Littafan Hausa Novels

Matsalar Gidan Miji Hausa Novel Complete

Hotunan Yadda Ake Kwanciya Da Mace
Written by Hausa_Novels

Matsalar Gidan Miji Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

MATSALAR GIDAN MIJI

(GIDAN AURENA)

 

 

STORY AND WRITTEN BY

 

 

GIMBIYA AYSHU

 

 

 

ELEGANT ONLINE WRITER’S

 

 

 

BOOK 1:CHAPTER 27&28

 

 

 

________________________Gyara tsayuwar ta tayi tace”ina wuni,ya aiki da gida”.

 

Alhmd wlh ya gida ya su Mama da Abba.

 

Murmushi tayi idan ta ya tara hawaye tace”Alhamdulillah”.

 

“Baiko kula da yanayin da take ciki ba sabida babu wadatatchan haske a unguwar”.

Jalila Hausa Novel Complete

“Unnn….kinyi mamakin ganina kohhhh!”.

 

“Daga mishi kai tayi a hankali jikin ta a mace”.

 

Wato a gaskiya tun randa na hadu dake a napep naji kin kwanta min a rai.

 

“Amman a lokacin banyi tunanin komi ba,a zatona zan manta da lamarin,amman inaaa………na kasa”

 

A gaskiya bazan boye miki ba gimbiyar mata”da haka zan kiraki tunda bansan sunan mutuniyar ba”ya fada yana murmushi.

 

Murmushi Hauwa tayi har sai da Kumatunta ya loba sabida yanda yayi maganar ya mugun bata dariya amman ta gintse.

 

Haka ya cigaba da janta da hira,tun tana shiru har ta fara amsawa da umm a’a daga karshe dai ta wassake ta biye mai suka sha hiran su.

 

 

“Tun takwas da minti talatin ta fita,ba ita ta dawo ba sai tara da minti arba’in da biyar”.

 

Tana shiga gida ta kulle kofar,sai a lokacin gaban ta ya fadi tace”na shiga uku,daga fita nagawa yazo shikenan na bige da hira,toh yanzu wa zancewa Mama yazo wurina”ta fada tana buga uban tagumi.

 

“Ganin tana batawa kanta lokaci yasa ta fara tafiya cikin tsanda,har ta nufi dakin Mama sai kuma tayi reverse ta nufi nasu”.

 

Tana gabda shiga kenan taji Mama tace”ki gama kizo ina jiran ki”.

 

“Sossai gaban Hauwa ya fadi,hannu tasa tana sosa kai kanta a kasa ta nufi dakin Mama”.

 

Abinda bata sani ba shine”tun lokacin data shigo Mama ke kallan ta,kuma duk abinda tayi akan idanta tayi shi”.

 

 

“Zama tayi kusa da Mama ta sunne kai kasa kamar mara gaskiya”.

 

 

“Kince ba kisan wanda ya kira ki ba?,toh ya akayi kika jima”,ta fada tana¬† tsareta da ido.

 

 

Kara dukar da kai tayi tana wasa da yatsun hannun ta tace”emmm………..dama……dama ummm………shine mutumin dana taba haduwa da shi a napep a wani yammaci dazan dawo daga gidan Mami,kuma ya biya min kudin napep”,ta fada tana kara dukar da kanta kasa dan tasan zata sha fada.

 

Shiru Mama tayi tana nazarin ta,chan kuma tace”a kullum bazan gaji da gaya miki ba,ki rike mutuncin kanki,sannan shi mutumin da mai yazo”.

 

 

Kara sadda kanta kasa tayi tace”ban sani ba Mama”.

 

“Baki sani ba kika ce?”.

 

“Ehhhh! Mama,ni cemin kawai yayi….nan ta fara gaya mata abinda yace mata”.

 

 

Girgiza kai Mama tayi tace”tashi ki tafi”.

 

 

“Tashi tayi sum-sum kamar munafuka ta fita”.

 

“Ajiyar zuciya mai karfi irin na samun relieve ta sauke bayan ta fita”.

 

Ko data shiga dakin su Asiya tayi barci,kayan jikin ta ta chanja zuwa kayan barci tabi lafiyan gado.

 

Addu’a tayi ta kulle ido dan tayi barci amman ina abu ya faskara data kulle ido wannan gayan take gani,sossai mutumin ya birgeta (sunan data rada mishi kenan).Dan har suka karaci surutun su bai fada mata suna ba haka zalika itama.

 

Tuna sunan daya saka mata tayi”Gimbiyar Mata”bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba.

 

Wani bangare na zuciyar ta tace”haba ke kuwaaaa………daga haduwa da mutun yau shine har kin fara tunanin shi,sai kace dama jira kike,toh wa ya sani ma ko ba sonki yake ba kawai ya fada ne dan ya gwada ki”.

 

Saurin gyara kwanciya tayi dan kawai ta rabu da tunanin da take.

 

“Amman inaaaa…….ta kasa bari,haka dai tayi ta tunanin shi har barci barawo ya dauke ta”.

 

 

Kafar Hauwa ya warke sumul kamar bata taba jin ciwo ba.

 

Zaune suke a tsakar gida gabadayan su suna hira,Mama na kwancewa Hauwa kitso,Asiya kuma na yanke farcen ta,

 

Wayar Mama dake daki ne ya fara ringing.

 

 

“I da sauri Asiya ta mike kamar dama jira take,

 

Tun kafin ta karaso tace”Mama Mami ce ke kira wlh”ta fada tana washe hakora.

 

Girgiza kai Mama tayi tana mamakin son da suke yiwa Mami.

 

Ko kafin ta daga ya katse,tana gabda dialing wani kiran ya shigo,dagawa Mama tayi tare da yin sallama,bayan sun gaisa Mami tace”ya mai kafa da jiki”.

 

Wlh jiki Alhamdulillah ta warware sossai.

 

“Toh masha Allah,ina yaran nawa suke”.

 

Ga sunan duk sunmin kuri da ido.

 

Dariya Mami tayi tace”basu wayar”.

 

Mikawa Ummi wayar Mama tayi.

 

Amsar wayar tayi jikinta har wani rawa yake tace”Hello Maminmu ina wuni,ya gida ya Abban mu da yayyin mu ya kowa da kowa ya”……….

 

Oh uwar surutu ya ya bai kare ba,baza ki bari a amsa wa’inan ba kina karo wasu.

 

Dariya Mami dake sauraran Mama tayi tace”ki kyale min yarinya tayi magana iya son ranta”.

 

 

“Ummm……….toh shikenan na bari”.

 

Saka wayar a Hans free Ummi tayi,sossai suka sha hira dan sun shafe minti Arba’in suna hira kafin su kayi sallama.

 

 

 

Da misalin karfe takwas da minti ashirin da tara wannan guy din yazo,wani yaro ya aika yace”ka shiga kace ana sallama da Baban Hauwa”.

 

Da sauri yaron ya shige cikin gidan yace”wai wani yace yana sallama da Baba wai”.

 

Yana dire maganar ya fita a guje.

 

Sossai Mama da yaranta suka shiga mamakin jin abinda yaran nan yace.

 

Ajiyar zuciya Mama ta sauke tace”ku saka hijabi,Kuluwa saka min tularan wuta a parlor.

 

Ke kuma Ummi je kice wa mai sallama ya shigo.

 

“Da toh Mama ta amsa,dama da hijabi a jikin ta,parlorn Mama ta nufa ta kunna tularan kamar yanda Mama ta fada”.

 

Da sauri ta kunnan tularan ta fice daga parlor.

 

 

Jagora Ummi tamai har zuwa parlor…………………………………

 

 

 

 

By Gimbiya Ayshu.

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment