Littafan Hausa Novels

Nana Maryama Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Nana Maryama Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

NANA MARYAMA

 

 

_Labari da rubutawa:_

*UMMYN FADEELAH*

 

 

*AMBITIOUS WRITERS ASSOCIATION*

_A.W.A_

 

 

 

 

_Wannan littafin yak’unshi tsantsan hak’uri da soyayya, wanna k’agaggen labarine. In suna ko hali yazo daya to ayi hak’uri ba ganganci bane sai ayi hak’uri. Kuma ina buk’atar gyara duk wanda yaga abin gyara yagyara min nagode._

 

_kuma wannan littafin shine littafina nafarko Allah yasa munfara asa’a Allah yabamu ikon gamawa lfy_

_banyarda wani ko wata yacanzamin rubutu ba don yin hakan laifine_

 

 

 

_SHAFI NA DAYA DANA BIYU_

*1-2*

 

 

 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 

Tafiya take yi, A nitse yayin da ta d’auki hanyar, mkrnt tafiyar ta d’auke tsawon 30mnts saboda akwai d’an nisa tsakanin gidansu da mkrntr, hakan yasa tayi latti, tana zuwa tasamu malam shamsu yana dukan latti hakan yabata damar canza akalan fiskanta izuwa natausayawa tana isowa gareshi tace malam banida lfyne munje asibiti ne kuma gaisuwa, gaisuwa kukaje ko kuma ke aka kai kince baki da lfy, a’a malam bani aka kaiba munje gaisuwa ne amma banajin dadi shiyasa ban iya yin sauri a hanya ba. Malam yace “bani hanunki, dan Allah malam kayi hakuri wllhy bazan k’ara ba. bulala biyar ne amma zammiki hudu, haka dai nayi ta bashi hakuri har dai akarshe yace min to in sha Allahu sainamiki rabi saiga hawaye haka dai namika masa hanuna yarike tsakiyar bulalan yamin amma saida nayi kuka ina shiga aji nazauna banjima ba monita yacemin tashi tsaye maryam d’aga ido nayi nakalleshi saikuma dai na tashi nacigaba da karatuna atsaye harkusan goma da kwata saiga malam al’amin yace “zonan maryam, nafito nazo nace malam gani “wai meyasa maryam bakyaji ne kullum nazo nake samun ki atsaye? wlhy malam babu abinda nayi kawai kullum haka yake min ina zuwa makaranta sai yace natashi, amma dai kinsan bazai daga ki haka kawai ba tace to shiknan malam nikullum banida abokin magana nikadaina sainayita surutu kullum ana d’agani. duk da haka dai kikiyaye, shiknan malam. tunda nayi shiru haryagama yimin fad’ansa bansake cewa komaiba yagama yace kikoma aji anata tilawa. Namike nace nagode malam……

Sakayya Hausa Novel Complete

Har aka tashi a makaranta dai bansake kula kowa ba muna tafiya da ummi ne take cemin “wai ke mekikayi wa monita ne yake miki haka? to ai ke kika jawomin yana ganin kamar nina hanaki kiso shi amma kirabu dashi wata rana zai bari ummi tace yanxu to haka zaki bari kullun yata dukanki? to y zanyi rayuwa ne ai wata rana ma saiya nemeni yarasa. ummi tace to wai bakya fad’a a gidane ina fad’a wa mamana mana amma kullum hak’uri take bani akan watarana sai labari. ummi tace hmmm to shiknan amma dai yakamata adauki mataki; nace mata “hmmm. kawai muka cigaba da tafiya harmuka yi wa juna sai gobe lahadi. ina zuwa gida mamana tayimin sannu nacire uniform d’ina nayi alwala nayi sallah nad’auki alqur’ani na nafara shigarda hadda har aka k’ira isha’i natashi nayi nace wa mamana dan ban aran wayarki nayi kira tad’auka tabani, nayi dialing numberrshi yashiga harya tsinke bai d’agaba,. dama yasabarmin da haka yana yankewa saiga k’iranshi yashigo nadauka nayi sallama ya amsa yace dafatan dai kina lfy nace lfy klau y jiki yace jiki dasauki sosai ina cika sati biyu zandawo inaso naganki nace Allah sarki nima ina so naganka kuma yanxu gajiya nakeyi idan naje makaranta akafa nafada ina hawaye yace to kiyi hakuri idan nadawo komai zai wuce. nace to Allah yasa! yace amin nace baka fadamin abuna ba, yace to I LOVE YOU BABYNA yana dariya. Nima nayi dariya nace nagode saida safe yace Allah yatashemu nakashe wayar natafi nakwanta. washegari haka yasake kasancewa a makaranta ina zuwa bandade ba monita yasake d’agani natashi har zuwan malam, yakalleni kawai yawuce batare da yace komai ba. Malam yafara tunanin anya ba gaskiya nake fada masa akan da gayya yake da gani haka yabar abin aransa sbd akwai abinda yab’oye a zuciyar sa akaina ni ban saniba…..

 

More comment more typing.

NANA MARYAMA

 

 

_Labari da rubutawa:_

*UMMYN FADEELAH*

 

 

*AMBITIOUS WRITERS ASSOCIATION*

_A.W.A_

 

 

 

 

_Wannan littafin yak’unshi tsantsan hak’uri da soyayya, wanna k’agaggen labarine. In suna ko hali yazo daya to ayi hak’uri ba ganganci bane sai ayi hak’uri. Kuma ina buk’atar gyara duk wanda yaga abin gyara yagyara min nagode._

 

_kuma wannan littafin shine littafina nafarko Allah yasa munfara asa’a Allah yabamu ikon gamawa lfy_

_banyarda wani ko wata yacanzamin rubutu ba don yin hakan laifine_

 

 

 

_SHAFI NA UKU DANA HUDU_

*3-4*

 

 

 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 

Bayan antashi a mkrnt nakoma gida muka sake waya da babyna yake cemin “to y hanyar mkrnt nace masa ” alhmdllh yace min “kiyi hakuri kaddarar muce tazo a haka amma in sha Allahu komai zai wuce, nace to Allah yasa, yace ” ameen nace “k’arayar ya hade kuwa? yace “yahade mana saura k’wana biyu nadawo, nayi sauri nace aikuwa kana dawowa zanzo naganka, yace ” to nana na nagode Allah yadawo miki dani lfy, nayi alamar jin kunya kamar yana kallona nace “ameen. A karshe yacemin I LOVE YOU BABYNA YAU BASAI KIN ROK’A BA. Nayi dariya nace ” I MISS YOU. Can naji muryar mamana tana kirana ” nana! nana kina ina ne bani wayar nan nakira babanku har yanxu bai dawo ba. Nayi sauri namai sallama nakai mata wayar tak’ira babanmu bai dauka ba, hankalinta atashe, nace “mama bari inje in duba shi, tayi saurin cewa a’a “nana kin san ranan haka yayi amma dana masa magana sai yace ” b’ata zanyi sai kace wani karamin yaro. Nace a’a mama bari dai in bishi hankalinki zaifi k’wanciya. Tace to nana Allah yakare ki, nace ameen.

Nafita nad’au hanya can nahango shi yana ta tafiya da abokinsa zai koma gida nace “sannu baba, muka gaisa da abokinsa nace baba biyoka nayi, munga kadade baka dawo ba shiyasa, kuma hankalin mama naaga yatashi ne. Abokinsa yace “gaskiya kinyi abinda yadace to shiknan “malam umar mukwana lfy, abokinsa yafada muka fara tafiya da babana yace ” ina motsa jikina ne shiyasa natafi babban masallaci nayi sallar magriba da isha’i, nace to ai baba duk ka daga mana hankali kaga baka da lafiya shiyasa , yace in sha Allahu ma babu abinda zai faru da izinin Allah. Haka muna tadi muna dariya har muka iso gida, nadauko wa babana cokali yaci abinci, yace “maryama kitashi kije ki kwanta ki kuma yi addu’ah natashi natafi nakwanta nayi addu’a, nafara tunanin Abubakar dina a zuciyata nake tunanin, lallai wannan karen turoshi akayi wato suna nufin idan yakarye zanfasa aurensa ne? Afili nace wllhy saina aure shi in sha Allahu. Ahaka bacci me k’arfi yayi awon gaba dani.

Washegari antashi monday, muka shirya zuwa mkrntr boko, saboda ni banaso a jirani nima kuma bana jira, hakan yasa nakama hanyata izuwa makaranta nan muka hadu da hauwa kawata take cemin “ai malami me TP din nan ne yarage min hanya. Baki ganshi ba wllhy yahadu, Sainaji zuciyata na mararin ganinsa, sai naji tana tab’ani “kikalleshi yanxu zai wuce, najuya fiskata ixuwa kofa naga yawuce kofar ajinmu ya shiga office, atake naji zuciya ta ta tsananta bugawa.

Nan dai aka cigaba da darasi, darasin karshe muna da English language kuma shima malamin TP ne sai suka shigo ajinmu tare saboda suna sallama ne daga ranan sungama.

ana mana darasi yanata zagayawa, nan ne yakalli yatsuna nayi musu lalle hakan ya burge shi, ana cikin yin tambayoyi yaji nayi magana dasauri yajuyo don ya gaskata hakan yakara burgeshi kuma muryata yayi masa dadi, daga karshe malamin mun yabashi damar yin magana yayi mana fada akarshe ya rubuta numbern sa da sunansa akan allo, yace bayaso yayi dogon magana ne sbd yana mura daiyi sauri yatafi gida yasha magani yakwanta.

Ahaka dai zucuya ta takasa barina washegari sai da na kirashi, yana dagawa, nayi sallama kafin y amsa naji yace “ALHAMDULILLAH” malam dama na kirakane akan naji ya jikinka yace “jiki alhmdllh dama nadauka bazaki kirani bane, nace kagane ni ne? Yace “sure ba maryam bace?…..

 

 

 

 

_More comment, more typing_

NANA MARYAMA

 

 

_Labari da rubutawa:_

*UMMYN FADEELAH*

 

 

*AMBITIOUS WRITERS ASSOCIATION*

_A.W.A_

 

 

 

 

_Wannan littafin yak’unshi tsantsan hak’uri da soyayya, wanna k’agaggen labarine. In suna ko hali yazo daya to ayi hak’uri ba ganganci bane sai ayi hak’uri. Kuma ina buk’atar gyara duk wanda yaga abin gyara yagyara min nagode._

 

_kuma wannan littafin shine littafina nafarko Allah yasa munfara asa’a Allah yabamu ikon gamawa lfy_

_banyarda wani ko wata yacanzamin rubutu ba don yin hakan laifine_

 

 

 

_SHAFI NA BIYAR DANA SHIDA_

*5-6*

 

 

 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 

Nace “kagane ni ne”? Yace “sure ba maryam bace”? Nace “nice mana, amma fa baka bari mun gaisa ba, “ai dama kinsan ina alla-alla ne ki kirani, shiyasa, nace “to ina wuni y jiki, yace ” jiki yayi sauki, tunda naji muryanki ai, nan take naji k’irjina yabuga, nace “iyye? Yace “bari inkiraki kar katin ki yakare, nace to. Yakirani, nadauka. Yace “wlhy maryam bazan boye miki komai ba, dafarko yatsunki ne suka burgeni, daga baya naji muryarki, nan take naso kitashi nakalleki, shiyasa nace kitashi tsaye a mkrnt, idan kin lura sai da nace kimai maita maganar da kikayi, wllhy ko kadan banji me kika fada ba da farko, sbd muryanki ne kawai yake yawo a k’wak’walwa ta, sannan kuma nakalle ki naji kuma kinmin”, sai naji kuma yayi shiru, yasauk’e murya yace “maryam kimin magana mana”, nace “hmmmmm sai nayi shiru, yasake cewa “dan Allah kice wani abu ko zuciyata zatayi sanyi mana, nace ”to ai bana so nafada maka abinda zaisa hankalinka yak’ara tashine shiyasa dan bazan maka karya ba, gaskiya inada wanda nake so, kuma an san shi a gidanmu”, yace “knan maryam bakya so na”? Nace “ni bance ba, amma dai bazan boye maka ba, yace “to dan Allah kibani damar kiran ki, in dinga jin wannan muryar taki me dadin gske, nace “badamuwa malam nagode, nan mukayi sallama nakashe wayata. Nakwanta nayi bacci, dake bayan azahar ne.

 

 

 

Bayan natashi a bacci, nayi wanka natafi islamiya, saura sati biyu ayi musabaƙan makaranta, haka muka cigaba dai da monita, kullun nazo makaranta sai ya ɗagani, malam Al’amin kuma yaƙiyi masa magana dan kar na raina monitan, yana ganin kamar zai daina, amma abin yaci tura, ahaka dai muka zo ranan musabaƙa, ranan yakama ranan asabar akayi na ‘yan izu biyu da goma, yan izu ashirin kuma sai gobe lahadi, nima ina cikin ‘yan izu ashirin din, washegari muka zo makaranta muka zauna a jin ‘yan gaban mu, muna ja wa juna karatu, su ja mana a izu ashirin, su kuma mu ja musu a izu arba’in, hakan yasa mukayi lattin shiga ajin musabaƙa, kafin mushiga, monita yace ” mutsaya awaje dukanmu”. ƴan ajinmu muka tsaya, yazo yace” sai yamana bulala hudu hudu”, yafara ni kuma gani da tsoron bulala, amma haka dai na daure nake zuwa, amma yamin yaki, saida yagama nazama naƙarshe, yamin bulala hudu, yace ” baisameni ba”, yakara min wani hudun, yasake cewa “bai sameni ba”, nadaga ido nakalle shi yace min cikin tsawa “bazaki bani hanunkin bane? Nace masa”” bazan bayar ba tunda kamin, ka maimaita min, wllhy bazaka karamin ba”. kawai banyi aune ba naji bulala ajikina, jiri yakwashe ni, kawai jina nayi a hanun malam hassan. Ashe yazo lokacin da yaji ina ma monita musu akan bazai kara dukana ba, nace masa “malam wllhy gida zan tafi, yamayar dani kamar jaka, kullum sai yamin mugunta, kullum a makarantan nan nice jakansa, kuma nafada wa malam Al’amin amma baice masa komai ba”.. Allah sarki malam hassan yaga inata kuka, yace “maryam kiyi hakuri kinga yanxu za’ayi na ‘yan ajinku”. nace ” nifa malam bazan zaunaba kaina ciwo yakemin”. yace bari nakama miki idan yaso saiki fara, idan kinyi sai ki tafi gidan, nace “to malam”.

 

Aka gama shirya wajen musabaƙa, aka kirani, ina yi nace wa malam hassan, ” malam zantafi gida, yace “to maryam Allah yasauwaƙe, nace “ameen.

Ina isowa bakin anguwar mu, naga yayana wanda nake bi mesuna Bashir, ya tambayeni na faɗamasa abinda yake faruwa, saiya tafi wajen babban yayan mu me suna Adam, yafada masa, yasan idan nafada wa mamana hakuri zata bani, kuma hakanne yafaru ina zuwa gida, nafada wa mamana, tunkafin nakarasa ta dakatar dani, tana cewa, cikin daga murya ” wai nikam banace miki ki riƙa yan haƙuri ba ne kam, kullum matsalar ki da bawan Allan nan baya ƙare wa, kullum akan abu ɗaya”..

Babana yak’wala mata kira, yace “to ni wannan abin ya ishe ni, idan ba’a dakatar da shi ba kashe min ita zaiyi, to wallahi bazai yuwuba”.

Nan yaɗauki wayarsa ya danna numbern ya Adam akan yazo muje makarantar aji dalilin takuramin dayakeyi. Ya Adam yaɗauke ni mukaje makaranta ahanya yake cemin, “kuma wallahi duk abinda yafaru kifada, har akan yana aikenki wajen ‘yan mata duk kifada”, nace “a’a ya Adam, abar wannan maganar, saboda kar mutuncin sa yazube a makaranta, abari idan bai bari ba, agaba sai ayi wannan maganan dan Allah”

yace” to shiknan, amma idan yakara, wllhy dakaina zan dau mataki”, dayake ya Adam yanada saukin kai.

Muka isa makaranta ya Adam ya sa mu su malam hassan, da malam Al’amin, sukayi magana, aka k’ira monita aka ja masa kunne akan kar ya sake dukana ba bisa k’a’ida ba, ya Adam yace “wallahi idan bai daina ba, zai dauki mataki da kansa, kuma abin bazaiyi kyau ba”, su malam hassan suka bashi hakuri.

 

Amma fa ya bashir yatara abokansa, akan zasuyi wa monita duka, idan yatashi a masallaci, dake yana kaiwa 11 nadare yana tilawa a masallacin, to awannan lokacin ne zasu masa dukan shan gishiri,

 

 

 

 

_More comment. more typing._

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment