Littafan Hausa Novels

Masifaffiyar Kauna Hausa Novel Complete

yadda ake tsara budurwa a waya
Written by Hausa_Novels

Masifaffiyar Kauna Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Masifaffiyar Kauna Hausa Novel Complete

_MASIFAFFIYAR KAUNA_

 

 

 

_DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI_

_Wanan novel din na kudine is 500 naira, amman yanzu free pages nakeyi, so you can share and share and share, idan kinason ki shiga group din this novel send 500 to 3107021073 Aisha Muhammad first bank, saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461, Thank you Fanmily_

 

✍🏾M SHAKUR

 

 

 

 

_MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_

 

Nida Malamata Hausa Novel

 

EPISODE 1️⃣

_FREE PAGE_

Tsaye take cikin shagon kafen komputa, tana tsaye agaban kantan shagon tana sanye dawani dogon maroon hijab daya kode sosai yana jamata kasa tana kallon mutumin shagon wani dogon matashi dake zaune kan kujera gaban system yana danne danne a system din, daga gani kasan aiki yake aikin ma hala na yarinyar dake tsaye ne sabida yanda take kallonshi kaman tana hango abinda yakeyi akan system din. Zare manyan oily idanunta kawai take tana kallonshi gabanta nafaduwa tana fargaban karta fadi waec dinan bayan tasan da kyar Baba yabiya mata kudin tazana, batason abinda zaisa bazata shiga koda dan FCE bane, tana cikin dogon tunaninne taga Matashin mutumin yatashi dagakan kujeran dayake kai yay wajen printer dan daukan paper data bullo daga printer, cigaba da faduwa gabanta yayi tana kara zare idanun kaman kwan lantarki, daukan paper yayi yakoma table din yadau katin waec dinta yazo gaban kanta yamika mata takardan yana murmushi yace “congratulations Fatima Zarah an tsallake Waec kinada credit guda shida, 6 credit gareki natayaki murna, Allah ya sanyama takardan albarka” yay maganan yana mika mata takardan, karban takardan tayi da sauri tana kallon takardan tanada C a maths English da sauran important topic din dayakamata science student nadashi, wani wani irin cool charming murmushi daya lobar da dimples dinta duka biyun tasake fararen hakoranta suka bayyana, batai wata wataba tawani irin zube akasa tai sujjada, dariya mai shagon yayi yajuya abunshi yakoma kujeran zaman shi yana dariya yace “wayaga su ustaziya Faty” tashi tayi tana murmushi tasauke yar jakanta da fatar jikin jakan dukta daye tsabagen wahala ta bude zip tasaka takardan da katin ciki sanan ta maida zip din ta zage sanan takalli mai shagon tace “nagode Yaya Habu” juyowa yayi ya kalleta ya kureta da ido ita bamata lurada kallon dayake mataba tajuya tafita daga shagon da saurinta tana tafiya takasa daina murmushi tsabagen yanda take murna kaman ba gobe, ahaka taketa tafiya ita kadai har zuwa anguwan su da yara suka cika layin suna wasa ana ihu ana wasa, wucewa tayi ta shiga cikin wani dan babban gida dakeda dogon zaure, gidan na hayane dake dauke da dakuna biyar, kowani daki falo ne sai uwar daka guda biyu, bayin gidan guda hudu biyu na wanka biyu na kashi General bayi, ga makwarara wajen wanke wanke ga dankararen kitchen dinsu inda kowa ke zuwa yay girkinshi, gidan yaci uban siminti kal kal kaman zaka taka ka zame.

 

_MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_

 

 

 

 

Babu kowa a tsakar gidan, ganin machine wayyo kudina agaban dakinsu yasa tagane Babanta na nan da sauri tai dakin nasu bayan ta gaida matan gidan datagani sun fito daga kitchen suka amsata ba yabo ba fallasa, sallama tayi ahankali ta shiga falon, falone mai dan kyau daidai, yaci ledan daki, ga kujeru masu kyau ga TV bango amman karami ga labule masu kyau da agogon bango bango dakin yaci fenti milk color, yarane adakin su hudu suna wasa, dan shekara sha biyu shine babban cikinsu mai suna Habib, sai mai binshi Ishak, saina ukun Bashir, ta hudu mace karama auta wacce dabo takeyi daga ganima ba’a yayeta ba mai suna Abida, yaran gasunan kai da kai kaman gwaranni farare kyawawa dasu, Babban cikinsu Habib dake sanye da kayan kanikawa ne ta kalla tace “Baba yadawo Habib?” gyadamata kai yayi yana tashi daga inda yake yace “eh yana daki shida Mamanmu” gyadamai kai tayi sanin idan Baba da Mama nadaki duk basa shiga ciki yasa tawuce dayan dakin dake facing dakin su Baba ta shiga katifa ce katuwar gaske akasa mai tudu takusan mmaye dakin sai wata yagaggiyar katifa yar karama da aka jefa adan space din gefen dakin dayarage kusada inda ganamasgon kayansu yake, kan katifar taje ta zauna ahankali tana murmushi tasake ciro takardan waec din tana kallo shikenan itama zata shiga University kaman su Hafiza, idan Baba yafito zata gayamai yabata wayanshi takira Mami ta tasanar da ita.

 

_MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_

 

 

 

Tana zaune akan katifar taji muryan Maman su tafito tadauki Abida dake kuka tana lallashi sanan taji tana tambayarta. “ina Zakiyya kai Habib”? Kafinma Habib yabata amsa daga ciki sukaji muryan Baban su yana. “haba Habee nafa hanaki kiran yarinyar nan Zakiyya ki kirata da Fatiman ta, wani irin zakiyya yarinya nada suna mai kyau haka sunan diyar Annabi kina chanza mata” cikeda masifa tace “kai wlh Baban Habibu korafin ka bayi karewa kana daki kunenka na nan kana sauraron abinda mukeyi, yanzu dai me acikin suna dakake wanan bala’in da ranan nan” tai kwafa ta zauna tashiga bama Abida nono. Sanin zata sake kiranta yasa ta mike kawai tafito da saurinta tazo gabanta ta tsugunna cikeda girmamawa ahankali tace “gani Mama” harara ta watsa mata tace “kina ciki kina jina kikai shiru, saida ubanki yasa bakine sanan zaki fito mai halin munafukai, sai shegen yawo da hijabi kaman matar boka, oya ga Abida goyata kije kitchen akwai ruwa dana daura akan murhu ki hada ki kaima Baban ki bayi yaje yay wanka ki daura abincin rana” gyadamata kai tayi ta karbi Abida da zanin goyon ta datake mika mata, zata goyata kan hijabin ta daka mata tsawa tace “wai bazaki cire hijabin nan ki goya yarinyar nan ba kosaikin sakamin ita kuka nasamu tai shiru, autar Tawa zaki kashemin da zafi”? Batace komiba tacire hijabin ta ijiye sanan tajuya mata baya sabida kunya ta shiga goya Abida, binta da harara Mama tayi, shegun nonuwan nan dasuke nema sufi karfinta take boyemata yarinya kullum niki niki da hijabi, goyata tayi sanan tafice daga dakin tai hanyar kitchen itakuma Mama tajuya ta shiga ciki, ledan biredi ta dauko tafito tawurgama Habib tace “acici, shabiyu batayiba amman ka gudo daga wajen aiki kaman bakaci na safe ba, yaro saici uwa an aikoka duniya ne dankaitacin abinci, gashinan raba kaida kanninka ka kora da ruwa ka kama hanya ka koma aiki kadaiga sai yanzu zama adaura sanwa, ka kwashi su Ishak ka ijiyesu amakarantan allon malam idi” tai maganan tana watsamai harara yaron na turo mata baki yana kunkuni tawuce ta shiga dakinsu batare data karabi ta kansu ba.

 

Kwance wani magidanci yake akan gado wanda duka duka bazai wuce 45 to 50yrs ba yana lullube da zanin gado yadaura hannunshi abayan keyanshi yana kallon fankan dake kadawa ajikin silin din dakin, kana ganinshi kasan yayi nisa a tunani gyara labulen kofan tayi ta tsige dan zanin datake daure dashi tahau kan gadon tadaga zanin gadon ta shige takai hannunta kan joystick din ta taba jin ya kwanta yasa ta kalli fuskarshi, turo baki tayi saikuma ta shiga mannewa cikin jikinshi sabida tasamu ta tayardashi sucigaba, cikin dan fushi yatureta kaman jira yake yace “Haba Rukayya ke ina cikin babban matsala bakida damuwa, kinjefani cikin matsalan keko ajikinki, kawai kin kirani gida baki barni wajen nemana ba kawai nazo gida naita miki wanan abin uwa banda wani aikin yi” yay maganan cikeda dan takaici, yace “wai sabida kinga ina sonki saisa kikemin hakane Ruka? Miliyan uku fa Rukayya ina naga hanyar miliyan uku yanzu iyye nanda sati daya zasu zo kuma, idan ban basu ba kinsan mizasuyi, kuma kekika turani naciyo bashin nan bakisa na tsinana komi dashi ba saidai kikasa nazo na kama wanan gidan hayan dayafi karfina, na saya miki kayan daki harda TV bango kikasa muka saya da fridge da katifun mu na daki yara da wanan rantamemen gadon dana siya miki kaman na amare, inda ace nai sana’a dashi da nasan inada at least wata hanyar biya amman bandashi kuma ko ajikinki, ke kawai daga safe har dare ki ganni manne dake kaman da tarayyan zamu biya bashi” cikeda kulewa tace “ya za’ayi kace ban damu da bashin da ake binka ba? Kanata wani cewa nasa ka kashemin kudin, naga aidai kaima kasai galleliyar machine wayyo kudina kana paparazzi akan titin gandujiyya, kai bakajin dadi yanda yan gidan nan suke bautamana mune yan uwan yan gayun gidan nan fa, yau taliya gobe farfesu, kullum ina jefar da ledan tsiren daka sayamin a tsakar gida suna gani, ga fridge ga TV, irin namasu kudin nan, kai bakaga yanda suke maula wajena ba, komi Maman Habib kai bakajin dadi? Babu abinda fa ba’a rokonmu, karka damu kudi zaizo zamu biya bashin sati daya ai akwai lokaci” cikeda fada yace “waini kika maida yaro Ruka? Tsafi zanyi dazan sami miliyan uku acikin kwana bakwai? Wai inama adashin dakika dinga karban kudin kina zubi kince min kwasa dubu dari biyu at least koshine nasamu nabasu wani abun” turo baki tayi tace “ni titini na kwasa nayi hidima da ita, nasoma yima Abida tari ne” wani kallo yamata yace “Abida ko Fateema”? Dauke kai tayi tace “nidai nasan kajini da kyau kakemin wanan tambayar Abida nace nafara ma tarin kayan daki, kana duba karkashin gadon nan zakaga abubuwan danasiya ma” wani irin kallonta yake saikuma yanisa yace “Abida dako shekara biyu batayi ba kokuma nace ko yayeta ba’ayibane kikema tari bama kiyi tunanin auren Fatima ba idan wani tsayayye yafito” dan gajeren tsaki taja tace “wanan batada farin jini har yanzu ko mashinshini batada shi, gwara Abida ma tun yanzu makota sun fara booking ma yaransu”

 

 

 

 

_MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_

6/23/21, 6:09 PM – My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

 

 

_MASIFAFFIYAR KAUNA_

 

 

 

 

✍🏾M SHAKUR

 

_MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_

 

 

EPISODE 2️⃣

_FREE PAGE_

Ganin yanda ya maida ita kaman TV yana kallo yasa tacigaba tace “Inda kaga kayan dana saya dabakai korafi ba Baban Habib Mom Afreen Pre-order collection na shiga fa, nabiya kankanin kudi tayomana order gangariyan kaya tundaga kasan waje, wallahi bantaba ganin irin design din tukwanen da flask din dana sayaba har yanzu, wasu irin designs ne nadaban dan kayan danama Abida order babu irinsu agarin nan sai agidan masu kudi, ko masu kudin ma sai daidaiku, babu abinda zancema Maman Afreen sai Allah ya sakamata da alkhairi, gashi order kaya awajenta babu tsada, farashinta nada mugun rahusa kaga kaya kaman baka akayi kyauta, jira nakema wasu kudin su shigomana mukara yo order kaya daga kasan waje daga wajenta inyaso saimu bude shago ko Rabinraina mudinga saidawa” tunda tafara maganan kallonta kawai yake cikeda takaici matarnan tasashi amatsala Babba amman kuma ko ajikinta, ita batasan rigiman dasuke cikiba sai surutun banza takemai, abinda ke kara cimai rai yanda bai iya mata fada kaman an kullemai baki. Ganin yanda yake kallonta bayako kyaftawa idanunshi sun cikada hawaye sosai yasa sai jikinta yay mugun sanyi, ahankali tadaura kanta kan kirjinshi tana shafa kan nonon shi da hannunta tace “kayakuri Baban Habibu kaji, komi lokacine zaizo ya wuce kaman ba’a yiba, kudi zaizo In sha Allahu kaji zamu biya bashin nan kanka farau, ai ba’a kanka aka faraci ba, nidai kawai na hanaka karka sake kaje kana dako salon yan gidan nan sugano mekakeyi sudinga min gori, karka damu zan maka tunanin abu kaji” gyadamata kai kawai yayi sanan yadan tureta yatashi ya zauna yana mika hannu yana daukan jallabiya shi dake gefen gadon yasaka sanan yasauka daga kan gadon, dogone fari fat kana ganinshi kasan duka yaran falon nan dashi sukai kama, Maman cema baka, binshi da kallo tayi dudda taji haushin yanda baimata abinda takesoba amman saita share tace “muje naraka bayin daganan naduba yarinyar nan naga girkin” baice mata komiba Hijabi tadaura kan daurin kirjin dake jikinta suka fito tare, matan gidan na tsakar gida tana fitowa tawani dagakai kaman bata gansu ba tabi bayanshi da sauri dan yamata nisa kanshi akasa bai masan ko akwai mata a tsakar gidan ba danshi baya kallon matan wasu yay hanyar bayi itakuma kawai sai tai kitchen koda ta shiga gani tayi Abida ma tayi bacci itakuma Fatima na fifita wutan wutan daya kama dan har sanwan ma natafasa bama tasan an shigo kitchen dinba sai fama takeda wutan idanunta sunyi jajir sabida hayaki, balla mata harara tayi tace “inkin gama ki fifita wutan kije ki kwantar da ita adaki” kai kawai ta gyadama Maman nasu dan batason tace wani abu takara kwafta mata zagi, juyawa tayi zata tafi saikuma kawai tai tsaki tazo ta bayanta tace “bani y’ata” takai hannunta zuwa saman kirjinta zata kwance zanin runtse idanunta tayi amugun firgice hakan yasa Mama ta tsaya tana kallonta da mugun ban haushi saikuma ta dakamata tsawa tace “dalla kwantomin y’ata kina rurrufe idanu kaman mai surkulle” har wani ajiyan zuciya ta sauke tace “uhn to” sanan ta kwance Mama ta karbeta suka fita itakuma tacigaba da girkin.

 

_MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_

 

 

Wuraren 3 tagama girkin tadauki tukunyar a wata tray tafito tai dakinsu dashi Babansu tasamu zaune kan kujera yana rikeda remote Mama zaune gefenshi da alamu abincin duk suke jira tana ganin Babanta tasake sakin murmushi da kana ganinta kasan daga zuciyanta yake, harara Mama ta watsa mata tace “Malama ajiye tukunyar ki kwaso kwano na zubama Baban ki” da sauri Baba ya watsa mata mugun kallo yace “bazaki bar yarinya ta hutaba” ya kalli Habib daya shigo yayi kini kini da rai sabida yunwa yace “wuce ka kwaso kwanuka azuba abinci” da sauri Mama tace “wai sai insa abu kanuna agaban yara ban isaba” ahankali Baba ta hanyar rage murya yace “tagaji ne tahuta, tanada kannai intai girki sai asaka kannan suyi wani abu ko” Mama zata kara magana ya kalli Fatima datake tsaye inda take kanta akasa sai zufa take yace “Zahra’un Baba ya jarabawan andubo”? Da sauri tadagamai kai tana murmushi tana kallonshi kana ganin yanda take kasan yarinyar na mugun son mahaifinta, shima murmushi ya sakin mata cikeda sonta yace “dauko takardan nagani” da sauri tai uwar dakin su Mama tabi bayanta da harara daidai lokacin Habib yakawo plates karba tayi ta zuzzuba musu abinci tazuba na Fatima kadan ta ijiye agefe har Baba zaiyi magana saikuma yayi shiru kawai baice mata komiba, yadau nashi yasa cokali ya shiga ci murmushi kawai yayi shi kanshi yana alfahari da Fatima wajen girki danko Ruka bazata nunama yar karaman yarinyar nan yanda ake girki ba. Fitowa tayi daga dakin hakan yasa tun kafin ma takaraso ya ijiye abincin shi agefe yamika mata hannu tasamai takardan wajen kafanshi yanuna mata yace “zauna ga abincin chan dauko kici” kallon abincin tayi saikuma ta kalli na kannenta ba tace komiba Allah ma ya taimaketa batada wani cin hauka data mutu da yunwa, daukowa tayi tazo ta zauna kusada mahaifinta shikuma yana duba takardan murmushi kawai yayi ya gyadakai yace “uhmm Masha Allah wanda baida Fatima baida mene…..” dan murmushi tayi murya chan kasa mai shegen zaki tace “sa’a” bata fada da karfi ba sabida mamansu, murmushi Baban yasakeyi ya kalli Maman su yace “yarmu tacinye waec tass” sanan ya kalli Habib dake kallon takardan yanacin abincin yace “kagani haka nakeso kaima kadinga kokari a makaranta kaine namijin gidan nan, babanmu amman kullum na bayan kashi kake, abu daya kawai ka iya shine son abinci” daure fuska tamau yayi baice komiba Baba yataba kan Fatima dakecin abinci tana murmushi yace “yanzu sai kwaleji ko Zara’un Baba, lawyer gidan nan, Allah shi albarka, Allah ya sanya ma certificate din albarka yanzu dazaran wani tsayayye yafito sai aure ko” wani irin kunya ne yakamata da sauri ta tashi tadau abincin ta tai dakinsu, kyalkyacewa da dariya Baba yayi Habib natayashi, Baba ya girgiza kai kawai, tabe baki Mama tayi tace “yartaka da Batada mashinshini gwarama kadena tunanin aurenta yanzu dan ko almajiri batada shi ballema mutumin arziki” sosai maganan ya sosama Baba rai hakan yasa yace “aure lokaci ne Rukayya, yana zuwa akeyi kodako kana coma ne, dududu ma shekarun nata nawane? Ko ashirin bataiba dan haka kisha kurumin ki mijin Zara’una na nan tafe ko Habibun Babanshi” da sauri Habib ya gyadama Baba kai yana murmushi yace “eh Baba wlh inaso inga muma munyi biki kaman gidansu Mansur yayar su tai aure, nima inaso Ya Faty tai aure” murmushi Baba yayi yakai abincin shi baki yana sauraran labarin da Habib ke basu na bikin yayar abokin shi. Saida yagama tsaf sanan yatashi yakalli Mama dake bama Abida data tashi nono yace “bari nafita nema saina dawo” yataba kafan Abida dakeshan nono yace “Yan Matan Baban ta yauko kallona ba’ayi sabida an sami Mama” ture hanunshi tayi dagakan kafanta dan bata kaunar abinda zau hanata shan nonon nan, dan dariya yayi yace “au abun na fadane, zanga mai kawo miki cizi anjima kiyita shan nonon ki” ya kalli Mama yace “natafi” cikeda kuncin rai Mama tace “a dawo lpy” fita yayi rikeda takardan a hannunshi yana gungura machine dinshi ya kwalamata kira. “Zara’u” daga daki ta amsa “na’am Baba” cigaba da gungura machine dinshi yayi zuwa zaure, fitowa tayi sanye da hijabi kanta akasa tawuce tafita daga falon tai hanyar zaure Baba tagani haryay parking machine din awaje ya shigo zauren murmushi yamata yamika mata takardan waec din yace “Allah yamaki albarka yabaki miji nagari kinji, wanda zai soki sanan yakula dake sama dani, kome ake miki kicigaba da hakuri dudda nasan ke yarinya ce mai hakuri ga kunya, ga kawaici wata rana sai labari kinji” gyadamai kai tayi ahankali, ahankali yace “kin koshi da abincin data zuba miki”? da sauri ta gyadamai kai tace “nakoshi wlh Baba” shiru yayi yana kallonta kaman wanda yake wani tunani ganin yanda yake kallonta yasa saitaji tadamu tace “Allah Baba nakoshi kasan banamaka karya ko” sosai idanunshi sukai ja yace “nasani Zahra, bakimin karya na shaidake da wanan y’ata” hannunshi yatura a aljihu yaciro last 1k dayake da ita, mika mata yayi yace “gashi ki boye kidinga kashewa ahankali, kome kikeso ki dinga siya kinji yanzu banda kati awaya, nadawo zan loda kati saina baki ki kira Babarki ki fadamata sakamakon waec dinki kinji” karban kudin tayi tareda dan dukawa tace “nagode Baba Allah ya saka da alkhairi yakara budi” sosai idanunshi sukai jajir yace “wuce kitafi hudu nayi ki tattara kanninki kuwuce islamiyya kinji, ki dage dakaratu ilimi shine adon y’a mace” gyadamai kai tayi tace “Tom Baba” kanta yashafa da hannunshi yadan rungumota side dinshi yace “kiyi addu’a Allah bama babanki kudi, zan sayamiki waya tunda kema yanzu kin dawo budurwa kaman kowace budurwa, da sababbin zannuwan da takalma kinji, da kayan kwalliya” murmushi tayi akunyace tace “Baba karka damu komi lokacine, Allah ya azurtaka da arziki na halas katafi karkai latti” tai maganan tareda juyawa da sauri batason ta nunamai kalamanshi sun tabata, tsayawa yayi shima yabita da kallo harta shige ciki, maganan da Ruka tamai dazu ya sosamai rai ba kadanba kuma deep down yasan da gaskene Zara batada ko mashinshini guda, kuma laifinshi ne yarinya batada kayan arziki tana mace kuma budurwa datake tasawa yanzu amman kayanta sunfi name abincin saidawa kodewa, hijaban ta biyu kacal da maroon dawani mai ruwan toka sun kode harsun fara ja akai tsabagen kodewa, batada wani takalmi na fita sai silifas, kullum fuskarnan nata fayau babu komi aciki yaza’ayi saurayi zai gani ya yaba, koya sami kudi yace zai mata Ruka tahana, saisa yakeson yarinya yanzu ta shirya taje wajen Babarta hutu amman yasan Ruka bazata bariba, ganin dogon tunanin dayake yasa kanshi yafar*a sarawa yasa yajuya yafita kar hawan jininshi yatashi, machine yatada yafice daga anguwan gabaki daya.

6/23/21, 6:09 PM – My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

 

 

_MASIFAFFIYAR KAUNA_

 

 

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_

 

 

 

✍�? M SHAKUR

 

 

EPISODE 3️⃣

_FREE PAGE_

Koda takoma daki bataga Maman nasuba hakan yasa ta shiga dakinta ta ijiye komi taboye kudin da Baba yabata sanan tafito tatattare falon inda sukaci abinci ta share tafita da kwanukan ta wanke sanan tadawo ta kunna turaren tsinke afalon ganin ana kiran la’asar yasa tadauro alwala ta shigo tai salla sanan ta shiga dakinta ta sanya Ash color hijabin ta har kasa dan shine na islamiyyan su sanan tadauki jakar islamiyyan tafito, gaban dakin Maman su taje ta tsaya tai sallama ahankali, daga ciki maman tace “lafiya kin isheni da sallama yarinya saikace rainon mayu” batadamu da maganar ba dan inda sabo tasaba, ahankali tace “zantafi islamiyya ne Mama natafi”? Ihu tamata daga taciki tace “au so kike ubanki yazo yace nahanaki zuwa islamiyya ko uwar shairi da kinibibi wuce ki bacemin daga gaban daki, mayya mai neman rabani da mijina” juyawa tayi ahankali tafice tai waje da sauri sauri take tafiya kaman mai jiran wata, tayi nisa sosai tahango wata yarinya kana ganinsu kaga sa’oinnin juna itama tana sanye da Ash color hijabin kaman nata tana tsaye karkashin bishiya tun kafin takaraso wajen tace “wlh kika samu latti Fatima saina rama dukan lattin da za’a min ajikinki” dan dariya tayi ta bangaje mata kafada tace “dalla chan bamuyi latti ba har yanzu hudu bata cikaba” binta da sauri yarinyar tayi tace “au hakama zakice”? Murguda mata baki tayi tace “eh din” dariya yarinyar tayi tace “tokijirani sai sauri kike FatynBaba” juyowa tayi ta tsaya chak tareda rike waist dinta tace “ohkay ke Maryam dinan kin cika wayau, sabida muyi lattin kirama dukan ajikina ko saisa kike cewa najiraki” dariya Maryam tayi takaraso inda take tareda mika mata wani leda tace “gashi nakine” da sauri ta karba tabude taga sabon hijabin islamiyyan sune Ash wanan ma anyi dinkin mai hula mai kyau juyowa tayi ahankali ta kalli Maryam din dake kallonta, murmushi tayi ta bangaje mata kafada tace “ke dalla common, Babanmu nacema hijaban mu na Islamiyya sun tsufa, shine yace nazo shago anjima a aunani a dinka mana, shine naje kinsan yanada yadin hijabai masu kyau, na zaba yabama yaron shagonshi ya dinka mana dinki daya, nima bansa nawa bane sabida nasan bazaki saka naki yauba, sai gobe zamu saka mu fasa islamiyyan tareko” gyadama Maryam dinkai tayi saikuma ta rungumeta kawai, da sauri Maryam ta tureta tace “dalla ke dadina dake son jiki awaje zaki wani rungumeni sabida hijabi, har yanzu maganana nanan kikasa mukai latti saina rama dukan ajikinki” Maryam tai maganana tana dariya taredayin gaba, share hawayenta tayi ahankali sanan tabi Maryam din da sauri tace “toni kijirani” haka suka dinga tafiya suna shirme cikin ikon Allah koda sukakai ba’a fara taron latti ba hakan yasa suka wuce ajinsu direct aka fara karatu.

 

 

 

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_

 

 

Karfe shida aka tashesu daga islamiyan, saidaa ta tattaro kansu Sadiq dasuka taho tareda Habib sanan suka fito Habib yay gaba da kannin nashi itakuma suna jerowa tareda Maryam suna hira har sukakai wajen bishiya suka tsaya Maryam tace “kinga yanda Malam Sani keta kallonki kuwa dakike biyamai karatu” dan hararanta tayi tace “kallo, kallon lafiya, ni banmasan anyi hakaba kin iya sa ido Maryam” murmushi kawai Maryam tayi tace “nidai kidinga saka nikabi, kyanki yay yawa yarnan” hannu takai zata kwadama Maryam din duka ta kwashe aguje tadau hanyar layinsu itakuma tacigaba da tafiya tana dan murmushi, ana magrib suka shiga gida, gaida mutanen gidansu tayi sanan tai dakinsu Mama tasamu afalo zaune tana bama Abida nono tana ganinta tace “wuce kije ki kada miyan dake wuta” dakinsu ta shiga ta cire hijabin islamiyyan ta tasaka maroon tafito zatai kitchen, da sauri Mama tamata ihu. “sokike kije ki kone a kitchen Babanki yakusa cinyeni, wuce dan ubanki kicire hijabin nan bansan ubanwa kike boyema yan kirgan dangin nan dakika faraba” cikin kunan rai Habib yace “waike Mama kullum saikin ma Ya Faty fada dawani wai kirgan dangi mehaka dan Allah, ni wlh kidena damun Ya Faty” cikin fushi ya kalli Fatima da kanta kekasa yace “Ya Faty jekiyi da hijabin ki kinji ai Malam yace bakyau mace na yawo haka ba lullubi” mugun dundu Mama takaimai abaya tace “kai dan ubanka ko ubanka bayaja da maganata balle kai yaushe aka haifeka? Duka duka shekarunka sha biyu kake gayamin magana eh dan ubanka” cikin kuka da fushi yace “to meta……” da sauri Fatyma tajawoshi taredakai hannu bakinshi ta taushe tahanashi magana dan Allah ya zuba mata son kanninta kaman me, cikin fushi Mama ta ijiye Abida kan kujeran ta tashi tace “ni uwarka kakema rashin kunya kan wanan yarinyar eh Habibu” da sauri Faty ta tura Habib din bayanta tace “kiyakuri Mama dan Allah” gauramata mahaukacin mari Mama tayi da saida yasa tai layi kaman zata fadi sanan ta fizgota da karfi ta kumata da bango tareda shake mata wuya tace “ni zaki juyawa yarana akaina? Yaran dana haifa zaki batamin su? Harda kama Habib kina boyewa a bayanki irin ga danki dinan ke uwarshi wlh yauna lahira saiya fikijin dadi” tai maganan tareda fizgo wayan TV tashiga lafta mata tun tana daurewa bata ihu tahau kuka sosai tana ihu tana yakuri Mama, Habib na tsaye gefe yana kuka sosai kaman ranshi zai fita, duka yaran harda Abida ma saisuka hau kuka ganin ana dukan yayansu ga Mama sai uban ihu take tana jibgarta kaman daman tana tikeda ita, wata makociyarsu ce dake shiri da Maman tashigo tana zuwa rike Mama tayi tace “ya isa hakanan Maman Habib” cikin kumfan baki tace “barni na kashe yarinyar nan nahuta Zainabu, yarinya tarabani da mijina, mijina saiya hanani kudi yabama wanan makiran, komi ita komi ita, yanzu kuma nema take tarabani da yarana, to wlh bata isaba saina kasheta nakashe banza taga idan da abinda ubanta zai iya yayi kuma zama daram sai yanda nayi da uban nata datake takama take tunkaho dashi” tai maganan tana haki sosai kaman zuciyanta zai fito baki, kallon Fatima dake duke tana kuka sosai tayi kanta akan guiwanta tace “kekuma tashi kibar nan kije kiyi girkin, kafin natayata kara miki algunguma mai kama da larabawan jahannama” ahankali tashiga tattaba bango tamike tsaye da kyar jikinta har kyarma yake tsabagen wayan wutan datasha sanan tawuce ta lallaba tafita daga dakin tai kitchen, saida tafita sanan matar tace “kiyakuri kedai kiyita addu’a Allah bata miji ta tattara tabar miki gidan nan ki sakata ki walada mijinki” da sauri tace “ina Allah yabata, yarinya sai bakin jini gadon uwarta, ko mashinshini batada shi” da sauri matar tace “duk kyan nan nata” da sauri Maman Habib tace “kyan dan maciji ne, tayi gadon bakin hali ina zata samu wanda zai kwasheta yakaita gidanshi amatsayin mata”? “adai dinga hakuri Maman Habibu amman dai ina bayanki kitashi tsaye karki bari tabata miki yara” murmushi tayi tace “nagode Maman Zainab, bari ta sauke abinci zan aiko miki dashi, wlh nagaji dacin shinkafa taliya kullum yau kawai nai marmarin tuwon shinkafa da miyan taushe da kan rago zai aiko miki dashi nariga nagama miyar” cikeda jin dadi har wani sude baki Maman Zainab take tace “Allah bar mana Maman Habibu kap gidan nan babu kaman ki, godiya nake, bari naje to”, fita tayi tana karamata godiya, itakuma Mama ta kalli Habib dake kuka har lokacin tace “zonan” zuwa yayi yazauna agabanta shafa kanshi tayi tace “kaga kasa nadakeka a banza ina ruwanka da wanan shegiyar nace muku ba yar uwarku bace, ya isa dena kukan jedaki kadauko biredin dana ijiye muku kaci kaida kanninka” ko kallonta baiyiba yatashi ya shige dakinsu fuuuu, tabe baki tayi tadauki Abida tace “mayyar nono ungo kafin ki kashemin dodon kunne” .

 

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_

 

 

Taci kuka harta godema Allah sanan tai shiru, babu indabaya mata ciwo ajikinta haka adaddafe ta kada miyan ta kashe wutan tadaura miyan atray tadauka tana tafiya ahankali tawuce daki, har gaban Maman takai tukunyar ta ijiye ahankali murya chan kasa tace “Mama gashinan nagama” ko kallonta Maman batayiba hakan yasa ta dafa kujera tamike tsaye da kyar zata wuce dakinsu Mama tace “ubankine zai dawo daga wajen neman dayaje yakawo miki kwanukan daza’a zuba abincin”? Girgiza kai tayi tawuce takwaso kwanukan da Mama tazuba tuwon already, miya Mama ta zuzzuba ta mikama yaran sanan tadau kwanonta ta zuba miya kafin tadau kwanon ta wurga mata da tuwon da miyan suka bare kan hijabin ta ihu tayi sosai dan yadan tabamata jiki ta tashi tacire hijabin tana kuka sosai, hararan ta Mama tayi tace “bacemin daga gani jaka kawai mai bakin jini” dakinsu tawuce ta shiga ta ijiye hijabin awaje daya ta kwanta akan gadonta jikinta na kyarma har lokacin tana kuka ahankali, Habib najinta amman yakasa cemata komi but bakaramin tausayinta yakeji ba, tayi kuka tayi kuka ahaka bacci yay gaba da ita batai magrib ba balle ma isha’i.

 

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_

 

Wuraren goma da rabi baba yashigo lokacin duka yaran sunyi bacci lekasu yayi ganin duk suna bacci yasa yasaki labulen yawuce dakinsu zaune yaga Mama tana kullama Abida datai bacci pampers yace “kowa yaci abinci ko Ruka” fuska adaure tace “jeka tashesu katambaye su mana” murmushi yayi yace yau yan rigiman na nanne, kulanshi yaja yashiga cin abinci batare daya karace mata komiba saida yagama sanan yay yan abubuwa kafin yarage kayan jikinshi ya kashe wuta yazo yahau gadon ya kwanta yay shiru, juyowa tayi ahankali tace “kasamo wani abu?” girgiza mata kai yayi yace “duk wayanda nake tunani zasu iya bani bashin kudi basu baniba, lokaci na gudu Ruka ya zamuyi bakiji yanda kaina keciwo ba wallahi” tabe baki tayi tace “karkaje kajama kanka jininka ya buga abanza duk yanda kaddara tasamu mutum haka yake daukanta” shiru dukansu sukayi basu sake cewa komib*a kowa da abinda yake tunani aranshi……

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment