Littafan Hausa Novels

Maryama Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Maryama Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

MARYAMA

 

 

“`Daga alƙalamin

“`Mrs Ibrahim“`

 

“`MARUBUCIYAR

RAYUWAR MARIYA

MUGUN ABOKI

AND NOW

MARYAMA“`

 

 

“`Ina ƙara godiya ga Allah da ya bani damar fara wannan book ɗin,Allah ina roƙan ka yan da na fara lpy Allah kasa nagama lpy,abinda na keson isar wa zuwaga Al’umma Allah ka da famin,Allah ka ƙara ɗaukaka alƙaminmuAmeen

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

Badi ba rai Hausa Novel Complete

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

“`بسم الله الرحمن الرحيم“`

 

 

Page 1&2

 

 

“”””””””””””Ƙauyen Fadawa, ƙauye ne da ke Jahar Yobe, gari ne wan da ya ke da albarkatu kala-kala ƙaramin gari ne wan da duk abinda ya faru agidan mutu kowa sai ya je, babu ruwan su suna da haɗin kai sosai da sosai.

 

 

 

Wani ƙaramin gida na shiga wan da kana gani kasan cewa masu gidan bisa alama sune masu halin garin, ɗaki uku ne agidan sai banɗaki sai kitchen sai filin tsakar gidan.

 

 

 

Sallama aka yi wata kyakkyawar mata ta amsa “Mairo kin dawo?” cewar wannan matar da ke magana a Mairo.

 

 

 

“Eh Inna na dawo” cewar Mairo, “yauwa sannu ga abincinki can aɗaki ki je ki ɗauka idan kinci kizo ki hura mana wuta”, “to Inna” bata kuma ce wa komai ba ta wuce ɗakin.

 

 

Zama Inna ta yi akan kujera ta ɗauko gari tana tankaɗewa, Mairo fitowa ta yi tace “Inna ai da kin bari nazo nayi yanzu zan gama dama ba yunwa na keji sosai ba” cewar Mairo.

 

 

 

“Ke kam bakya gajiya da aiki kije ki huta kinga yanzu kika dawo Allah ya in yaso sai ki mana girkin” cewar Inna.

 

 

To shikenan Mairo ta amsa tana murmushi.

 

 

*WACECE MAIRO*

 

Mairo yarinyar ce mai shegen kyau wanda iya haɗuwa ta haɗu tana da fari fiye da tunanin mai karatu tana da manyan ido wanda idan ka fiye kallonta zasu baka tsoro tana da gashi har gadon bayanta, su kansu iyayan ta suna yaba kyan yarinyar.

 

 

Ita ɗaya ce awajan iyayen ta Mahaifinta Malam Ahmad wanda suke ƙira da Baffa da Mahaifiyarta Hafsa wanda suke ƙira da Inna mace ce kyakkyawa, da ya ke su d’in fulani ne kana ganinta haka Mairo suna kama sosai gata bul bul abinta kamar ƴar birni sosai suna ji da Mairo shi yasa duk abin da ta keso za tayi, tunda su kai aure wajan shekara 30 ita ɗaya Allah ya basu ita ma sun ɗan jima kafin suka haifeta shi yasa su ke ji da ita, amma wani lokacin Mairo akwaita da wauta irin ta ƴan fari ga ta da barkwanci, wajan karatun addini suna kulawa da ita haka ita ma boko, da ya ke akwai ƙaramar makaranta agarin Mairo tana j s 2, sosai tana karatu, sa bo da Allah ya bata ilimi sosai, su kansu Malaman suna yaba ƙoƙarinta.

 

 

 

*Mun dawo labari*

 

 

*************************

Bayan Mairo ta fito girki ta ɗaura komai tana yinsa cikin nutsuwa shi yasa komai nata na daban ne, ta gyara gidan tsaff ya sha shara.

 

 

 

Sallama aka yi, Mairo ta amsa “sannu da zuwa Baffa” cewar Mairo, “yauwa ƴar Baffa sannu da aiki”.

 

 

Inna ce ta fito daga ɗaki tana yi wa Baffa sannu da zuwa, cikin murmushi ya amsa mata, ɗaki suka shiga Mairo ta ci gaba da aikinta.

 

 

 

Bata ɗau lkc ba ta gama komai, zama tayi kusa da Baffa sai da ya gama cin abinci tsaff tace “Baffa ya kasuwar dai?”, “kasuwa tayi kyau sai dai muce Alhmdllh” cewar Baffa.

 

 

 

“Yauwa Baffa ka ce min idan ka dawo zaka ta fomin da jan baki irin na ƴan birni sa bi da nima na shafa nayi kyau” cikin ya nayin shagwaɓa ta ke maganar.

 

 

“Haba Mairo wai shin ke ba za ki daina wannan wautar ba, ya kamata ki san fa yanzu kin girma” cewar Inna.

 

 

“Wayyo Allah na Baffa kana jin ta ko? wai na girma ni wallahi ban girma ba wayyo Baffa, ta daina ce min na girma” cikin kukan shagwaɓa Mairo ke maganar.

 

 

 

“Kiyi shuru ƴar Baffa dan an ce kin girma ai ba wani abu ba ne ko? ya kamata ki dinga jin maganar Innarki” cewar Baffa.

 

 

“Baffa ai ina jin maganarta, ba kai ne ka cemin idan mutum ya girma aure ake masaba, ni kuma wallahi babu wanda zai min aure dan haka kar wanda ya ƙara ce min na girma” cikin ya nayin shagwaɓa ta ke maganar.

 

 

 

Sai a lkcn Baffa ya tuna ya taɓa mata magana akan hakan can ya ce “ehh haka ne amma ke kam ba yanzu zan maki aure ba sai kin zama Babba sosai” ya faɗa ya na dariya.

 

 

Da sauri ta kai masa rumguma, tana ihun daɗi ita a dole ya ce ba zai mata aure ba, Inna kam abin duniya ya isheta sam Mairo ba ta jin kunyar rumgumar kowa, ita har yanzu bata san ta girma ba.

 

 

 

“Shikenan tashi ki shiga ciki ga alawa na siyo maki sai aje ayi ta sha” cewar Baffa.

 

 

 

Tashi ta yi tana ta ƙunƙuni wai ita adole Baffa ya koreta.

 

 

 

Comments shi zai nuna kun karɓi book ɗin, idan banga comments bazan sake typing ba

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment