Littafan Hausa Novels

Ni Da Malama Ta Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Ni Da Malama Ta Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

page3⃣to4⃣

 

 

Fita tayi daga cikin ajin ranta a ɓace,ita kuwa ko a jikin ta daman hakan take so ,tana jin zafin maganganun da Aunty ke gaya mata,shiyasa ta ke son ganin ɓacin ranta.

 

 

 

” *Sabreen* *Muhammad* *mai* *taƙama*”

Da ƙarfi ya kira sunan cikin faɗa.

 

“Kina ina?yana maganar yana kallon ƴan class ɗin.

 

Gaba daya ajin yayi shiru kamar ba halitta a ciki dan ko numfashi a hankali suke yi dan tsabar tsoron wanda ya shigo ajin.

 

Jikar Maguzawa Hausa Novel Complete

 

Cikin nuna ko a jiki na ta tashi daga gurin da take zaune ,hankali kwance ta nufi inda suke,kallon Aunty ta fara yi wacce tare suka shigo class ɗin da shi.

 

 

Saida ta matsu kusa da shi sosai sannan ta tsaya ,ta kuma zuba mishi manyan idanuwanta wanda ba alamar tsoro a tare da su.

 

 

“Me kika cewa Malama *Haulat* *Hashim* *Kabir* ?eyeeh ba dake nake ba,kin kafe ni da ido”

 

 

Saida ta kalle malama Haulat ɗin sanan ta dawo da kallonta gare shi “Ce mata na yi ni bana jin turancin ƴan chaina,tamin na ƴan nigeria”

 

 

 

Shi kanshi bai san lokacin da dariya ta suɓuce mishi ba,dan duk makarantar kowa yasan iyayenta gurin turanci amma ba wanda ya taɓa mata magana sai Sabreen.

 

 

 

Ganin shi ma ya fara dariya abin ya ɓata mata matuƙa ga yan ajin suna dariya,a fusace tabar class ɗin,tsanar sabreen kuma da niyyar ɗaukar fansa.

 

Ganin ta fita yasa shi ma yai sauri yabar ajin.

 

 

wani annuri ya baiya na a fuskar sabreen dan jin daɗin yadda ta ga ranta a ɓace,komawa tayi ta zauna amma duk ji take yi bata rama hulaƙancin da malama haulat ɗin ke mata.

 

 

 

Zaune take ita kaɗai a staff room tana tunanin wani irin abu zata ma Sabreen ta huce,murmushi naga tayi wanda ya ƙara baiyana kyawun ramammiyar fuskarta,wato abinda zata ma Sabreen tayi shi yasa ta yin murmushi.

 

 

 

Ƙarfe ukku daidai aka buga ƙararrawar tashi,koya hankalin shi ya koma gidan, gaba ɗaya malamai da ɗalibai sun fito kuwa ya nufi hanyar gurin ajiyar motoci.

 

 

 

Har aka gama zuwa ɗaukan dalibai Sabreen tana zaune ita kadai ,ranta ya ɓace sai huci take yi,tana turo baki,tashi tayi zata fita bakin get.

 

 

 

Da mugun gudu motar malama Haulat ta zo wuce wa,ta gabanta kamar zata ɗauke ta,da sauri a ruɗe sabreen ta matsa har saida ta faɗi kasa,wani irin ƙululon takaici ya kamata,da zafin nama ta tashi ta nufu motar.

 

 

Tana ganin ta nufota ,ta fito daga motar tana wani yamutsa fuska kamar wacce tai arba da kashi

 

” U are very no what u are,okkk i forget u are illiterate ,baki da gwagwalwa ne ko a garin mahaukata aka daukoki da kina ganin mota ba zaki iya kaushewa ba”

 

 

Tunda ta fara magana Sabreen ki binta da idanuwa wadanda sukai jajiir dan tsabar takaici.

 

 

Ita kuwa malama Haulat ganin ta cinma burinta yasa ta wuce ta barta anan tsaye, ta kuma ja motar da karfi har saida ta watsa mata kura.

 

 

 

Wani lafiyayyan hawaye ya fara bin fuskar Sabreen wanda ita kanta bata san da zuwan su ba, sai jin su tayi a fili ta ce tana huce kamar wacce tai faɗa da zaki “Hmm baki san waye Sabreen Muhammad mai taƙama ƴar Aljanna ba ne,bana yafiya kuma bana biyar bashi zan rama ramuwar gaiyya”

 

 

Tana faɗa ta sa hannuwanta ta fara goge hawaye tana faɗin “Hm kika sa ƴar aljanna hawaye zai kin biyasu”

 

 

 

“To yah zanyi idan na gayawa hajiya ,A’a ba zan gayawa hajiya ba,ni da kai na zan ji da ita ”

 

 

Ita fitowa bakin get ɗin direban ta ya zo ,bata ce mishi komai ba ta buɗe motar ta shiga.

 

“ƴar aljanna kiyi hakuri wallahi faci tayar motar tayi,jikin shi har rawa yake yi dan tsoron karta gayawa Hajiya”

 

Banza tayi da kamar bata san da wani a cikin motar ba.

 

 

Sai magiya yake mata akan karta gayawa hajiya.

 

 

“To naji amma zai kamin abu ɗaya ta faɗa tana kallon shi

 

 

“to zanyi ƴar aljanna koma meye zanyi”

 

 

Murmushin mugunta tayi da jin daɗi ,harda sauke ajiyar zuci.

 

 

 

Daidai wani katafaren gidan direban yayi horn aka buɗe mishi,giɗan ya haɗu iya haɗuwa abin sai wanda ya gani,dan tsayawa kwatanta muku sai ya ɗauke ni lokaci mai tsawo.

 

 

 

Tana jin ƙarar motar su,ta fito da sauri har bakin motar ta fito tana wace baki ,ita da buɗe mata kofar hade da faɗin “Ƴar aljanna kin dawo tun ɗazun naji shiru ina ta jira hankali na ya tashi ina fatan dai kina lafiya”

 

 

Murmushi tayi sannan ta rungumeta “Kina lafiya hajiyata yau bamu fito da wuri ba ne,wanan ƴar iskar malamar ce ta tsayar da mu”

 

“Cikin nuna damuwa ta janye jikin ta tace”Wai ko sai na tura anje gurinta ne aja mata kunne,ko na fitar da ke daga makarantar gaba ɗaya ma”

 

 

 

“A’a Hajiya ki barta kinji ”

 

“to ni bansan duk wani mahalukin da zai ɓata miki rai,zan iya yin komai akan farincikin ki”

 

Daidai da isar su cikin katon falon wanda shi ma ya ƙyyatu har tsoro yaban dan tsabar kyaun shi,ga wani asirtaccen kamshi wanda ya haɗe da AC ɗakin.

 

 

 

Murmushi tayi cikin shagwaba ta ce “Nima na sani hajiyata,amma tunda na ce ki barta kawai ki barta zanyi maganin ta ,zan gwada mata ni ɗin ƴar gata ce”

 

“Hajiya bari na hau zama nayi wanka sai nayi sallah na huta”

 

 

 

“Yawwa ƴar aljjanna na manta ban gaya miki ba,ɗan india ya dawo an jima sai ki je ku gaisa”

 

 

Yamutsa fuska tayi yin sunan wanda ya dawo din”Wanan dan iyayin wanda aka je ɗauko mu tare”

 

“Eh shi fa”

 

“Tabbb gaskiya ni ba zani ba saida shi ya zo “ta faɗa tana hada rai

 

 

“to shikenan ba zai kin ɓata rai ba,zan sa ya zo da kanshi,kinji hankalinki ya kwanta”

 

ta washe baki “eh hajiyata,ta haye sama ,a ranta tana faɗin yadda zata ganshi dan tun sanin farkon da ta mishi kafin yaje india dan iyayi da kinibibi ne,to bari yanzu da yaje india….

 

 

 

 

Yawan comment yawan typing✅ote me on wattpad@fatimaumarmoddibo

 

 

 

 

~Bhatoolerty~

[10/17, 9:10 AM] Fatima Umar Moddibo: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹

 

 

 

 

 

 

 

*By*

*fatima* *Batula*

 

 

*Dedicated*

*to* *my* *shadow*

 

 

wattpad@fatimaumarmoddibo

 

 

 

 

 

 

 

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

 

 

 

 

*~We are bearer’s of so golden pen🖊~*

 

*~we write assidiously perceive no pain~.*

 

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

 

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

 

 

“`DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI,DUKKAN YABO DA GODIYA SU TABBATA GA UBANGIJIN TALIKAI.

 

 

 

Da farkon zan mika godiya ta ga allah wanda ya bani ikon fara wanan littafin,sanan kuma ina rokan allah ya bani ikon gamawa lafiya.

 

 

Ya Allah kasa na rubuta alkairi ka hane ni da rubuta sharri,ka yafe kuskuren da zanyi ya allah.

 

 

Gareku jama’a kuskure ya zama dole dan hakan na san dole nayi kuskure, ku yafe min kuskuren da zaku gani a ciki.

 

Bazan iya gode maka ba yaya umar saidai na biki da addu’a har karshen rayuwata.

“`

 

 

page1⃣to2⃣

…..Cikin yanga da ƙasaita take saukowa daga matakalar benan gidan, idan ta ɗaga kafa daya kafin ta ƙara ɗaga ɗayar ta sai ta ɗau saƙonni,duk wanan abun cikin kayan makaranta take yi,sikit ne ɗan ƙarami iya gwuwarta nevy blue sai rigarta fara mai ratsi-ratsin blue ba hijjab a jikin ta sai hular da ke kanta.

 

 

 

Wata kyakykyawar dattijowar matar da ke zaune a cikin tanƙameman falon ta hango yadda take saukowa daga benan murmushi tayi sanan ta ce “ƴar aljanna!! ke kullum sai kinyi latti,kinsan ƙarfe nawa ne yanzu kuwa?

cikin tausasawa take mata maganar.

 

 

It kuwa wacce aka kira da ƴar aljanna ko a jikinta banda ma ƙara rage saurin da tayi.

 

 

Wanan dattijowar bata ƙara ce mata komai ba, binta da kallo da tayi ko kaɗan bata nuna alamun ɓacin rai ko wani abu makamancin haka a fuskarta ba banda ma wani lafiffayan murmushi da take yi .

 

 

 

 

Ƙamar ta ƙarye dan tsabar yanga,ta iso falon,kan jikin dattijowar ta faɗa ,kanta matar ta taɓa,cikin so na nuna damuwa ta ce “Ƴar aljanna ko ba zaki makarantar ba ne? idan ba zaki ba muje ki cire kayan sai ki gayamin inda kike son zuwa mu je”

 

 

Kamar mai tsoron magana ta buɗe bakinta cikin shagaɓa ta ce “Zani *Hajiya* bana son wahala ne gashi wanan ƴar iskar malamar ce maiyar turanci zata fara shiga ajin ,ta kai ƙarshen maganar haɗe da ramutse fuska tana kallon Hajiyar.

 

 

“Kam to kina jina,duk abinda aka miki ki kira ni,zasu ga wanda ya tsaya miki,ni da su ne shege ka fasa ɗan halar sai yanka”

 

 

Washe ƙaramin bakinta tayi ,tana jin daɗi da alfahari,rungume hajjiyar tayi “Ina sonki hajiyata”

 

Tana faɗa ta tashi tabar falon cikin jin daɗi.

 

“Nima ina sonki ƴar aljanna sai kin dawo”

 

Tun kafin hajiya ta gama maganar ta bar falon.

 

Ɗaidai waata ƙatowar makaranta wacce kallo daya zaka mata ka fahimce makarantar bata ƴaƴen yara ba ce,ta tsaro da navy blue da farin fanti,yanayin makarantar idan ka gani ka ce ba’a j9 ba ne dan yadda suka tsarata,ƙatowar motar ta tsaya.

 

 

horn ɗaya direban yayi aka buɗe ya kunna kai,saida ya isa inda ake faking ɗin motoci sannan ya tsaya,bata wani tsaya ɓata lokaci ba ta fito.

 

 

 

J S S 3

Aka rubuta a saman ajin,kai tsaye ta kutsa kai ba tsoro ba tantamar komai,kanta a ƙasa.

 

 

“Hy how dare u enter me class without any excuse”

 

 

Saida nayi da ƙyar sanan naji abinda take faɗi,dan yadda take turanci kamar ba ƴar 9j ba,ko wacce tai karatu a kasar turai.

 

 

Ko ƙadan bata ji tsoro ba ta ɗago kai ido biyu suka yi,da wacce tai maganar

 

 

Tsaye take a gaban Allon,kyakykyawa ce ajin farko kallo daya zaka mata ka fahimce yadda tsarin halitar jikinta yake,ƴar gajerace ba cancan ba,sirirya ce ga dogon hanci kyakykyawa,bata da wani girman jiki amma kana kallon fuskarta zata san cewa wanan ba yarinya ba ce,dan ta kwana biyu.

 

 

Tun a kallo na farko na gane ƴar iyaye ce,dan yadda take yamutsa fuska kamar tana kallon ɗanyen kashi.

 

 

Ido cikin ido suke kallon juna,bata ɗauke idanta ba ta fara tafiya.

 

 

“Keee wacce irin dabbace mara hankali da wayau kuma jahila”

Cikin ɓacin rai da kausassaiyar murya ta faɗa.

 

 

 

Wani irin mugun kallo ta bita da shi mai cike da tsana ,amma sai naga ta sake wani ɗan karamin murmushin keta ta ce “Au sari kinsan bana jin turanci balle irin naki me kama da yaren chaina”

 

 

 

Tana rufe baƙi yan class ɗin suka fashe da dariya wanda daman tunda ta shigo hankalin su ya dawo gareta dan sun san sai anyi drama…

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment