Littafan Hausa Novels

Miskilanci Ko Gidadanci Hausa Novel Complete

Miskilanci Ko Gidadanci Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

MISKILANCI KO GIDADANCI

 

Written by Manshart

 

~In dedicated to my luvly Dad (Alhaji) nd (Bissalam)~

 

 

 

*Part 1*

 

*BISMILLAHIR-RAHMANI-RAHIM*

 

 

 

Da shirinsa yafito, sanye d kananan kaya riga white da wando red color, kayan sunyi matu’kar dai-dai da halittar jikinsa. Farine dogo bacan ba, kuma yanada karfaffin kirji ba sosai ba guy ya hadu matuk’ar haduwa.

 

Sauri² yake yana saukowa daga benen dake cikin k’ayataccin falon nasu. Wata dacci juwa hakan nagani da shekarunta bazasu daramma 45 b tafito daga wani daki. “Daga ina haka sai famar sauri kake kamar wanda zai bar 9ja?” Cikin murmushi ya dubeta yace “Mummy barka da sfia” tace “Yawwa, nace ina zuwa haka sai famar zuba sauri kake? Incedai gurin daurin auren kayi?” “Daurin aure kuma?” “Ohh harka manta kenan? Toh na wannan abokin naku Sadiq yake ko wa?” “Ohh Mummy na tina, aa ba daurin auren zani ba Mummy , yaya Sabir ne ya aikeni skul akan maganar saka Junior a makaranta, ko jiyama ya tunamin amma na shaafa kinga sai yanzu na fito” yakara sa maganar tareda dubin agogon dake a hannusa” “ok, naji, bazakaje daurin auren bane?” “Mummy zanje idan nadawo da huri” Mummy ta kalleshi kallon rashin yarda tace “Hmm wlhy ka gyara rayuwarka Alhaji! ace mutum baya shiga mutane, sai kace wanda za’a cinye, idan bakaje nasuba kana ganin idan naka yazo su zasu takoma ne? Wlhy ka gyara rayuwar ka, mtwss” ta huce kitchen batareda ta ko sake kulashiba.

 

Oum Sharifa Ce Karin Bayani Akan Novels Group Namu

Shi kanshi yasan Mummy ta fusata, sanin Mummy bazata kulashi yanzu b yasaka shi kaba kai yahuce.

 

Pkg spc ya zarce yadauko mota ash, yashiga ya fice batareda ya kula yan uwansa dake nan harabar gidan suna tattaunawa ba.

 

15mints ya isa gate din makarantar, mai suna *Brilliant Footsteps Academy* batareda bata lokaci ba akayimasa iso zuwa office din principal din mkrntr.

 

Baayi wani wstn tm ba komai ya daidaita, kasan cewar Alhaji yazo da cash ba wata matsala. Nan aka bashi komai har uniform da littattafan da zai fara karatu dasu. Godiya yayima principal din yafito.

 

Tafiya yake tinanin maganar Mummy yake, yasan idan yakoma gida yanzu zatamai fada baije daurin auren ba. Juyarda akalar motar sa yayi yanufe gidan gonar Dady’n su dake bye pas.

 

Horn yayi masu garin gidan suka wangale gate din, sanin ko waye ke horn. Shiga yayi gadangadan sai inda aka tanadar na ajiye motoci, anan ya tsara tashi yafito cikin takunsa mai daukar hankali.

 

Masu gadin gidan sai sannu da zuwa suke masa amma ko yajuyo ya kallesu, hasalima murtuke fuskarsa yayi, kai kace wani kumarci ne.

 

Inda aka tanadar na shan iska ya nufa, runfunonine gewaye ta ko ina, can bangarin na dama wasu stones ne anmusu adu da paint green sak da fulawoyin dake hurin, daya bangarin hurine dake manne da glass ga tsuntsaye kanana wurin sai kuka suke cikin muryarsu mai dadi tsoi-tsoi-tsoi🐧

 

Can daga nesa gadina ce faffada, mai cike da plants kala-da-iri, sai sanyi ke fesowa tako ina kace cikin a,c ne kake. Kasan cewar hurin kusa da teku ne ga kuma stream ta bayan gidan.

 

Cikin runfunan yanufa cike da shauqi, danshi a rayuwar sa yafiso yaganshi irin wannan hurin da ba wani bil’adam dazai takuramasa. Nan fa ya wuni sai da misalin karfe 3:30 yafito daga gidan, yakama hanya ya nife gida.

 

A layin nasune ya hadu da group² na yan unguwar tasu, kasancewar unguwar GRA ce, baka ganin kowa sai yan kwarorin samari, sun fito shak’atawa. Banda Alhaji danshi bashida wani aboki ko daya wanda zaace azo a gani. Shi a rayuwar sa yafiso yakadaita shikadai tillo!

 

Tafiya yake ko ina yakai cikin layin zai hadu da gungun samari ana zaman layi, zaman kashe wando, zaman kallon yan mata aga wacece tafi aji ko tafi iya dressing, hannu kawai yake musu, shima sai idan sune suka dagamai yadaga musu idan ya lura, dan ko gefensu baya kallo.

 

Haka yahuce hurin gungun wasu samari sai firar girlfriends dinsu suke. Rage gudun motar yayi tana tafiya slow².

 

Har yakawo inda suke, wucewa yayi batareda yace dasu uffan b. Can wani daga cikin guys din yace “Mazaa gafa nakunnan ya doso!” daya yace “Hmm wai Alhaji kake nufi?” Guda yace “ai JB ni a rayuwata ban taba ganin mutun irin wancan guy’n ba wlhy, shikadai yake rayuwarsa, idan ma kakada kanka kayimai mgn toh fa yarfaka zaiyi” nan wani yanisa yace “ohhh ni duniya! ba aiwa dan Adam dai-dai! Yanzu da ace yana kula mutane kuma ace ga abinda yayi, miye naku na wani baya kulalaku waye² nd other? Ni kunga wlhy rayuwar sa tana mugun burgeni, musamman rashin surutunsa, guy’n so silent miye na damuwarku akan wanda bai damu da kuba”.

 

Sai can dayan yaci “gaskiyar ka Shafson, nima yana burgeni wlhy sosai, shidai baya zaman layi, baya da surutu bale kace yayi gulmar wani, idan kaganshi yafito toh masallaci zashi ko fita zaiyi” Shafson yace “toh kagani just face our business mana” nan fa suka hada baki sukace “hakane fa wizzy”

 

Shi gogan baimasan miyar da akeshaba, haka ya isa gida a gajiye.

 

Dadi sosai yaji ganin ba kowa a falo, ya haura sama abinsa. Da shigarsa birthroom yanufa yatube tufafin dake jikinsa ya sake washa, haka ya kammala wankan ya fito, waldrop yabude yadauko wata jallabiya milk ya saka, fitowa yayi yanufe dakin Mummy dayasan sarai ya gama bata mata rai a yau.

 

Da sallama ya shiga, yatarad tafito daga toilet da alamu wanka tayi ta fito.

 

Ko kallon inda yake batayiba tacigaba da shafa manta, nufota yayi, yayi hugging dinta tabaya yace “pls Mummy nasan na bata miki rai, amma dan Allah kiyi hakuri, dont b sed with me pls” yagama maganar a shagwabe. Ita kanta Mummy yabata dariya irin yadda ya isa maganar. Amma ta daure tace “Alhaji kenan, kai ba yaro ba amma a koda yaushi matsalar ka bata k’arewa, nifa mahaifiyarka ce! Idan akwai abinda ke damunka kasanar min mana”.

 

Cikin ladabi yasauko daga kan gadun yace “wlhy Mummy ba abinda ke damuna, idan ma akwai kinsan am told u, bazan boye miki komai ba” Mummy ta girgiza kai tace “dole akwai abinda ke damunka, ni a iya rayuwata bantaba ganin mutun like u b Alhaji, wannan abin yana jazama karan tsana tsakaninka da mutane. Yakamata kagyara mana” takai karshe maganar tana kallon sa.

 

“Toh Mummy, in shaa Allahu i will change” Mummy tasake murmushi irin nasu na manya tace “Yawwa Baba nah!, wai ina kashiga ne yau tun safe sai yanzu” tabe baki yayi yace “Mummy naje gidan gona ne nadan rage zango” yafada tareda tashi yakoma kan gadun, kusa da ita.

 

Mummy tayi dariya tace “nasan zaayi haka shiyassa ma ban wani nemekaba, nasanka da gidan gonan nan, zuwa ma zanyi na kerama makekin gida acan kazauna kaida surukata” “dagaske Mummy zaki? Wlhy ina matu’kar son gidan gonan nan ” Mummy tayi dariya tace “wasa nake kasan sarai Daddynku bazai yarda ba” “Zai yarda man Mummy idan kika gayama sa” Mummy tace “kaga ban iyawa da sagartannan taka. Kaci abinci ne?”

 

Yatsina fuska yayi yace “Yap Mom ” Mummy ta dubeshi tace “Ban yarda ba, nasanka ai bakasan cin abinci ko nan gida nice mai matsama nabaka abaki bale can gidan gonar waxai baka” “Mummyy, nacifa wlhy” Mummy takai tsaye zata saka tufafinta tace “Can da kaida cikinka, tunda baka tsoron ulcer” “Bazama ta kamaniba”

 

Dai² nan aka kira sallar magriba, tsam yamike tsaye yace “Mummy bara naje nayi sallah” Mummy tace “toh adawo lfy, ayo muna addu’a” yakai k’ofa yana cewa “kullum anai muku ai Mummy, fatan mu dai Allah yasa munayi a bakin mala’iku” Mummy tace “Ameen Baba nah” yafita.

 

Nasan masu karatu zasuso sanin wanene wannan ALHAJI Musamman Manshart novels akwai son jin kwakwaf toh kubiyo BASAKKWATA

 

*MISKILANCI KO GIDADANCI

 

`Written by Manshart

 

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) nd Mummy (Bissalam)~

 

 

 

*Part 2*

 

*Usman Abubakar Ibrahim*

Shine asalin sunansa. Mahaifinsa Alh. Abubakar , dan asalin garin Bissilam ne, acikin babban birnin sakkwato. Mahaifinsu sunansa Ibrahim wanda ake kira da IBRO yanada mata 1 mai suma khadija, khadija yar uwar IBRO ce, auren Zumunci ne akai musu.

 

Inda ankayi aure wata tara ta zankado danta mai kyau na ji da fada. Kasancewar fulani ne dukkansu, haka ran suna yaron Inna khadija yace suna Abubakar, bayan shekara biyu ta haihu mai bima Abubakar wato Sulaiman, bayan wasu shekaru Allah yabata zankadediyar budurwa wacce taci sunan mahaifiyar Ibrahim wato A’isha.

 

Sun samu gata da kulawa sosai, dan kuwa malam IBRO mutun ne mai zafin nema, baya wasa da iyalansa ko kadan. Aduk fadin garin ansan malam IBRO mutun ne na mutane, ga mutunci da karramawa. Haka kuma dansa Abubakar yagadosa, sai Sulaiman shima baabarsa a bayaba. Haka Aisha yar autarsu wadda dagareta Inna khadija bata sake daukar wani cikiba, Allah yawa Aisha kunya sosai.

 

Rayuwar su suke cikin jin dadi da kwanciyar hankali, malam IBRO yasakasu makarantar yaki da jahilci ta garin, ba laifi suna ganewa duk da makarantar government ce bawani kulawa sosai akeyi ba.

 

Inda Abubakar yana primary 5, Sulaiman na primary 4, auta na primary 1. Inna khadija tana matu’kar son yar tata, a cewarta auta ce har tamaidata auta. Abubakar yana ji da A’isha, komai yasiyo A’isha dai A’isha, ba abinda ke rabashi da ita. Bacci ma a daki daya sukeyi, idan yafita yayo kwadagonsa A’isha zai yoma siyayya yakawo mata, shiyassa itama takeson hamma Abubakar, idan yafita komai hamma Sulaiman yayi mata idan Abubakar yadawo zata sanarmai sai ya ramo mata.

 

A kwana atashi Abubakar yakammala primary skul, kuma jarabawarsa tayi kyau, haka ya shiga bording school Jss 1 a *Government day secondary school Bissilam* karatu yake sosai. Yana final exams dinsa mahaifinsa yarasu.

 

Inna Khadija tayi rashin mijinta mlm IBRO wanda kowa a garin yasan shi mutunin kirki ne. Bayan Abubakar yakammala jarabawarsa yadawo gida yatarad da mugun labari na rasuwar mahaifinsa! Wanda yayi kuka sosai da bakin cikin rasa mahaifinsu.

 

Bayan wata 1 result dinsa yafito na waec da neco dinsu. Kuma yace credit sosai kusan duk credits dinsa A ne sai can zakasamu B. Gomnati ce tadauke nauyin karatunsu kasancewar Abubakar yanada kokarin sosai, yana dai daga cikin wadanda ake alfahari dasu a makarantar.

 

*USMANU DAN FODIO UNIVERSITY SOKOTO (UDUS)* acan yajona yacigaba da karatunsa a Inda yakarance business education. A can ya hadu da Shafa’u wadda suka fara soyayya! Shafa’u yar asalin skt ce. Bayan sun kammala degree ne Abubakar yasanar ma iyayensa akan maganar Shafa’u, Inna Khadijat ta amince da maganar kuma ta yaba da hankalin ta. Baba Hamza ne kanin margayi Ibrahim yajagorance auren, Inda aka biya sadaki aka saka ranar aure.

 

Ba laifi Abubakar ya hada kayan lefe duk da ba wasu kaya ne akeyiba, kasancewar ma su Shafa’u a birni suke, suna irin yar riyar nan ta aure. Abubakar baiyi wata riyaba cos kar-tasan-karce tsakanin sa da Shafa’u, tasan ko waye Abubakar ba wani haline dashiba.

 

Haka akasaka ranar aure Rabi’ul-auwal. Shirye²n aure akafara tsakanin bangarin nan guda biyu. Barin su Inna Khadijat da wannan shine farko, su auta sai murna akeyi hamma Abubakar zai aure yar burni, lolz.

 

Akwana atashi asarar mai rai! Yau takama Asabar acikin watan Rabi’ul-auwal. Dinbin alumma suka shede dauren auren *Abubakar Ibrahim* da *Shafa’atu Usman* anyi taro lafiya, inda yan uwan Inna Khadijat sukazo sokoto dan ganin gidan amarya sakamakon skt Abubakar yazauna Dan yanaso ya cigaba da masters dinsa anan. Auta tayi tsayin daka akan sai anje da ita taga matar hamma Abubakar, badason Inna Khadijat ba, yan uwata suka turza akan abarta taje tunda suna tare ai zasu sawota a gaba su dawo da ita.

 

Kaddara ta rigaye fata! Bayan sun iso sokoto garin fitowa mota auta ta subuce musu, aka nema aka rasa Auta, yan uwan Inna Khadijat kasa komawa sukayi Bissilam sbd jin kunyar yanda zasu tunkare Inna Khadijat da maganar batan yarta!

 

Haka aka sanar ma Abubakar da har kwanci saida yayi asibiti sbd girgizar dayayi na rashin kanwarsa tillo wadda yafiso fiye da komai na duniya. Barin Inna Khadijat wadda shine sanadiyar jininta yayi up! Daga karshe dai shine musabbabin rasuwar Inna Khadijat!

 

Abubawa goma-da-goma suka tararrama Abubakar, bakin ciki baya kwana kullum sallah yake yana rokon Allah yasake hada tozalin idanunsa Dana Auta. Abubakar dai rayuwar auren zan iya cewa alhamdulillahi dai! Sulaiman yadauko suka dawo nan skt din da zama.

 

Allah majirokon bawansa (akoda yaushe abinda Allah yabawa Dan adam shine mafi alkhairi agareshi! So dayawa mutun zaiyi addu’a yadawo cewa: wlhy nayitayin addu’a amma Allah bai amsaba! Toh musani Allah yayi alkawarin duk lokacin da bawansa yarokesa da ihlasi zai amsa masa. Wani zai iyayin addu’a ta Allah ya azurtashi, shiko Allah yafika sanin abinda yafi dacewa dakai. Mai yuwa idan Allah yabaka arzikin yazamoma hanyar dazata jaka zuwa wuta! Zaka iyayin sabon Allah cikin arzikin ka, kasha giya, kaje gidan rawa, kayi zina, da sauransu. Amma sai Allah yajuyema wannan addu’a dakayi ta dukiya tazamto# idan Allah yarubuta cewa zaka fita kayi accident ka kakkarye a k’afa da hannu! Toh sakamakon wannan addu’ar dakayi sai Allah yasa kana tafiya kadanyi karo da dutsi kan hanya ya jima cewo kadan! Kaga ai ko nan Allah ya amshe addu’ar ka. SBD hk yan uwa ako yaushe mukasance masu komawa ga Allah masu kaskantar dakai ga Allah, masu kyautata zato ga Allah.)

 

Allah yabaiwa Abubakar aiki awani company ba laifi yana samun albashi mai tsoka wanda yake ciyarda matarsa da dan uwansa.

 

 

MISKILANCI KO GIDADANCI

 

“`Written by Manshart

 

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) nd Mummy (Bissalam)~

 

 

*Part 3*

 

Haka rayuwa taci gaba da tafiya yau dadi gobe ba dadi! Har Allah ya baiwa Shafa’u ciki, wata tara ta haihu danta mai suna Sabir, sai kuma bayan shekara biyu tasake haiho yarta mai suna Zainab. Ta jima bata koma haihuwa ba.

 

Abubakar arziki sai karuwa yakeyi, har yasake wani aure. Yanzu mata biyu ne dashi, Shafa’u da Saratu.

 

Saratu tanada ‘ya’ya 2 itama amma duk mazane Jabir da Saddiq.

 

Bayan wadansu shekaru Allah yabaiwa Shafa’u ciki mai cike da laulayi, tunda tasamu cikin bata aiki ko kadan, wani fitinannin cikine Allah yabata, Shafa’u tadai gode Allah da wanga cikin, har ta fidda rai ga rayuwa a duniya.

 

Sai da aka samo mata mai aiki tadinga tayata aikin gida da rainun yaranta 2. Kasancewar itama Saratu cikin ne da ita, kusan duk watansu daya.

 

Zuwa² ciki yakai watannin haihuwa! Ohohooo! Ranar wahala tadawo sabuwa, duk wanda yadube Shafa’u da wannan cikin sai ya tausaya mata. Ranar jumu’a da misalin karfe 11am nakuda tataso gadan²n, kuma Abubakar yafita aiki, sai Saratu da mai aiki kawai. Hankalin su yayi matu’kar tashi ganin Shafa’u tana cikin tsananin wahalar naquda, da taimakon Allah Shafa’u ta haihu da misalin 3pm.

 

Tirkashiiii karkuso ganin wannan hadaddin baby’n, masha’Allah! Haka akayima yaron wanka aka kimtsashi, tsintsar kyaunsa yakara bayyana, duk wanda yazo ganin yaron sai ya fita da maganar kyawonsa. Abubakar yaji dadin ganin wannan baby’n nashi mai kama da kanwar sa A’isha sosai, lokacin batan auta yadawo mai a rai. Ran suna dan yaci sunan mahaifin Shafa’u, wato *Usman* kasancewar Abubakar yayi mata alkawarin saka sunan mahaifinta. Amma Alhaji suke kiransa, sbd shima mahaifin Shafa’u haka ake kiransa. Shafa’u taji dadi sosai na saka sunan mahaifinta.

 

Sati 1 da haihuwar Shafa’u Saratu tahaiho yarta tubarkalla! Wadda ake kira Labila. Bayan Labila Saratu ta haihu twins mace da namiji Husnah da Alhasan.

 

Haj Shafa’u tana matu’kar ji da wannan dan nata, batasan ganin bacin ransa ko kadan. Duk da bayan hauhuwarsa Shafa’u tayi haihuwa 2 A’isha wadda Abubakar ya sakamata, sa’annan autar Mummy Shafa’u mai suna Sajida .

 

Shekaru sunja, Sabir yayi aure da matarsa mai suna Kubra har ta samu haihuwa da namiji Abdullah, Zainab ma tayi aure a Kaduna. Tanada yara biyu, Musaddiq da Sadiqa.

 

Jabir ma yayi aure da diyarsa Munawwara. Sai sadiq dayake kanyi a yanzu.

 

So da gata Mummy take bawa Baban nata sosai.

Amma sai dai kash!!! Alhaji yanada wata rayuwa, wadda kowa a familynsu yakejin haushinsa bayason surutu, baya magana sai tazama dole, ko waye kai Alhaji baya zama yayi fira dakai, Mummy ce kawai yake iya zama suyi fira, itama sai idan ba kowa a dakinta zai shiga suyi fira, ga matsananciyar kunya harta tashin hankali! Duk yadda zan zayyana muku irin kunyar Alhaji toh ya d’aramma can. *Miskiline* na karshe! Dariya ma wahala take bashi, bale ya zauna ayi fira dashi.

 

Wannan shine cikakkin tarihin Usman wanda akafi sani da *Alhaji*

 

*Mun dawo labari*💃🏿💃🏿💃🏿

 

Misalin karfe 8 na dare, kwance yake kan bed dinsa, yana duba wadansu takardu, ga alama wani abun yake nema.

 

Guntun tsaki yaja tareda daukar takardun ya tusasu a locker, yadawo yakwanta yajawo wayarsa ya kunna data. Sakone turoro suke famar shigowa ba full stop, jiran su yayi saida suka gama shigowar dasuke yafara chart abinsa.

 

Duk da ba kowanne grp yake magana ba, grp daya yake magana shima gaisu kawai yake yafito nanufe istgrm ko Facebook IMO da BBM da sauran su.

 

Yau kam fitowa yayi yanufe browser domin yin browsing, karar shigowar message yajiya ta WhatsApp dinsa. Sharewa yayi yaci gaba da aikin gabansa. Bayan minti 5 wani yakara shigowa, tsaki yaja yafito daga browser yanufe WhatsApp din dan ganin wannan no din data dameshi. Yatsine fuska yayi ya dallama no din harara, yafito yaci gaba da browsing dinsa.

 

Sai karfe 10:15pm yakashe data yahau baccinsa cikin kwanciyar hankali.

 

Ita kuwa haushi taji. a ranta tace “wannan wani irin dan rainin hankali ne? Ko waye mai wannan no yacika MISKILI! Mtwssss” taja tsaki ta kashe datar ganin shima yadade da sauka. Littattafan ta tajanyo taci gaba da muraji’ar ta dan gobe zasuyi jarabawa a islamiyya.

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment