Littafan Hausa Novels

Mata ta ce Hausa Novel Complete

Hotunan Yadda Ake Kwanciya Da Mace
Written by Hausa_Novels

Mata ta ce Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

MATA TA CE?

 

By

 

*Hajara L Sadeq*

 

@Miss Hajo

 

“`2023 GIFT

 

Marubuciyar

 

Auren wata Tara

Ni da Yaya Arman

Komai mukaddari NE

Najmat Abiy

KHADIJATUL SABREEN

And now

Mata ta ce?!

 

“`BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM“`

 

*ALHMDULILLAH Ina godiya Ga Allah s w a da ya Bani ikon Fara rubuta wannan kirkirarren littafin ba Dan Komai ba saidan farincikinku masoya insha Allah labarin Nan salo Ne da na tabbbatar zai amshi a zukatanku kyauta ne comment dinku da zazzafan sharhi kawaii nake Bukata Banyi alkawarin posting kullum ba Amma nayi alkawarin gamashi Cikin sauri insha Allah bazan gaji da gode Muku ba bisa ga zallar Soyayyar da ba haufi a Cikinta masoyan asali ku sani miss hajo Taku CE ta har abada ban yarda wani yayi amfani da wani Bangare ko juyamun labarin muddin Hakan ya Faru Zan dauki mummunan mataki*

Lalata Hausa Novel Complete

16✓02✓2023

 

 

🅿️…………..*1 & 2*

 

 

Babban Gida ne na Gani na fad’a da ya gaji da Kayan morewa.

 

Tankamemen gidane Mai dauke bangarori Da Basu wuce hud’u ba Parking space din gidan bazai Gaza Daukar mota sama da ashirin ba babban Gida ne Wanda fadar tsaruwarsa kanshi Bata Baki ne Daga Gani kasan mamallakinshi gidan ba kananun mutane bane.

 

Wata hamshakiyar dattijuwa ce fara sol jawur kallo Daya zakayiwa fatarta kasan ba karamun hutu take samu ba ,Yar gayu ce ta bugawa a jarida Saida da Ka kalleta kasan Bata hada ko Jini da hausawa ba Sanye take Cikin makeken lace na Alfarma danbareriyar sarkar gold Ce jikinta hannayenta Gaba D’aya Awarwarayen zinare ne Banda zobuna.

 

Zaune take ta hakimce a hadaddun cushion din dake shake da palourn na Alfarma Komai yaji Daga ganin furnitures din dakin kansu kasan dukiya Tayi kuka.

 

Pen da biro ne a Hannunta yayinda Y’ar aikinta Ke gabanta Tayi kasa da kanta Saida ta Gama rubuce rubucen kafin ta dago fuskarta da ba alamar fara’a a Cikinta ta kalli Yar Aikin ta ce”saura Kiyi mistake a abunda na rubuta Kije driver na jiranki”Cikin sauri ta Amsa Tana kakkarwa dan Tasan hajiya ba Wasa Bata rageka da komai ba ci sha sutura sadaka da sauransu Saidai Akwai Nuna Dagawa Batasan Hulda Da na kasa Da ita Dan zata iya rantsewa Bata tab’a ga fara’ar hajiyar tasu ba Tsawon shekarun ta biyu a gidan.

 

 

Kukan Jaririyar ko jaririn da ya kaurade gidan ne ya sanyata Saurin Tashi ba Shiri ta ce “Subahanallah kukan belah nake ji “har hadawa take da gudu wajen nufar Stairs.

 

 

Cikin sauri ta bude k’ofar tare da kutsa Kanta ba abunda ya Bata mamaki sai ganin yanda yarinyar ke tsala kuka a kusa dashi ya sadda Kai baiko motsa ba Cikin sauri ta Dauketa tare da sabarta a kaf’ad’a.

 

da Bata wuce wata shida zuwa biyar ba jijjigata ta Fara tare da Maida dubanta ga kanshi har Lokacin Bai dago ba Cikin Wace Irin Murya ta ce

 

“Aliyu ?Bai Dagoba haka Batasa ran zai Amsa mata ba “Zama Tayi ta na cigaba da jijjiga Babyn ta ce “Haba Aliyu me yasa Ka zabawa rayuwarka haka,meyasa bazaka cire mutuwar Nabila a ranka ba ,sanin kanka ne Wanda Ya mutu baya Tab’a dawowa Aliyu a Halin Yanzu Nabila ba abunda take Bukata sama Da Adduarka yawan zubda Mata hawaye da kake ba shine Soyayyar ba Addua da tawakkali shine babban abunda zaka Mata ruhinta ya kwanta Cikin salama Nabila ta Tafi Tafiyar da ba dawowa kamar yanda dukanmu Nan Jiranta muke Ka godewa Allah Da Nabila Bata tafi ba Saida ta barmana Jininta,ta bar Mana abunda Zamu dinga kallo muna Tunawa da ita”.

 

“goge hawayen da ya zubo Mata ta gefe tayi ita Kanta tasan Daina kukan Rashin Nabila abune Mai wahala a Cikin ranta bare Shi,Amma Kuma hakuri shine maganin Komai”A Hankali ya dago tare katon frame din dake hannunshi Wanda koni Banga meye ciki ba Gaba Daya fuskarsa ta jike da hawaye Magana yake so Yayi Amma kukan da Yake cinsa Ya kasa Koda furta kalma Daya Kyakyawane ajin Karshen chocolate colour ba fari bane Haka bazaka kirashi Baki ba Fatarshi kawai zaka kalla kasan ba karamun D’an hutu da gayu bane Dukda baya Cikin nutsuwar hakan gaba Daya fuskartsa zagaye take da kyakyawan sajen da ya Kara Mata kyau da haiba Karamun lips dinshi da Yake ja kamar Yana shafa Lipstick ba abunda yafi Daukar Hankali na dashi kamar girar sa ,Irin shape din da take dashi ko mace ta samu haka ta more Aliyu Handsome guy ne kyakyawa na bugawa a jarida kallo Daya zaka Masa kasan Bai haura shekaru Talatin Da ukku ba.

 

Ganin yanda Yake sikewa ne ya Sanya Momy saurin aje Bela da har Lokacin kuka take fridge ta Daga ta da dauko Ruwan sanyi a bottle ta zuba a glass cup din dake saman fridge din Tana nufarsa tare da sa Masa cup din a Baki a Hankali Take Daddabar bayansa Cikin sigar lallashi ta ce.

 

“calm down habiby,calm down sorry sorry”kawai take fad’a Ya na Shan Ruwan yaji zuciyarshi Tayi sanyi ganin yanda Yake sauke Ajiyar Zuciya ne Saida ya Gama Shan Ruwan Kafin ya dago Saurin goge Masa hawayen Tayi ta na sakar Masa Murmushi ta ce

 

 

“bansan Jarumi na Da rauni ba Ina son kullum zuciyar habiby na Ta Kasance jajurtacciya Ka kwanta kayi bacci Nasan Jiya baka samu bacci ba Oya Yaron momy”ta fada ta na sakinsa “Kamar yanda ta fada haka Yayi ya kwanta kamar wani yaro Kafin ta ja Masa blanket ta na rage gudun AC ta yo Saurin Daukar Kyakyawar farar yarinya Mai zubi sak da Yaran Larabawa ta ce

 

“Sorry Belah na Muje naji waya tabamun ke”Suna fitowa kasa Taci Karo da Yar aikinta Ta na Shigowa Da Kayan da ta aiketa Cikin hanzari ta ce “Jamila Yi sauri had’awa Bela Abincinta aidai kin sayo Komai “Eh Hajiya ta fada ta na nufar Aikin da ta sanyata

 

Cikin kankanin lokaci ta Gama ta na Mika Mata da kanta ta dinga feeding yarinyar har ta Gama Bata Wanda Da Kanta ta ture Kafin ta Bata peck a kumatu ta ce “good girl babyna Allah Miki albarka”zillo yarinyar ta Fara ta na dariyar jikinta ta na son Janyo Mata Dan kunnenta

 

“Jamila zoki amshi yarinyar Nan na shirya wajen Aiki Kar na makara”Tana mikata Taki zuwa ta sa kuka “OMG ta fada ta ce “jeki kawai mtswww na Rasa ubanme kikewa yarinyar nan da take gudunki Tak’i yarda Da nanny Kwata-kwata yarinya”Kafin ta harari yarinyar ta ce .

 

“kin Hana mommy zuwa wajen Aiki ko Keda dadynki”lafewa Tayi jikinta ta na luma babbar Yatsarta a hannu Batayi kokarin hanata ba Dan Bazata hanu ba tun ta na jinjira ta Saba Da tsotsar yatsa Kayan wasanta tasa aka dauko ta Baza Mata Kafin kace me Ta hau wasanta Hankali kwance ta na zullo daka kalli yarinyar kasan Akwai isashiyar lafiya tattare da ita.

∆∆∆∆∆∆∆∆

Dattijuwa Mata ce bak’a Irin black beauty dinnan da Bata haura shekaru arba’in ko k’asa da haka ba a duniya zaune take gaban Tap ga uban wanki tuli-tuli a gabanta Dirja kawai take Dan tun safe Take Aikin nan gashi har azahar Ta wuce Bata samu ta Gama ba

 

Jin saukar mutum a Bayanta ana shashekar ne ya sanyata tsagaita wankin tare da tsame hannunta Ta juyo gareta tare da son ta dagota ta kasa Cikin Murya Mai rauni ta ce “Nasreen me ya Faru eh y’an Mata na “Cikin shsheka da Muryar kuka ta ce.

 

“mama me yasa Mutane bazasu Daina Kirana Da shegiya mayya ba,mama me yasa bazasu Gane Ni kalar Tawa kaddarar ba Mama Ni Nace a haife Ni ba uba,ko Ni na zabawa kaina Hakan ,mama me yasa bazasu Daina Kirana da Hakan ba bazan Kara Komawa Makarantar ba Tunda Nan d’inma da muka dawo bamu tsira ba na Riga na hakura da rayuwar y”ancin da kike so inyi mama Saboda bani da Shi na hakura”.

 

“Ta karasa fada Cikin kuka Zazzakar muryarta da ita Tafi tsayamun a Rai,Daman da gaske Akwai masu Murya da ake Kira kamar Busar sarewa?na tambayi kaina.

Fara’ar ar matar ne Gaba d’aya ta dauke Cikin kasalalliyar Murya ta ce “Nasren Ki dago ki kalle Ni”Ba Shiri ta dago fuskarta Jab’e Jab’e da hawaye

” tsarki Ya tabbata ga ubangiji Sammai da kassai Mahaliccin wannan zankadediyar surar A Gaskiya Zan iya cewa Tsawon rayuwata da kallace kallacena bantaba Gani ko Jin labarin Akwai kyau Irin na yarinyar Nan ba Kyakyawa ce ta gagara misali na tabbata ko da Ita Za ace ta yo Kanta da kanta bata Isa ta bawa kyanta haka ba Dan Gaba Daya kyan ya wuce misali Da mizani ,Kyakyawace ajin Karshe Fara sol ba alamun ko tabo a fuskarta dara-daran magananta masu Dauke da zara-zaran gashin Ido Karamun bakinta ga dogon hancinta siriri round face Dinta Motsa bakinta Tayi Wanda Hakan ya Bawa dimples Dinta Daman lotsawa gabaki Daya kaga yarinyar Ko giyar wake kasha baka Isa Ka Sata a sahun jerin Hausawa ba sak balarabiya zaka kirata.

 

“na am mama”ta fada Cikin rawar Murya “Rasa Abun cewa Mama Tayi ji take Ita Kanta kamar Tayi kukan ,da Bawa Yana da ikon chanzawa Kansa kaddara da ta Jima da chanza Tata da ta y’arta tana Kama hannunta “muje nasan Akwai Yunwa tattare dake”shine kawai abunda ta iya fad’a ta na Jan hannunta Suka nufi wani karamun daki dake chan Bayan Babban gidan Saida ta Mike Naga Tsawonta da Kuma diri Masha Allah kawai shine abunda na iya fad’a.

Samira Irin ta, da ta Janyo tare da budewa bayan sun zauna lafiyayyar shinkafa da Miya ce sai kamshi ke Tashi ta bayyana Tuni Miyan Nasren Ya biya Daman Yunwa take ji janyo kwanan Tayi ta na Saurin Sa hannu

 

“Murmushin so da kaunar mamantata ta Mata ta ce “Ai Nasan Akwai Yunwa tattare dake ba Karin kirki kikai ba “Tana Kai Loma Ta ce “Kema Nasan haka Mama Tare za muci “ta fada ta na Kaimata itama a Baki”Dariya sukai gaba Daya Ina Mamakin kamar ba itace ta Gama kuka dazu ba……….✍️

 

 

_Hmmm ya kukaji salon a Cikin ranku zaiyi muku Dadi ko akasin haka_💃

 

Zazzafan sharhi ne zai tabbbatar mun Da amsuwar labarin a Cikin zuciyarku Idan kunjini gobe to naji sharhi da yamun ne idan kunjini shiru to banji abunda nake so ba Dan Kadan Daga Cikin aikina aje labarin dan Ban shirya dawowa kusa haka ba

 

 

_*Miss Hajo ce*

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment