Littafan Hausa Novels

Naga Ta Kaina Sodangi Hausa Novel

Soyayya Da Karamar Yarinya
Written by Hausa_Novels

Naga Ta Kaina Sodangi Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

NAGA TAKAINA*

 

*NA SADNAF

 

 

 

 

*Free Novel*

 

 

*Tun kafin nayi nisa a rubutu nake da burin rubuta wanan labari Allah bai nufa ba sai yanzu labarin Nan ya faru a gaske tun 19’s wahalar rubuta shi nake gani Sabida yanda xan na had’a present da past Amma a yanzu Allah ya nufa zanyi insha Allah zai na zuwar muku sau uku a sati idan na samu sarari ma zaku iya samun pages fiye da haka labarin Nan ya bambanta da sauran novels Dina na baya za’a ga abubuwa da za’a ga Anya dagaske zai faru kuwa ya faru dagaske zaka iya aikata Abu da baka d’aukeshi a bakin komai ba sai bayan shekara da shekaru sai abun ya dawo maka Allah ya tsare mu da tsarewarsa ya tsaremu da imanninsa Ameen*

 

 

*Page 1*

 

*1992*

 

Da Sauri na shige d’akina na rufo k’ofa a lokacin da Umma ta hangoni ta biyoni a guje ko nauyin cikin dake jikina banji ba sabida tsabar tsoronta da nakeji.

 

Jingina nayi da k’ofar d’akin Ina sauke numfashi Umma kuwa sai tura k’ofar take Tana auna min zagi iyayena da kasa ta Dade da rufe musu Ido da take ta Kiran sunansu Tana zaga yasa naji wani irin hawaye na zubomin Sanin na riga da na kulle k’ofar yasa naja k’afana na nufi Kan gadona Sabida kaina danaji Yana neman fad’owa sabida tsananin ciwo rabona da abinci har na manta lemon kwalba da bredi su kawai suka zama abincina a matsayina na Mai tsohon ciki nida gidana ban Isa na fita ba sai uwar mijina ta nada min duka bredin ma da lemo sai na fakaici Bata palon nake fita na siya kamar yanda yanzu na faki idonta na fita Ina dawowa ta gani ta biyoni a guje sabida kawai na fita siyan abinda zan sawa cikina.

 

A Gidan Mu Take Hausa Novel Complete

 

Dan cikina dake ta mutsu mutsu yasa na tuna da yunwar da nakeji na tashi na mik’e dak’yar na jawo ledar bredi da lemo Dana siyo na fara tusa bredin Ina hawaye Dan ko kad’an ba dadinsa nakeji ba ci kawai nake.

 

Abban Zahira daya fad’omin a Raina yasa naji na k’asa ma had’iyar bredin bansan lokacin da kuka ya k’wacemin ba na fara magana a fili cikin tsananin kuka

 

“Nasiru Mai nayi maka haka Dana cancanci haka daga wajen Kai da mahaifiyarka?laifine Dan na zab’eka a cikin dumbin masoyana na aureka ka raboni da dangina da kowa nawa ka kawoni wani garin kana wulakantani Mai nayi Dana cancanci haka daga wajenka”?

 

Kukan dayaci k’arfina yasa na kasa cigaba da maganar da nake a fili na koma na kwanta sabida rawar da jikina keyi na cigaba da kukan da ya zame min jiki ko da ba’a min komai ba fuskata Bata rabo da hawaye sosai nake k’ewan yarana Amma uwar mijina ta hanani ganinsu Mahaifinsu kansa sai dai na jiyo muryarsa rabon Dana saka shi a idona wata hud’u kenan da sunan muna gida daya.

 

Mahaifiyarsa ta zama tamkar itace matarsa Dan komai ita ke masa kwana ne kawai Bata yi a d’akinsa.

 

 

“Mommy Mommy”

 

Naji siririn muryar Zahira Tana tab’a k’ofata

 

Zumbur na mik’e nayi hanyar k’ofa har Ina cin tuntub’e rabon dana ga ita da Nadiya har na manta Dan k’arfi da yaji Umma ta hanani ganinsu a d’akinta suke kwana ko d’akinsa da ta ga sun nufo d’akina zata daka musu tsawa tasa kanwar Nasiru Safiyya ta d’aukesu ta maidasu daki ta kulle tun yaran Ina jin suna kukan hanasu da akayi su zo wajena har suka zo suka Saba

 

Idona ya rufe sosai da San ganin yarana hakane yasa ko kad’an ban tuna da wata Umma na palon ba Dan inajin tashin muryar ita da Safiyya da kanwar Safiyya Lami a palon suna Hira.

 

Da Sauri na bud’e k’ofar banyi wata wata ba na d’aga ta Sama na rungume ta a jikina inajin wani irin Sanyi a zuciyata Wai ace Kai da danka karfi da yaji a nemi rabaku itama zahiran lamo tayi a jikina Tana sauke ajiyar zuciya ko damuwa banyi da yanda naji cikina ya dunkulle ba sabida yanda na Dora Zahira a jikina wuwurga Ido na fara yi ko zan hango Nadiya Amma Banga alamarta ba da Sauri na sauke Zahira na ruk’o hannayenta nace Mata “Ina Nadiya”?

 

Cikin maganar Yara tace min “dazu Yaya ya rik’e hannunta suka fita Ni Kuma inasan ganinki Dana ga Umma Bata kallona shine na taho wajenki mommy Dan Allah zan kwana a dakinki Aunty Safiyya Tana yawan dukana ta mitsini na har da tsintsiyar kwakwa take Zane Ni”

 

Zahira ta karasa fada tana Kara fad’awa jikina

 

 

Rungumeta nayi kukan da nake d’annewa ya k’wacemin Wanda hakan ne ya jawo hankalin su Umma da kallo ya d’aukewa hankali kaina

 

Wani irin Ashar Umma ta lailayo tayo wajenmu har zaninta na neman fad’uwa

 

Kara rungume Zahira nayi a jikina ko kad’an banji tsoron yanda ta taho wajena gadan gadan ba Dan gani nake kamar Zahira na iya taremin dukan da zata kawo jikina Tana isowa ta fusge Zahira da k’arfi daga jikina ta wancakalar da ita daga Ni har Zahira ihu muka saka lokaci guda Dan Zahira ta Bugu Ina k’ok’arin mik’ewa Umma ta jawo hannuna ta murd’a Tana “Bana hanaki tab’a yaran Nan ba kin Raina Ni ko toh wlh Kika Kara tab’a yaran Nan sai na saka waya na zaneki babu ruwana da cikin jikinki shegiya Yar mayyu jikar mayyu gidan uban wa ma Kikaje dazu”?

 

Duk maganar da take sheshek’a kawai nake Ina kallon hannun Zahira daya kumbura sabida bugawar da tayi ko kadan banji zafin yanda take murd’amin hannu ba

 

Kamar numfashina zai d’auke na fara magana Ina “Umma idan Wani Abu nayi Miki Dan Allah Dan annabi kiyi hakuri ki yafemin Dan Allah ki daina azabtar Dani banida kowa sai Allah sai ku Dan Allah kiyi hakuri kibarni Naga yarana”

 

 

“Kinci ubanki Naeema ba dai kin dage sai kin zauna da Nasiru ba azaba yanzu na fara gana miki nace miki bana sanki bana kaunarki tunda Kika Haifi wanan faratun Yar Taki nace ki tafi Kika k’i sabida maita kafin ma tayi shekara Kika Kara k’unsar wani cikin ke gaki kin Samu gidan arzkiki Zaki baje ki cike Mana gidan da Yaya itama Nadiyar ko shekara biyu batayi ba Kika Kara d’aukar wani cikin Zakici ubanki Dani kike magana wlh azabar da zan gana Miki a gidanan sai kin roki mutuwa da kanki Nasiru kuwa sai dai ki hangoshi daga nesa ya Miki nisa wanan tsinanan cikin jikin naki Kuma ki haifeshi nagani”

 

 

Ta karasa Tana wancakalar da hannuna tare da juyawa ta fusgi hannun Zahira dake ta tsunduma ihu har lokacin tayi hanyar dakinsu da ita ta wurgata Kan katifa ta jawo k’ofar ta rufe.

 

Ni kuwa kukan ma kasawa nayi na koma na zuci

 

Ina kallonta ta dawo zauna ta cigaba da kallo ita da yaranta da duka suka girme min Dan banfi Sha takwas ba lokacin Dan inada shekara Sha hud’u Mukayi aure da Nasir shekara hud’u kenan da auren mu.

 

 

“Ke Naeema zo ki wuce kiyi wanke wanke zan Dora Mana girkin dare kafin Yaya ya dawo”

 

 

Safiyya tace Tana jefomin harara.

 

Ban tashi ba sai da Umma ta juyo ta Kara zabga min wani mugun harara na mik’e jikina na rawa cikin dafa bango na Isa kitchen din na fara tattara lodin kayan wanke wanke Wanda wasu Dan keta ba amfani akayi dasu ba aka jibgashi wajen wanke wanke Dan kawai a bani wahala.

 

A hankali na fara wanke wanken hawaye nata zubarmin har da majina ban damu duk na hanasu zubowar ba Dan gani nake zan samu sa’ida idan suka zubo zuciyata datamin nauyi zata ragemin nauyi

 

Guntattakin abincin da suka rage na hada naci Dan banida abinda xan sawa cikina anjima bredin Kuma na gaji da ci Yanzu wajen sati kenan bana iya ba haya sabida Basir daya sakoni gaba.

 

Bani na fito daga kitchen din ba sai da na musu jajjagen kayan Miya na Dora musu farar Shinkafa sanan Umma ta umarceni da na fito na koma d’akina Dan danta ya kusa dawowa Bata San yayi arba Dani zuciyarsa ta tashi.

 

Ahaka na koma d’akina inajin duk gabobin jikina na min ciwo sallah ma kasawa nayi sai kwanciya kawai da nayi Ina tunanin shekara biyu da.suka wuce da nake rayuwa da mijina Naseer dake balain Sona kamar ya goyani da irin soyayyar daya shayar Dani daga Kan haihuwar Nadiya zuwa Kan cikin jikina Naga ya fara sauyamin tunda mahaifiyarsa ta dawo gidan da kannensa Akan tunda babansu Tijjani ya saketa Bata da gidan zama sai gidansa tunda shine babban danta d’akin daya Kamata ya zama mallakin su Zahira ta gaje d’akin da yayanta.

 

Da tunanin da iyayena suna raye da kila duk Banga irin wanan rayuwar ba mahaifina da kowa ke shakka da Yana Raye da kila ya kwatomin yancina da kila ban Sha wanan wahalar ba sai dai Kash Allah baya barin wani Dan wani yaji dadi bansan lokacin da baccin wahala yayi awon gaba dani ba

 

 

*Mafarki*

 

Karar bud’e k’ofar d’akina ne yasa na bud’e idona da Sauri na mik’e na zauna Ina tunanin kila Umma ce na mata ba daidai ba tazo jibgata

 

Ganin babu wanda ya shigo d’akin yasa na mik’e daga kwancen da nake Ina mamakin wanda ya turo k’ofar Ina k’ok’arin nufar kofar na rufe kawai Naga mahaifiyata ta shigo da farin lullubi har saman kanta fuskarta kawai ne a waje.

 

Gwallo Ido nayi nace “Ummaaaa”

 

Kallona kawai take batayi magana ba Ni kuwa na durk’ushe akan gwiwata na fashe da kuka Ina “Haba Umma meyesa Kika tafi Kika barni a lokacin da nake tsaka da bukatarki? Umma kinsan wahalar Dana ke Sha kuwa a gidanan Dan Allah karki Kara tafiya ki barni ki tafi Dani Dan Allah”

 

Nace Ina Kara fashewa da kuka

 

Har lokacin Bata ce da Ni komai ba in Banda kallona da takeyi Ni kuwa Ina ganin haka na mik’e da sauri Dan na d’auko mayafina Dan bazan Kara yarda ta tafi ta barni ba nagaji da zaman gidan Naseer da bashida bambanci da kurkuku gwara nabi mahaifiyata zanina dake Kan gado kawai na rarumo na juyo da Sauri Dan ko batamin magana ba wlh sai na bita sai dai Ina nufar kofar Naga Ina ta tafiya na kasa isa wajen da take a tsaye sai kallona take idonta itama kamar da hawaye har da Dan guduna Ina mik’a Mata hannu Amma sai Naga kamar nisa takemim Ina hangota daga nesa kuka na fashe dashi Ina “Umma Dan Allah karkimin haka ki tafi Dani wlh azaba nake Sha a gidanan Dan Allah Umma ki tafi Dani ko ki Kaine wajen yan uwanki ko na Abba

 

Ihu nake sosai ina Kiran Sunan Umma da take tamin nisa Ina ta k’ok’arin tadota a haka naga ta zauna a dakalin dake tsakar gidan ta jawo buta naga ta fara alwala cak na tsayar da kukan da nake da naji muryarta Tana “Naeema bazan iya taimaka Miki ba Shawarar da zan baki shine ki daina Wasa da Sallah ki Kara kusanta kanki ga Allah ki Kai masa kukanki Yana sane dake Yana Kuma ganin duk abinda ke faruwa dake addu’a na iya canza komai ki dage da addu’a Naeema daga ni har mahaifinki ba zamu iya taimaka Miki da komai ba ki dage da addu’a Naeema ki tashi daga baccin nan kije kiyi sallah Naeema ki gayawa Allah komai Yana jinki Kuma zai kawo miki mafita ki tashi Naeema Umma ta fad’a da k’arfi tana cigaba da alwalar da take”

 

 

A firgice na tashi daga baccin da nake duk nabi na had’a Gumi k’ofar na kalla Ina Umma tare da wuwurga idona a tsakiyar d’akin Dan gani nake kamar ba mafarki nayi ba kamar dagaske Naga Umma maganarta sai dawomin yake ni ba wani ilimi ba ballantana inyi addua iya fatiha kawai na iya shim wajen Naseer na koya dan Naseer nada ilimi sosai yayi sauka har sau biyu sai da mukayi aure yasan banida ilimin Arabi na bokon ma iya Aji biyu nayi aka cireni daga makaranta Ana ta zuga mahaifina idan nayi karatu zan zama ‘yar iska hakane yasa daga na bokon har na islamiyyar banyi ba Sallar ma ba sosai nake maida Hankali nayi ba Kuma hakan bai wani dameni ba sabida bani kadai bace duk yan garinmu da saoi na kusan haka muke rayuwarmu.

 

Mafarkin danayi da Umma ba karamin tsayamin yayi a Rai ba hakane yasa na mik’e da sauri na shiga bandaki nayi alwala na fito na fara Rama Salolin da banyi ba Dan sallar asuba kawai nayi a rashin ilimina gani nake shi ne ya zama Dole ayi sai Dana auri Naseer yake Dan nusar Dani nasan duk salolli biyar din wajibine sai Naseer na nan ma nakeyi cikakkiyar sallah Idan baya Nan kuwa ba kasafai nakeyin biyar d’in ba Naseer Yana Dab da kawo haske rayuwata mahaifiyarsa ta shigo rayuwarmu ya juyamin baya inasan ganin Mijina inasan muyi magana naji idan Wani Abu nayi masa na nemi yafiyarsa Amma mahaifiyarsa ta kafa ta tsare ta hanani ganinsa

 

 

Ina daga Kan sallaya na cigaba da zubar da hawaye

mafarkin da nayi da Umma ya tsayamin a Rai sosai Allah datace na kaiwa kukana na tuna na d’aga hannayena na fara gayawa Allah matsalolina Ina rokonsa ya kawomin agaji ta window labule d’akina nagane dare yayi duk da bansan ko karfe nawa ba a lokacin

 

Haka kawai naji inasan ganin Naseer a yau d’inan ko ta halin k’ak’a abinda Umma kemin bai min ciwo kamar yanda Naseer ya shareni ya watsar Dani a kwandon shara ko da ba auren soyayya mukayi ba bai Kamata ya watsar Dani haka ba ballantana auren soyayya mukayi Yana Sona Ina Sansa mukayi aure hasali ma duk Wanda yasan mu yasan yafi Sona Amma bansan Mai ya canzamin shi haka ba har yasan akwai cikinsa a jikina ya manta Dani haka bayan duk alkawarin dayamin na zame min uwa da uba tunda iyayena suka mutu yayi alkawarin rik’eni da Amana sanin banida kowa sai Allah Yaya na daya tal danake bi ya tafi makaranta Sojoji har yau bamu Kara Jin labarinsa ba ballantana na saka Rai Yana Raye tun Kan iyayenmu su rasu ake nemansa banida kowa sai Allah sai Naseer Dan haka na taso iya iyayena kawai nasani ba wani wajen muke zuwa ba ballantana nasan danginmu haka ma ba Mai zuwar Mana lokacin banida wayo balle nayi tambayi mahaifina ko mahaifiyata danginsu.

 

A hankali na mik’e daga Kan sallayar na nufi k’ofa na tsugunna Ina lek’a palon ta Ramin mukullin k’ofata ganin ba kowa a palon fitilun gidan ma a kashe yake yasa nasan dare yayi sosai Dan su Umma basa kwanciya da wuri sai wajen Sha biyu ko dayan dare suna kallo.

 

Bud’e k’ofar nayi a hankali gabana na fad’uwa addua kawai nake Allah yasa Kar Umma ta kamani cikin sand’a na nufi d’akin Naseer dake can karshen palon gabana Banda fad’uwa babu abinda yake yi Ina zuwa Tsakiyar palon haske ya gauraye palon gabana yayi wani irin tsinkewa na tsaya cak jikina na rawa ko kad’an bansamu k’arfin gwiwar juyawa ba.

 

“Shegiya tsinananiya Mayya wato ke Mai wayo ko? kina tunanin nayi bacci shine Zaki tafi d’akin Naseer sabida tsabar kwartuwa ce ke Ana dole ne Naeema wlh bazan Kara yarda ki rab’i Naseer ba asirin da iyayenki suka miki kike neman juyar min da Kan d’a na karya asirin lokaci nake jira kawai nayi maganinki

 

Umma tace Tana juyo Dani a fusace.

 

Da Sauri na runtse idona a lokacin da muka had’a ido da ita sabida yanda na tsorata da ganin ta Jan doguwar Riga ta saka har kasa ta rambada kwalli gata da manyan idanu hakan yasa na balain tsorata da ita kunnena data Kama da k’arfin tsiya yasa nayi saurin Kai hannuna na dafe hannayenta Dan kamar zata ciremin kunnen ko damuwa batayi da cikin jikina ba ta fara jana da karfi tayi hanyar d’akina sai da muka shiga d’akin ta sakarmin kunnen tare da rankwashina Tana

 

“Wlh duk ranar da Kika Kara gingin zuwa d’akin Naseer sai na kusa kasheki a gidanan kinyi kad’an ki b’atamin aikina D’ana Yana da arzkiki bana San ya zauna da macen da zata Haifa masa ya ko d’a Sama da daya tunda Kika Haifi Zahira nace ki tafi Kika k’i tafiya ke alailai sai an zauna dake toh wlh tunda Kika min taurin Kai zakigane shayi ruwana idan ma tunaninki idan Kika Haifa masa Yaya Zaki samu lasisin zama dashine toh karyarki taci karya Dan ko na jikin Nan naki wlh baki Isa ki haifeshi ba sai kin tafi D’ana ya auro wata tsalelliyar itama taci rabonta ta tafi banasan in Kara ganin kafarki a waje kiyi zamanki a d’akin Nan duk ranar danaga kafarki a waje wlh sai na b’allaki banza shashasha”

 

Umma tace Tana Kara dunguremin Kai tayi waje a fusace Tare da bugomin k’ofa

 

 

Kuka na fashe dashi Ina Kiran ummana akan tazo ta taimakeni ta tafi Dani nagaji a daren ranar ko kadan bacci bai ga idona ba tunanin rayuwata kawai nake da ace nasan hanyar garinmu wlh da na gudu na koma garinmu gashi ba ‘yan uwa ne Dani ba banida kawaye ba Wanda na sani ballantana na Gaya masa halin da nake ciki ya kawomin agaji.

 

 

 

Naseer kuwa a lokacin daya dawo daga wajen aiki a Palo ya tarar da Umma dasu Safiyya sai Mai bi masa Tijjani da shima yayi rashe rashe a palo Yana Kai lomar abinci bakinsa sannu da zuwa suka masa ya amsa

Ya tsugunna gaban mahaifiyarsa ya gaisheta tare da jawo hannun Zahira dayake Jin Santa daban a zuciyarsa wanda hakan nada Nasaba da balain kamar da take da mahaifiyarta rungumeta yayi a jikinsa Yana “Mamana kinci abinci”?

 

“To da zamu barta da yunwa ne kake wani tambayarta taci abinci nifa bana San irin haka”

 

 

Umma tace Tana banka masa harara sauke Zahira yayi ya sunkuyar da Kai Yana “Allah ya baki hakuri”

 

Ya mik’e Yana satar kallon d’akin Naeema Yana Jin wani iri a zuciyarsa bai San Mai yasa idan zai tuna ta sai yaji kansa kamar ya rab’e gida biyu ba Yana balain kewarta a zuciyarsa Yana balain San ganinta Amma ya rasa Mai ke sa shi Jin wani irin nauyi da d’ad’aurewar jiki

 

“Ka tafi d’aki kaje ka watsa ruwa kazo kaci abinci”

 

Umma tace Tana Kara hararsa sabida yanda taga yana satar kallon d’akin Naeema.

 

Su Safiyya da suka zubawa tv ido yabi da kallo Yana Jin wani irin Mugun Haushin rashin tarbiyya da basu dashi

 

A tsawace yace musu “Kunyi Sallah kuka zauna Kuna kallo”?

 

Da Sauri suka mik’e mahaifiyarsu kuaa tace “Ku koma ku zauna ku cigaba da kallonku sabida na tab’a yar gold yake neman hucewa akanku Banda iskanci irin na Naseer har yazo Yana tambayar ‘yarsa taci abinci a gabana”

 

 

“Umma wlh ba haka bane gani nayi Ana sallar isha suna zaune suna kallo shiyasa nayi musu magana”

 

 

“Dalla rufemin baki bazasu tashin ba sai ka bugesu yanda ka Saba bugunsu akan wancan mayyar matar taka”

 

“Allah ya baki hakuri”

 

Naseer yace Yana Kara kallon su Safiyya da suka koma suka zauna har da Kara volume din tv shi kuwa ya wuce d’akinsa Yana Jin wani irin d’aci a makogaransa shi Kuma nashi jarrabtar kenan Mahaifiya bai San Mai yasa take masa haka ba har gida ya Kama Mata tak’i yarda ta dage sai ta zauna dashi da kannensa wajen su uku.

 

Alwala ya daura ya fito ya tafi massallaci bashi ya dawo gidan ba sai wajen takwas da rabi har a lokacin suna zaune suna kallo.

 

Ko sallamar da yayi ba Wanda ya amsa masa Inda sabo ya Saba hakane yasa ya kinkimi Zahira da ke bacci a kasan carpet ya Kai ta d’aki ya dawo ya d’auki Nadiya itama ya kwantar da ita a gefenta ya dawo palon ya zauna duk da ba yunwa yake ji ba bai isa yace ya koshi ba dan Umma fad’a zata rufeshi dashi kamar zata Kai masa duka.

 

Yana zama umman ta mik’e ta nufi kitchen da kanta ta d’auko farantin data jera abincinsa a Kai ta ajiye masa yace mata ya gode.

 

Yana bud’e abincin yaga baki bakin gari a kwance akan farar Shinkafa a hankali ya saka cokali ya fara jujjuyawa Yana mamakin abubuwan da yake yawan gani a abincin da umman ke bashi Amma bai isa ya tambaya Bismillah yayi ya fara cin abincin.

 

Umma kuwa tayi Tsaki Tana zabga Mai harara taurin Kan Naseer din na balain Bata mamaki.

 

Yana gama ci ya koma d’aki ya kwanta ya zubawa Zahira Ido Yana kallon ta tamkar itace Naeema sosai yake so ya tuno ta wani Abu na danne shi har karfe goma sha biyu na dare bacci yak’i zuwar masa hakane yasa ya d’aura alwala ya hau Kan sallaya ya tadda sallah Dan tun Yana shekara goma sha biyu ya sauke al qurani Mai girma Naseer nada ilimin addini sosai Wanda duk mahaifinsa Mallam Ibrahim ya gado Dan shahararren mallami ne

Sosai har almajirai ne dashi da yawa har sai daya rasu.

 

 

Har karfe biyu Yana Kan Sallaya a zaune Yana Jan carbi maganar da yake juyowa kasa kasa yasa ya mik’e a Hankali ya bud’e k’ofar d’akinsa ya fito a tsakiyar palon ya hango mahaifiyarsa sanye da jar doguwar Riga har kasa hannunta rik’e da kunnen Naeema.

 

Sallati ya fara yi dayaji kansa ya balain Sara masa ya koma d’akinsa da Sauri ya zauna akan sallayar ya dafe kansa da hannu biyu Sabida nauyin da kansa ya masa.

 

“Naseer ka dage da Addu’a mahaifiyarka Tana cikin kungiyoyi da yawa bansan wacece ita ba sai Dana aureta”

 

Kalaman da mahaifinsa ke yawan Gaya masa kenan a lokacin da yake rayye.

 

“Watarana zaka ganewa idonka watarana zaka San wacece ita Naseer mahaifiyarka Bata bacci daddare”

 

Kansa ya Kara rik’ewa Gam a lokacin da yaji kansa ya Kara Sara masa daya tuno maganar mahaifinsa…..

 

 

Share

8/19/21, 10:30 PM – My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

 

*NA SADNAF*🌸🌸

 

 

®�? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_{We Don’t just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_

 

 

 

*Free Novel*

 

 

*Page 2*

 

*Naseer*

 

Mahaifinsa Mallam Ibrahim Dan Asalin Kauyen Modobi ne dake jihar Kano fitattacen Mallami ne a kauyensu har daga wasu garuruwan Ana zuwa d’aukar karatu wajensa manomi ne Yana Kuma had’awa da kiwo tun Yana da shekara ashirin yayi aurensa na fari da wata hindatu a cikin shekara hud’u ya auri Mata hud’u bayan hindatu akwai Aisha akwai Fatsima sai Zinnira Zaman lafiya ake sosai a gidansa Dan matansa sun had’e kansu Mallam Ibrahim a tsaye yake sosai Akansu hindatu nada Yara biyar Aisha nada hudu Fatsima nada hudu itama sai Zinnira dake da biyu

 

Duk yayan Mallam ibrahim suna da shekara goma sha Suke sauke Al Qurani Mai girma da littattafan addini ya tsaya musu sosai wajen inganta tarbiyyarsu ko kadan bai wani damu suyi Boko ba sai dai idan yaran sun girma akaran kansu wasu suka shiga na Boko wasu Kuma suka rungumi sanaar da mahaifinsu ya dorasu akai wato noma da kiwo a lokacin Mallam ibrahim Yana cikin masu kudin garin Dan Yana da shanaye da yawa gonakinsa ma bazasu kirgu ba

 

Hakane yasa yaransa maza dukansu suke da sana’ar da sukeyi har da masu Dan fita zuwa birni

Yaya matansa kuwa duk ya aurar dasu Dan suna shekara goma sha yake aurar dasu.

 

 

A haka rayuwa take tafiya girma na zuwar wa Mallam Ibrahim da matansa Watarana hindatu uwargidansa ta kamu da rashin lafiya kwana biyu da fara rashin lafiyrta ta amsa Kiran mahallacinta

 

Sosai Mallam Ibrahim yaji mutuwarta Inda aka ringa zuwar Mai gaisuwa ko ta ina dalibansa da duk sukayi karatu awajensa haka sukayi ta zuwa daga garuruwa daban daban suna Masa gaisuwa da suka ji labarin mutuwar a cikinsu Akwai wani Kabir da ya kasance dalibinsa Dan garin borno kasuwanci ne ya maidashi garin Calabar anan ya had’u da matarsa Sakeena ya Aureta yayansu Hud’u Sulaiman shine na fari sai Mai bi masa Hajara sai Hassan da Husaini duk a cikin yayansa.

 

Hajara ta fita daban a cikinsu taurin Kai ne da ita da ruk’o gashi ko Yaya kayi Mata Abu ko bisa kuskure ne sai ta nemi hanyar da zata Rama ko mahaifiyarta da mahaifinta Bata barsu a baya ba indai suka yi Mata sai ta San hanyar da ta bi ta rama batare da sun sani ba wani irin bakin haline da ita Kabir da matarsa Sakeena har mamakinta suke a irin haka watarana aka aiketa ta Kai Nikan Massara a hanyar ta tafiya wani yaro ya tsokaneta ta zubar da nikan tabi shi a guje Dan baa Mata ta kyalle Sai data tayiwa yaron lilis ta dawo ta d’auko buhun ta koma gida tace wa Sakeena massarar ya zub’e ta ajiye Mata buhun a gabanta ta nufi d’akinta kamar batayi komai ba Sakeena kasa magana tayi Tabita da kallo Sulaiman kuwa dake palon a zaune ya mik’e a zuciye ya bita a baya ya hau ball da ita sai daya Mata lilis ya fito daga d’akin Dan yana Jin Haushin taurin Kan hajara.

 

Yana fitowa daga d’akin itama ta fito a guje tayi waje Tana ranstuwa da sai ta rama.

 

Abu kamar Wasa har Sha biyun dare Hajara Bata dawo gidan ba anan hankalinsu ya tashi suka hau nemanta

 

Hajara kuwa Tana fita daga gida ta nausa cikin daji ta samu wani katon bishiya tayi zamanta a wajen Tana ta kuka alwashi kawai take akan sai ta Rama dukan da yayanta sulaiman yayi Mata har dare ya farayi Bata motsa daga wajen ba mugayen abubuwa kawai take ayyanawa a ranta tsabar rufewar da idonta yayi da San d’aukar fansa akan yayanta Bata San dare ya Yi ba wajen karfe Sha biyun dare ta fara Jin wani irin busa da tafiyar mutane sun kunna acibalbal sun Dodora Akansu sunyi layi suna ta tafiya sunyi daurin kirji da jajjayen yadi da tukunyar kasa a hannunsu dukansu Mata ne sunfi su Ashirin.

 

 

Hajara kuwa Ido ta zuba musu ko kadan Bata tsorata da ganinsu ba

 

Su kuwa mamakin ganin yarinya a gindin bishiya yasa shugabarsu tayi musu magana da idan sunje wajen bishiyar su tsaya haka kuwa akayi suna Isa wajen da Hajara take zaune suka zagayeta suna kallonta.

 

Zubinsu bai saka ta tsoro ta ba illa mik’ewa ma da tayi ta kakk’ab’e rigarta ta fara k’ok’arin matsar da d’aya daga cikinsu tayi wucewarta.

 

Shugabarsu kuwa dariya ta kyalkyale dashi ta jawo Hajara Tsakiyar su da karfinta ta wancakalar da ita Tana tambayarta wacece ita.

 

Tsaki Hajara tayi ta Kara mik’ewa ta zabgawa shugabarsu harara Tana “Ina ruwanki Dani”?

 

Mudubi shugabarsu ta ciro daga tukunyar kasar ta zuba masa Ido bayan yan sakanni ta dago ta kalli Hajara Tana “Kinaso ki dau fansa akan yayanki daya dakeki Sabida kin zubar da Massara”?

 

Da Sauri Hajara ta gyada kanta ta matsa kusa da ita Tana “Inaso na dau fansa inaso nima na zaneshi kamar yanda ya zaneni”

 

Dariya shugabarsu ta kwashe dashi tana “matso Nan kigani wanan shine”?

 

 

Jiki na rawa Hajara ta matsa kusa da ita ta lek’a mudubin Tana lek’awa taga yayanta a tsaye da mahaifinsu a k’ofar gida suna ta dube dube almar dai ita suke nema.

 

Da Sauri tace mata “eee shine yayan nawa”

 

“Ungo Nan Rama dukan da yayi Miki”

 

Hajara da Sauri ta karbi bulalan da shugabarsu ta mik’o Mata ta daddage da iya karfinta ta fara laftawa mudubin Sulaiman dake tsaye da Mallam Kabir kuwa ya hau zunduma ihu Yana burgima a kasa.

 

Sai da bulalan duk ya karye Hajara ta jefar da bulalan Tana Jin wani irin farinciki na ratsata rungume matar tayi tana “Nagode Ina sanki”

 

Wani irin dariya shugabarsu ta kwashe dashi tana “Nima Ina sanki shiyasa nake so ki zama daya daga cikinmu sabida ki ringa taka duk Wanda ya taka ki karbi ki shanye”

 

Hajara da Sauri ta karbi kwaryar da ta mik’a Mata da Bata San ko menene a ciki ba ta kafa Kai ta shanye tas ta mik’a Mata tana “Yanzu kina nufin duk Wanda ya tab’ani zan iya dukansa ta irin mudubin nan”?

 

 

“Sosai ma kuwa cire kayanki ki tsaya a tsakiyar mu ”

 

 

Da Sauri Hajara ta hau cire Kayanta cikin murna

 

suka hau zagayeta suna Mata wani irin hayaki bayan sun saka Mata Jan yadi a jikinta

 

A takaice a ranar Hajara sai karfe biyu ta koma gida fuskar ta a had’e

 

Gidansu kuwa Sakeena da Mallam Kabir hankalinsu a balain tashe yake da suka ga Sulaiman na birgima jikinsa ya tatashi lokaci guda tuni Mallam Kabir ya hau totofa Masa adduoi Yana tunanin ko Aljannu ne suka shige shi.

 

A lokacin da Hajara ta dawo kasa Mata magana sukayi gabadaya suka ringa binta da Ido Sabida yanda suka ga ta canza kamar ba ita ba Sakeena kuwa tsigar jikinta har wani tashi ya ringayi idan suka had’a ido.

 

 

A takaice tundaga lokacin Hajara ta fara wasu irin Abubuwa daya dasawa Iyayenta tsoranta Sulaiman kuwa tunda ta zaneshi bai Kara samun cikakken lafiya ba .

 

Duk dare mahaifiyarta idan ta shiga d’akin Hajara haka zata ga tayi d’aura kirji da Jan yadi Wanda hakan ke haddasa Mata tsoron Hajara sai ta fito daga d’akin da Sauri.

 

 

Ahaka ta tari Mallam kabiru da zancen Hajara Akan kila ba ita kadai bace Hajara nada Aljannu.

 

Tuni Mallam Kabir ya gasgata zarginsa akanta Inda ya bazama Nemo Mata magani a wajen mallaman addini Idan ya kawo Mata a gabansa zata zubar dashi bai Isa yyi magana ba hakane yasa ya shiga matsanacin damuwa ya fara tunanin hanyar da zai bi Dan ya raba Hajara da Aljannun dake jikinta a cikin irin wanan yanayin yaji labarin rasuwar Matar Mallam Ibrahim da yake ta San zuwa wajensa akan Maganar Hajara.

 

Da Wanan damar daya samu yazo bayan anyi Sadakar Bakwai ya samu Mallam Ibrahim da zancen Hajara da Abubuwan da takeyi dake nuni tana da Aljannu Inda ya roki ya taimaka masa ya rabata dasu.

 

Mallam Ibrahim kuwa ce Masa yayi yaje ya taho da ita zai rabata dasu insha Allahu.

 

 

Hakan kuwa akayi bayan sati daya da komawarsa Calaba ya zo da Hajara wajen Mallam.

 

Mallam Ibrahim da karfinsa ya dagewa Hajara da addu’a da manyan ayoyi Al Qurani Wai Nan duk so yake ya raba Hajara da Aljannun jikinta Nan kuwa bai San Shugabarsu d’auketa takeyi idan an fara rukiyyar ahaka yayi mata rubutun kwana bakwai

 

Washegarin da suka cika sati yacewa Mallam Ibrahim zasu iya tafiya Yana kyautata zaton insha Allahu Hajara ta rabu da Aljannun.

 

 

Mallam Ibrahim kuwa gefe yaja Mallam Ibrahim cikin sunkuyar da Kai ya nemi alfarmar da ya auri Hajara Dan a ganinsa in Yana tare da ita sai tafi samun lafiya.

 

 

Mallam Ibrahim kuwa bai k’i tayin da Mallam Kabir yayi Masa ba a cikin Sati d’aya aka daura auren Hajara da Mallam Ibrahim washegarin da aka daura auren Mallam Kabir ya dauki hanyar Calaba cikin tsananin farinciki Yana tunanin auren mallam Ibrahim da Hajara shine zai saka Hajara ta samu lafiya.

 

Hajara ko kadan Bata damu ba a lokacin da mahaifinta ya Gaya Mata ya aura Mata Mallam Ibrahim da zai iya jika da ita Dan tasan akwai abinda ta taka.

 

Shi kuwa Mallam ibrahim ganin yarinya sabuwar jini yasa ya Dan fara rawar kafar zai angonce da yarinya lafiya Lau yayi mata kwana bakwai dinta cikin doki a ranar da zai bar d’akinta a ranar ya fara dasa zargi Akan hajaran tunda tazo gidan bai tab’a ganin ta kalli gabas ba gashi indai zasu kwanta sai ta daura Jan yadi.

 

 

Kuma idan dai zaiyi adduar Daren daya Saba tashi take ta bar d’akin ta koma waje har sai ya Gama

 

 

Hakane yasa washegari ya shirya zama a d’akin Dan ya gasgata zargin da yake Mata na ko da sauran Jinnu a jikinta.

 

A ranar bai fita Waje karatu ba wajen karfe Takwas na safe ya kalli Hajaran da ke ta sharar bacci Sabida bata baccin dare.

 

Ido ya zuba mata Yana ganin yanda ta rambada kwalli a goshinta da idonta.

 

Matsalar Karfe Hud’u yake fita massallaci da asuba sai karfe shidda na safe yake dawowa gida hakane yasa baya sani ko tayi sallar Asuba ko batayi ba Azahar da sauran salllolin kuwa Yana k’ofar gida da dalibai da suke d’aukar karatu hakane yasa baya sanin tana sallah ko batayi.

 

Hannu ya Kai ya fara bubbuga pillon data Dora kanta akai.

 

Hajara ta bud’e idonta da suka kad’a sukayi ja Dan meeting suke a cikin baccin da take Mallam Ibrahim ya tasheta.

 

Mallam Ibrahim da Sauri ya k’au da kansa a lokacin da suka had’a ido da ita.

 

Hajara kuwa tace Masa “Mallam lafiya baka fita karatu ba yau”?

 

“Kinyi Sallah Asuba kuwa?

 

Cikin mamaki Hajara ta Masa wani irin kallo tana “Nayi Mana Mai yasa kake tambayata”?

 

 

Mallam Ibrahim baice komai ba ya tashi daga Kan gadon a zuciyarsa Yana zargin har yanzu Hajara Tana da Jinnu a jikinta Alwala ya dauro ya dawo d’akin ya shimfida Sallaya ya d’auko Al Qurani ya bud’e Yana gyaran murya Hajara ta duro daga Kan gado da Sauri tana “Mallam yau Kuma karatun a daki zakayi”?

 

 

Wani irin kallo ya Mata ita kuwa tayi waje da Sauri.

 

Mallam kuwa ya girgiza Kai Yana gasgata zarginsa ya fara karanta Suratul Baqarah.

 

Hajara k’in dawowa tayi d’akin ta fita zaure tayi Zamanta

 

Sallamar da ake tayi da Mallam Ibrahim ne yasa akan Dole ya fita bayan ya shiga d’akin Fatsima da suka koma zaman d’aki tunda aka d’aura auren Hajara da Mallam Ibrahim Dan sosai suke ganin wani Abu a tattare da ita indai suka had’a ido sai gabansu ya fad’i sosai sukejin tsoranta hakane yasa duk suke zama a daki abinda ke fito dasu kawai girki ne da alwala Mallam Ibrahim kuwa bai tab’a lura ba Dan shi ba zama yake ba.

 

Fatsima tsugunnawa tayi ta gaishe shi daya shigo shi kuwa yace Mata “aiki nake so kimin naso nayi aikin da kaina Amma Ana ta zuwa nemana Ido nakeso ki sawa yarinya Nan Hajara akwai zargin da nake akanta inaso kiga idan Tana sallah kinsan Ni ba zama nake ba ballantana nasan ko tanayi ko batayi har yanzu akwai wayanda ilimin addini bai je musu ba a zub’e kawai suke suna rayuwa”

 

Fatsima kamar zatayi magana Kuma ta fasa Dan a cikinsu ba Wanda ya tab’a sa Abu tak’i yi

 

Ko kallon Hajaran dake zaune a zauren baiyi ba ya fice Dan a yau zai rabata da bakaken Jinnun dake jikinta.

 

Hajara kuwa Yana fita ta nufi d’akin Fatsima kanta tsaye ta bankad’a labulen d’akin Fatsima dake kwance akan Gado ta tashi zaune gabanta na balain fad’uwa da ganin Hajara a d’akinta Dan Bata tab’a shigo Mata ba.

A haife dai ta haifi Hajara Dan zata iya cewa ma zata iya jika da ita.

 

 

Wani irin kallo Hajara ta Mata tana “Wato kece munafikar gidanan kece Zaki sakamin Ido kenan toh sai Naga da bakin da Zaki Gaya masa nayi Sallah ko banyi ba.

 

Daga nan Hajara ta juya ta bar d’akin.

 

Fatsima kuwa ta hau sallati Tana adduar duk daya da yazo bakinta.

 

Mallam Ibrahim bai shigo gidan ba sai karfe Tara na dare.

 

Yana shiga gidan d’akin Fatsima ya shiga da Sallama.

8/19/21, 10:30 PM – My Mtn Number: *NAGA TA KAINA*

 

*NA SADNAF*🌸🌸

 

 

®�? *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_{We Don’t just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_

 

 

 

*Free Novel*

 

 

*Page 3*

 

 

Fatsima da kanta ke balain ciwo tunda Hajara ta shigo Mata daki ta tashi zaune dak’yar.

 

Bata tab’a Jin tsoron mutum kamar yanda take Jin na Hajara ba ta tsorata da maganganun da Hajara tazo tayi mata dazun hakane yasa ko kad’an Bata samu nutsuwar saka Mata Ido ba

 

“Ina aikin Dana saka ki”

 

Fatsima murza hannu ta fara yi ta rasa ta Inda zata fara Masa bayani kamar ance ta dago ta kalli bakin kofa aikuwa ido biyu tayi da Hajara ta zubo Mata Ido”

 

Inda Fatsima kuwa ta daka tsalle ta tsaya tana Shirin magana bakinta ya karkace.

 

Sallati Mallam Ibrahim yayi ya ajiye jarkokin rubutun da ya shigo dasu yayi Kan Fatsima dake ta zabure zabure.

 

Sosai hankalin Mallam Ibrahim ya tashi a ranar yayi ta totofawa Fatsima adduoi Dan gani yake kamar itama gamo tayi abinda ya d’aukewa Mallam Ibrahim hankali daga Kan Hajara kenan.

 

A takaice tundaga ranar Hajara ta ringa hargitsa gidan cikin sirri batare da an ganota ba Dan dai kawai Kar Mallam Ibrahim ya samu nutsuwar tunkararta da Sunan rukiyya.

 

Nan kuwa Mallam ibrahim tuni ya gane Hajara ba Jinnu ke damunta ba ba dai San a wane matsayi zai ajiyeta ba Mayya ce ko matsafiya addua kawai yakewa kansa da sauran iyalinsa da duk sai da Hajara ta tab’asu.

 

Duk abinda yayi na addua Dan ya kawo karshen abinda Hajara yak’i tasiri akanta Dan yanzu Bata ma Abunta a boye a Sha biyu nayi zata zura jajjayen Kaya tayi ta abubuwanta

 

Zuwa lokacin an fara gane wacce Mallam Ibrahim ya aurowa kansa.

 

Waazi da nasiha ba Wanda Mallam baiyi wa Hajara ba Amma duk a banza.

 

Ana saura sati biyu tayi shekara a gidan ta haifo santalelen danta Mai Kama da Mallam Ibrahim sak.

 

Mallam Ibrahim na d’aga bakin kofa ta haihu Ana yanke masa cibi Yasa aka mik’o Masa shi ya kafa bakinsa a kunnen jariri ya masa huduba ya lullubeshi ya bar gidan da jaririn Dan ya Sha alwashin Hajara bazata ga kalar jaririn ba ballantana ta shayar dashi.

 

Tunda yaganta da ciki ya Samu wani amininsa Mallam Hassan dake Jos da sukayi makaranta tare ya zayyana Masa komai Dan har yafi Mallam Ibrahim din ilimi hakane yasa Mallam Hassan yace Masa tana haihuwa ya kawo masa jaririn.

 

 

Ruwan zam zam yayi ta bawa jaririn har suka Isa garin Jos Da isarsa Matar Mallam Hassan ta karbi jaririn tayi Masa wanka a cikin matan Mallam Hassan d’in akwai Mai shayarwa aka bata Jaririn ta shayar dashi.

 

 

A takaice Kwanan Mallam Ibrahim uku a Jos ya dawo bayan ya bar amanar Jaririn daya sawa suna Naseer a hannun amininsa da yake hazikin mallami ya Kuma ce Masa duk tsafin Hajara Bata isa ta gano Inda Naseer yake ba hankalinsa kwance a dawo gida.

 

Inda dawowar da yayi yazo ya tada tashin hankali Dan Hajara haukace musu tayi a gida Akan sai an fito Mata da jaririnta Inda tayi ta azabtar da matan gidan akan su fito Mata da jairirnta ko ta kashe su.

 

Ahaka ta rik’ewa Zinnira da kafa Fatsima kuwa har lokacin bakinta a karkace yake Aisha kuwa ta Mata turen Aljannu

 

Mallam na dawowa gidan taci kwalar rigarsa akan ya bata danta shi kuwa yace Mata ita da ganin danta sai dai a lahira domin dansa Jinin musulunci ke yawo a jikinsa.

 

A takaice sosai Hajara ta hargitsa gidan yan kungiyar ta suka ringa tayata

 

Sai da Mallam Ibrahim ya dage da Addu’a sosai a ranar da yaga abin yaci tura ya yanke igiyar auren dake tsakaninsu.

 

 

A takaice silar rabuwar Mallam da Hajara kenan.

 

Inda rabuwar ma da yayi da ita ya Kara haddasa wani tashin hankalin duka iyalinsa sai data sako su a gaba har Fatsima ta Kai ga rasa ranta.

 

Hajara sosai ta dage Masa akan idan Yana San ta bar rayuwarsa gabadaya ya bata danta Dan har yan kungiyar su sun kasa gano Inda Mallam ya boye Naseer.

 

 

Mallam Ibrahim kuwa tuni ya daina bacci ya dage da Addu’a da Saukar Qurani kafin ya d’an Samu Hajara ta rabu dashi duk da hakan Bata fasa zuwa tambayarsa danta ba.

 

Koda lokacin da suka rabu da Mallam ibrahim data koma Calaba ta tarar da Sulaiman ya rasu Mahaifiyarta ma haka Dan lokacin ba waya ballantana taji labari Bata wani damu ba Mahaifinta da Hassan da Husaini ne kawai sukayi bakin cikin mutuwar Aurenta tunda Mahaifiyarta ta rasu Mahaifinta bai cika lafiya sosai ba.

 

Ita kuwa Hajara baje kolinta kawai take cikin shekara Biyu manema sukayi Mata caaa dayake tana da kyanta ba laifi a wanan lokacin.

 

 

A cikin manemanta ta zabi wani Tijjani Cikin wata uku sukayi aure lokacin da matansa guda biyu.

 

Ko wata uku batayi a gidan ba tasa duk ya saki matansa ta ringa ganawa yayansa azaba Tijjani nagani babu yanda zaiyi Dan bashida bambanci da danta Sabida ta riga da ta Mallakeshi sai yanda tayi dashi.

 

 

A cikin shekara Shidda ta Haifa masa Yara Uku Danta na fari yaci Sunan Mahaifinsa Tijjani sai Mai bi masa Safiyya Sai Lami har a lokacin ita da yan kungiyarta suna iya kokarinsu wajen ganin sun gano Inda Mallam Ibrahim ya Kai Mata danta Amma Ina abin yaci tura sun kasa gano Inda Mallam din ya kaishi wanan kenan.

 

 

 

B’angaren Naseer kuwa sosai ya karantu ya ilimantu ya tarbiyyantu a hannun Mallam Hassan ya samu ilimin Arabic da Boko daidai gwargwado Mallam Ibrahim na zuwa ganinsa akai akai Dan duk cikin yayansa yafi Jin Naseer a Ransa ya Kuma fi tausaya Masa sabida halin mahaifiyarsa har Misra Mallam Ibrahim ya tura shi ya Karo karatu Sabida Yana so Naseer yayi ilimi Mai zurfi da zai iya na Kare kansa daga sharrin masu sharri duk cikin yayansa babu Mai balain hakurin Naseer ga k’ok’ari Yana da shekara Ashirin ya fara kasuwanci Dan ba laifi Naseer nada zafin nema cikin kankanin lokaci at Age of 23 ya zama successful bussines man duk abinda ya juya sai Allah ya saka Masa albarka.

 

Har a lokacin Yana wajen Mallam Hassan jefi jefi yake zuwa Modobi wajen mahaifinsa ya Sha tambayarsa game da mahaifiyarsa sai Mallam Ibrahim yace yayi hakuri ya bashi lokaci zai bashi labari wanan kenan.

 

 

Naeema

 

Mahaifinta Lawan yaren Ribina ne dake Kauyen Toro dake jihar Bauchi Shida matarsa Aminat Auren Zumunci akayi musu Mahaifin Naeema maharbi ne Kuma Yana had’awa da noma kyakyawa ne kamar Fulani gasu da gashi har gadon Baya Lawan karfaffan mutum ne Mai balain Zuciya ya tsani raini da wulakanci shiyasa bai fiye huld’a da kowa ba iyalinsa kawai ya sani sai mak’otansa matarsa Aminat Mahaifinta da mahaifinsa uwar su daya ubansu daya wuta ce ta Kama bukkarsu daddare sukayi gobara Inda iyayensu duk suka rasa ransu Lawan da Aminat ne kawai Allah ya tseratar hakane yasa awancan lokacin rukon Amina ya koma hannun Mai gari har ta Isa Aure ya aura Mata Lawan da tun mutuwar iyayensu yake Fadi tashi.

 

Tunda sukayi aure Amina inta samu ciki sai ya zub’e idan kuwa ta haifeshi sai yazo babu Rai ahaka sukayi shekara Goma da aure kafin Allah ya tsayar musu ta haifi Namiji da suka sawa suna Aliyu bayan shekara hud’u ta Kara haifar ‘ya mace Inda aka saka Mata Naeema.

 

Naeema kyakyawa ce sosai Dan tun tana jaririya take da balain farin jini Sabida kyanta rububin zuwa daukarta sai zata sha no-no ake dawo da ita da kuwa aka yaye ta idan makota suka d’auketa sai dare suke dawo da ita.

 

Daga Lawan Har Aminat din ba wani ilimi sukayi ba a wancan lokacin balle su saka yaransu masu karatu ma a wanan lokacin sai yan wajen gari haka.

 

Aliyu ba inda ya baro mahaifinsa a wajen k’arfi da Zuciya hakane yasa Mai unguwa ya shawarci Lawan ya saka Aliyu a makarantar Sojoji da Lawan k’i yayi dak’yar aka samu aka shawo kansa ya amince.

 

 

Few mutane lokacin suna Dan zuwa karatun allo a lokacin hakane yasa Aminat ta yiwa Lawan Magana ko zaa saka Naeema da take da shekara goma a lokacin bai k’i ba Naeema ta fara zuwa sai dai tana fara zuwa Samari sukayi ca akanta Dan Naeema nada tsayi sosai hakane yasa wasu suke ganin girmanta sosai ga kyaunta daya fita Dan tana da Dan girman jiki she so innocent and Calm Dan haka ma Mahaifiyarta take.

 

Ko wata uku batayi da fara zuwa makarantar ba Lawan ya cireta dayaga yanda maza ke bi masa ya har gida Inda tuni ya koma Yi Mata kulle.

 

 

Tana da shekara Sha uku Lawan ya fara barinta kula Samari a wancan lokacin Dan 13 ko 14 anyiwa yarinya aure a wancan lokacin idan Kika Kai 15 16 haka zaayi ta kanannun maganganu kin tsufa bakiyi aure ba.

 

 

One faithful day Naseer ya Kai kayan daya Saro garin Bauchi cikin kwana uku ya Gama abinda ya Kai shi a ranar da zai tafi wani abokinsa mustapha ya nemi ya raka shi kauyen dasu Naeema suke zai Kai Sako ahaka kaddarar Had’uwar Naeema da Naseer ya kasance.

 

 

Naseer dake Shirin barin garin Bauchi sai gashi ya fasa komawa a ranar Dan ba karamin kamuwa yayi da San Naeema da itama ruwa taje dib’a suka had’u dashi a hanya Bata wani kula shi ba Amma fuskarsa na Nan daram a kwakwalwarta.

 

 

Dayake ba wani fita take ba hakane yasa Naseer bai Kara samun ganinta ba da aka kwana biyu.

 

Lawan kuwa sosai ya damu da rashin ganin Aliyu da aka ce Masa Zai na zuwa ganin gida duk karshen wata hakane yasa yaje wajen Mai unguwa Akan yaji ko lafiya Dan shi ya had’asu da mutumin daya tafi da Aliyu a lokacin Mai Unguwa ya d’auko letter da aka kawo masa daga birni dayake ba dukansu ne sukayi Boko ba basu San Mai wasikar ya k’unsa ba sai da aka Nemo Wanda ya d’an iya karatun a wasikar ake bayanin baa ga Aliyu ba sun b’ata shi da wasu dalibai da sukaje.

 

 

Hankalin Lawan Dana Amina ba karamin tashi yayi ba sosai aka hau neman Aliyu cikin samu ganinsa ba addua kawai suke akan Allah ya bayyana musu shi rashin Aliyu yasa Amina ta Dan fara rashin lafiya a cikin irin wanan Halin Naseer yaje neman Auren Naeema da kansa a wajen Lawan Inda farkon ganin da Lawan yayiwa Naseer yaji Naseer din bai kwanta Masa kamar yanda wani abdullahi yafi kwanta Masa a maneman Naeema ba Dan har a zuciyarsa yafi San Abdullahi ahaka iya shi ya yarjewa Naeema take kulawa sabida yabawa da yayi da hankalinsa Dan Naeema nada manema da yawa daga Samari zuwa manyan masu kudin sai dai ya lura kamar Naeema tafi San Naseer Kuma baya San yayi Mata dole.

 

A takaice ahaka Mallam Hassan yazo ya nemawa Naseer auren Naeema bisa jagorancin Mallam Ibrahim daya sakarwa Mallam Hassan ragamar komai.

 

 

Cikin mutunci akayi komai bayan Lawan ya danyi bincike akan Naseer da a garin Jos yayi binciken nasa bai San suwaye asalin iyayen Naseer ba.

 

Naeema kuwa kawayenta sai tayata murna suke da samun miji kamar Naseer Dan Naseer San da yake yiwa Naeema baya b’uya.

 

Wata uku aka saka bikinsu.

 

Inda matan Mallam Hassan su suka Dan had’a Masa lefe aka Kai lokaci kawai ake jira.

 

 

Naseer kuwa tuni ya Gina katafaren gidansa a garin Jos.

 

B’angaren Hajara kuwa haikan ita da yan kungiyarta suke neman Inda Mallam Ibrahim yaje ya b’oye Naseer Dan har lokacin Hajara na zuwar wa Mallam Ibrahim akai akai akan a nuna Mata Inda danta yake.

 

A cikin irin wanan lokacin Ana saura wata daya auren Naseer da Naeema .

 

Naseer da Mallam Hassan suka tafi Modobi wajen Mallam ibrahim.

 

Dan shima Mallam Hassan akwai wani kanin mahaifinsa dake garin Modobin dayake San duba jikinsa.

 

 

Suna zuwa aka musu tarb’a Mai kyau Mallam Ibrahim sai murmushi yake Yana bin Naseer da kallo a Ransa Yana tunanin a yau zai Dan bashi labarin Mahaifiyarsa Amma bazai Gaya Mata wacece ita ba.

 

Zai dai bashi wasu adduoi ya ringayi na kariya daga sharri duk da Yana tunanin duk hatsabi bancin uwa bazata tab’a danta ba.

 

Wajen karfe hud’u suna zaune gabadayansu a k’ofar gida har da yayyen Naseer da ke zuwa wajen mahaifinsu haka da yamma duk da ba uwa d’aya ce ta haifesu ba suna da balain had’in kai.

 

 

Cikinsu kuwa har da Mallam Hassan

 

Kamar wacce aka jefota haka suka ga Hajara a gabansu.

 

Dan shugabarsu ce tagano Naseer ta mudubi shi da Mallam Hassan hakane yasa tayi saurin gayawa Hajara shine ta bayyana gabansu afujajan.

 

 

Mallam Ibrahim Sallati ya saki a lokacin da ya ganta ya hau addua a Ransa.

 

Mallam Hassan shima Yana ganinta yasan itace duk da bai taba ganinta ba.

 

Hajara kuwa Naseer kawai ta zubawa Ido tana kallonsa tamkar yanda yake kallonta yanajin wani iri a jikinsa

 

Hajara kuwa da Sauri ta dauke idonta daga kansa data ga katon tabon Sallah Goshin Naseer nata shigar Mata Ido haka kawai taga kamar kallonsa na neman haddasa Mata ciwon Kai.

 

Ranar wanka ba a boye cibi inji Mallam ibrahim “wanan itace mahaifiyarka Naseeer”

 

Naseer mik’ewa yayi da Sauri ya Isa gabanta ya tsugunna har kasa ya fara gaisheta Hajara kuwa kamar ta Kama da wuta sabida tsananin bakincikin ilimin addinin data ga ya ratsa Mata d’a Dan har ga Allah hakan na iya zame Mata barazana.

 

A takaice a ranar Hajara ta kebbe da Naseer tana Masa masifa bai tab’a nemanta ba hakuri kawai yake Bata Yana shima bai San dalilin daya sa Mahaifinsa yak’i Basa labari game da ita share maganar tayi ya hau Masa fadan da yanzu basu had’u ba sai dai yayi aure batare da sanin ta ba.

 

Anan mmaki ya rufe Naseer Dan yasan bai mata zance aurensa ba Kuma tunda tazo bai ga ta kebb’e da wani ba ballantana yace anan taji labari.

 

 

Hakuri kawai ya bata

 

Ita kuwa tayi murmushi tana “Ai matar da zaka aura kyakyawa ce ba laifinsa”

 

Kara dagowa yayi cikin mamaki Yana “Kinsanta ne”?

 

“Sosai ma nasanta dazu duk naji labarinta da zuwanka gurin mahaifinka Kai yanzu dai kafisan mahaifinka akaina ko shiyasa baka tab’a nemana ba Dan haka yanzu gobe zanzo na d’aukeka muje gidana ka Kuma ga ‘yan uwanka”

 

 

“Murmushi Naseer yayi Bai ce komai ba Yana Dan Jin wani iri a jikinsa kasancewarsu waje daya data zo tafiya kuwa sai data bi Mallam Hassan da wani irin kallo tayi kwafa tayi tafiyarta.

 

Bayan sallar isha Mallam Ibrahim ya d’an fara yiwa Naseer hannunka Mai sand’a da Naseer ya bashi labarin Hajara zata zo gobe su tafi yaga gidan da take zaune.

 

“Naseer ka dage da Addu’a mahaifiyarka Tana cikin kungiyoyi da yawa nima bansan wacece ita ba sai Dana aureta zama Bai Kama ka ba Dan kaima baka wuce ta sako ka a gaba ba Dan su ba basu San Allah bama balle suji tsoron sa a zuciyarsu basu San Mai tausayi ba ballantana suyi Imani”

 

 

Watarana zaka ganewa idonka watarana zaka San wacece mahaifiyarka tun sanin Dana Mata Bata baccin dare bansan a wane matsayi zan sakata ba Mayya ce ko matsafiya Allah kadai ya barwa kansa sani Allah kadai ke kareni sanin wacece ita yasa na dauke ka tun kana jariri na kaiwa aminina Sabida ya kularmin da Kai Ina tausayinka Naseer a cikin yarana kafi kowa hakuri Kaine Kuma bakayi dacen uwa ba tun a yanzu ka dage da Addu’a Naseer.

 

 

A takaice ire iren kalmomin Nan ya koma Yiwa Naseer da Naseer ya haddace Gam a kansa Amma a akaran kansa ji yayi ya kasa gasgasta zancen mahaifiinsa a wajensa mayyu apperance dinsu daban yake Dana mutane Amma zai dage da Addu’a kamar yanda mahaifiyansa ya bashi shawara….

 

 

Share

 

dis page is fiction gaskiya Dan wacce ta bada labari Bata San ya mahaifiyarsa ta zama matsafiyya ko Mayya ba but tunda novel ne hakane yasa zamu Nemo yanda ta zama mayyar

 

 

Next page zamu tsunduma cikin labarin gdan gadan insha Allah ur comments give me strength d more u comment d more na samu kwarin gwiwa tnk u

8/19/21, 10:30 PM – My Mtn Number

 

 

 

 

 

 

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment