maganar auran shi da Hassana ya maida kan Usaina. Babana cema Iyayan teacher Kabir ya yi tom su bari zaiji daga bakin Kabir d’in sannan. Aiko haka akayi Babana kiran teacher Kabir ya yi ya tambayai ya akan maganar da Iyayanshi suka zo da ita”.

Bud’ar bakin teacher Kabir sai cewa ya yi, “Eh hakane shi Usaina ya ke so”.

Wannan maganar sosai ta d’aga hankalin Babana. Washe gari da safe Babana ranshi b’ace ya je d’akin Umma Rabi. Babana nazuwa ya kalli Umma Rabi, ya ce, “Rabi ina son kisan wani abu duk k’ula-k’ular da kika yi, ki ka maida auran Hassana ya koma kan ‘yarki tom tun wurima ki warware shi, dan ni bazan tab’a aura auran Usaina da Kabir ba, garama kisani tun wuri.

Haka Babana ya gama fad’anshi Baba Rabi bata tanka mai ba.

Abu kamar wasa yazo ya zamana gaske, dan teacher Kabir idan yazo gidanmu sai inga Usaina taje suna hira, ni ko ko gaisuwata baya amsawa. Abin ya daman Sosai, hakan yasa na kaima Babana k’arar teacher Kabir. Babana kallona ya yi cikin alamun tausaya min, dan ya lura ina son teacher Kabir sosai. Hakan yasa Babana cikin lallashi, ya ce, “Hassana kinsan dai wani baya aurar matar wani ko?, haka kuma wata bata auran mijin wani, inji hausawa sunce matar mutum kabarinsa. Tom Hassana dan Allah karki tambayan dalili dan nima ban sani ba, amma ina so ki hak’ura da Kabir “.

Wannan magana da Babana ya fad’a ji nai kamar ya lumamin wuk’a azuciya, dan Allah ya sani ina son teacher Kabir sosai, kodan shine saurayina na farko.

Kuka na fashema Babana da shi jin abinda ya ce.

Babana duk wata magana mai dad’i da zai fad’amin wadda zata sa in yi shiru ya fad’amin, amma ina na kasa. Sosai kukana ya d’agama Babana hankali. Ni ko kafin kace me sai ciwan kai tsabar kukan da nayi haka kaina ya yi ta min ciwo. Aranar dai da ciwan kai na kwana.

Iyayan Kabir ko sun yi ake kamar me akan Babana ya maida auran Hassana da Kabir kan Usaina ya k’i.

Umma Rabi ko ganin Babana yak’i amsar maganar Usaina da Kabir, yasa taturasu wajan k’aninta. Tom da ya ke shima k’anin nata gashi ga irin shi. Hakan yasa batare da binciken komai ba, ya amshi maganar, nan dai ya yi jagoranci aka tsaida ranar auran Usaina da Kabir, wata biyu masu zuwa.

Wannan ranar nayi kuka kamar raina zai fita. Wannan kukan da nayi sosai ya tadama Babana hankali. Kafin kace me hawan jinin Babana ya tashi. Washe gari da safe shiri-shiru Babana be ne meniba. Hakan yasa na lallab’a na tashi dan kaina sosai ya ke min ciwo. Ina tashi d’akin Babana natura nashiga. Ganin Babana kwance kuma harna tura d’akin bai tashi ba, yasa na k’arasa gun shi ad’an tsorace. kiran sunan Babana nayi ina bubbuga k’afarshi amma shiru. Kuka na fasha dan duk da ban san Mutuwa ba jikina ya bani kamar babu rai ajikinsa. Babana ya tafi yabarni yatafi in da bazan sake ganinsa ba. Haka akai zana’izar Babana.

Nayi kuka sosai dan Babana shine abokin shawara, shine abokin firata idan yana gida, shine wanda abu in yasaman nake fad’amawa sai ko teacher Kabir, tom shima anrabani da shi.

Bayan wata d’aya da rasuwar Babama, abubuwa sun cakud’e min, ga aiki na gidan duk ni ke yi, wanke-wanke, shara, girki, wankin kayan mu.

Ana gobe d’aurin auran teacher Kabir da Usaina na gudu saboda zuciyata bazata iya jure ganin auran teacher Kabir da wata ba, ba ni ba…………

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment