Littafan Hausa Novels

Mutuncina Hausa Novel Complete

Soyayya Da Karamar Yarinya
Written by Hausa_Novels

Mutuncina Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

*MUTUNCINA

 

 

Na

Jiddah S Mapi

 

*Chapter 1*

 

 

~Amma da yarki ce bazaki aiketa a daidai wannan lokacin ba! Ki duba yadda hadari ya mamaye garinnan, iska yana kad’awa ko ta Ina, ruwa me karfi ze iya saukowa a kowani lokaci, Kuma kinsan dare yayi domin an idar da sallan Isha da jimawa, da ‘yar cikinki ce zaki aiketa a wannan lokacin?

Wani mutum nagani Wanda ya haura shekara 50 Yana tsaye acikin wata Yar karamar gida Yana yiwa matar datake tsaye daga gefe tana tab’e baki, tareda gunguni alamar abinda yake fad’a Mata baya shiga kanta ko kad’an,

Fakiri Hausa Novel Complete

Cikin yanayin tausayi yace “Dani kika aika dayafimin kwanciyar hankali akan ki aiketa a wannan lokacin, ko ba komai ita ‘ya mace ce, Kuma kowace mace Allah yabata daraja, mace tanada Rauni Amma ba kowane yake ganewa ba, kowace mace anaso arink’a kula da ita daga farkon rayuwarta har zuwa Tsufanta, meyasa kikeso ki wulakanta wannan baiwar Allahr?”

 

Matar dayake yiwa magana naga ta juyo tana hararanshi tace “Haba Malam wai meyasa babu dama a aiki wannan yarinyar? Itafa macece idan Bata koya yanzu ba Sai yaushe kakeso ta koya…?”

Kafin takarasa maganar ruwa ya sauko me karfin gaske, da Dan gudu tashige d’aki tana cewa “kaga tsabar surutunka so kake ruwa ya jikani yasani ciwon Kai”

Ranshi a b’ace Shima yashiga Dan madaidaicin d’akin yace “kiduba yadda kike tsoron ruwa ya jikaki Amma ita kin aiketa”

 

Tsaki taja tahau gado taja bargo sannan ta lulluba jikinta,

Kasa zama yayi sabida hankalinshi gaba daya atashe yake, bayason abinda ze tab’a mutuncin ‘yarshi,

Ranshi ab’ace yake sosai Amma bashida Daman yin magana.

 

~sauri take sosai sabida ruwan da aka fara me karfi, ganin saurin baze yuwuba yasa ta d’auko bread din data siyo tasa a hijabinta Wanda yake da tsayi, sannan ta d’angale Skirt d’in jikinta tafara gudu, mutane kowa Yana neman mafaka, ita Kuma gudu take kamar bazata tsaya ba, tasan idan ta tsaya unguwarsu Yana da nisa da inda taje siyo bredin, daidai wani kwana tayi tuntunb’e da wani katon dutse, ihu tayi sosai sannan ta Fadi kasa, gwiwanta ya bugu da dutsen take jini yafara zuba, zama tayi a wurin tana rike kafarta tana kuka, hijabin jikinta ta cire sannan ta yaga karkashin ta d’aure gwiwan dashi, kafin tamike tafara d’ingishi tana kuka, bread din ya lotse yazama karami, tana d’ingishi har takusa zuwa gida, akayi wani tsawa Wanda yasa ta firgice tafita a hayyacinta, batason tsawa ko, iska Kara karuwa yake, gaba d’aya idonta yacika da kura, ganin hanya ma yafara b’ace Mata yasa ta tsaya a daidai lungun datake, mannuwa tayi da jikin bango, hawaye yafara bin kuncinta, a daidai lokacin naga kyaun fuskarta, fara ce sosai, da idanunta manya manya, bakinta d’an karami sai hancinta dayake da tsayi, tanada tsayi sosai Kuma ba siririya bace sosai, tanada d’an kib’a kad’an, a takaice dai ita tsaka tsakiya ce, gashin kanta yanada tsayi Wanda har goshinta Yana dauke da wani kwantaccen gashi, tsayawa na kwatanta yadda take b’ata lokaci ne, hawayen dayake sauka a fuskarta tasa hannu ta goge, sanyi tafara ji sosai har hakoranta suna haduwa da juna, a zuciyatarta tafara magana kamar haka “da uwata tana raye nasan bazan fuskanci hakan ba a matsayina na ‘ya mace, Amma duk da haka zan kare MUTUNCINA, wulakanci da tsangwama bazesa na zubar da MUTUNCINA na ‘ya mace ba”

A hankali tafara silalewa zuwa kasa tana kuka sosai, tana kewar mahaifiyarta,

Hasken motane ya hasko idonta, a hankali tasa hannu tarufe fuskarta domin ya kashe Mata ido,

 

~gudu yake a motar batareda yasan inda zeje ba, gaba d’aya a buge yake yau yashawu dayawa, ganin ya hasko wata kyakkyawar yarinya a lungu yasa yayi parking a wurin, lekawa yayi Yana murza idonshi, gani yake kamar shawuwan dayayi ne yasa yake ganin Abu haka, ganin kamar da gaske mutunce yasa ya bud’e marfin motar ya fito yafara tafiya Yana layi, karasowa wurinta yayi Yana kallonta, d’ago idonta tayi ta kalleshi sannan ta Mike a tsorace, hanyan gudu tanema, ya cafko hannunta, cizo ta danka mishi Amma ko a jikinshi, janyota yayi jikinshi taji warin giya ya bugata, tureshi tafara tana bugunshi tana ihu, babu Wanda ze jiyota sabida Ana tsaka da ruwan sama, hijabin jikinta ya karasa yagewa sannan yasa hannunshi cikin riganta, ihu takuma kurmawa tana bugunshi da iya karfinta, ganin haka yasa yafara janta zuwa motarshi, turjewa tayi sosai, ganin haka yasa yafara yayyaga rigan jikinta, taki Bari ya rabata da komai, idonshi a rufe yafara, Mata magana irinta Yan kwaya, yace “ke ki nutsu dalla biyanki zanyi kifad’i ko nawa kikeso”

Tureshi tayi tana ihu, rufe bakinta yayi da karfi, ya kwantar da ita akasa cikin ruwa da cab’i, da karfinshi ya kwance belt d’in wandon jikinshi, ganin Bata daina ihuba yasa, ya watsa Mata belt d’in sannan, ya kulle ido yafara raping d’inta cikin tab’o da ruwa, ga iska ga duhu, tin tana ihu tana hawaye har hawayen ya kafe daga idonta, shiru kawai tayi tana kallon sama.

 

“Malam ya kamata ka kwanta fa, ba yau muka fara aikanta ba, Amma duk kabi ka d’aga hankalinka akan wannan ruwan, dama yau muka fara aikanta cikin ruwan sama?”

Baba gaba d’aya hankalinshi yakasa kwanciya besan meyasa ba yau ji yake zuciyarshi tafi b’aci da aikan da ake yimata akan kowace Rana, haka kawai yakasa nutsuwa, Zama yayi abakin kofar yayi tagumi, jiyake kamar yafita ya dubata, saude ruwan yayi yawa ga karfi, hannu yad’aga zuwa sama yafara addu’a Yana rokan Allah ubangiji daya kare mishi ‘ya’yanshi a duk inda suke”

Yasani gara d’a namiji akan mace, mace lalacewar rayuwarta yanada sauki, Addu’a yayi sosai, saide har yanzu hankalinshi yakasa kwanciya.

 

 

“Kayi hakuri” shine abinda yake fita daga bakinta wanda, be kyaleta ba Saida bukatarshi tabiya, sauka yayi daga jikinta, saide wannan lokacin jikinshi a mace, dukda Yana cikin maye Amma yaji tausayinta, wandonshi yasa sannan yamike a wurin cikin maye ya d’agata sannan yasa Mata rigan daya Dan yage, hijabin yasa Mata ya jingina ta da jikin bango, bazaka ga fuskarshi ba sabida duhun da ake ciki, Amma dagani shi farine sabida hasken dayake acikin duhun, hannu yasa a aljihunshi yaciro wasu kudade ya riko hannunta yasa Mata aciki, sannan cikin muryan maye yace “ga wannan ki taimaki kanki dashi, Allah yabaki lafiya”

Tafiya yayi yashiga motarshi ya kunna, sannan yabar wurin da mugun speed.

 

*Wattpad*

_Jiddah S Mapi_

About the author

Hausa_Novels

2 Comments

Leave a Comment