Littafan Hausa Novels

Ni da Bodyguard Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Ni da Bodyguard Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

NI DA BODYGUARD DINA..

By khaleesi.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

 

HELLO ma’abota karanta littafi, ga labarin Raees da Khadija wanda nace zan rubuta, a karshen littafina Atsakaninmu gashi Allah ya bani iko, ina fata zaku ji dadin wannan littafi, yours khaleesi.

 Kibiyar Ajali Hausa Novel Complete

1.

Tafiya sadaf sadaf yakeyi sai ya bada dakika biyu uku kafin ya kara taku, night vision goggles dinshi su suke taimaka mai wajen ganin inda yake takawa cikin duhun daren da koh taurari babu ballantana jaririn wata, har yadda numfashinshi ke fita yake controlling, cak ya tsaya dayaji kar yewar sanda yasan ba shi bane ya taka sandar sai ya nemi wurin boyewa sannan ya fara observing wurin dan sanin ko ya karaso inda mutanen da yake nema suke, tafiya yaji dap dap dap sai kuma aka tsaya kara yaji wacce ta tabbatar mai da cewa daya daga cikin kidnappers dinne ya dan zagaya dan fitsari,

“Samuel do quick na i need to take a leak too”

“Relax my guy them oga no dey nah”

“No bi that i know want the ppl to run away ne”

” we tie them well well, come i don finish”

Yana jin karan an ja zip sai tafiya dip dip ya mike tsaye ya fara tafiya a hankali Samuel ya koma gadi yana kallon wata bukka dan can nesa shi kuma dayan yana fitsari a jikin wata bishiya meh kauri, sai da ya bari mutumin ya shagala sannan ya afka mai wani abu ya sokamai a wuya take mutumin ya sume, a hankali ya tallaboshi ya jashi zuwa bayan bishiyar

“You don finish”

Beh yi wani tunani bah ya mike da sauri ya nufi meh magana, yasan yana da advantage dan shi yana ganin Samuel wanda baya rike da koh waya balle torch light, shima tsinke me dauke da poison ajiki ya coka mai sannan ya jashi zuwa bishiyar da dayan wand ya fara sokama wa yake, agogon hannunshi yayi ma seti alarm bayan minti 25,lokacin ne poison din ze sakesu su farfado, shi kuma by then yana fata ya bar wajen, luck dinshi ne mah ogan baya nan da sauran yan jagaliyarshi saidai biyun nan kawai

Duk da yasan baze samu kowa cikin bukkokin bah, saida ya shiga da sanda sannan ya bi duk bukka ya duba har yazo wacce ta sada shi da mutane guda biyu daure, suna ganinshi suka zare ido tare da matsawa baya, ko kuma kokarin matsawa baya ya lura dacewa kaffafu da hannaye duk daure suke, hannu ya dora samman bakinshi sannan ya fito da waya daga aljihunshi ya nuna masu wani mutum, lokaci daya su duka biyu sukayi ajiyar zuciya da sauri ya kwance su sannan ya musu jagora,

“Akawai wasu mutane cikin bukkokin nan ne”har sun kai kusa da dajin ya tamabaya

Girgiza kai kawai sukayi, kayan daya gani cikin bukkokin yasa shi tambaya, amma yanxu daya gano na yan fashin ne bukkokin yasan akwai matsala in suka dawo suka iske su saboda haka sai ya yanke shawarar raba jaha dasu shi yabi hanyar dake leading directly cikin gari dan su biyoshi su kuma subi hanyar da zata kaisu kauye na gaba in yaso sai ya fada a daukesu acan.

“Aa tare zamu tafi”

Daya ya fada tun kafin ya karasa fadan plan dinshi.

“Sorry but ku nake ba order ba the other way around bane, kuje can kauyen zansa azo a dauke ku ni kuma zan ja hankalin yan fashin”

Bayan sun bata time yana kokarin sasu su tafi amma sukaki, sai sukaji shewa ba shiri su duka suka fara gudu suka nufi titi direct, addua’r shi daya Allah yasa basuyi nisa da inda yayi parking van dinshi bah, dayake mutanen daya taimaka masu nawin jiki ne sun kara slowing dinshi down.

Sun fita daga cikin daji yanxu yasan sun kusa kaiwa titi headlights din mota kawai yake jira ya hasko koh zega direction din motarshi, magana da gudu yaji kusa kusa dasu

“Ku shiga gabana” ya fada musu sannan ya koma bayansu yana kokarin karesu daga bullets, bindigar shi ya ciro daga holsters dinsu dake daure kirjinshi sannan ya ciro karamar itama daga marikinta dake daure a guiwwar kafanshi, flash ya gani sannan ya kara ganin wani flash din haske.

“Ku kara gudu sun cin mana fah”

“Wai dama ba wani rescue team hakanan yusuf ya turoka”

“Ba lokacin explaining bane yanxu, yanxu lokacin gudu ne kaman hell hounds na binku a baya”

“Right zakuyi fast”

Ya fada yana kokarin maida wayarshi aljihu, bayan ya duba tracking device din motar a wayanshi yaga direction din da take, first shot din da akayi firing yasa su kara gudu shi kuma ya juya ya basu nashi shots din saida ya amayar da duka bullets din bindigoginshi dan ya watsa su kuma ya tsoratar da yan fashin sannan ya cigaba da gudu

“Key yana cikin motar ku tada motar koh ban karaso bah” ya fada masu da karfi dan sun kusan kaiwa cikin motar, sabon setin alburusai ya sama bindigarshi ya kara harbawa dan ya samu damar karsawa gurin motar kafin yan fashin su lura ya isa cikin motar, amma sai suka maida mai martani da nasu wankan bullets din

“Oh crap” yace dayaji zafi a left side of his chest tsaki yayi, wai a haka yasa bullet proof vest gashi bullet yayi penetrating har ya tabashi, amma yasan if hes lucky ciwon is not deep, fasa harbi yayi ya juya kuma harda kari ya kasa daga hannunshi balle yayi harbi harya kai motar wani bullet ya kara saminshi a shoulder blade sannan kafa, beh san meh yasashi murmushi bah amma yasan yaji dadi da Allah yasa yan fashin basu da saiti kaman yadda yake dashi yasan da saidai gawarshi yanxu tunda sune masu haskashi, saboda haka sai ya juya one last time yayi amfani da direction din da torch ke haskowa ya harba bindiga sabanin da dayake harbi kawai, wani murmushi ya karayi da yaji duka shots dinshi guda bakwai saida aka biyosu da ihu, alamin ya harbi target kenan, da kafa daya yayi hopping ya shiga mota sanna aka fara tuki,

“Nan zamuje” ya nuna masu wani address da aka tubuta jikin wata paper.

“Toh” kawai Alhaji Abdulrazaq babangida yace shi kuma Honourable Marwan isa turaki ya juyo yana tamabaya

“Ba a sameka bah?”

“A vest dinane ba matsala muje kawai”

“Indai an sameka toh zuwa wannan address yayi nisa ka fara ganin likita tukunnan”

“Am fyn kawai kuyi tuki fast but steady” yaji dadi a nijeriya ba a bada speeding ticket.

Ciwon kafarshi ya fara dubawa bullet din ya gurjeshi ne beh shiga jikinshi bah saboda haka ya daure gam, sannan ya cire vest din, true bullet din beh shiga deep bah dan yana ganinshi, bandage kawai yasa ya zagaye shoulder dinshi da chest sannan ya lalibo sabon riga cikin bag dinshi sannan yasa, tadashi yaji anayi beh masan yayi bacci bah koda ya bude ido gari ya dade dayin haske gashi kuma sun iso address din, da alamu har anzo tarban mutanen daya ceta dan yaga manyan motoci ga kuma na police.

“Kawu”

“Well done Raees,ni dama nasan cewa zaka iya ake cewa ayi inviting sojoji gashi kai one man ka dawo dasu”

“I was just doing my job”

“Kuma kayi da kyau”

Da wannan kawun nashi ya barshi ya nufi abokinshi senator marwan, shi kuma yasan meh ze biyo baya kuma Allah yasan baze iya going through it bah yanxu dan ji yake kaman an bashi kashi ga wani zafi daya isheshi, cikin motarshi ya shiga beyi tuki a hankali bah har saida ya ganshi a gidan daza a bashi taimako.

“Finally zanganki Asma’u”.

💍💖💍💖💍💖💍💖💍💖💍💖💍💖

NI DA BODYGUARD DINA.

By Khaleesi

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

02.

“Am sorry sir”

“Sorry for your self, kana cikin aiki kaji rauni a ina ya kamata abaka treatment”

Raees ya tsaya kame beh motsa bah koh yayi magana

“Nace a ina ya kamata abaka treatment”

“Agency is responsible for any injury obtained during duty sir”

“Toh meh yasa”

“I needed to see my family shi yasa and akwai doctor at hand shi yasa”

“Ka tabbata abin kenan kodan Kawunka ke da agency dinnan shi yasa kayi making wannan decision din”

“Aa, am sorry sir”

“Gashi wannan”

Raees ya karbi envelope din hannun captain dinsu, beh bude bah saida ya wuce, ya xata zega wani sabon assignment ne instead sai yaga invitation card zuwa welcome back party din Marwan isa turaki, typical of rich people ya fada, shi dama sun gane job dinshi yayi ba wani abu bah da suka wani turo mai kudi, first dukansu suka turomai 10 million as reward sannan invitation zuwa party, i get they are grtful but abin yayi yawa ai, din din yaji daga wayar shi ya fiddo daga aljihu dan dubawa.

• toh robocop har ka tafi aikin koh, kadai kula da kanka dan ko robots na bukatar hutu •

Murmushi yayi da yasa dimples dinshi suka lotsa, lokaci daya fuskarshi tayi transforming daga wani bakin soja zuwa yaro girar sama ta rabu dana kasa goshin shi yai sumul ba wani tamoji, idanunshi suka haska

Asma’u kenan ya fada sannan ya latsa ✆, bayan ringing biyu ta dauka

“Am surprised daka kirani naxata har ka kashe wayan”

” na tashi lfy, Ina fata kema kin tashi lfy “ya fada yana ignoring comment din datayi

“Eh, na tashi lfy haka kowa mah, ya jikin ka”

“Sai yau kke yi min ya jiki after how many days”

“Am sorry, ban samu dama bane shi yasa, kuma yaya kabir na fada min yadda kake”

“Ya kyauta, ya su mama”

“Duk kowa na nan lfy, me yasa baka dade bah wannan karon koh har ka kaji da ganina”

“In zan dinga ganinki ba dare ba rana bazan taba gjiya bah, amma kema kinsan abinda yasa husna”

“Na sani, toh yaushe kuma zan kara ganinka”

“Yanxu mah in kina son gani na zan zo”

“Hmmm, take care of your self Raees”

“Meyasa lokacin da muke tare bakya kiran sunana amma yanxu kike kira”

“Nima ban sani bah amma nasan da, it felt somehow ina ki ranka da sunanka but now i can manage without feeling funny”

“Naji dadin haka it meant kina ganin girma na shi yasa kika kasa kira tnk u”

“Bakomai, kana office ne yanxu”

“Eh zanje inga uncle dina ne, are you sure you are OK if not ki fadamin i can help, kinsan yanxu na gama wani aiki i get paid well zan iya taimakawa financially in kin gane nufina”

“We are okay, an biya su baba salary dinsu wanda suke bi, so komai ze zama okay,eventually, kuma kayi enjoying kanka da kudin da aka baka kayi deserving dinshi sosai ”

“Toh matar Salisu”

“Da alamu ka kaji da magana dani bari inyi saving battery dina”

“Sorry ban fada dan inyi offending dinki bane ya tunomin abinda zan rasa ne da kuma abinda he’ll be lucky to have”

“Allah ya zaba mana mafi Alkahiri”

“Amin husna, sai munyi waya kuma”

“Toh sai anjima”

 

“Good morning sir, ka aika a kirani”

“Yes Raees akwai wani issue da naji nakeson miyi magana akai,but bana san inyi putting wannan aikin aside bari in gama”

“Yes sir” ya maida nawinshi akan kafar da ba’a harbeshi bah amma yaji ya gaji, kallon kanshi ajikin wani babban frame yasa ya manta radadin ciwonshi, Bakaken kayane jikin kamar kullum black belt black shirt shoes mah military kind bakake ba kasafai ya cika sa suit din daya zo da uniform din bah,tunda yayi joining YOUR SHIELD rabi da kwatan kayanshi suka koma bakake, sai yan kadan ne masu kala suma beh cika samun lokacin daze sa

su bah.

“All done” Raees ya kalli uncle dinshi yaga shima kallonshi yake, dayake yasan wannan tactics din sai ya shirya fadan abinda yake tunanin shine dalilin dayasa aka kirashi

, straight to the point ya nufa beh tsaya wani boye boye bah.

“Sir in dama akan kudin danayi receiving ne na assignment dinnan danayi inada niyyar maidawa ban ma san yadda akayi suka samu account details dina bah”

Ya dauko invitation card din da aka kawo mai ya dora saman table din uncle dinshi

“Wannan mah declining dinshi nayi amma bah formally bah”

“Toh meye na declining ina son kaje, Marwan abokina ne kuma ka taimakeshi, dayace zeyi rewarding dinka outside of work ban hana bah shi yasa na ba yan finace dept daman ba Assistants dinsu account number dinka, kuma nima ina shirin baka nawa reward din kuma zakaje party dinan”

“Sir in ba wani disrespect zanso a min uxuri”

“Raees koh zaka fadamin yaushe rabonka da kayi taking vacation, kuma real vacation nake nufi bah na recovery daga injury bah”

“Sir___”

“No excuses tare zamuje it’s an order”

“Yes Sir”

Uncle dinshi ya tashi daga kujerarshi ya zagaya wurin Raees ya dora hannunshi saman kafadar shi sannan suka fita daga office din tare

“Ina fata kana da tuxedo koh wani formal wear fit for a party”.

“💖💍💖💍💖💍💖💍💖💍💖💍💖💍

BODYGUARD DINA.

By Khaleesi

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

03.

” ban san wayafi worse bah cikinku keda aunty jameela, ace ana munar dawowar babanku amma kunki zuwa”.

“Nashirya Allah zanzo amma kishiyar aunty jameela ta batamin kaya, kuma ina ganin uncle ya hana aunty jameela zuwa da tare zasu tafi”

“Ya daddy yake, mommy fah”

“Duk suna nan gida for now, i can’t believe bazaku zo bah, kuma daddy yaso ganinku”

“Kaman bamuje ganinshi bah da suka dawo, kuma uncle ya fada mana duk abinda ya faru da yadda wani yazo ya taimakesu”

“Daddy yace ze zo yau, ina san in ganshi nima, dan yayan uncle Yusuf kin sanshi ay friend din daddy meh Security Agency dinnan”

“Na ganeshi yana san tsokanan mutane”

“Yap shi”

“Kice ma mommy da daddy sorry bamu samu zuwa bah”

“Ki kirasu ki fada da kanki manah”

“Dan Allah khadija karki manta”

“Toh safwana zan fada karki dameni”

“Bye”

“Bye”

 

Dama yasan haka zata kasance, mutane iri iri kowa na sanye da kaya masu tsada an taru anata ci da sha da sunan taron murna, at least wa yanda ya taimaka are genuinely happy to be alive dan har gajiya yayi dace masu bakomai aikinshi yakeyi basai sun godemai bah, uncle dinshi ya hango yana wasa da dariya da wata yarinya meh sanye da riga da siket fuchsia yana ta daukan ido, kusa da ita kuma Alhaji Abdulrazaq ne da surikinsa Honourable Marwan, dayake ya saba ko ina yaje he’s always alert sai yabi kowani kusurwa da kalo tareda assessing duka mutanen wurin koh zega wanda yasha jinin jikinshi, komai lfy ya lura by the time daya gama checking ko ina, ya lura yanxu ba yarinyar acikin dattawan da aka yi taron dansu, tie din wuyanshi yayi adjusting, ya cigaba da kallon ko ina, idonshi yakai kan wani mutumi dazu shi kadai ya ganshi yanxu ma shi kadai ya sake ganinshi, girgixa kanshi yayi sannan yace kaima din ay tsaye kake kai daya kana bin mutane da kallo, besides kafin ka shigo inda ake party din mah sai anyi checking kusan sau uku, in kana cikin motar in zaka shiga hotel din da kuma in zaka shiga hall din da ake party din. So don’t worry ya fada ma kansa now ina ushers yana san drink time to let loose.

Koda ta dauki drink daga usher din batayi mamakin ganinshi bah dan tunda aka fara yawo da refreshments data shanye drink dinta zata ganshi a gabanta, yanxu ma tana daukan sabo bayan ta aje kofin tsohon tayi mai murmushi, shima yayi wanda beh kai idanunshi bah bata kawo komai a ranta bah dan ita a ganinta haka ya kamata a bata kula na musamman , tana waigawa taga ana kallonta, taso ta gane waye sai ta nufi wurinshi shi kuma ya kauda kai,

Bata sanni bah me yasa zata zo nan, sai ya maida hankalinshi kan usher din daya bata drink yana son yai signaling ya bashi shima, straight usher din ya nufa direct zuwa mutumin da Raees ya gani shi kadai yanxu har taba ya kunna, usher din yayi making show din bashi ashtray anan ne ya lura ba ashtray kawai sukayi exchanging ba hadda wani karamin abu kaman paper, ta gefen ido ya koma kallonsu dan karsuyi zargin ya gansu, yarinyar ya gani tana hira da wasu samari da yammata,hankalinshi ya maida kan wanda yake zargi yaga mutumin yana shan taba yana kakkabe tokar saman ashtray din da aka bashi sannan yaga ya bi hanyar fita da sauri training din Raees ya motsa, ya fara binshi ta yadda baze san ana binshi bah, har saida ya kai parking lot sannan raees yaga mutumin na dube dube dayaga ba kowa sai ya nufI wata mota can karshen parking space, bayan motoci ya dinga labewa har saida yakai mota dayace tsakaninsu da target din da yake bi, dariya yaji

Muryar maza hudu, ya fada ma kanshi,baze je ya tambayi business dinsu a wurin bah dan four to one is not fair bakaman yanxu da beh gama warkewa bah,saurarawa yayi dan jin abubuwan da suke fada, bayan ya tabbatar da yaji mai isarshi sai ya fara jogging a hankali yana barin wurin, securities din wurin ya nuna ma badge dinshi sannan ya fada masu abinda yakeso suyi, suka raba jaha shi tare da securities hudu sannan wasu suka tafi parking lot dan kamo wayancan.

Daga sama kawai taji an kabar da kofin dake hannunta da mammaki tareda masifa ta juyo taga ko waye, lokaci daya kuma wurin yayi tsit

“Ku tattaro duka ushers din wurin nan gaba daya”

“Yes sir” suka fada securities dinsu duka

“Waye kai, kana fama da matsalar tabin hankali ne”

Beh kulata bah instead sai ya fara neman usher din da ke ta bata drinks tun dazu.

“Raees meye haka,meye dalilin abinda kayi”

“Uncle ina zuwa” khadija ta fara masifa harda yan tayi, shi kuma idanunshi sai surfing crowd din sukeyi yana neman wani target

“Gotcha ” ya fada ya nufi dan saurayin da securities din suka taho dashi tare da sauran ushers din, yana ganin Raees ya nufoshi ya yarda tray yana san ya gudu amma ina, raees ya cha kumoshi ta wuya sannan ya jawo har gaban khadija.

“Right now akwai wasu mutane guda hudu a waje da security suka kama, sun biya wannan yayi making sure yasa maki abu cikin drink, and yayi succeeding dan tun dazu kike sha, gsky nake fada”ya hankada saurayin wanda ke tsugunne da kafa

“Yes, kumin afuwa sani sukayi, ni ban san komai bah”

Nan kowa ya fara tofa albarkacin bakinshi shidai yasan ya kalli uncle dinshi wanda yayi mai nuni daya zo, be bi hanyoyin daya kamata bah dan cikin taro ne kuma ba’a san a tada hankalin al’umma dan haka ya daga ma uncle dinshi kai sau daya sannan ya cigaba da abinda ya kamata,

“Calm down everyone, babu wani abun tada hankali, enjoy” sai ya rike usher din suka nufi kawun shi sauran kuma aka barsu suka koma kan aikin su, Khadija dai kyarma ta fara dan ta zata ☠ poison take ta sha

“Daddy ” ta fada da dan kuka kuka bayan tabi bayan su da suka shiga cikin wani daki

“My baby, wani irin abu kuka bata” kafin a bada ansa taji amai ya taso mata.

Taku har kullum khaleesi. 🤗

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment