Littafan Hausa Novels

Mr Bello Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Mr Bello Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

MR BELLO

_(The young Teacher)_

 

*NA*

 

*JANAFTY*💕

*Wattpad:Janafnancy13*

 

 

_*Bismillahir Rahamanir Rahim in the Name of ALLAH the most  Beneficient the most mercerfull praise be to Allah lord of the words…..*_

 

_Assalamu Alaikum my Follow fans,am starting my new Book i ask ALLAH subhanahu wata”ala to guide me throught and make me it sussufull till End Ameen ya Allah_

 

*Copycats are not allowed to transform this book by any means without the prior written permission of the writer.Immediate action will be taken if caugh?*

 

DEDICATED TO: *Bashir Sufyan Sardauna* and *Nazifi yarima* Sakallahu fil jannah Dudes..For ur all Support,care and Concern..Allah yabar zumunci Ameen_

 

SHIMFIDA.

 

*🅿?1*

 

*GGUSS KWATAR-KWASHI*

 

A haraban Babbar Makarantar ta GGUSS, Goverment Girls Unity Secondry School Kwatar-kwashi Dake Tsakanin Dajin kwatar-kwashi Zuwa Gusau, Da Misalin ƙarfe 10:30am na Safe.

 

Daga Cikin Babban Filin Haraban Makarantan Na Hangi ɗalibai Birjit ba Adadi mata ne Zallah Ta Ko”ina Suna Yawo Wasu Suna Tsaye da Tarin Akwatunsu da Jakunkunansu Wasu kuma Suna ta Tururuwan Shiga Doguwar Mota Fara mai Ɗauke da Tambarin GGUSS KWATAR-KWASHI, gefe ɗaya kuma Kowaccensu Tana Sanye da Uniform ne Ajikinta wasu Nasu Wando light green ne Both Riga da Wando da Ɗan kwali sai Farin Hijabi A yayinda Wasu kuma ke Sanye da Dark green d’in Wando sai Both Farin Riga da Da’n kwali da Hijabi.

Amfanin Habbatus Sauda Guda 31 Ga Dan Adam

A yadda Haraban Makarantan ta Rikice da Hayaniya da Murna da Iface ifacen Ɗalibai zaka Fahimci Hutu ne Ɗaliban Suka Samu Tun ma Ba Daga yadda Wasu Iyayen Ɗaliban keta Zuwa Ɗaukan yaransu Wanda basu yi Register da Motar Makaranta ba, Ayayinda Wasu ke Ta Fitowa Bakin Get d’in Mkrantar ga masu Mashi nan suna ta Ɗaukansa Zuwa inda zasu Hau Mota Zuwa Gida.

 

Daga chan ɓangaren Na Hangi Wasu ‘Yan mata su Uku Tsaye A bakin Wata Bishiyar Dalbejiya Dukkansu Gabansu Akwai Tarin jakunkuna, da Sauran Tarkacensu masu yawa, sakamakon Wannan Hutun Third term ne ƙarshen Zangon karatunsu na Jss 3 sai Shiga SS1 Kenan, Suna Sanye da Uniform ɗinsu na Junior, light green both Riga da Wando da Ɗankwali sai Hijabi Fari, Dukkansu Ukun Tsawonsu Ɗaya Sai dai kuma Biyu Daga Ciki Farare ne Tas, Sai Ta Ukun Wacce ke Tsakiyansu Ɓaka ce Sulub ammh Bak’inta bamai Duhu bane mai haske ne, Wanda Ke Shining, Doguwa ce Mai K’arancin Girman Jiki, Fuskarta tana da Faɗi Ammh ba Sosai ba, Tana da Manyan Idanuwa Masu Ɗauke da Gashin Ido Zarara sai Ƙaramin bakinta Wanda Yake Baƙi baki, A shekaru Dukkansu bazasu gaza Shekaru goma Sha Shidda ba Daga Kallon Farko Zaka Fahimci Zallar Ƙuruciyarsu A lokacin.

 

Daga bayansu sukaji Ance ” *ANEESA…*” atare Suka Waiga dukkansu suna Kallon Ɗaya Daga Cikin Senoirs ɗinsu Jidda Madaki Waɗanda Suke Kan Zana Jarabawarsu ta Fita Ma’ana WAEC, Saboda Haka Su Suna Makaranta basu Azuwa Hutu sai Sun kammallah Neco wanda kuma bazai yi ba Sai ya Tattara ya koma gida.

 

Itama ɗin Sanye Take da Uniform ɗinsu na Senior, Dark green da Farar riga da Hijabi, Kyakkyawar Gaske ce Gata Fara gata Doguwa mai Ɗauke Da Daran Daran Idanuwa masu Haske Cikin Siririyar Muryanta tace “Aneesa Plz D’an zo na ganki…” Ta faɗa Cikin Yanga Wanda ya Zame mata Halitta.

 

Jin Abunda tace yasa Aneesa Ta ƙara Haɗe Ran Kamar Wacce Aka Aikoma da Saƙon Mutuwa Saɓanin Sauran ƙawayenta da Fuskarsu ke Washe na Farin cikin Zasu koma gida yau, Cikin Sanyi Jiki da Takun Ɓacin Rai Aneesa Ta Nufi Jidda tana Faɗin ” *S. JIBIYA, B. KAITA* Ku jirani bari na Dawo..” Jin Haka yasa S. Jibiya tace “Ok *A. BUKAR BULAMA*…” Ta faɗa Tana bin Aneesan Da Kallo kafin Ta Maida Kallonta kan B. Kaita Suka haɗa ido Suna Ƙunshe Dariya.

 

Aneesa kamar bazata Taka ƙasa ba Haka ta Rinƙa jan ƙafa Zuwa Wajen Jidda Dake Tsaye tana Jiranta Tana ƙarisowa ta Riƙo Duka Hannayeta Cikin Salon Muryanta tace “Aneesa Don Allah karki manta da Alƙawarin mu Kinji..” Ta faɗa Tana Sakar mata Fararen Idanuwanta.

 

Gyara Tsayuwa Aneesa Tayi Tana Jifan Jiddan Da Wani Banza Kallo A fakaice, kafin tace “Wani Alƙawari kenan…?” Ta faɗa Da Sigar Rainin Wayau Lokaci Ɗaya Itama tana Sakar mata Manyan baƙaƙen Idanuwanta masu Ɗauke da Zara zaran Gashinta baƙaƙe masu ƙara Fito da Salon Kamaninta da *KANURI*, Jidda Ta Saki Ajiyar Zuciya kafin Ta ƙara Riƙe Hannun Aneesa Tana bin Haraban Mkrantan da Kallo Yadda Taga Kowa na Haraman Tafiya sai D’ai d’ai Irinsu ne Suke Hidimar gabansu.

 

Cikin ƙara Kwantar da Murya Tana faɗin “Haba My Anee, har kin manta da mganarmu na Kiyi ƙoƙarin Saka yayanki Ya Soni koda bai kai Kwatankwacin Irin Son Da Nike mai ba, plz Anee Ki Taimake ni Don Allah Wlh bazan iya Rayuwa ba Matuƙar babu *MR BELLO JIƘAMSHI*….” Ta faɗa idanuwanta Sun ciko da Ƙwallah Suna Ƙoƙarin Zubowa.

 

Cikin Wani Baƙin ciki da Takaichi, Aneesa ke Bin Jidda da Kallo kafin Tace “Oh..! Na Manta ammh Tunda kin Tuna min zanyi k’ok’ari sosai Anty Jidda..” Ta faɗa tana Zare Hannunta Cikin na Jidda Wace ke Share Ƙaramar Kwallar data Ziraro mata, Murmushi ta sakarma Aneesa kafin tace “Yauwa ko kefa Anee, Ammh zaki Dawo ki Ɗora SS1 Ɗinki Anan ko Aneesa..?”

 

Ɓata Rai Aneesa Tayi kafin tace “A”a bazan Dawo ba Nifa Na gama Wannan karatun Har Abada Tunda bana Shiga Aljanna bane..” Ta faɗa Cikin Nuna yadda Ta Tsani Karatun Gaba ɗaya, Dariya Jidda Tasaki Cikin Aji da Wayewa Tace “Oh Anee Wai ke bazaki Chanza ba Shiyasa bakwa Shiiri da Mr Bello sam, Kuna gida Ɗaya Ammh Ra”ayinku ya bambanta Shida baya son Zama da Wanda baya son Karatu..” Tura baki Aneesa Tayi kafin Tace “Aiko da Muke gida Ɗaya ba Uwarmu Ɗaya ba Kuma ba Ubanmu Ɗaya ba, Ba Abunda Na Haɗa Dashi Hanyar jirgi Daban na Mota Daban..” Dariya Jidda Ta ƙara Sakawa Tana kallon Aneesa Wacce ke Kallonta Tana ƙara Haɗe Rai Fuskar nan na ƙyalli baki da kuma Uban man Vaseline d’in Da Aneesa ta Shafama Fuskarta.

 

Haushin Dariyan Jidda yasa ta Juya Zata Tafi Da Hanzari Ta Riƙo Hannunta tana ‘yar Dariya tace “Sorry my Anee, na daina Dariyan Kinji ko? Na yarda baku Haɗa komai ba Ammh dai gidanku Ɗaya, zaki min Abunda na Sakaki ko..?” Aneesa Data Waigo Tana Ƙara Tamke Fuska tace “Nifa bana Shiga Harkanshi Sai dai nama Anty Rahila mgana Tayi mishi Tunda Ita Naga Suna Shiri Sosai..”

 

Da Sauri Jidda Tace “Yauwa Ki Gaya mata Kinji ko, Ga Nombar Wayata In kin koma gida ki kirani ko da wayar Anty Rahilan ne Kinji ko my Anee..” Ta faɗa Da Sigar Lallashi Lokaci Ɗaya Tana Saka mata Takardan Data Rubuta mata Lambarta Karɓa Aneesa Tayi Cikin Ƙosawa Tace “Naji Anty Jidda bari na Tafi Su B. Kaita na Jirana..” Fuskarta Jidda Ta Shafa tana Faɗin “Ok Aneesa nagode sai naji kiranki..” Da Sauri Aneesa Ta Ƙwace Hannunta ta Wuce Tana Sakin Tsaki Acikin Ranta Take Faɗin “Ai sai kiyi Tayi Iska na Wahalar da mai kayan kara Uban Waye zai kiraki kan Wannan Mugun..” Ta faɗa Harda Tsirtar da yawu kafin tace “Allah ya Tsareni da Haɗa Shirgina Da Mara Imani.”

 

Ta faɗa Tana Ƙarisowa Wajen Dasu S. Jibiya Suke Suna Jiranta Tun kafin Ta Ƙariso ta Dunƙule Takardan Da Jidda Ta bata ta Wurgar Da Ita gefe Tana Waigon Jidda Wacce ta Juya ta Nufi Hostels ɗinsu na DAURAMA part 2, Da kallon Mamaki B. Kaita tace mata “A. Bukar me aka baki kika yaga Haka..?” Tsaki Aneesa Taja Tana Gyara Tsayuwa kafin tace “Nombar Wayar yar Wahalar ce wai na Kirata in na Koma gida..”

 

S. Jibiya tasaki Dariya kafin tace “Ikon Allah Toh kan mene..?” Aneesa Tace “Kan Wannan Mugun mara Imanin Wanda ya baroni da gidanmu ya kawoni Cikin Wannan Dajin yana Cin Zalina mana..” A tare S. Jibiya da B. Kaita Suka Haɗa baki Suka ce “Wai *MR BELLO MUHAMMED JIƘAMSHI*….?” Aneesa Ta Ƙara Jan Tsaki tace “Bello dai kam Don ni bazan ce mai Mr Bello ba Wlh…”

 

B. Kaita tace “Gaskiya Aneesa bakya kyautama kanki ina Laifin Mr bello Da Kika bi kika Tsaneshi, taimakon ki fa yayi Daya kawoki mkranta kikayi karatu kika zama ‘ya kamar Kowa..” Da Mamaki Aneesa Ta kalleta kafin tace “Nace ne ya Taimakeni ko Kinji nace miki ina Buƙatar Taimako ne, King B. Kaita Ki kama bakinki karki gaya min mganar banza nace Baƙin Mugu Wanda ya Kawoni Wannan Dajin Allah Yana Cin Zalina ko Zaki Rama mai Ne Domin Naga Alamar Kema Cikin Layin Su Jidda ne na Son Wanda bai Dace daku ba..” Ta faɗa Cikin Fushi.

 

B. Kaita ta Harzuƙo ma Aneesa Tana Faɗin “Eh ɗin Faɗi ki ƙara Ina Son Mallam Bello kuma so na Aure Aneesa Zuciyata Kullum Tana Zafi da Takaichi Duk Sanda Naji Kina Aibatan Mr Bello, Haba Shikenan kuma don Jininku bai Haɗu ba, baki Sonshi sai ki Hanamu mu Masu Sonshi mu Soshi ko mu nuna muna Sonshi, Tsakaninki dashi Daban muma tsakaninmu Daban, Saboda Haka Muma Kibar mu Mu nuna Muna Sonshi Domin Babu Abunda yayi mana Kuma yayi Dai-dai Da Ra”ayinmu..” B. Kaita ta Faɗa Cikin Nuna Masifarta Harda Ɗaga Murya.

 

Aneesa da Wata Zuciya ta Ciyota ta Tsallake S. Jibiya ta Dira gaban B. Kaita taci Kwalan Hijabinta tana Faɗin “Ina Ruwana da Son da Kuke mai Nidai sai na Faɗa ba Kuma Zan Fasa Faɗan Bello mugu ne mara Imani ba, Ko zaki iya Rama mai ne…? sai naga Ƙarewar Son da Kike mai Banza Kawai mara Aikin yi..” Ta faɗa Indanuwanta Sun Kaɗa Sunyi Jajir.

 

B. Kaita da Abun na Aneesa Ya kaita Wuya sai kawai ta cakumo Aneesa Suka Fara Dambe Tana Faɗin”Ni ba banza bace kece babbar Banza butulu mai Raina Alheri..” Tuni Faɗa ya kacame, S. Jibiya ce ke ƙoƙarin Rabasu da Sauran Student d’in da basu gama Tafiya ba, suka ƙariso Suna Raba Kawayen Juna Faɗa, S. Jibiya ce ke Faɗin “Haba Aneesa, Billy meye Haka Wannan ba girmanku bane Aganku kuna Faɗa da Junanku…” Aneesa Data Shaƙe Wuyan B. Kaita da Hijabi Take Faɗin “Aganmu munayin Mana Uban Waya ja In ba Ita ba Dama Tuni Billy Take Shigan Hanci Da Ƙudundune Wlh yau kafin mu bar Mkrantan nan Sai mun Goge Raini Tsakanina Da Ita..” Take Faɗa Tana Haki tana ƙara Tamke Wuyan B. Kaita Wacce ke Ƙoƙarin Ƙwace kanta.

 

Daga bayansu Sukaji Ance “Are u Stupid Aneesa Bukar Bulama….?”

 

Sukaji An Faɗa Daga bayansu Cikin Kakkausan Murya, gaba ɗayansu Suka Waiga Suna Kallon Uncle Aminu da Mr Bello Suna Tahowa, Hannunsu Sarke da Juna, Kamar Wasu Tagwaye Dama Duk Sch d’in ba Wanda baisan Abota Da Shaƙuwa Irinta Uncle Aminu da Mr Bello ba, Uncle Aminu Yana Sanye da Riga da Wando black And White, Sai Wani Rufaffan baƙin Takalminsa na Fatar Damisa Sai Mr Bello yana Sanye da Riga da Wando Rigar Dark Blue mai Dogon Hannu sai Wandonshi mai Ruwan Blue mai Haske, Ƙafarsa sanye da Takalmi Baƙi booth sai kansa Dake Sanye da p cap, wanda ya Rufe Rabin Fuskarsa Dukkansu Dogaye ne masu Surar Jiki Ƙirar Maza Cikakku Masu Zati da Haiba.

 

Uncle Aminu Fari ne Mai Faɗin Fuska da Dogon Hanci yana da Gemun Shi ɗan Dai-dai Wanda yake Ƙara mai kyau mai Haɗe da Zagayayyen Bakin shi mai faɗi Kaɗan, Mr Bello Fuskarsa bata bayyana ba Sosai Sai dai Daga yanayin Fatar Hannunshi Inda Rantsantsen Agogo na Kamfanin Rado ke Ɗaure A tsinsiyan Hannunshi na kallah na Fahimci Fari Ne Sosai Saboda Yadda Fararan yatsunshi ke Kwance da Gashi Sun Kwanta Zara zara Gwanin Ban Sha”awa, Yana da Faɗi Kaɗan Daga Sama Saboda In yana Tafiya Zaka ga yana Buɗewa, a kallon yanayin Tafiyarshi kaɗai ya Isa Zatinsa da Jarumtarsa Su Dakeka Tun kafin kaga Fuskarsa ma.

 

Duka Ɗaliban Dake Wajen Suka Fara Matswa Jikinsu na Rawa Suna Tsoron Kada A haɗa dasu Uncle Aminu da Mr Bello A lokaci Ɗaya ai Fire ne, babu Wanda Baisan yadda Suke cin Ƙaniyar Ɗalibai ba Acikin Mkrantan Musamman ‘yan Taurin kai Irinsu Aneesa, Aneesa Ko Ajikinta Sai ma Ƙoƙarin Ƙara Riƙe Wuyan Hijabin Billy Kaita Da takeyi Itako Tuni Ta Saki Wuyan Aneesa Tana Ƙoƙarin Ƙwace Kanta Salamatu Jibiya Kuwa Baya ta Matsa Tana Zare Ido Aranta Tana Addu”ar Allah yasa yanzu Motar gidansu tazo Ɗaukanta.

 

A gabansu Suka ja Burki Uncle Aminu ne ya kalli Aneesa Dake Wani Hura Hanci ga Bakinta na Ƙara Ɗaukan Ido Cikin Tsawa Yace “Leave her Hijab Now Don Ubanki…” Ya Faɗa yana Sakin hannun Mr Bello Wanda kanshi ke ƙasa yana Danne Danne Cikin Wayarsa, Kamar baima san Abunda Ke Faruwa Awajen ba, Aneesa na Ƙunƙuni Harda Ƙwallarta ta Saki Wuyan Hijabin Billy Kaita tana Faɗi ƙasa ƙasa “Nidai ba Ubana ba Wlh..” Ta faɗa Tana Share Hanci ba Zato ba Tsammani Taji Gam!! An Buge mata baki, da Hanzari Ta Dafe Wajen Tana bin Hannun Wanda ya Maketa da Kallo Mr Bello ne Cikin Muryan Sanyi Ammh Cike da Faɗa yace “Ba Ubanki ba sai Ubanwa..?” Ya faɗa ammh Still kanshi na Kan Wayarsa Dake Hannunsa.

 

Uncle Aminu ne ya Riƙe Kugu yace “Au haka tace Bello? ƙanwar nan Taka fa Zan ci Ubanta, Duk da Mun Riga mun basu Hutu..” Mr Bello Dake Danna Wayarsa yace “As u wish…” Ya faɗa yana Ɗago da kansa Lokaci Ɗaya Ɗaliban Wajen kowani ya fara kama gabansu Wasu ma Jakunkunansu Suka Ɗauka Suna Nufar bakin Get, Jikinsu na Rawa Kada Laifin Aneesa ya Shafesu Domin kaf Mkrantan Kwarta-kwashi ba Wanda baisan Waye Uncle Aminu da Uncle Bello ba wajen iya cin ƙaniyar Ɗalibai Kuma ba Wanda bai san Wacece Aneesa Bukar Bulama ba wajen Rashin kunya da Rashin Tsoro.

 

Jin Abunda Mr

Bello yace ne ya sa S. Jibiya ta Marairaice Fuska tana Kallon Aneesa Tana mata alamun Ta bada Haƙuri Ita kanta Billy Kaita Tsoro ya Shigeta ganin Uncle Aminu ya isa Bishiyar Dalbejiya yayi Tsalle ya Katso Reshe Ɗaya ya Tsinketa Wata Doguwar Bulala Ta bayyana Kafin ma ya Ƙariso B. Kaita da S. Jibiya Suka Matsa Gefe Suna Rawan Jiki Shiko Mr Bello Baya ya Juya Bayan ya Ɗaga Wayarsa ya Ɗaura a Kunni ya fara Tafiya kamar Zai Fita bakin Get.

 

Cikin Tsawa Uncle Aminu yace “Kneel Down…” Aneesa Ta kalleshi tana Ɗaga Idonta sama Irin Banji me kace ba Sanin Raininta yasa bai Jirata ba ya Fara Zuba mata Bulalar Dake Hannunshi Cikin Ƙwarewa da Mugunta Tun Aneesa na Tsaye tana Cijewa karta yi Kuka sai da Hawaye Suka Fara Fita Daga Idanuwanta ta Duƙe Ƙasa Tana Kuka bai barta ba sai da Bulalar Ta gama Karairayewa A jikinta kana ya ƙyaleta ya kalleta yana Faɗin “Wannan na Bye bye Kwatar-kwashi ne In kika Dawo First Time SS1 akwai Welcome to GGUSS SS1 kwatar-kwashi Tunda Ke Har yanzu bazaki yi Hankali ba Bush girl kawai wato ba Ubanki ba sai dai nawa ko..?”

 

Ya fada yana Saka ƙafa ya Shureta Dai-dai Lokacin da Wata Arniyar Motar Buggati baƙa ta Shigo Cikin Mktanta Kallon Farko Kowa yayi ma motar Suka san Motar da Zata Ɗauki Mr Bello da Aneesa Ce Domin duk Faɗin Mkrantar babu Wanda Ake Zuwa Ɗauka da Motocin Alfarma sai Su, Aneesa Dake Duƙe tana Kuka Ko Ɗagowa batayi ba nan Uncle Aminu ya Juya ya Nufi inda Mr Bello ke Tsaye yana gaisawa da Direbansu Mallam Inuwa, Tuni Ɗaliban Mkrantan Masu Tafiya Sun Watse Su kuma ‘yan SS3 sun Shiga Jarabawa.

 

Lokacin da Mr Bello ke gaisawa Da Mallam Inuwa yaja p.cap Ɗinsa Sama kyakkyawan Fuskarsa Ta Bayyana Wow.. Haƙiƙa Allah yayi Halitta Domin Wata kamilalliyar Fuska na Hanga mai Cike da Kyau da Haiba Farin Namiji ne mai Ɗauke da Dogon Hancinsa Har Baka A kallon Farko In kayi mai Zaka Fahimci ya haɗa Nasaba da Fulani Zagayeyyen Baƙin Sajensa ne ke Ƙara mai kyau Wanda yayi ma ƙaramin Bakinshi Kwanya matsakaitan Idanuwanshi masu Ɗauke da Wasu Fararen Idanuwa Masu Kyau da Narkan da Zuciyan ‘yan Mata, Sai zara zara gashin Idanuwansa Masu Tsawo da baƙi Da Gashin Girarsa Baƙi Siɗik Haɗe da Wani Kwantaccen Gashin Kansa Irin na Fulani Mr Bello baya barin Gashi Ya Taru Akanshi ko A yanzu Ma Babu Cikar Gashi Sosai

 

*MUHAMMED BELLO MUHAMEED JIƘAMSHI* Kenan wanda Ɗalibai da Malamai kema Laƙabi da _MR BELLO_  kuma Ƙani ga Cheif Army of Staff na ƙasa Gaba ɗaya Wato *LT. GEN. MUKTAR MUHAMMED JIƘAMSHI* Cikkaken Namiji ne mai Aji da Zati Wanda Kaf ‘yan Matan Dake GGUSS kwatar- kwashi ke Rubibi Akanshi, Tun daga Kan Malamai da Ɗalibai, Kan ‘yan Junior ne da Senior, Kaf Ɗinsu ba Yarinya Da Zatace bata Crushing Ɗinsa, Mkrantar Tana ji Dashi Domin Tunda Ƙasa Zuwa Sama Shine kaɗai Malami ƙwara Ɗaya Tak da yake Ɗaukan Su Mathematics Sakamakon yana da Master Digree Akansa Wanda ya Haɗosa a babban Birnin America Wato U.S.

 

Da Sauri Billy Kaita da Salamatu S Jibiya Suka ƙariso ga Aneesa Suka Riƙota Billy na Faɗin “Aneesa Don Allah ki daina Wannan Taurin kan Wahala kawai zaki Dinga Sha..” Aneesa Na Miƙewa Ta Fizge Jikinta Tana Share Kwalla tace “Bazan bari ba Ki Rabu Dani Munafuka Ai Burinki ya cika Tunda Yau ɗin ma Ina Murnan zan Bar Uƙuba sai da Aka ƙara Zalunta ta, In kika ƙara Nuna Kin ma Sanni Billy Allah ya Isa Tsakanina Dake Domin Duk Masoyina bazai so Wanchan Mutumin ba..” Tana gama Faɗin Haka ta Ɗauki Trolley ɗinta da ƙaramar Jakarta Da Wata Jaka Ta Rataya abaya kafin ta kalli Salamatu Jibiya tana Faɗin

 

“S. Jibiya Sai munyi Waya Ga Mallam Inuwa chan yazo zan Tafi kada yasa atafi Abarni irin na Wanchan Term din..” S. Jibiya bata samu Zarafin mgana ba Aneesa Ta Wuce Ruƙu Ruƙu da Kaya Billy da Salamatu Jibiya Suka Bita da kallo Suna Kaɗa kai Sanin Halin Aneesa na Masifa da Saurin Fushi Ammh Akwai Saurin Sauka Nan da Gobe zata manta komai don Duk Faɗin Kwatar -kwashi bata da kamar Billy Kaita da Salamatu Jibiya.

 

Tana ƙarisowa Mallam Inuwa Ya Tareta da Fara”a yana Faɗin “A”a ga Ɗiyata ‘yan Makranta, Kai Masha Allah Hajiya tace Kin kammallah zangon karatu na Farko..” Ya faɗa Cike da Murna Cikin ɓata Rai Aneesa Tace “Wlh na gama Dawowa wannan Mkrantan Baba kama ji gaskiya Haba na gaji da Wannan karatun Mkrantar Ta Isheni Baba Wahalar Tayi yawa Tunda bana Shiga Aljannah bane..” Ta faɗa Tana Sakar mai Akwatunanta Guda Biyu Ɗauka yayi yana Dariya gefenshi ya kallah yaga Basu Bello Sun gangara Zuwa Quarters d’in Malamai Mr Bello zai Ɗauko Jakarsa.

 

Booth ya Buɗe yana Zuba mata Akwatunan, Hannu ya Miƙa yana Faɗin “Au hakane fa Kin gama Toh kawo Jakar itama asaka A ciki Karatu kam Kin gama Tunda bana Shiga Aljannah bace Wanda Kika samu Allah samai albarka..” Washe baki Tayi Tana Faɗin “Yauwa Baba Allah sa Yadda ka Fahimta Haka *YAYA MUKTAR DA ANTY RAHILA* Suma su Fahimta ko da yake Ko Sun barni nasan Wannan Mugun bazai barni ba ammh Wlh Wannan karon ko Guduwa ne Sai na Gudu Borno Wajensu Yaya Ali In dai Aka matsamin sai na Dawo Mkrantar nan…” Ta faɗa Harda Sharɓe Ƙwallah..

 

Kallonta yake bayan Sun gama Saka kayan ya Rufe Booth d’in Motar yana Faɗin “A”a ‘yata mai yayi Zafi basai kin gudu ba, Insha Allahu Shima Zai Fahimceki..” Ya faɗa Yana Danne Dariyansa Ganin Tana Wani Taɓe baki gidan baya ya Buɗe mata yana Faɗin “Ɗiyata kinbar ƙawayenki gasu chan..” Jin Haka yasa Ta Juya Tana kallon Salamatu Jibiya da Billy Kaita Suna Tsaye Suna kallonta, Harara ta Makama Billy Harda Murguɗa mata baki Tana Faɗin “Sai Wata rana na bar Muku Mkrantar..” Ta faɗa kai Tsaye Tana Shigewa Mota, Dariya Suka saka Aran S. Jibiya Tana Jaddada Dawowar Aneesa SS1 Dole kamar yadda Yake Awajensu.

 

Basu Daɗe ba sai ga Uncle Aminu da Mr Bello Sun Ƙariso Yana Ɗauke da Wata bak’ar jakar Baya, Musabaha Sukayi da Aminu Suka Ɗanyi Mgana kafin Suyi Sallama don Uncle Aminu sai Next Week zai Tafi Sakamakon Ɗaliban SS3 Dasuke WAEC basuyi Darasinshi na Na Turanci ba shikuwa Mr Bello Da yake Malamin Lissafi Kuma Jiya Sukayi Paper, d’in Dat Why Shi Zai Wuce Gida Shima Kuma Uncle Aminu Dake Kano sai Sati na Sama Zai Tafi.

 

Shi ya Buɗema Mr Bello Ƙofar gaban Motan ya Shiga Suna Ƙara Sallama, kafin ya Rufo ƙofar Motar Mallam Inuwa ya Tada Motar Suka Fice Daga Mkrantan Uncle Aminu na Ɗaga musu Hannu Aneesa na Cikin Mota tana Makamai Harara Aranta tana Faɗin “Mugu sai Abi Wani Sarkin Ba Aneesa ba..” Ta faɗa Harda Yar Dariyanta Karaf Ko Suka Haɗa Ido da Mr Bello Yako Makamata Harara yana Faɗin “Don Ubanki Ɗauke waɗannan baƙaƙen Idanuwan naki Akaina ko nasa Mallam Inuwa ya Faka Motar nan na Wurgaki Dajin nan.” Ya faɗa Cikin Tabbatar da mganarsa.

 

Jin Haka yasa Tayi Saurin Sadda Kanta Cikin Rawan Jiki Saboda Tasan Zai aikata Don Wanchan Term d’in ma Tafiya yayi ya barta sai da tabi Direban gidansu Salamatu Jibiya ta tafi gidansu ta Kwana Washegari Akazo Aka Ɗauketa, Haɗe Rai Tayi kanta ta maida Gefe Tana Ƙunƙuni Acikin Ranta Shiko Gyara Zama yayi yafito da Wayarsa yana latsawa Mallam Inuwa na gefe yana Tuƙi yana kanne Dariyarsa ganin Yadda Aneesa Take Tura Baki kamar Zai Tinko Ya Faɗi Saboda Ƙunƙuni.

 

Suko su Billy, su Aneesa Suna Tafiya ba Daɗewa Kusan Tare Motocin Gidanasu S. Jibiya da Billy Kaita Suka zo nan da nan Kowacce Ta Ɗauki Kayanta Suka Loda Amota Sukama Juna Sallamar sai sunyi Waya Kafin Su Dawo mkranta.

 

*Anitha…*

*20/07/2020…a: *MR BELLO..!*

_(The young Teacher)_

 

 

 

*Wattpad:Janafnancy13

_Mallakar:Janafty

 

*🅿�?2*

 

#Home..

 

*ABUJA-Area-GARKI*

 

“”Karfe 4pm da wani abu Motarsu Tafara Zuba Hon Abakin Wani Shimfideden Tamgamemen Get Dake Amguwar nan ta masu Kudi ko Nace Kusoshin Gwannati Wato Garki,Tunda ga Layin Sojoji ne ke Tsaye Har Zuwa Cikn Haraban Makeken Gidan Mai kama da Alkarya Guda,Aneesa Bakinta yaki Rufuwa Ganin Sun Kawo Gida,kafin ma Mallam Inuwa ya gama Daidaita parking a parking Space inda Tarin Rantsantsun Motoci na Alfarma ke Fake Sunfi guda goma,Kai Daga Ganin Gidan kasan Wani Soja ne Wanda yake da Mukami mai Matsayi agwannati Tun ballatana ma Dakarun Sojojin Dake yawo a Haraban Gidaan

 

 

Da sauri ta balle murfin mota ta Fito da gudu Ta Kwasa Zuwa Cikin Gida Da Jakarta ta Mkranta Goyo Abayanta.

 

Daga Mallam Inuwa Har Bello da Kallo Suka Bita Shi Mallam Inuwa Mirmishi yayi yana Kada kai, Shi kuma Uncle Bello Tsaki yaja Takaichin Aneesa kamar ya Kasheshi yarinya kamar Haihuwar Hauka Bai Tsaya Sauraran Gaisuwan Tsiraran Sojojin Dake Haraban Gidan ba ya Kama Hanyar Wani makeken Mension mai Dauke da upstair Inda nan na Shashen Uncle Bello Shi kadai Mai kama da Wajen da Za”a Saka mata Goma ma Babu Wanda ya Matsu Wani.

 

Itako Aneesa da ihun Kiran Anty Rahila Ta Shiga Wani Katon Falo mai kama da Aljannar Duniya Tana Fadin”Anty Rahila.,Daada Ku Fito na Dawo Hibbata kina ina Yau na gama Wahalalliyar Mkrantan nan Na Dawo gida..”Take Fada Daidai Sanda ta Shigo Tsakiyar Falon Tana Dariya Yayinda Duka Fararen Hakoranta Dake Haskata Suka bayyana.

 

Dariyarta da Murnanta Sun Dauke ne Lokacin Da Suka Hada Ido da *Zubaida* da *Zulfa* wadanda Ke Hakimce Kowacce Ta Samu Daya Daga Cikin Kujerun Falon Ta Zauna Tana Dannen Waya Gefe Daya Kuma suna Kallon Katon Wani Magijin Talabijin Wanda yakusa mamayen Bangon Wajen, yan mata ne masu ji Da kansu,Zulfa ce Fara Zubaida kuma Chaculate Colour ce,Dukkansu Atare Suka Dago Suna Sakarma Aneesa Wani Matsiyacin kallo Lokaci Daya Suna mata kallon Sama da Kasa kafin Su Hada Ido Lokaci Daya Suka Saka mata Dariya Zulfa ce tace”Ikon Allah yan Makarantan boko ko Ansha Wuya…”Tafada Tana Kara Saka Dariya.

 

Abun ya mugun batama Aneesa Rai Ta Kallesu Awulakance Kafin Ta Saki Siririn Tsaki Tana Fadin”Aikin banza Tusa Alasifika Wanda Dai Ake Zuwa Domin Shi bai san Anayi ba Andai Fadi ba Nauyi Wlh..”Tafada Lokaci Daya Tana Runtumawa Da Gudu Zuwa koridon da zai Sadata da Sashen Anty Rahila Wacce Taji Karadin Muryan Aneesa Ta Nufo Falon Hannunta Rike dana Hibba,Suka Ci karo da Aneesa Ta Kwaso da Gudu.

 

Anty Rahila tace”Innalillhi Anne Bi Ahankali Mana..”Wata Mata nagani Baka mai kyau da Dogon Hanci Kallo Farko In kamata Zaka Ga Tsantsan Kamar da Suke da Aneesa,kallonta Aneesa Tayi kafin ta Rumgumeta Tana Fadin”Anty Rahila nagama karatu..”Take Fada Tana Dariya kafin ta Saketa ta Rarumi hibba yar Shekara Hudu Dake Mata Dariya Tana Fadin”Annee..”Cikin Muryan yara Cafeta sama Aneesa Tayi Tana Fadin”Hibbatullahi Kin kara girma..”Anty Rahila na Gefe Tana kallosu Tana Mirmishi Aranta tana Fadin”Anee Sarkin Rigima wai tagama karatu..”

 

Dagachan Falon Kuwa Zulfa Ta kalli Zubaida tana Fadin”Kan bala”i Dawa Wannan yarinyar Take..?”Wani kallon Wacece Sakara Zubaida Tamata kafin Tace”Da wanda ya Tanka mana Nidai kinsan bana Sakarmata Fuska Tunda na gane bata da Kunya Gashi Daada Ta Daure mata Gindi Ita da Daddy ba Daman Ayi magana sai Suce yarinta Ke Damunta..”

 

 

Wani Uban Tsaki Zulfa ta Saki kafin Ta Mike Tana Fadin”Ni babu Ruwana Tana Kawomin Raini Ubanta Zanci ai gwanda mu gidan D’an Kanin iyayenmu muke itafa Kalan Dangin Daga yayarta na Auren Daddy Shikenan Aka Taremana Agida..”Tafada tana Tafiya Zuwa Falon Anty Rahila da kallo Zubaida ta Bita Dashi Kafin ta Saki Mirmishi Ta Mike Tsam Tana Kara gyara Fuskarta Acikin Madubin Wayarta ta Nufi Hanyar da Zai Sada ta da Waje Cikin Wani Yanga Kamar Wata Wahainiya.

 

Koda Zulfa fa ta iso Falon Na Anty Rahila Tuni Aneesa ta Dauki Hibba Sun Shiga Shashen Daada Tsohuwa mai Ran Karfe Kakarsu Bello da ya Mukatar Ita ta Haifi Mahaifiyarsu Hassatu,Anty Rahilan Kadai Ta Iske Tana ma Mai Aikinsu Jumai bayanin Abunda Zata Dafa Tunda Bello ya Dawo,Ganin Suna mgana yasa bata Tanka ta ba sai Ta samu Daya Daga Cikin Kujerun Falon Ta Zauna Wanda Shima iya Tsaruwa ya Tsaruwa An Zuba Dukiya Sosai.

 

Sai da Anty Rahila ta sallami Jummai kana ta Kariso Tazauna Kusa da Zulfa Tana Fadin”A”ah Zulfa ya”akayi ne…? Dan Sakin Baki kadan Zulfa tayi kafin tace”Wai ni Anty Rahila Tare da Uncle Bello Aneesa Ta Dawo…”?Anty Rahila ta Murmusa kafin tace”Eh Tare Suka Dawo..”Tafada Tana Gyara zaman Sarkan Azurfan Dake Wuyanta.

 

Baki Zulfa ta Washe Cikin Farinciki Tace”La! Da Gaske..?Shine bai Shigo ba..? Anty Rahila Ta Mike Tana Fadin”Ai kinsan bazai Shigo yanzu ba May be sai Daddy ya Shigo Tukunnah..”Mikewa Zulfa tayi Tana Fadin”Kai Naji dadin Dawowar Uncle bello Daman Domin Shi nazo Wannan Hutu bari na Shiga Kichen na hadamai Dinner kafin Anjuma..”Tafada Tana Nufar Hanyar wani dogon Korido Wanda Zai Sadaka da Kichen din Gidan Gabadaya.

 

Da kallo Anty Rahila tabita kafin ta Dan Murmusa Afili tace”Dama baki Wahalar da kanki ba Zulfa indai Bello ne zaki yi Nadama Kila Sai kinyi kuka..”Tafada Tana Komawa ta Zauna lokaci daya tana yar Dariya Tuna yadda Zasu kwashe da Bello in ma ya gansu Acikin Gidan Balle ma Wannan Rawan Kafan da Zulfan keyi kuma ko Ita Zubaida Itama Saboda Bellon Tazo Gidan Kuma ta sani Duka iyayensu sun Turosu ne Saboda Ko Bello zai Gani ya kyasa,kamar basusan Waye Bellon ba.

 

Dagachan Shashen Tsohuwa Daada Kuwa Aneesa na Hango Zaune kusa da Wata Farar Dattajiuwa mai kimanin Shekarun 66 aduniya Daga ganinta kaga Bufullatana Ta Gaba Da baya,ga Zanensu na Fulani nan Agefe da gefen bakinta Kana ganinta Zaka Tsinkayi Inda Bello ya Samu Hasken Fata da Kuma kyau,bata Sha Wuya ba Domin Kudi da Jin Dadi Sun Zauna mata zaune take kan Wani Lafiyayyen Jan Cafet Dake malale Cikin kayatacen Hadadden Falon wanda yaji Alatun Rayuwa Tana Sanye da Riga da Zani da Dankwali Hakoranta Suna Washe ne har Hakoran Makkanta Guda Biyu Suka bayyana Daga ganin yadda Take Dariya Tana Dafa Cinyar Aneesan zaka san Lbrin da Aneensa Ke bata ya mata Dadi Sosai

 

Kanta Daada ta Shafa kafin tace”Dakata da lbrin nan Anee Hakanan Tashi ki Tube kaya Kiyi Wanka kiyi sallah kici Abinci sai kizo mu Cigaba Ko kin manta yau Tare zamu Kwana Kiyi Ta bani lbrin Mkrantar Har ki gaji kinji ko..”Aneesa Na Dariya Ta Mike Tana Fadin”Hakane Kuwa Daaada Naji Dadin Gama Karatun nan Dama na gaji Da Mkrantar Da Wahalar Cikinta..”Daada tace”Koni nayi Murna Ina Dadi Irin Wannan Uban Wahalan Dakike bani lbrin Ana baku Ai Shima laifin Mukatar din Dayake Biyema Yaron nan Bello ne”Aneesa na Dariya Jin Daada ta Ambaci bello wanda ba ta iya kiran sunansa saboda sunan marigayi mijinta ne kakansu Bellon kenan

 

Bedroom dinta ta Shige wanda ke kusa da na Daada ta Fada Tiolet Cike Da Fara”a Domin Tasan Daada bazata bari Akara maidata Wannan Shegiyar Mkrantar mai Aljanun Tsiya ba.

 

Shigarta ba Dadewa Anty Rahila ta Shigo Dauke da Trolley din Aneesa da Jakunkunanta Guda Biyu Tana Fadin”Aneesa ba Hankali chan ta bar Kayan Nata Sai da Mallam Inuwa ya Shigo Dasu..”Daada dake Wasa Da Hibba Tace”Ina Ruwa Anee yan Mkranta Tadai Shigo ita kan Abunta..”Tafada tana yar Dariya Cikin Bedroom din da Aneesa ta shiga Ta Shigan Mata da kayan Ta Fito ta isketa Haryanzu Tana Wanka Bata Fito ba nan ta Zauna Falon Daada Suna Cigaba da Hira Sama Sama.

 

****

 

Zubaida kuwa Cike da yanga Ta Isa Mension din Uncle Bello Wanda Ke upstairs Matattakalan Benen Tafara Haurawa Tanayi Tana Kara gyara Tafiyarta Har ta Iso Kofar Falon Nashi Ta saka Hannu zatayi Kooking kenan Taji Kofar ta Bude Kanta Cikin Jin Dadi Ta Tura kanta Falon da yar Siririyar sallamarta Lokaci Daya Kamshin Turaransa na MAN ya Daketa Wanda Duk Duniya ba Jikin Wanda Take Jin Dadin Kamshin Turaran Irin Jikin Uncle Bello Wanda Hatta bangarensa ma ya Saba da Kamshin mai Dakin..

 

Falon mai kalan Blue and black ne Babu Kowa aciki sai Karan Talabijin Dake Tashi Shi kadai,Takawa Tafarayi Zuwa Tsakiyar Falon tana bin Ko”ina da Kallo Cikin Burgewa,Jin Shuru kamar babu Motsin Kowa yasa Zubaida ta Nufi Cikin Bedroom din Uncle Bello ta Tura ahankali ta Shiga Tana Sanda kamar Wacce Zatayi sata

 

Wani kamshi mai Hade da Sanyin Dadi ya Daketa Lokaci Daya Lumshe ido Tayi Tana Sauke Tagwayen Ajiyar Zuciya kafin Tafara bin Dakin da Kallo Komai Very Net,dashi Koda bayanan Anty Rahila bata barin Bangaren Bello Da Datti Duk Bayan Kwana Biyu Zata Saka yan Aikin bangaren Share Share Su Shiga Su Tabtacemai,Makeken Royal bed ne ya Cinye dakin Sai Dressing Mirror sai Wani Wargajen Wardrope na Glass Wanda Shima ya mamaye Rabin Bango Daga Gefe Kuma Ma”ajiyar Takalmansa ne gasunan Burjit kama Daga Rufaffu na Fatar Damisa da Budaddu,Sai Wanda yaga Dama zai Saka Daga Cikin Wani Korido Kuwa Kofar Tiolet Dinshi Ne,Maida kallonta Tayi Bisa Side Drower din Gefen Gadonshi nan ta Iske Wani karamin Hoto Cikin Frem Da Hanzari Ta karisa ta Dauka Tana kallo

 

Shida Muktar ne da Wata Farar Mata Wacce kana ganinta kasan Mahaifiyarsu ne Saboda Tsabar Kamar da Suke da Juna Kurama Bello ido Tayi yana Rumgume Jikin Mahaifiyarsu Duka Hakoransa na Waje,Hannu ta Sanya Tana Shafa Fuskarsa Wani Shauki na Kwasanta Bata ji Fitowarshi ba Sai ji Tayi An Daka mata Tsawa Da Cewa..”Ke.! Waye Anan…? Yafada Cikin Muryan Sanyi Ammh Cike da Fada

 

Jin Muryansa Daga Sama ya Sanya Tsoro ya Shigeta Tana Kokarin Ijiye Hoton Jikinta na Rawa Taji ya kara Daka mata Tsawa”I said Who are u…? Yafada Wannan karon Cikin Alamun Fushi Tsautsayi ya saka Hoton Bai zauna ba ya Subuce ya Fado Jikake Tass..! Glass din ya Fashe Gaban Zubaida ya Fadi Jikinta na Rawa Ta Juyo Saboda Sanin Waye Bello ba Karamin Aikinshi bane ya Mata Dukan Tsiya babu Ruwanshi

 

Shiko yana Tsaye sanye da Karamin Towel A kugunshi Wani kuma Bisa kanshi yana Tsane Ruwa Gabadaya Ranshi ya kara baci Lokacin Dayayi Tozali da Zubaida,Ta juyo tana kallonshi Cike da Tsoro Cak ya Tsaya yana Kallonta Sama da Kasa Cike da Raini Yace”U….? Yafada yana Sakin Wani killer Smile Wanda Aneesa tama Lakabi da Dariyan Mugunta

 

Jikin Zubaida na Rawa tafara Fadin”Am Srry Uncle Bello naji Dawowarka Shine nazo maka Sannu da Zuwa…”Tafada Tana Hada Numfashi Ko kallonta baiyi ba Ya Juya ya Isa Dressing Mirror Dinshi Ranshi na kara baci In Ya Budi Ido yakara ma Kallon Fuskarta Domin Yana kallon Fuskar Mugun Mahaifinta Aciki Wato Abba Kabiru,Shi bai san Meya kawosu ba,Lokacin da Suke Neman Taimako basu Taimakesu ba Suka Cinye Dukiyar Mahaifinsu Suka Wofintar da Rayuwarsu yau ba Domin Daada ba Kila da Tuni Yunwa da Wahala Ta kashesu Shida ya Muktar… …

 

Yafada cikin Ranshi yana Gogama Kanshi Wani oil,Cikin Sand’a Zubaida Ta kama Hanyar Fita ganin Kamar baya Ganinta Ta Dora Hannunta Kenan kan Handle din Kofar taji yace”Ubanki ne zai Kwashe miki Abunda Kika Fasa…? Ko kuma Ni…? U better be Carefully In ba Haka ba Wlh Sai naci Uwarki Yanzu Acikin Dakin nan Tunda naga alaman kin Rainani..”Yafada Bai Waigo ba Kuma Hankalinshi Kwance yana Cigaba da Abunda yakeyi.

 

Tsoro ya kara kama Zubaida Aranta Tana Fadin Ta kawo kanta.,Jikinta na Rawa Ta Fara Fadin”Kayi…yi..Hakuri Zan Gyara…”Ko kallonta baiyi ba Yabuga mata Tsawa”Get Out…Kazama kawai ..”Yafada Harda Sakin Saki Jikinta na kyarma ta Bude Kofa ta Fice kamar Zata Kifa Wani Bakinciki ya Kamata Ta Fito tana Share Kwallah Wai Har yaushe ne Bello Zai Daina kyaransu Tasani Tuni ya Fahimci Tana Sonshi Hatta Zulfa ma ya Dade da Fahimta Ammh Duk Lokacin da Suka Hadu da Juna sai yaci Zarafinsu Wata Zuciyarta tace karki manta Har iyayenku bai kyale ba.

 

Ajiyar Zuciya ta Sauke Tana Dauke Kwallarta daidai Lokacin Data Sauko daga Steps din Motocin Ya Muktar suka Shigo Gidan Shiya Hanata karisawa Cikin Babban Falon Gidan,Agaban Idonta Wani Soja ya Budemai Murfin Motarsa Benz2k20,ya Fito Sanye Cikin Kakinsa na Sojoji Hulan kansa Kuma Tana Rike Ahannunshi,Da Mirmishi Zubaida Ta karisa gareshi Aranta Tana Fadin”Ga mai Kirkin gidan ya Dawo..”

 

Tundaga Nesa ya Hangeta sai ya Saki Ranshi Ya juya yana Mgana da Wasu Sojojin Dake bayanshi Cikakken Dogon Namiji ne mai Dattako da Kamala Dan Kimani Shekaru 59 aduniya Fari ne Ammh bai kai Bello Hasken Fata ba Sosai,ammh Kusan yanayin Tsarin Fuskarsu Daya sai dai Shi Muktar yana da Fadin Fuska Kadan Da Kuma Jiki irin ta Cikakkun Maza masu Jarumta da Sadaukanta,a kallo Farko Zaka Fahimci Tsantsan Hakurinsa da Kamewarsa *LT.GEN.MUKTAR MUHAMMED JIKAMSHI* Kenan Chief Army of Staff na Kasa Baki Daya Namiji ne mai Kishin Kasarsa da kuma kishin kansa Mai Fara’a Da Barkwancin Sabanin Bello da Yake Miskilanci mara son Jama”a Da Fara”a a komai dai Sun Samu Sabanin Halaye Sosai.

 

Cikin Fara”a ya Wareta Mata Hannunshi yana Fadin”My Dota Come here…”Da Hanzari ta karisa Ta Fada Jikinsa Tana Fadin”Welcm Home Daddy…”Rumgumeta yana Shafa kanta Kafin ya Dagota yana Fadin”Thanks Dota..,Daga Ina Kike Haka..? Yafada yana Rike Hannunta Suka Nufi Kofar glass din da Zata Sadasu da Cikin Gidan,Jin tambayan Dayayi mata ya Sanya Idonta ya Ciko da Hawaye Cikin karaya tace”Shashen Uncle Bello naje Daddy Naje yimai Sannu da Zuwa ne ya Koroni Harda cemin Kazama..”Tafada Kwalla Suna Zubomata Tunda ta ambaci Bello yake Mirmishi kafin ya Waiwaiya yana kallon Motocin Wajen Sai yanzu ya lura da Motar Mallam Inuwa Direba Domin Shine Amintattacen Direbansa Wanda ke Mu”amalan Cikin Gida da iyalanshi.

 

Hannu ya Sanya yana Dauke Mata Hawayenta Kafin yace”Don’t Wrry Stop craying kinji ko..?gyada mai kai tayi kafin Takara Share Kwallarta Mirmishi ya Sakarmata kafin tayi gaba Shikuma ya Biyota Abaya yana Kallonta Acikin Ranshi yana Nanata”Bello bazai Taba Chanzawa ba..”Yafada Yana Sagale Hulansa Wajen Hammtarshi Lokaci Daya Kuma yana Sakin Mirmishi Cikin Muryan Zatinsa ya Sako kanshi Falon Tare da Sallama.

 

 

*MR BELLO..!*

_(The young Teacher)_

 

*Wattpad:Janafnancy13*

_Mallakar:Janafty

 

*A page 2 ansamu Kuskure akan Wajen da zanyi Numbaring Shekarun Ya muktar da Daada,Am very Sorry shekarun ya Muktar 49 Daada kuma 76 ne….Tanque so much Mr Farooq❤️ for d Correction…Na Tabbata bakya karatun littafan Janafty da Zuciya kadai kina Hadawa Da Sarrafa kwakwalwarki… Son so Fisabilillah*

 

*🅿�?3*

 

Falon Farko Babu Kowa Sai Talabijin Dayake Ta Faman yi Shi kadai,Kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon Zubaida ta Zauna Tana Fadin”Daddy Anty Rahila Inaga Tana ciki..”Kallonta yayi kafin yace”Ok…Taso mu Shiga ya zaki zauna Anan ke kadai..”Jim tayi kafin Ta Mike tayi Gaba ya Biyota Har Zuwa Falon Anty Rahila Nan ma Shuru,Suna tsaye sai ga Zulfa Ta Fito Daga Kichen da Faranti Shake da Kolili da Jug da Kofuna Baki ta Washe Tana Fadin”Lah Daddy u are wlcm…”Mirmishi ya saki kafin yace”Thanks Zulfa Dota..”Yafada Yana D:an Bin Falon da kallo.

 

Zubaida Ta kalleta kafin ta Samu bakin Mgana Alheri da Jumai ma”aikata gidan Sun Fito da Manyan Wasu Food Flks masu Kyau,ganin Daddy Tsaye yasa Suka Ramkwafa Suna Gaisheshi ya Amsa Cikin Sakin Fuska,Kafin Su Wuce Zuwa Babban Dinning Din Dake Gefe Guda Daga Cikin Kayatattacen Falon.

 

Da kallo Zubaida Ta Bisu Kafin Ta maida Hankalinta kan Zulfa Wacce Ta Nufi karamin Center Table din Dake Falon Ta Dora Farantin Tana Fadin”Daddy inaga fa Anty Rahila na Shashen Daada…”Tafada Tana yarfe Hannu,kafin yayi magana tace”Let me call her..”Da Hannu ya Dakatar da Ita yana Fadin”No need Dota bari na karisa Ciki..”Yafada yana maida Hulansa Bisa kai Mirmishi Tayi kafin Tace”Ok Daddy..”Bai Kara Bi Takansu ba ya Shige Koridon Da Zai Sadashi da Dakin Daada.

 

Sai da ya Kule Kana Zubaida ta Kariso gaban Zulfa Tana Fadin”Ke kadai yau zaki Taking Dinner…? Yamutsa Fuska Zulfa Tayi kafin tace”A’a me kika gani Hala..? Tafada Tana Kokarin Shashantar da Zencen.

 

Zubaida tabi Abincin Dake gaban Zulfa da kallo Tace”Dis..”Tana nunawa da Baki Wani Mirmishi Zulfa Ta Saki kafin tace”Oh..! Is for My Uncle Bello..”Tafada Cike da Wani yanga Kamar Tana gabanshi Wani Kallo Zubaida ta Watsa mata kafin Tace”Ur”s..? Fari da ido Zulfa ta mata kafin tace”yes of Course…'”Tafada Tana wani Tsuke baki.

 

Kallo kallon Suka ma Juna mai Cike da Jin Haushi da Kishi kafin Zulfa ta Kauda kai ta Tafara Taku kamar Zata Fice Daga Falon tana Fadin”Let me take my Shower First…”Take Fada Tana Kada Mazaunanta Da gayyah har Tayi Kwana zuwa Wani Korido inda Shashen Saukan baki yake,Da Kallon Bakinciki Zubaida Tabi Zulfa kamar ta Shakota Takeji,

 

Kugu ta Rike Kafin Ta Fada Bisa Kujera Tana Dafe kai Cikin Sanyin Murya tace”Oh my goodness…”Take Fada Tana Tattare Naman Goshinta Waje Daya Cike da Damuwa Lokaci Daya Ta Saki karamar Ajiyar Zuciya Ita Fargabanta Daya kada Zulfa ta Sace Zuciyar Bello da kyawunta Da Kuma kyan Jikinta Domin ba karya Zulfa ta Cika Mace da Kowani Namiji zai yi Fatan Mallaka Tafita komai Ta bangaren Cikar mace,Tuna Hakan Datayi ne yasa Ta Mike Tana Fadin”No…it’s can be…”Kafin Ta Yi Mirmishi ta Furta..”We shall See Zulfa..’

 

Tafada Tana Sakin Numfashi kadan Cikin Sassarfa Ta Nufi Hanyar da Zulfa Tayi Gefe Daya Kuma Tana kallon Alheri da Jumai da Suketa kaida kawon Jera Abinci Bisa Dinning Table.

 

****

 

Tun Kafin ya kariso Kofar Falon Yaji Muryan Daada Suna Hiran Aneesa Ita da Anty Rahila Mirmishi ya Subucemai kafin yace Afili”D 2 sturborn are back…”Yafada yana Tura Kofar Falon ya Shiga Da Siririyar Sallama

 

“Assalamu Alaikum…”Yafada yana Washe Baki Atare Daada da Anty Rahila Suka Dago Suna kallon Kofa Lokaci Daya Suna Amsa Sallamarsa,Cikin Fara”a Daada tace”Ah babban Mutum Andawo…? Tafada Cike da Fara”a Hibba ko Da Gudu Tatashi Daga Jikin Daada ta Nufeshi Tana Fadin”Daddy…”Takalmin kafarsa ya Salube kafin ya daga Hibba Sama yana Fadin”Oh my God….my One and Only Dota Hibbatullahi…”Yafada yana Sabata a kafadansa Tana Dariya da Fararen Hakoranta ta Saka Hannu ta Cire hulan Kansa ta Dorama Kanta tana Fadin”Daddy Toja…”Tafada da Muryan yarinyata.

 

Dariya ya Saka yana Fadin”Yes my Princess..”Yafada yana Sakarmata Kiss a gefen baki Anty Rahila Data Mike Tsaye ta Kariso Tana Fadin”Daddy Sannu Da dawowa Thank god Mijina Is Back Safely…”Tafada Tana Jifanshi da Wani Shu”umin Kallo.

 

Dago da kanshi yayi yana Fadin”Thanks Rahi Queen…”Yafafa kafin ya Fara Takowa Zuwa gaban Daada yana Fadin”Daada wai meyasa Kike da Son Zama kasan nan ne..? Baki Hawa Bisa Cussion…”Daada Tace”Kai ni Rabani da Wani cusa Nagaji kullum Mutum na saman Abu ba Hutawa,Kune yaran zamani da Kuka lalace da Hutu mu Ada Waya san Wani Cusi…”Tafada Tana Dariya..

 

Dagashi Har Anty Rahila Dariyan Suka saka Kafin ya Zauna Kusa da Daada yana Dora Hibba kan Cinyarsa Lokaci Daya yana Fadin”An bari Daada Kiyi yadda Zaki fi jin Dadi kun Wuni Lafiya ina Anee yan Mkranta..? Yau Duka Masu Ciwon kan gidan Sun Dawo Lokaci Daya..? Yafada yana yar Dariya.

 

Daada tace”Umh Aneesa kadai muka gani Megidan nawa bai Shigo ba Tukunnah kasanshi Kila yaji Zuwansu Zulfa ne Shiyasa Yaki Lekomu Daya Dawo..”Gyada kai yayi yana Fadin”Kobama Haka ba Daada Megidan naki bayajin mgana Har yaushe ne zai Ta Rike Abunda ya Riga ya Wuce,Ayi mutum da Shegen bakar Zuciya da Naci Haba Daada..”Mirmishi Daada ta Saki kafin tace”Muhammed bello Sunan nan ya Samo Asali ne fa Muntari Sunan Kakan ku ne Wanda kaf Halayenshi Bello ya kwaso Shima Haka nayi Fama Dashi da Shigen Kafiya da Zuciya Shiyasa wani Lokacin in naga Bello na Wani Abu sai Kakanku ya Dinga Fadomin Araina..”Tafada Tana Share Kwallah.

 

Ido Muktar ya Zaro yana Kallon Anty Rahila Kafin ya daga mata Gira Yar Dariya Tayi kafin Ta make Kafada,Ta karisa ga Daada Ta Zauna Kusa da Ita tana Fadin”Daada Wai har yaushe ne zaki Daina ma Kaka Kukan Mutuwa ne..? Daada na Sharbe Hanci Tace”Har Abada ne Rahila Bazan Taba mantawa da Megidana Bello ba Kusan Irin yadda ya Soni bane ya Kula dani sai da fa yayi Shadi kafin ya samu Aka bashi Aurena..”Muktar da Rahila Suka Kalli Juna kafin Muktar yace”Ah lalle kice Kaka Shima Jarumi ne..”

 

Daada na Mirmishi tace”Sosai Ku bari Watarana Zan Baku Lbrin Kakanku da Jarumtar Dayayi Sosai Alokacin Rayuwarsa..”Kai Muktar ya Gyada kafin yace”Tom Daada..”Yafada yana Wasa da Hannu Hbba kafin yace”Wai Ina Anee yan Mkrantan Kwana Banji Motsinta bane..?Anty Rahila tace”Tana Cikin Bedroom Dazu dai Wanka na barta tayi yanzu zaka kaga ta Fito inajin bataji Shigowarka ba Andawo Ana Ta Murnan Angama Karatu gabadaya..”Tafada tana Dariya.

 

Shima Dariyan ya Saka Kafin yace”Kai…Ina Ruwan Aneesa Wato Da gaske yanzu batason karatun,Dazu ma Yaya Ali ya Kirani yana Tambayana Wai ta Natsu Kuwa..? In da Wata Mtsala na Kirsa har Abuja zai zo ya Sake Cin kaniyarta .”Anty Rahila Tace”Oh ya Allah..! Ya Ali Dodon Aneesa ne,Bata jin Tsoron kowa kamar yadda Takejin nashi..”Daada tace”Ba dole Taji Tsoronshi ba Tunda Bai da Hankali yana babba Ammh ya kama yarinya karama Kamar Aneesa yayi Ta Duka Kamar ya Zauce..”Tafada Cike da Jin Haushi.

 

Anty Rahila tace”Daada Kema kin So ganin Laifin ya Ali ne Kinfa Gannin ma Idonki Rashin Jin Aneesa Nan Ranar da Bello zai Tatafi da ita Mkranta baki ga Abunda Tayi ba Wlh ba Domin Zuwan ya Ali ba Anee bata zuwa Makrantan nan Bata Shiri da Makranta Tun tana Borno Koda Baba Nada Rai bata Zuwa Shi kuma Bayason Matsa mata Shiyasa kika ganta batajin mgana Sam…”

 

Daada Ta tabe baki tace”Toh Dole ne karatu Ku kyale yarinyarnan Hakanan Don Allah ,haba Kuduba fa ku gani Shekaru uku ammh haryanzu bata saba ba in Zata Tafi da Kuka Take Tafiya..”Muktar yayi Dariya Kafin yace”Daada Wannan Hurumim Megidan ne ki kiyi mai Mgana In ya Kyaleta Shikenan sai Asamata Wata Day Anan sai Ta Cigaba da Zuwa In kuma yaki Dole Anee ko Tana so ko bata so sai Ta Koma Makrantar nan ta Dora Daga Inda ta Tsaya Kinfi kowa Sanin Tuni ya ce na barmai Ragamar Karatunta Ahannunshi Kuma yakawomin Hujjojin Daya sanya Ya kai Aneesa Mkranta Dayake Koyarwa Kuma Nima na Gamsu In ba Bello ba Bamai iyawa da Rigimar Aneesa..”

 

Yafada Cikin Sauke Numfashi Anty Rahila Zatayi mgana Kenan Aneesa ta Bude Kofa Ta Fito Tana Fadin”Daada Ruwa Goma nayi ma kaina Allah a mkranta bama Samun Ru….”Mganarta yamakale ne na Hada Idon da Sukayi da Muktar Wanda ya Dago yana Kallonta Tana Sanye da Doguwar Rigar Atamfa Mai Red And Ash,Washe baki tayi kafin tace”Ya Muktar…”Tafada Hakoranta Duka awaje .

 

Yana Dariya Shima yace”Aneesa yan Mkranta Wlc back Home…”Da Sauri ta kariso gabanshi ta Zauna Harda Tankwashe Kafa Tafara Fadin”Nagode ya Muktar Saura Murna na Biyu..? Tafada Tana kallon Idanuwanshi Zaro Ido yayi kafin yace”Wow..Menene Shi..? Dariya Tayi Tana Kallon Anty Rahila da Daaada Tace”Baku Sanar Dashi na gama Karatun bane..”

 

Tafada Cikin Tabbatarwa,Tare da Anty Rahila Suka Hada Ido Suna Kunshe Dariya Cikin Shanye Dariya yace”Oh..Anee,Da Sauranki fa Yanzu dai zaki Shiga Shashen manya SS1 Ko ba Haka ba Rahi queen..? Anty Rahila tace”Hakane kam..”Tafada da yar Dariya.

 

Bata Rai Aneesa Tayi kafin Tace”Wa..? Wai ni zan Koma Wannan Dajin Makrantan Wanda bakomai Cikinta sai Wahala Tabdijam na Rantse da Allah Wannan karon Ko mai Zai Faru Sai dai ya Faru bazan Koma ba…”Tafada Idanuwanta na Cika da Kwallah Dukkansu da Kallo Suka Bita Anty Rahila tace”Bazaki Koma ba Kika ce Aneesa..”?

 

Idanuwanta na Zubar kwallah tace”Eh bazan Koma Wlh bazan Koma ba..”Tafada Tana Share Kwallah.

 

Ido Anty Rahila ta Bude kafin Tace”Lalle ko Ya Ali zai Zo kamar Zuwanki na Farko kin dai san Halinshi ko..? Toh Tun Wuri Kiyi Shirin Komawa Makranta da Zarar Firt time yayi Lokacin Shigan yan SS1…”Tafada Tana kallon Aneesa Wacce Tana Jin Haka ta Kama Buga Kafa Tana Kuka Harda Birgima Tana Fadin”Wlh Allah bazan Koma ba Ko Za”a kasheni Dama ba”a Sona Wayyo Baba,Baba ka Tafi ka barni bani da mai Sona Sai kai,Wayyo Baba…”Take Fada Tana Kuka Tana Wani Zabure Zabure Kamar karamar yarinya…

 

Anty Rahila da Muktar Suka Kalli Juna na Wani Lokaci Kafin Su Maida Kallonsu kan Aneesa Wacce ke Shan Hanci da Majina,Daada ce Ta Mike Ta Isa ga Aneesa Tana Fadin”Aneesa yaki nan Taso maza ki bar Wannan Kuka Matukar ina Gidan nan bamai Maida ki wannan Mkrantar Tunda baki Sonta  “Tana Jin Haka Ta Mike tana Fadin”Da gaske Daaada..”?

 

Kai Ta gyada mata Tana Mikar da Ita Tsaye Hannu Aneesa Ta Sanya Tana Share Hawaye Kafin Tace”Daada To ya zanyi da Uncle Bello..? Wayyo yaya Ali ma Daada in Anty Rahila Ta gayamai Kasheni zaiyi in yazo..”Daada ta Girgiza kai Tana Fadin”Duka ki barni Dasu Bamai Tabaki Shima Alin bazai zo ba Insha Allahu Sai dai zaki man Alkawari Daya..? Tafada Tana kallonta.

 

Cikin Saurin Aneesa Tace”Fadi komiyeshi Zan yi Miki Daada Aini kingamamin Komai Tunda Kika goyi bayana .”Daada tace”Alkawarin zaki min Matukar nayi ma Megidana Bello mgana ya kyaleki Anan To zaki Yarda Anema Miki Wata Mkrantar Anan Sai kici gaba Kinji ko..”Kuri Aneesa Ta mata da Ido Tana Tura Baki kafin tace”Nifa Daada nagaji da Karatun ne..”Daada ta Dafa kanta Tana Fadin”Toh Shikenan Zan barki Da Bellon..”Jin Haka yasa Tayi Saurin Fadin”A”a Daada na yarda Allah da dai Amaidani Wannan Dajin Da ko Ruwa fa Babu Daada,ga Aljanun Tsiya Allah Daada Muna Shan Wahala Uncle Bello baisan gaya Muku ne..”Tafada Tana Matse Kwallah.

 

Daada na Shafa kanta tace”Ai yanzu komai ya kare bazaki koma ba..”Jin Haka yasa Aneesa Ta Daka tsalle,Ta Rumgume Daada Tana ma Anty Rahila Gwalo Tana Dariya Bude Ido Tayi Tana Kallonta kafin Tayi Mgana Aneesan Ta Saki Daada Tana Fadin”Daada bari natafi nayi sallah Ana Kiran Mangariba..”Tafada Tana Shigewa cikin Bedroom dinta.

 

Ajiyar Zuciya Muktar ya saki kafin ya Shafa kanshi yana Fadin”Daada Bazaki iya Tankwasa Bello Akan Aneesa ba Why Kika mata Wannan Alkawarin…”? Daada na Kokarin Shiga Dayan Bedroom Din Tace”Dole ya barta Tunda bata so Shidai dayake so sai ya Koma Shi kadai kar Abun ya Zama Zalunci..”Tafada Tana Tura Kofar Bedroom Din Ta Shige Domin Dauro Alwala.

 

Shuru yayi yana Nazarin Abun Acikin Ranshi kafin ya Dago yana Kallon Rahila yana Fadin”Bansan ya Zanyi da Bello ba Rahila…Yana Sakani Ciwon kai..”Mirmishi Tayi kafin Ta Mike Tana Fadin”U will Discuss later yanzu ka Tashi muje Sama kayi Wanka ka Sauya kaya kayi Sallah sai mu Sauko Dinner..”Baiyi Gardama ba ya Mike Yana Rike da Hibba Hulanshi ta Sojoji Ta karba kafin ya Riko Hannunta,dayan hannun Kuma yana Dauke da Hibba Suka Fice Daga Falon Daada Zuwa Sheshen Rahila Steps Suka Haura Zuwa Sama Inda Dakunan barcinsu yake

 

******

 

Zaune Yake Atsakiyar gadonsa yana latse latsan Laptop din Dake gabanshi Sanye da Riga da Wando Masu Ruwan Toka na Jc,Tun Dazu yakejin Karan Mad Door,bai maida Abun Serious ba Domin yana Kyautata Zaton Zubaida ne Tsaki yaja ya Cigaba da Abunda yakeyi kamar bai ji Mad Door din Da”ake ta Danna mai ba,Ransa bace yake tun bayan Fasa mai Hoto mai muhimmanci datayi dayace ta dawo ta kwashe sai ta gudu dole shi ya tattara glass din Hoton kuma ya Zareshi cikin gidan Album din ya sakashi cikin Durowar gadon.

 

Zulfa Dake Tsaye da Faranti Taci Kwalliya Cikin Wata Doguwar Abaya na Kamfanin Armani ta yane kanta da Karamin Bakin gyalen Kayan,Fuskarta ta Dauki Haske Saboda yadda ta Tsaru da Kwalliya Tafi Minti goma Sha Biyar Tsaye tana dannan Ring Ammh ba Alamun za”a azo Abude Cikin Bacin Rai da Kufuluwa Zulfa tace”Plz Open d Door Uncle..”Tafada kamar Tayi kuka ganin Tsayuwa na Neman gagararta gashi Tagaji yasa ta Juya Tafara Saukowa daga Steps Din Jikin Sanyi Jiki da Nadama mai Tsanani.

 

Dukkansu Suna Bisa Dinning,Anty Rahila,Muktar,Daada,Aneesa Hibba,Zubaida Suna Dinner Suka ga Shigowar Zulfa Falon da Sauri kamar Zata Kifa Dauke da Tiren Abinci Riki Riki Tana Kwalama Alheri kira Gabadayansu da Kallo Suka Bita kar Zubaida Taji lbri Wacce Tun Fitan Zulfa Zuwa Shashen Uncle bello Taji ta Kasa Natsuwa ganinta Cikin Wannan Fushin yasanya Zuciyarta Tayi Sanyi Har Mirmishi ya Wanzu Akan Fuskarta.

 

Cikin Mamaki Anty Rahila tace”Oh”ah…Zulfa ya kuma kika Dawo Da Abincin Bellon ya Fita ne..? Zulfa na Kokarin Daidata kanta tace”He is not open d Door Anty i Did know if he is Inside da Room…”Tafada Daidai Lokacin da Alheri ta kariso ta Mika mata Farantin Kenan Anty Rahila Ta Mike tana Goge Bakinta da Tissue tace”No Wait Bari na kaimai Tunda ya Dawo fa baici komai ba ya Allah! Bello nasan Horan kanshi da yunwa..”Tafada tana Karisa wa ga Zulfa ta karbi Farantin Kololin Tana Fadin”Hibba Bring my phone..”Muktar ya Dauki Wayar Rahilan Dake Kusa Dashi ya Mikama Hibban ta Sauka Da Gudu Zuwa Wajen Anty Rahila wacce Tayi gaba Tana Fadin”Keep Follow me Princess..”Jin Haka yasa Hibba Tabita Suka Fice Daga Falon.

 

Aneesa Dake kallon Zulfa Tunda Ta Shigo Ta Saki Dariyan Datake kannewa Da Mamaki Zulfa ke kallonta Cikin Kuluwa tace'”Ke  Aneesa Wa Kike ma Dariya..”?

 

Tafada Tana Karisowa Wajen Babban Teburin Aneesa Ta Dago Tana Kallonta Cikin Rainin Wayau tace”La Anty Zulfa Nifa bada nake ba Me kikayi balle nayi Dariya..”Tafada Tana Kara Sakin Dariyan Wanda ya kara Harzuka Zulfa ta Kariso Azuciya Zata Daki Aneesa Daada Tace”Ke miye Haka..? Daga Tana Dariya sai kice da Ke Takeyi Hala Kinyi Wani Abun Dariyan ne. ? Nifa bana son Mugunta Zulfa’u..”

 

Tafada Hankalinta Kwance tana Sharban Ferfesun Kayan Cikinta Turus Zulfa Tayi Tana Bin Daada da kallo Ita da Aneesa Wacce Take Kada kai Tana yar Dariya,Muktar ne yace”Zulfa Sit…”kallonshi Tayi Hawayen Datake Rikewa Suka Zubomata Mai Zubaida Zatayi In ba Dariya ba Harda Dukawa kafin ta Mike tana Goge Bakinta da Tissue Cikin Muryan Shakiyanci Tace”Lost Zulfa…”Tafada Harda Dafata tana Kada mata ido kafin ta Wuce Tana yar Dariya Zulfa Ta kawo Wuya da Hanzari Ta Bi bayanta tana Kiran Sunanta Cikin Muryan Kuka Cike da Fada Bayansu Muktar da Daada Sukabi da Kallo Aneesa Ko kamar ta Zuba Ruwa Akasa Tasha Saboda Jin Dadi Aranta tace”Wahalallu Sai kuyi Tayi indai Wannan Mugun ne baku ma gama Wulakanta ba.

 

Ita kanta Anty Rahilan Tayi ta Danna Mad Door din ammh Shuru Sai ta kalli Hibba Tana Fadin”Bani Wayar Princess..”Da Hanzari Hibba Ta Mikamata Da Dubara ta Rike Wayar kada Farantin Hannunta ya Subuce mata ta Lalubo Nombar Bello.

 

Yana Tsakar Aiki yaji Ringing Din Wayarsa Cikin Kasala ya Jawota sunan *ANTY* ya Fito baro baro Da Sauri ya Daga yana Fadin”Anty…!” Cikin Sauri  Anty Rahila tace”Ina Kofar Mension Dinka Bello…”Tafada da Alamun Gajiya da Hanzari ya Datse Kiran ya Dira daga kan gadon ya Bude Kofar ya Fice Daga Bedroom Din da Sassarfa Zuwa Falo da Hanzari ya Bude Kofar yana Kallonta da Hibba Dake Tsaye Cikin Mamaki ya kariso Fitowa yana Fadin”Am Srry ban…”Is ok bello Help me Wit Dis..”Ta Katseshi Tana Mikamai Farantin Hanunshi karba yayi yana Basu Hanya Lokaci Daya yana Fadin”Oh my God Our Little princess u are Wlmc..”

 

Yafada yana Kallon Hibba Wacce kemai Dariya Tana Fadin”anchu..”da Muryanta na Yarinya Shigewa Sukayi ya Tura Kofar da Kafa Karamin Center Table din Tsakiyar Falon yaja ya Ijiye Farantin yana Fadin”Anty Banzaci ke bace..”Tana Zama Bisa Daya Daga Cikin Kujerun Falon Tace”I know..”Tafada Tana kallonshi Hibba ya Dauka Wacce Ta Dafemai ya kariso Kusa da Ita ya Zauna yana Fadin”Anty ya gida..? Daada na lafiya..?

 

Anty ta kalleshi kafin tace”Bansani ba Bello..Meke Damunka ne Tunda Kuka Dawo baka Shigo ba ko Abinci baka Nema ba,Kana so kullum yayanka ya Dinga Fushi Dakai bakajin Mganarsa Komai yace baka bi sai dai Naka Ra”ayin..”Bello ya Zaunar da Hibba kan Cinyarsa yana Shafa kanta kamar Bazai yi Mgana sai Chan yace”No Anty Ba Haka bane u know my problem Bazan iya Shiga Barayin ba Indai yaran nan basu Barmana gida ba I Mentiond it..”Kura masa Ido Tayi Kafin tace”Naji Ammh kasan yayanka bazai koresu ba kuma Infact is ur Family bello..”

 

Cikin Halin ko In Kula yace”they are not my Family Anty At All,Only yaya and Ur,Daada and Hibba…Kune Ahalina…”Yafada yana Kokarin Danne Fushinsa.

 

 

Ganin yanayin Daya Shiga ne yasa Tace”Is ok..Take ur Dinner ok..” kai ya gyada mata kafin yace”Insha Allah Anty..”Yafada yana Kallonta Cike da Kulawa Mikewa Tayi Tana Fadin”Hibba come let go..”Hibba ta Sauko daga Jikin Bello tana mai Bye bye Yana Mirmishi ya Daga mata Hannu Mikewa yayi Sanda Anty Rahila ta kama Hannunta Zasu Fice Daga Falon Cikin Muryansa ta Kasaita yace”Anty ki gaida yaya..Am plz Take Good Care Of Him karki barshi yayi Damuwa saboda ni U see am ok..”Juyowa Tayi kafin tace”Ok i Will…”Tafada Kafin ta Fice Daga Falon Shi kuma Ya Bita ya Kulle Kofar.

 

Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya Kimikimi Tiren Zuwa Kichen Cikin Fridge ya Sakashi Domin baya Jin Wuya yanzu yagama Shan Tea sai dai da Safe Falon ya Dawo yana Faman zagaye Wajen Duka Hannayensa Sarke Abayansa Fuskarsa Tana bayyana Damuwar Daya ke Ciki Duk da baya bama Hakan Muhallin Bayyana Cikin Wasu Dakikai Abubuwa Dadama Suka Fara Dawomai Cikin Kwakwalwarsa..

 

*Shakira…* *MR BELLO..!*

_(The young Teacher)_

 

*Wattpad:Janafnancy13*

_Mallakar:Janafty

 

*🅿�?4*

 

*#FLASH BACK…*

 

🌟 *ALHAJI MUHAMMED HASHIM JIKAMSHI* Shine Asalin Sunan Mahaifin Bello Da Muktar Wanda ya Kasance Haifaffan Garin Jikamshi ne,Dake Hukumar Da’n Musa Dake Cikin Babbar Jahar Katsina.

 

Alhaji Hashim Mahaifin Muhammed Ya kasance Ma”aikacin Hukumar Wutar Lantarki na Garin Jikamshi Yana da Rufin Asirinshi Daidai Gwargado,Matarsa ta Farko Hajiya Maryam Ta kasance Yar Dangi ce Auren Zumunci Akayi musu Ita yar nan garin Jikamshi ne,Wata tara nayi Ta Haifo Kyakyawan Danta Namiji Aka Sanya Masa Suna *KABIRU* Sai Haihuwanta na Biyu Ta karayin *ABUBAKAR* suna Kiranshi Garba,wanda Tsakaninsu shekara Daya ne.

 

Tana da Cikin na Uku Hashim ya kara Aure da Wata Yar Malumfashi mai Suna Aisha Auren Dayasha Mganganu Sosai Har Saida maryam Tayi yaji Zuwa gida Saboda Ta Tada Hankalinta kan Hashim bazai kara Aure ba Shi kuma yace Sai yayi Toh iyayensu mata ba Wanda ya Goyi bayanshi Saboda Maryam Iyayensu maza ne Suka Shiga Mganar Har Maryam Ta Koma Gidan Hashim Akayi Biki Lafiya Aisha Tatare Agidan Mijinta.

 

Tun Zuwan Aisha gidan bata taba Jin Dadin zama da Maryam da ya”yanta ba Saboda yadda Take Nuna mata Tsana Kirikiri Hakama Dangin Hashim Din Sun Koma bayan Maryam, Aisha ta Zama bata da Wani gata agarin Jikamshi Tunda Ita iyayenta Sunyi Nisa,Tana Shan Wahala Wajen Maryam da Dangin Hashim Ammh ko Sau Daya bata taba Furtama Hashim ba Sai ma Kokarin Farantamai Cikin Hanyoyi Dadama Wannan Shi ya Taimaka Wajen Bata matsayi mai Girma Acikin Zuciyar Hashim Uwa Uba ga Hakuri da Kawaici ga Sanin ya kamata.

 

Wannan Kulawar da Hashim ke Nunawa kan Aisha Har saida Maryam ta kai Karanshi Agida Wai yana Fifita Aisha Akanta Wanda Dangi Sukamai Chaaa Aka Tarasu Dukkansu Akayi Musu Fada Abun ya bashi Mamaki ammh Kuma baya jin zai Fasa Nuna Soyayyarsa ga Aisha ,Watan Aisha Uku da Zuwa gidan Ta Samu Ciki mai laulayi Sosai yana bata Wahala sai ya kasance ko Wanka Sai Hashim yayi mata yake Fita Wajen Aiki Wanda ya karama Maryam Wutar Kiyayyar Aishan da Kishinta Shikuma Hashim yace bazai Fasa ba.

 

Cikin Aisha na Wata Biyar Maryam Ta Haifi yarta mace Wacce taci Sunan Mahaifiyar Hashim Wato *RUKAYYAH* Ita Kuma Aisha Sai da Cikinta yakai Wata Goma kana aka mata Operatin Ta Haifi katon Danta Namiji Yaci Sunan *MUHAMMED* Wanda Dangi Sukayi ta Ceceku Game da Haihuwar Saboda Yadda Hashim ya Kashe Kudi Sosai ga Hidimar Aisha Tundaga na Asibiti har Zuwa na Hidimar Suna,Duk da Haka bai kulasu ba Kuma Itama Aisha bata maida kai ba Duk ko Da mganganun da Maryam din Ke Jifanta Dashi.

 

Watan Muhammed Goma Sha Tara Aisha Ta kara Samun Wani Cikin Wanda yazo da Sauye Sauye Dadama Domin An Sallami Hashim Daga Wajen Aikinshi batare Dayasan Laifin Daya Aikata ba Kuma Sallama babu Biya kowani karin Bayani Abunda ya matukar Tadamai Hankali Shida iyalanshi Gabadaya Gashi Lokacin Kabiru da garba Asanyasu A mkranta Harda Rukayyah Muhmmed ne kadai ba’a Sakashi ba,Abunda yafi Dagamai Hankali Shine Lokacin da Zai Auri Aisha yana gidan gado ne To Shine yaci bashin Banki,ya Siya Fili ya gina gida Duk Wata yana Cire Wani Abu Daga Cikin Albashinshi yana Biya Toh gashi An Sallameshi Kuma Banki bata Jira Dole ka a Biyata Kudinta.

 

Lokacin da Dangin Hashim Sukaji Wannan lbrin Shikenan Sai Aisha Takara Shiga Gararin Rayuwa na Cewa Itace mai Farar Kafa,Itace Tunda Hashim ya Aurota Karayar Arziki ta Kamashi Sai dai Ta Shige Daki Tayi ta Kuka Tana Rumgume da Muhmmed ga Cikinta ya Tsufa Alokacin ne kuma banki Suka Nema Kudinsa Shine Dalilin Saida Duka kaddarorinsa da Motocinsa Harda Gidan Da Suke Ciki Suka Tattara Suka koma gidan Gado.

 

Aisha ta Shiga matsi da gararin Rayuwa Domin ba Inda Takejin Dadi Sai Ta bangaren Hashim Kuma Koda yan”uwanta Sunzo bata Nuna Musu Wani Abu Sai Dai Su Tafi Suna Zencen Ramarta Acikin Wannan Halin Ta Haifi yarta Mace mai Suna *HIDIYA* wanda Tunda Lokacin Da Aisha Ta Haifeta bata kara Lafiya ba Harta Koma ga Mallicinta ta bar Marayin ya”yanta Hannun Matar Hashim Wato Maryama.

 

Hashim yayi kukan Rashin Aisha Sosai ga Talauci ga Kewar Aisha Sai Suka Taru Suka Sanyamai Hawan Jini,Dangin Aisha Kuwa Sukayi ta Kokarin ko Hidiyan Hashim ya basu Su Tafi da Ita Ammh yan”Uwanshi Suka Hana Wanda ba Kowa bane ya Kitsamusu Haka sai Maryam Domin bataso  Adauke ya”yan Tafison Abarsu Tayi ta gana Musu Azaba Domin bata taba Son Uwarsu ba Suma bazata Taba Sonsu ba

 

Haka ko Akayi Dangin Aisha Sunaji Suna gani Suka Tafi Suka bar Muhammed Dan Shekara Uku da Wani Abu yayinda Hidiya Keda Shekara Daya da Rabi Abun Tsausayi Ammh Sun Sanar Dasu Cewa Lokaci bayan Lokaci Zasu Dinga Zuwa Dubasu Suka Amince,Bayan sun Tafi Aka Dauki Amanar su Muhammed Aka Damkama Maryam Wacce Ta karbesu kamar Gaske nan ko Cikin Ranta Mugun Nufi ne

 

Tun kafin Rasuwar Aishan Dama Ta Dade da Karantama Duka ya”yaanta Cewa Su Muhammed ba yan”uwansu bane Abokan Gabansu ne Saboda Babansu yana Fifitasu Fiye dasu Tayi ta saka musu Mugun Nufi acikin Zuciya Abunga ga yara nan da Nan Suka Haddace Karatun Nata Shiyaasa Muhammed Da Hidiya Suke Shan Wuya Ahannuta Ita da ya”yanta In Hashim yayi mgana ta Fashe da Kuka tace ya Raina Kokarinta,Data Fahimci Yana Damuwa da Halin da Suke Ciki Sai Koma yi musu Mgunta Aboye Abinci ma Kanzo Take basu,Ga Wahala Akasa Suke Kwana Cikin Sanyin Kasa Kafin Arufe Shekara Daya Yara sun Chanza Kamanni Tun balle ma Hidiya Wacce Bata da Lafiya Saboda Kwanan Kasa Nomomiya ta kamata Hashim baidata Cewa Domin Da yayi mgana yan Uwashi Zasu Tasomai da Fadin Uban me yake Tsinanawa Banda Zaman Banza,Yanaji yana gani sai dai yayita Kuka Shikadai Saboda Tsausayin Muhammed da Hidiya.

 

Amkrantar Gwannati Aka Sanyasu Sakamakon Kabiru da garba Dasuke na Kudi Tunda yan”uwan Hashim Sunfi Son So,Muhammed Tun yana Yaro yasan Gwagwamaryan Rayuwar Duniya,Sau biyu Dangin Mamansu na Zuwa Dubasu Suna Komawa da Kuka Saboda Tausayin Halin da Suke Ciki Tun Bama Muhammed ba Wanda Ke Karami Ammh Wahala ta Zama Cikin Jikinsa.

 

Tun yana Aji biyar yasan In An Tashi Mkranta ya Kama Hannu kanwarsa Su Shiga Cikin Kasuwa Yaringa Dako yasamu Abunda Zai Siya musu Abinci Domin Ko Sun Koma Gida Mama maryam bazata basu ba,Toh Ahakan ma basu Tsira ba In Suka Dawo sai ta kamasu Ta Masu Duka Hidiya Kuwa Kullum Cikin Kuka Take garba ya Daketa Kabiru ma Haka Rukayyah ma Sai dai in Muhammesd ya Ramata Mama ta kamashi Tayi mai Dukan Tsiya basu da Wajen da Suke Jin Sanyi sai Wajen Abbansu Wanda Shima Hawan Jini ya Kwantar Dashi.

 

Muhammed Dana Shekara Goma Aduniya Ita Kuma Hidiya Bakwai Allah yayima Hashim Rasuwar Mutuwar Data Raunana  Zukata Dadama Babu Uwa ba Uba Maraici ya Lullubesu Dama Ganin Abban Nasu ba”a musu Wani Abun Ammh yana Fadi ya Mutu Shikenan Wahalansu ya Karu Hidiya ta zama Jakar Aiki Itace debo Ruwa,Share Share,aike aike ,Wanki ne da Guga Ammh Rukayyah na Zaune Jangal batayi Muhammed Kuma Fita yake Tun Safe yana yawon Dakonsa Sai dare yake Dawowa Ya Siyoma Hidiya Abunda zataci Domin yasan Duk Wunin Aikin Da Zatayi bazata Bata Abinci ba.

 

Da Farko Adaki Suke Kwana Tare da Su kabiru Ammh Sai Mama ta Kullama Muhammed Sharri Akan ta Kamashi yana Turama Rukayyah Ahannu Awando Wanda Iyalan gidansu Suka Hadu basu Duba kankantar Shakarun Muhammed ba Sukamai Dukan Mutuwa Suka kuma Koreshi Agidan,Haka yafita yana Kuka Itama Hidiya tana Kuka Wannan Shine Silan barin Muhammed gidansu Ya bar Hidiya Cikin gararin Rayuwa Bai yi Nisa da garin Jikamshi ba,Cikin kasuwa yake Wuninshi Sai Dare ya Tafi Tasha ya Kwana yana Tara Kudinshi Kuma kullum Daddare zai Siyan ma Hidiya Doya da Kwai yazo Zauren Gidan ya Tsaya ta Sadado ta Fito ya Bata bayan ya Zaunar da Ita taci Tasha Ruwa Haka Zasu Rumgume Juna Kukan Tsausayin Kansu Hidiya tasha cemai Su gudu Wajen Dangin mamansu Ammh Muhammed yaki Saboda Shi kanshi bazai iya gane Gidansu Maman nasu ba Don yana Karami Sosai Lokacin Da ake Zuwa Dashi.

 

Muhammed bai bar Zuwa Mkranta ba Hidiyace dai Mama ta Kashe mata mkranta Bashi da yarda Zai yi yanaji yana gani Rayuwar Kanwarsa Tana lalacewa Su kabiru ko Suna Haduwa Dashi suda Abokansu Haka zasu dingamai Dariya Suna Tofamai Miyau Shiyasa ko ya gansu yake Saurin Chanza Hanya Hidiya Kuwa Tagama Wahalan Amfanin da Ruwa da Rana Daddare kuma ta Kwana Akasa nan da Nan Ciwon Nomoniya Takaramata Yawa Sosai Kullum Cikin Mura take Kwana da Sanyi Ammh ko Muhammed yazo bata Sanar mai Saboda Karta Tadamai da Hankali Koda yaushe yazo Jikinta yayi Zafi sai ya Tambayeta tace bakomai.

 

Adaddafe Muhammed ya kamallah Jss3 sai ya Ijiye Karatun ya Maida Hankalinshi kan Dakonshi hade kuma da Jari Bola Kwata Kwata Zuciyarsa ta Kekahe Neman na Kanshi yake ba Domin Shi ba Sai Domin Tilon Kanwarsa Hidiya,yayi kwana Biyu yana Zuwa Baya ganin Hidiya na Fitowa sai Hankalinshi yatashi Ranar dayazo na Uku Azauren Gidan ya kwana yana Jiranta Ammh batazo ba,Tundaganan Jikinsa ya bashi ba Lafiya Gudun kada Wani ya ganshi ne ya sanya ya Koma kasuwa Hankalinsa Duk Atashe Wajen Karfe 1 na Rana yana Kasuwa yana Sana”ar Dakonsa Wani yaron Kawun Abbansu yazo yake Sanar Dashi Wai yazo Hidiya zata Mutu Cikin Fitan Hayyaci ya Watsar da Abunda Ke Hannunshi Suka Rumtuma Zuwa Gidansu.

 

Sai dai Suka ganshi Kwatsam ya Shigo Har Shashensu Alokacin Wajen Shekara Biyar Bai kara Shigowa Gidan ba,Hidiya tana Kwance Akasa Siminti Hancinta ya Toshe da majina Numfashinta baya Fita Ta Rame ta lalace Kasa ya Zube gabanta yana Kuka Hannu Ta Mikamai Tana Fitar Da Hawaye Daidai Lokacin kuma Kawun nan  nasu Suka zo Dama mama ganin Hidiyan ta Kusa Mutuwa ne Shine taje ta Kirasu Wai Suzo Su gani Ita bama tasan Bata da Lafiya ba Alhalin Tana sane Itama kema Kara Saka Ciwon Tashi Domin Wanka take Zuwa tamata Da Ruwan Sanyi Kuma Ta Hanata Sauya kaya Har sai Sun Bushe Ajikinta.

 

Muhammed ya Rude da ganin Halin da Hidiya ke Ciki ko Ta kan Kawunsu Dake mgana baiji ba ya Ciccibi Hidiya yana Kuka Ya Fita Da Ita Waje,yana Ihun Mutane su Taimakamai Ana Cikin Wannan Halin ne Allah ya jeho Alhaji lawal Acikin Motarsa Zai Wuce Katsina Alokaciin ganin Muhammed Dauke da Hidiya yana Kuka ya sanya ya Faka Motarsa ya Fito baima Tsaya Tambayan Muhammed ba ganin Halin da suke ciiki ya sanya ya karbi Hidiya ya sakata Abayan Mota ya Umarci Muhammed Daya Shiga Su Tafi Agaban Idon Dangin Mahaifnsa Suka Tafi Asibti da Hidiya ammh ba Wanda yayi Tunanin Binsu.

 

Babban Asibtin Garin Sukaje sai dai Suna Shigowa Get din Asibtin Hidiya tafara Wani kakari Muhammed ya Rude ya Rumgumeta yana Kuka yana Kiran Sunanta ganin Idanuwanta na Kafeewa ne ya sanya ya Kuramata ido hawaye na Fita Daga Cikin Idanuwanshi Yana ji yana Gani Agaban Idanuwansa Aka Zare Ran Hidiya Abunda ya kasa barin Zuciyarsa Kenan Har Shima ya koma ga mahallincinsa.

 

Muhammed yayi kuka Tamkar zai Zauce Saboda Mutuwar Hidiya basu Juya ba sai da Suka Shiga da Ita Cikin Asibitin Aka Tabbatar da Mutuwar Hidiya Kafin Alhaji Lawal ya Daukosu Zuwa Gida ganin Kukan da Muhammed Ke Yine yasa ya Tambayesu ina Mahaifinsu nan Muhammed yana Kuka yana bashi Lbrinsu Wanda ya Matukar bama Alhaji lawal Tsausauyi.

 

Abun Mamaki da Suka Dawo da gawan Hidiya ba Wanda ya Nuna Jimami ko Damuwa,Taruwa kawai Sukayi,Abun Takaichi Muhammed Shi yayima Hidiya Wanka Gawa Yanayi yana kallon Cikin Idanuwanta yana Kuka Ahaka Har Aka kaita gidanta na gaskiya A makabartan Aka Watse Aka barshi Alhaji lawal shi ya rikoshi Suka Fito ya Sanyasa Cikin Mota bai Zarce dashi ko”ina ba sai Katsina.

 

Alhaji lawal shi da Matarshi Hadiza basu Taba Haihuwa ba Gashi yana da Tarin Dukiya Ta Dalilin Kamfanonin Dayake Dashi kama daga na Robobi kanfanin Sarrafa Atamafa,na Takalma ne da Sauransu. ya Tara Kudi masu yawa Tunda yazo da Muhammed yabata lbrinshi Shikenan Tsausayi ya kamata ta kama Muhammed Ta Rumgume tana Kuka Kuma Sukaci Alwashi Zasu Rike Muhammed Tsakani ga Allah.

 

Bayan Rasuwar Hidiya ba Dadewa Dangin Aisha Suka zo ganinsu suka Iske bakin lbrin Rasuwar Hidiya da Lbrin wai Muhammed ya Gudu ya Shiga Duniya Haka Suka Koma Malumfashi Suna Kuka Sosai na yadda Rayuwar ya”yan Aisha suka lalace Acikin Duniya,Shikuma Muhammed ya samu Chanjin Rayuwa ya koma mkranta,bayan ya gama Secondry Sch Suka Tafi Dangin Alhaji Lawal A malumfashi Alokacin ne kuma Aka gano Ashe Shi Alhaji lawal Abokin Wasa yake ga Marigayiya Aisha Mahaifiyar su Muhammed nan fa Sabon Kuka ya Tashi Ana Ta Rumgume Muhammed,Wanda koda da Rana Daya Mutuwar kanwarsa Hidiya bai Taba Bacemai ba.

 

 

Akasar England ya Hado Digree dinsa na Farko Akan Harkan Kasuwanci Haka kuma ya Wuce Kasar Calponia ya Hado Master dinsa Akan Accouting da Hada Hadar Kasuwanci Koda ya Dawo Nageria sai Ragamar Dukiyar Alhaji lawal Ta Dawo Hannun Muhammed,Shi kuma Alokacin A England yayi Aiki da Wani Kamfanin Turawa na Sarrafa Takalmam Maza so sai Suka Hada Huldar Kasuwanci da Kamfanin Alhaji lawal Dake Nageria kuma Alhamdulillah Lokaci Kadan Huldar ta kawo musu Kudi Sosai Suka Cigaba,.

 

Muhammed ya Wuce Duk Tunanin Mai Tunanin jin haushinshi ko Hassda Daga Danginshi Kuwa Suna da Lbrinshi Domin Alhaji lawal na Matsamai Lokaci bayan Lokaci Yana Zuwa Dubasu Rukayyah Tayi Aure Akano Su Kabiru kuma Angama karatun Ana Zaune ba Aikin Mama maryam kuma girma ya Kara kamata da Kuma Hakkin Hidiya da Muhammed Domin Taga yarda Allah yake Maida bawanshi Lokaci Daya.

 

Kafin Rasuwar Alhaji lawal Sai da Tabbatar  ya mallakama Muhammed Duka Dukiyarsa bayan Ancire na yan”uwansa,Wannan Abun yabama Mutane mamaki da kuma Girmama Soyayyar da Alhaji lawal Kema Muhammed Su Kabiru kuwa Hasaada da kyashi bai bar Zuciyarsu ba,Sai Sukayi lambo Suna Shigema Muhammed Harda Rokonsa Gafara Saboda Suma Su Shiga Jikinsa Su Samu Arziki Sun kuma yi Nasara Domin Daga Kabiru Har Garba ya Daukesu Aiki A kamfanonin Alhajin lawal Duk da Abun da Suka Aikata gareshi bai Taba bacemai ba Ammh in yayi Duba ga Yadda Allah ya Daga Darajansa sai ya Godema Allah.

 

Mutuwar Alhaji lawal Da Matarsa Sakamakon Hadarin Mota Shiyakara Fito Da Sunan Muhammed Aduniya Domin ya Samu Dukiya mai yawa Yawancin Kamfoninin Alhaji Lawal Shi ya mallakesu Gashi Shima yasan Kan Kasuwanci Kafin Ya Rufe Shekara Daya ya Mallaki *Jikamshi shopping mall* Jikamshi Store* Jikamshi And Sons Nageria Limited..* Lokaci Daya Sunanshi yayi Suna A nageria Gefe Daya ya jawo Yan Uwansa Da Dangin Mahaifinsa yamusu Gata duk da Abunda Suka Aikata garesa Dangin Mahaifiyarsa kuwa Dama Sune Ahalinsa.

 

Tuni ya Tattara Kabiru da Garba da Mama Suka koma Katon Gidan Daya gina A Katsina Komawarsu Wannan Gidan Mai kama da Aljannar Duniya Shiya kara Saka Zuciyoyin Su Kabiru Gudirtan Cewa Ko Ta Halin kakane sai Sunga bayan Muhammed Sun mallake Duka Dukiyanshi Ita ko Mama Maryam ta Saduda Ance magaji mafiyi Domin Su Kabiru ya”yanta ne Ammh Sun Fita iya Kulla Makirci da Sharri Duk da Muhammed na Kanninsu Haka Suke Sadda kai Suna mai Biyayyah Duk Don ya Saki Jiki Dasu.

 

Cikin Shekara Uku ya Siya Musu gidaje da Motoci ya kaisu Makka Kuma yayi Musu Aure Kabiru Akaduna ya auro Karima sai Garba dayayi Aure a Kankara Ya Auro Sahura Dukkansu Sukazo Suna Cin Arziki da Dukiyar Muhammed Wanda Suka Wulakanta Rayuwarsa da Farko Mama maryam bata Rasu ba Sai bayan Auren Muhammed,ta rasu ta kukan Neman Gafaransa kan Abunda ta aikata garesa Shida kanwarsa,muhammed anso a tusamai auran Dangi A Ammh yaki Domin Allah ya Hadashi da Hassatu Wata Bafullata ne Daga Jahar Yola

 

Hassatu marainiya ce Bata da Uba sai Mahaifiyarta Data ke cema Daada Farar Bafullatana ce Kyakyawa da Ita Dangin Mamansa Suka yi komai na Auran Cikin Lokaci Hassatu Ta tare Agidan Mijinta Dake Katsina,Tun kuma Daga Lokacin Sai Abubuwa Sukayi ta Cigaba Arayuwar Muhammed gefe Daya Kuma su Kabiru da Matansu Suna ta Ta Hada Tuggunsu A boye Ita kanta Hassatu ta sani Domin ba kyashin Da basu Nuna mata Ammh bata taba Nuna ma Muhammed Ba bataso ta Rabashi da yan”uwanshi.

 

Karima matar kabiru wabi Takeyi In ta Haihu sai anyi Suna Su koma ga Allah Ita kuma Sahura matar garba Shuru Haihuwan, Itama Din Shuru Kwatsam Hassatu ta samu Ciki Su kabiru ba Kulle kullen da basuyi ba kar Hassatu Ta Haihu Ai kuwa hakansu bai Cimma Ruwa ba Domin A Babban Birnin India Delhi Hassatu Ta Haifi Kyakyawan Danta Namiji Wanda yaci Sunan *MUKTAR* Basu dawo Ba sai da Sukayi Wata Biyu Suna Dawowa Kuma ya kaita yola Wajen Daada tayi Wata Daya kana Ta koma Katsina.

 

Lokacin da Muktar yazo Duniya yazo Cikin Gatan Rayuwa Sosai Saboda Mahaifinshi na kan Samu Hassatu Ta Fahimci komai Shiyasa Take ta Kafa kafa da D’anta bayan Tana Sanar da Daada Duk Abunda Ke Faruwa Ita ta Haneta da Karta sanarma Muhammed Ammh Dai Ta Kiyayi Kanta ta Kuma Dinga Lura Saboda Hakama Dukkansu Suka baro Gidajensu Suka Dawo Gidan Muhammed ke zaune Shida Hassatu katon Gidane mai Dauke da part part da Zuwan Wai Sunfi Jin Dadin Zama tare Dashi Shi kuma bai kawo komai ya Amince Suka Tattaro Suka Dawo nan da Zama.

 

Inna Rukayyah ma Dake Kano Babu Abunda Muhammed baya Mata tana Kuma Zuwa Akai Akai Sai dai ita Tunda Tayi Aure Allah bai bata Haihuwa ba Sai da Muktar ya Shekara Bakwai Aduniya kana Karima matar Kabiru Ta Haifi Danta Namiji yaci Sunan kakansu *Hashim* Lokacin Tuni Ansaka Muktar A mkranta *International Community School Abuja* Cikin Gata da Soyayyah mai Tsanani Wanda Ke Kara Wutar Kiyayya Azuciyarsu Kabiru Suna Tunanin in Suka Kauda Muhammed ya Zasuyi da Muktar Dansa na matarsa mai Sauki ne.

 

Hassatu bata kara Haihuwa ba Sai da Muktar ya Shekara 15 aduniya Ta samu Cikin *MUHAMMED BELLO* Wanda Ikon Allah ne da Kuma Rabo ya kawoshi Duniya Domin Har mganin Hana Daukan Ciki Kabiru yake bama Karima tana Sanyama Hassatu Acikin Lemo Tana Sha Sai dai Kuma Abunda Allah ya Riga ya yanke bawa bai isa ya Kauce musu ba.

 

Wannan karon ma A India Hassatu Ta sake Haihuwan Danta Namiji mai kama da Mahaifinta Sak Shine Dalilin Dayaci Sunan *BELLO*,Haihuwan Data zoma Muhammed da Sauye Sauyen Arziki dadama Acikin Rayuwarsa Haihuwarsa da Shekara Suka Tattara Muhammed Zuwa Kasar Chicago Domin ya Hado Digree dinsa na Farko Tunda yana da Kokari Sosai Shiyasa yagama Karatu Yana da Kananan Shekaru.

 

Akabar Bello Agidan

Shida Iyayensa Suna Cigaba da Kula Dashi Shima yana Shekara 4 aka Kaishi Nagerian Turkish Acadmy,inda Aka kai Hashim Din Wajen Kabiru,Tun Bello na Karaminsa Kowa ya Fahimci Sadauki ne ga Zuciya ga Riko ga Kuma Kulafuci ga Saurin Fushi,kuma Iyayenshi na Matukar Sonshi kar ma Daada Taji lbri.

 

Lokacin da Muktar ya Dawo Nageria yana da Shekara 22 cif ya Hada Digree Dinshi na Farko Dayake yana Sha”awar Aikin Soja sai Muhammed ya kaisa NDA Nageria Defency Acadmy Domin karban Horan Sojoji Lokacin Shima Bello na jss1 misalin Dan Shekara 8 saboda kokarinsa ya saka akayitamai Jumping ,Kuma Sannan ne Haihuwa ta Budema Abba Kabiru da Abba Garba Bayan Hashim yayi Kasim Wanda Tsakaninsu da Bello Wata goma Sha Daya ne,,Sai kuma Wasu da Sukayi ta Mutuwa basa Tsayawa Dakyar ta Karshen Ta Tsaya Zubaida sai Sahura matar Garba Keda Zulfa,Ummu salma,Hamdiya Duka mata Suna Sun Taso Cikin Gata ne Sosai na Rayuwa Daga Dukiyar Muhammed Wanda baya kyashin yi musu komai na Jin Dadin Rayuwa

 

Abunda yakara Bata Ran Abba Kabiru Shine Muhammed ya Dauki Hashim yakaishi University Of lagos bai kaishi Kasar Waje ba Shiya kara Fito da Wutar Kiyayyah Hakan Acikin Ranshi yana ganin Muhammed na Fifita matanshi da yayanshi Akan nasu Matan da yayansu Batare da Sanin Kowa bq Sukayi Shawara Shida Garba Sukayi Hayan Wani mutum ya K’wance Birkin Motar Muhammed Din Wanda Suka Shiga shida Hassatu Zuwa Yola Lokacin Bello na Makranta Hakama Muktar yana NDA,Kuma Muhammed yaso Suyi Tafiyan a Ajirgi Ammh Dayake Sun San Abunda Suka Shirya sai Suka Hanasa Tafiya Ajirgi Garba ne dama mai Cukun Cukun Tiket din Tafiye Tafiyen Muhammed din nan Yacemai babu Jirgi mai Zuwa Yola Dole Suka Tafi ,Amota Tunda Tafiyar ta Dole ne Daada ce ba Lafiya Tafiyan da basu Dawo ba Kenan Har Abada sai dai Duka Iyalan Sukaji Sakon Mutuwarsu nan Take.

 

Allahu Akbar.

 

*Janafty..*a: *MR BELLO..!*

_(The young Teacher)_

 

 

*Wattpad:Janafnancy13*

_Mallakar:Janafty

 

*🅿�?5*

 

 

“””Mutuwan Data Girgiza Zukata Gabadaya,Daga Muhammed Har Hassatu da Direbansu Allah yayi Musu Rasuwa nan Take kuma da Abun yafaru kabiru Aka Kira Aka Fara Sanarmawa..

 

Sun Nuna Alhininsu da Kuke kukensu na Rasuwar Muhammed Haka Mutanan Yola Suka Samu Lbri  tun kamar kar Daada Taji lbri Sai Jikinta yakara Rikicewa Shi Kuwa Muktar Daga Kaduna Aka Daukosa Zuwa gida Harda Bello Wadanda Suka zo Suka Iska Mugun Lbrin Rasuwar iyayensu Sunyi kuka kamar Ransu Zai Fita Domin Sun Shaku da iyayensu Sosai Koda Dangin Hassatu Suka Nemi Sanin Komai game da Dukiyar Muhammed Sai Su Muhammed Suka hada baki da Ma”aikatan Kamfononin Tare da Accountans Din kamfafonin Muhammed marasa Tsoron Allah Domin alkarukan Makudan kudi su Abba kabiru suka yi musu alkawari matukar suka goya musu baya

 

Su suka taimaka wajen Hada Jawabin Karya Wajen Cewa Kamfoninsu Biyu Sun Ci Bashin Wani Kamfani Domin Farfado Dasu To yanzu Kudi Sun karu kan Kamfanonin kuma Babu Riba ya Tabbata Kamfanin Daya Hada Hannun Jari Dasu zasu karbi Wadanan Kamfanonin Guda Biyu Domin Biyan Kudin Da Sukayi Asara Hakan bai Isheshi su ba,Haka Suka Dinga Kawo bayanan karya da Mahintan Ma”aikata Harda karya n Bashin Banki na Wajen Miliyan Talatin da Biyar Dangin Hassatu Suna ji Suna gani bayani ya Tafi kan Duka Dukiyan Muhammed Wai batashi Bane Sakamakon yana Da Hannayen Jari masu yawa kuma basu kawo Riba ba Illah Binsa Bashi Da Sukeyi.

 

Muktar na gani Ammh bashi da Ikon Mgana Bello ne mai Zuciyan Shi Kuma yana Karami ne Lokacin Sunaji Suna gani Abba Kabiru da Abba Garba Suka Hamdame Dukiyarsu Daga Karshe sai Duka Kamfanonin mahaifinsu ya Dawo Tsakaninsu Shida Abba garba da Sunan bayan Anyi Gwanjonsu Suka Siya Duniya ta Dawo Musu Sabuwa Hajiya Sahura da Hajiya Karima ba Wacce bataje Makka da Ummura ba Suna ta Facaka da Kudin marayu su da ya”yansu basu taba Tunanin cewa Cin hakkin da ba naka ba wani Nauyi ne wanda ko bayan ranka sai ya tambayeka ba.

 

 

Muktar da Bello ko ba Wanda ya kara bi Takansu Domin Dangin Hassatu Na yola bayan anyi bakwai Suka Koma,sunyi kokarin abasu yaran Hassatu su tafidasu wajen Daada ammh Abba kabiru yace ba wannan mganar yara suna karatu bazasu lamunci katse musu karatu ba,suka rabu akan su zasu rike yaran suna ta kukan karya Dana munafunci nan ko mugun Nufi ne da Tsabar mugunta ke cin ransu kamar Abba kabiru yaji labari yafi Abba garba Dora buri Bisa Dukiyar da bako zufanshi wajen Tarata.

 

Daada bata zo ba tana chan Babu Lafiya,Su da gidan ubansu Ammh Sun Rasa Dukkan gata ba Wanda yayi Tunanin maidasu Makranta Shi Bello Bai koma Negrian Turkish Academy ba Shi kuma Muktar ba”a Maidashi NDA ba Ammh Hashim Tuni Abba Kabiru ya Turasa Kasar Spain yana Cigaba da Karatunsa.

 

Wahala Rayuwa da Matsi ba Wanda Basu gani ba,Acikin Gidan da Ubansu ya Gida da guminsa ba,Abinci ko Sai dai indan Sun Rage,suna Rabe raben kankaran kanzo ko ma”aikatan gidan sunfi suvgalihu da Daraja watarana ma sai wanda ma”aikatan suka rage ne suke samu wani lokacin sai dai muktar yaci girma ya barma Bello,saboda tsausayin kanin nashi Wani lokaci haka zasu zauna suyita kuka Bello yana ganin dashi ne keda girma da Shekarun ya muktar wlh da su Abba garba sungane basu da wayau sai dai kash shi Muktar yana Da sanyin Hali irin na mahaifinsa sam komai za”a musu acikin gidan baya Daga kai Bello ne Wani lokacin ke Tubure musu,Tuni suka gano yaron zai iya basu matsala wata rana suka Fara Tunanin yadda zasu maganinsa.

 

 

Abba Kabiru ma saboda Samun waje Shashen Mahaifinsu ya koma Shida Iyalanshi Kasim dasu Zubaida Ana Ta Cin Duniya Da Tsinke Cikin Kwanciyar Hankali Muktar da Bello Aboy Quaters Suka Koma Kwana Hatta da Masu bama Fulawa Ruwa Asallamesu Da masu Wankin Motoci domin kaf motocin mahaifinsu Data Mahaifiyar suvdata muktar din Duka ko Abunda ba”a so basu barsu dashi ba.

 

 

Bello da Muktar su suka koma wanke motoci da bama fulawowi ruwa wani Lokaci Bello ke nuna Taurin kai Sai yaki yi Haka  Abba Kabiru zai Ta Marinshi Ammah yakiyi,Yana da Saurin Saka Abu Acikin Ranshi Shiyasa komai yakasa Bacemai Hajiya Sahura ko da Hajiya Karima ba irin Wahalan da Basu ba su ba Kamar basu Taba Saninsu ba,Sunsha lakaba ma ya muktar sata,Mussmman Bello da ya cika bakar Zuciya yafi muktar shan wuya agidan Hatta da su Zubaida dake yara Suma Sun Iya Wulakanci Musamman ga Muktar Wanda baya da Fada da Hayani Wani Lokacin bello ke kwatanshi Shiyasa Duk yafishi shan Wahalansu, Cikin Shekaru uku Suka Chanza Kamanni Rayuwarsu Duk ta lalace Kamar basu bane ya”yan Hutu ba Tuni Hashim ya Dawo ya Zama Saurayi dayake yana da girman jiki Har yafara Aiki da Kamfanin da Abba Kabiru ya Hamdamai Wai Muktar ne ke Budemai get in zai zai Fita Yau ya Hau Wannan Mota gobe ya Hau Wannan yana Cin Duniyarsa da Tsinke

 

Basu da inda zasu je Ataimaka musu Dangin Babansu na Jikamshi Duk sun kare sai D’aid’ai na nesa wadanda suma fama suke da kansu,kuma na nesan ma wadanda ke cikin kauyuka,Malumfashi ma Sau Daya suka taba zuwa suma duk sun kare Dangin kakarsu ta wajen Uba basu san kowa ba,sai Dangin mamarsu na yola sai kuwa su Abba kabiru.

 

Kwatsam Sai ga Daada ta Diro Gidan Halin Data Tarar da Jikokinta Sai da ya sakata Kuka Ta Dingama Su Abba Kabiru Allah ya Isa Ba Kunya ba Tsoron Allah Sukace Allah ya isa ya Bita Dukiya ne suncinye In zata Kwatan musu ne Bismillanta Daada bata Damu ba ko Kwana Batayi ba Tattaro Muktar da Bello ta Taho Dasu Gidan yayanta Baffa Hadi,Daman bayan Rasuwar Mahaifin Hassatu Wajensa Take Zaune Ta karantamai Duk Abunda yafaru nan Take ya karbi su Muktar kuma yayi Alkawarin Rikesu Amana su kuma Su Abba Kabiru yace zai makasu kotu Daada ta hana tace ya kyalesu duk wanda yaci hakkin maraya sai Allah ya tambayeshi Badai cin Hakkin Maraya ba Zasu girbi Abunda Suka Shuka ne.

 

Ya Maida Muktar Kaduna NDA Dole ya Dawo baya a karatunsa domin tuni yan batch dinsu sun dade da gamawa bai damu ba ya Cigaba da karban Horaswan Sojoji Shi kuma Bello ya Sanyashi Wata Makranta ta masu Hali Ya Dora Daga SS1 duk Abunda ya Faru bai bacema Bello ba ya Rikeshi Sosai Acikin Kanshi yakuma Ji Duk Duniya babu Wanda Ya Tsana kamar Su Abba Kabiru da Iyalansu,Shiyasa Ko Alama baijin Zai iya Hada hanya ko Wata Mu”amalan Arziki dasu har gaban Abada.

 

Lokacin Daya kamallah Secondry Sch Dinsa ya Tafi University of Ibadan Shikuma Muktar yagama Short Service dinsa ya Fito Amatsauyin Second Leutanant,Yana Aiki A barikin Jaji Dake Kaduna,Bello Dama Tun yana Karaminsa yake da Burin ya Zama malamin Makranta Yasha Fadama Daada Haka da Muktar Ammh Sai basu Daukan Abun da Muhimmci,Mathematics yake Karanta sai inda sun Samu Hutu yake Zuwa Gida.

 

Yana Kara Girma Duka Murdadun Halayansa Suna Kara Bayyana Koda da Rana Daya Bello bai Manta da Abunda Su Abba Kabiru Suka Aikata Garesu ba Ayayinda Shi Muktar Yake da Saukakkiyar Zuciya Tuni Abun ya Fitar Mishi Arai bai kuma Rikeshi Ba Sabanin Bello Wanda Ta Kowani bangare Suna da Bambancin Ra”ayi.

 

Lokacin daya Kammallah First Digree Dinsa ne,Yatafi Makrantar GGUSS KWATAR KWASHI yayi musu Bautar Kasa Ko Alokacin Muktar yaso ya Hanashi Ammh Ya Nuna Shifa Abunda yake Ra”ayi kenan Lokacin Har Muktar yakai Matsauyin Captain ne yana Aiki a Barikin 1 Division Barrak Dake Kaduna.

 

Bello yaji Dadin Bautar Kasar Daya Gudanar A Makrantan Kwana ta Kwatar kwashi,Wanda Suma Makranta Taji Dadin Zuwanshi Tunda dama suna da Karancin Malamin Lissafi Tun Alokacin Bello yayi yaki da Mata Sosai Saboda Yadda ya Tara komai na Cikar Zatin Da Namiji bai maida kai ba Tunda Kowa yasan Muhammed Bello Jikamshi bashi da Wasa ko kadan.

 

Batare da Saninshi ba yayanshi Muktar da Baffa Hadi Suka samarmai Wata Makranta a Babban Birnin America Wato U.S inda yaje ya Hado Masters Dinshi Akan Mathematics.

 

Rayuwa tayi ta tafiya yarda Allah ya Tsara Muktar na Aiki yana Kara Samun Girma Awajen Aiki,har yakai Matsayin Cononel Lokacin ne kuma Bello yadawo Daga America bayan ya Hado Masters Dinsa yana Da Shekara 26aduniya Shi kuma Muktar nada 40 alokacin kuma Baiyi Aure ba akuma Lokacin ne Su  Abba Kabiru Suka Nemesu bayan Duka Dukiyar da Suka Hamdemai Ta Gudu Ta barsu Dama Hakkin Maraya bazai Taba Zama ba.

 

Har yola Suka tako Duka Suda iyalansu Suna Kuka Suna Rokonsu Muktar gafara Sakamakom Sunga Bala”i kala kala Gashi komai na Dukiyar baya Cigaba ga Mugayen Mafarkai da Kuma Rabuwar kai Tsakaninshi da Abba garba Matayen Suma sai Cin Juna,da Fada Hakama ya”yansu basa zaman lafiya,Saboda Dukiya wacce kwata kwata batayi albarka ba Sauran kamfanonin ma Tuni sukayi gwanjensu saboda ba ma”aikata kowa ya gudu tunda babu albashi ba hannayen jari ba kuma ba Shugaban kwarai kafin kace kwabo komai Da suka Hamdame ya fara gudu ya barsu kamar kudaden suna kamawa da Huta gidaje da Filaye dama Tuni shi da Abba garba suka raba kowa yaja rabonsa suma basu kai labari ba saboda yadda suka sakarma matansu da ya”yansu Ragamar komai suna cin karensu ba Babba Da Dukiyar ta fara salwanta Kusan mugunta Fitsarin Fako ne sai suka fara Zargin junansu da cewa cikinsu ne wani ya sakama Dan”uwansa Hannu komai ya lalace shine Dalilin Rabuwan kansu Dana ya”yansu domin Daga Sahura har Karima kowa tabi bayan mijinta da ya”yanta.

 

 

Suna Kuka Suna Sanar Dasu Abunda Suka Aikata ga Muhammed da Matarsa Hassatu, da Muktar da Daada ne Keta Kuka Basu da Abun Cewa Domin ko haka aka Tsaya Sunga isharansu nan da nan Sukace Zasu Mika Sauran Dukiyan ga Muktar da Bello Shi kuma yace Su Rike kawai Sun bar musu Duk da bai Shawarci bello ba yafi kowa sanin Bazai Taba Karba ba,Shiko Bello Suna Zuwa Gidan ya Fita bai kuma Dawo ba Har Suka Tafi Abun yamishi Ciwo yadda yaga Muktar bai Damu ba har yana Sakar Musu Fuska Lokacin Su Zubaida da Zulfa Duk Sun zama yan Mata Kowacce na SS2 alokacin Ummu salma kuma Da Hamdiya Suna Wajen Inna Rukayya Dake Kano Hashim Kuma yayi Aure Har ya Haihu Sai Kasim dake Jami”a Alokacin sunji matukar mamaki da Muktar yace sun bar musu Duka Dukiyan Daya rage ahannunsu,Dama suna tunanin taya rayuwarsu zata kare in suka karbi komai tunda hatta hashim yanzu zaune yake baya aikin komai Tunda Duka kamfononin sun sanyasu akasuwa sun karbi yan kudadansu.

 

Muktar baiyi Aure ba Sai da ya keda Mukamin Major Shekarunsa Lokacin 44 aduniya Kana yayi Aure da Matarshi yar Garin Borno Kanuri ce gaba Da baya Mai Suna Rahila Wacce Suka Hadu Lokacin Daya Jagoranci Wata bataliya Zuwa Maiduguri.

 

Bayan Aurensu ba Dadewa Ya Dauko Matarsa Daga Yola Zuwa Abuja Inda yake aiki a Abacha barrak,Shi kuma Bello ya koma Makrantan kwana ta Kwatar-kwashi Yana Koyarwa Wanda Muktar da Daada Sun yi Sunyi Ammh ya Kafe yace Shi zaiyi Hatta Jami’ar Dayayi Ta University of Ibadan Suna Nemanshi Su bashi lecturing Ammh yaki Dole Suka Sanyamai Ido Tunda Haka Allah yayi Shi da Taurin Kan Tsiya.

 

****

 

“” *ANEESA BUKAR BULAMA* Shine Cikakken Sunan Aneesa Kuma Itadin kanwa Take ga Anty Rahila matar Muktar,Ubansu Daya Uwa Kowa da Tashi.

 

Sun Fito daga Tsatson Yaren Kanuri na Garin Bornon Maiduguri Kanuri ne na Gaba da baya Irin bakaken nan masu Kyau da Tsari,Suna Zaune a Unguwar Damboa Road.

 

Ahaji Bukar Bulama Shine Mahaifinsu Wanda ya Kasance yana Da Rufin Asiri Daidai Gwargwado Tunda Dan Siyasa ne Sosai yana da Matan Aure Biyu Wato *Mama Yana* sai * Mama Falmata* wacce Itace Mahaifiyar Aneesa.

 

Su Bakwai ne agidansu Mama yana Keda ya”ya Bakwai Falmata Sai Daga baya Aka Aurota ,Babban Gidan Shine Yaya Ali,Sai ya Sunusi,sai Anty Nafi,Sai Anty Yagana,Anty Rahila sai Anty Aisha,Sai ni Aneesa Auta, Falmata Tafi Shekara goma bata samu Haihuwa ba sai Akan Aneesa,Wacce  Tun bayan Haihuwata na Taso Agidanmu Cikin gata Sosai Daga Duka bangoririn iyaye na Aneesa yarinya ce mai Shiga Rai Gata Auta Wannan Dalilin ne Alhaji Bukar Bulama ya Sangartata Sosai Duk Abunda Takeso Shi yake mata.

 

Aneesa Tataso Tun Tana Karamarta da Tsiwa ga Rashin Kunya da Rashin Tsoro Ko Falmata datake Mahaifiyarta Bata Isa ta Daketa ba yanzu Alhaji Bukar Bulama zai Fara Fadanshi na Fama Kan Aneesa Ko Kukanta bayaso yanzu Ran Kowa Zai  baci,Wannan Dalilin ne ya Sanya Aneesa Tataso Cikin Gatan Sangarta Ko yayyinta su Anty Nafi Ba Wanda ya Isa yaga Tana Abu yayi mgana Yanzu Zata Saka Kuka In ko Alhaji Bukar Bulama yaji Kukan Aneesa ka Shiga Uku..

 

Saboda Son Daya ke mata da Kuma Sangarta ta Dayayi ko Ina Zashi Tun Tana karamarta Tare yake Zuwa da Ita Koda Taronsu na Siyasa ne Shiyasa Duk Wanda Ke Tare da Alhaji Bukar Bulama yasan Wacece Shalele yar Auta,Tun Tana karamarta Har Zuwa Lokacin Data isa Zuwa Mkranta da Alhaji Bulama yayi Kokarin Saka Aneesa Amakranta Sai Rigimarta ya Tashi Kullum Da Dambe Ake Shiga da ita Makranta Su yaya Ali ne ke Kaita Watarana Sai Sun Hadamata da Duka Kuma Haka za”a Daukota Tana Kuka Batama Tsayawa ta Fahimci karatun Hakama Islamiya bata Zuwa Duk ko Ranar da Aka Matsamata Haka zata Wuni Kuka Har Alhaji Bukar ya Dawo Kuma In ya Shigo yaji Kukanta Ran Kowa sai ya baci Agidan Manya da yara.

 

Ganin Haka yasa yace akyaleta Tunda batason Karatun yarinta Ke Damunta in takara Girma Zatayi Haka ko Akayi Dakyar Aneesa Ta Kamallah Primary 2 Shima ba Kullum Take Zuwa ba Sai yan Rigimarta Basu Kusa,Yaya Sunusi da Yaya Ali Dukkansu Sun kamallah Karatunsu yaya Ali Ma”aikacin banki ne Shi kuma Yaya Sunusi yana Aiki A Hukumar Man Fetur ne Wato NNPC,Anty Nafi Tayi Aure acikin Garin Maiduguri Yayinda Anty yagana Tayi Aure Agarin Ibadan,Suma ba Wacce Batayi karatu ba,Aneesa ce Ta Bambanta Domin In Tana Kaunar Mutuwarta tana Kaunar Karatu.

 

Mama falmata ba yadda batayi ba Tayi Lallashin Tayi Fadan Harda Dukan Ammh Abanza Aneesa Taki Karatu Sam,Shikuma Alhaji Bukar baya som Matsamata Wani Lokacin Sai yayi Tafiya ne Su Yaya Ali ne zasu Dauketa Sukaita bayan sun Mata Dukan Tsiya Tun Barema Yaya Ali Sarkin Fushi Da Zuciya ganin Aneesa na Cin Wuya sai ta Hakura tana Zuwa Makrantan Ammh bawai Don Tana maida Hankali ba Da Kuka Take Zuwa Kuma Da Kuka Take Dawowa babu Abunda Ta sani sai Rashin Kunya da Tsiwa Domin Karya ne Taje Makranta Atashi bata Daki yara Goma ba Muguwa ce ta Sosai.

 

 

Rana Daya Akayi Auren Yaya Ali dana yaya Sunusi Dukkansu Kanuri yan”uwansu Suka Aura Matar Yaya Ali Khadija Ita kuma matar yaya Sunusi Sadiya Sunanta Dukkansu Anan Cikin Gidan Alhaji Bukar Bulama Suke Zaune Saboda Katon Gida ne,Aurensu ba Dadewa Akayi Auren Anty Rahila da Muktar Anty Aisha kuma Tana Auren Wani Sojan Ruwa a kano Rana Daya Akayi Bikinsu Gida ya Rage Daga iyayensu sai Auta Aneesa,Wacce Dakyar da Sodin Goshi ta samu Ta gama primary Daga Nan Alhaji Bukar yace Akyaleta Domin Hatta Makrantan Kwana sai da ya Ali ya samoma Aneesa Ammh Alhaji Bukar ya Hana Dole Suka Sakamata Ido Tana Abunda Tagama Dama Sune kadai batama Rashin Kunya Tasan Halinsu yanzu Zata ci na Jaki ammh matansu Kuwa Duk Ta Ranmusu kuma basu da Cewa don yanzu sai Alhaji Bukar yaci Mutumcinka kan Aneesa Saboda Yadda bayason Wani yatabamai Ita.

 

Aneesa Tanada Shekara Goma Sha uku Aduniya Allah ya Karbi Ran Alhaji Bukar Bulama Mutuwar Data Girgiza kowa Musamman ma iyalanshi,Wanda ya Kwanta lafiya lau sai Tashi Akayi Rai yayi Halinsa ba Wanda yafi Gigita da Mutuwanan Irin Aneesa Domin Sun Dade Suna Hira Dashi kafin Tatafi Daki Ta Kwanta sai dai Wayan gari Sukayi da Mutuwa Wayyo Rayuwa Aneesa Sai da Tayi Awa Uku Asume kafin Ta Farfado Koda ta Farfado Har An sallaci Alhaji Bukar Bulama Zuwa gidansa na gaskiya sai da Ta Iske Su Anty yagana dasu Anty Rahila Sunzo Anata Kuka Gida ya Cika da Jama”a.

 

Aneesa ta tabbatar tayi Maraici Domin ko bakwai din Alhaji Bulama Ba”ayi ba Tafara cin Ubanta Domin Adane za”a mata mgana tana Gardama yanzu Kuwa Duk Wanda yamata Mgana Ta Tsaya Wani Iskanci Sai dai Taji Duka Hatta da mama Falmata Bata ta Ragamata Tunda Daman Ta Dade Tana Tusama Mutane Haushi da Sangartanta,Bayan Rasuwarshi Aneesa Ta Tsiri Sangarta kala kala na Ta Wuni tana Kuka batacin Abinci Ko Mgana Aka mata sai Ta Hau Ihu Tana Kuka Tana Birgima Tana Kiran Sunan Alhaji Bukar Bulama ganin Haka ya sanya Yaya Ali ya Sanyata Adaki yamata Dukan Tsiya Wannan Shine Dalilin Daina ma Mutane Kukan Banza da Aneesa Tayi

 

Sai Abu na gaba Mganar Makranta tun bayan Rasuwar Yaya Ali ya maidata Makrantar Islamiya Ammh Aneesa bata Zuwa In ta Fita Gida sai Ta tafi Wata Primary Gwannati Tayi ta Wasanta Har Atashi gida Batasan Yaya Ali na Zuwa Makrantan Dubata ba Ranar Daya gane bata Zuwa Sai da ya barta kwance Da Duka ya gama Nashi mama Falmata ta Kara mata Mama yana ce ma Ke Amsanta Wani Lokacin Ammh Duk da Haka Aneesa batajin Mgana In Lokacin Islamiya yayi sai Anemata Araasa Ta Gudu Su Yaya Ali Sunyi Dukan Ammh Duk Abanza Sai Suka Zauna Shida Yaya Sunusi Suka kawo Shawaran Barin Aneesa da garin Borno Gabadaya Kila Awani Wajen Ta zama yarinyar Kirki Tayi karatu.

 

Haka ko akayi Haihuwan Matar Yaya Ali na Biyu Duka Su Anty Nafi Suka zo Toh Awannan Zuwan ne Yaya Ali ya bama Anty Yagana ni Tatafi Dani chan Ibadan Da Niyyar ta Sanyani Amakranta Da Farko Bataso Tafiya Dani ba Ammh Sai Yaya Ali yace Dole Tatafi Dani,Aneesa bata san da Zencen Tafiya ba sai Ranar da Zasu Tafi Aiko Sai da Yaya Ali da ya Sunusi Suka Hada Karfi Wajen Sakata Cikin Mota Haka Take Kuka Tana Kiran Sunan Alhaji Bukar Bulama kamar Wacce za”a Tafi da Ita Inda bata sani ba.

 

Anty Yagana Tayi Nadamar Tafiya da Aneesa Yafi Cikin Kwando Domin Koda Suka Isa Ibadan Aneesa Kin Shiga Gidan Anty Yagana Tayi ta Coge bakin Get Tana Ihu Tana Kuka Tun Tana Lallashinta Harda Karshe Tabata Haushi Tabarta nan Tayi Shigewarta Cikin Gida Aneesa nan Ta Zauna tana Kuka harda Majina Har Mijin Anty Yagana ya Dawo Ganinta Awaje yasa yagano Bakin Zaren Wanda Dama Tun Da Suka Iso Anty Yaganar Ta Mishi Waya ta Sanar Dashi Dakyar da Sidin Goshi ya lallasheta ta Shigo gidan Yan aikin Anty yagana na mata sannu da zuwa ko kallo basu isheta ba,Dayake Tunda Anty yagana tayi Aure Allah bai taba bata haihuwa ba.

 

Kwana Tayi kuka da Gunjin Tana Fadin Ita Akaita gida Tun Anty Yagana na Kallonta da Takaichi Hartafara Saka mata Hannu Da Zaran Tafara mata Wannan Kukan Banza Cikin Wannan Halin Aka samar mata Makranta,Ranar ko Da Anty Yagana Da Mijinta Suka kai Aneesa Makranta Sunga Tijara Domin Cikin Mota ta Coge Tana Kuka da Ihun Ita bazata Shiga ba Ba Lallashin Duniyan da Mijin Anty yagana bai mata ba Ammh Aneesa bata Saurareshi ba Karshenta Shida Security,Suka Shiga Da Ita Office din Principal din Mkranrta Abun Kunya Aneesa Tana Birgima Akasa Tana Kuka Saboda An Kawo ta Makranta Tun Alokacin Anty Yagana ta Zargi Cewa Aneesa ba Ita Kadai bane tana da Aljanu.

 

Direba Ke Kaita Makranta yaje ya Daukota,Ammh Kullum da Kuka Take Tafiya Domin ya Ali Har Ibadan yazo yamata Duka Sai da ya mata Targade,Shine Dalilin Daya Sanya Take Zuwa Mkrantan Jss1 wanda Kullum sai an kai Sunanta Office din Principal Tasaka sargent ya mata dukan tsiya saboda rashin jinta da kuma zaluncin yara wadanda tafi karfi.

 

 

Kullun da Case din Da Aneesa Ke Jawowa a cikin makarantar hukumar Makaranta gaji Suka Kira Mijin Anty yagana Suka Sanar Dashi Suka Kuma Bama Aneesan Suspention Abun yayima Anty yagana Ciwo Har Itama ta Saka Aneesan Daki Tayi Ta Dukanta,cike da takaichi Wannan Dalilin Shi ya Sanya Aneesa Ta Hada kayanta Tsab ta Gudu Daga Gidan Anty yagana Dakyar da Sodin Goshi Aka ganta bayan An Wuni Ana Nemanta Sai Daga Baya Aka ganta Atashan Mota Ai Washegari nayi Suka Sakata Amota da kayanta sai Borno Anty Yagana Ta Dawo Da Ita tace Bazata iya ba.

 

Abun yana Damun mama Falmata Ammh Aneesa Ko Ajikinta Dadima Takeji Ta Dawo Wannan Abun yabatama ya Ali rai Sosai Batare da Shawara da Kowa ba Ya Dauketa ya kaita Maiduguri Wajen Anty Nafi,Wanda Ko Sati Daya Aneesa Batayi ba Ta Gudo ta dawo gida,ba Saboda Komai sai Mugunta Anty Nafi bata da Kirki ga Saka Aiki ga Mugunta Tayi ta Dukanta Kwatam Rana Tsaka sai ga Aneesa Ta Gudo Daga Maiduguri Zuwa Borno Abunda ya Hasala Yaya Ali ya sata Daki yana ta Duka,gashi bata jin duka domin da tanaji da tuni Aneesa ta natsu ta dawo mutum kamar kowa ammh ina dukan ma kamar kara famdarar da ita yake,kwata kwata bata tsoro ko kadan,wani lokacin ne ma take jin tsoron ya Ali ya sunusi kuwa tagama Raina kurarsa dama tuni

 

ya Ali na cikin mata fada yana Kai mata Duka sak Allah ya Kawo Muktar Dashi da Anty Rahila gidan Suka Tarar da Aneesa na Cin Ubanta Hannu yaya Ali kowa na gani kuma ba Wanda ya Ceceta Saboda Tafara Isar Kowa da Hallayarta.

 

Lokacin Ko Wata Biyu Ba”ayi ba da Gwannatin Nageria ta Zana Sunanshi Amatsayin Chief Amry Of Staff Na Kasa baki Daya bayan Duka Mukaman Daya Taka da Gwagwamarya,Har Sun koma Katon Gidansu Dake Garki Abuja ya Kuma Dauko Daada Daga Yola Tunda Shekaru Biyu Kenan da Rasuwar Baffa Hadi

 

Muktar Shi ya Kwaceta Hannun ya Ali Aneesa na Kuka da Majina Ta Lafe Jikin Muktar Tana Raba Ido Shiko Yaya Ali Haka yake Fada yana labartama Su Anty Rahila Abunda Aneesan Tayi Jin Haka yasa Muktar yace Zai Tafi da Aneesa Abuja Kuma Insha Allahu ya Tabbatar da Cewa Zan Zauna Kuma Zanyi karatu.

 

Abunda yabama Kowa Mamaki yadda Aneesa batayi Tijaran Data saba ba indai za”a kaita wani waje ba, Sai dai Har Muka Isa Abuja Ina Kuka Harda Shessheka bakomai ke Sata kuka ba sai In Ta Tuna Zencen Makranta Shike Kara Sakata Kuka,Aneesa Bata taba Zaton Akwai Wanda yafi Karfin Iskancinta ba Sai da Anty Rahila tatafi da Ita Abuja Chan Mafarin Haduwarta da *MR BELLO* the young Teacher Wanda yayi Rugu Rugu da Aljaninta,na Rashin Son Makaranta ya kuma ya Dauketa yayi Nisa da Ita da Kowa Nata,ko ahaka aka bar Bello yaci Babbar Nasara wajen inganta rayuwar Aneesa amatsayinta na ya mace.

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment