Littafan Hausa Novels

Ni da Yaya Hassan Book 2 Hausa Novel

Written by Hausa_Novels

Ni da Yaya Hassan Book 2 Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

Ni da Yaya Hassan Book 2 Hausa Novel

*CHASING MY HEART*

*NI DA YAYA HASSAN BOOK 2*

 

By sl rimi family’s

 

Page. 1

Free page

 

Littafin Ni da yaya Hassan na kudi ne, akwai shi complete, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057, na rokeki da girman Allah idan kin san baki shirya siya ba kadda kiyi min magana, na rokeki da girman Allah idan kin san ba littafina kike so kadda kiyi min magana

 

Budurcina Yancina by Benaxir Omar Hausa Novel

Ikhlas tace, “Su waye muka wuce a parlour?”.

Hafsat tace, “Yaa Hassan ne da Yaa Hussein… Duk wanda ya sanni yasan shakuwata da yaya Hassan kasancewar a kasar nan yayi karatunsa, shi kuma yaya Hussein yayi karatunsa ne a London, a lokacin ina yarinta har fad’a muke da yaya Hussein akan kowanenmu yana son kasancewa da yaya Hassan, musha dirama har yanzu idan na tuna dariya nike… Duk wanda ya sanni zaiji sunan yaya Hassan a bakina… Abba shine mahaifina su kuma daddy, saboda muzgunawar da matar uba takeyi min a wancen lokacin ya saka na dawo nan… Momcy itace mahaifiyarsu… Ummyna ta rasu tun bani da wayo….”.

************

Washegari,

Hassan da Hussein ne zaune a parlour suna hira cike da nishad’i, wayar Hassan ce tayi ringing ya janyota ya duba, da sauri yayi picking yayi jim sannan yace,

“Sure Abba… Gamu nan zuwa…”.

Sai kuma ya mike yace,

“Hussein tashi muje Abba ne yake kiranmu…”.

Hussein ya mike suka fice suna tafiya a jere suna hira….

Abba ne zaune a parlour, Hassan da Hussein suka shigo da salaam akan bakinsu, suka zame kasan carpet suka gaidashi ya amsa fuska a sake yana jansu da hira, yayi murmushi sannan yace,

“Na kiraku ne saboda ina so muyi wata magana mai muhimmanci…”.

A tare sukayi nodding head suna murmushi….

Abba yace, “My boys kun girma, kun gama karatu, ya kamata ace kun ajiye iyali, ina sone a gudanar da walimar kammala karatunku tareda bikin bude asibitinku bayan aurenku don haka kuje kuyi shawara, bazan maku dole ba, wanda yaga yana da buk’atar auren haka nike so, wanda yaga bai shirya auren ba sai nan gaba shima bazan mashi dole ba, kuje kuyi shawara komai kenan sai ku fadaman, ku tashi kuje Aallah yayi maku albarka…”.

A tare suka ce,

“Aameen”.

Suka mashi salaam suka wuce yana zolayarsu suna murmushi, Hassan yaja hannun Hussein suka wuce bedroom dinsu, Hussein ya fada akan dago….

Hassan yace, “Hussein meyyy kake tunani akan maganar Abba?”.

Hussein yace, “Yeah… Ina bukatar inyi aure…”.

Hassan yace, “Ni kuma sai nan gaba…”.

Hussein ya dubeshi da sauri yace,

“Mey?”.

Hassan yace, “Yeah… Ba yanzu zanyi aure ba…”.

Hussein ya cune fuska sai kuma yace,

“Shikenan nima na sauya ra’ayi, duk lokacin daka tashi auren sai muyi a tare…”.

Hassan yace, “Barkwanci kenan…”.

Hussein yace, “A ganinka kenan amma ni abun da na fadi shi nike nufi”.

Hassan yace, “No..”.

Hussein yace, “Yes..”.

Hassan yayi taking steps zuwa inda Hussein yake ya kama mashi hannu, Hussein ya fizge hannunsa, dakyar Hassan ya shawo kan Hussein ya yarda ya janye furucinsa…

Hassan yace, “Who is that lucky woman?”.

Hussein ya dubeshi yace,

“Yeah… Ina bukatar inyi aure saidai bani da wadda nike so, ban tab’a soyayya ba, ban tab’a kallon wata mace da sunan so ba, duk da kuwa yawan en matan dake crushing a kaina… Hassan ina son auren mace mai kamun kai, tarbiyya, rikon addini, mai ilimin addinin da na boko, mai kunya, wadda zata soni a yadda nike, kafi kowa sanina ka san ra’ayina… Ina zan samu mace mai wannan dabi’u?”.

Hassan yayi murmushi sannan yace,

“Indai wannan ce na samar maka”.

“Wacece?”.

“Hafsat Angel…”.

Hussein ya ware idanu yace,

“What… Meyyy… Hafsat… You must be joking… Hafsat fa kace?”.

Hassan yace, “Yeah… Ko baka yarda da tarbiyyarta bane ko kuma kana ganin bata da qualities da kake so?”.

Hussein yace, “No amma….”.

Hassan ya daura hannu akan lips dinsa yace,

“Ban san wata magana, ka amince ko kuwa baka amince ba…”.

Hussein yace, “Hassan….”.

Hassan yace, “Amsa nike so ka bani…”.

Hussein yace, “Ni bance ban sonta ba amma ai…”.

Hassan yayi wani tsalle tareda hugging dinsa yace,

“Yeah that is my twin brother… Kayi sa’ar mace, ina fada maka duk wanda ya auri Hafsat yayi babbar sa’a… Bari inje in fada mata, nine zan zab’a mata miji kuma na zab’a mata tuntuni, kaga na tafi…”.

Sai kuma ya duro daga saman gadon yayi taking steps ya fice yana murmushi, Hussein ya bishi da kallo cike da mamaki idanu waje baki bude….

Hassan tafiya yake a hankali ya ware hannuwa yana murmushi jinsa yake cike da nishadi, yana enjoying yanayin, burinshi ya kusa cika…

Yasmeen ce ta rugo da gudu, dukawa yayi ya tareta yayi sama da ita yana jujjuyawa da ita suna dariya, direta yayi kasa yace,

“Kice Hafsat ta sameni a garden…”.

Sai kuma yaja hancinta yaja ya mike ya nausa cikin garden wurin wasu flowers masu daukar hankali yana jiranta da murmushi akan fuskarsa yana kallon flowers din…

Hafsat ce kwance akan gado tayi hugging pillow idanunta a lumshe tana murmushi, mikewa tayi wani tsallen murna, tace,

“Today am happy, yanzu am free babu karatu babu damuwa babu kuka, no more tension…”.

Ta kunna kida tana zagaye bedroom din tana cashewa tana rawa da duk abun da ta dauka, cike take da farin ciki, tana jin kanta cikin wani yanayi mai dadi, jinta take cike da nishadi…

Yasmeen ce ta shiga bedroom din, Hafsat bata lura da shigowarta saboda sautin kidan da ya karade dakin, cashewarta take abunta, yasmeen ta tab’ata…

Hafsat ta juya da sauri tareda ware idanu, ta sauke ajiyar zuciya, kidan ta kashe tace,

“Yasmeen meyyy?”.

“Yaa Hassan yana kiranki yace ki sameshi a garden….”.

Hafsat ta ware idanu cike da mamaki tace,

“Yaa Hassan… Kuma ni yace ki kira…”.

“Eh…”.

Saida tayi jim sannan tace,

“Okay then… Kinga leatherr chacolate can na siyo maki ki dauka… Ga kuma kaya can na ashraif ne…”.

Yasmeen tace, “Yes, thank you…”.

Hafsat ta kalli kanta, gown ce english design a jikinta don haka ta lullube kanta da veil tareda zura takalma flat ta fice tana taking steps fuskarta dauke da mamakin wannan kiran da Hassan yake mata don rabon da ya kirata kamar haka har ta manta, tayi jim tana kallonshi ya bata baya ne dan haka bayanshi kawai take iya gani, gani tayi ya juyo yana jefarta da murmushi, ya fitota da hannu yana nuna mata kusa dashi, jim tayi ta kalli gefe sannan ta karasa ta zauna opposite dashi, Hassan ya kalleta ya kalli kusa dashi yana murmushi…

A hankali tace,

“Gani… meyyy?”.

Hassan yace, “Nayi laifi ne don na kiraki…”.

Kallonshi tayi kawai, ya mike ya koma kusa da ita ya zauna, a hankali yake mata magana kamar wanda yake shirin ce mata _I love you_ _yana sonta_ yana magana yana lumshe idanu ba ya gajeriyar jimla saidai doguwa yana motsi da cute lips dinsa a hankali….

Hafsat ta zuba mashi idanu cike da mamaki don tasan baya doguwar magana, ji tayi yace,

“Hafsat nayi maki miji…”.

Hafsat ta ware idanu tana kallonshi, tayi murmushi tareda hugging dinsa, peck tayi mashi a kumatu, ta mike ta ware hannu tayi wani juyi mai matukar k’ayatarwa, ta koma ta zauna while saying,

“OMG… Waye?”.

Hassan ya dungure mata kai yace,

“To sakeni sai in fada maki…”.

Hafsat ta turo baki ya buge mata bakin tayi er k’ara, tace,

“Aauch… Wannan cin zalin ne… Ka fada min ni bazan yarda kayi min ruining mode ba… Kawai ka fadi abun dake tafe da kai… Fad’a min mana… Who is he?”.

Hassan yace, “Hussein ne… D’an biyuna…”.

Hafsat ta dubeshi da sauri, yace,

“Baki sonshi ne…”.

Hafsat tayi jim sai kuma tace,

“Ina sonshi mana, kai yanzu idan nace bana sonshi sai ka yarda…”.

Hassan yace, “Yeah…”.

Hafsat ta cure fuska, ya kwashe da dariya, ta buge mashi k’eya, yayi er kara, yace,

“Aauch… Cin zalin…”.

“Shikenan an tashi daya da daya, kaci min zalin nima naci maka…”.

A tare sukayi dariya, Hassan yace,

“Hafsat…”.

Ta kalleshi kawai, yace,

“Hussein ya zama boyfriend dinki… Suitor dinki… Yanzu Hussein ne komai naki… Bani ba… Bana so ki k’ara nuna nine komai naki… Daga yau Hussein ne komai naki… Daga yau NO MORE NI DA YAYA HASSAN kinji…”.

Da sauri ta dubeshi feeling so how sai kuma tayi nodding head tana murmushi wanda iyakarsa a fuska ne kawai, tace,

“Okay then…”.

Hassan yace, “Good girl, my cousin sis sannan kuma my in-law….”.

Sannan ya ciro flower ya mik’a mata da murmushi akan fuskarsa, yace,

“Ki kula min da d’an biyuna… Kadda ki karya mashi zuciya… Kadda ki karya zuciyar da nafi tattali… Ina matukar sonshi… He mean a world to me shiyasa na zab’a mashi ke a matsayin abokiyar rayuwa… Please kadda kiyi disappointing dina… Ki nuna mashi kauna a duk yadda yake sannan wani abu kadda ki tsaya jan aji wa handsome saurayi kamar dan biyuna gudun kadda ya subuce maki…”.

Kallonshi tayi, ya kwashe da dariya tareda kwace furen dake hannunta ya mike ya ware hannuwansa yana tako a hankali, ya nausa cikin garden fuskarsa dauke da tsantsar farin ciki….

Hafsat tayi jim ta mike tana tafiya kamar butum-butumi babu abun dake mata yawo a kai sai maganar Hassan a inda yake cewa _NO MORE NI DA YAYA HASSAN_ babu kowa a parlour ta wuce staircase, a hankali take taka stairs boob dinta suna sama suna kasa don Aallah ya azurtata da manyan boob, taimakon Aallah ne yasa ta haye upstairs lafiya don kwata-kwata hankalinta yana wani wurin, a hankali ta murda handle din kofa ta shiga ta rufo ta jingina da kofa kawai, jim tayi ta karasa wajan mirror ta tsaya duk abun da take abu daya ne ke mata yawo a brain sai _NO MORE NI DA YAYA HASSAN_ ta dauki wayarta tayi jim sannan ta soma sarrafata ta goge duk wani abu wanda keda _NI DA YAYA HASSAN_ tayi dropping wayar ta soma bincike duk wani picture da wani design da wata paper da wani drawing da wani pattern dake dauke da _NI DA YAYA HASSAN_ ta tattara su tayi destroying dinsu tana acting kamar butum-butumi, ta zauna gefen gado ta janyo laptop dinta ta goge duk wani abu dake dauke da _NI DA YAYA HASSAN_ ta janyo wani babban kit din jewellery ta bude gold dinta masu design din _NI DA YAYA HASSAN_ ne suka bayyana ta jima tana kallonsu sannan ta rufe kit din ta mike ta fita, a matakalar bene ta hadu da Hassan, kallonta yayi ta kalleshi, tace,

“Here you go… Ban san yadda zanyi dasu ba…”.

Hassan yayi murmushi yayinda ya amshi kit din, yace,

“Yauwa good girl… Angel ta girma… My in-law…”.

Hafsat tayi jim sannan ta juya tayi gaba, tayi crossing da Hussein, yayi mata murmushi, tayi kasa da kai ta wuce, ya bita da kallo, Hassan ne ya dafashi yace,

“What up?”.

Hussein yayi murmushi sannan yace,

“She look lovely har na fara missing dinta….”.

Hassan ya d’age brow, yace,

“Ko in kira maka ita…”.

Hussein yace, “No, kana sone Momcy ta karya min kafafuwa…”.

Suka kalli juna sukayi dariya, suka wuce bedroom….

A hankali Hafsat ta murda handle din kofa ta shiga ta durkushe tareda sakin kuka wanda ita kanta bata san dalilinshi ba, koda za’a tambayeta bata da amsa, ta cigaba da kukanta saida ta gaji don kanta sannan ta mike ta fada bathroom ta wanke fuskarta ta jima tana murje jikinta sannan ta sakarwa kanta shower ta daura towel ta fito, tsaye tayi gaban mirror tana karewa figure 8 dinta kallo, tana bin duk wani sako da lungu na jikinta da kallo, MashaAallah, Aallah ya hore mata diri, idan tana tafiya baki daya jikinta rawa yake, manyan boob dinta suna sama suna kasa, bayan ta tsane jikinta ta janyo hand dryer tayi drying gashinta wanda ya sauko har ya wuce gwuwarta, ta shafa cream ta janyo wayarta tayi dialing wata number, tayi jim sannan tace,

“Salaam Alaiki… Haloo… Beebah… Ya kike ya aiki.. Daina ki tambayeni sweety dai… Hhhhh… Kinga parrot sun hadu surutu ya tafo bari in fada maki tun kafin in manta… Kinga hijab nike so kiyi min guda sha biyu… A’a wadanda zasu tsaya min daidai gwuwa… Ehhh amma shidda masu hannu, shidda marassa hannu… Yauwa kuma kaloli daban-daban nike so kuma kinsan kalolina… Hakane amma plan yard nike so marar pattern wanda ba ya da daukar hankali, kinsan dai yard din da ya dace da hijab… Normal, yadda nike so kadda ya kasance mai rubber, kin gane dai… Amma zuwa gobe da safe nike sonsu… In shaa Aallah… Nawa ne kudin… Ahhh kai Beeba… Hhhhhh… Ahhhh… Ohhh… Babu damuwa yanzu In shaa Aallah zakiga alert… Beeba damuwa, keda zaki min maganar sweety kina min maganar wani can… Hhhhh… Haka dai kika ce… Kinga zan gudu sai naga sakona… Bye… Kinyi min yadda nike so fa… Ahhhh… Hhhhhh… Nikam zan gudu…”.

Sai kuma tayi hanging call din ta ajiye wayar, tayi jim ta ware idanu tareda dafe kai ita bata iya transfer ba, koda tayi ciniki Hassan ne yake biyan kudin, idan tayi shopping shine yake biya, idan taga abu tana so shi take yi ma magana ya siya mata, komai nata shine, saida tayi jim sannan ta janyo wayarta tayi typing message tayi sending ma Hussein, mikewa tayi ta shirya saidai kuka ne ya kufce mata wanda ta rasa dalilinshi ta jima sannan ta mike ta fada bathroom ta wanke fuskarta tana fitowa ta jawo wayarta, hoton Hassan ne a gaban wayar, tayi jim sannan ta sauyashi da wani selfie da tayi ita da Hussein, ta janyo system dinta ta sauya hoton dake gabanta….

Hassan da Hussein ne zaune suna catching fun wayar Hussein tayi k’ara, janyota yayi, saida yayi murmushi sannan yayi transfer din kudin….

Hassan ya mike ya wuce bathroom sai bayan 30 minute sannan ya sakarwa kanshi shower ya d’aura towel, yayi tsaye gaban mirror hakanan yaji hawaye suna bin fuskarsa, ya ware idanu domin shi kanshi bai san dalilin yinsu ba…

Later at night,

Hafsat ce zaune a bedroom wayarta ce tayi k’ara ta janyota tayi picking ta kanga a kunne, tayi jim sannan ta ajiye wayar ta mike ta bude sirf ta zaro wata hijab karama wadda ta tsaya mata daidai gwuwa saida yard din rubber ne, ta zura hijab din ta fito boob dinta sunyi appearing daga cikin hijab tana tafiya suna sama suna kasa, hannu ta saka ta kare kirjinta…

Daddy, Momcy, Hassan, Hussein, kowa ya hallara a dinning table, taja kujera ta zauna ta gaida Daddy da Momcy sannan ta gaida Hassan da Hussein…

Fareeda ce tayi serving dinsu, Hafsat ta dauki spoon tana cakurar abincin, bayan sun gama ita da Fareeda suka kwashe abubuwan da aka b’ata suka wuce dasu kitchen suna wankewa….

Fareeda tace, “Hafsat what the sudden change?”.

Hafsat tace, “Ehhh… Besty mey?”.

Fareeda tace, “Naga kin sauya ne cikin kankanin lokaci shiyasa nike tambaya… Ko kina tunanin gaidaki zanyi ne… Angel…”.

A tare sukayi dariya….

Hafsat tace, “Haka…”.

Daga nan bata sake magana ba….

Hussein ne ya shigo kitchen din, kallon Fareeda yayi da sauri ta dauraye hannunta ta fice, yaja stool ya zauna tareda zubawa Hafsat idanu ba ya koda blinking, ya lumshe idanu ya bude sannan a hankali yace,

“Kawo min apple….”.

Hafsat ta dauraye hannunta ta k’arasa wajen fridge ta dauko apple ta saka a bowl ta kai mashi don neman magana saida ya hada da hannunta ya rike, kallonshi tayi ya kalleta, yayi murmushi sannan a hankali yace,

“Princess kinyi kyau… You look lovely….”.

Hafsat ta fizge hannunta ta wuce ta cigaba da wanke kayan, yana cin apple yana kallonta sai kuma ya mike ya fice, tana gamawa ta dauraye hannunta ta fice….

Washegari,

Daddy da Abba ne zaune a babban parlour na sashen daddy suna hira cike da nishadi….

Hassan da Hussein ne suka shigo fuskokinsu dauke da fara’a, suka zame kasan carpet suka gaidasu….

Abba da Daddy suka amsa fuska a sake, Abba yana jansu da hira, sukayi kasa da kai suna murmushi….

Abba ya dubesu yace,

“Yarana da alama akwai magana a bakinku… Miye?”.

Hassan yayi murmushi kanshi a kasa yace,

“Akan maganar da kayi mamu ne na aure… Ni sai nan gaba… Shi kuma Hussein, Hafsat yake so…”.

Momcy da shigowarta kenan taji wannan maganar, da sauri ta dubi Hassan saura kadan tray din dake hannunta ya sub’uce yayinda a lokaci guda gabanta ya yanke ya fadi….

Abba da Daddy suka dubi juna suka fadada fuskokinsu da murmushi….

Abba yace, “Abu yayi kyau…”.

Daddy ya dubi Momcy yace,

“Ki shigo ciki akan diyarki ne…”.

Momcy ta shigo tareda ajiye tray din ta zauna akan kujera….

Abba yace, “Wannan abu yayi kyau… Shikenan… Kai Hassan bazan matsa maka ba… Akwai gidajen da na gina maku nan gabanmu, jere suke, komai nasu iri daya ne tunda nasan yaran nawa… Kai Hussein zan damka maka makullin gidanka kai kuma Hassan sai idan ka tashi auren sannan zan baka…”.

Momcy ta dubi Hassan gani tayi yana murmushi…

A tare Hassan da Hussein suka ce…

“Mun gode… Aallah ya kara budi na alkhairi…”.

“Aameen… Aallah yayi maku albarka…”.

“Aameen…”.

Daddy yace, “Ba wannan ba… Ni ba zanyi wa diyata auren dole ba, duka’duka shekarunta ba zasu wuce sha hudu ba, sai na kirata naji ra’ayinta, idan tace a’a saidai d’anka ya nemi wata…”.

Hafsat tana kwance a bedroom dinta tana kuka, wayarta ce tayi k’ara ta janyota, tayi picking jim tayi sannan tace,

“Gani nan…”.

Sai kuma tayi dropping wayar ta mik’e ta fada bathroom ta wanke fuskarta tana tunanin abun dake faruwa da ita hakanan idan ta zauna bata da aikin da ya wuce kuka wanda ta rasa dalilinsa, mikewa tayi ta k’arasa wajen sirf ta zaro hijab wadda ta wuce gwuwarta ta zura ta fito, jim tayi sannan ta shiga parlour din da salaam a bakinta, kallo daya tayi ma Hassan da Hussein ta samu kasan carpet ta zauna opposite dasu, ta gaida Daddy, Abba da Momcy sannan ta gaida Hassan da Hussein….

Ji tayi daddy ya kira sunanta, yace,

“Hafsat…..”.

A hankali ta dago tace,

“Na’am…”.

Daddy yace, “Zamuyi magana ne… Hussein yace yana sonki… Meyy kike gani? Shin kin shirya aure a wadannan shekaru?”.

Hafsat kanta yana kasa, a hankali ta dago tana kallon Hassan, Hassan yayi murmushi tareda gyad’a mata kai, ta gyad’a kai….

Daddy yace, “Maganar karatunki fa? Idan kika gama secondery kina da sha’awar cigaba da karatu ne ko kuwa?”.

A hankali Hafsat ta dago ta dubi Hassan…

Daddy yace, “Ra’ayinki nike bukata, ba na kowa ba…”.

Hafsat tayi kasa da kai sai kuma ta dago ta dubi Hassan, murmushi yayi ya gyad’a mata kai, ta dukar da kai sannan ta dago ta gyada kai….

Daddy ya dubi Abba sannan yace,

“Ina sharudda guda biyu kafin in bawa d’anka auren d’iyata, na daya zai barta ta cigaba da karatu har ta gama secondry wannan ra’ayina ne, na biyu zai barta ta dora daga secondary wannan ra’ayinta ne… Idan ya yarda da wadannan sharuddan shikenan idan kuma bai yarda ba, shikenan sai ka nemar mashi wata…”.

Abba ya dubi Hussein, Hussein ya gyad’a kai, Abba yace,

“Mun yarda, mu da za’a bawa diya sunkutukum da guda ai dole mubi…”.

Dariya sukayi…

Daddy yace, “Hafsat tashi ki tafi… Aallah yayi maki albarka..”.

Hafsat tayi motsi da bakinta sannan ta mike ta fice tana fadawa bedroom ta durkushe gefen gado ta saki kuka saida tayi mai isarta sannan ta mike ta fada bathroom ta wanke fuskarta ta fito ta zauna gefen gado….

_saida yayi wa d’an biyunsa tallar aurenta sannan ya fahimci yadda yake matukar sonta_

 

Littafin Ni da yaya Hassan na kudi ne, akwai shi complete, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057, na rokeki da girman Allah idan kin san baki shirya siya ba kadda kiyi min magana, na rokeki da girman Allah idan kin san ba littafina kike so kadda kiyi min magana

 

 

Follow me on this interested love saga

Hassan, Hussein and Hafsat love saga

One love 😍

[30/01, 6:43 pm] +234 916 947 2057: ⚓⚓⚓

*CHASING MY HEART*

*NI DA YAYA HASSAN BOOK 2*

⚓⚓⚓

 

By sl rimi family’s

 

 

 

 

Page. 2

Free page

 

Littafin Ni da yaya Hassan na kudi ne, akwai shi complete, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057, na rokeki da girman Allah idan kin san baki shirya siya ba kadda kiyi min magana, na rokeki da girman Allah idan kin san ba littafina kike so kadda kiyi min magana

 

 

Abba da Daddy sun gama magana sun yanke shawarar nan da wata biyu za’ayi auren, kafin su Hafsat su fara zuwa ss kenan, daga baya sai a bude asibitin da Daddy ya ginawa Hassan da Hussein….

Da marece, Fareeda ta samu labari ta shigo bedroom din Hafsat tana mata tsiya…

“Kishiyoyi sun zama love birds… Duk fadan da kuka dake da yaya Hussein ashe duk cikin love ne, wannan irin love haka, kishiyoyi sun zama masoya…”.

“Wasu dai gulma cinsu take kamar ciwo…”.

“Wasu kuma boye-boye da nuku-nuku kamar garar kunya… Hhhhh… Ohh yarinyar nan ashe aure kike so, aiko kin tara kin samu domin shi zamuyi maki mu hutu… Ohhh yaran zamani…”.

Ta ida maganar kamar wata babbar mace….

Dariya sukayi Hafsat ta kai mata punch, tace,

“Tashi ki tafi tun kafin in kirashi yayi min maganinki, kin zo kin tusa mashi princess a gaba zaki saka mata ciwon kai, kinga tashi kadda in kira sweety yayi min maganin surutunki…”.

“Ke kuma parrot,” Fareeda tace tareda mikewa tana dariya ta nufi kofa….

“Bari inje in fesawa besties”.

“Banda dai kara salt da magi wa story…”.

Fareeda tayi dariya kawai tana mai ficewa daga bedroom din….

Hafsat ta dafe kai tareda fashewa da kuka, girgiza kai take tana goge hawaye wasu sabbin hawaye suna zubowa, hawayenta sun kasa tsayawa, kuka take wanda bashi da dalili koda yana da dalili ita bata da knowledge akan dalilin, mikewa tayi ta fada bathroom ta jima sannan ta fito tana daure da towel ta tsane jikinta tareda applying cream, powder da lipstick kawai ne a fuskarta amma sunyi suiting dinta looking lovely, ta zura gown ta kwanta akan bed tareda lumshe idanu har bacci ya fara daukarta ta bude idanu ta kalli watch _5:08PM_ ta gani zumbur ta mike tana zaune har aka kira sallar Magrib ta mike ta dauro alwalla ta tada sallah tana zaune akan praying mat har aka kira sallar Isha’i ta mike ta tada sallah, ta dade a zaune sannan ta mike ta cire long hijab ta saka wata hijab wadda ta wuce mata gwuwa jim tayi sannan ta fito tana tafiya ta hango Hassan da Hussein, Hussein yana jefarta da murmushi, tayi rolling idanu ta kalli gefe…

“Princess…”.

Hafsat ta tsaya cak, Hassan yayi gaba yayinda Hussein ya nufi inda take while saying,

“Princess babu magana ne…”.

“Ina wuni?”.

“Kema ina wuni?” ya kwaikwayeta…

Kallonshi tayi ya turo baki yana aika mata da wani kyakykyawan murmushi, kallon gefe tayi, yaja oxygen yace,

“Princess kinyi kyau… You look lovely… Damn cute… Gorgeous… Breathtaking… Stunning… Mesmerizing… Alluring… Charming… Your smile… Your laugh… Komai naki na daban ne… I love you… I really love you my princess… My heart desire… My wife to be…”.

Hafsat ta kalleshi ta ware idanu, yayi winking idanu yana pouting lips kamar yana nuna mata abu, jan kafa tayi yasha gabanta, kallonshi tayi ya sakar mata murmushi, yace,

“Haba Princess… Uhm yaushe kika tab’a ganin anyi haka… Princess a gaba ni a baya… No… Haramun…”.

Sai kuma yayi murmushi yana girgiza kai, tsaf ta gane inda ya dosa, yayi gaba saida ta bari ya sauka kasa sannan ta soma sauka daga stairs, direct ta wuce dinning table kowa ya hallara, ta zauna kusa da Hussein, kamar koda yaushe saida ta gaida Daddy da Momcy sannan ta gaida Hassan da Hussein….

Fareeda tace, “Bestiee yane kina jin sanyi ne?”.

Hafsat tayi banza da ita….

Hussein ya dago yana hararar Fareeda…

Fareeda ta rufe lips da hannu tana dariya kasa-kasa mikewa tayi tai serving kowa ta zauna, kowa ya natsu yana cin abinci, Hussein ne yayi ma Hafsat magana ta yadda babu wanda zaiji abun da yace sai ita (ko ni ban ji abun da yace ba, duk kuwa yanda na baza kunne don in dauko rahoto da kyau, hhhh lols) gani nayi ta kalleshi ta wani zaro idanu, yayi mata winking idanu yana dariya kasa-kasa, jim tayi ta cigaba da tsakurar abincin, koda suka gama Hafsat da Fareeda ne suka tattara abubuwan suka kai kitchen suka wankesu, suka fito parlour suna kallon series, mikewa Hafsat tayi ta haye upstairs tana zama side din bed wayarta tayi k’ara dubawa tayi tai picking…

Daga daya bangaren Hussein ya ja oxygen yace,

“Princess…”.

Hafsat tayi shiru, Hussein yayi murmushi har tana jin sautinsa, a hankali yace,

“Ina jiranki a parlourn baki…”.

Sai kuma yayi hanging call din, ta jima tana juya maganarsa meyyy kenan, mikewa tayi ta wuce bathroom ta b’ata lokaci tana wanka sannan ta fito ta zura gown ta janyo hijab wadda ta wuce mata gwuwa ta zura saida ta duba fuskarta a dogon mirror sannan ta fita, a parlour ta tadda Momcy da Fareeda….

Momcy tace, “Hafsat sai ina?”.

Saida Hafsat tayi jim sannan tace,

“Yaa Hussein ne ya kirani akan yana jirana parlour din baki…”.

Momcy ta dubeta da mamaki baki bude yayinda Fareeda take dariya kasa-kasa, Momcy tace,

“Zance zakije a haka… Dubeki… Haba… So kike ace ban koya maki komai ba… Kije bedroom dina ki bude closet dina akwai gown daidai ke ki saka… Ki kawo min makeup kit da perfume mai saukin kamshi… Akwai heel shoes ki sakasu… Kinga wuce bana san wata magana…”.

Hafsat ta juya ta haye upstairs, a hankali ta murd’a handle din door ta shiga saida ta tsaya na wasu seconds sannan ta wuce wurin closet ta bude ta zaro gown din…

“OMG… Wow… What a breathtaking gown!” tayi exclaimed suddenly very happy and loudly, gown ce mai kyau hawa biyu ce, ta kasa normal take black mara design mai circle neck, ta saman red ce tana da design, bude gabanta yake kamar afterdress, tana da madauri a gaba, ta rufe closet din ta rage kayan dake jikinta ta zura gown din, ta daure maudarin a gaba sannan ta feshe jikinta da perfume mai saukin kamshi, ta janyo veil tareda zura wasu heel shoes masu heel mai tudu ta dauki makeup kit ta fito ta sauko downstairs ta zauna kusa da Momcy tareda mika mata makeup kit….

Momcy tace, “Kai sweetheart kinyi kyau… MashaAallah… Wow… Tunda kika fito na kasa rufe bakina ga er uwarki nan ta gaza rufe min…”.

Dariya suka saka….

Saida Momcy ta shafe mintina ashirin tana k’awata fuskar Hafsat da heavy makeup wadda tayi matukar mata kyau abun saidai ace MashaAallah…

Momcy tace, “Smile”.

Hafsat tayi murmushi, Momcy tace,

“Kiyi rolling idanu…”.

Hafsat tayi rolling idanu, Momcy tace,

“Kiyi pouting lips…”.

Hafsat tayi pouting lips, Momcy tace,

“Kiyi sama da iris dinki…”.

Hafsat tayi sama da iris dinta, Momcy tace,

“Kinga yanzu shagwab’e fuska”.

Hafsat ta shagwab’e fuska, Momcy tace,

“Kuma yanzu kiyi fuska kalar tausayi…”.

Hafsat tayi pity face….

“What about kukan shagwab’a?”.

Dariya sukayi Hafsat tayi yadda aka ce….

Momcy tace, “Angel… Kinyi kyau irin sosai da sosai… Ki mike and turn a round…”.

Hafsat ta mike tayi wani juyi….

“Ma shaa Aallah,” Momcy tayi exclaimed suddenly happy sannan ta dora saying,

“Zo inyi shooting mamu selfie…”.

Momcy ta kashe masu selfie suna murmushi…

“Hafsat tashi ki tafi kadda ki d’ad’e… Fareeda dauki wannan makeup kit din ki wuce sama… Hafsat tsaya kiyi tafiya in gani… Yauwa tafiyarki na kyau kamar wata model… Amshi tray ki tafi dashi… Yauwa… Tafi abunki”.

Hafsat ta wuce tana tafiya a hankali tareda saka kowace kafa a side din data cire dayan, tana shiga parlourn wani kamshi mai sanyi ya daki hancinta, ta lumshe idanu ta bude tana dagowa tayi idanu hudu da Hussein wata kunya ce ta kamata ta daburce ta tsaya cak ba tareda ta cigaba da tafiya ba….

Hussein ya sakar mata murmushi har cute dimple dake a right cheek dinsa yayi appearing tareda cute white teeth dinsa, yace,

“Welcome princess… Kin shanyani ashe makeup kika tsaya kika yi min… Kinyi kyau… You look lovely… Karaso mana ko inzo da kaina in tafo dake ne…”.

Saida tayi jim sannan ta k’arasa gabanshi tayi placing tray dake hannunta wanda yake dauke da home made drink tareda da glass cup, kallonta kawai yake, shiga tayi decently tayi matukar kyau, tana dagowa sukayi idanu hudu, ya sakar mata murmushi tareda d’age gira, mikewa tayi ta koma kujerar dake nesa dashi ta zauna tayi kasa da kai tana fidgeting zoben diamond dake hannunta, a hankali ta dago ta dubeshi sanye yake cikin kananan kaya jeans da shirt yayi kyau, looking handsome and hot, ya tsiyaya drink yana sipping a hankali, sumar kanshi tasha gyara _MashaAallah_ wata diamond wrist watch ce ta gani a hannunsa, yana dagowa suka hada idanu, yayi murmushi yana mata waving hannu, da sauri ta dukar da kai yayinda ya duke yana danna waya, Hassan ne ya shigo ya zauna gefenta, Hussein ya mike ya zauna a daya bangaren suka sakata tsakiya….

A hankali Hussein yake mata magana kasa-kasa ta yadda ita daya take jin abun da yake fadi, bata da amsa sai uhm ko tayi smile, rolling idanu, zaro idanu…

Hassan yana kishingid’e ya daura kafa daya akan daya busy with his phone, kamar hankalinshi ba ya wajansu amma ba haka bane, yana jin feeling biyu ne, daya farin ciki dayan kuma hawaye amma ya rasa dalili….

Hussein ya karkato da kai yana mata magana, tayi kasa da kai tana murmushi, yayi dariya yana motsi da cute lips dinsa har da wani turosu kamar wanda yake shirin daukar hoton selfie, so hot, cheek dinsa ya nuna mata yana murmushi, ta rufe baki tana dariya, yayi rolling idanu yana shagwab’e fuska, cikin hikima yasa ta saki jiki dashi suka sha love abunsu, saida momcy ta kira wayarta sannan ta mike, tace,

“Momcy tayi kira… Good night and sweet dreams…”.

Hussein ya lumshe idanu tareda jan oxygen yana mata waving hannu, yana kallonta har ta fice, ya juya ya fizge wayar dake hannun Hassan, Hassan ya dago a hankali yace,

“Daga yau bazan k’ara maka rakiya, wannan ai rashin kishi ne, ka zama mai kishi…”.

Kallon juna sukayi suka kwashe da dariya, suka mike suka wuce ciki suka wuce bedroom suka zauna suna duba laptop suna catching fun, Hassan ya mike yana dariya ya fad’a bathroom ya sakarwa kansa shower, ya jima sannan ya murje jikinsa da sabulai masu kamshi, ya dauki mintina ashirin sannan ya dauraye jikinsa ya daura towel ya k’arasa gaban mirror yana brush, hawaye ne suka soma zubo mashi ya rasa dalilin wannan hawaye da kuka ya jima sannan ya wanke fuskarsa ya fito….

Hussein ya mike ya fada bathroom, yana taking shower yana murmushi….

***********

Hafsat ce tsaye a bedroom, ta rage kayan dake jikinta ta fada bathroom ta dauki lokaci tana murje jikinta sannan ta sakarwa kanta ruwa ta daure towel, tayi brush ta fito ta duke gefen bed ta fashe da kuka ta dauki mintina talatin tana kuka sannan ta mike ta fada bathroom ta wanke fuskarta ta fito ta shafa cream da perfume tayi slipped into her half night gown ta tofe bedroom din da addu’a, ta kakkabe bed ta kwanta tareda lumshe idanu, ta janyo wayarta dake ringing tareda bude idanunta, tayi picking, in a sleepy tone tace,

“Halooo”.

“Princess”.

Daga voice dinsa ta gane Hussein ne, good night words sukayi exchanging sannan yayi hanging call din, ta maida wayar akan bedside drawer ta lumshe idanu, ta rasa dalilin ya saka ta kasa saida ta raba dare sannan ta samu bacci yayi awon gaba da ita….

*************

Washegari,

Hassan da Hussein ne zaune a garden suna catching fun, suna sanye da kananan kaya, wando three quarter da shirt mai kama jiki, kafafunsu sanye da shoes kirar gucci, sumar kansu tana sheki tana walwali tana daukar idanu, suna zuba kamshi na best perfume din Hafsat, sunsha kyau _MashaAallah_ kallon abu suke a wayar Hassan suna kyakyata dariya iri daya mai yanayi daya tareda appearing a salo daya……

Hassan yace, “Hilarious…”.

Hussein yace, “Unbelievable… Hmm… Funny… You know what na kasa daina dariya…”.

Hassan ya wafce wayan ya ajiye akan table, suka tsiyaya zobo suna sha suna murmushi…

Hussein yace, “Ina tunanin daukar Hafsat in kaita shopping… Ya kake gani?”.

Hassan yace, “Ka kira ka fada mata mana… Sai kaji ra’ayinta mana…”.

“Yeah haka za’ayi”.

Hassan ya mike had’e da jan wayarsa, yace,

“Am going…”.

“To where?”.

“No where”.

“Bari in maka escort…”.

Suka kalli juna sukayi dariya….

Hassan yace, “Ni na tafi”.

Hussein yace, “Gudun budurwata kake…”.

“A’a tsoro nike kadda in kalleta inyi nightmare da ugly face dinta…”.

Dariya sukayi yayinda Hussein ya kai mashi punch, Hassan ya goye, yana dariya yace,

“You know what?”.

Hussein ya maida hankalinsa wajansa yace,

“Nop but i guess labarin ban dariya ne”.

“Yeah…”.

Hassan yayi kasa da kai yace,

“Once upon a time……”.

A hankali yake motsi da cute pink lips dinsa, labarin yana da tsayi, suka kwashe da dariya…

Hussein yace, “Aahh hilarious…”.

Hassan yace, “Yeah shiyasa na baka…”.

Sai kuma ya bashi hannu suka tab’a yace,

“Am leaving…”.

“Ka tsaya…”.

“Kaifa baka da kishi…”.

Dariya suka saka, Hassan yayi cikin garden din yana ware hannunsa kanshi a sama da murmushi kwance akan fuskarsa, yana more yanayin, yana cike da annutsuwa, can wani wuri ya tsugunna ruwa yaji suna bin fuskarsa, ya saka hannu yaji hawaye ne, ya ware idanu duk yadda yaso ya tsaida kukan ya kasa, ya dafe kai yana jujjuyashi totally helpless duk yadda yaso tsaida hawayen fuskarsa amma ya kasa….

Hussein ya jawo wayarsa yayi dialing call….

A hankali Hafsat ta sauko daga stairs sanye da hijab wadda ta wuce gwuwa ta fiddo hannuwanta ta hannun hijab din, da waya a hannunta wanda yasha henna na jan lalle, ta zauna akan cushion, tace,

“Momcy barka da warhaka… Besty an samu kallo anyi shiru, baki da hanci da idanu duk akan television kamar wadda ta warke makanta, thou rufe bakin kadda uhmm ya shige…”.

Dariya suka saka, Fareeda ta nunata tana girgiza kai sannan ta maida hankalinta akan kallon da take sai kuma tace,

“Yanzu zulfa’u ta kira an fidda ankon bikin gidansu, ta turo min sanfarin atamfa ce, less, lifaya da material, amma sunyi kyau, tace tana kira bakya dauka, har tace min busy ne ya dawo, nace a’a watakila hankalinki yana wani wurin shiyasa…”.

Hafsat tayi nodding kai tana duba wayarta, ta dago tace,

“Kai… Wow… Amma wannan anko da kyau duka babu na yardawa… 150k… Sunci kudinsu…”.

“Kiyi ma yaya Hassan magana”.

“Ina case dashi ne…”.

“Yeah… Ni dake da Hameeda muna da case dashi mana… Ankon nan mana…”.

“Fiddani a wannan lissafin, kinga ga wanda zan aura kike min maganar wani can…”.

Da mamaki Fareeda take kallon Hafsat……

“Yaa Hassan ne wani can?”.

Hafsat tace, “Yeah… What ever mah… Akan yaya Hussein shi kam wani ne can ko kina tunanin na hada yaya Hussein da wani… Impossible…”.

Fareeda tace, “Unbelievable!”.

Hafsat tayi shiru ba tareda tace wani abu, wayar dake hannunta ce ta soma ringing ta duba, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, tace,

“Shhh yaya Hussein ne… Aallah sarki yanzu nike niyar kira inyi mashi magana ankon nan”.

Sai kuma tayi picking tayi jim sannan tace,

“Haloo… Ahhhh… Where?… Ohhh… Sweety… Right?… Ahhh… I just laugh… Alright… Sure… Shikenan… Ahaa…”.

Sai kuma tayi hanging call din ta dago tace,

“Momcy… Yaa Hussein ne yake kirana…”.

Momcy tace, “Alright… Kiyi mashi kwalliya mai kyau kadda ki sake kije kamar yadda kika so fita jiya… Kina jina…”.

“An gama…..”.

Hafsat tana shirin mikewa Hameeda ta shigo da salaam, bayan ta gaida Momcy ta zube akan kujera ta fiddo wayarta……

“Babe kunga kuwa ankon gidansu zulfa’u?”.

Hafsat tace, “Yanzu muke maganarsa yana da kyau…”.

Hameeda tace, “Kyau kam ba’a maganarsa…”.

Fareeda tace, “Har na hangoni cikin lifayar… Gorgeous…”.

Hameeda ta dubi Hafsat sannan tace,

“Ina yaya Hassan?”.

Hafsat tace, “Bansan inda yake ba… Ko kuwa kin bani ajiyarsa…”.

Hameeda ta dubeta da mamaki idanu waje baki bude, tace,

“Yaya Hassan fa nace…”.

Hafsat tace, “Thou sweety ne da zan nemi sanin inda yake kin ganki da wata magana… Kinga bari inje in shirya sweety yana jirana… Yaa Hassan kuma nemeshi inda kika ajiye…”.

Fareeda tace, “Lallai yarinyar nan soyayya ta rufe maki idanu…”.

Hafsat tace, “Yeah… Kema kije kiyi saurayi kiga inda kika gaya min magana akan shi zanji haushi… Ai sone… Duk wadda ta samu handsome saurayi mai quality kamar nawa ai bazatayi wasa dashi ba… Hakanan in zauna wata ta gwace min…”.

Momcy tace, “Yauwa cwtheart, fada mata”.

Hafsat tace, “That is my momcy bari inje in dawo in dauki lecture yadda babu wadda zata kwace min saurayi…”.

Fareeda tace, “Ke…”.

“Idan uwata bata fada min ba… So kike inje in tambayi wata can ta bani gurguwar shawara… So kike inje a bani makauniyar shawara… A sakani a damuwa… Uwata itace k’awata, abokiyar shawarata, mu haka mu binne tare, wannan itace alakata da momcina, uwa mai share kukan y’ay’anta… Aallah yaja da ran momcina… Kunga nayi sama nikam…”.

Sai kuma ta haye sama ta shige bedroom ta ajiye wayarta akan bedside drawer tareda zare hijab ta fada bathroom bayan mintina talatin ta fito tana daure da towel durkushewa tayi ta fashe da kuka tana goge tears wasu new tears suna zubowa ta kasa tsaida hawayenta, ta dafe kai, bayan mintina talatin ta mike ta fada bathroom ta wanke fuskarta sannan ta fito ta dauki almost half hour tana kwalliya sannan ta mike ta zura wata gown irin ta jiya ta saka saidai colour da design dinsu ya banbanta, ta zura flat shoes ta rufe kanta da veil, ta fesa perfume mai saukin kamshi, saida ta dubi kanta a madubi ta dubi idanunta da kyau sannan ta fice, ta kofar baya tabi ta fice, tunda nesa ta hangoshi ya duke yana danna waya, dagowa yayi fuskarsa dauke da damuwa amma yana tozali da ita ya saki murmushi yana tattaro hankalinsa a kanta, kai ta dukar kasa saura kadan ta fadi taja kujera ta zauna….

Hussein yayi murmushi yana kallonta ta dukar da kai tana fidgeting zoben diamond dake yatsanta, ta dago suka hada idanu ya sakar mata murmushi yana lotsa hannunsa akan dimple dinsa, da sauri ta maida kanta kasa, a hankali yace,

“Princess kinyi kyau abunki… You look lovely… Kin shanyani kamar wasu kayan wanki raina ya b’aci amma tunda na ganki naji na huce ashe kwalliya kika tsaya kika min, da fatan ni na fara ganinta… Ai da ace fitowa kikayi da kaya can makarde ya zuba, can ruwan tea, can lipstick, can mangoro, can miya, ai da fada zamuyi…”.

Da sauri ta dago tana kallonshi ya kanne mata ido, ta sunkuyar da kai, ya mike ya zauna kusa da ita, a hankali yake mata magana tana sunne kai, koda ni bana jin abun da yake cewa duk da san dauko rahoto (my afra, besty, oum waheeda, zeezee, arabgirl, lungo girl kuzo ku tayani ji watakila wata taji abun da yake cewa na fadi min in rubuta amma banda kara maggi da gishiri da mai da yaji, kuma duk wadda aka ji motsinta aka maketa kadda tayi min kuka, aradu babu ruwana, nikam ina daga nesa yadda ina jin uhm in kwasa da gudu, hhhhh lols) murmushi yake yana karkato da kai yana motsi da cute pink lips dinsa, ta dago ta ware idanu ya gyada mata kai yana waving hannu, jim tayi ya kwashe da dariya tayi rolling idanu ya kwaikwayeta sukayi dariya, ya nunata ya nuna kansa ta sunne kai, yayi wani cute smile, ya mike ya koma opposite da ita yana kallonta tana dagowa ya juya mata baya yana cune fuska…..

Jim tayi tana kallonsa, hannu ta yarfe kamar zatayi kuka tace,

“Sad face kuma… Nayi maka laifi ne?”.

Hussein yace, “Ki rinka kirana sweety…”.

Hafsat tace, “Shine ka razanar da ni…”.

Hussein yace, “Ni kuma kike min rowar muryarki malama hafsatu….”.

_saida yayi wa d’an biyunsa tallar aurenta sannan ya fahimci yadda yake matukar sonta_

 

Littafin Ni da yaya Hassan na kudi ne, akwai shi complete, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057, na rokeki da girman Allah idan kin san baki shirya siya ba kadda kiyi min magana, na rokeki da girman Allah idan kin san ba littafina kike so kadda kiyi min magana

 

 

Follow me on this interested love saga

Hassan, Hussein and Hafsat love saga

One love 😍

 

*CHASING MY HEART*

*NI DA YAYA HASSAN BOOK 2

 

By sl rimi family’s

 

 

 

 

Page. 3

Free page

 

Littafin Ni da yaya Hassan na kudi ne, akwai shi complete, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057, na rokeki da girman Allah idan kin san baki shirya siya ba kadda kiyi min magana, na rokeki da girman Allah idan kin san ba littafina kike so kadda kiyi min magana

 

 

Kallonshi tayi ta ware idanu dariya yayi yace,

“Ohhh ashe kinfi son princess, wannan kallo haka, tunda baki so na daina ce miki malama Hafsatu koda kuwa ina son ince miki malama hafsatu zan daure inki ce miki malama hafsatu koda kuwa hubbyna ne kiranki malama hafsatu, kin tashi daga malama hafsatu kin koma princess, daman princess kike, tsokanarki nike… Ina tunanin kaiki shopping… Ya kike gani?”.

“Momcy bazata bari ba ballantana kuma Daddy”.

“Saboda meyyy?”.

“Saboda hakan ba daidai bane”.

“Na fahimta, sai yasmeen ta rakamu…”.

“It make no difference… Hakan ba mai yiyu bane…”.

“Sai muje tareda besties dinki guda biyu haka…”.

“Alright, ka bari zan sanar da Momcy inji yadda zatace…”.

“Alright…”.

Sai kuma ta duke ta danna wayarta sannan ta mika mashi, ya amsa, yace,

“MashaAallah… Ankon nan yayi kyau… How much is it?”.

“150k…”.

“Ki turomin account number dinta zan mata transfer…”.

Sai kuma ya mika mata wayar, ta amsa tace,

“Na gode… Zan wuce”.

Hussein ya dubeta ya ware idanu, yace,

“Idan kin gaji dani ne, ni ban gaji dake ba, yanzu na soma enjoying…”.

Sai kuma ya mike ya koma kusa da ita sai bayan mintina sha biyar sannan ta mike ta koma ciki lokacin ana kiran sallar Asr ne, sama ta wuce ta shige bedroom tayi alwalla ta tada sallah ta jima akan praying mat sannan ta tashi ta nannadeta ta sauya hijab ta fito ta shiga bedroom din Momcy ta sameta tana lissafin kasuwanci, ta kwanta akan cushion ta lumshe idanu….

Momcy ta juyo tana kallonta ganin bacci take shirin tayi, tace,

“Kadda kiyi bacci a wannan lokacin…”.

Hafsat ta bude idanu ta kalli wallwatch sannan ta gyara zama ta fadi ma Momcy yadda sukayi da Hussein, Momcy tace,

“You can go, babu damuwa…”.

Fareeda da Hameeda ne suka shigo, Hafsat ta dubesu, tace,

“Babe zaku min rakiya, sweety zai kaini inyi shopping…”.

Fareeda tace, “Muyi shopping dai…”.

Hameeda tace, “Haka…”.

Hafsat tayi shiru tana wani tunani, suna zaune har aka kira sallar magrib, Fareeda da Hameeda suka mike suka fita, Hafsat ta mike ta fito taci karo da Hussein, yayi mata waving hand yayinda Hassan yaja hannunsa suka wuce…..

Hafsat ta wuce bedroom, tayi juyi ta lumshe idanu ta bude, ta ajiye wayarta ta fada bathroom tayi alwalla tayi sallah tana zaune har aka soma kiran sallar isha’i ta mike ta tada sallah ta jima a zaune sannan ta mike ta nade praying mat ta ajiye ta sauya hijab daga long hijab wadda take sharar kasa zuwa wadda ta wuce gwuwa mai hannuwa, ta fiddo hannunta tareda daukar wayarta saida ta dubi kanta ta mirror sannan ta zura takalma flat ta fito, tunda ta sauko daga stairs ta lura da yadda Hussein yake satar kallonta, tayi murmushi, taja kujera ta zauna kusa dashi….

Hussein yana motsi da lips yana kallon Hafsat kamar zaiyi nabbing dinta, suna hada idanu ta turo baki ta tsakuri abincin ta kai baki tana grinding tana turo baki, da sauri ya kawar da kai har yana neman kwarewa, ta ware idanu, glass cup ya ajiye bayan ya shanye ruwan dake jikinshi yaja Hassan suka wuce, jim kadan wayar Hafsat tayi kara tana dubawa ta mike tayi excusing kanta….

Hangoshi tayi tsaye a garden yayi crossing kafafu hannayensa a cikin pocket din jeans dinsa, murmushi tayi tana lekenshi holding hannuwa tayi tace,

“Sweety…”.

Hussein ya juyo yana kallonta yace,

“Angel, rigima… Kin sakani kwarewa…”.

“Abun da kake ne sai ka saka in rinka jin kunya…”.

“Alright, na daina…”.

“Sorry…”.

Hassan ne yayi appearing dafa shoulder din Hussein yayi, yayi mata waving hand yace,

“Hi…”.

Hafsat tayi mashi waving hand tace,

“Hi…”.

Hussein yace, “Angel… Good night and sweet dreams…”.

Sai kuma yabi Hussein suka wuce, ruwa taji a fuskarta tasa hannu taji hawaye, duk yadda taso ta tsaida hawayen dake dropping daga idanunta amma ta kasa, tana goge wasu hawayen wasu suna zubowa, ta rasa dalilin wadannan hawaye, ta durkushe tareda fashewa da kuka sai kuma ta dode bakinta da hijab ta wuce da gudu tana kuka, tabi ta kofar baya ta shige bedroom dinta, ta fada akan gado ta cigaba da kukanta saida tayi mai isarta sannnan ta mike ta fada bathroom ta wanke fuskarta ta fito, ta durkushe gefen gado tana kuka….

_10:30PM_

Hussein ya dubi Hassan dake danna system yace,

“Ina kiranta amma bata picking…”.

Hassan yace, “Watakila fushi tayi ne…”.

Hussein yace, “About what?”.

Hassan yace, “Watakila kayi mata laifi ne ko kuma tayi bacci ne…”.

Hussein yana danna wayarsa ya fesar da iska sai kuma ya gangara yana kallon abun da Hassan yake a system, bayan mintina Hussein yayi bacci, Hassan ya ture system dake gabansa ya duro daga saman gado, hawaye ne suka soma bin fuskarsa, ya dafe kansa da hannuwa biyu duk yadda yaso ya tsaida hawaye daga idanunsa amma ya kasa ya rasa dalilin wadannan hawaye……

 

_12:00AM_

 

Hafsat tana duke tana kuka, mikewa tayi tana dafe da kanta ta fada bathroom ta wanke fuskarta ta sakar kanta shower ta dauro alwalla ta fito cream kawai ta shafa ta fesa perfume ta zura night gown ta tofe bedroom din da addu’a ta kakkabe bed ta kwanta taja blanket ta rufe half jikinta, ta lumshe idanu tayi likimo….

 

_12:30AM_

 

Hassan ne dafe kai yana hawaye, motsi Hussein yayi, da sauri Hassan ya mike ya fada bathroom ya sakarwa kanshi shower, bayan mintina goma ya kashe shower, ya jima yana murje jikinsa da sabula masu kamshi sannan ya dauraye jikinsa yayi brush ya dauro alwalla ya fito, cream ya shafa ya fesa turare sannan ya kwanta bayan yayi addu’a lumshe idanu yayi yai hugging pillow ya rasa abun da zaiyi tunani akai kuma ya kasa bacci….

***********

_Washegari_ _11:30AM_

 

A hankali Hafsat ta bude idanunta daga baccin da ta koma bayan sallar subh, ta mike zaune tayi mik’a, ta janyo wayarta ta duba, ta jima sannan ta mike ta fada bathroom bayan ta fito, ta zauna akan mirror tana applying cream, powder da lipstick kawai ne a fuskarta amma she look lovely, ta mike tareda taking steps ta zaro wani breathtaking less dinkin fittet gown ta zura ta fesa perfume mai saukin kamshi, closet ta bude ta zaro hijab wadda ta wuce gwuwa ta zura ta zauna akan cushion tana duba wayarta sai kuma ta mike ta fice, tafiya take tana jin wani feeling wanda ta rasa dalilinsa idanunta suna tsaye akan gabanta ne kawai amma bata tantance abun da take wucewa, tana jin kafarta akan stairs tayi firgigit lokaci guda incident din london ya fadowa mata a rai, cak ta tsaya ta zuba ma downstairs idanu….

“Hi…”.

Hussein ne tareda Hassan, kallon Hussein tayi ta harari Hassan, kallon juna sukayi sukayi dariya suka wuce suna d’aga mata hannu, saida suka dade da wucewa sannan ta daidaita nutsuwarta ta sauko parlour ta gaida Momcy ta amsa fuska a sake, tace,

“Kin tashi lafiya?”.

“Laiya lau…”.

“Na jiki shiru nace kila kin koma bacci ne…”.

“Na koma bacci ne saboda tsabar bacci sai yanzu na tashi….”.

“Habibty breakfast dinki na akan dinning table…”.

“Aha…”.

Sai lokacin ta lura da Fareeda da Hameeda dake zaune, tayi masu waving hand tace,

“Y’an mata adon gari… Besty ansha kyau sai kace wasu amare… MashaAallah…”.

Fareeda ta dubeta kawai ta maida kanta akan kallon da take……

Hameeda tace, “MashaAallah… Kema kinyi kyau… Cute in hijab… Bani ce miki matar liman…”.

Sukayi dariya, Hafsat ta wuce dinning table tayi taking breakfast dinta, ta jima a parlour sannan ta wuce sama….

Da daddare,

Hafsat na shiga bedroom wayarta dake akan bedside drawer tayi ringing, ta dafe goshi tace,

“Ohhhh Aallah… Ina da damuwa…”.

Sai kuma tayi taking steps tareda zama gefen gado ta dauki wayar miss calls ne da yawa, na Hussein da wasu numbers gasu, message da ya turo ta bude…

“Princess… Idan mun gama lunch ki sameni a guest parlour… Maman twins…”.

Jim tayi sannan ta ajiye wayar ana kiran sallar Isha’i ta mike ta fad’a bathroom tayi alwalla ta fito koda ta sallame ta jima akan praying mat sannan ta mike long hijab dake jikinta ta cire sannan ta linke praying mat tayi placing dinshi, ta wuce bathroom ta jima sannan ta fito tana daure da towel, tayi applying cream tareda zura hijab wadda ta wuce gwuwa ta fito, Hassan da Hussein kawai ta tarar a parlour kallon daya tayi ta harari daya sannan ta samu kujera ta zauna tana cune fuska tana ji suna kallonta suna kus-kus amma tayi banza dasu tayi kamar bata son dasu ba….

Fareeda da Hameeda ne suka sauko suka baje akan kujera suna gaida Hassan da Hussein….

Momcy ce ta sauko cikin shiga ta alfarma sai baza kamshi take, kusa da Hafsat ta zauna….

“Habibty… Zahrau ta haifi twins maza masu kama dake sak…”.

A tare Hameeda da Fareeda suka saki murmushi….

Hafsat ta mike zumbur, fuskarta dauke da murmushi ta dafe kirji idanunta a ware tace,

“MashaAallah… Momcy kice na zama maman twins… Wayyo twins dina… Amma momcy meyyy yasa ba’a kira aka fada man ba?”.

“Numbarki bata shiga ne… Kuma a rude nike bayan tafiyarku ya kirani ya fada min suna asibiti, wajen karfe biyu ta haihu… Yanzu ma Hajja safna (maman zaid) ce tayi insisting akan in dawo zata zauna da ita, ban dade da dawowa ba kuka shigo…”.

Hafsat tace, “Ai banga ta zama ba… Yanzu zanje inga twins dina… Sweety bani makullin motarka in tafi don bazan iya komawa dauko makulli ba… Am eager to see my twins…”.

Hassan da Hussein suka kalleta suna gumtse lips yayinda Hameeda da Fareeda suka kwashe da dariya….

Hafsat tayi sororo tana kallonsu, Fareeda tace,

“Momcy wannan autar taki tana da abun dariya… Koda yake abu biyu ne suka tarar mata… Ga wautar en fari ga sangartar auta…”.

Hafsat tayi mata wani mugun kallo sannan ta kalli wallwatch ta dafe goshi tace,

“Na manta amma gobe tunda safe zanje inga twins dina, am eager in gansu…”.

Sai kuma ta janyo wayarta ta dannawa zaid call….

“Salaam Alaika… Haloo… Ba wani maman twins… Ba wani dadin baki da zakayi min… Ya sis… Bari kaga kukan twins dina nike son ji… Kayi min wannan kawai amma maganar hakuri babu, nayi babies twins masu kama dani amma ka gaza kirana ka fada min… Kai… Aallah?… Nima neman magana ne amma kaga gaisuwa naje, hali zanen dotsi na manta wayar a gida, wata besty na ce Abbansu ya rasu… Aameeen… Yeah tabbas shine… Ahhh ayya… Aameen… Adda zahrau barka… Ya jiki… Ahhhhh… Hhhhh… Sis an shiga labour room… Hhhh har na hango wata shagwab’ab’b’iya tana nakuda… Hhhhhh… Har na hango reaction din fuskarta… Ahhhh Ga tanan kusa dani ita da er uwar dayar… Ahhhh ita mana… Hhhh ai tasan da ita nike… Ahhhh… Ahhhh abun dariya… Ahhh ai Adda kin gama min komai da kika haifa min twins masu kama dani… MashaAallah na samu twins maza masu kama dani… Kedai bari zaki gani a account dinki, zakiga alert mai kauri… Aallah… Good, kice mashi ya turo min pictures dinsu… Alright… Bye… Aallah ya kara sauki… Ahhhh…”.

Momcy tace, “Barsu gobe idan Aallah ya kaimu sai kinje kiga twins dinki…”.

Hafsat ta gyad’a kai….

Daddy ne ya fito ya nufi dinning, suka mike suka rufa mashi baya, kowa yaja kujera ya zauna, kamar kullum Fareeda ce ta mike tayi serving kowa sannan ta zauna taja dish, Hafsat ta kai spoon baki with exciting tace,

“Ahhh gobe idan Aallah ya kaimu zan….”.

Daddy ya kalleta, shiru tayi bata kara uttering word ba har ta kammala ta mike ta bar Fareeda da Hameeda da tattare abubuwan da aka b’ata, ta wuce bedroom dinta ta maida kofa tareda zare hijab dake jikinta, ta fada bathroom tayi brush tareda wanke fuskarta sannan ta fito ta karasa gaban mirror ta cancara light makeup, ta shafa lipstick, powder da kwalli kawai amma she look lovely, kamar kullum ta zura wata gown mai kauri, hawa biyu ce, ta daura madauranta, ta saka turban maimakon kallabi bayan data had’e gashinta tayi hiding sauran a bayan rigarta, ta janyo veil ta kalli kanta a mirror smile ne yayi escaping akan lips dinta ta fesa perfume mai saukin kamshi ta zura takalma flat ta fice ta bar wayarta akan right bedside drawer, a hankali tayi taking step har ta karasa guest parlour, da salaam ta shiga, duke yake shima ya sauya kaya shirt ne da jeans a jikinsa, yayi zanzaro yana baza kamshi, he look gorgeous, a hankali ya dago tareda amsa salaam da tayi, yana sakin murmushi, ta zauna kujerar dake opposite da wadda yake zaune, a hankali yace,

“Princess kinyi kyau, you look lovely…”.

Sai kuma ya mike ya koma kusa da ita yana mata magana kasa-kasa tana murmushi, wayarshi ya nuna mata yana murmushi, ta ware idanu sai kuma tayi murmushi, sai karfe goma ta mike ta koma ciki, bayan mintina biyar ya mike yabi bayanta, ya wuce nasu bedroom ya tarar da Hassan….

Hafsat ta rage kayan dake jikinta ta fada bathroom, ta sakarwa kanta shower tayi brush tayi alwalla ta fito ta jima a gaban mirror sannan ta zura transparent half night gown ta tofe bedroom da addu’a ta kakkab’e bed ta kwanta tareda lumshe idanu, ji take kamar tayi tsuntsuwa taje taga twins din da Zahra’u ta haifa, lumshe idanu tayi bayan wani mintina bacci yayi awon gaba da ita….

Washegari tunda safe ta shirya ta dauki breakfast din en hospital tayi wa momcy salaam sannan ta wuce a motarta….

Hussein ne ya fito daga bedroom, ya shiga bedroom din Momcy, har ya mike yace,

“Angel?”.

Momcy tace, “Ta wuce asibiti a motarta…”.

Hussein yayi jim sannan ya fita, ya shiga motarsa, yayi horn mai guard ya wangame mashi get, yabi bayanta, parking motarsa yayi sannan ya zaro waya ya kira direbansu, ya b’alle murfin motar ya fito tareda shigewa cikin asibitin….

Hafsat tana zaune tana kallon kyawawan en biyun masu kama dasu sak….

Hussein ne ya shigo da salaam akan bakinsa, ya zura hannunsa a pocket din wando yana murmushi yana kallon Hafsat wadda aka amsa salaam din a tare da ita amma tana still kanta a duke, yaba zaid hannu suka gaisa sannan ya ja kujera ya zauna yana ma Zahra’u sannu cike da kulawa……

Direba ne ya shigo ya gaida Zahra’u tareda yi mata barka, ta amsa da fara’a, Hafsat tace,

“Nice nayi twins amma baka yi min barka…”.

Dariya sukayi yayi mata barka ta amsa tana tsokanarshi, Hussein yace,

“Angel bani makullin motarki…”.

Hafsat ta mik’a mashi ya amsa tareda mik’awa direba, direba ya amsa cike da girmamawa, yayi masu salaam ya wuce…

Mamin zaid ce ta shigo, Hussein ya gaidata ta amsa tana tambayarshi mutanen gida, tace,

“Angel tayi twins na manta dani…”.

Hafsat tace, “Mami ke daban ce, matsayinki daban ne… Ina gamawa dasu zan tafo musha hira abunmu”.

Mami tayi dariya tace,

“To ai shikenan…”.

Dariya sukayi….

Hassan ne ya shigo, Fareeda da Hameeda na bayanshi, suka gaida Mami, Hassan yaba Zaid hannu suka gaisa sannan ya tsaya bayan Hafsat yana kallon cute babies din, Hafsat tace,

“Kadda ma kace in baka don ban gaji da ganinsu ba…”.

Dariya aka yi, ya juya wajen Zahra’u, Hafsat tayi breakfast tareda Mami, lokacin da zasu tafi tsayawa tayi tana ma twins ban kwana, tace,

“Twins dina shopping zan je inyi maku…”.

Suka wangale baki suna mata dariya, tace,

“Kun gani sun san Mamansu…”.

Dariya aka yi, sukayi masu salaam, Hafsat tana taking step tana juyowa tana kallon cute babies din, ji take kamar ta koma wajensu….

Hussein ya bude mata mota ta shiga sannan ya zagaya daya bangaren, kallonta yayi yace,

“Ina muka yi?”.

Hafsat tace, “Shopping zanyi masu…”.

Hussein yayi nodding head yace,

“Sai Maman twins…”.

Sannan ya ja motar yayinda motar Hassan take biye dasu, inda Hassan ne yake driving, Fareeda na gefenshi yayinda Hameeda take a backseat, a bakin wani katon mall yayi parking, ya fito ya bude mata kofa ta fito, Hameeda da Fareeda suka fito, Hassan yayi zamanshi cikin mota bayan wasu mintina ya fito ya shige ciki, yaja kujera ya zauna, Fareeda da Hameeda na hango suna jidar kaya, Hussein ne yake jan trolley yayinda Hafsat take zura hannu tana daukar dukkanin abun da yayi mata tana dropping ciki, kaya take jida sosai amma rabi da quarter duk na twins ne, wani agogon maza ta nuna mashi tana murmushi, yayi mata nodding head kai ta dauki daya ta saka, ya zura hannu ya dauki irinta shima ya saka, kallonshi tayi ya kalleta ya ware idanu, gefe ta kalla tayi gaba ya bita yana ture da trolley din yana murmushi, bayan sun gama suka nufi wajen bill, a can suka tadda Fareeda da Hameeda, aka masu bill, Hussein ya zaro master card, Hassan ne ya ture mashi hannu tareda mika master card dake hannunsa, har mota aka kai masu kaya dake cikin manyan leather, direct suka wuce gida, Hussein yana driving Hafsat tana mashi hirar babies har yayi parking a harabar gidansu, bayan mintina biyu Hafsat ta fito ta wuce ciki daman an wuce mata da kayanta, babu kowa a gidan sai Hassan, Fareeda da Hameeda da suka dawo tare, sai kuwa maids, upstairs ta haye ta wuce bedroom, tana zare hijab wayarta ta soma kara, jawota tayi tai picking…….

“Assalamu Alaikum… Anyi discharging dinku?… Okay then… Alright…”.

Later at night,

Hafsat ce ta fito daga wanka tana daure towel daidai kugu, ta tsane jikinta tareda cancara makeup, wata fitet gown ta zura wadda ta matseta figure dinta sukayi appearing, ta janyo kallabi ta tamke kanta taja veil ta zura takalma flat ta fice……

Hussein na zaune guest parlour yana danna waya ta shigo, a hankali ya dago tareda kallon direction din da take, ya ware idanu ya mike da sauri ya fice, jim tayi tana bin kofar da ya bi da kallo, wayarta ce tayi kara tana dubawa taga message ya turo mata…..

“Kije ki sauya kaya sannan ki fito…”.

Kamar ta fashe da kuka ta juya ta koma ciki, tana mita ta cire gown din ta zura irin gown din da take sakawa taja veil ta fice tana hawa tana sauka kamar wata fulawa, yana zaune ta shiga ta rike kugu tana cika tana batsewa, saida yayi murmushi sannan yace,

“Princess smile mana… D’azu you looks hot… Yanzu you look lovely… Ai kinga lovely din yafi…”.

Da sauri tayi kasa da kanta, tayi taking steps ta zauna akan kujera, dariya yayi ya mike ya koma kusa da ita ya zauna yana mata magana kasa-kasa tana kallon gefe, komi yace mata naga ta kalleshi da sauri ta wani ware idanu, yayi dariya yana pointing a kanta, sannu a hankali yake janta da hira har ta saki jiki dashi suka sha hirar love sannan ta mike ta koma ciki…

Durkushe Hassan yake yana kuka wanda ya rasa dalilinshi…..

Hafsat na shiga bedroom idanunta suka cicciko da hawaye, durkushewa tayi ta fashe da kuka, bayan mintina ashirin ta mike ta fada bathroom, ta sakarwa kanta shower wanka tayi alwalla ta fito ta kwanta tareda lumshe idanunta….

Some days later,

Hussein ne ya kaita gidan suna, yara sunci suna, babban yaci sunan Abba wato Hisham yayinda karamin yaci sunan mahaifin Zaid……

Hafsat tace, “Duniya ba kara, ke mai uba shine kika zagaya kika saka aka saka sunanshi, Daddyna yana gefe…”.

Zahra’u tace, “Ehhh na saka sunan Abbana ai kowa babanshi ya sani, kema idan kikayi aure kika haihu sai kiyi zuciya ki saka sunan Daddynki, nikam sunan Abbana na saka…”.

“Aiko kinyi da er halak tunda yanzu zamani ya sauya ba’a kara, yanzu dai mai sunan Abba za’a kirashi Afzal shi kuma mai sunan Abbu za’a kirashi da Afraz…”.

“MashaAallah…”.

Dariya sukayi abun nasu gwanin ban sha’awa, abu ne mai matuk’ar wahala mutum ya gane waye d’an Daddy waye na Abba, shiryawa Hafsat tayi ta cancare, tare da ita aka yi ta zurga-zurgar hidimar suna, anci, ansha, mata sun rankwashe, mai jego da babies sun samu kaya, washe gari bayan an gama soye suka dawo gida tareda Zahra’u da cute babies dinta…..

 

_saida yayi wa d’an biyunsa tallar aurenta sannan ya fahimci yadda yake matukar sonta_

 

 

Littafin Ni da yaya Hassan na kudi ne, akwai shi complete, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057, na rokeki da girman Allah idan kin san baki shirya siya ba kadda kiyi min magana, na rokeki da girman Allah idan kin san ba littafina kike so kadda kiyi min magana

 

 

Follow me on this interested love saga

Hassan, Hussein and Hafsat love saga

One love 😍

 

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment