Hausa Novels Complete Documents

Hausa Novels Complete Documents

 

 

 

 

 

 

 

ƘADDARATA CE A HAKA

  ©Maryam Abdul’aziz.

         MAI_ƘOSAI.

 

P__1

 

  Bisimillahir Rahmanir Raheem.

 

 

 Zaune take gefen kan lafiyayyan gadonta. Hannuwanta duka biyu shimfide bisa kan kyakkywan kuncinta. Kallonta a haka kaɗai ya isa ya gamsar da kai cewar lallai tana cikin matsananciyar damuwa. Hawaye ne suke gangarowa daga cikin kurmin idanuwanta zuwa kan dandamalin fuskarta.

   ” Me ya sa gwaggwo da Baffa za su yi mini haka?? Me ya sa suke son saka ni cikin Wani hali? Me ya sa ba za su bar ni na aure Wanda zuciyata ke da muradi ba? Su ne maganganun da ke reto a cikin zuciyarta. Kuma tabbas tasan lallai babu mai amsa mata waɗannan tambayoyin sai su. Hakan ya sakata miƙewa daga zaunen da take zuwa tsaye tare da saka kai ta fice daga d’akin.

   Gwaggwo na zaune kan kujerar tsugunno a tsakar gida,tana yankan farce, ta kalle ta tare da furta, 

   ” Gwaggwo don Allah ki daɗa yiwa Baffa bayani akan lamarin nan  nasan idan yaga kin daɗa dagewa akan batun zai duba lamarin nan nawa don Allah. Ni Wllh ban san me ya sa bakwa son aurena da yaya Nasir ba? Wai Gwaggo wani laifi ya aikata muku haka da ba za ku iya amsar shi ba? Me ya yi muku da ba zaku ƙauna ce shi ba?”

    Gwaggo ta dubeta a karka ce kafin takai ga cewa,

   ” Ai hakan da kika yi yana da kyau kizo ki tutsiye mahaifiyarki akan wani ƙaton gardi ko? Kema ai za ki iya zuwa ki sami shi gyatumin naki ki yi masa magana ,sai ya fi jin maganarki ma akan ni, sai dai ina so ki sani tunda muke bamu ta’ba ƙin wani d’an Adam ba, amma ki sani munsan mahimmancin *alƙawari*”

 Tana kaiwa nan ta mayar da magananta kan yankan farcen da take yi ba tare da ta ƙara ce mata komai ba.

 Ita kam ganin yadda Gwaggon ta harzuƙa ya saka ta miƙewa ta koma d’akinta , tabbas tasan da man Gwaggon na ta ba za ta ta’ba goya mata baya ba, amma ta bawa zuciyarta amanna da abin da take son aikata wa yanzu.

 Cikin sauri ta miƙe tare da faɗawa bayi shaf-shaf ta watsa ruwa ta fito, ko mai ba ta tsaya shafawa ba da yake garin ana zafi, kayanta ta sanya tare da zarar mayafinta ta fice.

     Har lokacin Gwaggo na zaune inda ta barta, kallonta ta yi kana ta ce ” Gwaggo ni zanje wajen Inna , ba dad’ewa zan yi ba”

    ” Ki yi sauri dai ki dawo, in kika jima har Baffanki ya rigaki dawowa to tabbas zance ban ma san kin fita ba. Kin ji ko?”

  Zun’buro baki ta yi kana ta ce ,  ” Kai Gwaggo! To ayi mini sassauci kada a ce haka”

   ” Oho miki ki tsaya kar ki tafi” Gwaggo ta fad’a.

    ” In banda ma kisa baiwar Allah surutu ni banga uwar abin da za ki je yi a can ba”

   ” Ni dai na tafi, sai na dawo “

  Ta fad’a tana mai ficewa daga gidan. 

” ki gaisheta ” gwaggon ta fad’a tana d’an daga sauti yadda za ta jiyota.

 

**********

    Tafiya take yi sannu a hankali duk da wani sashe na zuciyarta a cunkushe yake da abin da iyayen nata suke son yi mata amma hakan bai sakata kasa tunawa da mafi soyuwar abincin ruhinta ba.

      ” My one”

Kamar daga sama haka ta jiyo sautin zazzaƙar muryarsa wacca ba za ta ta’ba manta mai ita ba balle ita kanta muryar. Caak ta tsaya tare da juyowa ta fuskance shi cike da murna da annushuwar ganinsa da ta yi ,dan sosai ta yi matuƙar kewarsa.

  Ya d’an matso kaɗan kusa da ita har suna masu shaƙar numfashin junansu kafin ya kai ga cewa, ” Hankalina ya gaza kwanciya musamman yanzu da naga duk kinyi wani iri My, naga fuskarki kamar kinyi kuka me aka yi miki? Me yake faruwa dake?”

 Kallon shi ta yi tare da son daidaita nutsuwarta, kana ta ce da shi,

   “Kai yaya Nasir waya ce ma na yi kuka? Ni ba abin da ke damuna babu komai”

    Ƙara kallonta ya yi na wasu ‘yan sakanni kana ya ce, 

  ” Gaskiya ban yarda ba, tabbas akwai abin da gimbiyar tawa ke son boye mini ko ma take kan ganiyar ɓoye min , ma za fad’a mini ko sai na yi miki kuka?” 

Ya karashe yana mai langwabar da kai.

   Sanin halinsa wanda indai ba fad’a masa ta yi ba bazai ta’ba barinta ta wuce ba ya sanyata rausayar da kai kana ta ce, 

   ” Ya zan yi yaya Nasir? Tabbas ina cikin damuwa ba kaɗan ba , sanin kan kane idan na rasaka bazan iya rayuwa ni kad’ai ba. Ina sonka yaya Nasir son da bana yiwa kaina shi, sai dai har yanzu Baffa da gwaggo sunƙi amince wa da kai amatsayin wanda zuciya da gangar jiki ke muradin kasancewa tare da shi, ta yaya hankali na zai kwanta? kasan abin da ba zai ta’ba yiwu wa ba ne yaya Nasir”

  Ta karashe tana mai share kwallar da ta gangaro mata zuwa kan kundugugin kuncinta.

    Nasir ya kalleta cike da boyayyen tashin hankalin da ya sake yi masa ƙawanya yanzu,  tabbas suna son junansu sosai iya matuƙa gaya, shi kansa ba zai ta’ba san cewa ace yau basa tare da junansu ba in har dai ba mutuwa ce ta riski ɗayan su ba, sai dai yaya zai yi? yardar iyaye ita ce yardar komai cikin rayuwarsu.

  Cikin tattausar murya ya ce ” Na sani my one, na san muna son juna sosai, sai dai ba yadda muka iya har sai iyayen mu sun yarda da maganar mu, har sai sun amince mana sannan zamu iya zama abu d’aya, amma insha Allahu muna tare da juna zasu amince mana babu kuma wanda zai rabamu”

   “Shi kenan yaya Nasir na ji amma wallahi muddin Baffa da gwaggo suka ƙi amincewa to na rantse zasu sami gawata a koyaushe kuma a kowanne irin lokaci”

    Cikin sauri Nasir ya tare da fadin, ” Haba my one , karki kuma fad’ar haka, Ni na san abin da su Baffa suke yi me kyau ne akan mu, dan haka mu jiraye hukuncinsu, amma kada mu yankewa kanmu danyen hukuncin da ƙarshensa ba zai yi mana kyau ba.

 A hasale ta kalle shi tare da mayar masa da raddin…

 

Yawan comment, yawan typing. Ba Hannun banza gareni ba ehh.

 

Mai Ƙosai.