Littafan Hausa Novels

Muna Daki Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Muna Daki Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

MUNA D’AKI

 

By

 

Fatima Abdallaah kano

( Autar marubuta )

________________________________________

 

LAFAZI WRITERS ASSOCIATION®✍🏻

 

 

 

 

Da ganin yanayin cikin garin Kaduna ba a jima da dena ruwan sama ba , domin ga hanya mara kyau nan ruwa sai ambaliya yake a ciki .

 

Anan cikin gidan wani bulo da bulo kuwa , mutanen gidan ba wai masu kud’i bane , suna dai da rufin asirinsu .

 

 

Jamila ce ta kalli mahaifiyarta tana cewa, “Mama Wallahi karki bar yaya Jalilu ya yi auren nan , mama kinsan gaskiya ko gida ba shi da shi , sannan ba wani hankali ya cika ba.”

 

 

Da sauri mahaifiyar tasu ta kalli Jamila tana cewa, ” Ah’ah , sannu Jamilla ‘kanwar Jalilu mara hankali, to wallahi ki fita daga idona na rufe , karna sake jin kin yi magana a kan wannan aure.”

 

 

Jamila tai ajiyar zuciya tana kallon mahaifiyar tasu . Ita kuma cikin fad’a tace ,”Kinji ko ba ki jiba kika wani kafe ni da idanu.”

 

Jamila ta d’auke idanunta tana cewa, ” Naji mama .”

Kwantan Bauna Hausa Novel 2023

A lokacin wasu muryoyi suka fara yo sallama cikin gidan

 

Jamila jin cewa tasan su waye yasa ta fita tare da amsa sallamar

 

 

‘yan mata ne da babu wacce ta wuce shekara 21, amma idan ka gansu kace matan wasu ne , kowacce da wayarta a hannu Android , su su biyar ne duk sunsha mai bleaching

 

Jamila ta kallesu kowacce tana kiran sunanta ,”Samira , Salma, Bintu ,Baby , Aisha, duk sannuku ‘yan duniya ku shigo .”

 

Ta shige d’akinta suka bita ciki

 

Bayan sun zauna Baby ta cire hijabi tana cewa, “Kai gaskiya akwai zafi .”

 

Duk idanu suka kai kanta suna kallonta

 

Aisha ce taja tsaki tana cire hijab tana cewa ,”Kun ji rainin wayo, wai zafi , alhalin kirjinta take son mu gani , sai ki nunawa wanda ba shi dasu .”

 

Tsaki Jamila taja tana cewa, “Zaku fara abin naku gaskiya bana so .”

 

Baby tace ,”Rabu da banza mana.”

 

 

Salma ta kalli Aisha tana cewa, “To kema ina abin yake .”

 

Duka Bintu ta kaiwa Baby a kan kirji tana cewa, “Ke banza .”

 

Ita ma Samira ta kaiwa Bintu ya yin da tai sauri ta kauce .

 

“Innalillahi wa Inna ilahir raji’un ”

Jamila ta fad’a tana kallonsu cikin haushi , “Wai ku dan Allah mene haka ne , wannan fa iskanci ne kuma wallahi duka a brest yana jawo cancer.”

 

 

Samira tace ,”To sahiba an dena , amma ni Wallahi aure nake so.”

 

Bintu ta jefa mata harara tana cewa, “Ko ba aure ba , to ke me kika sani da za ki wani aure .”……..

 

 

 

Jalilu ne tsaye kofar gidansu abokinshi Faruk , Jalilu dai ba wani hankali ne da shi ba sosai , ya kan yawan tafki a rayuwa ga gajeren tunani

 

Abokin nashi ne ya fito ,” Haba Faruk ya mun yi da kai zamu gun Laure kuma har yanzu ba ka shiya ba.”

 

Faruk wani kallo ya jefa masa yana cewa, “Bana son hauka malam , to wallahi ba zan d’auki ‘kafa yanzu naje wannan ‘kauyen ba , sai ka ce ba ruwa a kai ba , wannan mahaukacin garin mai nisa .”

 

Jalilu kawai haushin Faruk yake ji saboda maganar da yake ,

 

bayan Faruk ya had’iyi yawu ,”ya ci gaba da cewa ,”Wai ma dan Allah dan annabi ina zaka ajiye yarinyar nan , ga shi babu abin data sani sai ‘kauyenci.”

 

Cikin fusata Jalilu ya fara cewa ,”Bana san iskanci fa , ina ruwanka ko a ina zan ajeta daga ni sai Allah nasan inda zamu , kuma kana maganar babu abin data sani , to ni saboda babu abin data sani nake sonta , kuma sai na aureta ko ba ka so .”

 

Faruk ya yi ajiyar zuciya yana cewa, “Allah ya baka hakuri, amma maganar gaskiya ba zan je wannan garin ba.”

 

Jalilu ya yi tsaki.

 

 

 

Anan cikin wani ‘kauye kuma mai matukar nisa tsakanin shi da gari kuwa , ba a cewa komai ga jar kasa , ga mutanen ciki da miyagun al’adu , yawanci fulani ne ciki amma akwai sauran… .

 

 

Babban gida ne ginin kasa , gidan sashi -shahi ne da yake cike da mutane ‘yan uwa tun iyaye da kakanni

 

Saidai a cikin gidan akwai wani D’AKI wanda yake had’e da band’aki a ciki , a cikin d’akin kawai tabarma ce sai abin shimfid’a , wannan D’AKIN a tarihin gidan ba a shigarsa babu wanda yake shiga ko hanyar gurin ba a yi , dalili kuwa a ciki wanda ya fara zama a cikin babban gidan ya rasu , wato kakan kakan kakan……..😹

hakan yasa ba a shiga ciki bisa al’adarsu , har sai ya rushe sai a tada shi sannan a shiga amma D’AKIN ya ‘ki rushewa.

 

 

Laure ce ta fito kofar gida sanye da riga da zani sai d’ankwali , kowanne da kalarsa

duk da tsani ne jikinta kuma tayi mahaukacin d’auri zaka hangi hip d’in ta , wanda kamar tana gyarashi ,al halin bata San

dashi ba ma 😺

 

 

 

Abin da baba ya hanani fad’e kuwa damm suke a jikinta domin ko tafiya take kamar zasu faso su fito , babu abin kuma da ta tsana irin sa bra , wannan ba kowa ba ce face Lauren Jalilu.

 

 

Mi’ka tasa a kofar gidan tana kallon wani ba fulatanin saurayi da shi da abokinshi da babu imani a fuskokinsu

 

 

Saurayin mai suna Surajo rike da san da ya kalli Laure yana cewa, “Ke shegiya ‘yar iska .”

 

Da sauri Laure ta kalleshi cikin tsoro kuma tana cewa ,”Kai ne shege me yiwa mata ciki .”

Gudu tasa a million ta koma cikin gida ta nufi sashinsu , sakamakon biyo ta da ya yi , sa’a kawai taci ya hakura ba tare da ya bita gidan ba .

 

Tana fad’awa gida ta zauna tana ha’ki , mahaifinta yace ,”mene ya faru .”……

 

Surajo tsaki yaja yana d’ora sandar shi kan kafad’a yana cewa….. “Da kin tsaya ai yanzu na tuburbudaki kema nai miki cikin shegiya.”

 

Abokin nashi ne mai suna Gemu yace, “Wallahi kuwa da munsha madara yau hhhhhh.”

 

 

 

 

*Ki hanzarta biyan naki kafin free pages su kare*

 

*Naira d’ari biyu ce kawai*200

ki tura 7040805269 opay 👉Fatima Abdullahi Ismail

 

ki turo shaidar biya a wannan number 07040805269.

 

*Ni kuma zan saki a group da kullum ake posting, amma banda ranar litinin*

 

 

*MUNA D’AKI*

 

By

 

Autar marubuta

 

LAFAZI WRITERS ASSOCIATION®

 

 

Page 3&4

 

 

 

 

Kawai dogon tsaki yaja ya nufi hanyar gidansu.

 

Surajo Shi ne ubansa yafi kowa kud’i cikin wannan ‘kauyen da shi da mahaifinsa Bala manyan jahilai ne da suke tashe ga rashin kunya , da farko Surajo shi ne ya fara neman auren Laure , amman Laure Allan baran tace bata san shi , aiko mahaifinta yace shi ke nan , baza a basu ba , tun daga lokacin Bala da d’anshi suke nuna ‘kiyayya ga babban gidansu Laure .

 

Surajo ba komai ba ne a gunshi yanzu ya ci mutuncin yaro , babba tsoho ko budurwa, ‘yan matan garin ko hanyar da yake bi basa bi domin Yanzu zai musu ….. . kowa yana tsoronsu hakan yasa yake sake zuba iskancinsa .

 

 

 

“Laure wa ne ya biyo ki ne .”

Mahaifinta malam Sadi ya tambaya ,”Laure tace ,”Babu kowa baba , kawai ‘kihin ruwa ne ya biyo ni.”

 

“Amma shi ne za ki shigo haka .” yaja tsaki

 

Malam Sadi mahaifin Laure ne , wanda yaransa biyu , d’yan na mijin yana cikin birni yana sana’a , ya samu rufin asiri domin har ta yi yayiwa mahaifinsa kan cewa su dawo birni , amma ya’ki , sun fi gane ya ringa aiko musu da kud’i kawai , hakan yasa ya rabu dasu

 

Mahaifiyar Laure ce ta fito daga d’aki tana cewa, “Laure yau Jalilu bai zo ba ne.”

 

Cikin kunya Laure aka wani rausayar da kai kasa ana girgiza kai alamu ehh

 

 

Mahaifiyarta Lanto ta kalli Laure sama da kasa sa’ilin da tace ,”Zo Laure. ”

 

Baba Lanto ta shige d’aki yayin da Laure ta bita , zama Baba Lanto ta yi a bakin gado , yayin da Laure ta zaune a kasa

 

“To Laure kin ga dai auren ki za ai , kuma shiyasa nake koya miki zaman aure domin karki bamu kunya kisa ana nuna mu a gari .”

 

Laure ta girgiza kai baba Lanto taci gaba da cewa ,”Shi zaman aure hakuri ake , kuma kada kiga mijinki ya yi miki wani abin ki ce za ki dawo gida d’an iska ne , kamar yadda ‘yar gidan liman ta yi .”

 

Laure tace, “Ai babata na sani ko ba yadda ake yi mata da miji su haihu ba .”

 

baba Lanto ta ri’ke ha’ba cikin kunya da mamaki

 

“Laure wa ye ya fad’a miki wannan maganar, ashe ma ba abin da zan koya miki .”

 

Laure tai Dariya tana cewa, “Wallahi babata sanda munkaila ya auri Habi , sun yi shi ne take fad’a mana .”

 

Baba Lanto ta tsaya tana kallon Laure .

 

 

 

 

 

⚡⚡Ba za mukai da nisa ba fee pages zasu ‘kare😹

 

Ki biya ki huta tsilla-tsilla ba yawa fa .

 

 

 

 

 

 

Bayan Sati ‘Daya

 

 

“To wai kai Jalilu babu lefe za ai bikin ne .”?

 

Faruk ya jefawa Jalilu tambayar

 

Jalilu ya kalleshi yana cewa ,” Ai su babu ruwansu da llefe ni fa Wallahi ko yanzu na shirya a d’aura , domin na matsu naga Laure ta zama matata , domin ni a yanzu ma ji nake kamar kawai na satota muke kwana tare .”

 

“Kuturun uba “.

 

Faruk ya fad’a ,” Jalilu ka ga dai ni abokin ka ne , dan Allah dan annabi , a ina zaka aje Laure , ni wallahi kamar ba son Allah da annabi kake mata ba fa .”

 

 

Jalilu ya kalli Faruk yana cewa, “Na farko idan ka cika d’an halak karka sake mini maganar inda zan aje matata , na biyu kuma ina son Laure , amma abin da yake ‘kara mini kaunarta shi ne abin da baba ya hana fad’e .”

 

 

Faruk yana jin haka kawai ya tashi ya bar wajen , Jalilu yana ta kiranshi , amma ya’ki dawowa.

 

Shi ma gida ya tashi ya nufa , aiko yana shiga gida mahaifiyarsu ta kira sunanshi , hakan yasa ya cire takalmi ya shiga zuwa d’akin nata , ta kalleshi cikin nasiha tana cewa, “Jalilu ka ga dai wannan biki yanata kawo kai .”

 

Ya kalleta cikin jin dad’in zancen yace,”Haka ne mama .”

 

Mama tace ,”Sanin kanka ne ku marayu ne , amma ance babu maraya sai rago .”

 

Ya sake jinjina kai alamun haka ne

 

 

“To amma Jalilu har yau banga inda zaka aje yarinyar nan ba , domin tun abin ba ya damuna to yanzu ya fara , shin ina ne zaka ajeta .”

 

Dariya Jalilu ya yi yana cewa, “Mama ke nan idan kikaji makaho yace ai wasan jifa to ya taka dutse.”

 

 

Tace ,”Gaskiya ne .”

 

Ya cigaba da cewa ,”Mama karkiji komai , ni Jalilu ba zan baki kunya ba , kawai lokaci ya zo kusha sha’aninku .”

 

 

Mama ta rangad’a ‘bud’a tana cewa, “Allah yasa ayi damu Jalilu na .”

 

 

Bayan Jalilu ya bar wajen Mama ya sake fita waje , can bakin titi yaje ya hau mashin aka tafi dashi ‘kauye wajen Laure.

 

 

 

Nan kuwa su Jamila ne cikin islamiya, kamar yadda suke dai su shida suke tafiya duk inda zasu

 

Samira ce tace ,”Wai ku me yasa ba kwa karanta novels ne , gaskiya bazan iya rayuwata babu shi ba , novels duniya ne Wallahi. ”

 

Jamila ce tace ,”Tabbb aikin wahala na zauna naita wani karatun iskanci , gara na karanta Alkur ani .”

 

 

Aisha tace ,”To Wallahi dan ba ki san dad’in sa bane , da kud’i na ma nake siye , ga inda zaka koyi komai a saukake .”

 

 

Jamila taja dogon tsaki

 

 

Salma ce tace ,”Naku wasa ne tom ni wallahi practical nake kallo ga wayata ina zan zauna wani karatu .”

 

Ta fara kokarin bude wayar ta tana shiga videos

 

 

Hasko musu wayartai yayin da duk suka kawo idanunsu kan wayar

 

video wata mace ne dana miji suna ta ‘yankancin su , hakan yasa Jamila tashi tana cewa, “Allah ya kyauta wallahi ya shiryeku .”

 

Ta bar wajen tana harararsu

 

Baby ce ta fisge wayar tana cewa, “A’a wallahi bani da tura , wannan irin fashion haka .”

 

 

Bintu tace ,”Tura ki bani nima , amma gaskiya Salma kin ci amanar zaman tare .”

 

 

Salma ta kalli Su Samira tana cewa, “Ku baza ku tura ba .”

 

 

Suka ce ,”Me zai hana .”

 

 

Videos kala-kala da basu dace ba birjik a wayarta , aiko duk suka tura ta musu alkawarin tana sake samun wasu za ta tura musu .

 

Nikam na ce Allah ya shirya mana Al’umarmu .👐

 

 

 

A can kofar gidan Bala kuwa wato gidansu Surajo , wata yarinya ce tazo wuce wa shi ne Surajo yake ce mata da yaren fulani, “Ke ‘yan mata zo mana mu huta .”

 

Yana yi kamar zai cire wando , dake yarinyar daga can gaba dasu ta fito batasan waye ba , hakan yasa ta aje kwaryar furar ta tana cewa, “Allah wadaranka d’an iska kawai bazan zo ba .”

 

Hakan ya hassala Surajo ya kalli Gemu yana cewa, “Je ka d’auko mini ita .”

 

Gemu ya nufi yarinyar da ko ratsana ba tai ba

 

Abin mamakin shi ne mahaifin Surajo, Bala yana ji yana ganin abin dake faruwa

 

 

Gemu ya wancakalar da kwaryar ya cicci’bota yazo ya ajeta gaban Surajo , mari ta wanka wa Gemu

 

aiko Surajo ya feka rigar dake jikinta yana cewa , “Wayyo dad’i .”

 

Hakan yasa ta fara kuka tana ba shi hakuri.

 

Sukam dariya suka kece da ita ,Surajo yana cewa “yarinya babu hakuri”.

 

Yasa hannu yana kunto zanin jikinta wanda ta rike zanin gamm tana son cetar kanta

 

Mahaifin Surajo ne ya taso yana cewa,” Barta haka kai Surajo ai bazata kuma rashin kunya ba .”

 

 

Surajo ya had’e rai yana cewa, “Baba ka barni tukun wallahi.”

 

Mutane da yawa suna ganin abin dake faruwa amma babu wanda zaai iya magana sai dai ya kauda kai .

 

 

Bala ya jawo yarinyar yana dariya yana shafa jikinta , sannan ya d’auko ‘barkakkiyar rigarta ya ba ta .

 

Yace tai maza ta koma rugarsu , shi kuwa Surajo gabadaya haushin baban nashi ya ji , da ya yi masa haka

 

 

 

Idan free pages ya ‘kare zaki shiga tsilla-tsilla🥱

 

ki biya Naira 200 kacal ta wannan 🤙 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay

 

ki bani shaidar biya a 07040805269

Nai na saki a group da nake posting.

 

karki dogara da free pages🥺

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment