Littafan Hausa Novels

Nafi Karfin Talaka Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Nafi Karfin Talaka Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

NAFI K’ARFIN

_TALAKA_

 

 

*NA*

*ZEE MD*

 

 

 

*Bisimillahir Rahamanir Rahim*

 

 

_Dasunan Allah me Rahama me jin k’ai , tsira da Aminci su tabbata ga shugaban Halitta Annabi Muhammad s.a.w

 

*Wannan littafin k’irk’irarre ne banyishi dan rayuwar wata ko wani ba ,*

_duk Wanda yayi dai dai da rayuwar sa to anyi arashi ne aka hakan_

Wata Hanya Hausa Novel Complete

*Ban yadda wani ko wata ya juyamin littafina ta kowacce siga ba , duk Wanda nasamu dayin hakan to tabbas zamu fuskanci matsala dashi*

 

_Sai Akiyaye

 

 

 

 

*Chapter* 1

 

 

Wurgo Masa mukullin motar tayi tana duban sa Cike da Isa da tak’ama tace ” inason ka wanke min motar ta zanfita da ita Nan da minty 10 , cike da girmamawa Shitu ya d’auki mukullin motar yace ” angama ranki shi dad’e ko kallon sa Bata sake Yi ba takoma cikin gidan ……

 

Wani had’adden palor Naga ta shiga Wanda yagama tsaruwa da kayan zamani , wata Hamshak’iyar Mata nagani zaune a cikin d’aya daga luntsuma luntsumar kujerun palor , tana shigowa Matar Nan Naga ta kalleta kafin tace ” Noor in kin hau sama kituromin Husna , wacce aka Kira da Noor ta tsaya cak batare da ta juyo ba tace ” Mum kinsan bana k’ask’antar da kaina a ko’ina Kiran Husna kuwa tamkar k’ask’antar da Kai ne , tana gama cewa haka ta haye sama batare da tasake magana ba ,……

 

Hajiya Lubabatu wacce itace Mahaifiyar Noor binta tayi da kallo , tabbas tasan halayyar Noor da izzar ta da jin kanta ba a wajen kowa ta gajeshi ba sai wajen Mahaifinta , inda sabo ta Saba da halin Noor kawai wani lokacin takan manta wacece Noor da kuma munanan Halayen ta……

 

Noor na shiga cikin d’akinta Wanda yagaji da had’uwa komai na cikin d’akin kalar Milk ne , toilet ta fad’a da sauri ta sakarwa kanta ruwa tafara wanka ,…

Bayan minty 5 ta fito Nan ta bud’e durowar kayanta aikuwa Ni kaina sai Dana ja da baya ganin irin tsadaddun kayan dake cikin durowar tata , wasu kayan ma kana kallo kasan Bata tab’a saka su ajikinta ba kawai dai an d’inka an ajiye sune ko Dan wata rana , wata atamfa ta d’auko tsadaddiya wacce akayiwa d’inkin Riga da siket sakawa tayi siket d’in tamkar zai yage saboda tsabar kamata da yayi , ko mayafi Bata saka ba kawai ta d’auki jakarta da takalmi me tsinin gaske ta fice , tunda ta taho kawai k’arar takunta ke tashi harta sakko k’asa ta nufo wajen da Hajiya Lubabatu ke zaune da Husna , tana zuwa ta zame glass d’in idanun ta tace ” Mum Ni zan fita sai zuwa jimawa , tana gama fad’in haka tasa Kai ta fice tana wani irin taku ga wani fitinannen k’amshi dake tashi a jikinta , binta sukayi da kallo daga Hajiyar har Husna kafin kowannen su ya girgiza Kai tare dayi Mata addu’ar shiriya…….

 

Noor na fitowa tuni Driver yagama wanke Mata motar ya goge , Yana ganin fitowar ta da sauri ya k’araso ya durk’usa har k’asa Yana Bata mukullin motar , a wulak’ance ta ansa tayi tsaki sannan ta nufi wajen motar sai data Gama k’are Mata kallo sannan ta bud’e ta Shiga ta kunna , sai data Fara saka kid’a sannan ta tashi motar tuni Megadi ya bud’e k’ofar gate gudun samun Matsala……

 

 

Yaya Umar yaufa a makaranta da k’yar aka barni na zauna da anan jarrabawa , Umar ya d’ago Yana duban k’anwar tasa sannan yace ” nasan akan baki biya kud’in Jarrabawar bane ko ? Ameera ta d’aga Masa Kai sannan tace ” wallahi Yaya Ni dama hak’ura nayi da zuwa makarantar Nan saboda a inah zamu samu d’ari bakwai akai , tunda dai inajin hausa Kuma na iya rubutu ai shikenan , Umar ya d’ago ya dubi k’anwar tasa cike da tausayawa yace ” insha Allah bazaki daina zuwa ba har sai kinyi candy , yanzu haka tashi zanyi zanje neman aikin ko gadine a gidajen masu kud’i tunda yanzu ko naje d’aukar dakon basamu nake ba , gashi yanzu tunda aka sace kayan wannan Alhajin yazo da ‘yan sanda akayimin wanann tozarci kwata kwata andaina kawomin wankin da guga , Innar su ce ta fito daga band’aki hannun ta d’auke da buta ta dubesu cike da tausayin yaran nata Wanda talauci yayi musu katutu duk sun fita daga hayyacin su , samun wajen tayi ta zauna sannan tace ” Babana da gaskiyar Ameera fa wannan karatun yakamata tabarshi haka tunda ansamu na rayuwar duniya , Murmushi Umar yayi sannan yace ” Inna saura shekara d’aya da rabi tagama fa Dan Allah kiyi Mana addu’a Allah ya bud’amin in biya Mata ta kammala , Inna tayi Murmushi tace ” ai dama inayi maka addu’a Babana Allah ya bud’a maka ya kawo abinyi Wanda zaka tallafemu dashi , dukan su suka amsa da Ameen kafin ya tashi yace musu Yana zuwa……..

 

 

Noor tana tafe tanajin kid’a da wak’a sai wata rawa take har sakin kan motar take saboda shauk’i , a haka ta k’araso wani had’adden wajen shopping , fitowa tayi ta nufi ciki tana wani taku d’ai d’ai tare da d’aukar Manyan mayuka da turaruka , duk kusurwar data shiga intaga mutane sai tayi tsaki sannan ta furta ” wannan wajen Shopping d’in a gaskiya bazan k’ara zuwa ba , Ashe *TALAKAWA* ma suna zuwa ? a haka ta gama shopping d’in ta biya kud’i tana fitowa ta watsar dasu a bakin hanya tashiga motar cike da Isa tana cewa bazan Yi amfani da kayan wajen da *TALAKAWA* suma suke amfani dasu ba ,………

*NAFI K’ARFIN*

_TALAKA_

 

 

 

*NA*

*ZEE MD*

 

 

 

*Bisimillahir Rahamanir Rahim*

 

 

 

 

 

*Chapter* 2

 

 

Wani katafaren Shopping mall ta nufa tana Shiga taga irin ta wato yaran masu kud’i masu ji da kansu , haka tabi sahu itama tafara zab’ar kayan datakeso cikin nuna isa da tak’ama , sai data gama sannan ta nufi wajen biyan kud’i , tana zuwa taga wani had’adden Saurayi Wanda yagaji da had’uwa ana duba kayan da yasiya , satar kallon sa ta shigayi har aka gama ya Basu 🏧 d’insa suka ciri kud’in su sannan ya nufi hanyar fita yaron wajen ya bisa a baya da kayan da yasiya ,….

 

Noor ganin wannan Saurayin yabar wajen batare da ko kallo ta ishe ba , mamakin isar sa da izzarsa tayi dan tana ganin harya kusa finta jin Kai , itace zatazo waje ace samari had’add’u suganta Basu yaba ba , tabbas wannan d’in shi nadaban ne Kuma tayi alk’awarin duk lokacin da suka sake had’uwa Dole zai karyar da ajinsa wajen Yi Mata magana….

 

 

Umar tunda ya fito daga cikin gida yashiga bulayin yadda za’ayi yasamo musu abinda zasu ci , Yana tafe duk abin duniya ya mishi yawa sai zancen zuci yake , a dai dai lokacin yaji mutane sun d’auki salati tare dajin k’arar birkin mota , waigawa yayi saikuwa yaga wani tsoho ne Ashe motar ta kusa bigesa , da sauri Umar ya k’arasa wajen suka taimakawa Tsohon suka d’agashi , Noor a fusace ta fito daga cikin motar ta nufo wajen da su Umar suke suna cewa tshon Nan ” sannu Baba bakaji ciwo ba ko ? Tsohon yace ” banji ciwon komai… tsayar da maganar yayi lokacin da yaji saukar Mari a kuncin sa , aikuwa dukan su a firgice suka dubi Noor wacce ta tsinkawa tsohon Mari ,…..

 

Cike da Isa da rashin mutunci Noor ta kalli tsohon tace ” tsabar kaid’in dabbane talaka Wanda baisan kansa ba shine zaka dunga shiga tsakiyar titi kana tafiya , wallahi Dana taka ka wlh nataka banza Babu abinda aka Isa ayimin , Bata gama rufe baki ba itama taji saukar wani gigitaccen Mari har guda biyu a kuncin ta , ganinta da jinta tuni suka d’auke na wucin gadi saboda Azaba , tunda tazo duniya ba’a tab’a dukanta kwatankwacin hakan ba sai yau , dafe kuncin nata tayi tana duban Umar Wanda yake fitar da huci tace ” Ni zaka d’aga hannu ka Mara ? Umar a fusace yace ” an mareki d’in banza sakarya dabba wacce batasan ciwon kanta ba , da alamu ma ke ba me tarbiya bace , dan duk me tarbiya bazata aikata wannan dabbancin naki ba , duk mutanen dake gurin Saida suka jinjinawa Umar duk da tawani gefen sunfara tunanin abinda hakan zai janyo Masa ,….

 

Noor rik’e da kuncin ta tayi gefe ta Kira Dpo ta sheda Masa yazo maza tana da case da wani , Umar hannun tsohon ya rik’e sukabar wajen yanata bashi hak’uri..

 

Koda ‘Yan sanda suka k’araso sunsamu Umar baya Nan , sai dai tuni aka nuna musu gidansu , harda Noor akaje wacce tuni ta shedawa Dad d’inta abinda yafaru , tuni Dad ya rud’e tare da cewa Dpo lallai akama Masa Umar a ajiye shi a cell bayan sunyi Masa dukan mutuwa , Inna ita da Ameera suna zaune suna hira sukajiyo hayaniya a k’ofar gida tare da sallama a cikin soro , Ameera tasa hijab d’in ta tana cewa Innah Bari Nagano suwaye , sai dai tana lek’owa tayi turus ganin ‘Yan sanda a tsaye , da sauri ta furta Subhanallah lafiya kuwa Malam wa kuke nema ? .

 

‘Dan sanda ya dakawa Ameera tsawa Yana fad’in ki koma ki shedawa Yayanki Umar yafito mutafi dashi ko kuma mu mushigo cikin gidan , Ameera da sauri ta koma cikin gida tana kuka tare da shedawa Innar su ‘Yan sanda ne sukazo tafiya da Yaya Umar , a zabure Inna ta nufo soro ko mayafi Babu tafara magana ” bawan Allah Dan Allah me yayi muku haka ? Wlh Umar ko sa’insa Basu tab’ayi da wani ba kuyimin Rai kushe damin abinda yayi karku tafi dashi , …..

 

Noor ta tako har gaban Inna ta kalleta sannan tace “Tsohuwa kenan ai kifarawa d’anki addu’ar cikawa da imani , tunda haryasa hannu ya mareni to tabbas zai fuskanci babbar wuk’uba a hannuna , juyowa tayi ta kalli Dpo tace ” tunda bayanan inaso ka Kama Uwarsa da ita k’anwar tasa kutafi dasu , inya kawo kansa sai kusake su su Kama gabansu ,..

 

Tana Gama fad’in haka ta nufi wajen motar ta sukuma ‘Yan sanda suka tusa k’eyar Inna da Ameera suka tafi dasu…..

 

Umar sai daya raka wannan tsohon har gidansa , aikuwa haka yayi ta Masa godiya tare dasa albarka harya taho gida…..

 

Sai daya biya wajen dasuke dako cikin ikon Allah yasamu d’ari biyu aikuwa tuni ya nufo gida cike da murna , sai dai Yana zuwa yaga gidan nasu wayam gashi Kuma a bud’e , tunda yake da Inna Bata tab’a fita batare da yasani ba kuma sai sun kulle gida , tuni ya fito ya nufi wani me kanti dayake kallo gidan nasu yashiga tambayar sa ko yasan inda suka tafi ,…

 

Nura me kanti ya kalli Umar sannan yace ” ai Malam Umar ka tab’owa kanka bala’i domin kuwa wannan budurwar daka Mara itace tasa ‘Yan sanda suka kwashe Inna da Ameera suka tafi dasu , a zabure Umar ya kalli Nura Yana fad’in ” wanne division ne ? Nura na fad’a Masa sunan Division d’in Umar ya kwasa da wani irin gudu ya nufa , …

 

Gudu yake iya k’arfin sa tare da ambaton sunan Innar sa Yana fad’in ” ki yafemin Inna nasa ansaki a k’unci batare da hak’k’in kiba…

 

 

Daga unguwar su zuwa Division d’in akwai nisa me yawa Amman tuni Umar ya isa wajen ,..

 

Yana zuwa yaga Inna a cikin Cell ita da Ameera sai kuka suke , gadan gadan ya nufi Cell d’in Yana fad’in ” gani nakawo kaina asakar min Mahaifiyata , Nan Dpo yasa aka rik’e Umar aka shigar dashi cikin Cell d’in sannan aka rufosu baki d’aya……..

 

 

 

 

*Comment and share plss*🤝✍🏻✍🏻

[14/12/2022, 10:24 pm] +234 706 487 0343: 💝 *NAFI K’ARFIN* 💝

_TALAKA_

 

 

 

*NA*

*ZEE MD*

 

 

 

 

*Bisimillahir Rahamanir Rahim*

 

 

 

 

 

*Chapter* 3

 

 

Ameera da Inna suka dubi Umar suna goge hawayen idanun su , shima kallon su yayi sannan yayi k’asa da idanun sa Yana furta kalmar ” Kuyi hak’uri na janyo muku Shiga cikin wannan wajen batare da kun aikata laifin komai ba , Inna ta katse shi da cewa ” meyasa kazo Babana da kasani bakazo ba mu kabarmu Anan d’in nasan Dole in suka ga bakazo ba zasu sake mu , Umar ya kalleta cike daso da k’auna irin ta d’a da Mahaifiya yace ” bazan tab’a barin ku anan ba Inna kinsan zuciyata bazata tab’a lamuntar hakan ba , Ameera ta dube sa cikin sanyin Murya tace ” Yaya Umar Wai me ka aikata da suka Yi Mana wannan cin mutuncin ? ..

 

Umar ya dubi k’anwar tashi sannan yace ” akan na Mari wata Yarinya saboda ta Mari wani bawan Allah Kuma dattijo , take Umar ya sheda Mahaifiyar sa da kuma k’anwar sa akan abinda yasa suka kawosu Cell , aikuwa Inna tace ” kamin dai dai Babana tabbas wannan yarinyar Bata da tarbiya Koda ganin yadda take , Amman Babu komai duniya ce Wanda bai zo ba ma jiran sa take…..

 

Noor Koda ta koma gida tana shiga palor tasamu Husna da Mummy su suna karatun kur’ani , tana kallon su so d’aya ta kawar da kanta batare da ta kula kowa ba ta haye sama d’akin ta , suma ba itace a gaban su ba dan haka tamkar Basu san ta shigo ba suma haka sukayi ,…..

 

Wanka tayi tasa wasu K’ananun Kaya sannan ta fito Dan yunwa takeji , tana zuwa kan Dinning taga abinci kala kala a jera sama tayi ta zuba da kanta tafara ci , tana ci tana chat cike da kwanciyar hankali , Kiran wayar tane ya shigo taga sunan Dpo ya bayyana , d’agawa tayi Dpo cike da girmamata yace ” ranki shi dad’e wannan yaron daya mareki fa yazo yanzu ya kawo kansa , Noor najin hakan take taji ranta ya b’aci wato yanzu harta shiga cikin sahun Wanda za’a dunga kwatan tawa da an Mara , tsawa ta dakawa Dpo d’in tana cewa ” karka sake cewa Wanda ya mareni ka canza akalar maganar , da sauri Dpo yace ” sorry ranki shi dad’e bazan sake ba , wani Huci tayi tare da furzar da wani hayak’i daga bakin ta tace ” inaso kuyi Masa dukan da zai kasa gane Wanda yake tare dashi zuwa da safe kafin nazo , Dpo yace “angama rank’i shi dad’e ta kashe wayar ta ajiye tana dafe kanta tare dajin tsantsar tsanar Umar wand ya kafa Mata tarihi a bayyanar nasi…..

 

 

Aikuwa haka akayi Dan tuni Dpo yasa aka Fara dukan Umar duka na fitar hayyaci , Inna da Ameera Banda kuka da bada hak’uri babu abinda suke , Umar kuwa duk irin dukan da ake Masa hankalin sa nakan Innar sa da k’anwar sa , duk irin azabar da suke Masa Amman in yakalli Inna da Ameera sai yayi musu Murmushi , haka sukayi Masa lilis sai daya daina motsi sannan suka k’yalesa suka fita , Ameera da Inna har rige rigen zuwa wajen sa suke suna jijjigasa tare da Kiran sunan sa , aikuwa shiru sukaji take kukansu ya tsananta sun d’auka ko ya mutu ne ,…

 

Tsawa Dpo ya daka musu sannan yace ” kuyi Mana shuru ko kuma nasa Kuma ayi muku yadda akayi Masa , shuru sukayi dan tabbas sunga alamar Dpo d’in bashida mutunci komai zai iya…..

 

 

*Washe gari*

 

Anan cikin cell d’in suka kwana dukan su bawanda ya runtsa , Dan dukan su kwana sukayi suna kuka , Umar kuwa ya farfad’o sai dai baya magana kawai sai dai kaga hawaye na zuba a idanun sa , Inna kuwa tagaji da kukan kawai addu’a take tare da kaiwa Allah kukan su , tasan duk saboda sun kasance Talakawa shiyasa akayi musu wannan cin zarafin , Amman Allah shine gatan su Kuma shine zai saka musu wannan tozarci da akayi musu…..

 

Noor sai shad’aya ta mik’e daga gadon ta shima Kuma badan tasoba sai Dan tashin da Mum tayi Mata , toilet ta fad’a ta goge bakinta sannan ta fito , duban ta Hajiya Lubabatu tayi sannan tace ” Noor kinyi sallar asuba kuwa ? Noor ta turo baki sannan tace bana Yanayin da zanyi sallah , shigowar Husna d’auke da sallama itace ta katse musu maganar tasu , Noor ta wurga Mata Harara tare da cewa ” bana hanaki shigomin cikin d’aki ba ? Husna ta kalli Noor sannan ta tab’e baki tace ” ai Nima bani da abinda zan d’auka a cikin d’akin naki saboda Mahaifiyata nashi go , Noor tayo kanta tana cewa ” Ni xakiyiwa rashin kunya ? Dasauri Hajiya Lubabatu ta mik’e tana Jan hannun Husna suka fice Don tasan yanzu zasu Fara fad’an nasu……

 

Sai wajen shabiyu Noor ta fito ta nufi division d’in da su Umar suke ,….

 

Sanye take da Riga da wando sun Kama jikinta haka ta shiga cikin division d’in , tana Shiga aka Fara girmamata tare da d’auko Mata kujera ta zauna , duban kowa take d’ai d’ai tana taunar cingum tasa aka fito Mata da Umar da Innar sa da kuma k’anwar tasa Ameera , a gabanta Dpo yasa suka durk’usa gwiwoyin su , duban sa Noor tayi tana wani murmushi tace ” shugaban marasa mutunci Wai harni Noor Shareef zaka d’aga hannu ka Mara ? Inna da sauri tace ” dan Allah Yarinya kiyi hak’uri ya marekine bisa kuskure bai San wacece ke ba , Noor ta dubeta a wulak’ance tace ” ai yanzu yasani bashi bama ke kanki Uwar tasa yanzu kinsan wacece Noor Shareef………

 

 

 

 

*Kuyi Hak’uri Yau na fita banyi typing dayawa ba*

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment