Littafan Hausa Novels

Mu da Yaran Mu Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Mu da Yaran Mu Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

Muda yaran mu.

 

Ramadan gift

 

 

 

*JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hDDDDD

 

 

OUM SHARIFA CE

 

(Wayoyin mu)

 

Asslam alaikum warahmatullah.

ƴan uwana ykk ya ibada Allah ya karɓa mana.

 

 

Wace irin gudumawa wayar hannu ke bada wa wajan rushewar farin cikin iyalan mu?

Wace irin kulawa kike bawa yaran ki bayan sn dawo daga School?

 

Lokuta da dama waya na dauke hankalin iyaye daga kan yayan su,

Ko kina kallo ko kina chart,

 

idan har yaran mu zasu tafi wasa subar mu muyi chart bamu da wata matsala,

 

sauda dama yaran na waje ko tsakar gida ko dakin su suna wasa mukuma may be muna kan bed mun baje muna chart muna shewa,

 

Matan Ramadan Hausa Novel Complete

Kinsan inda yaranki suke ? Kinsan dawa suke wasa? koda suna cikin gida kinsan wane irin wasa sukeyi?

 

 

 

Baki sani ba amsar kenan

 

 

Indai ba zasu dnga kawo mana kara ba norml a wajen mu,

shiyasa bama son kawo kara da yara keyi,

 

 

 

Na farko kin nisan ta kanki da yaranki,

 

Tn suna kananan yara baki saba da zama dasu kuyi fira ba,

 

bare kisan idan sunje makaranta ko wani waje menene ya faru a wajan wanda zaki tusawa ƴarki/ɗan ki son abun idan mai kyaune ko gudun sa idan mara kyaune,

 

 

toma yaushe ne zasu saba da faɗa miki damuwar su kina matsayin uwa mahaifiya amma ɗan ki / ƴarki dk sirrin su naga aboki ko ƙawa? ,

 

 

menene amfanin kiran ki mahaifiya ? sunan dai kin haihu ko?

 

 

Kananan yara idan suka samu kulawa dk abnda ya faru har sauri zakiga sunayi wajan fada wa maman su,

 

haka baya nufin ki basu dama su dinga dakko miki zancen wani,

 

to ai sai kin basu dama sannan zaki fahimtar dasu abinda ya kamata da wanda bai kamata ba,

 

 

kina nufin yaranki sai sngama primary sannan zaki fara basu tarbiyya,

 

Ko kinsan tarbiyya basai kin bude baki kin fadi wata magana ga yaran ki ba ?

 

 

Ki basu dama su zama a jikin ki, ki basu dama su mai dake mafififciya,

 

domin wannan matsayin ubangiji da kan sa ya baki,

 

 

Yana yin rayuwar da kikeyi a gidan ki da mu’amalar ki da mutane da biyayyar ki ga mahaifin su shi kadai babbar tarbiyya ce ga yaranki,

 

zasu taso tamkar hoton ki komai naki sun dauke yanayin nutsuwar ki wajan magana nutsuwar ki wajan aiyuka da kuma kame harshen ki daga gulmace gulmace,

 

haka yaran ki zasu taso abin shaawa kowa naso,

 

 

Karfa ki manta ba haushe yace nagari na kowa na banza kuma na iyayen sa ne,

 

 

Amma kin dau waya yaro/ yarinya sn taho jikin ki kafin suce komai kinja gefe , menene haka? Kunzo sai nanika ta kuke kamar zaku koma ciki! uwar me zan muku ? ba kunci abinci ba? haka yara zasu daga kai alamar amsawa su fita su baki waje bayan kin daka musu tsawa,

 

jiki ba kwari zasu fice su koma inda suke wasa, sai sn dan jima kafn su cigaba da wasan yara kenan,

 

 

 

Kinsan me suka zo fada miki?

Kinsan meyake damunsu?

Yaran da suke tafiya school su barki a gida wasu wuni sukeyi wasu kuma su dawo da azahar da snci abinci sunyi sallah sai islamiyya,

 

amma ranar da ba makaranta ba zaki iya zama dasu ba kwana 2 a sati yaran ki sun isheki,

 

 

To haka yarki/ danki zasu taso da taaddancin zuciya,

 

Menene taaddancin zuciya?

 

Zata/ya bar abn a ransu har sukai shekarun da zasu san menene kawa/ aboki su fara fada musu damuwar su idan suma kawar/ abokin suna da irin wannan iyayen to fa daga nan zasu gane cewa,

 

iyayen su sun haife su ne zasu basu ci da sha da sutura amma bangaren maganin damuwar su kowa takan sa yake,

 

daga lokacin yaran mu zasu fara tinanin hanyar da zasu bi wajan solving dn damuwar su,

 

 

 

Daga ranar da suka fara solver matsalar su da kansu wllh baki isa su dawo gare ki ba,

Kuma ki shirya zubar da zafafan hawaye dalilin.

 

 

Oum sharifat ce.

Muda iyalin mu

 

Ramadan gift

 

OUM SHARIFA CE.

 

 

🔔📚

*JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION📚*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hDDDDD

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

 

*⚜️©J.A.W📚

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم.

 

 

Mi salin karfe biyar da rabi na yamma yara ne su uku tsaye kofar wani madaidaicin gida suna ta buga kofar saidai shiru babu alamar mutum a ciki babbr cikin su wacce zata kai shekara Tara taja gefe ta zauna tayi shiru tsananin gajiya da yunwa ke kwakular cikin ta me binta ta kalle ta cike da sare wa tace yaya Naufal momy bata nan ko ? ɗaga kai naufal tayi tare da cewa “eh bata nan amma bari na duba gidan maman boy ko tana ciki, ɗan ƙaramin cikin su wanda bai jima da shiga makaranta ba ya fashe da kuka yana kiran yaya yunwa nake ji ita ma dai yayar dauriya kawai take amma ji take kamar an mata yasa a cikin ta

 

“” kayi haƙuri sadiq bari na nemo momy kaji? gyaɗa kai yaron yayi yana shanye hawayen sa ku tsaya naje na dawo kar kuje ko’ina da to Nana ta amsa dn shi sadiq ko magana ya kasa,

 

saida Naufal ta zagaye a ƙalla gidaje huɗu sai a na biyar ta samo momyn tndaga driving ɗn gidan take jiyo hayaniyar mata da maganganu kala kala na batsa, da sallama Naufal ta shiga gidan amma babu wacce ta amsa gaba ɗaya hankalin su yana kan maman meera dake fasalta musu yanda zaa rikita oga gabansu kuwa tulin kwalayen maganin mata ne kamar hauka dk sallamar da Naufal keyi basu san tanayi ba, ƙarasowa tayi kusa momyn ta taɓa ta ta baya a zabure Zainab ta juyo dn ganin wanda ke son katsemata labari ,

 

Naufal ta gani tsaye cikin kayan makaranta fuskarnan babu alamun jin daɗi wata uwar harara ta watsamata sannan ta ƙara da cewa saar ki ce niko? dn ubanki ni zaki wa irin wannan iskancin uwar ki zan miki sunkuyar da kai Naufal tayi tace dn Allah momy kiyi haƙuri dama mndawo bakya nan ina ta neman ki ga sadiq sai kuka yake,

 

Wata harar ta sake watsa mata kafin tace “”to uwar iyayi kije gani nan zuwa jiki babu ƙwari Naufal ta fito ta dawo wajan ƙannen ta zauna tana rarrshin sadiq sun jima a haka kafin zainab ta ƙaraso ta buɗe gidan suka shiga wasu shegun ƙudaje ne suka tarbesu sakamakon tulin kayan wanke wanke dake dake bakin rijiya a jiye,

 

 

kallon Naufal Zainab tayi tace ki cire kayan kizo ki yi wanke wanke ,

 

 

 

 

Hawaye ne suka fara zubowa Naufal tace “”momy yunwa muke ji dn Allah ki fara bamu abunci ciki na ciwo yake,

 

Wata uwar ashar Zainab tayi tace “” ina abincin da aka kai muku?

 

 

saida Naufal ta goge hawaye sannan ta ce ai na jiya ne kafin muzo ci ya lalace akuya muka bawa a hanya ta cinye ba muci komai ba,

 

 

 

Tabe baki Zainab tayi sannan tace sai ki cire kayan kizo ki fara wanke wanken sannan a samu tukunyar da zaa dora girkin da to ta amsa tana dafe da cikin ta tashiga dakin su ta canza kaya ta fito ta fara wanke wanken,

 

 

 

Sadiq da nana ko kayan basu cire ba suka fice sai makota cikin saa kuwa an zubawa yara abinci suna ci gefe suka ja suka tsaya suna kallo,

 

 

 

Uwar yaran tana kallon yanda su nana suka zubawa abincin ido amma batayi magana ba saida suka kusa cinye wa sannan tace suzo su ci kamar basu taba cin abinci ba haka suka taho suna rige rige suka saka wa abincin wawa hannu baka hannu kwarya suka tashi dashi.

 

 

OUM SHARIFA CE.

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment