Littafan Hausa Novels

Me zanyi da ita Hausa Novel Complete

Karin hips
Written by Hausa_Novels

Me zanyi da ita Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Da sanyin safiya ta fito daga rugar fulanin cikin wata bukka dake daga gefen rugar sanye take da kayan fulani irin usul din fulanin nan fuskarta a cunkushe da mabayyanin ‘bacin rai. Tana tafe tana kunkuni alamar ba dan son ranta ya fito ba.

Kwarya ce a kanta da nono a ciki a tsakar gidan ta tarar da mahaifiyarta zaune da turtsesten ciki a gabanta ta had’a kai da gwiwa .

Me zanyi da ita

Har zata wuce sai kuma ta dawo ta tsaya mata’kerere a ka, bakinta a zun’bure tace “innaji zan tafi” innaji ta saki ajiyar zuciya kafin ta furta “idan kinje ki gaida modibbon saura kuma idan kin fita ki tsaya dukan d’iyoyin jama’a ko tumakinsu “ “ aradu duk yaran da ya higa gonata nima sai na higa ta uwarshi “ cikin takaici innaji ya watsa mata harara “ ina magana shatu kina cewa aradu sai kinyi to ai shikkenan kije kiyi Allah ya shiryeki ni dai ina gaya miki ki kula da kanki kina sani ba kowa ne damu a garinnan ba idan mune yau fa anjima gawa muke bana son ace har yanzu kina wannan halinnaki kowa unguwar nan yasan halinki ba mai fad’ar alherinki sai aibunki shatu don Allah ki shiryu kada kizo nan gaba kina wahala a lokacin da ‘kasa ta rufe min ido “  .

Karanta Littafin Gidan Mu Complete Hausa Novel

Duk da jikinta yayi sanyi bata fasa cewa “yo innaji sai na bari yara suna tsokanata suna ce min mai idon mujiya kamar ubansu ya rad’a min “ innaji ta mi’ke da kyar da alama cikin yayi mata nauyi murya can ‘kasa ya kama hannunta “ suyi ta fad’a miki mana kyau idanun suke musu masha Allah zaki dinga cewa idan suka fad’a miki yi sauri ki tafi kinga hadari na hadowa ki gaidar min da modibbo ki kar’bo min rubutun idan ya rubuta “.

 

Da sauri ta fice kamar zata tashi sama tana ayyana “ wallahi innaji ba zan kyalesu ba jibgar d’iya ni kayi idan ya shiga gonata’yan kwal uba masu kan faranti “.

Da tsallanta take tafe da wa’karta duk da ‘kwaryar nonon da take kanta har da cilla sanda duk yaran da ta wuce’kus suke da bakinsu kada suyi magana suci Na jaki sai dai tana wucewa suke tuntsira dariya murya ‘kasa’kasa suke cewa “mujiya idonki a loko “ sai su taka da gudu.

 

Shatu ‘kwafa take tana haddacesu d’aya bayan d’aya ta kuma tabbatar wallahi sai sunyi bayani.

A saman buzu ta tarar da kakanta Na gurin uba moddibo wanda ya kasance gawurtaccen malami a garin nutsuwa tayi sosai don shi kad’ai take tsoro a garin , ta ra’be gefensa ta tsuguna sai da ya kai aya sannan ya d’ago ya kalleta fuskarsa ba yabo ba fallasa yake amsa gaisuwar da take masa “ Gashi inji innaji tace tana gaidaka “ moddibo ya girgiza kai had’e da jan’kwaryar yana girgiza kai “ ‘yar nema ai Na zata yau ma kinyi halinnaki kin zubar dashi wallahi da yau ma sai na zaneki dan na lura sam ke baki tausayin innarki idonki a tsakar ka yake d’auki ki kaiwa salame Ta adana shi a ciki” mi’kewa tayi zuciyarta a tunzire kamar ta kai masa mari ita fa ta tsaneshi bata ‘ki ya she’ka barzahu ba don ya takura mata baki kamar shantu ta fad’a a zuciyarta zanyi maganinka aradu gobe. A tsakar turken tumaki ta tarar da ita salame ta amsa gaisuwarta tana kar’bar’kwaryar nonon fuska a sake tace “ya jikin innar taki?” “ ba sauki sai na Allah yo wannan uban ciki yayi mata turtsitsi ta ina zata samu sau’ki Idan ba haifeshi tayi ba aradu duk ranar da Ta haife abin da yake cikinta sai na jibgeshi “ salame ta zaro ido tana kallon shatu da take zaro zance “ashe kuwa dai shatu da ake cewa baki da kai zancen ya kusa tabbata jaririn zaki jibga?” Ta ta’be baki “ yo idan ban jibgehi ba ai aradu ban haifu ba a cikin innaji ko sallah fa a zaune take yi gashi tun a ciki shegen karanbani garai yayi ta kwarafniya jiya fa ina kallon cikin yana wutsilniya wallahi tana cin abinci kika ji d’if  tun kan yazo duniya ma ya nuna halinsa” salame ta girgiza kai tana katse’kwaryar ta mi’ka mata daidai lokacin da modibbo ya shigo yana dogara sanda “ to uwar shashashanci kina nan kina zuba kamar ‘ya’yan kanya zo ki wuce ki kai mata rubutun Allah ya raba lafiya”  “ ameen “ ta furta murya can ‘kasa “ ai kai na gado a kwakwazo duk gari an sani” mai kika ce “? A guje ta arce tana fad’in cewa nayi Allah ya tashe mu lafiya salame kuwa girgiza kai tayi don ita taji abinda tace sarai don dai shi ma kunnensa yana da matsala ne.

Tun a hanya take Allah-Allah taga d’aya daga cikin yarannan sai dai bata gansu ba haka ta koma gida ranta a ‘bace da rashin cikar burinta.

 

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment