Littafan Hausa Novels

Ni Da Prince Complete Hausa Novel

Written by Hausa_Novels

Ni Da Prince Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

NA AYUSHER MOHD*

 

*No. 1

 

 

“Bissmillahi Rahmani Rahim”

Da sunan Allah mai rahama maijin kai…

 

 

 

Mikewa tai azabure tare da kallan agoggon bango na dakin dasauri tamike ganin takusa makara, mamaki take yanda bacci yadauketa akan sallayar datai sallar asuba, kaya ta cire tai saurin fitowa tsakargida taja ruwa a rijiya tafada toilet, wankan minti 5 tai tafito tafada daki tazura doguwar riga baka tasa hijab fari tare da daukar nikaf dinta da jakar makarantarta, dama ita sam kwalliya bata dameta ba.

Download 1000+ Hausa Novels Ebooks

Dakin ummanta tashiga azaune taganta tana ninke kaya tashiga da sallama tare da gaidata ta amsa cikin daure fuska Salmah kam tasaba da wannan hali na ummanta dan yanzu abin baya damunta, mikewa tai tare da cewa umma banga Abba ba koya fita ne? Kara hade rai umma tai tace ki wuce kigaida Goggo dan shikam ya fita tadan tabe karamin bakinta tare da karasawa dakin goggon ranta duk ba dadi, sam batasan matar.

Maganin Cikowar Gaban Mace

Sallama tai Goggo dake kwance ta amsa mata cikin gadara salmah tashiga tare da gaida ta goggo ta amsa tare da cewa yawan banzan za’a tafi? Salma tadaure tace goggo nidai makaranta zani.

 

Goggo tai tsaki tace oho dai tunda ke da kamal kunfi karfin iyayenku ai sai kuyi tayi tace goggo yaza’aikifadi haka? cikin zafin rai goggo ta mike zaune tace karya aka muku? Wayasani ma ko kamal din yamanta dake yayi auransa acan kasar dayake ke ya barki nan kina yawon nuna jiki? Idanun salma suka ciciko da kwalla tadaure ta mike tace natafi makaranta goggo tace ke kika sani munafuka mudai kika kuskura kika dauko mana abun kunya sai kinsha mamaki, Salmah tai saurin yin waje tana share kwalla umma tagani a tsakar gida alamar duk zancen dasukai taji dasauri ta wuce dan tasan umma baxata taba sa baki a wannan maganar ba, nikaf ta daura takarasa waje.

 

 

 

Titi ta fita tasamu bus din dazatai Buk tahau, acikin mota kanta kawai ta jingina a kujera tana tunanin wannan al’amari wai ace tsakanin ta da mahaifiyarta bawata shakuwa? Wai ‘yar fari? Ita atunaninta tin yaushe aka dena wannan abun? Intayi magana sai Abba yace mata uwarta ai bafullatanace tai wata ajiyar zuciya tare da dauko hoton kamal cikin jakarta takuramai ido aranta tace yaya yaushe zaka dawo? I really miss you, lissafin kwanan wata tashigayi yaci ace yaya kamal yadawo dan ayanda yafada mata randa sukai waya saura 3wks su taho to yanzu gashi taga harda durin kwana 5 lalai yaya kamar bai matsu yaganta ba? Rabonsu da juna tun shekara 3 dasuka wuce, maida hoton tai ganin sun iso tafito daga motar ta shiga makaranta.

Karanta Littafin Farar Haihuwa Hausa Novel

Lalai yau tayi late cikin hanzari tafara tafiya sam bataji motsin mota a bayanta ba sai da motar tazo daf da ita dasauri ta juyo cikin razana tare dayin gefe amma ina motar gudu takeyi gashi kamar dan koyo ne ke tuka motar sam ba’a seti take tafiya ba motar sai data gogi jikinta hakan yasa tafadi kasa tim.

 

Tabi motar dakallo idanta taf da kwalla dan mutane sun taru suna kallanta abin haushi bawanda yataimaka mata, ahankali motar tafara yowa baya sai alokacin takalli number motar Prince 1 ne rubuce a jiki.

 

Sai da motar tazo daf da ita dan harta runtse ido tadauka murkusheta za’ayi jin shiru yasa ta bude idanta ahankali kafar mutane uku tagani ahankali tafara dago idanta har ta dure su akan nagaban wanda tasani shine Prince Salman dan tanaganin rashin mutincin dayake yi a school din wani wahalalen yawo ta hadiya.

 

Salman yakashe mata ido sannan yace limamiya bakya gani ne? Aranta tace limamiya? Yacigaba kosai muntaimaka miki da glass ne? Salmah tamakamai harara sannan tadaure tace ku bugeni maimakon kubani hakuri sai kuce me? Amir dake baya yai wata dariya yace hakuri? Oh prince kagane metake nufi ai? Salman yace ohh ai kaji halin talakawa sannan yaciro bandir din dari biyar yacilla mata yace sune matsalarki I know.

 

Najib dayai shiru abaya dan shi yake koyon tukin motar azahiri shikam baijin dadin abinda ke faruwa amma yazaiyi?

 

Salma tai wani murmushi tare da daukan kudin sannan takaraso kusa da Salman ta mikamai ganin yaki amsa ta daura akan motar sannan ta matso kusa da salman tace maza irinku masu daukan mutane banza sannan suke tunanin kudi na maganin komai suna matukar bani tausayi tana gama fad’ar haka ta juya tafara tafiya, mutanen dake gun suka shiga gulma, ran salman yagama baci yamaimaita afili Tausayi? Sannan yakalli kayan jikinta yaga gaba daya kayan datasa basu wuce kayan 2000 ba amma takalleshi tace yanabata tausayi?

 

Dasauri yakara kusa da ita ta baya ya fizgo hijab dinta, jikintane yafara rawa ganin bata taba shigowa makarantar ba nikaf bama bare hijab ahankali hawaye yafara gudu a idanta salma yadawo ta gabanta dasauri ta tsugunna tare da kankame jikinta, ya firgita ganin yanda Allah yamata kyau amma rashin mutuncin dake idananunsa sun rinjayeshi yatsugunno kusa da ita sannan yace tausayi? Nidake yanzu waye mai kalar tausayi? Hawaye kawai takeyi yai wata dariyar mugunta sannan yace banza ‘yar tallakawa ya mike yafara tafiya tace kai da kake d’an masu kud’i fin wasu kai? Tsayawa yai chak sannan ya juyo yace ke kinsan niko waye ma? Tace why should I know? Yace be careful dan zan iya ruguza miki rayuwarki mark my word ya juya ya tafi.

 

Amir yashiga tafamai yace woo Man kana burgeni, salman yai tsaki yafada mota yace najib zokaja cikin sanyin jiki najib ya shiga.

 

Salma kam suna tafiya tadau hijab dinta tasa da nikaf dinta tamike tare da kallan agogon hannunta shikenan tayi missing lectures dan kusan 40mins kenan dashiga class ahanakali take tafiya tana jin wata muguwar tsanar salman jitake daza’a bata wuka ace anmata uzuri takashe mutun daya data tsana a duniyarnan to lalai ba shakka salman zata lumawa wannan wukar.

 

Salma kam yaci alwashin sai ya nunamata shi basa’an yinta bane dan tunda aka haifeshi bawanda yataba fadamai maganar banza irin wannan banzar yariyar dabai masan ta ba, Amir yakalla yace adubomin ko ita wacece, Amir yace wannan yarinyar? Salman yace yes I can’t live her like this.

Amir yace angama prince….

 

About the author

Hausa_Novels

Add Comment

Leave a Comment