Littafan Hausa Novels

Naga Tawa Kaddarar Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Naga Tawa Kaddarar Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*NAGA TAWA ƘADDARAR*

 

Tsarawa da rubutawa

 

Zainab Muhammad (Mrs.Ramcharam)

 

PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION

 

P.W.A

 

*GODIYA*

Ina mai godiya ga Allah subhanahu wata ala da ya bani ikon rubuta wannan labari Allah yadda na fara kasa na gama lafiya.

 

*NOTE*

Wannan littafi ƙirƙirarran labari ne wanda aka tsara bisa tsari da kwakwalwa tai nazari.

Labari ne mai cike da soyayya,ƙaddara kala kala,faɗakarwa,ilmantarwa dama nishaɗantarwa.

Joystick Din Shi Hausa Novel Complete

*GARGAƊI*

Ban yarda wani ko wata suyi amfani da wani sassa na labarin nan ta kowane siga ba ba tare da izinina ba dan haka a kiyaye*

 

 

*1-2*

 

A guje ta shiga ɗakinta kamar wata zararriya ta kulle da key sannan ta nufin inda wayarta take a yashe akan gado ta ɗauka ta shiga laluben wata number idanunta na zubda hawaye masu zafi da una.

 

“Hello Rahma na shiga uku na lalace dan Allah ki zo gida yanzu”

 

Fateema ta faɗa lokacin da Rahma ta ɗaga wayar.

 

Cikin mamakin jin halin da ƙawar tata take Rahma Ta ce”Lafiya Teema meke faruwa naji kina kuka?”

 

“Ni dai dan Allah ki zo ina cikin matsala wadda ina da tabbacin cewa kece wadda zata fitar da ni”

 

Fateema ta faɗa tare da kashe wayar ta faɗa kan gado tana mai cigaba da rusar kukanta tana ambtar ta shiga uku.

 

Ita kuwa Rahma da sauri ta miƙe jin Fateema ta kashe wayar sauri sauri gudu gudu ta shirya ta fito tsakar gida inda mahaifiyarta ke zaune kan kujera tana kunna gawayi.

 

“Mama zani gidan su Fateema”

 

Mama ta ɗaga kai ta kalli Rahma sannan ta mayar da kanta ga abinda take.

 

Ta ce”Tofa Allah yasa lafiya?”

 

Rahma Ta ce”Lafiya ƙalau wallahi kawai dai zani ne kin san an fara shirye shiryen bikinta”

 

Mama Ta ce”Tofa Allah ya tsare ki gaishe da Maman nata”

 

Rahma Ta ce”Za ta ji insha Allah”

 

Sannan ta juya ta fice.

 

***

Duk suna zazzaune jugum jugum kowa da ganinsa kasan cike yake da damuwa fal amma ba wanda yai magana.

 

Knocking ɗin da ake yasa wata ƴar matashiyar budurwa wadda a ƙalla ba zata wuce 15years ba ta miƙe ta nufi ofar.

 

“Wane?”

 

Ta tambaya hannunta riƙe da hannun ƙofar.

 

“Nice Kairat”

 

Jin muryar kowace yasa Kairat buɗewa.

 

Da sauri Rahma ta shiga falon ko takan Kairat bata bi ba.

 

Gaishe da su Mommy ta yi suka amsa ba yabo ba fallasa saboda halin damuwar da suke ciki.

 

Bata jira me za su ce ba tai hanyar ɗakin Fateema, tana zuwa ta shiga bubbugawa.

 

Fateema jin bugu yasa ta ɗan dakata da kukan da take cikin muryar ta data fara dashewa, Ta ce”Wane?”

 

Rahma da sauri Ta ce”Nice Teema buɗe”

 

Jiki ba kwari Fateema ta miƙe ta nufi ƙofar ta buɗe, tana buɗewa ta faɗa jikin Rahma tare da saka wani sabon kukan.

 

“Rahma na shiga uku na lalace wa zai fahimce ni Rahma?”

 

Rahma ta kasa gane meke faruwa da ƙawar tata dan haka ta tura ƙofar ta kulle sannan taja hannun Fateema suka nufi bakin gado, zaunawa su kai sannan Rahma ta fuskanceta.

 

“Teema ina sauraranki meyake faruwa?”

 

Kukan Fateema ya tsananta, cikin kukan Ta ce”Rahma ciki ne da ni”

 

Damm! Damm!! Damm!!! ƙirjin Rahma ya shiga bugawa kafin ta miƙe a zabure cike da kaɗuwa…

 

 

*Yawan comments yawan typing in naga yana da masoya na cigaba*

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment