Littafan Hausa Novels

Ni da Yaya Rafeeq Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Ni da Yaya Rafeeq Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

[NI DA YAYA RAFEEQ

_chasing my heart_

By Hafsat Hisham

 

Page 1 and 2

Free page

 

Littafin Ni da yaya Rafeeq na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take so tayi min magana via WhatsApp 09169472057, amma na rokeki da girman Allah idan ba siya zakiyi ba kadda kiyi min magana, Na rokeki da girman Allah idan ba novel dina zaki siya ba kadda kiyi min magana

 

Ni da Yaya Hassan Book 2 Hausa Novel

Morning,

A wannan safiya sanyi ake sosai a garin katsina, garin duk yayi buji yayi hazo-hazo, idan mutum ya d’aga kai ya kalli nesa dashi sai yayi tunanin hayaki ne yake tashi wannan yanayi shi kesa lokaci yaja ba tareda mutum ya ankara ba kasancewar rana bata fiye fitowa sosai ba, mafi akasarin mutanen dake zirga-zirga a waje suna sanye ne da sweater da hular sanyi, wasu har glass suka saka suke rufe idanuwansu, wasu har hancinsu sun rufe, bujin da ake ya saka hair din mutanen da basu saka hula ba yayi fari kamar furfura….

Santa ce wanda take dauke da gidajen mutane masu karamin karfi, a yankin kofar kaura, gidajen dake akan santar mafi akasari kananu ne wasu ginin kasa ko shafe babu, babu kwalta a santar amma mota zata iya shigowa saidai akwai wajan da idan tazo dole ta tsaya, tsit santar take kasancewar yara sun tafi makarantar boko….

Wani gida ne na hango flat shoes wanda yake dauke da katon kwauren karfe amma babu get, soron gidan yana da girma, idan mutum ya shiga gefenshi kewaye ne can nesa kadan madafa ce opposite da ita wani empty din daki ne, akwai rigiya, idan mutum ya shiga can cikin gidan a gefen dama daki daya ne room and parlour, a gefen haggu kuma dakuna biyu ne a jere saidai na karshen yafi na farkon girma, gefen karamin dakin randar ruwa ce, gidan yana da girma sosai, yasha paint da tale a malale….

Bedroom ne babba wanda yake dauke da bathroom, wani katon royal bed ne wanda yake dauke da wani expensive bed sheets with pillows manya da kananu, a gefe closet ne tareda dressing mirror wanda yake shake da kayan makeup tareda designer perfumes da sauransu, the other side sofa ce tareda glass table, a both right and left side na bed, bedside drawer ne, wasu flames na hango wanda suke dauke da drawing na flowers, air conditioner, a gefe fridge ne, wani designer carpet ne mai laushi a malale akan tale dake bedroom din….

9:30am wall watch din bedroom din ta nuna, wata breathtaking Babe ce er kimanin shekaru goma sha shidda zaune a tsakiyar royal bed din tana jingine da pillow ta rufe rabin jikinta da blanket, waya ce kirar iPhone 7 plus a hannunta kanta a duk’e tana shafata, sanye da wata breathtaking black arebian gown ta tamke kanta da veil, gown din tana da white flowers wadanda suke tareda black flowers da alama tashi tayi daga bacci ta fara chatting din….

MashaAallah, OMG, Wow, she is cute beyond imagination, kyakykyawa ce sosai, fara ce sol har wani yellow skin dinta yake saboda haske, she is gorgeous, Aallah ya hore mata kyau, tana da tsayi amma not that much, tana da d’an jiki, Aallah ya azurtata da kalar shape din nan da ake kira figure 8, slander in shape, eyelashes dinta zara zara ne baki, eyes dinta farare ne sol kamar madara, tana da yalwataccen eyebrow yana kwance gashi yawo-yawo dashi yayi luf-luf, pupil din eye dinta black ne sosai, ga iris dinsa kamar ita ta zauna ta tsara abunta, tana da long pointed nose tareda small cute lips dinta reds sai sheki suke kamar tayi applying lipstick, tana da face marks wanda ya kara haske fuskarta, tsagen rumawa gareta a cheeks dinta da kuma gefen fuskarta, tsagen ya fito sosai yayi baki yanayinsa kamar tattoo saidai bashi da fadi yanayinsa yayi kyau a beautiful face dinta, abun mamaki maimaikon tsagar tayi mata muni sai ta k’ara mata kyau looking more and more cute and gorgeous, alluring and mesmerizing, tabbas wasu rakiyar wasu sukayi a duniyar kyau….

Gani nayi ta dafe goshi tareda zaro manya-manyan idanunta da alama wani abu ta tuno, tayi jim, murmushi ne yayi escaping akan lips dinta har dimple din dake makale a both cheeks dinta suka bayyana, white teeth dinta masu haske sukayi appearing sai lighting suke, ta sauke hannunta tareda maida hankalinta akan wayar dake hannunta tayi snapping video….

“Kiyi hakuri k’awata mantawa nayi amma ga hotunan nan na turo maki…”.

Tayi saving video din tayi sending ma wata tareda wasu pictures dinta da tayi selecting, ta juya tareda matsar da iPad dinta dake akan bedside drawer tayi dropping iPhone dinta, tayi jim tareda yaye blanket din data rufe jikinta dashi ta zuro kafafunta tareda durowa daga saman gadon, OMG her leg, kafafunta farare ne sol sumul-sumul kamar na new born, ta mik’e ta wuce bathroom, wayarta ce tayi ringing ta juyo da sauri wanda yayi daidai da buge goshinta da tayi da door din bathroom, ta dafe wurin tana murzashi wanda in the process veil din dake saman kanta ya sub’uce, yadda veil din yake a kanta kamar ta kunsa kallabuna ne a ciki amma abun mamaki yana warwarewa ya fadi kasa yalwataccen gashinta kanta ya bishi tunda daga tsakiyar kanta har wuce gwuwar kafarta, OMG wow tsayin gashin har gwuwar kafarta ya wuce gashi wara-wara kamar rubber ga cika….

******

Wani Handsome and breathtaking guy ne zaune a katon office dinsa wanda yake cikin kamfaninsa wanda daya ne daga cikin kamfanoni masu yawa da suke mallakinsa wadanda suke a garuruwa daban-daban dake a fadin Nigeria, Rafeeq kenan a birnin tarayya Abuja yake zaune tareda mahaifiyarsa, waya ce mak’ale akan kunnansa saidai har kiran ya tsinke ba’a yi picking ba, cire wayar yayi daga kunnansa tareda zubawa majigin manya-manyan idanunsa, fuskarsa dauke da mamaki, yace,

“Rumaaa…”.

Saida yayi jim sannan ya k’ara dialing numbar….

Rumaaa ta duk’e tareda daukar veil dinta, da sauri ta karasa wurin bedside drawer ta dauki wayar, ringing dinshi na daban ne, picking tayi tareda kangawa a kunne tayi jim tareda juyawa tayi taking steps toward dressing mirror….

Daga daya bangaren Rafeeq ya sauke ajiyar zuciya sannan yayi mata salaam a hankali cikin husky voice….

“Salaam alaiki…”.

Daga daya bangaren Rumaaa ta jawo stool dake gaban mirror ta zauna, smile ne yayi escaping akan lips dinta, a hankali tace,

“Wa alaikassalaam…”.

A hankali ya kira sunanta….

“Rumaaa”.

“Na’am yaya Rafeeq”.

“Na kira amma baki dauka ba”.

“Ehhh hakane”.

Daga daya bangaren Rafeeq yayi relaxing akan kujera ya lumshe idanunsa ya bud’e sannan under his breath yace,

“Why?”.

“Na shiga bathroom kenan naji k’arar wayar wurin fitowa na kume kai da kofa kaga har yanzu wurin yana min zafi daurewa kawai nike don kadda ace na cika raki…”.

A shagwab’e ta ida maganar wanda hakan yanayinta ne….

Rafeeq ya ware idanu sannan yace,

“Ohhh… Ayya… Sorry kinji… Ana Asif… Nine na janyo maki ki yafe min…”.

“Huh…”.

“Huh kuma?”.

“Bazan hakura ba…”.

Rafeeq ya zaro idanu sannan yace,

“Meyyy?”.

“Sau biyu kana laifi sannan kuma ba kayi min laifi ba amma kake bani hakuri…”.

Rafeeq ya dafe goshi yayinda smile yayi escaping akan lips dinsa yace,

“Ohhh… Kiyi hakuri na daina maki turancin…. Kin tashi lafiya?”.

“Lafiya lau… Ina kwana?”.

“Lafiya lau… Rumaaa na rasa yadda zanyi zuciyata kamar zata fashe nikeji…”.

Ya karasa maganar kamar zaiyi kuka, fuskarsa dauke da damuwa….

Daga daya bangaren Rumaaa tace,

“Kayi hakuri yaya Rafeeq kaci gaba da Addu’a…”.

“Na gode sosai rumaaa… Akwai abun da kike bukata?”.

Rumaaa tayi jim, yace,

“Idan akwai kika b’oye kin san abun da hakan yake nufi…”.

Rumaaa tayi jim sannan tace,

“Uhmmm… Akwai gown din da na gani ta burgeni sosai, sannan akwai wata niqab da na gani, zan turo maka hotunansu…”.

“Shikenan?”.

“Ehhh…”.

“Kin tabbata?”.

“Ehhh na tabbata…”.

“Alright then… Ki gaida man Abba da Umma…”.

“Zasu ji, ka gaida min Momy…”.

“Ni d’an aikenki ne, ki kirata ki fada mata da kanki…. Koda yake zan fada mata… I will call you later, am hanging…”.

Rafeeq yayi hanging call din ya dafe kai tareda lumshe manya-manyan idanunsa, fuskarsa dauke da damuwa….

**********

Rumaaa ta zare wayar daga kunnanta tareda dropping dinta akan dressing mirror, ta turo baki sannan tace,

“Yaa Rafeeq, mutum yana bahaushe amma magana daya biyu sai ya had’a da turanci, bana tunanin zai sauya…”.

Sai kuma ta mik’e ta wuce bathroom, ta jima a bathtub tana wasa da kumfa sannan ta sakarwa kanta shower ta fito tareda jawo bathrobe ta zura, ta d’aura karamin towel a saman kanta, OMG Wow, ashe haka skin dinta yake da kyau gashi sumul-sumul, ga santala-santalan cinyoyinta, tayi taking steps wurin sink tayi brush sannan ta fice, ta k’arasa gaban mirror ta warware towel dake saman kanta ta jawo hand dryer tayi drying dogon gashin kanta ta tajeshi sannan ta mulkeshi da mayukan gashi ta kara tajeshi ta had’eshi tayi mashi gammo da kyar, tayi applying cream, powder kawai ta shafawa fuskarta ta fesa body spray, ta juya tayi taking steps wurin closet dinta tana budewa naga ashe babba ne sosai, kayan sakawa kala-kala sukayi appearing, closet din yana da girma sosai, kayan sakawa dake cikinsa masu kyau da tsad’a, bangaren gown daban, bangaren atamfofi daban, bangaren komai daban, lace, material, hijab da sauransu amma babu kananan kaya a ciki, wata atamfa ta dauko dinkin riga da skirt ne, kayan sunyi mata kyau sosai, ta tsaya gaban mirror tana k’arewa kanta kallo duk da babu makeup akan fuskarta amma tayi kyau sosai looking lovely and breathtaking, skirt din eleven pieces ne ya matseta amma kadan itama rigar pieces ce ta matse wurin boob sai ta bada fad’i a kasa, hannun rigar karami ne style din yayi kyau sosai, figure dinta sunyi appearing sosai, wow tayi matukar kyau, smile ne yayi escaping akan lips dinta ta jawo wani box ta bud’eshi, wow wani necklace, earrings, ring da bracelet din gold ne sukayi appearing daga ganinsu suna da matukar tsad’a sakasu tayi sannan ta daura kallabi ta rufe gashin kanta rub daukar wayarta dake akan mirror tayi tai taking steps wurin shoes rack ta saka wasu stilettoes masu sling back heel, skirt din ya rufe takalman kasancewar yayi mata tsayi, ta juya ta kama handle tareda murd’awa ta fice saidai wani sanyi ne ya doki fuskarta da sauri ta koma da baya ta jawo long hijab har kasa ta zura sannan ta fice tareda shiga door dake daya bangaren wanda yake dauke da room and parlour, wasu manya-manyan set din kujeru ne a ciki, center table tareda fridge a gefe, salaam tayi sannan ta shiga, wata kyakykyawar mata barumaya dake zaune akan one seater ta amsa mata, saida ta gaidata sannan ta cire takalman dake kafarta tareda zare hijab, ta zauna akan sofa, tace,

“Umma… Yaa Rafeeq yana gaidaki…”.

Umma tayi murmushi sannan tace,

“Ina amsawa… Kunyi waya kenan?”.

Rumaaa tace, “Ehhh kafin in shiga wanka ya kirani…”.

Umma ta gyad’a kai kawai yayinda Rumaaa ta duk’e tareda maida hankalinta akan majigin wayar dake hannunta….

Umma tayi zuru tana tunani fuskarta dauke da damuwa, a hankali tears suka soma gangarowa daga fuskarta….

Rumaaa bata lura ba kasancewar baki daya hankalinta yana akan waya, pictures din wata gown tayi sending ma Rafeeq sannan ta duba Reply din da Besty dinta tayi mata…..

 

_Maasha Aallah_.

 

Murmushi ne ya sub’uce mata, cikin ranta tace,

“Besty na kenan… Aysha Abdul’aziz Muhammad…”.

 

Typing tayi….

 

_Hmmmm_

 

Reply aka yi mata….

 

_Kinyi kyau, you looks gorgeous_

 

Smile ne yayi escaping akan lips dinta tayi reply….

 

_Na gode_

 

Reply aka yi mata….

 

_Alright then, tabbas naji d’ad’i sosai da ya kasance na samu godiya daga Breathtaking and beautiful Babe kamarki_

 

Rumaaa tayi jim tareda zaro idanunta tana k’ara kallon reply din, da sauri tayi typing….

 

_Keh Aysha Abdul’aziz Muhammad ban san tsiya_ 😹

 

Reply aka yi mata…..

 

_Ba ita bace_

 

Rumaaa ta k’ara zaro idanu sannan tayi typing….

 

_Toh wacece?_ 🤔🙄

 

Reply aka yi mata…..

 

_Wacece ko waye ba? Please Babe ki daina maidani mace bayan ni namiji ne, ki duba dp dina koda yake anyway ba Aysha bace Brother dinta ne Adeel_.

 

Reply tayi…..

 

😨😱🙆🏻 _Ohhh amma wayarta ce koh? Don ita da kanta ta bani numbar tace in tura mata hotunana_

 

Reply aka yi mata……

 

_A’a wayata ce, wayarta ta samu matsalar screen_ 🤗

 

Rumaaa ta zaro idanu tareda dafe goshi, cikin ranta tace,

“Ohhh ni rumaaa na taresu, shikenan ya gama kalleni…”.

Dagowar da zatayi ta hango Umma a wani yanayi na damuwa, hawaye na bin fuskarta, da sauri ta saki wayar ta mik’e tayi taking steps ta karasa wurinta da sauri, ta kama hannunta tace,

“Umma… Umma… Umma… Mi ya sakaki kuka?”.

Umma tayi jim sai kuma tayi mata pointing wani katon frame na picture din Rafeeq, wani Breathtaking handsome guy mai kama da rumaaa sak, banbancin kawai shine ita macece shi kuma namiji sannan ita tana da tribal marks a fuskarta yayinda shi kuma ba ya dashi….

Ummaaa tace, “Rafeeq… Rafeeq yana bani tausayi yaron kirki amma ya kasa samun wadda zata soshi saboda Allah saboda tarin dukiyar dake gareshi… Kina gani duk wadda ya nuna yana so sai ta gama yaudararshi ta wankeshi ta samu dukiya a wajanshi sannan ta gujeshi, wasu kuma Allah ne yake taimakonshi ya gane ba don Allah suke sonshi ba…. En mata sai bibiyarshi suke saboda tarin dukiyar dake gareshi… Ya rasa wacce zata soshi saboda Aallah…”.

Rumaaa tayi rau-rau da idanu tareda goge hawayen dake fuskar Umma sannan tace,

“Umma Addu’a zakiyi mashi… Ba kuka ba…”.

Umma tace, “Rafeeq yaron kirki, kina gani duk mahaifinki yaqi yarda akan ya gyara gidan nan amma sai ya turashi Makka sannan ya saka aka gyara gidan nan… Kanne en mata guda ukku Rafeeq yake dasu a garin nan amma daga Abbanki har en uwanshi an rasa wanda zai bashi diya, yaron nan daga ganin yadda yake cikin damuwa za’a gane aure yake so”.

“Umma ki fahimci su Abba, yanzu cikinsu duk wanda yace ya bashi diya cewa za’ayi saboda kudinshi ne”.

“Hakane kuma…”.

Rumaaa tayi jim fuskarta dauke da damuwa, cikin ranta tace,

“Kadda ka damu yaya Rafeeq zan taimaka maka in nuna maka inda zaka samu wacce zata soka saboda Aallah, wacce zata zauna da kai koda zaka rasa duk abun da ka mallaka na tarin dukiya…”.

Muje zuwa 😘

 

 

 

Littafin Ni da yaya Rafeeq na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take so zata samu akan Naira dari hudu 400, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057, amma na rokeki da girman Allah idan ba siya zakiyi ba kadda kiyi min magana, Na rokeki da girman Allah idan ba novel dina zaki siya ba kadda kiyi min magana

 

 

 

*One love,*

[06/02, 8:04 pm] +234 916 947 2057: 💨 *NI DA YAYA RAFEEQ* 💨

_Chasing my heart_

By Hafsat Hisham

 

Page 3 and 4

Free page

 

Littafin Ni da yaya Rafeeq na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take so tayi min magana via WhatsApp 09169472057, amma na rokeki da girman Allah idan ba siya zakiyi ba kadda kiyi min magana, Na rokeki da girman Allah idan ba novel dina zaki siya ba kadda kiyi min magana

 

 

Rumaaa ta mik’e ta wuce bedroom dinta, wuni tayi tana kitsawa tana kwancewa akan abun da zuciyarta take kitsa mata, tana son ta taimaka mashi amma akwai risk….

NIGHT,

Rumaaa ce zaune akan praying mat bayan da ta gama sallar Magrib, bata mik’e ba har saida tayi Sallar Isha’i, tayi shafa’i da wutiri, ta mik’e ta wuce saida tayi dinner tayi hira tareda iyayenta sannan ta wuce bedroom ta rage kayan dake jikinta ta d’aura towel ta wuce bathroom ta jima cikin bathtub tana durje jikinta da sabula masu kamshi sannan ta sakarwa kanta shower, tayi brush tareda dauro alwalla ta fito tareda zama akan stool tayi applying cream tareda zura wata half night gown transparent tayi taking steps ta zauna gefen gado tayi jim, can kuma sai ta mik’e ta bud’e closet ta binciko wani SIM card da ta siya kwanan nan bata fara amfani dashi ba don haka babu wanda ya santa dashi, ta zauna gefen gado ta bud’e bedside drawer ta zaro wata k’aramar waya mai madannai, ta zare battery ta saka SIM din, ta jima tana rubuta text message tana gogewa har finally ta samu karfin gwuwar tura mashi, tayi jim sannan cikin ranta tace,

“Kayi hakuri yaya Rafeeq duk abun da na rubuta ba daga zuciyata yake ba, na rubuta ne domin in taimaka in fahimtar da kai a inda zaka samu wacce zata aureka ta zauna da kai duk rumtsi ta soka saboda Aallah…”.

Ta kakkab’e bed tayi addu’a tareda light off ta kwanta akan bed tayi lamo kamar tana bacci amma ba bacci take ba, ta jima sannan bacci yayi awon gaba da ita….

*********

_ABUJA_

Katon mansion ne sosai wanda yake dauke da katon part guda daya sannan kananan part haka, swimming, garden, parking lot, katon mansion ne sosai, Rafeeq ne a katon parlour din wanda yake dauke set din kujeru guda shidda, designer and expensive, yayi relaxing akan sofa yayi zuru yana jin wani ciwon mara mai tsanani, d’aurewa kawai yake, Rafeeq Ahmad Almustapha kenan, saurayi d’an kimanin shekaru ashirin da hudu, wata cute Hajiya ce zaune opposite dashi, ta dubeshi tace,

“Rafeeq ka rage sakawa kanka damuwa ka cigaba da addu’a, Aallah yana tare da kai, ka tashi ka wuce sama…”.

Rafeeq ya mik’e tareda mata good night ya wuce sama ya fad’a bedroom dinsa ya rage kayan dake jikinsa ya d’aura towel ya wuce bathroom, yayi tsaye tareda dafa glass ya sakarwa kanshi shower, ruwan suna dropping akan jikinsa yana tunanin duniya, desire ta dameshi yana tsoron shiga halaka, ya jima sannan ya kashe shower din tareda d’aura towel yayi brush tareda dauro alwalla ya fice yayi applying cream tareda feshe jikinsa da perfumes sannan ya saka boxer kawai ya haye saman katon royal bed dake cikin katon dakin wanda yake dauke da komai na more rayuwa, wayarsa ce tayi haske ya jawota tareda dubawa, wata bakuwar number ce ta turo mashi message kamar haka….

“Salaam alaika, tabbas ranar wanka ba’a b’oye cibi haka abun yake, a yau na yanke shawarar bayyana maka abun dake raina, na gaji da zurfin ciki wanda yake k’ara nisantani da kai, na jima ina crushing dinka, ina matuk’ar sonka saboda Aallah ba don tarin dukiya dake gareka ba, zan iya zama da kai koda kuwa baka da ko sisi… Na d’ad’e da sonka manne a cikin zuciyata, ina kaunarka, na dauki rabin shekarun dake gareni a yanzu cikin sonka, zan iya cewa a yanzu kaunarka nike, ina yawan tunaninka, idan nayi tozali da kai sai inji sanyi a cikin zuciyata ina jin tamkar kadda mu rabu, dole take sakawa nike hakura in rabu da kai, na d’ad’e a cikin rumatsar sonka, ina kaunar ganinka kamar yadda nike da ikon ganin tafin hannuna a dukkanin lokacin da nike so, kayi hakuri na duba nayi tunani nayi nazari amma na kasa samun jimlar da zan saka a cikin rubutun nan wadda zatayi daidai da yadda yake nike jinka a cikin zuciyata, ina bakin cikin halin da kake ciki kana neman wadda zata soka saboda Aallah, bayan akwai wadda ta d’ad’e tana kaunarka fiye da ranta, na b’oye kaina ne saboda bana son shiga damuwa, na gudun fassarar da za’ayi min, a dangantani da mai kwadayi ko son abun duniya, ka yarda dani saboda Aallah nike kaunarka… Daga mai kaunarka… Rafeeq Angel…”.

Rafeeq yayi jim yana karanta message din yana maimaitawa sai ya samu kansa da son sanin wacece wannan, yayi dialing numbar saidai tana ringing ba’a picking, saida ya ajiye miss call ukku sannan yayi jim sai kuma ya tura mata text message kamar haka….

“Wacece ke?”.

Smile ne yayi escaping akan lips dinsa ya kwanta akan bed yayi lamo ya jima sannan bacci yayi awon gaba dashi….

***********

The following day kiran sallar Subh ne ya tayar da Rumaaa daga baccin da take, ta mik’e tareda uttering addu’ar tashi daga bacci sannan ta duro daga saman gado ta wuce bathroom, Umma ce ta lek’o tashinta sallar Subh ta samu ta tashi ta juya ta koma, saida ta watsawa jikinta ruwa sannan dauro alwalla ta fito, ta shimfid’a praying mat tareda zura long hijab saida tayi raka’atanul Fijr sannan tayi sallar Subh, bayan ta gama akzar din safiya ta jawo wayarta ta bud’e data, message ne suka soma racing, suna shigowa babu kakkautawa, jim tayi tana kallon message aka turo mata daga numbar da k’awarta Aysha Abdul’aziz Muhammad ta bata ta tura mata pictures, jim tayi tana kallon majigin wayar tana k’ara kallon message da aka turo mata….

 

_Ya kikayi shiru ya kamata ki bada sako in hada da hoton in bata_

 

Saida tayi jim sannan tayi mashi reply….

 

_Kace mata Rumana Abdurrahim Rumah (Rumahhh) ta turo hotunan kuma ta kyauta, na gode da abun da tayi min_

 

Aka yi mata reply….

 

_Sure… Zan fad’a mata by the way Sunana Adeel Abdul’aziz Muhammad brother din Ayusher_ 😊

 

Tayi mashi reply….

 

_Ohhh_

 

Yayi mata reply….

 

_Ina kin bani dama ina son in bayyana maki sirrin dake raina, wani yanayi ne wanda na tsinci kaina tun daga lokacin da nayi tozali da hotonki_

 

Rumaaa tayi jim tana kallon majigin wayar sannan tayi mashi reply….

 

_Ni kuma_ 🤔🙄

 

Adeel yayi mata reply….

 

_Yeah_

 

_Ina jinka_

 

_Sunanki ya hadu, ki duba kiga wani hadaddan suna Rumana Abdurrahim Rumah, am serious, really sunanki yana da dadi, gashi baki daya sunayen guda ukku sunyi matching da juna_

 

Rumaaa ta dafe kai tana kallon reply gani tayi yana recording voice, voice ya turo mata ta bud’e, wata husky voice ce take magana, a hankali yace,

 

_Rumaaa ina sonki, I love you so much_ 😘

 

Da sauri tayi dropping wayar yayinda gabanta ya yanke ya fad’i, ta dauki wayar tareda kashe data, tayi dropping dinta akan bedside drawer, ta bud’e locker tareda zaro k’aramar wayar, silent wayar take kuma tana sane ta sakata silent, miss call ukku ya ajiye mata tareda sakon text message….

 

_Wacece ke?_

 

Saida tayi jim sannan tayi mashi sending message….

 

_Yaa Rafeeq… Ina daya daga cikin cousin dinka guda ukku dake jihar Katsina_

 

A hankali tace,

“Kayi hakuri yaya Rafeeq duk abun da na rubuta ba daga zuciyata yake ba, na rubuta ne domin in taimaka in fahimtar da kai a inda zaka samu wacce zata aureka ta zauna da kai duk rumtsi ta soka saboda Aallah…”.

Sai kuma ta mik’e ta soma kaiwa da komowa tana zancen zuci kamar haka….

“Anya kuwa ban yi ganganci ba… Idan ya gane nice akwai damuwa… Sunana shine Rumana Abdurrahim Rumah amma da Rumaaa ake kirana kasancewar both iyeyana sun fito ne daga dangin ruma, shekaruna goma sha shidda amma kasancewar ina da tsayi kadan shiyasa wasu suke ganin kamar na wuce hakan, ina da kyau sosai, good looking farar barumaya mai matuk’ar kyau fiye da misali, ina da haske sosai har yellow skin dina yake, domin idan mutum ya kalli kafata zaiyi wahala ya banbance tsakanin hasken saman kafata da hasken kasanta… Natural beauty…. Ina da dogon gashi wanda yake wara-wara kamar rubber ya sauko har ya wuce gwuwar kafata… Abubuwa guda biyar a game dani sune… Ni ma’abociyar saka long hijab ce in rufe fuskata da niqab… Saboda tsayin gashin kaina ina yawan yi mashi gammo ne in tamkeshi da kallabi ta yadda koda sili guda daya ba’a hangowa… Kalmar *rumatsa* ta zauna a cikin bakina zaiyi wahala mutum ya zauna tare dani ba tareda na ambaci wannan kalma ba… Idan ina magana ina yawan yin jim ina jujjuya idanuna… Idan mutum yayi min magana daga bayana ko kuma wani abu ya faru wanda zan juyo da kaina, ina juyar dashi ne ta gicce not straight, gammo da nike ma dogon gashin kaina in rufeshi da kallabi yayi zororo shine yake k’ara fitar da yanayin… Sunan Mahaifina Abdurrahim suleiman amma ina kiranshi da Abba, BARUMAYE NE, dan Asalin wani karamin kauyen Rumamawa dake karkashin karamar hukumar Batsari dake a jihar Katsina, su hudu ne a wurin iyayensu, Rabi’u ne babba wanda suke kira da Rabe, sai mahaifina Abdurrahim, sai k’anwarshi Shamsiyya, sai autarsu Mufida, baki dayansu suna kama da juna shiyasa nike matuk’ar kama da Yaa Rafeeq… Babban yayansu rabe, da mahaifina da autarsu mufida wadanda suka aura en asalin kauyensu ne, Shamsiyya ce ta auri bare, wani d’an kasuwa, mai kudi wanda yake a birnin tarayya Abuja, d’an Kaduna ne amma mazaunin Abuja, yaro guda daya suka haifa Rafeeq wanda yake kama da mahaifiyarsa sak babu abun da ya baro a kamanninta, Alhaji Ahmad Almustapha ya rasu tun kafin a haifeni, saida Rafeeq ya mallaki hankalin kansa ya kammala karatunsa sannan ya amshi gadonsa ya cigaba da kula da dukiyarsa…. Ni daya mahaifina ya haifa bayan shekara da shekaru da suka shafe babu haihuwa… Itama Mufida diyarta guda daya Ramlert wacce abokiyar haihuwata ce… Abba Rabiu shine kawai yake da y’ay’a maza masu yawa amma shima diyarshi mace guda daya ce, Raheelerh itama abokiyar haihuwata ce…. Bayan da Rafeeq ya gaji dukiya da kamfafoni da kaddarorin mahaifinsa, ya tashi ne mutum mai son danginsa, ina good time dashi sosai, yana da tausayi sannan ya kasance mai yawan taimako, shine wanda ya dauko en uwan mahaifiyarsa ya maido dasu cikin garin Katsina, shine ya maidomu cikin gari, ya siya masu gidaje a unguwanni daban-daban amma a lokacin ban da Mufida sai daga baya sannan mijinta ya amince suka dawo cikin gari, ya samu sana’a yana rik’e da iyayensa, a lokacin da Yaa Rafeeq ya maidomu cikin garin Katsina, ina karama ne shekaruna daidai sakawa a makarantar boko don haka ya sakani a wata private school, Yaa Rafeeq yana iyakar kokarinsa domin ganin ya tallafawa su Abba, a bangaren Abba Rabiu yana sana’a amma duk taimakon da ya bashi yana amsa ne yayi godiya tareda saka mashi albarka amma a bangaren mijin Aunty Mufida wani lokacin yana amsa, wani lokacin kuma yace ya barshi ya gode, a bangaren Aunty Mufida kamar Abba Rabiu itama tana amsa ne tayi godiya, a bangaren Abbana shi mutum ne mai san dogaro da kai, ba ya da son abun duniya, ba ya shishshigewa mutane musamman masu kudi, saboda ba ya da kwadayi haka ya tsani a dangantashi da wannan kalmar ta kwadayi ko san abun duniya, ina goyon bayan wannan abu, a lokacin da Yaa Rafeeq ya fara taimakawa Abba, Abba saidai yace ya gode amma ba zai amsa ba, ya nemar mashi aiki kawai kuma ba’a karkashin kamfaninsa ko inda yake mallakinsa ba, Yaa Rafeeq yaso Abba ya rink’a amsar alkhairi da yake mashi amma abun yaci tura shine ya nemar mashi aiki a wurin wani friend dinsa amma da yake cikin kurarrran lokaci ne, aikin ba wani babba bane, daga baya Yaa Rafeeq ya samar mashi wani aiki wanda yafi wancen amma Abba refused, yace yana jin dadin aikinshi don haka bazai dainashi ya koma wani aikin ba, dole Yaa Rafeeq ya kyaleshi, ya cigaba da yunkurin taimakawa Abba amma sai Abba ya nuna b’acin ransa kuma ba ya amsa, ni dai duk idan zaizo garin nan yana min tsarabar kayan sakawa, duk abun da ya gani Rumaaa, am his favorite cousin, shekaru sun shud’e gidanmu ya fara lalacewa yana gurgurewa, shine Yaa Rafeeq yayi maganar gyara gidan amma Abba refused shine ya bari saida ya tafi saudia sannan ya saka aka gyara gidan ya koma yadda yake a halin yanzu, before gurgurarran gidan kasa ne, lokacin da Abba ya dawo yayi godiya ba tareda yayi korafi ba… Lokacin da na gama primary school, Abba yace sam bazan cigaba da karatun secondary ba, aka yi juyin duniyar nan amma yaqi yarda yace tunda dai na iya karatun Hausa da na Turanci kuma na iya turancin a furuci, Alhamdulillahi karatun ya isa haka sai in cigaba da zuwa Islamiyya, ina gani Raheelerh ta cigaba da karatun secondary da yake tare muke, Ramlert ce take a bayanmu amma sai ban damu ba tunda dai babu yadda zanyi, duk da ina son karatun kuma ina da buri amma babu yadda zanyi, rashin cigaba da karatun secondary ya saka na koma zaman gida, ni kuma bana son zaman hakanan shine na fara what’sApp, watching movies and rest of it, sauran abun da ya biyo baya damuwar da Yaa Rafeeq yake ciki na rashin samun wacce zata soshi saboda Aallah, shine ni kuma na yanke shawarar in rink’a tura mashi text message, sannan in bayyana kaina a daya daga cikin cousin dinshi mata dake garin nan, ina fatan yayi tunanin Ramlert ce ko kuma Raheelerh na tabbata kowacensu zata soshi saboda Aallah koda kuma bashi ko sisi… Amma wannan abun yana tare da damuwa musamman idan ya gano nice… I can’t imagine abun da zai faru…”.

Ta zauna gefen gado yayinda gabanta ya yanke ya fad’i, saida tayi kalaci sannan ta shirya cikin kayan islamiyya tareda rataya bag ta zura long hijab wadda har tana sharar kasa ta rufe fuskarta da niqab, ta fito tayi ma parent dinta salaam sannan ta wuce saida tayi doguwar tafiya ta wuce manya-manyan gidaje sannan ta karasa makarantar, bayan an tadosu ta jero tare da wata cute fullo Babe, Rumaaa tace,

“Gaskiya Ayusher abun da kikayi min ya b’ata min rai sosai kin san wayar namiji ce amma kika saka na tura hotuna at least tunda brother dinki sai kice in tura hotunanki kawai…”.

Aysha tayi dariya sannan tace,

“Ohhhh besty am sorry… Uhmm kiyi hakuri…”.

Rumaaa tayi mata banza sai kuma tace,

“Ace mutum magana daya biyu sai ya saka turanci…”.

Aysha tayi murmushi kawai sukayi tafiya kadan suka rabu kasancewar gidansu Aysha yana kusa ne da makarantar, tana shiga ta lek’a Umma sannan ta wuce bedroom dinta ta ajiye bag ta rage kayan dake jikinta ta wuce bathroom tayi wanka ta fito ta shirya cikin wani leshe cikin fittet gown ta fito ta wuce bedroom din Ummy, wani yaro d’an neighbor dinsu ya shigo yace,

“Wani yana kiran Rumaaa…”.

Rumaaa ta dubeshi da mamaki, Umma tayi murmushi sannan tace,

“Kaje kace mashi gata nan zuwa…”.

Yaron ya juya ya koma, Rumaaa tayi jim, Umma tace,

“Ki tashi ki tafi tunda yace ba zakiyi karatu ba, wannan yana nufin aure yake son yayi maki…”.

Rumaaa ta mik’e ta wuce bedroom dinta ta zura long hijab har kasa sannan ta fice….

Adeel ne yayi parking motarsa opposite da door, yayi crossing kafafu yana kallonta yana murmushi, yana sanye da jeans tareda wata shirt mai wani irin neck amma ta sanyi ne, da hular sanyi a kansa yayi mata wani style, yayi folding hannuwa looking breathtaking and hot 🔥, kyakykyawan saurayi bafullo d’an kimanin shekaru goma sha tara, kallo daya tayi mashi ta tsaya a bakin kofa, Adeel yayi murmushi sannan yayi taking steps ya tsaya gefenta, da husky voice dinsa yace,

“Rumana…”.

Rumaaa ta d’aga mashi hannu ✋ cike da damuwa tace,

“Yaa Adeel kayi hakuri, kafi karfina, wannan soyayya ba mai yiyuwa bace, am not what you think am…”.

Adeel ya dubeta da mamaki sannan yace,

“Why did you say that? Saboda mi kika ce haka?”.

Rumaaa tace, “Saboda kafi karfina…”.

Adeel ya dubeta na tsayin wasu seconds sannan yace,

“Who told you that?”.

Saida ta juyar da kanta a gicce sannan tace,

“Yaa Adeel kai d’an masu kudi ne, ni kuma diyar talakawa, akwai dukiya a gidanku, ni kuma bamu da ita, kayi karatu ni kuma daga primary na tsaya, gidanku na alfarma ne, wannan kuwa gurgurarran gidan kasa ne ban da an gyarashi… Yaa Adeel kayi hakuri tsarin rayuwarmu ya banbanta, kaje ka nemi daidai kai diyar masu kudi, ni kuma in auri talaka daidai ni…”.

Adeel yayi jim yana kallonta yana murmushi, Rumaaa tace,

“Ba zan iya auren mai kudi ba, talaka zan aura, ni da k’anwarka Ayusher *KAWAYE NE* amma ko k’awance da kaga muna yi don ba ni da yadda zanyi ne shiyasa amma kaga ko k’awance nafi son inyi da diyar talakawa daidai ni, Yaa Adeel ka barni a matsayina, kadda ka kaini inda ban kai ba…”.

“Rumana… Shin miye laifi ne don kinyi soyayya da ni kuma kin aureni?”.

“A wurin kowa da kowa zai iya kasancewa abu mai yiyuwa amma a wurina bazai yiyu ba, laifi ne, kayi hakuri kaje ka nemi wata, kafi karfina, tsarin rayuwarmu ya banbanta, zamanmu a inuwa daya ba mai yiyuwa bane…”.

Adeel ya dubeta da damuwa sannan yace,

“Rumana… I really love you… I love you so much.. Ina sonki… Idan kina magana a haka sai inga kamar ina da hali marar kyau ne shiyasa kike guduna…”.

Rumaaa tace, “Yaa Adeel baka da mugun hali, amma kafi karfina, ka rabu da ni ka nemi daidai kai…”.

Sai kuma ta had’e hannayenta wuri daya alamar roko 🙏 sannan tace,

“Na rokeka kadda ka k’ara zuwa gidan nan, ban iya wulakanci ba, kadda ka saka a fara daukata a matsayin mai wulakanta mutane domin koda ka k’ara zuwa gidan nan bazan fito ba… Ka taimake ni, ka rabu da ni, ka manta da ni, ka nemi wata…”.

 

 

Littafin Ni da yaya Rafeeq na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take so zata samu akan Naira dari hudu 400, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057, amma na rokeki da girman Allah idan ba siya zakiyi ba kadda kiyi min magana, Na rokeki da girman Allah idan ba novel dina zaki siya ba kadda kiyi min magana

 

 

*One love,*

[06/02, 8:14 pm] +234 916 947 2057: 💨 *NI DA YAYA RAFEEQ* 💨

_Chasing my heart_

By Hafsat Hisham

 

Page 5 and 6

Free page

 

Littafin Ni da yaya Rafeeq na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take so tayi min magana via WhatsApp 09169472057, amma na rokeki da girman Allah idan ba siya zakiyi ba kadda kiyi min magana, Na rokeki da girman Allah idan ba novel dina zaki siya ba kadda kiyi min magana

 

 

Adeel yace, “Rumana…”.

Rumaaa ta juya da sauri ta shige gidansu, tayi turus tana k’arewa gidan kallo, ta zare long hijab dake jikinta ta rataya akan igiyar shanya, saida ta share gidan sannan tayi mopping dinshi kasancewar Umma bata jin dadi, ta goge tale ta wankeshi sannan ta fiddo kayan wanke-wanke tareda d’aura girki, tana girki tana wanke-wanke, tana gama girkin ta zuba a warmer ta wuce bedroom dinta saida ta duba time sannan ta rage kayan dake jikinta ta d’aura towel ta wuce bathroom saida ta gama wanke jikinta da sabula masu kamshi sannan ta sakarwa kanta shower ta fito daga bathtub tareda d’aura towel, tayi taking steps tayi brush sannan ta dauro alwalla ta fito tayi applying cream tareda zura wata gown mara nauyi ta zura long hijab tareda shimfid’a praying mat tayi sallar Zuhr, fitowarta daga bedroom yayi daidai da shigowar Abba yana dauke da leather, ta k’arasa tareda amsar leather dake hannunsa tace,

“Sannu da dawowa… Abba…”.

Abba yayi murmushi sannan yace,

“Yauwa er albarka…”.

“Ina wuni?”.

“Lafiya lau… Na sameku lafiya?”.

“Lafiya lau…”.

Abba ya wuce dakinsa, ta bishi tareda dropping leather ta fito ta dauki silver cup ta zuba mashi ruwan randa masu sanyi da d’ad’i ta kai mashi sannan ta lek’a dakin Umma, Umma ce ta fito ta wuce dakin Abba, Rumaaa ta wuce kitchen ta zuba abinci ta wuce bedroom saida tayi dam ta kora da ruwa, ta k’ara gyara bedroom din sannan ta dauko Husnil-Muslim tana dubawa….

********

_ABUJA_

Rafeeq ne zaune a study room yana going through wasu papers, black vest ce a jikinsa tareda long trouser cotton, looking hot, ya jawo wayarsa yana duba message yaci karo da wannan message, jim yayi sannan yayi dialing numbar amma a kashe take, saida yayi jim sannan yayi dialing wata number yayi jim sannan yace,

“Salaam alaiki… Hello… Hold on, ba zaki hanani magana da turanci ba, hausar guduwa takeyi… How are you… Angel… What wrong with it don na kiraki Angel after all you are my favorite cousin… Bye… Take care…”.

Yayi hanging call din tareda relaxing akan kujera ya lumshe idanu….

**********

Rumaaa tayi jim tana kallon majigin wayar cike da mamaki, ta ware idanu sai kuma tayi dropping wayar sannan ta cigaba da abun da take, tayi jim tana tunanin abun da zata tura mashi idan yayi mata reply domin ta kagara ta k’are wannan wasan….

Umma ce ta lek’o tace,

“Aahhh rumaaa karatu kike?”.

“Ehhhh….”.

“Da fatan kinyi sallah?”.

“Nayi sallah… Shine nike karatu…”.

“Aallah ya taimaka…”.

“Aameen…”.

“Yauwa er albarka…”.

Umma ta juya ta wuce, Rumaaa ta cigaba da karatun da take, saida ta fara taya Umma aiki sannan ta wuce bedroom ta watsa ruwa tareda dauro alwalla, tayi sallar Asr sannan ta shirya ta wuce Islamiyya….

NIGHT

Rumaaa ce zaune a tsakiyar gado tana juya k’aramar waya dake hannunta tana nazarin message da ya turo mata inda yake cewa….

“Wacece ke a cikinsu?”.

Saida tayi jim sannan ta soma mashi typing message….

“Barka da dare, wannan sako ne daga zuciyar Rafeeq Angel, bana son ka wahalar da kanka kana min wannan tambayar saboda ba zaka sameta daga gareni ba, ina ganin idan har na dace da kai zaka iya ganeni, idan baka ganeni ba then I think i didn’t deserve you… Watakila Ramlert Fuhad Ruma ce ko kuma Rumana Abdurrahim Ruma ko kuma Raheelerh Rabiu Ruma… Tabbas akwai sunana a ciki amma who’s know idan har zaka iya canka daidai, ban san shiga rumatsa don haka kayi nazari da kanka sannan ka gano wacece ni a cikinsu… Ka yarda da ni ina sonka ne saboda Aallah… Ka huta lafiya… I love you… From your Angel… From your crush… Rafeeq Angel…”.

Tayi jim tana magana cikin ranta….

“Kayi hakuri yaya Rafeeq duk abun da na rubuta ba daga zuciyata yake ba, na rubuta ne domin in taimaka in fahimtar da kai a inda zaka samu wacce zata aureka ta zauna da kai duk rumtsi ta soka saboda Aallah…”.

Sai kuma tayi mashi sending message din tareda kashe wayar ta sakata a locker ta kwanta tareda rufe jikinta da duvet ta lumshe idanu, a hankali ta bud’e idanunta tace,

“Yaa Rafeeq tabbas nice na turo sakon amma ka taimaka min kadda fahimci nice saboda idan ka gane akwai damuwa… Ka dauka Ramlert ce ko kuma Raheelerh… Ka dauka daya ce daga cikinsu ka aureta ku zauna cikin aminci, farin ciki da kauna…”.

Ta jima sannan bacci yayi awon gaba da ita….

**********

Rafeeq ne zaune akan kujera yayi jim yana tunani, brown jallabiya ce a jikinsa mai zip a gabanta, tunda yayi receiving message din nan ya kasa bacci yana tunani tareda nazari akan wacece, raba dare yayi yana nazari, ya kasa bacci, idanunsa har lumshewa suke saboda bacci amma he refused to sleep, a hankali yace,

“Kadda ki damu, you don’t have to worry yourself, In shaa Aallah zan ganeki a daren yau amma ba zan nuna maki ba har naji ina maki kwatankwacin son da kikeyi min…”.

Sai kuma ya lumshe idanunsa yana nazari akan messages din da ta turo mashi, tabbas a cikin su ukkun, dabi’unsu sun banbanta, experience dinsu na rayuwa ya banbanta, kowace tana da yanayin maganarta da yadda take magana, da yanayin yadda ya kamata rubutunta ya kasance, da maganganun da tunaninta zai bata, finally kwalliya ta biya kudin sabulu domin ya gano wacece saboda tabar baya da kura da yawa a sakonninta wadanda sune suka taimaka mashi wurin ganeta, smile ne yayi escaping akan lips dinsa, yayi jim yana ayyanawa a ranshi cewa bazai taba nuna mata ba har sai ya tabbatar da yana mata kwatankwacin son da take mashi….

 

_{Shin wacece yake tunani? Shin miye zai faru a nan gaba? Anya kuwa babu rudani a nan gaba? Muje zuwa_

 

Tunda Rumaaa ta tura mashi wannan sakon ta kashe wayar ta manta da komai ta cigaba da rayuwarta happily….

**********

Adeel ya kasa samun nutsuwa, tunda yabar gidansu Rumaaa tunaninta yake manne a ransa, he love her so much amma she refused to give him chance, yana matuk’ar sonta amma taqi kulashi, idan ya kira bata picking idan ya ajiye mata message babu reply, he is totally confused, karshe ya yanke shawarar ya samu brother dinshi Ashraim ya sanar dashi idan taso sai suje suyi magana da mahaifinta….

Waye Adeel?

Late Alhaji Abdul’azeez Muhammad, kafin rasuwarsa shararren d’an kasuwa wanda yayi suna a duniya, Aallah ya azurtashi da tarin duniya mai yawan gaske kuma yana kokari matuk’a wurin ganin ya taimakawa addinin musulunci, shekaru biyu kenan da rasuwarsa kuma ya samu shaida mai kyau a bakin mutane, kafin rasuwarsa yana da mata hudu, Khalifa shine sunan da suke kiran elder son of the house, late Alhaji Abdul’aziz yara da yawa da jikoki, bayan raba gado kowace ta koma separate house tareda yaranta amma duk da haka suna zumunci sosai, mahaifiyarsu Adeel itace mata ta ukku a wurin marigayi, bafullatana ce kyakykyawa, duk y’ay’anta ita suka biyowa shiyasa suke matuk’ar kama da junansu kamar tagwaye, tana da y’ay’a guda ukku, maza biyu da mace guda daya wacce itace autarta, Ashraim Abdul’azeez Muhammad shine d’anta na fari followed by his little brother Adeel Abdul’azeez Muhammad and then autarsu Aysha Abdul’azeez Muhammad….

Ashraim yana da shekaru ashirin da daya, yana aikin government kuma yana had’awa da kasuwanci wanda ya samu expressing daga mahaifinsu, yana da tarin dukiya amma har zuwa wannan lokacin baiyi aure ba, yana da gidaje a different part of the world, yana da gidaje a jihohi daban na wannan kasa tamu amma yana zaune ne tareda mahaifiyarsu, yana da matuk’ar kyau sannan kamarshi daya sak da Adeel ban da shekaru da suka banbantasu da babu tantama mutane zasuyi masu kallon tagwaye ne….

Aysha k’awar rumaaa ce, ajinsu daya a makarantar Islamiyya, shekarunta goma sha shidda….

Adeel kyakykyawan matashin saurayi ne d’an kimanin shekaru goma sha tara, good looking and hot, bafullo, fari ne sosai, yana da tsayi, dakkakken namiji mai suffar legends, yana da dogon hanci tareda madaidaitan idanu, cute lips, brow dinshi a kwance yake lub kamar rubber kuma yana da yawa, yana da yalwataccen gashi mai yawa wanda yake kullum a kwance kamar na Arabs, kuma naturally yake haka, yana da dabiu masu kyau sannan yana matuk’ar son rumaaa, normally yafi saka manyan kaya, yana saka kananan kaya amma ba sosai ba, yana karatu a university ne yana had’a degree dinsa ta farko…..

*********

Ashraim yana zaune a bedroom dinsa yana aiki akan system, Adeel ne yayi knocking tareda salaam sannan ya murd’a handle ya shiga ya zauna akan stool yana murmushi, Ashraim yace,

“Why are smiling?”.

“Yaa Ashraim…”.

“Am hearing you…”.

“Dama akan wata magana ne…”.

Ashraim ya ture system dake gabansa tareda maida hankalinsa akan little brother dinsa sannan yace,

“Alright then… Ina jinka…”.

Adeel yayi jim yana sosa kai sannan yace,

“Dama wata yarinya na gani ina so… I love her so much…”.

Ashraim yayi dariya sannan yace,

“Aahhh silly boy, miye na kunya after all you are mature… Uhmm… Bani labari… Daga nan sai aka yi mey?”.

Adeel yace, “Naje gidansu amma bata saurareni ba, tace ita ba zata auri mai kudi ba, talaka take so daidai ita, I love her so much amma she refused, shine nike son kayi magana kuje gidansu ku nemar min izini wurin mahaifinta in rink’a zuwa zance wurinta…”.

Ashraim ya ware idanu sannan yace,

“Adeel wannan shine abun da ya kamata ka fara tun farko amma shine ka tafi wurinta kai tsaye…”.

Adeel yayi murmushi kawai, Ashraim yace,

“Wacece wannan salihar wacce take gudun abun duniya bayan yanzu wasu en matan a wannan zamani idanu a rufe suke neman mai kudi su aureshi no matter what they have to do, amma ita gudun mai kudi take tana neman talaka… Buddy… Meyyy sunanta?”.

Adeel yayi jim yayinda smile yayi escaping akan lips dinsa yace,

“Sunanta Rumana Abdurrahim Rumah amma ana kiranta da rumaaa ne, BARUMAYA CE…”.

Ashraim yayi jim yayinda gabansa ya yanke ya fad’i, ya kalleshi idanu a waje sai kuma yayi sauri ya gyara yanayinsa, yayi murmushi sannan yace,

“Buddy kace aure kake so… Alright then zanyi magana da Hajiya da yaya Khalifa, kaga sai muzo mu tattara muyi maka aure tunda shi kake so…”.

Adeel yace, “No after all yarinya ce sosai, she is still young, ba zata wuce sa’ar Ayusher ba, besty dinta ce, ajinsu daya a makarantar Islamiyya…”.

Ashraim yace, “Alright then…”.

Sai kuma ya jawo system ya cigaba da abun da yake, ba tareda ya d’ago ba yace,

“Kadda ka damu zanyi maganar da yaya Khalifa sai mu samu wani muje gidansu yarinyar, mu nemo maka izinin, ga makullin mota can akan bedside drawer ka dauka na sabuwar mota dake compound ne, motarka ce tana cikin sabbin motocin da nayi order naga ka nuna interest a kanta ne…”.

Adeel ya mik’e da sauri tareda hugging dinsa yace,

“Thank you so much yaya Ashraim… Na gode sosai… Aallah ya saka da Alkhairi… Aallah ya k’ara arziki… Akwai chilling…”.

Ashraim yayi murmushi kawai, Adeel ya dauki makullin motar ya fice da smile akan fuskarsa, kyauta halin Ashraim ne, suna jin dadinshi sosai, ya maye masu gurbin mahaifinsu….

A ranar Ashraim ya samu Ammi sukayi maganar sannan yaje ya samu Khalifa sukayi maganar, the following day suka shirya suka wuce gidansu rumaaa tareda wani uncle dinsu wanda yake k’anin mahaifinsu….

_GIDANSU RUMANA_

Sunyi sa’a sun samu Abba a gida, ya saukesu a dakinshi, bayan an kawo masu drinks, Abba yace,

“Sannu da zuwa… Saidai ban ganeku ba…”.

Ashraim yace, “Hakane… Sunana Ashraim Abdul’aziz Muhammad, d’a a wurin marigayi Alhaji Abdul’aziz Muhammad, wannan shine babban yayanmu, wannan kuma k’anin mahaifinmu ne… Abun yake tafe damu shine k’anina Adeel ne yaga diyar wurinka Rumana shine muka zo nemar mashi izini ya rink’a zuwa zance wurinta…”.

Abba yayi jim yana kallonsu yana gujewa diyarsa wulakanci gata kuma mai sanyin rai amma kuma ba suyi kama da hakan, da murmushi yace,

“Naji abun da kuka zo dashi, kuma mahaifinku mutanen kirki ne, Aallah yayi mashi rahama, babu damuwa, kuce mashi na bashi izini ya rink’a zuwa zance wurinta, ya nemi so a wurin yarinya amma ku sani ban ce na bashi aurenta ba, na bashi izinin zuwa zance wurinta ne, macece ita, allura ce a cikin ruwa mai rabo zai dauka, Aallah ne kadai yasan mijin da zata aura, a matsayina na mahaifinta zanyi k’ok’arin hadata da miji na gari, ban damu ba koda yafi kowa talauci a garin nan, in dai zai riketa bisa amana akan tafarkin Addinin musulunci, Alhamdulillah, koda zata kawo min shi a matsayin wanda take so, idan na duba naga bai dace da halayen da nike so ba, tou bazan bashi aurenta ba…”.

Khalifa yaji dadin wadannan maganganun da Abba yayi, yace,

“Hakane, ai dama shi aure babu ruwanshi da kudi, ko sarauta ko kuma matsayi, hali na kwarai yake bukata da kuma soyayya, mun gode Malam, kuma zamu fada mashi abun da kace…”.

Abba yace, “Matar mutum kabarinsa idan Aallah yayi matarshi ce, shikenan, idan kuma ba matarshi bace, sai yayi hakuri, kadda kuga laifina saboda na fad’a maku d’azu kuma yanzu zan k’ara fad’a maku, izinin zuwa zance wurin Rumaaa kawai na bashi, ba aurenta ba… Allura ce cikin ruwa, mai rabo ka dauka… Aallah ya shige mana gaba…”.

A tare suka ce,

“Aameen…”.

Suka rufe taro da addu’a sannan suka wuce, Khalifa tareda uncle sun wuce a motocinsu, Ashraim yayi ma motarshi key call ya shigo wayarsa ya kashe motar tareda picking call din….

Rumaaa ce ta shawo corner tana taking steps a hankali ta dawo daga aiken da Umma tayi mata, tana sanye ne da long hijab har kasa ta rufe fuskarta da niqab, tunda daga nesa ta hangoshi ta glass, gabanta ne ya yanke ya fad’i she thought Adeel ne, tayi taking steps tareda tapping akan glass din motar, Ashraim ya bud’e motar tareda fitowa ya zuba mata idanu, yana kallon idanunta wadanda sune kawai yake iya gani, Rumaaa tayi sama da niqab dake fuskarta tana kallonshi cike da damuwa, Ashraim ya ware idanu yana kallonta, Rumaaa tace,

“Adeel meyyy haka? Na fad’a maka kadda ka k’ara zuwa… Na rokeka da Aallah ka rabu dani kaje ka nemi sa’arka ni talaka zan aura… Adeel… Meyyy haka ina maka magana ka zuba min idanu kawai…”.

Ashraim yayi murmushi sannan a hankali cikin husky voice dinsa yace,

“Jasmine… Your are amazing and unique…”.

Rumaaa ta zaro idanu tana kallonsa sannan ta juya da sauri ta shige gidansu, Ashraim ya bita da kallo yana dariya, tabbas itace irin matar da ya dauki tsawon lokaci yana nema, ya zaro kudi ya aika wani yaro wurinta sannan ya juya ya shige motarsa ya wuce….

Rumaaa ta fad’a akan bed tareda dafe zuciyarta, she don’t know meyyy yake faruwa da ita, salaam taji ta fito wani yaro ne d’an neighbor dinsu ya mik’a mata envelope tana bud’ewa taga wrapper din en dubu-dubu, yace,

“Wani mai mota yace in baki…”.

Rumaaa tace, “Ka maida mashi…”.

Yace, “Ya tafi…”.

Dole ta amshi kudin tareda dauko mashi chocolate, ta wuce bedroom ta fad’a akan bed tayi lamo tana wani tunani sai kuma ta jawo wayarta ta dannawa wata number call tayi jim sannan tace,

“Salaam alaika… Na’am… Yaa Adeel… Kazo gidanmu yanzu…”.

Daga daya bangaren Adeel ya ware idanu sannan yace,

“In zo gidanku kuma, tou meyyy zanyi maki bayan the other day korata kikayi, fatan magabatana sun zo gidanku…”.

Daga daya bangaren Rumaaa tace,

“Kazo ka amshi kudin da brother dinka ya aiko min dasu ka mayar mashi da kayansa…”.

Adeel yace, “Kadda ki damu ai ya fad’a min yadda kukayi, you thought nine, ban ga laifinki ba muna matuk’ar kama ce amma he is older than me, amma kadda ki damu zan turo maki numbarshi sai ki kirashi yazo ya amshi abunsa…”.

Sai kuma yayi hanging call din tareda turo mata numbar Ashraim….

 

 

 

Littafin Ni da yaya Rafeeq na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take so zata samu akan Naira dari hudu 400, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057, amma na rokeki da girman Allah idan ba siya zakiyi ba kadda kiyi min magana, Na rokeki da girman Allah idan ba novel dina zaki siya ba kadda kiyi min magana

 

*One love,*

About the author

Hausa_Novels

2 Comments

Leave a Comment