Littafan Hausa Novels

Mijinki Mijina ne Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Mijin ki Miji na ne Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

MIJINKI MIJINA NE

 

Rubutawa Karimatu Abdulhamid

( *MUMMYN MINAL*)

 

☘️𵠠*SUBBAHANALLAHI WABI HAMDIHI SUBBAHANALLAHIL AZIM*☘️

⚖️

*HAMDALA WRITIN’S ASSOCIATION💪*

_*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL’UMMA📚}}*_

 

*✨✨{{H.W.A}}✨✨*

 

🅿️ *1-2*

 

*BISSIMILLAHI’RAHAMANIRRAHIM*

*Dasunanka Allah nake farawa, Allah kayi dad’in tsira da Salati babu adadi ga Annabinmu habibinmu Muhammad Sallallahu ailai wasalam*

*Ya Allah kabani ikon rubuta abunda zai k’ari al’umma, ba abunda zai ‘batar dasu ba, ya Allah kayi rik’o da yatsun hanuna wajen rubuta alkairi*

 

*wanan Littafin sadaukarwa ne ga* *k’ungiyar Potiskum writer’s association*

*( POWA) ya Allah ka k’ara ha’baka k’ungiyar, Rabbi ka k’arawa Mabiyanta basira da* *fik’ira, jinjina gareku mabiyan( POWA) ina muku fatan Alheri*

Matar Aure Hausa Novel Complete

*Sak’on gaisuwa gareku Hamdala writer’s association Allah yak’ara muku basira mai amfani, ina mik’a gaisuwata zuwa gareku Majalisar Marubuta, Rabbi ya k’ara muku basira, shirye-shiryenku na burgeni over, jinjina gareku ‘yan MK palace, Rabbi ya k’ara muku basira, had’in kanku na burgeni over*

*INA K’ARA MIK’A GAISUWATA GAREKU MY REALLY PANS, GANINAN KUMA TAFE GAREKU DA K’AYATACCEN LABARIN DA NAZO MUKU DASHI INA NEMAN GOYON BAYANKU KUMA, MASOYAN ASALI. DOMIN IDAN BABU KU NIMA BAZA AGANNIBA NAGODE*❤

 

 

*PAGE 1&2*

*Masarautar Failura*

_____Masarautar Failura babban Masarauta ce awani gari ayankin arewacin Nigeria, Masarauta ce mai babban tarihi wanda a qalla sarakuna goma ne sukayi mulkin masarautar har izuwa sarki na yanzu wato Sarki Abdulgafar d’an Yazid, wanda yake adalin Sarki, Masarautar Failura tatara Abubuwan tarihi, sanan gata da al’adu, iri daban-daban, Masarauta ce maitafiya da zamani, yaude cikin Masarautar nafad’a domin kawomuku rahoton abunda ke tafiya acikin Masarautar.

Tafiya takeyi cikin takun qasaita tamkar hawainiya, wanda taci ado da wata jar atamfa Super Holland, wuyanta da kunenta da hannayenta sanye suke da gwala gwalai, fuskarta kuwa sai sheqi takeyi sbd kyau, jar alkyabba ta d’aura asaman kayanta wanda taji aikin surfani da Farin zare, bayi da kuyangine zagaye da ita, wasu agabanta wasu kuma a bayanta, jakadiya kuma tana gefanta tana mata kirari kamar haka.

“Taka lafiya Gimbiya ‘yar Sarki jikar Sarki tata’ba kunen sarki, matar Sarki, uwar sarki, kakar Sarki, saide har yanzu bakiga yarima maijiran gadon da yadace da keba, ko kuma shi kansa sarkin, ina kuke maza ku baiyana kanku domin Gimbiya TAFISU mai takalmin qarfe taga wanda yadace da ita, domin ita saide taza’ba bade aza’beta ba gaba sallamun baya sallamun ‘yar Sarki mai takalmin zinare.

Itako Gimbiya TAFISU sai wani jiji da kai takeyi, tana shashaqar iskar Masarautar ahaka suka nufi shashin Memartaba Sarkin Failura.

suna nufan shashin fadawa da suke gadin shashin nan suka farayiwa Gimbiya TAFISU k’irari, su kuma bayi da kuyanginta, suka tsaya anan domin jiranta, jakadiya ce tatakewa Gimbiya TAFISU baya, har zuwa cikin parlour d’in Memartaba.

Da Sallama abakinsu suka shiga parlour d’in wanda yagaji da had’uwa, Memartaba ne zaune acikin d’aya daka jerin kujerun da yake parlour d’in, kai tsaye Gimbiya TAFISU tanufi kujerar dake kusa da Memartaba, tazauna sanan ta duqar da kanta qasa, tace ” gaisuwata a gareka Memartaba”

Itako jakadiya zuwa tayi ta duqa agaban Memartaba sanan tace ” barka da hutawa ranka yadad’e, ga Gimbiya TAFISU nan ta’amsa qiranka”

Shiko Memartaba Abdulgafar hannu ya d’aga mata sanan yace ” angaisheki jakadiya Adama”

Tashi jakadiya tayi tajuya zata fita amma Memartaba yace ” zaki iya jiranta anan jakadiya”

Dan haka Jakadiya takoma can gefe tatsaya.

Shiko Memartaba kallon Gimbiya TAFISU yayi, cikin muryarsa ta mutanen kirki yace ” Maryama bansan sai yaushe zakiyi hankali ba, ki dubade kiga irin gaisuwar da jakadiya tayimin, amma ke maimakon kiyimin irinta, amma girman kai bazai barki ba, ki gyara halinki maryama ki zama mutumiyar kwarai kiduba fa kigani kece babba d’iya amasarautar nan kamata yayi sauran ‘ya’yan cikin Masarauta suyi koyi dake, bawai aringa Allah wadarai da halinki ba”.

 

Itako Gimbiya TAFISU kallon Memartaba tayi tace ” kayi haquri Memartaba amma ni nafison ka qirani da Gimbiya TAFISU, nafiji jin dad’in wanan sunan fiye da Maryaman da kake qira”

Kallon ta Memartaba yayi yace ” Allah ya shiryeki Gimbiya Maryama, qiran da namiki kema kinsan akan miye, nagaji da kallonki hakanan a cikin Masarautar nan, sbd haka ina fad’a miki da babbar murya nabaki lokaci qanqani kifitar da mijin aure, kafin raina yagama ‘baci akanki tabbas idan kika bari hakan tafaru zanyenke duk hukuncin da naga dama”

“Allah yahuci zuciyar ka Memartaba, amma ni har yanzu banga wani d’a namiji da yayi min ba, amatsayin mijin aure ba”

 

“Ashe ke mutumiyar banzace bansani ba, to kijirayi hukuncin da zanyenke miki, shekarunki nawa kina zaune ba aure mulki haukane ko akanki akafara zama ‘yar Sarki toni bashashashan sarki bane dole ne kifitar damiji koni nahad’aki dako waye kuma dole ki zauna domin kuwa yau kika cika shekaru 32 da haihuwa dan haka ko wata biyu bazan bari ki qara akaiba sai kinyi aure kuma kitashi kificemin anan karki qara zuwa gurina har sai kinsamu madafa” sosai Memartaba yake fad’a ransa a’bace itako Gimbiya TAFISU hawaye takeyi sbd jin zafin fad’an da Memartaba yake mata, sanan tatashi tanufi hanyar fita, Jakadiya ce ta dafata suka fice a shashin Memartaba, shiko Memartaba ransa ‘bace yayi shirin fita fada.

 

Gimbiya TAFISU kuwa tafiya takeyi zuciyarta na quna sbd fad’an da Memartaba yayi mata, bayi da kuyangi kuwa dake aiki, afilin gidan suna ganinsu suka shiga kaucewa domin sunsan Gimbiya TAFISU bata da kirki ko kad’an, wata kyakyawar yarinya ce qarama da baza ta wuce shekaru 16 ba, amma daka ganinta kasan baiwa ce, domin kuwa yanayinta da kayan jikinta yanuna hakan, tafiya takeyi baiwar tana rangaji tamkar iska zata d’auketa, kanta duqe yake aqasa domin haka take intana tafiya, hanayenta kuma d’auke suke da wani kwandon saqa mai kyau, wanda yake cike da kayan marmari irin su Apple da lemo da inibi da sauransu, kwata-kwata baiwar bata lura da kaucewar da sauran bayi ‘yan uwanta sukeyi ba, domin ita kanta aduqe yake, tana cikin tafiya kawai taji tayi karo da mutum, ai kuwa kayan hanunta yafad’i ya watse ko wanne yabi nashi hanyar, cikin sauri ta d’ago kai dan taga dawa taci karo, tana d’ago kai taga Gimbiya TAFISU atsaye agabanta tana huci ga jakadiya agefanta tariqe ha’ba alamun mamaki, da sauri baiwar ta dafe qirjinta, kafin tayi wata-wata, kawai sai sauqar maruka hud’u lafiyayyu akuncinta taji, da sauri baiwar tasa hanunta dukka biyu ta tallafe quncinta tana hawaye domin taji zafin marukan, hakan baiyiwa Gimbiya TAFISU sai da tasa qafarta takwarfe qafar baiwar, ai kuwa baiwar tazube aqasa, Gimbiya TAFISU kuwa takata tayi tabi takanta tawuce, wanda baiwar tasake wani ihun azaba sbd da wuyanta da Gimbiya TAFISU tataka da takalminta mai tsini, ai a take baiwar ta sume Agurin.

 

Itako jakadiya duqawa tayi kusa da baiwar tace ” kad’an kika gani ‘yar talakawa jikar talakawa wanda zata qare abauta ita da uwarta har abada, sauran hukuncin kima sai kinfarfad’o ki kar’bi laifinki”

Sanan jakadiya tatashi tabi bayan Gimbiya TAFISU.

Itako Gimbiya TAFISU ranta ‘bace tanufi shashinsu, da sauri gudu-gudu tashige parlour d’inasu wanda ya qayatu da kayan ado, wata hamshaqiyar matace fara tas, take zaune akan daya dake cikin kujerun dake parlour d’in bayi ne da kuyangi zagaye da ita wasu suna mata tausa wasu kuma suna wanke mata qafa, matar tana ganin shigowar Gimbiya TAFISU, saita d’agawa bayin nata hannu, ai kuwa duk sukabar abunda sukeyi suka watse, a parlour d’in, Gimbiya TAFISU ce ta qaraso da saurinta ranta a ‘bace tafad’a akan qafar matar tana kuka.

 

“Cikin tashin hankali Matar tafara shafa bayan Gimbiya TAFISU sanan tace ” lafiya Gimbiya TAFISU menene ? wanene yasaki kuka mekika nema baki samu ba arayuwarki har kike kuka fad’amin yanzunan?”

Cikin shesheqar kuka Gimbiya TAFISU tace ” Memartaba ne”

“Me ya miki Memartaba d’in Gimbiya?”

Matar tatambayi Gimbiya TAFISU.

“Cewa yayi nafitar da miji ko kuma ya had’ani da ko waye”

Cikin masifa matar tace ” qaryane wlh ni sarauniya Kaltum qaryane ayiwa ‘yata d’aya tilo auren dole sbd haka dolene ajiraki harkifitar da wanda yamiki domin kuwa kece babbar d’iya awanan Masarautar, sbd haka qaryar magauta suyi nasara akanmu”

Jakadiya ce tashigo cikin tashin hankali, sanan ta dubi Sarauniya Kaltum tace ” hutawarki lafiya Sarauniyar Failura uwar Gimbiya TAFISU, yaude kam infad’a miki Sarauniya ran Memartaba ya’baci matura akan har yanzu Gimbiya TAFISU bata fitar da miji ba, kuma tabbas Memartaba zai aikata abunda yace. Idan har lokaci yacika Gimbiya TAFISU bata fitar da miji ba”

Qarya kikeyi jakadiya!!!!!!!!!!!!

Sarauniya Kaltum tafad’a da qarfi Sanan tace ” ni bazan bari hakan tafaru ba, dolene Memartaba Abdulgafar yajira Gimbiya TAFISU har tafitar da gwaninta”…………

Hhmm muje zuwa, domin kuwa wanan somin ta’bine!

Wacece Gimbiya TAFISU?

 

Anya Memartaba zaijira Gimbiya TAFISU har tafitar da mijin aure kamar yanda Sarauniya Kaltum tace?

 

Hhmm shin wanan baiwar da Gimbiya TAFISU tataka mata wuya zata rayu kuwa?

Sharhinku shi zaibani kwarin gwiyar ci gaba da

typing.

 

 

Tsarabar Mummyn Minal zuwa gareku my really pants, domin gyaran aurenmu, please wanan sirrin iya matan aure keyinsa banda ‘yan mata.

Kenemi allonki da tawadarki mai kau ‘yar uwa, Kirubuta suratul fatiha qafa daya, amma idan kinzo rubuta hakuri da minjaye to ki budesu suyi fadi, sai ki rubuta sunan mijinki aciki da larabci, idan rubutun yabushe sai wanke da ruwa maikyau ki shanye, wlh ‘yar uwa zaki qara daraja agurin mijinki sanan zai qara jin sonki da sha’awarki, zakiyi farin jini sosai a gurin sa, Sirri ne mai kyau kugwada ku gani ba mallaka bace, kawai kara danqon soyayya sirrin yakeyi tsakanin ma’arauta, idan mijinki yana wulaqanta kine, ko yana neman matan banza insha Allah idan kinawanan sirrin fatihar zai dawo zuwa gareki, inma zaman lafiya kukeyi zai qara girmamaki da sonki, ku gwada kugani domin nima nagwada kuma naga amfaninsa idan baza ki iya rubutawa ba sai kinemi almajiri kibashi sadaka yarubuta miki kuma dan Allah idan kinsamu dama banda wulaqanci kede kiriqe mijinki tsakaninki da Allah, Allah yasa mudace, bawanda zai kwashi wanan gara’basar sai mai karanta Littafin nan, shi yasa nasaka aqarshen page, Allah yaqara mana zaman lafiya da mazajenmu Amin ya Allah.

 

Dan girman Allah in kun karanta kutura zuwa wasu groups d’in nagode.

 

Idan kina son shiga group d’in ki tuntu’beni awanan number d’in 09065120158

Mata zalla.

 

 

 

*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*

[05/11/2022, 8:50 pm] +234 906 512 0158: : *💘🌹MIJINKI MIJINA NE!!💘🌹*

 

⚖️

*HAMDALA WRITIN’S ASSOCIATION

_*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL’UMMA

 

*✨✨{{H.W.A}}✨✨*

 

🅿️ *3-4*

 

______ Gimbiya TAFISU d’iya ce ga Sarkin Failura wato Sarki Abdulgafar, itace d’iyarsa ta farko wacce take d’iya ga Sarauniya Kaltum, wato Uwar gidan Sarki Abdulgafar, Sarauniya Kaltum itama tagaji sarauta gaba da baya awajen iyayenta, auren soyayya sukayi ita da Sarki Abdulgafar, shekarsu goma da aure amma basu haihu ba, dan haka hankalin Memartaba yatashi yafara tunanin wa zai gajeshi bayan bashi tinda bashi da magaji, agefe d’aya kuma ga mahaifiyarsa wato Sarauniya Maryam, ta dame shi akan yaqara aure domin tana son ganin jikanta da zai gadi d’anta, Sarauniya Maryam wato mahaifiyar Sarki Abdulgafar macece mai mulki da izza wanda kowa tsoronta yakeji amasarautar domin bata da kirki ko kad’an, bata shakkar kowa amasarautar sanan kuma intafad’i magana yazauna dole ne abi umarninta, dan ko shi Sarki Abdulgafar bai isa yamata musu ba, to duk mulkin Sarauniya Maryama tana shakkar Sarauniya Kaltum domin Sarauniya Kaltum bata qyaleta ko kad’an.

 

Haka Memartaba yabi shawarar mahaifiyarsa inda acikin kuyanginsa ya ‘yanta d’aya ya aura domin yarinyar naburgeshi sbd nutsuwarta gata kuma marainiya ce, nan fa hankalin Sarauniya Kaltum yatashi dan aganinta abun kunyane agareta ace tana kishi da kuyangarta, bayanda batayi ba dan Memartaba Abdulgafar ya saki kuyanga Hafsa, amma shi kam fur yaqi, to itama Sarauniya Maryama batasan kuyangarsa zai aura ba, harsai da aka d’aura aure sanan tasani, ai kuwa tace fir bata yarda ba, tayaya d’anta yana sarki guda amma yaqare da auren kuyanga nan fa tace sai yasaketa, shiko Memartaba Abdulgafar yace bazai iyaba yana son ta shiyasa ya ‘yantata ya aureta, nan fa Sarauniyar Kaltum da Sarauniya Maryama, sukasa Memartaba agaba akan sai yasaki kuyanga Hafsa, shiko yaqi yama tatara shi da matarsa yabar musu qasar, inda yabar fadar ahanun wazirinsa, Shiko Memartaba Abdulgafar shi da Amaryarsa Hafsa suka tafi saudiya, wanan tafiyar kuwa tasa Sarauniya Kaltum baqin ciki dan har sai da takwanta ciwo, taita rashin lafiya ashe a lokacin shigar ciki ne da ita, gashi Memartaba Abdulgafar bayanan dan haka Sarauniya Maryam ne taita kula da ita, har tana da nasanin qarin auren da tasashi yayi tinda ma gashi kuyanga ya aura, harma yana nuna yafi sonta fiye da kowa.

Dan haka dole Sarauniya Kaltum da Sarauniya Maryam wato mahaifiyar Memartaba Abdulgafar, suka ajiye mulkinsu agefe suka had’a kai domin su yaqi kuyanga Hafsa.

 

Shiko Memartaba Abdulgafar watansu uku a saudiya suka dawo gida, Hafsa na da shigar ciki, inda cikin Sarauniya Kaltum ma, har yafara futowa, sosai Memartaba Abdulgafar yayi Murna da samun cikin Sarauniya Kaltum, domin ko ba komai yasan d’anta shine zaiyi gadon sarautar Failura, shikenan ya huta da qorafinsu ita da mahaifiyarsa akan kar d’an kuyanga yazo yayi mulki.

Sarauniyar Kaltum da Sarauniya Maryama bayanda basu yiba dan su zubar da cikin dake jikin Hafsa, wanda ma sun hana ace mata Sarauniya, amma yananan daram abunsa.

Haka Sarauniya Kaltum da Hafsa sukaci gaba da renon cikinsu, inda Sarauniya Kaltum ce tafara haihuwa, ta haifi ‘yarta mace kyakyawa, Sarauniya Kaltum da Sarauniya Maryama sunyi baqin cikin ‘ya macen da akasamu, domin kuwa sunsan idan Hafsa ta haifi d’a Namiji d’anta ne zaiyi mulki, shiko Memartaba Abdulgafar yayi farin ciki sosai da samun ‘yarsa inda taci sunan Mahaifiyarsa wato Sarauniya Maryama, ko da Hafsa tazowa Sarauniya Kaltum barka, korarta sukayi wai baza su bata da jaririyar ba karta cutar da ita sbd baqin ciki, haka Hafsa taja qafafunta da qaton cikin ta takoma, Itako Sarauniya Kaltum sai hararta takeyi dan baqin ciki, bayan wata daya da haihuwar Sarauniya Kaltum, Hafsa tahaihu inda tahaifi d’anta namiji, Murna kuwa afadar kamar me domin kuwa murna yakeyi Memartaba yasamu magaji, amma banda mutane biyu, wato uwar sarki da matar sarki, haka akasha taron suna mai lafiya inda Memartaba Abdulgafar yasawa d’ansa suna yarima Okasha, ‘yan baqin ciki kuwa kamar su mutu, haka rayuwa taci gaba da tafiya, tin yarima Okasha yana qarami su Sarauniya Maryama suka so kasheshi, amma sunkasa nasara akansa da mahaifiyarsa, dan haka sukaci gaba da qulle-qulle kashe shi, haka de rayuwa taci gaba da kayawa sosai Hafsa tatsaya da qafafunta tana bawa d’anta tarbiya mai kyau domin duk duniya bata dakowa daga Yarima Okasha sai mahaifinsa dan ita ko iyayenta bata sani ba, anan Failura Gimbiya Maryama tayi makarantar primary da scondary, Memartaba yaso yakaita qasar Madina tayi karatunta acan, amma fir taqi, tace ita England zataje, dan haka dole Memartaba ya yarda tatafi, domin fishinta tamkar fushin mahaifiyarsa ne, domin Sarauniya Maryama bata so ata’ba mata takwarata.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, yayinda Sarauniya Maryama tamaidawa takwararta suna TAFISU, tafi sauran Mata, dan kuwa da mulki da Izza Gimbiya Maryama ta taso, har tafi uwarta da kakarta mulki, dan haka kowa yake qiranta Gimbiya TAFISU, inda aka koma qiran Sarauniya Maryama da Kaka Sarauniya, sarauniya Kaltum kuma suna qiran ta da uwar gimbiya, ita kuma Hafsa ana qiranta da uwar yarima, domin kuwa duk wanda ya sake yaqira ta da Sarauniya to fa yasan sauran.

Tinda Gimbiya TAFISU taje karatu England, tasa ke wayewa idonta yabud’e bata tsoron kowa, bayan tagama karatun ne ta dawo Memartaba yace tafitar da miji itako itace. Bata gama karatu ba, dan kuwa yanzu ma tafara, domin so take taje Swaziland, ta yi degree d’inta amma sam Memartaba yaqi yarda, sosai kaka Sarauniya ta nuna ‘bacin ranta akan yaqin barin takwararta zuwa karatu, Amma duk haka Memartaba yaqi yarda domin shi yafi son tayi aure, Itako Gimbiya TAFISU mulki da iyayi ya hanata fitar da miji domin ita har yanzu bata ga namiji ba, bare ta aura.

Har Memartaba yayi mata wanan qiran.

Wanan shine asalin labarin Gimbiya TAFISU.

Ci gaban labari, Jakadiya kuwa cewa tayi “Allah ya huci zuciyarki ranki yadad’e” .

‘Daga mata hannu tayi Sarauniya Kaltum tayi, dan haka jakadiya taja bakinta tayi shiru, itako Gimbiya TAFISU tashi tayi tana share hawayenta sanan ta fita, itama jakadiya tabi bayanta kai tsaye shashin wazari Gimbiya TAFISU ita da jakadiya suka nufa.

 

Itako wanan baiwar da Gimbiya TAFISU tatakawa wuya, tananan tana kwance agurin asume, bayi da kuyangi duk sun kewayeta suna d’aura hannu aka, wani kyakyawan saurayi ne yazo gurin jikinsa sanye da kayan sarauta, sai qamshi yakeyi, aqalla saurayin zekai shekaru 30 ko 31; yana zuwa gurin bayin dake gurin spuka fara matsawa, wata baiwace da take kan baiwar da Gimbiya TAFISU tatakawa wuya tana girgizata tana kuka, tana ganin saurayin cikin kuka tace ” yarima Okasha Gimbiya TAFISU ce………. ‘Daga mata hannu yayi yace ” nasan komai, basai kin ‘bata bakinki ba, domin kuwa ina zaune asama naga komai da yafaru ku ni nasa wanan baiwar taka womin kayan fruit amma bakomai ku d’aga ta bari na d’auko mota nan, muje asibiti”

Haka Yarima Okasha yaje ya d’akko mota, saraun bayin su kasa baiwar amota, inda yarima Okasha ya tuqa motar suka nufi asibitin cikin gari dashi da bayi biyu mata, da kuma hadimai maza biyu, suna zuwa asibiti likitoci suka kar’bi baiwar suka fara bata taimakon gagawa.

 

Itako Gimbiya TAFISU da jakadiya suna shiga shashin Waziri, suka wuce d’akin qawarta Gimbiya TAFISU wato Gimbiya DIJA, Gimbiya DIJA d’iyar waziri ce, kuma ‘yar uwar Gimbiya TAFISU, domin da Waziri da Memartaba ‘yan uwane, na dangi, Dan haka Gimbiya TAFISU tariqe Gimbiya DIJA a matsayin qawarta kuma ‘yar uwarta, itama Gimbiya DIJA mace ce mai mulki da Izza amma ko kad’an bata kama qafar Gimbiya TAFISU ba, dan haka Gimbiya DIJA taji ta tsani Gimbiya TAFISU amma bata ta’ba nuna mata ba, domin kuwa ita Gimbiya TAFISU tsakani da Allah take tare da Gimbiya DIJA, kuma ita tasa ake qiran DIJA da Gimbiya domin aganinta ai dukkansu ahalin sarauta ne.

 

Gimbiya TAFISU tana shiga shashin DIJA tatarar da Gimbiya DIJA dawani yariman wata Masarauta yazo gurin Gimbiya DIJA suna hira dan sonta yakeyi, Gimbiya DIJA ce tadauki cop d’in glass da madara holandia aciki, takai saitin bakin saurayi nata, amma sai yajanye bakinsa, Itako Gimbiya DIJA, tasake nufar bakinsa da cop d’insa, kawai sai ga gimbiya TAFISU tashigo, tafa hanayenta tayi tadubi Gimbiya DIJA tace ” amma Gimbiya DIJA kinji kunya da girmanki zaki tsaya kina yiwa namiji bauta har da durqusawa kina bashi madara, Allah yakiyaye ni Gimbiya TAFISU banga namijin da zan durqusawa ba arayuwata, tinda har Memartaba ma ban durqusa masa ba to bawani namiji da zan duqawa, kallon Saurayin tayi a wulaqance sanan tace ” kai kuma daga ina daga wata Masarautar”?

Shiko saurayin tashi yayi, ya tsaya akusa da Gimbiya TAFISU, tsayinsu yazo yadaya harma yafita tsayi kad’an, shima kallonta yayi a wullaqance, yace ” ni Sunana yarima Faisal d’a ga sarkin garin postikum sarki mai daraja adalin sarki wanda yasan darajar mutane, mutum mai addini, a Masarautar mu akwai daula dajin dad’i sanan Masarautar mu ficeciyar Masarauta ce kowa yasanta a Nigeria harma da sauran qasashen waje”

“Hhhhhhhhh Gimbiya TAFISU tayi dariya sanan tace ” rufemin baki wawa kawai to bara kaji baza kasamu abunda kake so ba, domin baka yimin ba, sbd haka kafice amasarautar nan tin kafin nasa amaka rashin mutunci”.

‘Daga hannu Yarima Faisal yayi zai mari Gimbiya TAFISU, amma Gimbiya TAFISU tari qe hanunsa tace ” qarya kakeyi ni nafi qarfin mari” wullar da hanunsa tayi sanan ta wanka mar mari, itako jakadiya cewa tayi ” qarya kake yarima matane agabanka ba maza ba, sbd haka hattara yarima atattara aqara gaba domin kuwa bakayi nasara ba” Shiko yarima Faisal haushi yaji kamar me, nuna Gimbiya TAFISU yayi da hannu yace ” kinci darajar ke mace ce, kuma ni nasan mutuncin mata sbd mata sune iyayenmu, shi yasa bazan wulaqantaki ba, amma duk da haka ki rubuta ki ajiye zan dawo domin rama marin da kika yimin” ficewa yayi agurin ransa ‘bace Itako Gimbiya DIJA sai lokacin tasamu bakin magana, tabi bayan yarima Faisal tana cewa ” haba yarima dan Allah kadawo ina zaka? Itako Gimbiya TAFISU riqo Gimbiya DIJA tayi tace ” ina zaki? Namiji kike bibiya lalle kincika ‘yar wahala”

Itako Gimbiya DIJA tana kuka tace ” haba Gimbiya TAFISU meyasa zakiyimin haka wlh ina son yarima Faisal domin shi mutum ne adali yasan darajar mutane, da kuma mata, shi yasa Yau bai wulaqantaki ba, Itako Gimbiya TAFISU dariya tayi Hhhhhhhhh sanan tace ” adali ko kuma rago shi yasa yakasa mara marin da nayi masa, to bara kiji ni band’auki soyayya komai ba, shi yasa bana da rajata, kuma ni maza basa burgeni kuma ni har yau banga wanda yaburgeni ba”

Sanan Gimbiya TAFISU tayi tafiyarta itama jakadiya tabi bayanta, Itako Gimbiya DIJA cewa tayi ” wlh baki isa tinda kika korar min miji tabbas sai na shuka miki rashin mutunci arayuwarki, domin kuwa ki gama rashin mutuncinki nasan rana d’aya soyayya zata yimiki mugun kamu kamar yanda tayi min, sbd haka Gimbiya TAFISU tinda kika korar miji tabbas, *MIJINKI MIJINA NE* sai na auri mijin da zaki aura Gimbiya TAFISU, bazan ta’ba barinki ki huta ba arayuwarki tinda kika rusa tawa yaruwar sbd haka muje zuwa ni Gimbiya DIJA saina nuna miki hatsi bibanci na”……….

Hhmm muje zuwa dan yanzu za’a fara wasan.

 

Shin Gimbiya DIJA zata iya aikata abunda tace na auran MIJIN Gimbiya TAFISU?

 

Yaya labarin Gimbiyar Yarima Okasha yakaita asibiti.

 

 

*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*🤲👏

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment