Littafan Hausa Novels

Ni Matar Sa Ce Hausa Novel Complete

Siffofin Mace Mai Ruwa
Written by Hausa_Novels

Ni Matar Sa Ce Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

NI MA MATARSA CE

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

( YAR GIDAN IMAM )

BABI NA ARBA’IN DA BIYAR

**********

Mallam kallah ya saki salati Yana janyo Mallam Umar Yana fadin ” shigo sosai Ka ga abinda yar taka take aikatawa, ai dama barewa bata gudu danta yayi rarrafe Ka dai gani ko”.

 

Idanun Mallam Umar suka tsayu Kan muhseena wacce take ta kokarin tashi amma ta kasa.

Bakinta ahankali yake furta ” Baba abinda kuke zato bashi bane, bansan Shi ba babu abinda ya hadani da Shi, Nima farkawa kawai nayi na ganni a dakin nan na rantse bansan inda nake ba”.

 Kishi da Aljana Hausa Novel Complete

Mallam kallah da sauran mutanen su kayi Kan Taufiq cikin fusata suna tambayar me kayi Mata ?. Ayayin da Mallam Umar jiri ya shiga dibarsa yayi saurin jingina da jikin bango.

 

Cikin tashin hankali Taufiq ya Fara kokarin kare Kansa Amma mutanen gurin sun hana Shi damar yin hakan .

.maimakon hakan ma sai ingiza keyarsa sukayi cikin fada da karaji.mallam kallah ya dubi Mallam Umar yace ” mun wuce wajen megari kana iya taho da muhseena itama, domin ba zamu taba barin wanna shegantakar ba , abinda su keyi a birni ne zasu zo suna mana a kauye, idan bamu dauki mataki ba duk a haka zasu Gama bata mana yaran kauyen”.

Yana Gama fadin haka ya bi bayan su Mallam Hakilu Yana cigaba da fada da sababi.

 

Sai bayan tafiyar su ne Mallam Umar ya zubama muhseena Ido ,Yana kokarin lafarma da zuciyarsa radadin da take.

 

A sanyaye ya Matso kusa da yarsa idanunsa jajir saboda damuwa, yace ” muhseena ki ji tsoron Allah ki gaya min gaskiyar abinda ya faru makaranta kika tafi ta yaya kika kare anan?, Ina da kyakkyawan zato akanki Bana Jin zaki iya aikata abinda bai kai wannan ba balle wannan al’amarin da kika fi kowa sanin illarsa ta yaya kika shigo dakin nan”.

 

Ta kasa tsaida hawayen da tuni ya ke zuba Mata ta dube Shi sosai cikin zubar hawaye tace”Dana aikata abinda ake zargi na rantse Baba gara na mutu, domin idan akwai abinda na tsana arayuwata to zina ce, don Allah Ka yarda da ni bansan lokacin da na zo dakin nan ba bansan komai ba,”.

 

Ta cigaba da kuka tana fadin “Ràshin lafiyar da na tashi da ita tun safe ce ta matsa min a makaranta na kasa sukuni shine Mallam ya Bani izinin komawa gida, to ina cikin tafiya bansan inda Kaina yake ba na dai ji na daina gani daganan ban Kara Jin komai ba ban Kara sanin komai ba sai farkawa nayi na ganni a wañnan dakin wannan mutumin ya na shafa min ruwa a fuska “.

 

Mallam Umar ya dade Yana kallon gaskiyar zancen ta a cikin kwayar idonta, yasan yarsa yasan halinta hakika yasan ba zata taba aikata abinda ake zarginsu da aikatawa.kamar yadda yake ji aransa Shi Kansa Taufiq din ba zai aikata wannan ta’addancin ba ga muhseena.

Domin tun haduwarsu ta farko Wanda daga Shi ba su Kara haduwa ba ya gamsu da natsuwa da kamalar yaron.

Ya dubi muhseena jigatar ciwo ta bayyana sosai a fuskarta . Yace ” ki yi shuru ki daina kuka na yarda da duk abinda kika gaya min domin nasan ba zaki taba yi min karya ba”.

 

Ta Kara fashewa da kuka tace ” na ji saukin damuwata Baba tunda Ka yarda da ni duk abinda wani zai dauka bazan taba damuwa ba,”

 

Mallam Umar ya umarceta da ta kokarta ta tashi su tafi. Daker ta iya tashi suka tafi alokacin sauran masu hayar gidan suka Fara dawowa duk Wanda ya wuce sai ya juyo ya Kara kallon su muhseena.

 

Mallam Umar ya fahimci muhseena tana cikin jigatar ciwo da yayi niyyar su wuce gida amma ya ji tsoron sharrin su Mallam kallah hakan yasa su Ka wuce wajen megari.

Suna zuwa daker muhseena ta samu waje ta zauna jiri na kwasar ta. Sun tadda takaddama da hayaniya tayi yawa daker megari ya samu su kayi shuru.

Zuwa lokacin duk inda ran Taufiq ya Kai to fa ya baci sosai ya Fara Jin danasanin taimaka ma muhseena da yayi haushi da takaicin yadda mutanen garin ke kokarin Dora masa mummunan zargin da Bai aikata ba Bai da wata niyya da ta wuce na taimakon muhseena.

Amma ana neman a dora masa mummunan kazafin da zai iya bata dukkan wani kyakkyawan halinsa. Haka zalika mutanen garin kokarin dole sai ya yarda ya Kuma karbi lefin da bai aikata ba.

 

Taufiq yayi gaggawar kallon muhseena yace cikin daburcewa da damuwa ” ke bauwar Allah ki Fadi tsakani da Allah nayi miki wani abu” da sauri ta girgiza Kai tace ” Bansan komai ba saboda bana cikin hayyacina amma nasan koma meye ni babu abinda ya shiga tsakanina da Kai ,”.

 

Mallam Hakilu ya daka Mata harara yace ” ke da Allah can , ai dama dole ki Fadi haka saboda ki Kare barnar da kuka aikata, to Baki isa ba babu Wanda ya isa ya zo garin mu ya cimu da yaki”.

 

Mallam Umar ya daga masa hannu yace ” Don Allah Ku bar wannan maganar Ina son na Kai yata asibiti saboda bata da lafiya, duk Kuma wannan maganganun da kuke yi babu gaskiya a cikinta abinda muhseena da Taufiq suka fada gaskiya ne na Kuma yarda na gasgata su”.

 

Taufiq ya lumshe idanunsa saboda dadin maganar Mallam Umar, domin duk wajen Shi kadai ne ya Fadi abinda yake son ji.

 

Mallam kallah ya sakar ma Mallam Umar wata irin harara, sannan yace “Don Allah Mallam Ka dawo hayyacinka lokaci yayi da zaka daina mara ma mara gaskiya baya harka bashi mafaka, kana kokarin boye gaskiya Ka tusama mutane karya a zukatansu kamar yadda kayi alokacin matsala irin wannan ta mahaifiyarta, Ka dage dole saika wanketa Akan laifin da ta aikata, to ayau ba zamu yarda ba”.

Ya juya ya dubi megari yace ” megari kaji koken mu Ka taimaki mutanen garinka , Ka taimaki tarbiyyar yayan mu, kayi hukuncin da muka roka kawai wannan yaron ko yaki ko ya so sai ya auri yarinyar nan a yanzu ba sai anjima ba domin ta hakane kadai zamu kawo karshen wannan keta haddin da mutanen birni sukema yayanmu domin idan aka barshi na rantse sun dinga cigaba da aikata hakan Kenan yanzu kuwa idan akayi hakan zai Zama ishara ga masu son aikata hakan nan gaba”.

 

Nan da nan muhseena taji ta wartsake daga ciwon da take yi, domin Jin wannan maganar me kama da mafarki a daura musu aure? Ta tambayi kanta.

Mallam Umar ya dubesu yace ” wace irin magana ce wannan”. Taufiq shima ya Kara gyara tsugunonsa cike da tashin hankali yace ” Ta yaya Zan auri yarinyar da ban sani ba babu wata alaka a tsakaninmu”.

Megari yayi masa wani kyakkyawan kallo yace ” Rufe min baki mugu, babu wata alaka atsakaninku amma aka tsintota a dakinka, maganar banza kawai wa zaka maida kananan Yara, “. Ya juyo itama muhseena ya watsa Mata harara yace “Wa zai karbi shaidarki bayan bakinku daya meya kaiki dakinsa idan ba dama kun Saba aikata Masha’a ba, idan an tura ki makaranta sai ki wuce dakinsa ko, ai Baki yar akasa ba”.

 

Mallam Umar ya ce” megari kayi ma maganar nan kyakkyawan bincike…? Kafin ya karasa magana megari ya katse shi ” kaima ban son Jin komai daga gareka saboda yarka zaka kare, ni nine Zan yanke hukuncin da ya dace Kuma dole abi abinda na zartar”.

 

Zuwa lokacin kuka muhseena take me karfin gaske tana rike da kanta tana fadin ” innalillahi wainna’ilaihirrajiun”. Shi Kuma Taufiq gaba daya gumi ya Gama jike masa Riga ya Fara tunanin wace mahallaka ya kawo Kansa wace irin kaddara ce yau zata fada masa.

Ya daga idonsa gefensa mutanen gari ne daya gefen ma haka dukkan su a fusace suke sosai yake ji aransa babu abinda ba zasu iya yi masa ba.

 

Daker ya Bude Baki yace”Don Allah Ku yi hakuri na rantse babu abinda ya shiga tsakanina da ita taimakonta kawai nayi”

Itama cikin kuka tace “Nima na rantse babu abinda ya shiga tsakanin mu don Allah Kada Ku yi mana mummunan hukunci”. Mallam kallah ya daka Mata harara yace ” ki rufe min Baki ko na zuba Miki Mari”.

 

Megari yace ” fito da kudin aljihunka” cikin tsuma ya sa hannu a aljihu ya fito da duk kudin jikinsa kusan nera dubu talatin, megari yayi ma wani dogari umarnin ya amshi kudin ya Mikama Mallam Umar.

Cikin sanyin jiki ya amshi kudin Yana juya su alamun neman Karin bayani.

 

Megari ya dubi Taufiq yace ” matanka nawa?”, Cikin rawar murya yace”Matata daya”. Megari ya dawo da kallonsa ga Mallam Umar yace ” wannan kudin sadakin yarka ne,”. Taufiq da Mallam Umar da muhseena suka zaro Ido cike da gigita kafin daya daga cikinsu ya yi magana, megari yace “Jama’a ni megari nine Zan Zama waliyyin wannan bakon Mallam Umar Kuma zai Zama waliyyin yarsa, ga shaidu ga kowa yanzun nan zamu daura auren su”.

 

Gaban muhseena yayi dam ya Fadi gaba daya ta rikice ta rasa a wace duniya take cikin kuka take fadin ” Baba Ka taimakeni Kada Ka bari su kashe min rayuwa, ta yaya Zan auri mutumin da ban San wanene shi ba”

Shima Taufiq din gaba daya rikicewa yayi yace ” ta yaya zaku hukuntani da wannan mugun al_amarin bayan ba ni da laifi taimako kawai nayi”.

 

Mallam Umar ya wuce a sukwane gaban megari Yana cewa ” Kada Ka min haka megari yata tana da gaskiya kamar yadda bakon nan ya ke da gaskiya ba ko wane Dan birni bane yake da mugun Hali Kada Ku sabauta rayuwar yayan nan”.

 

Mallam kallah yace ” haba Mallam umaru gata fa zaayi ma yarka, yanzu kana tunanin ko babu abinda ya shiga tsakanin muhseena da Taufiq, akwai wani da zai iya auren muhseena bayan bakin fentin da ke shafe a jikinta sannan ta Kara da wannan Kuma to waye zai aureta, Kuma bayan haka lalle Bama son yayan mu su cigaba da ganin mummunar tarbiyyar da wata kila su yi tunanin Fara bin irin tarbiyyar”.

 

Gaba daya mutanen wajen suka dauka ” Kwarai da gaske mun gaji da irin wannan rayuwar muna neman canji ,dole ya aureta Kuma ya dauke mana ita agarin “.

Daker megari ya sassauta hayaniyar da ake yi a wajen.

 

Wanda zuwa lokacin Taufiq ya kusa shidewa a zaune saboda tsabar tashin hankali. Haka itama muhseena ta fada mugun tashin hankali mara misaltuwa.

 

Wanda bai sa megari ya fasa abinda yayi niyya ba domin Mallam Umar Yana ji Yana gani bashi da yadda zaayi haka aka daura auren Taufiq da muhseena.

 

Tashin hankali Wanda baa sa masa rana. Gaba daya Taufiq ji yayi kamar an dora masa dala da goron dutse turus yayi akasa kamar bashi da laka.

 

Megari ya dubi Taufiq yace ” ci da sha da sutura da wajen Zama da kula da lafiya da iliminta duk ya rataya a wuyan Ka , don haka idan ka tashi tafiya zamu tabbatar da Ka tafi da matarka”.

Taufiq ya kasa magana kawai ji yayi hawaye Yana fita a idonsa.

Ayayinda mutanen gurin kowa sai murna da son barka yake yi tare da jinjina ma hukuncin megari . Sosai suke Jin da wuya akara Samun wani me tsaurin idon da zai Kara aikata abinda Taufiq da muhseena suka aikata. Ahankali kowa ya Fara watsewa.

 

Amma Mallam Umar ya kasa motsa ko da kafarsa , sai alokacin ya Lura da muhseena ta sulale kasa sumammiya a gigice ya yo kanta Yana Kiran sunanta a firgice.

TO BE CONTINUE

 

DAGA TASKAR YAR GIDAN IMAM

[20/02, 10:25 am] +234 802 297 0646: NI MA MATARSA CE

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

( YAR GIDAN IMAM )

BABI NA ARBA’IN DA BIYU

*********

Wata daya kawai aka sa bikin Hajara . Haka zalika Mallam Umar Shi yayi Mata komai na daki dai dai karfina, hakan kuwa ba karamin karama Hajara kaunarsa yayi ba, ta yarda duk duniya bata da gata sama da Mallam Umar.

 

Mallam Umar a wañnan lokacin Yana da rufin asiri tunda Yana Dan bubbuga kasuwancinsa. Abubuwa da yawa basa masa wahalar yi.

 

Hakan yasa bai sami wata damuwa ba wajen tafiyar da komai na bikinsa da Hajara ba. Hatta daurin auren babu Wanda ya halarta sai tsirarun mutane da mafi yawanci ma Basu da alaka da Mallam Umar. Liman ne ya daura auren .

 

Daker sabira ta bi umarnin Mallam kallah ta raka Hajara gidan aurenta, tana kaita Kuma ta bar gidan. Awannan ranar Hajara tayi kuka kamar idonta zai fita taga ràshin gata yadda akayi bikinta ko bikin yar tsana ce sai haka, rasuwar mahaifanta ta dawo Mata sabuwa, tayi rashinsu matuka da gaske.

 

Hajara ta dauki dammarar yi ma Mallam Umar dukkan biyayya tare da mutunta Shi, domin Shi kadai gareta yanzu a duniya. Hakanne yasa duk musgunawa da Ande Dije ke yi Mata ita da yarta bai taba damunta ba. Domin dai tun zuwanta gidan Ande Dije ta maida ta tamkar baiwa komai itace take yi agidan babu Kuma yabawa ko darajawa. Ande Dije mulki take Kuma dole Hajara ta dinga bin duk abinda take so. Idan ma akwai abinda ke damun Hajara to bai wuce kiyayyar da Ande Dije ta dorama muhseena ba domin ko kusa da ita bata son ta je, bata daukarta bata kulata tsakaninsu sai kyara da mugayen maganganun da Hajara bata kaunar ta dinga yinsu Akan yarta da bata da laifin komai.

 

Duk da haka Mallam Umar Yana cike da damuwar abinda Ande ke yi ma su Hajara a kullum Yana kokarin fahimtar da ita ta dauki Hajara a matsayin ya muhseena Kuma a matsayin jika Amma taki. Bashi da yadda zaiyi tunda Uwa ce dole tasa sai dai ya dawo wajen Hajara yayi ta bata hakuri tare da nuna Mata ta dinga Kau da kanta akan komai wata Rana sai labari.

Hajara ta kanyi murmushi tace ” Ka daina damun kanka domin ba ni da damuwa, na dauki Ande a matsayin Uwa ta don haka babu abinda zata min na ji haushinta, ai Nama gode data yarda Ka aure ni. Irin wadannan kalaman nata Suna karama Mallam Umar kaunarta da ganin mutuncinta. Ya dauki dukkan hidimar muhseena komai Yana yi Mata ga wani irin so da yake Mata har cikin jininsa Yana Jin tamkar Shi ya haifi muhseena bai wasa da duk abinda ya shafeta, duk da kullum yayi hidimar sai Ande ta ci masa mutunci amma baisa ya daina yin abinda yake yi ba, domin ya riga ya daukar ma Kansa alkawarin Kula da muhseena a matsayin ya.

 

Cikin ikon Allah a kwana a tashi shekarar muhseena hudu, a lokacin Mallam Umar ya hadu da ibtila’in karayar arziki duk kasuwancinsa yayi kasa a hankali a hankali kamar wasa komai ya kakkabe ya zamana bai da komai. Alokacin komai ya Fara musu wahalar Samu tun daga Kan abinci har sauran abubuwan more rayuwa komai ya tsaya cak!.

To fa nan Ande ta Kara daukar kiyayya ta dorama Hajara domin acewarta Hajara ce mai farar kafa don Mallam Umar ya aureta ne ya tsiyace, ai daman tasan ba zata taba Zama alheri ga danta ba, ko tsakar gida daker Hajara ke fitowa saboda tsabar masifar Ande Dije, duk yadda Mallam Umar ya so ya fahimtar da ita komai da ga Allah ya ke babu hannun Hajara acikin karayar arzikinsa to fa Ande taki fahimta ko Kuma ta fahimta amma kiyayyar Hajara ta hanata ganin hakan.

 

Tun daga wannan lokacin har zuwa yanzu Mallam Umar cikin fafutukar rufama Hajara da muhseena asiri yake. Satittika sun shige cikin watanni , watanni sun shige cikin shekaru har zuwa girman muhseena tamkar zaa manta da labarin Hajara amma ina tunda muhseena ta Girma itama ake jifanta da Kalmar shegiya. Da Kan Shi Mallam Umar ya sa Hajara tayi masa alkawarin ba zata taba gaya ma muhseena cewa ba Shi ba ne mahaifinta ba.

 

Haka zalika iya wadannan shekarun har yanzu Hajara bata Kara Jin duriyar Alh ba balle Haj sun bace bat, babu su babu labarinsu.

 

**********

Hajara ta numfasa gami da goge hawayen da ya dade Yana zuba Mata , ta dago ta dubi Kabir da muhseena gaba dayansu kuka suke sosai.

Ta jinjina Kai tace ” wannan Hajarar ba wata ba ce illa ni, muhseena Kuma ba wata ba ce illa ke” ta nuna muhseena da hannunta.

 

Muhseena ta Kara fashewa da kuka Mai karfi , wani abu ne ya ke yi Mata yawo a cikin zuciya , kamar yadda ta ke Jin tamkar jinin jikinta Yana tafasa,kanta ya cigaba da Sarawa sosai.

Hajara ta dubi Kabir da yake kokarin tattara natsuwarsa waje daya tace ” Kabir Ka ji gaskiyar magana akan muhseena, haka zalika ina Mai Baka shawarar Ka hakura da muhseena domin bana fatan muhseena ta shiga rayuwar kunci da takura a gidan aurenta, don ina son muhseena tayi aure a gidan da zaa karbeta da daraja ba tare da kallon ita wacece ba”.

 

Ta Dan gyara zamanta tace ” Na so ace mahaifanka sun yarda da muhseena, amma tunda Basu aminta da ita ba dole za kayi hakuri da ita duk da kafi kowa cancantar Ka aureta”.

 

Kabir ya numfasa yace ” Inna na gamsu da labarinki na Kuma yarda da duk abinda kika fada, na Kara Jin son muhseena da tausayinta a raina fiye da kullum, amma ba ni da yadda zanyi Bani da karfin hali kamar Mallam Umar ta yadda Zan bata da kowa a Kan muhseena kamar yadda ya bata da kowa a kanki, amma Allah ya sani son muhseena ina kaunarta rashinta Kuma agare ni ba karamar masifa ba ce, amma babu yadda na iya sai dai Zan cigaba da roko da bin mahaifana har su amince”.

Hajara ta girgiza Kai tace ,” ba zasu yarda ba Kada Ka bata ma kanka lokaci, kayi kokarin cire ta kawai a ranka, Kuma ba Zan taba mantawa da dawainiyar da kayi da mu ba Ina fatan Allah ya baka wacce ta fi muhseena “.

 

Tana Gama fadin haka tayi saurin tashi ta fita daga dakin.

Kabir ya zubama muhseena Ido wacce bakinta ya rufe ta kasa cewa komai ita kadai tasan halin da take ciki.

 

Ya Kira sunanta a hankali ta amsa ba tare data kalle Shi ba.

Yace ” kiyi hakuri kowa da irin kaddararsa a rayuwa don haka kema ki dauka wannan itace kaddararki, Kuma ki sani dukkan tsanani Yana tare da sauki babu Kuma wani abu da yake dauwama, hakuri Kuma shine matakin nasarar ko wane bawa”.

Haka Kabir ya cigaba da yi Mata nasihohi ,Amma har yayi ya gama muhseena ta kasa cewa uffan tana zaune ne dai kamar gunki.

 

Fahimtar da yayi muhseena ba ta tare da Shi , yasa yaga kysutuwar ya bata fili ko ta Samu ta fito daga tashin hankalin data fada. Asanyaye cikin yanayi na damuwa ya fito daga dakin , zaune Kan tabarma ya tadda Hajara ya fito da kudi daga aljihunsa ya tsuguna a gabanta ya aje kusa da ita ya Kara da cewa ” gobe Zan koma kano, sai ki cigaba da yi mana adduar Allah ya daidaita yasa mahaifana su amince da muhseena” ta Dan yi wani bushasshen murmushi Wanda kasan sa damuwa da tashin hankali ne kwance. Tace ” Nagode Kabir, Allah ya kaika lafiya, ya Kuma zaba maka abinda ya fi alheri”. Ya amsa da ” Amin” sannan ya Kara Mata sallama ya tafi.

 

Wani abin mamaki Yana fita ya tadda Mallam Umar zaune Kan dankalin kofar gidan yanayin zamansa da alama ya dade zaune a wajen.

Mallam Umar ya waiwayo ya dube Shi yace ” Kabiru kun gama?”, Kabir yayi saurin risinawa ya gaishe shi. Mallam Umar ya cigaba da dubansa fuskarsa cike da damuwa yace ” Tun alokacin da Hajara take baku labari na shigo , Bana son na ji komai ne yasa na fito na cigaba da Zama a waje” ya Kara kallonsa yace ” duk arayuwata babu abinda na tsana sama da wani ya ce ba ni ne mahaifin muhseena ba, saboda ita din ya ta ce babu Kuma abinda zai kankare hakan saboda haka kaima ina son Ka cigaba da dauka a haka, lokuta da yawa ina Jin ràshin jindadi Akan ràshin goyon bayan da mahaifiyata bata ba ni ba na barin garin nan bayan aure na da Hajara saboda ta haka ne kadai ba zaa bijiro da irin wannan maganar agaban muhseena ba, mu je can mu rayu inda ba’a San mu ba, amma mahaifiyata ta ki yarda da hakan”.

 

Kabir ya numfasa yace ” A yau na Kara ganin kima da darajarka fiye da ko yaushe, Allah yayi maka sakayya da alheri da irin hidimar da kayi” ya gyara tsugunonsa yace ” Na so a ce ina da irin jarumtarka da babu Wanda zai hana ni auren muhseena” malllam Umar ya ce ” ko yanzu ina son kasama ranka duk abinda Allah yayi dai dai ne, Kuma babu jayayya tsakaninka da mahaifanka, wuce Ka tafi dare yayi”.

Kabir ya Mike Yana gaya masa gobe zai koma Kano, nan ma yayi masa fatan alheri su kayi sallama ya tafi zuciyarsa cike da tausayin muhseena da Hajara mara misaltuwa.

 

Har ya koma gida bai Sami wata nutsuwa ba, ya so Kara yin maganar da mahaifiyarsa amma ganin yadda bata bashi fuska ba yasa ya hakura. Washegari kuwa tun safe ya shirya zai tafi.

 

Mallam Hamza wanzami ya zuba masa Ido Yana hango tsantsar damuwa da ràshin nutsuwar atare da Shi, ya numfasa yace ” Kabiru Kada Ka taba dauka damuwarka ba damuwar mu ba ce, Allah ya sani da Zan iya hakura na taushi zuciyata Ka auri yarinyar nan da nayi amma maganar gaskiya bazan iya bata zuriata ba da abin da nasan bazai taba gogewa ba, don haka kayi hakuri ga Mata nan da yawa sai wacce Ka zaba kaje Allah ya zaba maka mafi alheri agareka”. Kabir ya bude bski zai yi magana yayi saurin ce masa ” Bana son wata magana data shafi wannan yarinyar Ka rufeta Ka manta da ita Ka je kayi harkar gsbanka domin Bana Jin a kwai wata magana da zaka Gaya min ko kasa a gaya min wacce zata sani na amince da bukatarka”.

Ya Kara yi masa kallon tsaf yace ” matukar ni na haifeka na datse dukkan wata alaka da ke tsakaninka da wannan yarinyar Bana sin Ka Kara min maganarta kamar yadda Bana son Ka Kara zuwa yanzu in da ta ke”. Kabir bai fita da ga cikin tashin hankalin da ya Kara fadawa ba , daga can bakin Kofa muryar Hafsatu ta Kara dakan dodon kunnansa tace “Nima a matsayina na mahaifiyarka na haramtaka cigaba da Hulda da muhseena da gidansu domin babu abinda tarihi ya manta don haka Bana son Ka shiga mummunan tarihin wannan bakar zuri’ar, Ka je Ka Nemo yarinya yar asali yar mutunci”. Cikin nauyin zuciya da fitar kwalla kamar ba namiji ba Kabir yace ” Na so ace kun fahimce ni amma babu yadda zanyi don bazan iya tsallake duk sharadin da kuka gindaya min ba, sai dai Ku sani ba ni da halin cire muhseena a cikin zuciya ta domin wannan ba yi na ba ne yin Allah ne, amma Zan nisanceta kamar yadda kuka min umarni “. Komai kekashewar zuciyarka sai Ka ji tausayin Kabir yadda yayi wujuga wujuga da yadda yanayinsa ya kasance. Yana Gama yi musu wannan bayanin ya Ciro kudi masu yawa ya aje musu ya juya yayi musu sallama ya tafi, cikin matukar tashin hankali, ya so ya Kara ganin muhseena kafin ya bar garin to amma babu halin hakan domin Shi Kansa yasan cigaba da kusantar muhseena zalincine a gareta domin idan ya cigaba da kusantarta yasan babu yadda zaayi ta fita daga cikin kuncin rashinsa ko mantawa da Shi , don haka ya Zama tilas ya nisanceta . Fitar sa Hafsatu ta numfasa ta dubi Mallam Hamza tace “Mallam , yaron nan yayi nisa Ina Jin tausayinsa matuka araina, don haka ina ganin dole a hada da Nemo masa rubutun dangana ko Allah yasa ya yi dangana ya manta da wannan bakar dagar yarinyar da Bana ko son tunawa da ita”. Mallam Hamza yace ” Ni Kaina nayi tunanin hakan , bazan yarda yarinyar nan ta sabauta min rayuwar da ba babu gaira babu dalili, Dan da nake mora fiye da kowa, don haka ina fita Zan Sami Mallam zangija nayi masa bayani idan rubutun danganar zai masa duk yayi kawai,” haka suka zauna suna cigaba da tattaunawa a tsakar gidan.

 

Kishiyar Hafsatu sahura ta fito daga dakinta da alama duk abinda suke tattaunawa tana jinsu, ta dube su tace ” Ni ko Mallam banga illar goyama Kabiru baya ya auri yarinyar nan ba, tunda Yana sonta ina ganin tamkar an shiga rayuwarsa idan aka raba Shi da ita”, Hafsatu tayi Mata wani irin kallo cikin fusata tace ” Allah sarki, ai da yake ba ke kika haife Shi ba , da ace Hassan ne ai da Baki Fadi haka ba, sai kace ba ki San yarinyar da ake magana akai ba”, sahura ta jinjina Kai tace ” Allah ya Baki hakuri bana nufin abinda kika fada, da Kabiru Kuma da Hassan Duka yayana ne babu wani bare acikinsu, kawai dai ina gaya muku gaskiya ne” Mallam Umar yayi Mata wani irin kallo yace ” To mun ji gaskiyar mun gode Kabiru Kuma ba zai aure ta ba komai runtsi komai wuya”. Fahimtar da tayi maganar tana so ta dawo wata iri yasa ta wuce kiciñ wajen girkinta ba tare da ta Kara yin magana ba.

 

Tabangaren muhseena kuwa, sosai ta Kara sa ma kanta hakuri, domin labarin mahaifiyarta yayi sanadiyyar data ji karfin guiwa kwarai da gaske,

Domin tasan cewa ko rabin kwatan halin kunci da tashin hankalin da mahaifiyarta ta shiga ita bata shige shi ba, ta Kara tausayama mahaifiyarta kwarai babu Kuma abinda wani zai Kara fada Akan mahaifiyarta da zai dameta. Kamar yadda son ta da son kyautata Mata ya Kara cika zuciyarta, Karo da dama Kenan da ta ji tana son Zama wata a rayuwa saboda ta jiyar da mahaifiyarta dadin da ko wace uwa take mafarki daga danta.A wannan lokacin ta Kara Shan alwashin sai ta Zama abar kwatance na alheri a kauyen Durmi Saita binne tarihin mahaifiyarta da kyakkyawan misali.

 

Kamar yadda ta gefe daya kima da kaunar Mallam Umar ya Kara kama ta , shine mahaifinta bata da wani uba sama da Shi , babu Wanda zai amsa sunan mahaifinta bayan Shi. Za Kuma tayi komai domin ganin ta Zama ya ta gari a gare Shi zata Zama sanyin idaniyarsa.

TO BE CONTINUE

 

DAGA TASKAR YAR GIDAN IMAM

[20/02, 10:25 am] +234 802 297 0646: NI MA MATARSA CE

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

( YAR GIDAN IMAM )

BABI NA ARBA’IN DA UKU

**********

kwarai matuka idan muhseena tace ràshin Kabir bai taba rayuwarta ba, hakika tayi karya sosai take Jin rashinsa , sai dai dole tasan zata sa ma kanta hakuri da dangana ta yarda da kaddararta.

Haka zalika ta jidadin hukuncin da Kabir ya dauka na nisantarta, kamar yadda ya gayá Mata a waya, bayan komawarsa, sai dai duk da haka akai akai abokinsa ya Kan kawo Mata sakon kudi ko kayan bukata, bata son Kabir ya cigaba da hidima da ita amatsayin tausayi don haka ta sanar da Shi bata bukatar komai ya dakatar da hidimar da yake yi, Wanda su kansu su Mallam Umar din sunga dacewar hakan.

Ko ya aiko da kudi ta daina Karba, gaba daya so ta ke ta manta da Shi duk da kullum zuciyarta cikin damuwa da ràshin nutsuwa ta ke, sai dai tana kokarin boyewa saboda bata bukatar aikata duk wani abu da zai zamo karin damuwa ga mahaifanta.

 

***********

Tabangaren mujaheeda da Taufiq kuwa Zama dai ya yi dadi, abubuwa da dama sun canja tunda itama mujaheedan ta canja sosai son Taufiq ya rinjayi izza da son ranta. Tana kokarin bin duk abinda yake so.

 

Sai dai har yanzu ragamar kulawa da Shi ta na nan ahannun masu aiki, har yanzu bata San ta girka abinci don mijinta ya ci ba, ràshin yi Mata magana ko Kuma nuna baya jindadin hakan yasa har yanzu mujaheeda bata fahimci tana aikata kuskure ba. Ita kuwa Haj murjanatu shurun da ta ji na zaman lafiyar da Taufiq da mujaheeda su ke yi tayi zaton aikin Mallam ne ya ci kamar yadda ta ke zaton aikin Mallam dinne ya mallaka Mata nata Mijin.

 

Haka zalika ta wajen aikin mujaheeda duk wani tuggu da kulle kulle Alh jibrin yayi domin ya ga aikin ya fita ran mujaheeda, amma babu wani cigaba da yake samu hatta murtala da ya ke Goya masa baya ya fahimci babu wata nasara da zasu samu, hakanne yasa ya zage ya koma wajen mujaheeda Yana cigaba da biyayya da neman fada. Shima Àlh jibrin din hakanan ya hakura Yana cigaba da adduar Allah ya kawo sanadiyyar da mujaheeda zata bar aikin da kanta.

 

A cikin haka ne mujaheeda ta Fara laulayi , gwajin farko likita ya tabbatar Mata da tana dauke da ciki harna wata biyu.suna hanyar dawowa daga adibitinne murna da farinciki gun Taufiq ba’a magana, sabanin mujaheeda da gaba daya fuskarta da yanayin ta ya canja tunda likita yace tana da ciki babu wani alamun farinciki a fuskarta, har suka Kai gida duk irin maganganun farinciki da Taufiq ya ke yi baisa tace uffan ba. Isar su gida ne hakurin Taufiq ya gaza ya dubeta sosai yace ” Ni banga alamun farinciki ba atare da ke, duk da irin wannan gagarumar kyautar da Allah ya bamu”. Mujaheeda ta dan muskuta ta gyara kwanciyar ta akan gado fuska ba yabo ba fallasa tace ” hmm ni fa yaya Taufiq ban shirya haihuwa yanzu ba, asalima ni ban taba kawowa araina wai Zan haihu nan ta kusa ba” ya kafe ta da kallon mamaki sannan yace ” Dama haihuwar shirya Mata ake ? Ban fahimce ki ba fa” tayi masa kuri da Ido tace ” Shi yasa nake son Ka fahimce ni yanzu” ta yunkura cikin ràshin karfin jiki ta zauna tana kallonsa tace ” ina son kayi hakuri a cire cikin nan, domin bazan iya ba , Ka duba Kaga ni yadda na fita hayyacina Bana jindadin komai ga ciwon da ban ma gane Kansa ba, wannan cikin zai tsayar min da abubuwa da dama a rayuwata, don haka don Allah Ka barni na cire Shi “.

 

Tsananin mamaki da bakincikin maganganunta suka baibaye Taufiq, ya dubeta sosai Ido cikin Ido yace ” mujaheeda anya kuwa kina so na?”, Ta dube Shi da sauri tace ” Ni ko na ke son Ka , wannan wace irin magana ce yaya Taufiq?”. Ya girgiza Kai yace ” idan har da irin wannan tunanin a ranki to ki Sani ni bakya so na, duk abinda kika fada na game da son da kike min karya ne, don idan kina Sona da Baki kyamaci hada jini da ni ba”, tayi saurin cewa ” Ya zaayi na kyamaci hada jini da Kai bayan na riga na hada rayuwata da taka, kawai dai ina son Ka fahimce ni , kayi min Kuma Uzuri, ina son na haihu da Kai amma ba yanzu ba……..?

 

Bata karasa abinda take fade ba, Taufiq ya juya a fusace ya fice da ga dakin cikin matukar bacin rai.Bai taba zaton Jin abinda ya ji daga mujaheeda ba, haushinta da haushin maganganun ta yake sosai.

Tun daga wannan ranar wata sabuwar fitinar ta kunno Kai tsakanin Taufiq da mujaheeda. Domin dai dagaske take bata son cikin bata son haihuwa yanzu Shi Kuma Yana son cikin Yana kuma son haihuwa yanzu. Haj murjanatu kuwa tsabar son rai da son zuciya da Kuma soyayyar mujaheeda data makantar da ita bayan mujaheeda ta bi duk da itama can karkashin zuciyarta tana da bukatar Samun jika daga mujaheeda to amma tunda mujaheedar bata so itama bata so.

Ranar farko da Haj murjanatu ta shiga cikin maganar, ta nuna ma Taufiq menene don an cire wannan cikin bayan gaba Allah zai bata wani. Cikin fusata Taufiq yace “Wane garanti gareta na Allah zai bata cikin alokacin da take so bayan Shi ya bata alokacin da yake so tace bata so, Bana son mu Sami gagarumar matsala akan wannan maganar domin babu Wanda ya isa ya cire min ciki, me kuka dauke ni ne sakarai Wanda baisan ciwon Kansa ba ko me?” Ya tashi cike da fushi yace ” Ina son Ku sani ni ba bawanku bane , na Kuma San darajata da yancina don haka duk Wanda ya taba min ciki ko waye Shi sai munyi Shari’a da shi ”

Yana Gama fadin haka Bai saurari komai ba ya fita daga falon,

Yana dukan iska, Bai taba Jin zafi da damuwa akan duk abubuwan da suke biyo bayan aurensa ba irin wannan.

 

Haj murjanatu ta jinjina Kai ta kurama mujaheeda Ido tace ” mujaheeda Taufiq ba bazai taba yarda da abinda kike so ba, ” mujaheeda ta numfasa cike da damuwa tace ” Ni Kuma mummy Allah ya sani Bana son haihuwa yanzu, gabana har faduwa yake yi idan na tuna wai ina da ciki, amma kwata kwata yaya Taufiq ya ki fahimtata”.

Haj murjanatu tace ” bazai fahimce ki ba,”. Sosai Haj murjanatu ta Fara tunanin ko dai asirin da malllam yayi ya Karye ne domin ba tayi tsammanin irin wannan kafiyar daga Taufiq ba.

 

Wannan Karon Kuma mujaheeda ba zata iya zuwa wajen surikinta da wannan maganar ba Wanda tasan shine zaisa Taufiq yayi Mata abinda take so.

Ràshin jituwa ta Sami matsuguni tsakanin Taufiq da mujaheeda.Babu wani kwanciyar hankali, ko gidan Taufiq baya son ya dawo.

 

Aikin hanyar da kamfanin su Taufiq ya ke yi, yayi nisa, anyi canjin ma’aikata Taufiq Yana daya daga cikin wadanda aka tura cigaba da yin titin kauyen Durmi.

 

Cikin lokaci kankani Taufiq ya gama shiri. Saura kwana biyu ya tafi ranar a gidansu ya uni har dare tare da iyayensa domin dai yasan idan irin wannan aikin ya taso yakan Dade Bai dawo gida ba, tun Kuma bayan aurensa bai je irin wannan aikin ba. Sai dare da zai dawo yayi musu sallama, kamar kullum sunyi masa fatan alheri da fatan dawowa lafiya.

A Daren ranar har sun kwanta, ya kasa jurewa ya tashi ya zauna gami da kunna wutar dakin, Yana kallon gefen da mujaheeda take kwance ya Kira sunanta a hankali, ta dan motsa a hankali sannan ta amsa.

Yace ” ki tashi ina son yin magana da ke”.

Ta dan yi Jim kafin ta motsa sosai ta tashi ta zauna tana kallonsa Wanda rabon da ta kalli fuskarsa haka ta kwana biyu.

 

Tace ” ina jinka”, ya jinjina Kai Yana kokarin gyara zamansa.

 

Sannan yace ” Ina son mu kawo karshen wannan matsalar da take neman ta rushe duk wata soyayya da jituwa da ke tsakaninmu”.

Tace ” Ni ban dauki wannan abin amatsayin abinda zamu zauna mu rasa kwanciyar hankali saboda Shi ba, Kai ne Ka dauka da zafi”.

 

Ya jinjina Kai yace ” Bana son wata magana kawai ina son ki sauka daga wannan akidar ta ki, kiyi hakuri mu rungumi kyautar da Allah yayi mana muyi masa godiya”

Mujaheeda tace ” Ka kasa fahimtata yaya Taufiq,…?.

 

” In dai akan wannan ne bazan taba fahimtar ki ba,kawai ina son ki cire tunanin cire cikin jikinki domin wannan cikin shine farincikina” shuru kawai tayi bata Kara magana ba, har ya cigaba da maganganunsa masu kama da nasiha.

Daga bisani yace ” jibi Idan Allah ya kaimu Zan tafi aiki daya daga cikin hanyoyin da kamfaninmu yake aiki, Kuma Zan dauki lokaci ban dawo ba,”

 

Ya dubeta sosai yace ” saboda haka ina son ki Kula da kanki da abinda ke cikin ki don Allah “.

Tace ” Allah ya kaimu” tana fadin haka ya juya ta kwanta abinta ba tare da nuna wani alhinin rabuwa da Shi ba.ya Dade zaune kafin shima ya kwanta amma ya kasa runtsawa matsalolin da ke cikin aurensa sun ishe shi.

 

Ko ranar da zai tafi ba wani sakin fuska ko wata kulawa da ya Samu daga mujaheeda.Hakanan ya tafi, zuciyarsa a jagule tunaninsa na ga cikin jikinta Yana adduar Allah ya tsare masa cikinsa.

TO BE CONTINUE

 

DAGA TASKAR YAR GIDAN IMAM

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment