Littafan Hausa Novels

Matan Asokoro Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Matan Asokoro Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Matan Asokoro Hausa Novel Complete

EPISODE 1️⃣

 

 

 

_BAYAN SHEKARA BIYU_

 

Bude idanuwanta tayi kadan kaman bataso tabude su saikuma tabude duka tareda daga left hand dinta ta kalli agogon Rolex dake daure a writs dinta, ganin 4:30 na yamma tayi yasa ta yunkura ta daga kanta daga jikin katafaren kujeran office din datakekai, ta taso gabaki daya tazauna da kyau sanan ta dubi uban takardun dake kan hadadden table din dake wajen cikeda gajiya, dan gajeren tsaki taja sanan ta mike tsaye ta taka har zuwa gaban wani dogon mirror dake cikin office din kiran turkey gyara zaman ash color gyalen dake kanta tayi sanan tadawo tadauki jakan monalisa dake kan table din dakedan girma da bala’in kyau kuma tareda car key dakuma wayanta kiran iPhone 13 pro max sanan tajuya tafara tafiya tasaka hannu tabude office din sanan tacigaba da tafiya kafin tai stairs tafara sauka kasa nan tashigo cikin wani tamkeken babban super market dakenan birjik da kaya shelve daban daban ga different sections na abubuwa kaman shoprite, ga ma’aikatan wajen suma kowa yana aikinsa suna cikin rigunansu mai suna Dawanau super market, staff din sai gaidata suke tanadan amsasu sama sama sanan tasakai tafice abinta tai wajen parking space dinsu direct zuwa inda tent yake tayi sanan tabude motan wajen ta shiga taja aka budemata gate tasakai tafice daga super market din.

 

Iyalina Hausa Novel Complete

 

Long tafiya tayi sosai sanan takai wani stadium mai suna youth stadium ta shiga da motar ciki har zuwa inda ake parking sanan ta kashe motan. Jakanta dake dayan sit din gaban tamika hannu tadauka sanan taciro wayanta tamaida jakan ta ijiye tareda bude wayan tai dailing wata number ana daga wayan tace “you guys should come outside mutafi gida Magrib tayi” tai dan jim kaman tana sauraron maganan da akeyi daga chan ne tawani yunkura dasauri tace “what! Subhanallahi, ina zuwa” dasauri takatse wayan tareda karasa kashe motan sabida Ac yadena aiki sanan tasa hannu tabude kofa tafito dasauri tashiga cikin filin.

 

 

 

Tundaga nesa ta hango yanda yara wanda sukenan kan yaran nata suka taru suka cika bama taganin me akeyi, yaran na hangota aka bubbude wajen hakan ya bayyana Khalid dake kwance yana huci yana gumi sabida azaba gawani magidanci daya bama kowa baya agabanshi yana tsugunne rikeda kafarshi yana treating wound din yana rufeta da bandeji, saishikuma Khalil yana tsaye kana ganinshi kaga ya bala’in damu ganin yanda dan uwanshi yaji ciwo, yana hango Mamansu kafinma takaraso yay wajenta da sauri yace “Mami kinga faduwa Khalid yayi garin ball, shine this uncle was helping us yana bashi first aid treatment” yay maganan yana nunamata mutumin daya basu baya wanda only his broadback take iya gani, daidai lokacin mutumin yamike tsaye sukuma suna karasawa wajen, batare daya waigo ko juyo ba yaygaba abinshi ta hanyar bin gefen Khalid din yay ciki itakuma da sauri ta tsugunna tarike kafan Khalid din da aka goge tatas anmasaka bandage tana kallo tace “saisa hankalina yaki kwanciya ina office ashe ciwo kaji, sannu does it hurt alot”? Tai maganan tana kallon Khalid din kaman zatai kuka, murmushi yamata shi adole namiji yace “Mami ni bayamin zafi dan Allah” yanda yay maganan tagane sabida abokanen shine inba hakaba Khalid din datasani kuka zaita mata, murmushi tayi tace “toku tashi mutafi, kuma duk kutafi gida tunda antashi” tai maganan itada Khalil suna daga Khalid din, sai alokacin tama tunada wanda yay treating ciwon tace “laaaa ina wanda yataimaka maka namanta banmai godiya ba” tai maganan tana wawwaigawa kozata ganshi, daya daga cikin abokanen su Khalid dinne dasuka jero tare yace “ni banma taba ganinshi a stadium dinan bama sai yau, kaman training suka shigo shida wasu ne ma bashi kadaiba, amman yanada kirki wlh” dasauri Khalil yace “eh wlh Mami yanatama Khalid sannu sannu harda bama Khalid Handkerchief yashare gumi, he’s so nice” murmushi Khalid yayi yaciro handky din yana mikama Mami nasu duk suna tafiya yace “ga Handky dinan ma Mami” batare data kawo komiba takarba kawai tasa ajaka suka cigaba da tafiya har zuwa wajen mota saida suka saka Khalid abaya sanan Khalil yabiyota yazauna agaba tarufe sanan tazagaya tazauna ta tada motan sukabar wajen suka shiga titi.

 

 

 

Khalil yace “Mami ni wlh nakosa Friday tayi muzo wajenki, Mami nagaji da gidan nan wlh” dasauri Khalid dake baya yace “and I hate that woman witch kawai, kullum itada dayan saisu dinga kai karanmu wajen Abba wai bama gaishesu” batare data kallesu ba har lokacin idanunta nakan hanya tace “nasha gayamuku banson raini kudinga gaida matan Babanku they’re your step Mums” turo baki Khalid yayi yace “ni wlh bazanyi ba Mami saidai su mutu, ni nakosa admission yafito mumabar kasan ko Khalil” dasauri Khalil yace “eh wlh, I can’t wait mutafi UK, Mami ai zaki rakamu ko har chan” murmushi tayi saikuma tai dan jim tace “it’s depend koma ban rakaku ba zanzo daga baya” daganan bata kara musu magana ba sai hiransu suke dayake last year sukai WAEC kuma duk sunci, sun kosa sutafi school saida tabiya takai Khalid wani clinic aka duba kafanshi aka tabbatar mata babu wani abin tashin hankali awurin sanan hankalinta ya kwanta aka bashi magunguna tamusu siyayya a pastry shop sanan suka fito, har ASOKORO takaisu sabida ciwon Khalid ne dan Normally ko wajenta sukazo inbadai direba ne zai maidasuba inda itane a gate din estate dinsu take saukesu sai yau itane har gidan rabonta dataga gidan yau 2yrs kenan.

 

 

 

Agaban gate din gidan tai parking tafito Khalil shima yafito sanan tabude kofan baya dan Khalid yafito kenan aka bude gate din hakan yasa dukansu suka dagakai Baban Khalid ne yafito yana sanye da jallabiya ya rame sosai kaman bashiba, kallo daya tamai tadauke kai ganin yanda ya tsareta da idanu, sanan takarasa fitoda Khalid daga baya tasama Khalil shi tace “kuwuce cikin gida” daidai lokacin Baban Khalid yakaraso wajen da sauri yana kallonsu yace “subhanallahi maiya sameka Khalid”? Yay maganan arude dan har gobe baya wasada yaranshi, Khalil ne ya tsaya yimai bayanin abinda yafaru itakuma tawuce abinta tazagaya ta shiga mazaunin direba tarufo kofa tai key motan tana shirin jan motan taji anyi knocking glass din motar hakan yasa tadagokai dasauri ta kalli wajen. Ganin Alhaji ne tsaye yana kallonta kaman yauya fara ganinta yasa ta saukarda glass din motar kasa, kallo daya tamai tadauke kai anatse tace “barka da yamma Baban Khalid” ahankali yace “Hassana!” Saikuma yay shiru yakasa magana yana kallonta kaman yabude motan yakama hannunta su shiga gida yakaita dakinta yakeji, jin shiru baice komiba yasa tadagokai tasake kallonshi akaro nabiyu tace “dawata magana ne kan yaran?” Girgiza matakai yayi dasauri gwanin ban tausayi yace “a’a babu komi dama…..” yakasa maganan yasake shiru, dauke kai tayi tace “in that case saida safe agaida iyalai” tana maganan taja motar tabarshi nan tsaye yana bin motarda kallo.

 

 

 

Sai bayan Magrib dan gari harya soma duhu sanan takarasa anguwansu. Horn tayi gateman yabude mata gate taja motarta ciki sanan yamaida gate din yarufe, daidai tafito rikeda handbag dinta kenan gateman din yazo dagudu, ganinshi yasa ta tsaya chak tace “lafiya Habu”? Washemata baki yayi yace “sannu dazuwa Hajiya, daman sako wani yaro yakawo min dazu ina zaune awaje inajin labari a radio, yacewai abama Hajiya Hassana” yay maganan yana bata wata yar karaman cute red bag, jakan tabi da kallo taidan jim tana tunani dan today is the fifth day take karban all this strange letters da flowers from a secret admirer data rasa waye, har office ana kawomata. “Hajiya” Habu yasake kiranta ganin bata karbaba kuma ta tsaya tai shiru tana kallon jakan tana tunani, rashin son jan magana dashi yasa tamika hannu anatse ta amsa tace “nagode Habu” sanan tajuya tai ciki tana tafiyan nan daidai cikin isa da gayu Habu yabita da kallo, aranshi yace duk wacce yasami wanan matar yahuta, wlh tayine arayuwa, batada hayaniya, bata daukan raini, gatada mugun kamun kai which mutane ke mistaking da girman kai, ga kyau gakuma kudi duk ita kadai, inamani wanine nayi wup da ita. Hannunshi yasa ya rankwashi kanshi yace kai sanan yawuce yatafi dakinshi.

 

MATAN ASOKORO II

 

 

 

 

M SHAKUR

 

 

SEX SEMINAR

_Ahayye nanaye jama’a M SHAKUR tahadama matan aure gagarumar SEMINAR na wayar dakan matan aure akan harkan zamanta kewan aure, inda ta gayyato mutane kwararrun marriage counselors dazasu baku ilimin daya dace yakuma kamata kowacce matan aure tasani. Ina matan dake fama da rashin shakuwa da mazajen su? Zaman aurensu ba dadi? Jima’in ba dadi, wanan spice da zaki zakin soyayyan nan duk ta bace a auren, sex din is as boring as hell, tokusha kurumin ku domin matsalanku tazo karshe dan wanan SEMINAR zai solva muku matsalolin nan_ _za’ayi wanan SEMINAR duk ranan asabar da lahadi na watan November har watan yakare ana koyardaku abubuwa da dama akan naira dubu daya kacal._

 

 

_Idan kinason shiga group din zaki turo naira dubu daya 1k to 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment tawanan number 07012181461 sai ayi adding naki a group din._

 

 

_Dan chatting M SHAKUR directly dan samin karin bayani zaki iya danna wanan link din dan magana da ita_ https://wa.me/+2347012181461

 

 

EPISODE 2️⃣

 

Tana shiga side dinsu direct dakinta tawuce, wanka tayo sanan tazo ta shirya cikin wani simple cotton gown tazura hijabi tai salla, saida tai isha’i sanan ta tashi hijabin ta cire ta linke tadauki mayafi tayafa tareda daukan wayanta tabude kofa tafito, Mama dake gyara dinning data juyo jin karan bude kofane tace “zokici abinci dama shiri nake nazo nakiraki” murmushi tayi tace “Mama ke baki gajiya” dan hararanta tayi tace “zozo, taho nan kiga, namiki tuwon semovita da miyan kuka, ga yaji ga man shanu best abincin ki” dasaurinta tazauna akan kujera tana shakan kamshin abincin tace “uhuuu Mama it smells delicious, nagode Mama” kujera Mama taja itama tazauna kusada ita tareda shafa kanta tana kallonta tace “anything for yarinya na” tai shiru tana kallon yanda takecin abinci har cikin ranta tanason yaran mijinta wlh batada wanan halin na wanna nawane wanan ba nawabane, batada burin daya wuce yanzu ta tsayarda miji tai aurenta.

 

 

Wayanta ne yashiga kara hakan yasa daga Mama har ita suka kalli wayan Alhaji Isyaka sunan daya bayyana kan screen din kenan, dan gajeren tsaki taja ta katse wayan tacigaba dacin abincinta, saida number yakirata kusan 4times duk Mama na kallonta tana katsewa sanan wayan yadena ringing yagaji yahakura.

 

 

Saida tagama ta wanke hannunta sanan tajuya ta kalli Mama ganin yanda Mama ke kallonta yasa tace “Mama” ahankali Mama tace “na’am Hassana” danturo baki tayi tace “tunanin me kikeyi?” Dan jim tayi saikuma tasauke ijiyan zuciya kafin takai hannunta takama hannuwanta tace “listen to me Hassana” tai shiru sanan tasake rage muryanta tace “after all that happen to you, I’ve supported you, nabarki all this while shekara biyu kenan da faruwan komi bantaba cemiki wani abuba because I understand you amatsayina na mahaifiyarki, I know u are afraid, you don’t want to make the same mistake dakikayi da, you want to take your time and marry the best man, kin wahala bakiso kisake wahala again but listen Hassana” Mama tai maganan ahankali takai hannuwanta takamo kafadunta tadaura kanta akan kirjinta tana shafawa ahankali hakan yasa itama tai lamo ajikin Mama tanajin kanta kaman yar yarinya tana tuna lokacin datake sweet 16, ahankali Mama tace “wani zubin idan ka tsaya jiran the best Hassana babu shine, Allah shikadai ne best and perfect, just look at all this men dake sonki ki samo wanda zuciyanki ta natsu da shi and marry, time is not on our side you are 38 yanzu Hassana, I think lokaci yayi dazakiyi making this decision on your own and settle down, rufin asirin y’a mace shine gidan mijinta kinji” gydama Mama kai tayi ahankali sanan tace “nagode Mama” gydamata kai Mama tayi tace “Allah miki albarka tashi kije ki kwanta kin gaji” tashi tayi daga jikin Maman sanan tadau wayanta tawuce sama Mama tabita da kallo saikuma ta girgizakai kawai.

 

 

Dakinta ta shiga ta chanza kaya zuwa hadaddun kayan bacci sanan tazauna akan sofa dake gado tabi table dinta na desktop dake jikin window da kallo yanda ta jejjera flowers da wasu sunma soma bushewa da wasiku akai wanyanda she has been getting tun kwana biyar dasuka wuce tarasa kuma wake aiko dashi dafarko tai tunanin Baban su Khalid ne amman hakanan kuma ranta yabata bashibane dan he’s not even romantic dazaiyi wanan tunanin. Dauke kanta tayi takalli kan gadonta inda ta jefar da jakan da gateman yabata, ahankali tamika hannu tajawo sanan tabude jakan flower ne aciki as usual da wasika, bata taba flower ba hannu kawai tasa tadauko wasikan sanan ta ijiye jakan ta shiga warware wasikan tashiga karantawa.

 

_ash color gyale sit damn pretty on your face takaiga har banson cire idanuna daga kanki, that lace gown Dear Lord who is the tailor? Cus I feel I need to see him and commend him akan kwarewanshi, you look breathtakingly beautiful……_ tsayawa tayi chak takasa cigaba da karatun jin yanda kirjinta ke bugawa data rasa maisa, kaman bazata cigaba da karantawa ba saikuma ta maida idanunta kan wasikan tacigaba.

 

_hannayenki da kafafunki kullum suna cikin lallen gargajiya da hakan namugun sani ina nitsewa cikin kogon sonki, wai bazakibar zuciyata tahuta ba Baby? Anyway nasan u must be tired now, u need to rest, and kidena tunanin wayeni danni bakowa bane face mai sonki, yauma zan ijiye miki number ta 07012345678 duk randa kika dauki number kika kira koda batai ringing ba hakan zai tabbatar min kin amshi soyayyata hakan zaikuma bani kwarin gwuiwa bayyana before your eyes dan kiganni. Ina sonki kaman na haukace saida safe_

 

Tadade tana kallon wasikan sai sake maimaita layin ina sonki kaman mahaukaci take, batasan mesa ba but har cikin ranta tundaga ranan da wasikun nan suka fara zuwa dudda anonymous ne batasan me aikowa ba but she finds joy in reading them koba komi mai turo mata wayan nan sakon baida aikinyi, murmushi tayi ta ijiye takardan ta kabar da flower tafada kan gadon sai bacci.

 

 

 

Wuraren 8 nasafe tafito cikin wata hadadden bakin Dubai abaya designer, babu kwalliya a fuskanta amman ka kalleta saika kara kallonta dan tai kyau, saukowa kasa tayi daga Baba sai Mama a dinning dan duka yaran gidan sunyi aure, karasawa tayi ta gaida Baba ya amsa mata yana murmushi sanan tagaida Mama sanan suka fara breakfast din, saida suka gama sanan Baba yashafa kanta yace “nina tafi aiki yan biyu sai anjiman ku” sai anjima Baba suka wuce suka tafi, tashi tayi tadauki jakanta tace “Mama bari natafi nima” center table din falon Mama tanuna mata tace “ga sakonki chan akan table gateman yakawo” dasauri tajuya takalli center table din ganin hadadden love envelope na wasika yasa taji ranta yabaci gakuma kunyan Mama dataji yalullubeta dasauri tajuya zata wuce tafita Mama tadan daka mata tsawa. “Dawo nan” juyowa tayi ahankali cikeda kunya ta saukar da kanta kasa, wasikan Mama tanuna mata tace “wuce kije kidauka” babu musu tawuce ahankali taje tadauki letter sanan tawuce tafice daga falon dasauri Murmushi Mama tayi tace “dudda basan waye wanan ba amman yanda yatasaki agaba da naci naji dadin hakan, maza irinsu kike bukata Hassana, Huwaile” tai maganan tana kwalama yar aikinsu kira dan zuwa kwashe kayan abincin.

 

 

Saida tabude motanta sanan ta shiga ta zauna taja kofan da karfi tarufe sabida haushi, ajiye jakanta tayi akan kujeran sanan tadaga letan tana kallo batare data budeba wani irin haushi da fushi na ruri akanta dan ta tabbatar Baba yaga wasikan sabida yanda yake afalo halama agabanshi maigadj yakawo, yaga envelope din tayi dafushi tabude tawani jawo wasikan cikeda fushi tabude……..

 

_Gaisuwa da fatan alheri to the woman my heart only beat for…karki fushi dani dan Allah, ina sonki sosai! Nakasa magance sonki araina! Dake nake kwana dake nake tashi, please save my life! Kibani dama na nunamiki kalan son danake miki, I love you dakomi da Allah ya halicceni dashi_

_Ina muradin jin muryanki amman banson na bayyana gabanki saikin bani izini, ki taimakawa rayuwata kiyi magana dani ko sau daya ce 07012345678

 

Sosai taji ranta yabaci samun kanta tayi dawani irin finciko jakanta tazaro iPhone dinta tashiga daukan number saida tadauka tass sanan tawani irin yarda letter tai dailing number tadaura wayan akunne tana tunanin irin rashin mutuncin dazatayi idan aka dauka, jin wayan tadau ringing yasa tawani irin gyara zama kaman baza’a dauka ba wayan ba dan tana gabda tsinkewa aka dauka shiru tayi bataree datai magana ba hakama dayan bangaren ba’ai magana ba, jin shirun yay yawa yasa taciro wayan daga kunnenta takalla ganin har lokacin wayan nakai yasa takomar da wayan kunnenta cikin wanan natsastsiyar muryan nata kaman ba itace ke tafarfasa yanzun nan ba tace “Hello” wani irin calm ijiyan zuciya taji ansauke da hakanan yasa taji gabanta yafadi bam! Dakewa tasakeyi tace “Hello” still shiru akayi ba’ace komiba, jin haka yasa tace “nasan koma waye kana jina, I just call danna gayama I don’t fancy sakonnin nan and whatever dakake turamin so koma wayene kai kadena please and stay away from me and my life” tana gama maganan kaman jira ake cikin wata irin husky voice da saida yay penetrating har heart dinta taji ance “please marry me Hassana am so in love with you……” wani irin faduwa gabanta yafara da inda kana tareda ita saikaji karan kuma tarasa maisa haka muryan dataji har brain dinta takejin muryan hakan yasa tama kasa koda kwakkwaran motsi, cikin wata kalan murya dake kara kashema mace jiki yace “zaki aure ni? I want to be your owner, I want you badly, please ki aureni” akai maganan ahankali kusanma shagwaba shagwaba zatace, yanda takame haka komi nata yakame ahankali ta lalubo dayan hannunta dake kan kujeran motan tadagashi yana rawa sosai sanan takai hannun kan wayan tadanna kashewa wayan ya katse sanan tawani irin yarda wayan da sauri takifa kanta kan siteri tana kokarin dawo da numfashinta daidai.

 

 

 

Rabonda zuciyanta yay skipping because of a man harta manta, ta manta when was d last time namiji yamata magana taji maganan har cikin zuciyanta, tamanta when was the last time namiji yamata magana taji komi najikinta yadena aiki….. knocking motar da akayi yasa tadago kanta adan firgice gateman ne yace “Hajiya lafiya kuwa tundazu nabude gate motan taki tashine” girgiza maikai kawai tayi tana key motan adan daburce taja motan dagudu sosai tawuce tafita daga gidan hartakai office tunani take waye mai muryan nan, waye guy din, muryan sounds familiar at the same time unfamiliar sounds strange, last maganan dayamata yashiga dawo mata, ahankali ta furta Murta……. saikuma tai shiru, murya chan kasa tace “he can’t read nor write ballema yay speaking English like that” tunanin hakan yasa takore tunanin aranta tabude office dinta ta shiga kasa komi tayi kawai ta ijiye jakanta ta kwanta kan coach din office din tarike wayanta tana jujjuyawa haka tarasa maisa tafara tunanin Murtala kuma but wanan ai ba number shi bane danhar yau takasa goge number shi, tana cikin tunanin wayanta ya shiga kara hakan yasa da sauri ta kalli wayan ganin Hussy ne yasa tai picking.

 

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment